Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito dukkaninsu Suka hadu a dining room Sukayi lunch inda suna gamawa sukazo Suka zauna itada dad din suna firar business ahankali tareda am din dake zaune kusada ita kamar wasu couples dadi sai sake Kama zeel yakeyi.

Suna cikin firar ne wayarta tayi ringing ahankali tace"

Excuse please""tareda daukar wayar tana miqewa ta koma gefe.

Wat????tafada cikin Dan bacin Rai kafin ta sake matsawa nesa dasu tana cewa"

Ya za'ayi suce abasu wannan proposal din akan 70% basuda hankaline?
Look Jasmin kusake meeting dasu idan sunason nayi musu hanya a Basu wannan deal din saisun yarda zasu zuba 80% Ni kamfanina na zuba 90% and cikin wata shida Suka dawo 150%
So idan zazu saka 80% kuyi magana idan babu kuwa tell them I'm backing out.

Ta jikin tangamemen agogon datake tsaye gabansa tagansu tsaye abayanta suna sauraron duk bayaninta tasaki wani murmushi tareda cewa"

Ok I'll talk to you later Amma yanzu zan turo miki information da details na investment company din saiki Basu.

Rubutu tayi ta turawa Jasmin text din ta juyo saita gansu zaune suna firarsu kamar Basu tashiba.

Tana zuwa ta ajiye wayarta gafen am tana cewa"

Baby I will just use a washroom and com back ok.

Cikin kulawa yace"

Ok.

Tana hayewa sama ta boye tana kallonsu taga am din ya dauki wayarta yayi forwarding din information da details din investment companyn zuwa email din kamfaninsu.

Ya goge ya ajiye wayar.

Kallonsa Dilla yayi tareda miqewa Yana cewa"

Ka tabbatarda ka riga kamfaninta neman wannan kamfanin ka shigar musu da percentage dinmu Mai yawa yanda zasu karbemu mune zamu samu wannan 150% din wannan karon.

Gyada Kai am yayi
Zeel kuwa cikin nutsuwa tace"

You better be very careful karta gano anmata zagon qasa a harkar business tazo tace tafasa aurenka.


Cikin murmushi tasauko tadawo kusadashi ta zauna tana cewa"

Baby nadawo na dauki wayana I'm little bit tired I will go and have some rest.

Tana zuwa daki ta rufe qofa ta nemi wayar JJ.

Yana dauka tace"

Be ready kowane lokaci zasu nemeka kace 70% share na dukiyarsu zasu saka within 3month zaku Basu 150%.

Harzata kashe yace"

Baby please be careful ok.

Ahankali tace"

You too please.

Kwantawa tayi tareda rufe idanuwanta ahankali tana neman relaxing.

Washe gari tunda safe Suka fice da fammah shopping sbd yaudai baqonta yace zaizo.

Daga can gidansu Annah ita ta sauka fammah din tadawo gida.


Zaune suke a office room dinsu dake cikin gidan am ya kalli dad din yace"

Dad munyi magana da wannan investment companyn gskia inaga akwai ha'dari fa musaka fiyeda rabin dukiyarmu aciki kar azo asamu matsala why not musaka kadan mugani.


Shiru Dilla yayi cikin nazari Saidai Kuma irin ribarda yaji nadey din tafada tasamu da tana waya yasa yaji Yana kwadayin mallakar fiyeda ribar barema tunda su Noah's sunyi sun samu manyan kudi shima zaiyi.

Kallon am yayi yace"

Ka saka fiyeda rabin kawai zamu fita idanma ansamu matsala zanji da kamfanin Susan dawa sukai.

Batareda hankalinsa ya kwanta da abinba yasaka hannu a takardun dad dinma yasaka ya kwashe files din ya fita dasu Dan zuwa suyi meeting da waincan kamfanin.


*****
Qarfe biyar na yamma wata baqar BMW E33class2018 ta iso gaban babban gate din Dilla mansion aka wangale masa yashigo sbd sunsan da isowarsa.

Tunda yayi parking a harabar fammah takasa hakuri ta fito cikin wani irin adon dayayi mugun yimata kyau tana tahowa gurinsa cikin daukar hankali tana farin cikin zuwansa data kasa boyewa yaudai iyayenta zasuga haydar datake damunsu akai.

