Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[10/9, 8:52 AM] Zeetty: [10/9, 8:46 AM] Maman Hanan: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE

Page 1-2


*Assalamu alaikum barkanem be nyalomare midon yela on nanai beldun kubaruji am*


*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka dafatan zakuji dadin wannan labarin*





*Wannan labarin nawa kagaggen labarine banyishi dan cin zarafin wani ko wata ba basira tace ba taki/taka bace sarrafashi ta kowane hanya zan dauki mataki aguji aikata hakan*

*Idan yayi dai-dai da rayuwarki/ka ayi hakuri Arashin sanine*



*DAN UWA RABIN JIKI*
Ubangiji Allah yagafarta maka hakika nayi rashi wanda bazan ta6a iya kankaresa daga raina ba harsai ranar da tawa tazo gareni,
Na jijjiga nayi kuka asanda labarin mutuwarka ya riskeni Allah yasa mutuwa hutuce a gareka Samarin Aljanna Allah yabamu hakurin Rashinka *Ibrahim Sulaiman* bazan manta dakaiba dan kana d'aya daga cikin wanda kake bani Kwarin gwiwa akan fara rubutun littafi Allah ga bawanka nan ya Allah kasadashi da rahamarka muma idan tamu tazo Allah kasa mucika da imani *We love u but Allah love u more* Dr.Sule family munyi rashin dan uwa mai zumunci
Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Garin yola kowa yasan mazauna wannan garin mafi akasarinsu fulani ne.

Anguwar DAMARE yan matane da samari yara da manya sunyi cincirindo a gurin diban ruwan Borehole da ake siyarwa bokitin sharon Naira Goma bokiti uku Naira ishirin,
Yawanci anfi zuwa gurin ranar da aka kwana biyu babu ruwa kasan cewar mafi akasarin wadanda suke siyan ruwa a gurin Masu saida ruwan jarka ne wanda suke amfani da kuran ruwa (amalanke)
Idan kaga wata yarinya ko yaro sunzo siyan ruwa gurin toh ba shakka iyayen marasa karfine sosai ko kuma masu cikakken son banza.


Aysher tana zaune a gefe tanajiran layi yazo kanta dan batazo da wuri ba saida Yadikko taga ankawo wuta sannan ta turota
Dan idan da wutan nefa zaka sayi ruwan yafi arha akan idan sun tayar da Gen.

Aysher tasowarta kenan daga makarantar boko harta zauna zata fara cin abinci yadikko tace tatafi ta nemo mata mai ruwa.
Toh ganin ankawo wutan Nepa ne yadikko tace tazo tasiya mata bokitin Penti babba guda uku.

Kasan cewar Aysher ba ma'abociyar son hayaniya bane yasata komawa gefe tazauna tanacin dankalin hausa danye wanda kawarta fatima Alhasan tabata daman ta6oye a jakarta ganin zata taho diban ruwan ne yasata daukowa aboye ta taho dashi.

Sai da tayi awa d'aya kafin akazo kanta aka zuba mata tadinga daukar bokitin da guda d'ai-d'aya harta gama tana shiga gidan da sallama kanta dauke da bokitin sahun karshe tana mai farin ciki zataci abinci ta wuce makarantar islamiyya dan shirye-shiryen saukar karatun Qur'anin da zasuyi nan da sati biyu masu zuwa.

Bayan tagama cin abinci ta mike ta wanko hanunta daman tayi sallah tundaga makaranta
Hijabinta ta dauko da alqur'aninta ta daga labulen yadikko cikin yaren fulatanci tace"Yadikko nagama zantafi makaranta"

Yadikko tadago fuska a had'e tace"Bazaki tafi yanzuba kitafi gidan Innawuro kigama mata aikinki na safe da baki kammala ba kafin kizo kitafi inyaso idan kidawo daga makarantar ko sha ukun dare ne saiki gama aikin gidan nan
Ina dalili ubanki yabugi kirji yace karatu zakiyi toh gaki ga karatun naji dadin wannan saukar da zakuyi aradun Allah kina gama saukar nan babu wata islamiyyar da zaki sake zuwa aiki zaki kamayi tukuru gidan Innawuro tunda ubanki yahana kimin talla toh ai shikenan"

Cikin sanyin jiki Aysher taja kafarta maida Qur'anin d'akinta kafin tafito tabar gidan takama hanya dan zuwa gidan Innawuro.


