Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki ba sai da ta zabgawa Dubu mari sannan ta ɗora da cewa, "Wallahi ba Balarabe ba ko Bala na sake ji a bakinki sai na yi ƙasa-ƙasa da ke. Na lura iskancinki ƙara yawa yake saboda baki da mafaɗi..." Dubu ta fisge hijabinta tana cewa, "Allah ya isa kuma wallahi bashi kika ɗauka. Na faɗa waye bai san Balaraɓe kwarto bane har ɗakin Baba Auwalu sai da ya taɓa leƙawa lokacin da Yahanasu tana amarya. Banza kina gida kina tare da ɗan iska..." Kukan kura Hansatu ta yi ta fisgo Dubu ta fara jibga kamar Allah ya aikota. Jin Hansatu na niyyar hallakata ya sa ta fara kiciniyar ramawa, ai kuwa Hansatu ta cukwikwiye Dubu a cikin hijabi ta riƙa dukanta ta ko'ina sai da ƙyar su Lawandi suka ƙwaci Dubu. Suna fisgarta sai ga hijabinta a hannun Hansatu nan fa kan Dubu ya fito ral da shi yana ƙyalli don ranar Yaya Babba ta sharɓane mata shi da man kaɗanya. Nan Ɗan'iya ya fara tafi yana cewa, "Yeeh Dubu mai kan Silba (Silver)" Ai kuwa kafin wani lokaci tuni yara suka taru ana kallo, dukda tsoron da suke yi wa Dubu amma ruruma ta ɗauke hankalinsu suka fara sowa da tafi suna cewa, "Yeeh Dubu mai kan silba."

Idanun Dubu ne suka kaɗa jawur saboda baƙin ciki, sai dai har lokacin idanun Dubu a bushe suke babu ko ɗison hawaye don gudun kar a ga hawayenta yara su rainata. Cikin takaici ta kalli Hansatu ta ce, "Kwarankwatsa dubu bashi kika ɗauka kuma da ni kike zan cen." Ta juya ta kalli sauran yaran da suke tsokanarta ta ce, "Ku kuma za mu gauraya da ku kowanne shege sai na sa an harbe Uwarsa." Tana gama maganar ta suri jakarta da ke cen gefe ta fisgi hijabinta ta ɗora aka ta yi tafiyarta. Sai dai kusan rabin yaran jikinsu ya yi sanyi don suna tuno Yayan Dubu soja ne hantar cikinsu ta kaɗa har da masu bin ta suna bata haƙura amma babu wanda ta waiga, bare ya sa ran za ta amsa masa.

Dubu tun daga soron gidansu ta fara barke baki tana ihun kuka, amma ci kanki babu wanda ya tanka mata saboda sanin hali irin nata. Matan kawunan nata suna gani ta wuce cikin gida. Tana zuwa sashen su Yaya babba Inna Furai ta tare ta da tambaya, "To ƴar nema wa kika tsokano wanda ya fi ƙarfinki?" Dubu ta goge majina da hijabin hannunta sannan ta kuma yage baki tana ihu har sai da Yaya babba ta fito tana tambayarta.

"Inno wallahi daga yau ba zan ƙara fita waje ba. Ki dubi irin cin mutumcin da Hansatu ta yi mini ita da Ɗan'iya yau kashe ni ne kawai ba ta yi ba. Yara suka taru suna ce mini mai kan silba. Ni dai wallahi Allah ya isa da askin nan da azzalumin nan ya yi mini." Dubu ta faɗa tana sake fashewa da kukan baƙinciki, don abin ba ƙaramin ciwo ya yi mata ba. Yaya Babba ta karɓe zan cen da cewar:

"Wallahi faɗi ki ƙara Dubu Allah ya iskan ki, don Allah me kika tsarewa Soja da zai sauke miki gashi ana zaune ƙalau? Hassada dai ka rasa wa za ka yi wa sai jininka. Na rantse da Allah ko uwarsa Nafisa ba za ta gwada miki gashi ba. Kanta da har gobe kamar hamtar ɗan isa ga uban sanƙo da almajiran ƙeya. Wallahi ni bansan abin da Garba ya gani a jikin gajeriyar matar nan ba ya aura, mace sai faɗin ran tsiya tana baje hanci kamar tattasai ya ji sanyi wuri." Dubu ban da tuntsira dariya babu abin da take yi har da hawaye saboda ƙeta don tuni ta goge hawayen idonta saboda ko ba komai Yaya babba ta biya ta, da ba'ar da ta yi wa mahaifiyar Aseem.

Inna Furai da ke gefe ta sa dariya ta ce, "Yaya ai ba za ki ga baje hanci ba sai ta shiga gaban mota yanda kika san funkaso." Sai kuwa suka sake kwashewa da dariya. Yaya Babba ta ce, "Furaira wai dama ranar da muka fita da Garba tana gaba kina ankare da ita?" Inna Furai ta ce, "Ina gani mana wai har ca take ka saya mana wani abin mana a danja wai ita mai miji." Ai kuwa dubu me za ta yi idan ba dariya.

