Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyara dasukasha na kusan sati biyu.

Nadey ma da ita akayi gyaran duk da hidimar kaida kawo datayi Mata yawa.

Da am aka daura auren sbd sosai yayita roqonsu suka barsa ya fito sbd ganin ya shiryu sosai sbd dama shaye shaye ba dabiarsa bace Kuma tun Randa aka tafi dashi yayi nadama yake tuba da kukan irin rayuwar batan dasukai.

Sutura Mai kyau suka bashi ya shirya a dakin nanu dake kallon na Mai gadi daga hanyar gate.

Wanka yayi ya shirya ya fito fes zuciyarsa cikeda kunya da farin ciki kwanciyar hankali da rufin asirin da 'yar uwarsa tasamu.

Dai bayan daurin aure Zaki yashigowa fammah dashi har palo Tana ganinsa ta rugo da gudu ta fada jikinsa suka rumgume juna cikin tsananin farin ciki suna hawaye.

Yanda takoma yake kallo Yana godewa Allah.

Da kanta yakirawo iya talatu datake cewa mama suka gaisa harda sauran Yan biki nadey ma tafito sun gaisa ya kalleta ya kalli Zaki da jj yasake yimusu godiya da neman gafara.

Fammah da kanta tayi feeding dinsa abinci Tana hawayen farin ciki duk sai JJ yaji notikan kansa na neman kwancewa ya juya ya fice bayan yayi Mata wani kallon qasa qasa sbd yanda take jijjjiga jikinta Tana riqo Dan uwanta.

Zaki ma kama hannun matarsa yayi suka nufi part dinsu Yana cewa"

Zo Nima nayi feeding naki nasan bakice komai sai dare yayi kifara complaining you're hungry.


Da yamma qarfe bakwai aka Kai amare gidanjensu.
Fammah gidan dad aka kaita a part din mijinta da dad yayi musu jeren sabbin furnitures masu kyau da tsada,

Sai asmau data tare a sabon ginindasu zakin sukayi gefen gidansu na part biyu dasune zasu zauna da matansu Amma suka fasa sbd kowa yazabi Zama gidan babansa Wanda Suma dad dinne yayi Musu furnitures.



Bayan sundawo daga Kai amaren daqyar tayi wanka ta kwanta Tana nishin gajiya da ciwon jiki sbd qirjinta dake ciwo ga jirin datake ji tun a jiyan.

Tausayintane yasashi Fara yimata tausa ahankali Yana sake sata jikinsa har bacci ya dauketa.


JJ kuwa tunda yashigo part din ya rufe koina ya nufi bedroom dinsa yayi wanka yasaka dogon wando da riga na bacci marasa nauyi.

Harya hau gado ya kwanta saiyaji baikamata bari yaje ya dubota.

Da sallama ya tura qofar dakin daidai fitowarta toilet cikin kayan daaka kawota dasu Riga da skirt na red super exclusive da yalwataccen mayafi sai qamshi da sirrin kyau take fitarwa.

Kallon juna sukayi ta sauke Kai tareda qarasowa tsakiyar dakin Tana gyara lullubinta.

Cikin basarwa yace alwala kikayi?

Kai ta daga Masa ahankali Tana sake gyara lullubinta.

Ba wani dogon bayani yace suyi sallah.

Sallah din sukayi suna gamawa ya miqe zai fice itama ta miqe zata nufi bakin gado gurin tashi mayafinta yasata komawa zata Fadi zaune yayi saurin riqota cikin saa hancinsa ya shaqo Masa wani sirrin qamshi dake fita a wuyanta ya lumshe idanuwansa batareda yasaniba yasake cusa kansa cikin wuyanta Jin haka ta qanqamesa da qarfi sbd faduwar gaba Wanda shikuma hakan ya qarasa kunnosa ya rungumeta jikinsa.

Qirjinsu na haduwa numfashinsa yakusa daukewa take ya dagota Yana kallon fuskarta da idanuwanta dake rufe Tana fidda numfashi da sauri jikinta na 'yar rawa.

Bakinta yafara dora bakinsa suka saki ajiyar zuciya kusan atare kafin ya cirata suka nufi gado ahakan.


Washe gari da zazzabi nadey ta tashi Wanda ya daga hankalinsa ba Bata lokaci yakira Dr sayyid yazo har gida ya dubata yasanardasu cikine da ita 4weeks.