WACECE AYSHER
Aysher Usman Abdullahi shine cikakken sunanta shekarunta 16 tana S.S one a boko, islamiyya kuma tana ajin karshe Aysher cikakkiyar bafulatana ce dan idan taga dama saita wuni batayi maka magana da hausa ba miskilace takarshe kyakyawa balaifi.
Mahaifinta yana harkan gwarine zuwa lagos balaifi yanada rufin asiri dai-dai gwargwado.
Mahaifiyarta kuwa aysher bata santa ba sai a hoto.
Ayanda mahaifin Aysher yake bata labari tuntana wata takwas wata rana da sassafe ta tsallake tabar Aysher akan fo tabar gidan.
A lokacin yadikko ce uwar gida tanada yara 3, Muhammad,Bilal, da zulai wanda yanzu haka anyi mata aure dan yadikko taki yadda tayi karatu.

Bayadda ba'ayi da mahaifiyar Aysher tadawo gidan ba amman taki dawowa kuma balaifin tsaye bana zaune tsakaninta da Baffa Usman (Kamar yadda ake kiransa)
Bayanda baffa zaiyi dole yasaki matarsa yanaji yana gani bakuma sonta bane bayayi.

Bayan tagama iddarta labari yazo masa cewa Hafsat (mahaifiyar Aysher ta tafi kano karatun aikin jinya)
Fatan alheri yayi mata tareda da cewa"inda rabon musake zama zamu zauna tare Hafsat"


Anguwar damare takasance anguwa wanda take gauraye da talakawa da masu kud'i.
Gidan inna wuro yakasance d'aya daga cikin gidaje masu sukunin anguwar
Aysher tana zuwa aiki gidan ne bisa neman alfarman da Yadikko tajeyi gidan batare da sanin aysher ba ta samo mata aiki gidan danyin wanke wanke shara da girki dan innawuro tana aiki a Nepa bata zama agida sosai mijinta kuma ma'aikacine a CBN.

Mahaifin Aysher baisan 'yarsa tana zuwa aikatau ba kuma yadikko taja mata kunne da cewa muddin ta tona mata asiri saita kaita lahira.
Aysher taji tsoro dan haka takame bakinta kam
[10/9, 8:52 AM] Maman Hanan: ***********
Durkushe yake gaban iyayensa mahaifinsa yanayi masa fad'a kansa a sunkuye.
Alh.Aliyu yacigaba da cewa"Nagaji nikam da kararka da ake kawomin duk gidan nan kaine babba shekarunka 28 amman ace haryanzu bakayi hankaliba yau kaine gurin wannan yarinyar gobe gurin wancan da zarar ance katuro manya saika gudu hartakai takawo ana zuwa ana sallama dani tare da gargad'in muddin baneman aure zakaje gurin yarinyar mutane ba kadaina zuwa

Nibansan meye yadawo dakai Nigeria ba daga Ghana kace lallai a Nigeria zakayi masters toh nikam nagaji kashirya tafiya cikin satin nan zan nema maka karatu a reshen makarantarku dake India.
Alh.Aliyu yana gama fad'in haka yabar falon yahaura sama ransa a 6ace.

Idanuwansa sun kad'a sunyi jazur Alamar 6acin rai yadubi mahaifiyarsa yana mai cewa"Umma kitaimaka kisa baki kar aturani India wallahi basai ankaini wata k'asa zan k'arasa lalacewa ba anan dinma akwai mataimaka dan haka kawai zancen zuwa india a fasashi"
Yana gama fad'in haka shima yabar falon fita yayi gaba d'aya daga gidan.

Umma tayi shiru tana jinjina maganar 'Dan nata cikin zuciyarta haqqun haka maganarsa take tasan d'anta bayajin magana amman tafiyarsa Ghana karatu danyin degree dinsa yadawo da wasu mugayen d'abiu marasa kyau babu abinda yaragu saima karuwa dayayi zuwansa can saukinta ma yadawo da sakamako maikyau.

