Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanyin murya tana dafa goshinta dake nade da bandage cikin tausayin 'yar uwarta.

Kwana biyu tashin shima yayi sauqi tasake warwarewa Saidai wasu irin qaidojinda Dr sayyid ya shimfida akan lafiyarta kafin ya sallamesu Suka koma gida cikeda kewarsa sbd sosai yake bawa Nadiya kulawa Kuma sosai hakan yayi tasiri a zuciyar dukkaninsu musamman dattiya dahar wani sabo sukayi Dan duk zai koma gida idan yazo sai Dr yabasa dubu guda yace yahau acaba.

Iya talatu ma girman dayake Bata Wanda Sam Bata samuba daga yayanta daga Nadiya saishi yasa take jinsa matuqa.

Zainab kuwa dama tuni takamu Dan baqaramin burgeta Dr sayyid yagamayiba.

Zainab ce tayi musu gyaran dakinsu tashare ta goge komai tareda fesa turare takaiwa nadiyar ruwa har bayi taje tayo wanka.

Tana cikin shafa Mai yashigo dakin idanuwansa Suka sauka kan daurin qirjinta datake qoqarin saka hijabi da sauri har jikinta na rawa.

Qarasowa yayi ya nufi bakin wardrobe ya zare rigarsa ya dauki towel dinsa ya fice.

Miqewa tayi ta dauki rigarta ta bacci Mai tsantsi doguwa har qasa tasaka bayan ta fesa spray.
Har safar qafa tasaka sbd sanyi ta sanya baqar wula ta rufe kanta tareda cusa gashinta ciki Dan tunda zainab tasa Mata relaxer gashinta yayi tsayi sosai sbd miqewar dayayi.

Sallar ishai tayi tayi kwanciyarta agurin tareda qudundunewa cikin hijabinta sbd yau sanyi Sosai takeji sbd asibiti kullum dakin datake dumi  Dr sayyid ke saka masa shiyasa yanzu har cikin qashin bayanta takejin sanyin har gabobinta na fara Mata ciwo.

Yana shigowa dakin yaga yanda ta dunqule waje daya saiyaji kamar hankalinsa zai tashi Amma ya basar yayi duk abinda zaiyi yaje ya rufe gida  yashigo ya rufe dakin ya kashe wuta ya nufi katifa saiya kasa Hawa ya tsaya Yana jujjuyo zancen Dr sayyid akan sanyin daya kamata gashi yanda yake Jin fitar numfashinta yanxu yasan ciwon ne yakeson tashi tunda dr yace ko kadan daga yanxu kar abari sanyi na shigarta.

Shiru yayi kansa na daukar zafi haryaji tana fidda wani irin Nishi alamar dai ciwon ya dawo Mata.

Cikin duhun Kai tsaye ya sunkuceta gabaki dayanta ya kwantar kuryar katifar tareda zare Mata hijabinta ya kwanta tareda bude musu jibgegen bargonsa Mai laushi.

Rawa jikinta keyi sosai na sanyin dake ratsa qashin jikinta ganajinsa kusada ita sosai gashi dama baya kwana da riga ajikinsa.

Jin rawar jikin nata yayi yawa da nishinta yasa ya jawota cikin jikinsa ya rungume tareda zagayeta ya rufe a qaqqarfan jikinsa ga dumin bargo

Baa wani jimaba sanyin jikinta yafara raguwa 'dumi na shigarta sosai ahankali tafara dawowa normal Saidai yanayin yanda qirjinta ke manne da nasa yasa takasa motsi sbd kunya da tsoro ahaka bacci ya dauketa Dan dama akwai maganin bacci sosai acikin magunanta Dan harda hutu Dr sayyid yakeson tasamu.

Bai bacci ba shiru yayi da ita cikin jikinsa akaro na farko yakejin kamar rayuwarsa tasamu nutsuwar datake buqata,
Wani irin sanyin Hali yaji na shigarsa sbd yanda dukkanin gabobin jikinsa suke karbar baquntar jikinta a nasa.