Fammah ma Saida Dr sayyid ya dubata sbd zazzabi da ciwon jiki.

Acikin dare guda jj ya susuce Mata abin harya fara Bata kunya ga dad ma Allah yasa ba ruwansa take aka kawo Mata sabbin masu aiki biyu tuni kulada ragamar gidan gabaki Daya yadawo qarqashinta itake abinci suna tayata da ayyukan gidan tuni gidan ya rayu sbd da Babu mace acikinsa.


Am duk yazo gurin qanwarsa dadi da farin ciki yakeyi ganin rayuwar data samu,
Shine yanxu a dakin nanu Daya bari nacan gidan Wanda shima Allah ya Dora Masa son baby z shiyasa shida kawu yanxu suke dasawa matuqa Dan shine abokin firarsa.
Ta bangaren aikin rayuwa kuwa Zaki ya damqa kula da harkar tallafin Hana dabanci da shaye shaye a hannunsa bayan kula da qwazonsa da yayi agurin aikin shiyasa shima yafara sauya sosai kyawunsa da kamalarsa suka dawo musamman sbd kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya Daya samu gashi yashige cikinsu kawu mutanensa tare suke zuwa daukar karatu tun daga fatiha suke yanxu sun kusa hizifi daya
Tun baisaba da masifar kawuba harya Saba abinsa.


Sati uku da bikin suka dunguma su hudu zuwa starling city US inda nadey ta tararda ayyuka sosai itada jj sukai sati biyu suka daidaita komai suka sake damqawa Jasmin komai suka wuce.

Shima haydar yayi wasu ayyukan Amma ba kamar nasuba sbd shi dama yabar wani Alan CEO chair din.

Amsterdam suka wuce acan sukai honeymoon din wata Daya zuwa lokacin itama fammah tafara nata laulayin.

Jikinsu su duka ba Dadi Dole suka dawo starling city kodan ayyukansu.

A gida Daya suke saidai kowa da part dinsa.

Anan sukai azumi da sallah zuwa lokacin cikin nadey yakai kusan wata bakwai na fammah na biyar.

Hajj suka nufa inda suka hade dasu kawu acan kawu yayita Harare hararensa harya gaji Amma farin ciki fal ransa koba komai yace sun Bata da wancan me kama da jiqar aljanun wato z sbd Kullum saisunyi fada shida ita.

Am ma yayi farin cikin ganin yakusa Zama uncle dukda ga z Nan ammadai zai samu qari.

Dagacan Nigeria suka dawo saidai daga airport asibiti aka wuce da nadey sbd naquda data taso mata haiqan.


Babu Wanda yabar asibitin acikinsu sbd damuwa saigashi Bata wani wahalaba ta haihu aka samu namiji sak mahaifinsa da kakansa asalin Fata da hasken Igbo.

Kallo Daya kawu yayi Masa ya riqo hannun baby z Yana cewa"

Ke jajayen kunnuwa Zo mushirya dake zanyi wannan ubansa ya dauko daga gani bakinane zai kamani Dan wannan saiyasani fitowa da hula a juye.

Janyewa tayi Tana cewa"

Aa kace bamu sake shiryawa kaje Nima da kaka(iya talatu) zanyi da sabon bany banayi dakai.

Ni kike cewa haka?
jeki indan wannan me kalar inyamuran ne Ina zaune Zaki nemi chetona.

Dariya dukkaninsu sukayi am yace"

Baba kamanta uwayensama daidai kake dasu bareshi.

JJ ne ya karbesa Yana Masa huduba yace"

Dama ai kawu wannan soldier din kaketa fatan samu tuni..

Yaketa tsoron samu dai"""cewar iya talatu Tana dariya.

Tsuke fuska yayi zaiyi mgn alee idi yace"

Kyaleta laifinane...

Ita talatun ta qarasa Masa da cewa"

Daka bari ya aureni ko???

Dariya dukkaninsu sukayi harshi alee idin da alhaji dattiya.

Shidai sarki Yana zaune kusada matarsa sai murmushi yakeyi cikin farin ciki Yana saurarensu hannunsa ruqedana matarsa.

Koda aka sallamosu gurin haj talatu aka maidota sbd samun kyakkyawar kulawa.

Aikuwa kulawa sosai suke samu har ranar suna ya zagayo jj yayi Masa huduba da sunan kawu wato Muhammad dattiya ana kiransa da sayyed.