Umma tamike jiki ba kwari yazaman mata dole tasamu maigidanta dan lamarin d'an nasu gaba yakeyi ba baya ba.
Saman tahaura itama tasameshi yana zaune a falon yana kallon news dan haka tashiga da sallama
Ya amsa mata,
Guri tanema tazauna tana fad'in"Alh. Kayi hakuri abar yaron nan yazauna a kasar nan yayi karatunsa dan Allah idan ba hakaba yak'ara komawa wata kasar ina gani abinda zaisake koyowa saiyafi haka kaduba maganata"

Alh.Yusuf yace"Shawarar da Alh.Labaran yabani kenan yanzu mukq gama waya dan haka zanbarshi anan din amman ba'a kano ba"

Umma cikin jindad'i tace"Shikenan Alh. Inaganin kawai katurasa Yola gurin yayana Lawan yazauna a gidansa nasan zaisaka masa ido sosai.

Kaitsaye Alh.Aliyu yayi na'am da shawarar matarsa.

WAYE ALH.ALIYU
ALH.ALIYU HAMEED shine cikakken sunansa d'ankasuwane nagaske a garin kano hamshakin maikud'i ne gefe guda yana harkar siyasa kad'an.
Matarsa guda d'aya ce maisuna Zuwaira wanda yaranta suke kiranta da Umma
Yaransu guda 7 Ahmad ne babba sai Saddiq, sai Amatullah, Nusaiba,Sai waleed da auta Safiya.

Anyi auren amatullah watanni 3 da suka wuce bayan tayi diploma a legal.

Ahmad tun tasowarshi mutum ne marajin magana ga taurinkai bashi da tsoro ko kad'an yanada fad'ar gaskiya baya 6oye laifinsa indai antuhumesa kai tsaye yake amsa laifinsa indai ya aikata dagaske.

Yanzu shekarunsa 28 yayi karatu a MAHATMA GHANDI UNIVERSITY dake accra a ghana ya karanci Medicine yanzu shekarunsa 2 da watanni dagama degree dinsa yadawo gida.

Ahmad masoyin matane acewarsa mata abin sone.
πŸ’πŸ’
Fitarsa daga gidan kai tsaye dabansu yatafi (Majalisa) da suke had'u wa a fine time restaurant
Yasamu abokansa wanda akasarinsu yaran masu hanu da shuni ne sunata d'an bushe-bushensu anan shima yanemi guri yazauna tare da karb'an tasa nad'in tabar wiwi din.
Bayan yagama zuzzuk'a yakalli Mudansir (abokinsane sosai sunfi shiri) yace"Ya nawan zo mu lafe anguwar birget mana gurin wannan 'yar k'wai-k'waidin
Mudansir yakalli Ahmad yace" Dole ne mu lafe nawa yafad'a tare da mikewa tsaye"

Wani daga cikin abokansu ne yakalli Ahmad yace"Nawa-nawa"

Ahmad yace"Ya akayi ne nawan"
Abokin yace"Nawa kanason mata"
Ahmad yace"Dole ne naso mata abokina domin sud'in abin sone"

Yakarasa fad'a tare da tafiya gurin daya faka motarsa mudansir yana biye dashi.



MAMAN HANAN
[10/9, 1:42 PM] Zeetty: [10/9, 12:18 PM] Maman Hanan: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE
Page 3-4

*Tabbas al-qur'ani mafitace ga dukkan wani musulmi*




Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP



Batare da 6ata lokaci ba aka samarwa Ahmad Aliyu Hameed admission a AMERICAN UNIVERSITY OF NIGERIA (APTI) university na garin yola.

Da daddare babansa yake sanar masa tare da cewa jibi zaka tafi dan anriga anfara lectures nima alfarma akamin aka dauke ka
Dubeka Ahmad babba dakai kaida za'ace kana tsaye akan karatun su saddiq amman kaine baya komai saina tsaya nayi maka saboda shiririta irin taka you are not serious about your studies at all but nasan maganinka kana gama masters dinnan aure zanmaka idanma baka kawomin mata da kanka ba nizan samo maka"

Ahmad kansa a sunkuye yace"Nagode Abba Allah saka da alheri"

Alh.Aliyu fuskarsa dauke da murmushi yace "bakomai Allah yakara shiryamin kai"

Umma tace "Amin"

Mikewa Ahmad yayi yana cema iyayensa zaije gidajen abokansa yafara musu sallama tun yau.
Suka masa fatan dawowa lfy yasakai yafita.