Ahankali ya bude qofar motar ya zuro qafafunsa dake sanye cikin brown amadeo testoni antiqued leather Oxfords shoes kafin yafito gabaki dayansa sanye cikin baqaqen Louis Vuitton.

Kadan ya rage fammah ta suma sbd yanda numfashinta yake neman sarqewa da sonsa.

Iskar harabar gurin ya shaqa ahankali tareda sauke ajiyar zuciya kafin ya kalli fammah cikin wani sahirtaccen murmushi.

Cikin tsananin farin ciki take qoqarin riqo hannunsa ya saka hannuwan cikin aljihun wandonsa Yana kallonta da mayun idanuwansa cikin maryarsa me dukan zuciyarta yace"

Shall we???

Da sauri tace"

Yes sweetie.

Palon gidan Suka nufa inda mum da da dinta ke zaune suna jiran isowarsa Yana shigowa Suka miqe cikeda farin cikin ganinsa akaro na farko,

Kyakkyawa ne Mai qaqqarfan jikin namijinda daga gani Yana motsa jikinsa sosai,

Farine Saidai ba sosaiba Saidai Dan gefen wuyansa dayayi Dan baqi alamar tabone agurin,

Sake kallonsa zeel tayi tana Yana kyawunsa da quruciyarsa dabai wuce shekarun am dinta ba Amma shine yakeda irin wannan tarin dukiyar.

Hannu Dilla ya miqa masa cikin sakewar fuska zaiyi magana haydar din ya rigada da cewa"

_Haydar A D_

kallonsa Dilla yayi cikeda mamakin muryarsa Mai wani irin amo
Murmushi yasaki tareda cewa"

Nice meeting you haydar.

Thank you yace Yana kallon hannunsu dake sarqen Dana juna.

Cikin farin ciki zeel ma ta Dan matso Suka gaisa ya amsa Yana kallonta da murmushi kan fuskarsa.

Kafin suka dunguma zuwa cikin tsakiyar palon Suka zazzauna suna sake gaisawa.

Daga gurin meeting din am ne yabiyo gidansu Annah ya daukota suka nufo gida tana sake masa wani irin salo Dan son Jin komai gameda sauran shares dinda suka rage musu Saidai Bai wani bude Mata zancen sosaiba har Suka iso gidan.

Sanye takeda riga da wando Palazzo sai wasu wadges brown a qafarta da Yar jakarta Suka nufo cikin palon suna fira murmushin tarkonta dasuka fada yakasa barin fuskarta shikuwa duk ya dauka sbd shine takeyi sai sake sake Mata yakeyi.

Am dinne a gaba gurin shigowa kafin tashigo tana murmushin dake qarawa fuskarta kyau.

Ahankali ya miqe tsaye Yana kallonta da idanuwansa dake rudarwa.

Am na qarasowa yasaki fuska cikin farin ciki ya miqawa haydar din hannu yana cewa"

wow Mr haydar wat a pleasant meeting.

Kallon am din yayi ya fiddo hannunsa daga cikin aljihu sai kawai ya miqawa nadey da kallo daya tayi masa ta dauke Kai sbd jin bugun zuciyarta na qaruwa.

Dukkaninsu da mamaki sukabi hannunsa daya miqawa nadeyn yace"

I'm haydar.

Kallon fuskarsa tayi tsawon seconds saitaji takasa Hana kanta miqa masa hannu ta dago hannu a hankali ta miqa masa murya na rawa tace"

ND Noah.

Murmushi yasakar Mata tareda zare hannunsa data qurawa ido.
#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*


_Mamuhgee31_
Da sauri tasake bin hannunsa daya janye daga nata dukkanin fuskarsa na bayyanarda wani boyayyan murmushinda yasake jefa kowa cikin mamakin abinda yafaru.

Fammah ce tasaki murmushi tana cewa"

Everybody just chill nadey and haydars are business partners I think so please let's all sit and talk about me and my haydar.

Dukkaninsu ajiyar zuciya suka sake a boye musamman zeel da dad din data fara shakkar kar 'daya daga cikin 'yayanta su rasa wainnan biyun.

Zama duk Sukayi ta dago qafafuwanta dasukai sanyi ta zauna kusada am tana qaqalo masa murmushin dole dako gama fitowa baiyiba.

Dagowa tayi ahankali lokacinda am ke gabatar masa da ita amatsayin wadda zai aura ta kallesa idanuwansu suka shiga cikin na juna sbd yanda ya xuba matasu ko qwaqwaran motsi kasawa tayi atake ta sarqe tafara tari ahankali.