Yaya babba ta saki dariya ta ce, "Furaira alƙur'an ni kuma fuskar Nafisa ta ƙi ɓace mini lokacin da muka karɓi haihuwarta ta wannan yaron soja kin tuna lokacin har cewa take wai Inno zo na goyaki. Na ce mata ke Nafisa rabani da zancen goyon nan, rabona da goyo tun shekaru tsububu sai yau da kike nakuɗa za ki goya ni, na turmushe ki Garba ya ɗau gaba da ni." Inna Furai dariya har da hawaye sannan ta ce, "Yoo kafin ki zo har cewa take Inna karɓi cikin, na ce Nafisa lamari ya lalace ina Uwar Garba na karɓi cikin Garba ai ba kanta sai cewa ta yi har Garban na bar miki gabaɗaya." Dubu ta kife a wurin ban da dariya babu abin da take yi.
*DUBU JIKAR MAI CARBI*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*


FREE PAGE 9
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

Sallamar Baba Munkaila ne ya dawo da Dubu cikin hayyacinta, ba shiri ta shiga nutsuwarta ta fara kumbure-kumbure don ta san babu makawa zai samu labarin abin da ya faru tsakaninta da Hansatu. A daidai kan Dubu ya tsaya fuska babu walwala ya ce, "Ke!" Kamar bata ji shi ba ta yi biris, sai da ya sake buga mata tsawa sannan ta amsa. Cikin faɗa ya ci gaba da cewa, "Dubu ki kiyaye ni fa, kullin iskancinki da iya shegenki ƙara gaba yake ko? Ƴar ƙanƙanuwarki da ke har kin isa tarar matar aure ki ce za ki yi dambe da ita. Wallahi a hir ɗinki idan kika shiga hannuna na lahira sai ya fiki jin daɗi." Dubu dama kamar me jira yana dire zancensa ta fashe da kuka tana faɗin, "Dama na san komai ni za a ɗorawa alhalin ita ce bata da gaskiya." Rankwashi ya sakar mata a tsakiyar ka aikuwa ba ƙaramin shigarta ya yi ba, a zabure ta yi gefe ai kuwa Yaya babba dama ta fara cika ta dubi Baba Munkaila cikin faɗa ta ce, "Munkaila nakasa marainiyar Allah za ka yi? Ka duba irin ƙusar da ka sakar mata a tsakiyar ka sai ka huda mata kai, ka cuceni ka cuci Ado. Ko da ya kasance likita ba sai an sayi magunguna da alluran da za a yi mata aiki ba. Gaskiya bana so ka fita rayuwar yarinyar nan shi ya sa ga tana kamar ruwan aski kullin bata kumari." Baba Munkaila bai tankawa Yaya Babba ya dubi Dubu ya ce, "Tashi ki ɗau hijabinki ki wuce makaranta. " Tun bai rufe baki ba Dubu ta suri kayanta ta fita waje tana kurma uban ihu.

Inna Furai ta ja tsaki ta dubi Baba Munkaila ta ce, "Munkaila wai me ya sa ko yaushe burinka ka zazzagewa yarinyar nan albarkar da ke kanta? Yanzu da ka kaɗa ta waje idan ta shiga gari wa ya shiga uku idan ba mu ba." Yaya babba ta cafe zancen da cewa, "Wallahi idan na rasa Dubu hukuma ce za ta raba ni da Munkaila dama na daɗe ina zargin ba ƙaunarta kake ba." Baba Munkaila ya yi murmushi sannan ya ce, "Inno yanzu so kuke a zurawa Dubu ido ta taso babu nutsuwa da rashin ilimi? Kuna ganin Fatima yarinyar nan kowa sha'awarta yake, saboda ilimin addininta. Mu kuwa wa yake sha'awar Dubu? Ku shaida ne a rana sai a kawo muku ƙara ta yi sau goma. Amma Inna furai ai bai kamata mu zura mata ido haka har girmanta ba."

Yaya babba ta yi shiru tana nazari sannan ta ce, "Munkaila ka yi tunani, kuma wallahi ina jin hannu aka sawa Dubu dole na sake nema mata maganin baki don wallahi baki ba ɗan'uwa ba ne." Baba Munkaila na ganin ya yi wa Tsofaffin iyayen nasa dabara ya tashi ya fice daga gidan.

Dubu na fita ta goge hawayenta ta maƙale jakarta ta ɗauki hanyar islamiyya, sai dai tana saƙa da warwarar abin da za ta yi wa Hansatu don ta fanshewa abin da ta yi mata. Kamar daga sama tana shan kwanar hanyar da za ta sadata da makarantarsu sai ga Ɗan'iya ya fito da tallar wake da shinkafa a kansa, hannunsa na riƙe da bokitin ragadada. Yana ganinta ya yi baya da sauri a tsorace don ya san mai ƙwatarsa a hannun Dubu sai Allah, don haka bai yi wata-wata ba tun Dubu bata tanka masa ba ya fara cewa, "Dubu don Allah ki yi haƙuri wallahi ba zan ƙara ba." Kamar wani abu bai haɗasu ba, haka Dubu ta basar da Ɗan'iya ta ce, "Da aka yi me?"