Kai tsaye gidansu Mudansir yafara zuwa yake bashi labarin tafiyarsa yola jibi domin yin masters
Cikin farin ciki Mudansir ya rungume Ahmad tare da cewa"Like seriously abokina nima wallahi jibin zantafi dazun tsoho yake fadamin (Baban mudan) daman inaso naje na fada maka ne tare da alhinin xa'arabamu ashe muna tare wayyo nawan"

Ahmad yace "Kai amman munada sa'a zomu tafi Musamu guys mudan busa kafin anjima"

Haka suka shige motar da Ahmad yazo da ita dan zuwa fine time restaurant.

_Mudansir abokin Ahmad ne na sosai a shekaruma zasu iya zama sa'annin juna tundaga secondry school suke tare har zuwa jami'a a ghana halinsu d'aya ne shisa suke abota sosai course din kowa daban Mudansir yakaranci engineering sa6anin Ahmad dayakaranci medicine_


Suna isa Majalisar tasu suka bama juna hannu aka gaggaisa gaisuwa irinta manyan yara Ahmad yana zama yajawo shisha yafara zuk'a tare da fad'in yau shishar nan babu flavour masu dad'i waye ya had'ata ne?

Harun ne yabashi amsa da cewa waye kuwa idan ba Farouq ba
Ahmad ya gyad'a kansa tare da lumshe idanuwansa kafin yace "Lads guess what we gonna missed u zamu wuce yola jibi muje mu karasa lalacewa acan nida Mudansir"

Dasauri sauran abokan sukace cikin hadin baki "Kaii zamuyi missing dinku nawan but bakomai ai ana tare"

Mudan cikin bacin rai yakalli Ahmad yace"Waikai bazaka rage bulbulawa cikinka wannan hayakin ba Alhalin ka karanta kasan illarta nida ban karanta illarta ba ina nesa-nesa da ita saboda lafiyata amman kai wai mai zama likita kenan fa nan gaba ko"

Ahmad cikin halin ko'in kula yace"kaji mudan (Haka yake kiransa) da zancen banza tun a secondry school naso nafara wannan harkan ta makewa nabawa zuciyata hakuri saida natafi ghana toh inama ruwanka ne wai, nifa gwarani da son matana abakine bana zina kaikuma fa"

Kuma da kake cewa zan zama likita ni nafada maka zanyi aiki a karkashin wani toh bari kaji dama irin wannan damar nake nema muna zuwa yola zanfara sake wakokin danayi na Hiphop da sunan da nake amfani dashi a ghana zanyi amfani dashi anan wato A.A.Hameed sai muga karshen lalacewa"

Mudan dai baikara tanka masa ba saima tabar wiwi daya nada shima yafara bankawa cikinsa saboda ransa ya baci.


Da daddare Ahmad ya lafe batare da yanemi rakiyar mudan ba zuwa anguwar kabuga gurin wata 'yar kwai-kwai daya hadu da ita kwanaki 4 dasuka wuce dan yau yanaso suyi sallama da itane kuma yanaso yadebi kairatin jikinta yabarta da dala'ilu ma'ana yanso yadanyi romancing dinta na bankwana yana zuwa yakirata a waya tafito kai tsaye bayan motar tabude tashiga Ahmad yaja motar zuwa wata bishiya wanda gurin ba wada taccen haske ya ajiye motarsa a gurin batare daya bude gaban motarba taciki ya zagayo bakinsa dauke da cheewing ghum mai dadin kamshi yana zuwa ya rungumo budurwan tare da aika mata da kiss ta ko'ina nidai anan nabar binsu nafito _Inamaijan hankalin "yan uwana mata dagaske karki yadda kisake jiki agurin namiji kafin aure koda ace auren naki zaiyi Allah kayi mana tsari da samarin shaho ko 'yan shan minti_