Da sauri am ya dauki ruwa ya Bata Yana Mata sannu cikin kulawa Saidai tana saka ruwan bakinta ta qarasa sarqewa sbd azabar dayake Bata da idanuwan nasa Dan har lokacin ko qyaftasu daga kanta baiyiba saima wani irin ja dataga sunayi

Take tsoro da fargaba suke neman shigarta ta miqe da sauri tareda cewa"

Excuse me daqyar tana tari ta nufi stairs da sauri ta haye.

Miqewa am yayi zaibi bayanta haydar yayi qyaran murya tareda cewa"

Ya dawo su Gama gaisawa Mana.

Dawowa yayi Suka cigaba da 'yar fira Saidai dukkaninsu hankalinsu na saman musamman haydar da tuni idanuwansa suka sake rinewa ya miqe batareda yaqara wani lokaciba yace zai tafi.

Duk yanda fammah tayi masa magiyar ya tsaya suyi dinner
Qarshema yanayinsa ya Bata tsoro tayi saurin tsuke baki ta rakasa mota ko qarasowa batayiba ya fice ya barta tsaye.

Hawaye taji sun ciko idanuwanta tana tsaye taji suna neman sauko Mata.,

Meyasa haydar baitaba nuna Mata kulawa ko so ba?
Meyasa tunda ta hadu dashi a airport Zurich take mutuwar sonsa tana bibiyarsa Yana wulaqanta rayuwarta.

Dafata taji anyi tana juyowa taga am tayi saurin fadawa jikinsa tareda sakin kukanta datake dannewa.

Shima jikinsa sanyaye yake sbd yaje yayi knocking qofa kamar me nadey taqi budewa tamayi kamar Bata jisaba.


Ita kuwa nadey hakanan taji hankalinta yayi matuqar tashi tarasa Ina zata saka kanta wani irin shakkar idanuwan wannan haydar din takeji ta rasa meke Mata daidai sai kawai ta zauna bakin gado hawayenda batasan Kona meyeba suna sauko mata.

Tabbas idan har tanason gujewa wannan fargabar koma ta meyene to Dole tayi tagama abinda yakawota tabar nan musamman yanxu da JJ yafara damuwa da maganarta dashi sbd kar wani Abu ya gifta musu ita kuwa idan Koda auren am ne ke nufin kawo qarshensu a shirye take da hakan,
Saita tarwatsa rayuwarsu ta yanda bata taba haduwa zata bar gidan.


Daqyar ta tashi tayi sallah tayi wani wankan tasaka doguwar Pakistani gown ta sauko lokacin dinner Sukayi dinner Yan gidan nata farin ciki da murnar zuwan haydar din.

Itadai Bata tsaya wani dogon firaba tana gamawa ta haye Suka bita da sannu cikin kulawa.


Washe gari tana tashi ta shirya cikin blue skinny jean da white loose lace chiffon half top tayi rolling din gefe da wata qaramar scarf ta dauki handbag da wayarta takalli fammah dake faman Kiran wayar haydar tunda safen Amma baya dauka qarshema ya kashe wayar.

Ficewa tayi tana cewa"

I have a morning private meeting da wasu client Dina so saina dawo.

Tana fita Bata hadu da kowa a Palo ba ta fice.

A harabar gidan ta hadu da am yafito daga sashenda yake geaming jikinsa sanye da kayan geaming din sai sneakers na Adidas.

Qarasowa yayi gurinta lokacinda take fitowa Yana Mata wani kallon so yace"

Gud morning luv.

Murmushi ta mayar masa cikin kulawa da kashe murya tace"

Morning baby.

Are you going somewhere???

Yes baby I have some clients to attend to.

Ok lemme freshen up and.....

Katsesa tayi da cewa"

No I can manage besides I won't be long.

Ok luv you can take my car then.

Keys din motarsa ya dauko Mata ya Bata ta karba tareda kashe masa ido tana cewa"

Thanks baby.

Shiga motar tayi tareda Bata wuta ta wuce sbd sauri takeyi tanajin wayarta na vibrating cikin Jakarta takuma San JJ ne sbd dashine zata hadu.