Da asuba koda ya farka bacci takeyi sosai wannan karon hannuwanta zagaye suke da qugunsa hularta ta zame ya qurawa fuskarta ido sbd nepa daya farka yaga akwai.

Zameta yayi ahankali tareda gyara Mata bargon ya sauko ya nufi electronic cattle dinda ke dakin ya zuba pure water hudu ciki ya jona ya fice zuwa alwala.

Kusan tareda kawun Suka fito sallah sbd sallar asubar yanxu tashiga kawun batareda yasaniba ta hanyar saka idonsa akansu.

Harya dawo bacci takeyi ya juye ruwan a flask yasake zuba wasu yazo bakin katifar ya zauna tareda Dan buga pillow ahankali.

Cikin yanayin bacci dake cinta ta bude idanuwanta tareda mayarwa ta rufe
Saura kadan zuciyarsa ta fado da hakan datayi Dan kuwa har wani tari ya miqe Yanayi sbd sarqewar numfashi daya kamasa.

Kyaleta yayi ya hawo katifar ya kwanta tareda rufe rabin jikinsa kawai Yana 'dan qara gyara muryarsa kadan sbd yawun dasuka sarqesa sbd qafafuwansu dasuka hadu cikin bargon.

Lumshe idanuwansa yayi ya rufe yanajin yanda dumin numfashinta ke sauka a wuyansa yana dumama dukkanin jikinsa har numfashinsa na slow.

Kamar Wasa sai baccin dabai wani yiba cikin Daren ya daukesa ahakan.

Qarfe bakwai maganin yadan saketa ta bude idanuwanta ahankali tana sake gyara kwanciyarta cikin jikinsa.

Da sauri ta qarasa bude idanuwanta baccin na sakinta gabaki daya tayi saurin matsawa baya tana kallon fuskarsa datayi wani irin kyau dayana baccin,

Bakinsa dayayi wani Dan ja kadan ta kalla zuwa dogon hancinsa da gashin girarsa dake kwance kamar na mace,

Tabbas farine sosai dayake sirke da 'dan yellow na asalin mutan Igbon asali Saidai shi Sam baya wani tara sumar Kai saita gemu Wanda yake bana ustazanciba saina tsabar qwarewa a ta'addanci.

Karo na farko data saki murmushi bayan qare masa kallo.

Ahankali ta sauko tana qoqarin daukar hijab taji yace"

Ki juye ruwan cattle din kiyi amfani dasu idan kika taba ruwan sanyi wlh saina karya dogon wuyankin nan.

A matuqar tsorace da kunyace ta juyo ta kallesa taga har lokacin idanuwansa a rufe suke kenan duk Yana saneda abinda takeyi tun tashinta.

Cikin tsananin kunya da rawar jiki ta dauki cattle din ta fice tana rufe jikinta da hijib sbd sanyi.

Da ruwan zafi sosai tayo alwala tadawo sbd cikin gidanma tsit duk Basu fitoba sbd sanyi.
#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee21_*
Tana komawa dakin ta nufi dardumar sallah saitaga wata sabuwar safa akai ajiye Mai tsananin kauri,

Dagowa tayi ahankali ta saci kallon gefensa taga alamar yatashi kenan shine ya ajiye Mata safar.

Dauka tayi tareda zama tasaka kafin tana miqe ta tayarda sallah.

Tana gamawa saitayi zuru da idanuwa tanason fita aiki Amma ganin yanda ya matuqar hade fuska sai tsoronsa ya taso Mata tafara kame Kamen son fita.

Miqewa tayi ta nufi bakin qofa tana qoqarin ficewa taji anfixgo hannunta tareda daga hannu zai sauke Mata lafiyayyan mari sai kawai ya kasa ya tsaya da hannu a sama ransa amatuqar 6ace.

Saurin rintse idanuwa tayi cikeda tsananin tsoron yanda Marin zai fasa bakinta saitaji tsit Marin bai saukaba.