Sun dade ahaka kafin Ahmad yasaketa bayan ya tabbatar yasamu nutsuwa daga gurinta yakalleta yana maida numfashi dakyar yace" Feedo Jibi zantafi yola karatu but zan nemoki awaya idan takama kizo sai kizo ma kinji"

Idon feedo a lumshe tabudesu dakyar tana cewa"Nikam gaskiya A.A.Hameed nagaji kai kullum bazakayi sex ba saidai romancing kabarni a wahalce nikam zandena sake maka jikina gaskiya"

Ahmad yadaure fuska yana fadin"Sau nawa zan fadamiki bana zina toh bazanyi ba ina neman tsari da kusantarta nifa duk lalacewata bankai nan ba kuma saida nafada miki tun farkon fara mu'amalarmu idan hakan bai mikiba sai na manta dake idan naje yolan'

Cikin sauri feedo tace "Haba nawan inajin dadin harka dakai a hakan ma balaifi inajiranka zan tsumayi kiranka awaya pls karkamanta da alkawarinmu na aure"

Ahmad yace"Bakomai muje nasaukeki a gida ga 50k kikashe ki kara kayan make up dasauri feedo takarbi kudin yaja motar suka tafi ko godiya batayi masa ba sai.
[10/9, 1:18 PM] Maman Hanan: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Fatima ce tayi sallama gidansu Aysher taji shiru ba'a amsaba kaitsaye dakin Aysher tadosa ta tarar aysher tana sallah dan haka cikin fulatanci fatima tace"Na nema ma'ajulaino la'asar ne (daman kina sallar la'asar ne)

Aysher da tayi sallama daman raka'ar karshe takeyi takalli Fatima tareda murmushi tace cikin hausa" eh fatima sallah nayi yanzu nadawo daga gidan innawuro yadikko kuwa tafita suna"

Cikin tausayawa fatima tace"Noi kugal (ya aiki) gaskiya yakamata kifadawa Baffa wannan azabar datake gana miki aradu abin yayi yawa yanzufa aikin gidan nan zaki fara tunda kingama na gidan inna wuro ko"

Aysher tace "eh mana"

Fatima tace" toh idan baffa yadawo yakukeyi kina zuwa gidan aikin kuwa"

Fatima tace "eh ina zuwa amman yadikko tace masa wai koyon dinki nake zuwa"
Fatima ta gyada kai kafintace bakomai akwai Allah yar uwa.
Aysher tace A hefta fatima (kina ganewa fatima)

Taso muje masa miki hannu mugama da wuri kirakani waje mardiyya tela nakarbo dinkin innata.

Babu musu Aysher tamike suka fara aikace-aikacen gidan nan da nan gidan yayi fes dashi.

Bayan sungama aikin tsaf aysher taleka lokacin yadikko ta tashi tace mata zata raka fatima gidan dinki yadikko tace kingama aikinki duka
Aysher tace 'Eh nagama yadikko"

Tace kuyi sauri kudawo kizo kidaura mana abincin dare.

Ahanzarce Aysher tafice tasamu fatima suka tafi

Sunzo giftawa dai-dai wata majalisar samari sukaji ankira sunan aysher basu juyo ba suka cigaba da tafiyarsu dan sunsan mai kiran bakowa bane face Ubaidullah wanda yanace yanason Aysher
Dasauri yabiyo bayansu harya cin masu fad'i yake haba boddo (kyakkyawa) yaufa nadawo nazo gurinnan nazauna saboda tsumayin zuwanki amman ko saurarata bakiyi ba
Aysher takalleshi tace"Ubaid kayi hakuri nace maka banda lokacin soyayya karatu zanyi dan Allah kabarmu haka kar asamu wani yaje ya fadawa yadikko dukana zatayi
Tana gama fad'in haka tasakai suka cigaba da tafiya ita da fatima sukabar Ubaid a tsaye cikin sanyin jiki.