Tana fitowa ta hau titi da speed sosai sbd yau Dole zasu hadu da lawyers dinsu su karbi takardun fiyeda rabin dukiyarsu Dillan dasuka karba a jiyan.

Wani babban restaurant dake cikin wani babbn 5star ta nufa inda acan suke haduwa da JJ.

Tana Shan kwanar restaurant din wata baqar jaquar Tasha gabanta da qarfi ta Danna burki tareda dagowa tana cewa"

Oh my God wayyo Allah banana.

A fusace ta dago zata fito tagansa ya fito motar cikin kayan geaming shima black dasuka fiddo kyau da farin fatarsa ya nufo mitarta cikin wani irin taku Saidai kallo daya zakawa fuskarsa kasan ransa a matuqar bace take.

Mugun faduwa gabanta yayi take jikinta yadauki rawa musamman yanayin qirar jikinsa datake neman fitarda ita hayyacinta hannunta na rawa ta bude motar tana fitowa Yana kawowa dad da motar zai bude qirjinsu ya hadu da qarfi
Tayi baya zata fadi ya riqo hannunta tareda fizgota ya matse jikin motar.

Rintse idanuwanta tayi da sauri jikinta na rawa sosai komai takasa tunanin yi.

Shima rinte idanuwansa yayi Yana qoqarin controlling kansa Saidai Sam yakasa da qarfi ya daga hannu ya daki jikin motar Saida ya lotsa yayi baya Yana dafe kansa dake qoqarin tarwatsewa jikinsa har wani rawa yakeyi jijiyoyin qarfinsa duk sun firfito.

Tana bude ido taga yanayinsa hankalinta yasake tashi a rude ta fada motar jiki na rawa ta tayar tabar gurin da mugun speed.


Tana Isa 5star din ko parking me kyau batayiba ta fito ta shige.

Saida tashiga elevator takuna tafara dawowa hayyacinta tana sauke ajiyar zuciya har lokacin jikinta na rawa.

Tana isa restaurant din tasake daidaita kanta sbd kar JJ yaga yanayinta hankalinsa zai iya tashi yayita tambayarta.

Share Dan zufanta tayi ta nufi table dinsu dake can qurya tana Dan sake fuskarta.

Tana qarasowa ya kafeta da ido Amma sbd suna tareneda lawyers dinsu guda uku saiya basar Yana tambayarta yanda take cikin kulawa.

Amsawa tayi tana sake daidaita kanta ta zauna tana gaisawa dasu Mr Jonas.

Fitarda takardun JJ yayi masu signature din dikko da am
Takardune na bayarda fiyeda rabin dukiyarsu ga wannan investment kamfanin da sunan su samu ribar fiyeda ninki biyun abinda Suka bayar.

Atake Suka gama duk bayananda zasuyi Suka gama akan daganan Courts zasuje ana bugawa takardun stamp shikenan komai nasu dillas yadawo nasu.

Tasowa Sukayi dukkaninsu cikin farin cikin samun abinda sukeso cikin sauqi.

Itace agaba itada JJ Suna fitowa tayi saurin yin baya ta boye tana leqen Dilla data gani tareda wata former Mayor din San Diego cikeda mamaki.

Kallon JJ yayi tace"

Is he having an affair????

Girgiza Kai JJ yayi Yana leqensu har Suka tsaya jiran lift cikin mamaki shima yace"

Dilla baya neman Mata ko kadan a rayuwarsa sbd son kudinsa da hadamarsa yasan mace zata iya rabasa da komai nasa shiyasa baitaba neman Mata ba sbd gudun sukawo masa matsala idan Kinga Dilla da mace to business ne Kuma babba.

Wani tunanine ya shigeta ta kalli JJ tana kallonsu suna Kiran budewar lift tace"

Dady j ka tattaro Mana press sumtin is about to happen.

Tana Gama fada ta warware scarf dinta ta rufe fuskarta tareda zuwa gefensu ta tsaya daidai lift na budewa Suka shiga itama ta shiga.


*_Dan Allah kuyi manage wlh inada wani babban uzurine yau da gobe Ina fatar zaku fahimceni🙏🙏_*
#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee32_*
6th floor suka nufa suna fitowa lift din itama ta fito ta tsaya tana latsa wayarta tana sake rufe fuskarta da scarf din harsai dataga room dinda suka shiga,
Juyawa tayi baya ahankali taga Babu kowa tayi saurin qarasawa taga room number din ta matsa sosai zata Dora kunnenta taji motsin tahowa tayi saurin matsawa tana tafiya tana Dan latsa wayarta Amma hankalinta nakan waitress dinda tafito wani room zata bar floor din.