Ahankali ta bude idanuwanta dasuka fara sauka Kam hannun dayake sama Amma baiyi marinba,

Kan fuskarsa take qoqarin mayarda kallonta ya rintse idanuwansa cikin bacin Rai tareda sakinta Yana fitarsa numfashi Mai zafi da takaicin abinda yasa yake biye Mata wani lokacin,

Cikin muryarda ta jima batajiba tasa ta tsantsan bacin Rai yace"

Daga yau bayan wanka da alwala kika Kuma fita dakin nan saina raba qafafunki biyu.

Sakin hannunta yayi yakoma ya kwanta tareda rufe idanuwansa kamar bashi yatashi yanxuba..Saidai kallo daya zakai masa kasan ransa amatuqar bace yake.

Sanyi jikinta yayi tadawo a sanyaye ta zauna kan daddumar sallah tareda dunqunqunewa cikin hijabinta.

Hakan sai kawai yaqara Bata ransa ya juya Mata baya tareda shigewa bargo ahaka bacci yasake daukarsa.


Qarfe goma ya farka yaganta kwance aqasa ta dunqule waje daya bacci ya dauketa.

Fuskarta ya qurawa ido daga idanuwanta har zuwa 'dan madaidaicin bakinta.

Nadiya ba fara bace sosai saidai Kuma ba baqa bace hakama ta 'dan Dara Wainda ake cewa chocolate haske danma yanayi na wahalar rayuwa da Rashin hutu yaqara canxa kalar fatarta,
Tanada dogon hanci sosai da fararen idanuwa masu Dan girma,

Sake kallon bakinta yayi tareda rintse ido ahankali ya dauke Kai tareda miqewa ya sauko.

Ahankali ya durqusa ya zare Mata hijab ya dauketa ta yanda bazata tashiba ya kwantarda ita kan katifa yana kallon fuskarta ta bude idanuwanta Suka qurawa juna ido akaro na farko kowannensu bai dauke ido ba.

Batareda tasaniba ta qanqame hannuwansa dake jikinta tanajin wani Abu Mai girma cikin zuciyarta dabatasan meyeba Saidai hawaye kawai dataji tanason zubarwa kozataji nauyinsa ya ragu,

Idanuwanta na cikin nasa hawaye Suka ringa gangarowa ta gefen idanun tana sake qanqamesa.

Hannunsa daya taji akan fuskarta yasa ta lumshe idanun da batasanma tanayin hakanba.

Bata bude idanuwantaba taji saukar hannun a wuyanta cikin wani irin sanyi
Batasan lokacin wani Nishi Mai qarfi ya qwace mataba Wanda yasa qirjinta yin sama ya mannu sosai da qirjinsa dake daf da nata gurin fitarsa Wanda hakan yasa qarfin jikinsa saki ya matseta jikinsa Yana sake cusa hannunsa cikin wuyanta zuwa bayanta.

Rufe idanuwanta tayi hawayen cikin nasake gangarowa tana Jin yanda hannuwansa suke zagaye da ita tanaji qarfin gabobin jikinsa na kashe 'dan qarfin nata gabobin dabasuyi ko kwatar nasaba.

Shiru sukayi ahaka ko motsi Babu Wanda yayi sbd duk sun dawo hayyacinsu daga Dan shagaltar dasukai Saidai har lokacin jikinsu a hade yake bai saketaba itakuma Bata motsaba tananan cikin jikinsa.

Dumin jikinsa Dana bargon yaqara sata Jin bacci bacci Saidai Rana tayi batason yi.

Sun Jima ahaka idanuwansa a lumshe bai budeba Saidai tasan ba bacci yakeba.

Harta fara lumshe ido zatai bacci taji ya zame ya sauka tana kallo ya dauki brush da toothpaste ya fice.

Ajiyar zuciya tasake sai alokacin tsananin kunyarsa tafara dawo Mata taji kamar tanason rasa kunya da control na kanta ne idan Yana tareda ita.

Saukowa tayi jiki a mace da kunya itama tadauki brush ta dauki flask ta fice.

Duk su iya talatu na tsakar gidan tai musu alamar gaisuwa tareda zuba ruwan zafin dake cikin flask ta sirka tayi brush tana gamawa ta nufi dakin zainab dake Shan waqa a wayarta tana gugar kayanta ta zauna gefen katifarta tana Mata alamar taje ta Dora abinda za'a karya dashi ita Yaya Zaki ya hanata daga yau.