Bayan suna qiri qiri yaso tadawo taqi komawa Saida sukayi sati shida harda kwana shida.

Ranardata koma ranar suka Dora inda suka tsaya abinsu cikin kewa da tsananin qaunar juna.




****Cikin tsananin murna ta ajiye wayar tareda rungumesa Tana cewa"

Uncle fammah ta haifi little z.

Cikin murmushi yace"

Saida yafara fadamin to cewa yayi karna fada Miki kice anmiki Yan ubanci.

Fadawa tayi kansa Tana cewa"

Wlh ko yanxu anmin.


Daga asibitin itama fammah gida aka dawo da gurin hajja kamar yanda suke Kiran iya talatu yanzu.

Zakine yayiwa babyn suna da ruqayya shima sbd JJ ne keson asa sunan umman Zaki datasa umman da itama ruqayya ne sunanta.


Ranar suna aranar jj yayiwa matarsa kyautar sabuwar mota fil hakama dad.

Ko aranar fammah da am sunyi kukan karamci da rashin qyashi da riqo da Allah baisaka a zuciyar bayin Allanba.

Sunriqesu tamkar dama asalinsu Daya Wanda sai yamzu suke gabbatarda ba lallai sai Wanda ka hada jini dashi bane yake Zama Dan uwanka yarda da juna tareda Amana nasa kazama Dan uwan mutum fuyeda wani jinin.

Bayan biki suna da sati uku suka shirya su uku sukaje Dilla dubo mum dinsu.
Am,jj da ita fammah din sai baby r.

Sosai mum dinsu taganesu duk da har lokacin akwai haukar atareda ita Amma ba laifi abin yayi sauki.

Dazasu dawo kamar karsu rabu suna kuka cikin jirgi jj ya rungume matarsa Yana lallashinta cikin soyayya da qaunar abarsa.


Itama Saida tayi sati bakwai takoma gidanta shima sbd gajiya da kawu yayi da irin rashin kunyar da ake zuba Masa a gida ya koresu,
Gata Zaki Daya Gama renasa gata jj din gata itama fammah din qafafu kamar zaren kitso ta iya rashin kunyar rako Miji idan zai tafi Tana wani maqalewa.

Ko wata hudu Basu Gama rufawaba suka tarkata suka komawarsu su duka dama kawun a matse yake Kullum yayita masifa kenan tun yanayi a fili Dole Yakoma a boye yakeyi sbd itama Kuma me jajayen kunnuwa batason duk yayi fada kwana takeyi Tana fushi dashi shiyasa yanaji Yana gani abinda yayansa Basu hanasa jikar Daya Gama hawala akanta ta canzasa sbd beda yanda ya iya tunda yafi qaunarta Alan komai yanzu.

*ALHAMDULILLAH.*

_SHI ALKHAIRI DANQONE KA TAUMAKI WANI BAKASAN WAYE ZAI TAIMAKEKABA GOBE._

_DA JINI DABA JINIBA KA RIQI MUTUM DA AMANA DA DARAJA SBD ZAI IYA ZAMA SHINE NAKA WATA RANA._

_RIQO A GABA KO CUTA BAIDA AMFANI SBD BAZAI DAWO DA BARNA BA KA ZAMA MAI YAFIYA ALLAH ZAI SAUKAKA MAKA RAYUWARKA CIKIN NUTSUWA DA AMANA._

_'DAN TA'ADDA MUTUM NE BA DABBA BA KOWA DA TASA QADDARAR,
KARKA KYARESA TALLAFA MASA IDAN KAGA DA HALIN HAKAN KO KABISA DA ADDUA._

_KAYAN MATA BA ILLA BANE IDAN KA ZAUNA KAYI TUNANIN SHAN ABINDA YAKAMATA A TSARI BA HAUKABA KAMAR YANDA WASU SUKA DAUKI ABIN._

*_INA MIQA DUKKANIN GODIYATA GA MASOYA DASUKA NUNA TSANANIN SO DA QAUNA GA DATTIYA DA IYALANSA._*

_*YA ALLAH YASA MU AMFANA DA ABINDA KE CIKI SABANINSA ALLAH YA YAFE MANA.*_

*_NI MARYAM SANI GUMMY WADDA AKA FI SANI DA MAMUHGEEE NAKE CEWA ALLAH YA HADAMU A WANI SABON LABARIN IDAN ALLAH YACE_*


*AMIN.*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment