Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

soon zasuga sunan kamfanin.

Duk yanda taso ta kebe da JJ Bata samu damaba sbd am daya kasa ya tsare yanata wani nunawa media ita tasace Wanda qarshe da wani yayi masa tambayar meyasa Noah's Suka taimakesu daga gidansu da suka kusa rasawa Kai tsaye yace"

Because she's part of the family,
She's going to be Dillas soon we are getting married in a 2 weeks time.

Wani irin kallo tayi masa files din hannunta na neman zubewa Saida JJ cikin taron yayi saurin zaresu a hannunta idanuwansa jajir ko kallonta beyiba yabar gurin tareda mutanensa.

Zagayeta Yan media Sukayi suna tambayarta da gaske ne ta rasa ya zatayi tafara qoqarin barin gurin Amma tuni suka zagayeta am din ne yayi saurin kallonta yace"

My love tell them mana.

Kallonsa tayi tareda sakin murmushin yaqe ta juyo ta kalli Yan media din tace"

Yes we are getting married soon.

Tana fadar haka ta juya tabar gurin zuciyarta na tafasa sbd abin yafara zama wani Abu Kuma,

Tabbas tasan akwai dalilinsa nayin hakan a gaban media Dole yakamata tasan nayi tabar gidan tun abubuwa Basu fara juya mataba.

Da daddare tafito kicin cin abinci taji motsi qofar kicin ta baya gabanta yayi mummunan faduwa sbd Jin motsin babbane.

Kasa hakuri tayi zargin ko am ne ke yin wani Abu cikin Daren ta sidado ta dawo Palo ta nufi qofa ta bude ta fito ahankali da tareda Kiran JJ Yana dauka tayi saurin yin qasa da murya tace"

Dady j am yanayin wani Abu cikin Daren nan bansan ko meyeba Amma Koma meyene is serious.

Cikin sauri yace"

Baby karkije idan yaganki zai iya cutatar dake.

No dady j bazai iya cutatar daniba he loves me...

No no pls baby wlh kashesa zanyi idan ya cutatar dake and.....just put me on video call inason ganin abinda ke faruwa.

Da sauri tasashi video call din tareda yin qasa da murya gabaki daya.

Ahankali ta zagayo ta bayan kitchen din tana karyowa taji an fizgota da qarfi tareda toshe bakinta tafara Shure Shure wayarta ta fadi tasa hannu tana qoqarin lalubo fuskar Wanda ke matse da ita din Saidai takasa hood dinda ya rufe fuska da ita kawai tasamu damar zamewa sbd tsananin rawar tashin hankali da tsananin tsoron data shiga da firgici.

Wani Abu ya shaqa Mata atake jikinta ya saki ya dauketa cak yabar gidan da ita.

Bayan motarsa ya kwantarda ita yashigo ya kwantarda ita a jikinsa driver dinsa yaja Suka bar gurin Yana kallon fuskarta zuwa jikinta dake sanyeda wasu sleeping dress riga da wando pink colour Mai duhu masu santsi da Rashin nauyi.

Hannunta ya qurawa ido tareda riqo yatsarta dake sanye da zoben white gold Mai tambarin A Wanda yasan ALEEYU a din ke nufi.

Akaro na farko yakai hannun bakinsa yayi kissing tareda lumshe ido yasaki numfashi Mai qarfi Yana cewa"

This is enough Mrs haydar Neyo.

Wani babban Banglore dinsa dake kusan 4 kilometers away daganan Suka Isa ya daukota ya nufi qofar palon yashige Bai tsaya ko Ina da itaba sai master bedroom dinsa ya shinfideta tareda rufeta da duvet cover ya zauna gefenta tareda yin shiru ya qurawa fuskarta ido zuciyarsa na wani irin narkewa aduk lokacinda yake kallonta amatsayin ita din tasace shikadai.

Yaso barin yaga yasamu dar qaddamar da burinsa akan Dilla's kafin bayyanar Mata da kansa Saidai kishinta kashesa zaiyi bazai barsaba
Zuciyarsa yau saura kadan ta buga Saida yasha magani da qila bugawa zatayi,
Bazai qara barinta Takoma koinaba tadawo hannunsa kenan daga nan sai Nigeria zasu koma.

Tashi yayi ya fice bedroom din bayan ya kashe lights ya rage Mata aircon.



JJ dayaga duk abinda ya faru sbd har lokacin da wayar ta fadi tana on video call Babu abinda yayi mugun girgixasa irin fuskar daya gani lokacinda hannun nadeyn ya ture hood dinsa,,,,,

Miqewa yayi tsaye tareda buga kansa da qarfi jikinsa na wani irin rawa sbd rudu da gigitar fuskar daya gani,

Sarki yafada""""cikin tsananin fargaba da shakka,

Gefen fuskarsa yagani Wanda yaga kamar fuskarsa,
To abinda yafi basa tsoro shine abinda ke daure a qwandar hannunsa Wanda tunda yasan sarki dashi yasanshi kozai mutu yadawo yasan wannan abin hannun na sarki ne.
#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee35_*
Kasa zama yayi ya zari key din mota da sauri ya fito waje ya fada mota Ya figeta da sauri sbd yariga yasan am ne yake qoqarin cutatarda nadey tunda ta riga ta taimakesu tabbas Dama yasan saisun biyo takardun dukiyarsu dake hannunta sun karbe kota sauqi kota wuya
Babu wani sarki daya gani idanuwansane ke masa gixo ganin kamarsa,

Buga sitarin motar yayi Yana girgiza kansa dake neman bugawa zuciyarsa sai wani tuquqin baqin cikin halinda nadey ke ciki yanxu takeyi,

Ikon Allah ne kawai yakaisa gidan ko kashe motar beyiba yafito yayo ciki securities suka taso ya Ware hannu ya naushi dayansu tareda ture dayan da qafa yabarsu kwance ya shige ciki da sauri ya qarasa inda yakesa ran nan ne yahau duba wayarta
Can cikin glass carpet dinda ke gurin yaganta yayi saurin dauka ya duba yaga wayar still tana aiki a fusace yayi hanyar palonsu Yana qwala kiran am cikin wani irin Amon bacin Rai.

Am din ne da fammah Suka fito tare cikin fargabar meyake faruwa.

Ganin JJ da yanda yanayinsa yake yasashi daure fuska a fusace shima yace"

After all the humiliation and deceit how dare you come hia you goon.????
Get out of here before I lose my control......

Wani mugun naushi JJ yakai masa a baki dayasashi zubewa dafe da bakinsa dake fidda jini ya miqe a matuqar fusace yace"

Hw dare you hit me..you bast......

Bai qarasa ba wani mugun Marin ya sauka fuskarsa shima cikin zafi ya dauke JJ din da Mari Yana cewa"

Don't you dare hit me again....

Shaqosa JJ yayi cikin tsananin fushi yace"

Where is nadey?????

Tell me Ina kakaita idan ba hakaba I swear I will rip your head...kafadamin Ina ka kaita???

Turesa am yayi da qarfi cikeda mamakin maganganunsa a hasale yace"

Meye ruwanka da matata????
Meye hadinka da ita dasai anfada maka inda take.???

Kallon am fammah tayi tana hawaye tareda matsowa sosai ta riqe hannunsa cikin yanayin kuka da tausayin Dan uwanta tace"

Am nadey fa Bata nan tun dazu Nima na dubata har baya Bata nan da gaske tana tareda Kai bayan nabaka shawarar karkayi wannan rayuwar before marriage.....

Kallonta yayi a hasale yace"

Bata taredani Amma nasan duk inda taje zata dawone karki biye zancen haukar wannan 'dan ta'addar da sare sare da shaye shaye kawai Suka iya....

Cikin baqin ciki JJ yashaqosa Yana kallon cikin idanuwansa yace"

Wlh bakasan 'yan ta'addanci sun iya sare sare ba saina Gama tabbarda nadey na hannunka ranar zakasan qarfinda 'dan ta'adda kedashi.

Wurgi yayi dashi ya juya a fusace yabar gidan Saida yayi nisa da gidan ya parka motarsa Jin hawayen cikin idanuwansa na gangarowa,
Wlh bazai iya jurewaba idan ya rasa nadey ko wani abin ya sameta gashi baisan ta yayama zai fadawa dad abinda ke faruwaba da abinda ya gani.

Sai dare sosai ya koma gida ya shige bedroom dinsa ya rufe tareda kifewa kan gado Yana sake zurfafa cikin tunanin inda zaifara nemanta a boye batareda ansaniba musamman media bayason zancen ya fita ga media.

Am kuwa bayan barin JJ gidan juyawa yayi ya kalli qofar shiga Palo cikin wani irin yanayi na zurfafa tunani,

Tabbas yaga wayar nadey a hannun JJ Kuma gashi fammah tace Bata nan to ya akayi JJ yasan nadey haryasan batanan????
To kenan waya tayi masa ko menene????
Something is really wrong here..

Tunda tashigo rayuwarsu komai yafara lalacewa gashi yanxu sun wayi gari basuda wata kadara ko daya sai kudi a banki Suma sun bararda kusan fiyeda rabi gurin shariar mum da qoqarin kwato dukiyarsu,

Idan Bai mantaba itace sanadinsa suka hadu da wancan kamfanin investment dinda Suka bayarda takardun kadararsu,,,

Hakama ranarda dad yake a hotel da mayor itace takira mum gurin,

Was that all really coincidence or was it all planned????

Something is really wrong here.

Cikin gidan Yayi da sauri ya nufi stairs ya haye fammah na bayansa tana binsa tana tambayarsa Amma ko kulata beyiba sbd haukar dayaji na neman kamasa lokaci daya.

Closet dinsu ya nufa yafara jawo kayan nadey din ya fiddo akwatinta ya bude tareda zazzagewa duka kayan ciki Suka zube har wasu takardu da da hoto ya fado.

Hannunsa har wani rawa yakeyi sbd fargabar abinda zai iya gani...

Takardun yafara dauka ya juyo dasu zuciyarsa na harbawa sbd bayason yaga abinda zai Saba tunaninsa akan nadey Yana Mata tsananin sonda bazai iya rabuwa da itaba Koda ita dince take musu cutar a boye..

Yana juyoda takardun yasaki ajiyar zuciyarda ta rage tsoronsa da fargabarsa akanta sbd takardun asibitine na normal checkup dinta.

Harzai aje idanuwansa Suka sauka kan complete name dinta
_NADEEYA DATTIYA NOAH_
Wanda dama shi ake nufi da ND Noah.

Dattiya yasake fadar sunan Yana sake maimatawa sbd kamar yasan yataba sanin sunan.

Hoton dake kife ya dauka Yana birkitowa Saida yayi saurin yin baya sbd fuskar daya gani tayi mugun murda hanjin cikinsa take yafara mazari
Fammah tayi saurin riqesa tareda daukar hoton ta duba cikeda mamaki tace"

Wannan Zane nefa ba hoto ba meyesa hankalinka ya tashi haka?

Wannan din waye shi??

*SARKI* "ya fada Mata Kai tsaye.

Sake kallon hoton tayi dakyau tasake kallawa har gefen fuskar zanen itama cikeda mamaki ta kallesa tasake kallon hoton tace"

Wannan asalin fuskar haydar Dina ne kawai banbancin shine haydar Dina ya qone a gefen wuyansa zuwa fusakarsa kadan tun Yana yaro yace shiyasa idan zai fito ake masa gyare gyare a fuskar ana sauya masa kamanni sbd baason iska na hawan gurin saiya warke gabaki daya.

Wani irin karaji yasaki Yana dafe kansa kamar zararre kafin ya damqota da qarfi hartana sakin qarar azaba yace"

Ya akayi kakasan wannan???
Tun yaushe kikasan hakan????
Fadaminnnn""ya fasa da mugun qarfi jikinsa na rawa.

Cikin tsananin tsoro da tashin hankalinda Bata taba ganiba murya na rawa hawaye nabin fuskarta tace"

Dama tun ranarda nafara ganinsa muka hadu a airport shine naji bazan iya son kowaba duniya idan bashiba tun a nan na ringa shishige masa hardai yadan kulani nasamu card dinsa shinefa na ringa bibiyarsa Ina kiransa wata rana ya dauka wata Rana yaqi ahaka dai harya fara kulani muna soyayya Saidai haryanzu baitaba zama Dani munyi firar soyayya ba,
Dama Ina yawan zuwa office dinsa shine ranar Ina zuwa shikuma ya fice sainabi bayansa har gidansa Ina zuwa na bawa securities card Dina da matsayina a gurinsa shine Suka barni nashiga har palonsa nan Naga.....

Zaro ido tayi cikeda mamaki da tuno abinda tafara gani a gidansa ranar,
Kallon am tayi tace"

Tabbas qatoton zanen hoton dake palonsa kamar wani qofa guda nadey ce,
Yes insha Allah itace sai yanxu nake tuno kamannin wancan hoton wlh itace....

Daga Palo Ina cikin kalle kalle saigashi ya fito palon daureda towel fitowarsa wanka kenan yafito daukar wayarsa daya Bari nan.

Cikeda mamaki da takaici yake kallona nikuma cikeda mamakin da qaunar tsananin kyawun fuskarsan nake kallonsa sbd Sam ban gane cewar shi bane Saida yayi mgn na ganesa take na rikice masa sbd tsoro da fargabar mutum daya da fuska biyu.

Ganin haka yasa ya zaunar Dani yamin bayanin Wai qonewa yayi Kuma baason iska na hawan gurin saiya warke shiyasa ake rufe gurin to idan aka rufe nan kawai saiyanayin wani iri shine ake sauya fuskar gabaki daya Amma yasa na masa alqawarin bazan taba fadawa kowaba ciki har iyayena nikuma na masa alqawarin bazan taba fadaba sbd Ina sonsa......

Wani wawan Mari am ya dauketa dashi a haukace yace"

Kinsan waye wannan???
Fatalwace ba mutum din gaske ba ya Dade da mutuwa da hannuna na kashesa shekaru sama da biyar dasuka wuce,
Wannan balai ne,shi masifa ne, marainiya zai maidaki gaba da bayanki Dan kuwa daga dad,mum harni wlh kinramu shikenan maraici zakiyi wannan alqawarinsa....

Jijjigasa fammah tayi da qarfi tana kuka sbd ganin ya haukace lokaci daya sai surutai yakeyi jikinsa na mazari tace"

Am pls stop all this Ni bana gane komai all I want is wannan tashin hankalin ya wuce muyi rayuwa kamar kowa cikin kwanciyan hankali,

My haydar bazai taba cutatarda familyna ba,
Shi ba mugu bane bazai muna komaiba,Yana Sona bazai cutatardaniba...

Tureta am yayi ya fice a dakin ko gani bayayi sbd tsananin tashin hankali,

Meye hadin nadeeyarsa da zanen hoton zaki?
Bazai iya rayuwa Babu nadey ba Koda ita din jinin Zaki ce,

Shin wannan da fammah ke fada zakin ne kuwa kokuwa shine yake qoqarin kasa fahimta
Gabaki daya qwaqwalwarsa ta toshe baya gane komai....

Kwalbar alcohol ya daga ya kwankwada kozaiji sauki Amma saijin yayi qwaqwalwarsa tasake hautsinewa ya daga kwalbar ya shanye
Atake yaji kansa ya kasa daukar nauyin balainta yafara ihu Yana wurgi ta komai.