Daqyar zainab tagane Mai take nufi sbd tun can dah Nadiya Bata damu da bayani ba shiyasa Sam bazaka gane Bata mgn ba idan Kai baqone sbd koyaushe Bata dogon zance bare tayi maka alama da hannu.

Wani ihu zainab tasaki tana cewa"

Iyye yarinyar nan kice mijinki ya hanaki aiki wahala sbd tsaro..?

Miqewa nadiyar tayi da sauri zata fice zainab ta riqota tana cewa"

Ke Yar bebiyar Yaya Zaki tsaya kiji to tunda yafara ji dake wlh kiyi sauri kisamu ciki kozamu qarasa samun yanci da Jin dadin duniya a gidan nan.

Zaro ido Nadiya tayi saikuma zancen yabata masifar kunya ta qwace tareda nufar qofa zainab takuma Shan gabanta tana riqo hannunta tace"

Ok let's be serious,wlh Nadiya yakamata kifara zagewa kiyi rayuwar auren,Ina nufin kifara aikinki kamar yanda kowace matar aure keyi a gidan mijinta,
Dukkaninmu Muna tsoron Yaya Zaki Amma yakamata ki rage tsoronsa ko kicire tsoron kwata kwata sbd ke matarsace Dole aringa ganin banbanci.

Zuba Mata ido Nadiya tayi cikeda mamaki da ganin wautar maganarta sbd Babu ranar dazata daina tsoronsa arayuwarta.

Riqo hannunta zainab tayi cikin wani irin yanayi tace"

Nadiya nikadaice 'yar uwarki Kuma tamkar qawa agareki
Ina fada Miki duk abinda yakamatane sbd zai iya yiyuwa wata Rana bananan bakida Mai fada Miki adaidai lokacinda yakamata ace kinada Mai fada mikin Wanda nasan alokacin zakiyi maraicina fiyeda kowa Nadiya,

Sanyi jikin nadiyar yayi ta kalli zainab din saitaga idanuwanta kamar sun ciko sai itama nata idanuwan Suka ciko ta riqo hannun zainab din tanajin kamar tsoron maganar zainab din nashigarta.

Murmushin qarfin Hali zainab tayi tace"
Nadiya Dan Allah kiyi amfani da matsayinki a gurin Yaya Zaki ki kawo sauyi a rayuwarmu gabaki daya muda iyayenmu sbd gyaran zai faro daga kansa ne to abin zaizo da sauqi,

Nadiya kimin alqawarin kulada iyayenmu karki Bari su mutu a kan turbar dasuke ayanxu.??

Rungumeta Nadiya tayi tana girgiza Mata Kai Dan jitake hankalinta na tashi tsoro na shigarta,

Batasan meyasa zainab ke Mata wannan zancenba Saidai tasan batason rabuwa da zainab itama,
Duk Wanda ke sonta takejin sanyi agurinsa tafiya sukeyi suna barinta wane irin baqin jini ne gareta?

Mamarta ta rasu Randa ta haifeta,
Umman Zaki dake tsananin qaunarta ta tafi tabarta,
JJ ma dayake matuqar qaunarta ya tafi,yanxu ga zainab na Mata wainnan zancen marasa dadi.

Sakin zainab din tayi zata miqe
Zainab ta saki dariya tana cewa"

Ke duk da Wasa nake Miki sbd kisaki jiki kiji da aurenki wlh Nadiya ke local ce kisaki jiki ki dinga haukata Yaya Zaki da shagwaba kiga yanda duk zai kwashe makamansa daga dakin nan yakaisu waje ya zubar.

Ajiyar zuciya Nadiya ta sauki Jin Wasa zainab din takeyi ta miqe tareda hararar zainab din ta fice tana murmushi.

Tana shigowa tagansa zaune Yana waya tasan Kuma breakfast yake jira tunda taga ledar bread a gabansa dashi yashigo kenan.