MAMAN HANAN
[10/10, 7:56 AM] Zeetty: [10/9, 9:23 PM] Maman Hanan: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE
Page 5-6



TUNASARWA
*Nadaina turama kowa novel dina ta private idan har naga kana cikin group din danake posting bazan turo maka novels dina ta private ba saidai idan sabon zuwane saboda wani dalili dafatan bazakuji haushi naba*

_Dis page is didected to U Little β“‚inate thanks for ur support Allah bar zumunci_


_Maman Ashraf inajin dadin yadda kike son novel dina da Nabeelan skt maman afnan Allah bar zumunci_



Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP

Ahmad sunsauka lafiya a garin yola bisa jagorancin mahaifinsa kaitsaye makarantar suka wuce ba'a hostel Ahmad zai zauna ba dan haka suka wuce anguwar DAMARE gidan Alh.Lawan yayan matar Alh.Aliyu wato mahaifiyar Ahmad
Alh.Lawan yakarbesu cikin farinciki daman sungama magana tunkafin zuwansa dan haka yasa aka gyarama Ahmad daki a boys quarters ciki da falo ne da toilet harda kitchen karami a ciki.

Karfe 4 Alh.Aliyu yajuya zuwa kano dan flight suka biyo kuma a jirgin zaikoma dan haka suka rabu da d'an nasa bayan yakara masa wasu nasiha bayan wanda yamasa a gida sannan suka rabu bayan ya cika masa account d'insa da kud'i.


Allah- Allah Ahmad yakeyi mahaifinsa yatafi dan haka daga airport dasukayi masa rakiya shida Alh.lawan yacema Alh.Lawan zaije school yaduba wasu abubuwa batare da Alh.Lawan yayi wani dogon tunaniba yasauke Ahmad dan yasan yola ba bakuwarsa bace.

Ahmad yana sauka wayar Mudan yakira yana dauka yace"shegen kasa ka'iso ne"
Mudan yace"Shengen sama gani nan a Apti har ankamamin hostel kaifa?

Ahmad yace"Kai tsohona yaki yadda da Hostel d'innan yakaini gidan yayan momcy but tunda kana ciki ai anatare ba abinda zai ragu nawan ganinan shigowa"

Mudan yace "Toh saika shigo nawan"

Washe garin randa Ahmad yadiro a yola wato ranar daya fara zuwa makaranta a ranar 'yan mata sukasan da zuwan A.A.Hameed saboda iya daukar wankansa gashi kyakyawane na gaske bakine amman bakinsa maikyau ne.

Motar da Alh.lawan ya mallaka masa sabuwa ce kirar BMW da ita yafara zuwa kansa sanye da facing cap wuyansa kuwa yasha sarka kamar mace hanunsa ma dauke yake da wani sarka duk na irin samari 'yan bana bakwai.

Tafiya yake yana watsa hannuwa irin yadda manyan guys sukeyi.

Balaifi yana maida hankali sosai a karatun dan koba komai yanaso yasamu result maikyau dan ya fitar da mahaifinsa kunya a matsayinsa na babba a gurinsa.

Gefe guda kuma yanata shirye shiryen zuwa studio dan fitar da wata sabuwar wakarsa na Hiphop dazaiyi.

Mudan yayi kokarin yahana Ahmad Amman sanin cewar Ahmad yanada kafiya indai yace zaiyi abu bawanda ya isa ya hanashi shiyasa yayi masa shiru .



*************

Aysher anata shirye shiryen sauka Innawuro tasata tadauki hoto takai mata zatayi mata sticer.

Da yamma bayan la'asar fatima tadawo daga gidan Inna tazo ta gama aikin gida a gurguje taleka d'akin yadikko ta tarar da ita suna hira da kawarta Yarbingel ta gaishe da yarbingel din kafin ta dubi yadikko tace"Yadikko Midillai jangirde (zantafi islamiyya)

Yadikko cikin fada tafara fadin" Nashiga uku ni jikan musa inace nahanaki yimin fulatanci amman dan tsabar munafurci bazaki daina ba toh daga yau naga kinsake yimin magana da fulatanci aradun Allah saina gicciyeki da kokara fice kibani guri saura kwana 3 ayi saukar kowama yahuta"

Dagudu Aysher taba gidan dan gani takeyi kamar yadikko xata iya kai mata bugu.