Fammah dake rakube tasake fashewa da wani kukan kamar zata shide
Tabbas ko Basu mutuba tasan ita ko yanxu tana cikin tsananin maraici
Dad na kwance sai antayar,mum na prison ga am kamar ya haukace.

Sunan nadey yake Kira Yana ihu tareda farfasa Kaya duk yajiwa kansa ciwo qarshe nan ya zube cikin fasassun kayan da kwalba yafara wani irin kuka ahankali sbd duk qarfinsa ya qare itama ahankali tadawo kusadashi ta rungemesa tana cigaba da kukanta itama.


***
_6:36 am_

Ahankali ta bude idanuwanta dasukai Mata wani irin nauyi ga kanta da shima yayi Mata wani irin nauyi..

Ahankali tafara qoqarin tashi tana qoqarin tuna abinda yafaru jiyan,

Kallon dakin tahau Yi tana dafe kanta tareda saukowa gadon ta miqe tsaye tana sake qarewa dakin kallo sbd yanayin tsarinsa da haduwarsa tasan cewa ba qaramin wurine takeba.

Kan qaramin frame 'din dake aje gefen bedside lamp idanuwanta suka sauka taga zanen hotonta tayi saurin daukar frame din taga tabbas itace take tasan cewa am ne ya daukota
Ta aje cikin tsananin baqin ciki tahau dudduba kanta gabanta na tsananin bugawa tana tsoron idan ba wani abin yamataba.

Ajiyar zuciya tasake data ganta lafiya kalau Amma yanda zuciyarta ta kasa daina bugawa da sauri da qarfi yasa hankalinta tashi ta nufi qofa cikin sanda ta fito ahankali tana lalleqawa cikin faduwar gaba.

Wani dakin dake kallon inda ta fito yajiyo faduwar Abu tayi saurin kallon qofar tareda dafe zuciyarta dake bugawa da qarfi ta nufi qofar ta daga hannunta dake rawa ta tura ahankali tana Shiga.

Cak ta tsaya bakin qofar dakin tareda waro idanuwa tana dafe qirjinta da numfashinta na sarqewa sbd abinda tagani.

Tsaye yake gaban mirror daureda towel alamar wanka yafito,

Bayansa zuwa qwandar hannunsa dake daureda abinda a duniya tafi kowa sanin na mijintane Dan baitaba ciresa daga hannunsaba,

Ahankali idanuwanta suka sauka kan tabon cizon datasan itace tayi masashi haryazama tambo a hannunsa duk da tasan Idan yaso zaiyi amfani da magani ya goge tabon Amma yaqi qoqewa sbd Yana buqatar ganin tabon...

Girgiza Kai tayi da qarfi tafara ja da baya tana dukan kanta da qarfi tace"

Oh my God I'm loosing it...ciwona na hauka yadawo,,,why am I seeing tinz....

Faduwa tayi tana neman fita hayyacinta...

da sauri ya juyo Jin faduwar mutum da mgn abayansa
Yana juyowa Suka hada idanu

Atake ta zaro ido tana kure fuskarsa da kallo saikuma idanuwanta suka fara rufewa ta zube kwance a sume.

Cikin tsananin tashin hankali yayo kanta Bai tsaya komaiba ya dauketa yayi gado da ita ya kwantar Yana Kiran sunanta.

Fuskarsa ya hanga cikin mirror yaga asalin fuskarsace cikin tashin hankali yace"

Darn it..tariga ta ganni.
#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee36_*
Sake dafe kansa yayi cikeda damuwar yanda zata fuskanci zancensa idan ta farka sbd ta riga ta gansa Babu wata kwaskwarima a fuskarsa takuma tabbarda shine ba fatalwa to Yaya zata karbi alamarin??yaso shine yafara bayyana mata kansa batareda itace ta fara ganowa ba.

Ruwa ya dauko a fridge ya dawo bakin gadon ya zauna ya xuba ruwan a hannunsa ya shafa a fuskarta Yana Jin wata irin kasala na saukar masa.

Sake shafa Mata ruwan yayi tafara bude idanuwanta ahankali ta waresu akansa ta qurawa fuskarsa ido hawaye na cikowa cikinsu gabaki daya,
Tsoro,fargaba tareda tashin hankali sun daddaure jikinta sai wani irin rawa da jikinta keyi hawayen idanuwanta na gangarowa,

Batasan mezatayiba sbd sbd dai ba qaramin alamari bane take fuskanta yanxu na ganin Wanda Suka San ya mutu shekaru biyar baya a gabanta ace bazata sake somewa ko gama wannan tunanin batayiba idanuwanta suka sake lumshewa zata sume yayi saurin girgizata Yana cewa"

No no Not again please....

Ware idanuwanta tayi murya na rawa jikinta na daukar sabon mazarin tsoro da tashin hankali daqyar ta bude baki tace"

Ya...ya...yya yaaa...

Daga Mata Kai yayi tareda sake girgizata sbd ganin alamar Bata hayyacinta sbd tsoro Kuma kamar Bata Gama tabbarwa da shi din bane cikin wani irin yanayi yace"

It's me,nine I'm real ba fatalwa bane ban mutuba da Raina,
Ki dawo hayyacinki karki illata kanki nine da gaske ba wani gixo ba Ni din daine a gabanki......

Wani mugun yunquri tayi ta turasa baya tareda yin baya tana masa wani irin kallo idanuwanta jajir da fargaba tace"

Kana cewa baka mutuba Kaine Kaine,
Kana tunanin gwaninta kayi ko dadi zaka sani da fadar hakan??
Qwalqwalwata bazata iya daukaba,
Ciwon haukana dawowa zaiyi I'm only imagining this,,,,ya Allah karka Bari na sake dandanar ciwo da radadinda ke cikin hauka....

Ya Allah ka tayardani daga wannan mafarkin danakeyi....wlh I'm going insane....

Da qarfi ya damqota tareda girgiza ta da qarfi ya Kira sunanta sbd ganin yanda jikinta ke rawa sosai tana surutai da qarfi....

Qwacewa take sakeyi tana neman ihu da fixgewa ya sake riqeta Yana Kiran sunanta hankalinsa na tashi Saidai Sam batamasan yanayiba gabaki daya ta fice hayyacinta..

Jin zuciyarsa na neman karyewa da halinda tashiga yasashi rungumeta da qarfi cikin jikinsa tareda kwantarda kansa cikin wuyanta Yana Kiran sunanta da wata irin muryar sanyin jiki kamar zaiyi kuka sbd gab yakeda zaucewar shima matuqar wani Abu yasake samunta.

Tabbas yasan Dole zata gigita da ganinsa sbd ana maganar mutuwane,
Tasan ya rasu shekaru sama da biyar saikuma tagansa yanzu Kai tsaye Dole hankalinta zai tashi.

Yanda ya matseta a jikinsa Yana Kiran sunanta ahankali tun tana fixge fixge hartayi sanyi jikinta ya saki gabaki daya alamar ta sake somewa.

Lumshe ido yayi tareda girgiza kansa Yana tallafota gaba daya yasake maidata ya kwantar Yana mamakin yanda take somewa ita tunda can.

Wasu ruwan yasake shafa Mata
Tareda tsayawa bakin gadon yayi folding hannuwansa zuciyarsa duk a hargitse.

Ahankali tasake bude idanuwanta ta kafesa dasu wannan karon ko motsi kasawa tayi ta lumshe ido tasake budewa ta sauke masa
Take taji zuciyarta ta karye sbd yanzu Kam tabbas tasan shi din ne Babu maganar fatalwa kokuma hauka..

Wasu hawayen dataso ruqewane Suka gangaro ta gefen idonta sbd tasake tabbatarda da dai shi dinne Yana raye.