Flask ta jawo tareda kayan tea ta ajiye gabansa ta zauna ahankali tareda hada masa tea din Mai kaurin gaske sbd Sam arayuwarsa bayashan sugar.

Miqa masa tayi tareda fara qoqarin miqewa yayi Mata wani kallon qasa qasa
Komawa tayi ta zauna tareda hada nata tea din kadan tafara Sha.

Kusan tare Suka gama ya miqa Mata magani ta karba ta shanye ta tattara kayan ta fitar ta dauki bread ta dibi kayan tea din taje takaiwa zainab Wanda zata hada musu itadasu baba tadawo dakin.

Gyaran dakin tahau Yi sbd yatafi wanka.
Shimfidar tafara gyarawa tsaf ta goge komai tayi shara ta fesa turare tana qoqarin tubewa yashigo da sauri ta mayarda rigarta tana kame kame.

Saidaya shirya ya fice tukuna ta tube taje tayo wanka tadawo ta shirya cikin doguwar riga Mara dogon hannu cikin Wainda ya siya Mata lokacin jinya ta fesa spray.

Abincin daza'a dafa ta Diba taje takaiwa zainab tadawo tana Jin jiri sbd maganin baccin dake cikin magunanta.

Bakin katifa ta zube take bacci yayi gaba da ita.

Bayan azahar sosai ta farka taje tayo alwala tayi sallah tana idarwa Yana shigowa hannunsa daukeda ledojin takeaways.

Ajewa yayi ya zare rigarsa ya fice waje Yana murza daurin qundarsa sbd wasu yara da aka kamo sun sassare yaronsa harya rasa hannunsa daya.

Yana fita qofar gidan gurin yayi mugun tsit bai tsaya komaiba ya dauki babbansu wani mahaukacin Marin dayasa hancinsa 6arewa da jini.

Goran hannun Nanu ya karba ya bugi qafafunsa atake ya zube qasa Yana roqansa da cewa"

Sarki Dan allah kayi hakuri kabarni da Raina wlh bansan yaronka bane da bazamu tabasaba muma ai yaranka ne wlh,
Dan allah sarki,
Dan allah sarki kayi hakuri
Kayi hakuri karka kasheni....

Wani bugu yayiwa bakinsa Saida haqoransa biyu Suka zubo qasa tareda jini da yawu...

Goran yasake dagawa ya bugi hannunsa,
Ihu yakeyi Yana neman afuwa da yafiya Amma dukan dayake masa bayan jini Babu abinda ke fita gashi guri yacika Babu Mai ikon cewa qala.

Dattiya daya dawo yaga guri yayi mugun cika yafara tambayar lafiya Yana ratso mutane Yana kawowa daidai Zaki ya daga Goran zai buga a tsakiyar kan wancan
Dattiya ya riqe goran

Ganin fushi da bacin ran dayake tareda zakin yasan yau antabosane a mugun wuri
Kai tsaye yace"

Bantaba shiga harkar ikonka ba a kan sarautarka sai ayau
Ayau dinma nashigane ba amatsayin kawunkaba sai amatsayin mahaifin matarka,
Ka kyalesa haka karkayi kisa sbd baka taba yiba idan kayi yanxu halinda 'yata zata shiga nake dubi.

Kallon kawun yayi cikin ido yaga tabbas yau ba kawunsa yake ganiba mahaifi uba yake gani Wanda keson Kare martabar auren 'yarsa.

Sakin gorar yayi akaro na farko da shima ya saurari maganar kawun shima baa matsayin kawunsaba Saidai amatsayin mahaifin matarsa.

Kallon Nanu yayi da jajayen idanuwansa yace"

Kasan abinda zakayi daganan sa Kai.

Da sauri Nanu yace"

Angama sarki.

Juyawa yayi yashige cikin gidan duk hannuwansa da jikinsa jini ya Dan batasu.

Akaro na farko dayaji bayason tagansa da jinin wani ajiki da hannuwansa ya tsaya bakin qofar dakin yakasa shiga.

Juyawa yayi yai cikin gidan zainab na aikin girki tagansa ya shigo jina jina tayi saurin dibo masa ruwa a bucket takai masa bayi saidata fito gabaki daya yashiga Yana cewa"

Kice takawomin towel da wani threequater.

Yana shiga ya rufo bayin.

Da sauri taje ta fadawa Nadiya saqonsa tana dariya qasa qasa tana cewa"

Wayyo love dadi wlh
Idan kin shiga bayin ki goge masa jiki kisaka masa wandon......

Da sauri Nadiya ta tureta tana miqewa ta dauki towel da wandon dayace ta fice.

Ahankali ta qwanqwasa qofar bayin.

Budewa yayi kadan ta miqo masa ya zuro hannu zai karba ya hango kawo na qarasowa da sauri ko gabansa baya kallo nadiyar yake kallo masifa nacinsa bakinsa sai motsi yake yazo yasauke mata Dan yasan Zaki ne Sarai a bayin.

Ganin hakan maimakon ya karbi towel din saiya riqo hannunta ba zato yajawota ciki ya rufe qofar.

Dattiya kuwa sai jinsa yayi ya jefa qafa cikin robar ruwan zafinda zainab tagama wanke shinkafa dasu masu shegen zafi.
#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee22_*
Wani wahalallen ashar ya jefawa zainab tareda yin gefe Yana jefa qafa cikin tsananin azaba Yana sake daga murya gumi na karyo masa.,

Da sauri iya talatu tafito daki jin muryarsa Yana zubo ashar kamar zaiyi kuka,

Tsayawa tayi kallon yanda ruwan daya zubar gurin fidda qafarsa suke hayaqi ga qafarsa riqe ahannunsa sai zuba fada yakeyi zainab na tsaye tana boye dariyarta cikin fada iya talatu take kallon zainab tana cewa"

Zainab yanzu uban naki kika qona da ruwan zafi Kuma kina tsaye kina kallo????

Ruwan sanyi ta debo da sauri takawo masa ya jefa qafarsa ciki da sauri sai alokacin yaji zufansa yadan taqaita ya kalli talatun yace

"nagode talatu kinji da kika bani ruwan sanyin nan na jefa qafata sbd ke kinsan mahimmanci na a cikin gidan nan,

Ita wannna ja'irar Mai kamada amaryar aljanu tana kallo na nufo ruwan zafin nan taqi dauke
Nafada ciki Kinga ta tsaya tana kallona da idanuwanda bansan na uban waye ta gadoba Dan banidasu kaf zuriata,

Ita Kuma waccan bebiyar Mai kamada bebin roba tana kallona Ina zuwa wancan qaton marasa kunyar yajata zuwa cikin bayi sbd kowa a gidannan ya rainani baa ganin girmana ga dattiyan banza......

Sa alokacin iya talatu ta katsesa tana watsa masa kallon raini da cewa"

To ita wannan anji ta qonaka ita waccan ta bayi meye ruwanka da abinda yake faruwa,
Wlh dattiya idan baka dauke idonka akan alamrin Zaki ba saiya makantaka wata rana Dan shi inda aka haifi kunya ma baisaniba bare cikakken sunanta da ma'anarta,
Idan ka matsa masa da wannan qananun idon naka wlh wata Rana gabanta sai turmushe maka 'yar taka kaga daga ranar zuciyarka ta buga Ni 'dan ciwon bakinda dama kake sani na huta shikenan daganan har tsohon ciki zakaga nadiyar na yawo dashi cikin gidan kana daga kwance kana jinya abanza.

Cikin zafin data qara masa da maganganunta yace"

Dama talatu tun shekarun bayan haihuwar zainab nasan kindaina so na bakya kaunar ganin Ina yawona Ina walwala kinfison ki ganni a nakashe to Allah dayayini shikeson ganina cikin walwala saiki hadiyi zuciya ki mutu talatu.

Zainab ya watsawa mugun kallo yace"

Bar nan Mai kama da dangin uwarta.

Da sauri ta wuce tana mamakin baban nasu harda masifarsa tasa taji ta matsu Nadiya da zakin su kusanci juna kozai samu salamar wannan masifar dayasa kansa.

Shima miqewa yayi Yana dingisa qafa ya nufi qofar fita Yana masifar gwara yaje gurin amininsa Dan uwansa mal idi ya shafa masa magani danshi kadaine yasan mahimmancinsa yake qaunarsa
Shi wlh Zaki kashesa yakeson yi da sauran kwanansa,
Banda Rashin sa'arsa ace agabansa ake masa abubuwa da 'ya Kai wlh Allah ya tsinewa shedanun Lagos dasuka qullo masa wannan balain ya dauka ba gammo.

Da harara iya talatu tabisa kafin Takoma dakinta tana nata kalar mitar.


Acan ciki kuwa tunda ya jawota ta rintse idanuwanta jikinta ba inda baya rawa numfashinta kuwa kamar zai 6allo qirjinta sbd bugawa da sauri.

Batareda ya kalleta ba ya zari kayan dake hannunta yasaka tareda karbar towel ya ratayo a wuyansa harzai fito yabarota saiya tuna kawun na tsakar gidan qila saiya daukota cak ya fito bayin da ita.

Sbd tsananin kunya kuka kawai ta fashe dashi harsuka Kai daki Allah ma yasa ba kowa tsakar gidan sai zainab wadda itama kallo daya ta musu tayi saurin komawa daki hartana tuntube sbd mugun kallonda zakin ya Aiko Mata.

A katifa ya ajiyeta ya juya kamar bashiba yahau shirinsa Yana gamawa ya zauna ya jawo takeaways dinda yashigo dasu ya bude yasha fruitssalad ya dauki wayarsa ya fice yabarta har lokacin kuka takeyi.


Bayan fitarsa samun kanta tayi dajin haushin abinda yamatan sbd har cikin ranta batason yanda yake wasu abubuwan Dan takalar babanta dukda dai tasan sunsaba tun Yana yaro tun ummansu nada Rai.


Da daddare koda yadawo tayi bacci a qasa ya dauketa yafara sata qurya ya kwanta ya lullubesu sukai bacci.

Washe gari qafar babanta tayi jajir alamar dai qonuwa ta tabbata a qafarsa saita samu kanta da nuna masa fushinta sbd ko kallonsa Sam ta daina idan Yana Dakin ficewa takeyi ta nufi cikin gida duk da Bata aikin komai yanzu zainab ce keyi wani lokacin Kuma iya talatu.

Kwana biyu da hakan tana zaune cikin dakin tana cire farce da Reza saigashi yashigo dakin Yana waya faduwarda gabanta yayine yasa rezar yankarta sosai
Ta saki rezar da sauri tana dafe gurin sbd jinin dake zubowa sosai.

Juyowa yayi yaga jini a hannunta bai kashe wayarba ya ajiye tareda riqo hannun da qarfi cikin fushi yace"

Ke wace irin wawuyan yarinyace?

Idan baki daina wannna shashancinba nakusa karya wuyanki.

Qwace hannun tayi ahankali tana neman zamewa ya fizgota da qarfi tareda matseta a bango zaiyi magana cikin tsananin fushi ta dago idonta yashiga cikin nasa
Ya rintse ido da cikin wani irin sanyi yace"

Idan kika motsa daganan zan mareki.

Kallonsa tasakeyi har lokacin hannunta na cikin nasa.

Hawayen datake riqewane Suka gangaro Mata ahankali tafara kuka tareda sauke kanta qasa a qirjinsa dayake matse da ita a bango.

Kasa motsawa yayi yanajin kukanta na shigarsa
Ahankali ya saki hannunta ya tallabota jikinsa gabaki daya ya rungume sai kawai itama ta qarasa fashewa da kuka tana qanqamesa.

Sun Jima ahaka Saida tayi shiru Dan kanta kafin ya saketa tareda riqo hannunta ya dauki flask Suka fito har tsakar gida yakalli zainab data saki baki da hanci tana kallonsu yace"

Ke so sirko ruwan nan.

Karba tayi ta surko a Kofi takawo tana zubawa Yana wankewa nadiyar hannu.

Iya talatu dake aikin kayan matanta a tsakar gidan ita ko kallo Basu ishetaba aikinta kawai takeyi,

Dattiya dake zaune miqe da qafa Yana fifita qafarsa qara gudun maficinsa yayi Yana Harare Harare dayaga dai bazai iya hakuriba a qule yace"

Ke zainab banafason barnar ruwan nan idan rijiyar gidan ta qafe waye zai Nemo masu yasarta idan baniba.

Babu wanda ya tankasa Suka gama suka bar gurin still hannunsa na riqe da nata Zainab tabi bayansu da murmushin farin cikin tana langabe Kai suna shigewa ta daka wani tsalle tareda cewa"

Yesssssss.

Tana juyowa taga idon babanta akanta Yana Mata wata muguwar harararda tasan da atsaye yake wlh saiya Kai Mata Mari ya sauke haushi a kanta.

Suna komawa daki yasa tissue ya goge Mata hannun ya kalli fuskarta datai wani irin da hawaye saiyaji dukkanin lakkar jikinsa ta mutu.

Matse hannunta yayi da 'dan qarfi
Saitaqi dagowa sbd tasan data dago saisun hada ido Dan tanajin idonsa na yawo ajikinta.

Sake matewa yayi Yana kallon fuskarta Jin murmushi na zuwar Mata yasa tayi saurin miqewa zata gudu ya riqota saita kasa juyowa ta rufe ido tana fidda siririn murmushi tanayin qasa da kanta.

Ki yayi kamar andaki qirjinsa murmushinta daya gani.

Jiyayi yanason sake gani ya miqe tsaye tareda dawo da ita har lokacin murmushi takeyi Jin wani irin yanayi atareda ita.

Juyo da ita yayi suna fuskantar juna ya dago fuskarta tayi saurin rintse ido.
Cikin wuyanta ya cusa hannunsa yanason yin magana Amma baisan mezaice ba sai kawai yaji fuskarsa na sakewa alamar shima murmushin zaizo masa da sauri ya saketa ya juya Mata baya Saidai dayake gaban madubin jikin banging dakin suke tsaye sai yazam suna ganin juna ta jikin madubin ta bude idanuwanta ahankali saitaga wani irin annurin murmushinsa da Bata taba ganiba tsawon rayuwarta sai kawai taji idanuwanta na rufewa alamar zata some
Ganin tayi luuuu yayi saurin riqota tareda girgiza ta tana bude ido taga fuskarsa tasake luuuu da ido yagano abinda yasata kusan suma sai kawai abin yabasa dariya saiga wani sabon murmushin ya sauka a fuskarsa ta zaro ido cikeda mamaki tana qoqarin luu da ido cikin murmushin dayake riqewa yace"

Idan kika kuskura kika Suma anan saina 6alla qafafunki.

Atare Suka saki murmushi wannan karon tafara qoqarin miqewa zatabar jikinsa ya dawo da ita ba zato taji numfashinsa Mai dumi cikin kunnenta yace"

Ki dauka ga ledar maganin quna nan ki kaiwa kawu.

Yana fada ya juya abinsa kamar bashine yayi maganarba yadauki wayarsa ya fice annuri fal fuskarsa.

Su Nanu na ganin yanayin fuskarsa suka ringa mintsilin juna suna son dariya da mamakin yau fuskar sarki asake.

Daukar ledar maganin tayi tareda sakin wani sahirtaccen murmushi ta dauki harda takeaways din tanufi cikin gida takaiwa baban
Yana fushi yana daure fuska haka ya karba yafara cin friedrice da kazar dake ciki still Yana mita.

Dakin zainab tashiga Dan yanzu tanason abinda zainab din ke fada Mata Dan kuwa tuni taji tanason samun cikakken matsayinta na mata agun zakin.

Abubuwanda zainab ke koya Mata Sam Bata taba Jin zata iyasu Saidai tana saurarentane kawai.
Oiling gashinta zainab ke Mata tana Mata firar harsuka Gama

Please Login or Register in order to submit comment