Yarbingel takalli yadikko tace shawarar dana baki da ita zakiyi amfani bari idan zankoma zanzo nakarbi hoton a sakata cikin hotunan yan matan daxan tafi dashi abuja.
[10/9, 9:54 PM] Maman Hanan: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Ahmad yana zaune a falon innawuro suna taba hira yau asabar ba aiki.

Alh lawan yana zaune suna kallo gefe guda suna taba hiran saukar su Aysher da za'a gabatar gobe a makarantar NURUL HUDA
Alh.lawan ne yace zan bata gudunmawa sosai kuwa dan yarinyar tanada kokari bansan maiyasa aka turota aiki gidan nan ba dan mahaifinta naga yanada rufin asiri dai-dai gwargwado

Inna wuro tace kasani ko sunada wata matsala ta cikin gidan Alhaji.

Alh.lawan yace hakane kuma amman ina sha'war dabi'unta shisa ko kin bar yaran nan a gurinta hankalina baya tashi sam nasan yarinyace mai amana gata da halin manya.

Ahmad dayake jin hirarsu jin yadda ake yabonta yayi tsagal yana cewa a ina take Baffa

Innawuro tace nan gabanmu kadan gidansu yake gobe ne saukar karatunta ai duk zamuje tunda ba makaranta kaga hoton sticer dana buga mata kalleta kaganta kyakkyawa da ita takarasa fada tare da bama babban yarta Nafisa wayar tamikawa Ahmad.

Dammm kirjin Ahmad yabuga yayinda idanuwansa suka sauka akan wannan fuska ma'abociyar kyau da Haiba yadade yana kallon hoton kafin yakalli inna wanda hankalinta yake kan Tv yace"inna nima kibani guda d'aya zansa a bayan wayata"

Inna cikin mamaki takalleshi tace"Nabaka zakasa a bayan wayarka, daman manyan yara irinku suna amfani da sticer bayan waya ne"

Ga zahiri kingani idan zaki bashi kibashi banason dogon bincike cewar Alh.lawan

Inna tamike tadauko masa guda biyu akan friged dinta tabashi a nan take ya bude ya manna abayan manyan wayoyinsa guda biyu.

Cikin zuciyar inna cewa take banza bayakai zomo kasuwa mudai zamu gani.

Da daddare Ahmad kasa bacci yayi saboda tunanin aysher idonsa kuwa yakasa daukewa daga kallon hotonta dake bayan wayarsa
_Tabbas inason wannan yar kwai-kwai d'in soyayyar nata ma dabanne cikin raina zanbibiyeta har Allah yakai damo ga harawa_

Ahmad baya aikata zina amman ganin hoton Aysher yasashi canja tunani da cewa idan har zata sakar masa jikinta sujone to tabbas zaikwashe kairatin jikinta tsaf saidai kash daga gani ustaziyya ce tunda gashi sauka zatayima gobe amman badamuwa wuyarta yanganta yasan gidan su.

Can yayi murmushi daya tuna cewa a gidan daya sauka take aiki lallai takwana gidan sauki dan haka yadauko kwalbar codin dinsa ya kwan-kwade tas anan bacci yayi gaba dashi



MAMAN HANAN
[10/10, 11:55 AM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE
Page 7-8

*Allah sarki nagode da ziyararki gareni hakika bazan manta da 9-10-2017 ba Allah yabar zumunci nagode da yabawar dana samu daga gareki maman Amatullahi daga Rukuba barrack plateau state jos Sakhallau khair*

Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA GROUP






Ranar saukar su Aysher Ahmad tare da mudan suka tafi dan Ahmad yagama bama mudan labarinta shima mudan din dokin son ganinta yake dan yadda abokinsa yake bada labarinta yaji sha'awar yarinyar da son ganinta yakamashi.


Gurin sauka yacika makil da jama'a mahaifin Aysher shima ya halacci gurin dan tunsanda saukar yarage saura kwana 3 yazo daga lagos.



Ahmad baiyadda sunzauna guri daya da Alh.lawan ba asalima tsayuwa sukayi a tsaye shida mudan yadda zasu hango daliban dakyau.

Fatima kawar Aysher itace tabude taro da karatun Alqur'ani sanda mudan yaganta

Please Login or Register in order to submit comment