Kasa cewa komai tayi sbd wani mugun nauyi da dukkanin gabban jikinta suka dauka sbd mutuwar jikin data sameta,
Wani irin sanyi qasusuwan jikinta suke sake dauka akaro na farko a rayuwarta dataji zuciyarta ta toshe da wani irin nauyin gaske Wanda ya Hana bakinta budewa bare magana.

Fuskarsa take sake qarewa kallo,
Haskensa da kyawunsa na nan saima qaruwa dasukayi sbd hutu da Jin dadin daya samu,

Ahankali ta sauke kallonta a gefen wuyansa zuwa kunnensa na dama dasukayi duku tareda alamar qonuwa Wanda tabonta yakusa bacewa gabaki daya wasu sabbin hawaye suka silalo Mata.

Ahankali ta dafa ta tashi zaune tareda dauke idanuwanta daga kansa ta sauko gadon yanabin jikinta dake wani irin rawa a boye Wanda ya tabbatarda na ganinsane.

Fuskarta ya kalla yaga yanda yanayinta ya sauya sosai Babu wata rahama a fuskar tata saima hawayenta data share tana miqewa tsaye daidai agabansa.

Am in trouble""yafada tareda sake ajiyar zuciya ya matso zai kamo hannunta tayi baya ahankali batareda ta dago ta kallesaba ta juya zata fice ya riqe hannunta tareda dawo da ita baya zaiyi magana ta rigasa da qwace jikinta cikin qoqarin danne halinda take ciki tace"

Please Ina buqatan komawa inda ka daukoni.

Kallonta yayi da fararen idanuwansa tareda dawowa gabanta ya kalli fuskarta dake sunkuye yace"

Ina kike maganar komawa kenan???

Inda ka dauko ni Dilla's.

Sakinta yayi tareda mayarda fuskarsa yanda yasaba wato a tamke shima ba sauqi Kai tsaye yace"

Bazaki koma can ba infact ko Ina bazaki komaba Ni nasan inda zan kaiki.

Dagowa tayi wannan karon takasa riqe tarin baqin cikin dake cin zuciyarta kamar zata mutu tace"

Nace gida zankoma so inaga Banga wani dalili ko iko dakake dashiba na hanani besides karka manta satoni kayi Wanda Ni bansan manufarka akan hakan ba and inada damar dazansa a Kamaka akan hakan.

Idanuwansa ya zuba Mata cikeda yanayi na tsananin mamakinta akaro na farko dayaga zallar fushi Mai qarfi atareda ita.

Kina tunanin banda wani ikon hanaki kokuma kina tunanin Zaki iya sakawa a kamani din sbd kina taqama da me????

Cikin fushi tace"

Koma Dame nake taqama it's none of your business,
Kai me kake taqama dashi dazakazo bayan shekaru ka tsaya gabana bakaji kunyar Allah da tsoronsa ba na barin matarka dakayi da 'yan uwanka tsawon shekaru kana raye baka nemesu ba,baka dawo garesu ba,
Bakasan irin halinda suka shigaba sbd rashinka,
Bakasan ya rayuwa tayi musu tsanani ba sbd Babu kai....rawa muryarta tafara Yi hawaye na ciko idanuwanta tace"

Dama basuda mahimmanci da wani matsayi a rayuwarkane daka zabi barinsu Babu waiwaye kokuwa dama lokacine ka dibar musu a rayuwarka,

Meye laifina Dana mahaifina daya bakani ko kuwa munzama takurane a rayuwarka????

Meye laifin babana Dani kaina???
Idan duk munada laifi damuka zabeka fiyeda kowa meye laifin baby z ita????

Sai alokacin ya matsota sosai Yana kallonta da idanuwansa dasuka rikide ja sosai ya daga hannu zai kamota tasake ja Baya cikin daga murya tace"

Enough..enough Mr haydar,,,ka daina kusantoni da yawa sbd haryanzu ban manta da darajataba ta 'ya mace Kuma musulma....