Saurin bin bayanta tayi tana Kiran JJ suna shiga lift Yana dauka qasa qasa tace"

JJ pls Ina buqatar tque a bar din cikin restaurant dinsu yanxun nan ganinan zuwa.

Restaurant din ta nufa da sauri bayan sunfito lft waitress din na gabanta.

JJ tafara nema cikin gurin tana duddubawa saigashi Yana zuwa gurinta ya miqa Mata a boye da sauri ta karba tasaka Jakarta ta nufi gurin wata waitress tasaki fuska cikin Dan karyar da Kai yace"

Please can you help me call room 409 I want to make sure of wat to order for my husband please.

Sure ma'am"" waitress din tafada tareda daukar wayar restaurant din tayi dialing room 409 din ta miqawa nadey tareda juyawa dauko wani menu Dan bawa nadey din.

Qasa nadey tayi tareda saurin canza murya ana dauka tace"

It's Restaurant sir wat are your orders???

Sam bai cika wani cin abinci ako Ina yajeba sbd gudun a cucesa shi haka Allah yayisa Sam baida yarda Amma ganin zasu Jima suna magana da mayor sai kawai yabada order din ya aje wayar suna cigaba da duba wani private project dasuyi tsakanin dillas empire da ita.

Aje wayar nadey tayi tareda kallon waitress din tana murmushi tace"

Oh thank you so much miss you just save my marriage today because my husband is very short temper.

Bayarda order dinsa tayi aka kawo aka ajiye ta kalla chicken sandwich ne da fish potatoe soup sai Italian sausage.

Ya mutsa fuska tayi tareda sake kallon  soup din ta zura hannu handbag ta fiddo qaramar kwalbar ta bude ta juye ciki tareda mayarda kwalbar Jakarta tareda sarin juyawa daidai nan waitress din ta juyo tareda daukar arder din ta tafi kaiwa room din bayan nadey tafada Mata room number.

Bayanta nadey tabi da kallo tareda dauke gira daya tana qissima abinda takeson yafaru din.

Komawa gurin JJ tayi tareda yin qasa da murya tace"

Ka kirasu kuwa?

Kai ya daga Mata Yana kallon qofa inda sosai ya qurawa qofar ido baya ko qyaftawa sbd abinda idanuwansa suke gani.

Haydar ne ke shigowa gurin sanye cikin Louis Vuitton black
ash suits fuskarsa sanye da warby shades fuskarsa ba asakeba Sam Saidai Kuma kwarjinsa da burgewarsa suke daukar hankalin mutane akansa.

Batareda nadey ta luradashiba takira JJ Suka bar gurin zuwa reception.

Agogo take kallo tana qiyasta lokacinda ta dibarwa aikin abinda ta zuba musu yacika ta miqe tareda kalon JJ ta daidai shigowar wani shagararran Dan press a gurin Wanda yake tamkar friend din JJ din ne.

Kallonsa nadey tayi tareda gyara tsayuwa tafara koro masa bayani abinda takeso.

Wani murmushin Jin dadi yasaki yace"

Karki damu miss Noah muda muke neman abin yadawa ido rufe musamman ma yau munsamu akan Dilla's empire I promise yau saina nuna masa the power of media sbd yataba zaginmu ya wulaqantamu.

Room number nadey tabashi cikin Jin dadi shida JJ ne Suka fara zuwa dakin bayan sun rufe fuskokinsu da facing caps.

Ahankali Suka tura qofar dakin ta cikin saa ta bude JJ yafara leqawa yaga dukkaninsu sun sunyi marus a inda suke zazzaune.

Nadeey ce tashigo dakin ta dauki takardun gabansu tafara duddubawa taga contact ne suke Shirin hadawa harma sunyi signing.

Kudine yakeson tabasa almost 1mil dollars yayi wata kwangilan wani babban project Saidai baida millions dinda project din ke buqata yanxu sbd sun zuba fiyeda rabin dukiya da kadarorinsu a wancan investment din.

Yaga takardar tayi ta bude Jakarta ta zuba takardun cikin sauri har handbag din na faduwa abubuwan ciki Suka zube tayi saurin tattarawa ta mayar tareda Kama mayor dake marus ta mayarda ita kan gadon dakin.


Ficewa Sukayi dukkaninsu nadey ta koma motarta ta zauna JJ Kuma restaurant ya shige ya zauna.

Amed paaris kuwa Yan media yakira yace anbasa information da cewa akwai abin dauka a room 409 dake 5star din take media tacika gurin Wanda hakan shine ya dauki hankalin mutane sosai nan Suka dunguma zuwa room din kafin ma managern gurin yasamu isowa.

Ita kuwa wayarta ta fidda takira zeel cikin yanayin murya kamar zatayi kuka tace"

Mum please come here I can't handle wats happening here alone, it's serious mum please come right away.

Hankali tashe zeel tace"

Ok sweetie send me the location I will be there in a minute.

Suna zuwa Suka bude dakin atake mamaki yacika duk Yan jaridar ganin yau mayor ambryam tareda dilla kenan they're having an affair...

Atake aka ringa daukarsu hotuna da video wasu Kuma live video suke Yi musu.

Gashi dukkaninsu suna motsawa alamar son miqewa Amma abin ya gagaresu sbd sunkai qarshen maqura gurin high drunk.

Cika 5star din yayi sbd yanda abin yafara qarfafa atake manager yakira police kafin yazo shiga security suna qoqarin korar Yan press Amma Ina sai qara cika gurin yakeyi.

Cikin hanzari manager yace akawo lemon mix Mai qarfi abasu sudawo hayyacinsu.

Ana kawowa aka Basu dai dai shigowar zeel da am sai fammah da nadey datace musu wani client dinta tazo gani agurin ta tararda wannan abin na faruwa shine takirasu.


Lokaci daya daga Basu lemon mix Suka dawo hayyacinsu ganin taron media akansu da dibbin mutane yasa dukkaninsu miqewa da sauri kafin yayi wata maga zeel Bata tsaya komaiba ta daukesa da wani mugun Mari ga Yan media na dauka.

Cakumo mayor tayi cikin tsananin baqin ciki da bacin Rai ta hau marinta tana zaginta da sauri nadey da wasu waitress tareda manager din harma da Dilla da qarfinsa bai gama dawowaba Suka hau qoqarin kwatar mayor wadda batada qarfin jiki Sam sbd abin Bai Gama sakesuba.

Cikin tsananin fushi da bacin Rai zeel take cewa"

I swear I will make your life a living hell,I promise I will make you pay for this you old bitch,I will kill you and whole your family.......

Police ne Suka Kori kowa ana hayaniya ana komai aka korosu harabar gurin aka samu aka fitoda mayor aka bar gurin da ita.

Qoqarin calming mum sukeyi itada am tajiyo qamshin royal possession na sandals water rose take taji gabanta ya Fadi taji tana neman rikicewa da zuwansa gurin,.

Batareda ya kalli inda takeba ya kalli police da Manager dasuke masa bayanin abinda tun a gida yagani live
Manager daya Kira masu bincike ayi binciken dakin tsaf yanason sanin meya faru sbd kowa yaga hakan yasan set-up ne aka hadawa su mayor yanason sanin komai sbd sunan 5star dinsu dasuma yake rawa.

Jin hakan yasa ta Dan dago ta saci kallon qofa tanason fita tayi waya da JJ akan yaje restaurant yayi handling dinsu sbd da an duba abincin dasukaci zaa gano daga restaurant matsalar ta fito Kuma ana zuwa zaa ganota.

Kallon plates din abincin tayi tareda qura musu ido tana neman yanda zatayi ta Hana a bincika abincin coz this is a serious issue suna ganota ansamu matsala sbd yanda sunansu yagama baci to the core wlh ko am dake kirarin sonta saiya kasheta baresu manyan.

Tana sake kallon qofa tana juyowa sukai ido biyu da haydar daya zuba Mata fararen idanuwansa Yana kallon yanayinta da yanda ta qurawa abincin idanuwa.

Fiddo wayarsa yayi yana latsawa Yana neman wata number ya nufi gurin window batareda Yana kallon gabansaba ya ture plates din gabaki daya zuka zube gurin tareda tarwatsewa.

Cikin sauri manager da fammah tareda securitie biyu sukayi gurinsa suna cewa"

Be careful sir..

Ohhhh shit""yafada Yana kallon kayansa cikin nuna takaici.