Ba zato ya jawoto jikinsa ya matse tareda zuba Mata jajayen idanuwansa jikinsa na rawa sbd bacin ran zancenta yace"

Shi wancan da kike tare dashi a gidansu shi musuluncin Bai hau kansa bane????
Wlh bazaki sake zama a gidanba idan Kuma kinason kwada qarfin ikon danake dashi ne akanki da rayuwarki ki gwada zakisha mamakina sbd inanan bawai canzawa nayiba.....


Fixgewa tayi itama cikin Hana kukanta zuwa tace"

Bana magana akan rayuwar kowa da canzawar kowa anan Ina magana akan rayuwatane da abinda Naga damar Yi da Wanda Naga damar bari,
Idan kana maganar baka canza ba to Ni na canza ba Nadiya bace wannan ND NOAH ce...and stay the hell out of my life.....

And bana buqatar ganin qarfin iko ko dukiyan dakake dashi sbd dama Abu ne nasa kaina sbd tunanin anrabani da abinda nakeso fiyeda tawa rayuwar Ashe bansaniba shine ya rabu Dani Dan haka Ni kaina daga yau na fita daga fadanda Babu ruwana zanje na fuskanci Wainda suka cancanci qaunata da lokacina.

Tana Gama fadar hakan ta fice da gudu sbd wani irin kuka Mai tsananin nauyi da qarfi dakeson zuwan Mata tana dannesa numfashinta har sarkewa yakeyi jikinta Babu inda baya rawa.

Kasa motsi yayi sbd duk jijiyoyin jikinsa sun daure da mamakinta da fargabar tashin hankalin maganganunta dake bayyanarda tsantsar radadin baqin cikin barinta datake ganin yayi.

Securities Basu wani hanata fitaba tana fita ta tari wata taxi data kawo ta fada kawai sai alokacin tasake wani irin kuka Mai tsananin cin Rai da damuwa tareda ciwon abin datake ji cikin ranta.

Har Sukayi nisa Bata saniba Saida yasake tambayar inda zai kaita ta bude baki daqyar tareda fada masa tana share hawayenta tareda qoqarin barin kukan duk da tasan bazata iya barinba.

Yana Isa qofar mansion din ta fito ahankali tareda ce masa ya jirata tafito.

Ciki tayi tana qoqarin maida kukan dayake sake taso Mata sbd fammah data hango tsaye jikin qofa tana knocking qofar side din am tana kuka sosai kamar zata shide.

Kasa riqe nata itama tayi tasakesa tareda wucewa ciki da gudu tanajin inama duk shekarun nan a gaban babanta ta zauna tayisu da tabbas bazata cutatu yanda takejin ta cutatu yanzu ba.

Sama ta haye tahau hada duk wasu kayanta tafara jawo luggage dinta tana share hawayenta dasuka qi tsayawa a Palo taci Karo da am da fammah tsaye dukkaninsu Babu Wanda baibata tausayiba take zuciyarta tasake karyewa ta silalo hawaye masu radadi ta rintse idanuwanta ta bude saitaji takasa kallon fammah ga am da zuba Mata idanuwansa dasuka shanye sukai jajir a dare guda ya lalace yakoma tamkar asalin Dan giyar dayayi shekaru ashirin Yana sha,
Hawaye ne cike da idanuwansa Saidai Basu saukoba sbd muguwar karayarda zuciyarsa da gangar jikinsa suke ciki,

bude baki tayi daqyar ta furta"

I'm leaving......

Ba zato qafafuwansa Suka sare ya zube gabanta tareda riqo qafafuwanta cikin wani irin yanayi na kuka da tausayi yace"

Baby Dan allah karki barni wlh bazan iya rayuwa Babu keba,
I can't live or survive without you,
Karki tafi kibarni a wannan halin I will die if you leave me.... please baby idan na Miki wani laifi ne forgive me Dan Allah please baby don't leave.....

Kuka tasake sbd akaro na farko daya

Please Login or Register in order to submit comment