Kallonsa tayi da sauri tana sake kafesa da ido sbd tabbas tasan da gangan yayi sbd taga lokacinda yasa qafa gurin ya buge table din.

Mamakinsane tareda sabuwar fargabarsa tasake shigarta ta kalli kayan daya zubar din cikeda mamakin yin hakan zata dauke ido idanuwanta suka sauka kan id card dinta a qasa gurin bakin gado.


Atake taji idanuwanta sunyi jajir suna neman cikowa sbd tabbas tasan yau komai ya lalace Mata gashi police din ya hango id card din ya nufi gurin Yana cewa"

I think we found something here.

Kallon gurin haydar yayi yaga fuskarta baro baro akai,
Police din zai dauka yarigasa dauka fuskarsa ba wani sakewa yace"

It's mine,I think it felt dwn from my pocket while I was taking my phone out.

Sakawa alhijun suits dinsa yayi tareda nufar qofa Yana sake goge jikinsa da tissue.


Bayansa tabi da kallo yau Kam mamakinta da tsoronsa sunfi na jiya da yau a ranta,

Ta tabbarda da gangan ya zubarda abincin saidai Bata San meyasa yayi hakanba,
Id card dinta kuwa tasan nata ne yasan nata ne Kuma yaganta a jiki Kuma hakan ya nuna baro baro tana dakin kafin yanxu kenan Dole akwai saka hannunta Amma ya dauka ya Hana police su dauka,
Meyasa zai kareta ya boyeta ya Hana asirinta tonuwa????

Idan harya kareta ya Hana akamata akan ta cutatarda in-laws dinsa it means kenan shima yanada wani motive akansu....
Zatai bincike akansa Dole saitasan wayeshi, meyene motives dinsa akansu dillas dahar zaiga Wanda yayi musu abinda akai yau ya rufata,

He seems to be more clever and dangerous than her Dole zatai taka tsantsan tasan wayeshi batasan da wa take dealing ba,JJ zai binciko musu komai akansa cikin 3days.


Suma su dillas din fitowa sukayi nadeey na riqeda mum din Suma su am duk ransu a bace yake musamman am daya San wannan abin baqaramar mummunan illa zai musuba sbd business deals dinsu kusan yanxu duk ja Baya zaa dasu sbd sunansu ya baci a media.

Qoqarin shiga motoci sukeyi Amma Ina media ta rufesu sai tambayoyi suke musu Amma Babu Wanda zaikarbu sbd Muni da 'dacinsa shiyasa securities ke kakkaresu su samu shiga mota.

Daga can cikin yan press din wani yace"

Mrs Dilla ko Zaki iya sake bamu bayanin abinda kike nufi gameda cewar da kikayi Zaki kashe mayor da familynta???

Dukkaninsu cak Suka tsaya Jin wannan tambayar sbd fitarta media balaice atake am yayiwa wani securityn dad dinsa ido tareda nuna masa Wanda yayi tambayar.

Nadey data lura da hakan takuma San me zasuyi masa sai kawai ta fidda wayarta cikin style ta dauki hotonsa atake ta turawa JJ tareda masa text.

Aikuwa suna barin gurin shima Dan press din yafito ya hau abin Hawa Yana barin gurin sunyi nisa kadan aka taresu aka fiddosa cikin motar wasu masu mask ne Suka hau dukansa suna cewa waya basa izinin yiwa Mrs Dilla wannan tambayar gaban media.

Dukansa sukeyi sosai tareda yayyanka masa wuqa zasu sokesa daidai nan JJ daya Kira police suka qaraso sukuma Suka gudu.

Da sauri JJ yaqaraso gurinsa Yana cikin ransa Yana cewa"

Sorry nabarka sun dakeka sosai kafin mukawoma ceta munada buqatar hakan ne sbd zaimana amfani gaba.

Daukarsa akayi aka nufi asibiti dashi shikuma JJ yatura Mata massage ya rubuta"""done"""


Wani irin sahirtaccen murmushi tasaki tareda sake riqe hannun mum din tana fuskar tausayi cikin munafurci tace"

Mum please don't stress your self about this ok??? everything will be ok wen the cops finds out who is behind this.

Wani numfashin takaici tasaki zuciyarta na qara qonuwa ita Sam takasa yardama da wani banxan

Please Login or Register in order to submit comment