Ɗan'iya ya washe baki ya ce, "Faɗanki da Innarmu mana." Dubu ta zurawa bokitin ragadadar hannunsa ido, take ta ji yawunta ya tsinke, ta kai hannu za ta taɓa ya janye da sauri. Dubu ta riƙe ƙugu tana jinjina kai sannan ta ce, "Ɗan'iya wallahi ko ka bani bokitin nan ko kuma in haɗa gabaɗaya da Shinkafa da waken da shi bokitin ragadadar in kifar da su don wallahi wannan rigimar mun fara ta kenan ni da ku."

Tun ba ta rufe baki ba Ɗan'iya ya soma hawaye ya ce, "Don Allah ki mun rai wallahi Innarmu duka za ta yi min." Dubu ta yi dariyar mugunta ta ce, "Idan ka koma gida in ta tambayeka ka ce ta zo gudanmu ta karɓi kuɗinta." Ɗan'iya ya fara ja da baya Dubu na tsaye ta ce, "Tsaya-tsaya Ɗan'iya gaya mini duka kayan naka na nawa-nawa ne?" Ɗan'iya a tunaninsa rangwame Dubu za ta yi masa idan ta ji tsadar abinci ya taƙarƙare da ƙarfinsa ya ce, "Shinkafa da wake na Dubu biyu ne Ragadadar dubu ɗaya ce." Dubu ta yamutsa fuska ta ce, "To Allah ya yi belinka saboda wallahi da babu kayan nan sai na jiƙa maka jikinka, amma yanzu dole za ka bani bokitin ragadadar nan wallahi, ko in haɗa da kai da su duka na damalmale ku a cikin ƙasa." Ɗan'iya ya yi shiru yana nazari don ya san ciniki ko hamsin ne babu a ciki, Innarsu cin ubansa take bare bokitin Ragadada gabaɗaya. Ragadadar da sai sun yi da gaske suke samu Mahaifiyarsu ta ke basu yanka ɗaiɗai yau ita ce zai ɗauka ɗungurungun ya bada bokitinta.

Dubu na ganin haka ta buga tsalle tana ƙoƙarin janyo robar shinkafar, Ɗan'iya na ganin haka ya miƙa mata da sauri don kar ya yi biyu babu. Wani wawan kuka ya saki lokaci ɗaya ya juya zai koma gida Dubu ta sha gabansa ta ce, "Maza wuce wallahi ba za ka koma gida yanzu ba sai ka sayar da abincin nan salan ka min mugunta tun ban gama cinyewa ba ka sa azo gidanmu. Munafiki yana zare idanu kamar shege a rabon gado." Ta ƙarasa maganar tana ɗake masa ƙeya. Babu yanda ya iya haka ya nufi titi yana share hawayen fargaba da tashin hankali.

Dubu sai da ta saita Ɗan'iya ya bi titi sannan ta bi wani layi bata tsaya ko'ina ba sai cikin wani sabon gini da ba a ƙarasa ba. Zama ta yi dirshan ta kwashi ragadada tana ci tana siɗar romo, kafin wani lokaci tuni ta cinye shi tas, saboda ba ƙaramin daɗi ya yi ba, ya ji farin magi zaƙwai ga ɗan yaji-yaji. Tana gama ci ta sa gefen hijabinta ta goge baki. Ta ɗauki bokitin ta cika shi da yaji ta ɓoye a cikin hijabi ta fice daga cikin kangon.

Dubu bata tsaya ko'ina ba sai ƙofar gidan Hansatu, Hansatu na tsaye a kan ƴarta Mairo da take ta zuba ragadada a ƙananan robobi, ta hango Dubu tsaye a ƙofar gida. Suna haɗa ido Dubu ta ƙarasa ciki kamar mutuniyar kirki ta ce, "A bani ragadada." Tana maganar tana sakin wani irin murmushi. Hansatu ta hangame baki tana yi wa Dubu kallon mamakin wato rashin kunyar Dubu ta bunƙasa haka. Balabare da ke bakin bishiya yana sharɓar ragadada ya yi zaraf ya ce, "Dubulliya ta nawa za a baki?" A fusace Hansatu ta ce, "Ta nawa za ki siya?" Ba musu Dubu ta miƙa naira ashirin nan fa Balarabe ya fara leƙenta yana kashe mata ido ɗaya. Dubu ta ɗauke kai kamar bata gan shi ba. A fakaice Dubu ta sunkuya tana gyara takalminta ta cikin hijabi ta dire mata bokitin ragadada, ta bayan ƙatuwar tukunyar ragadadar. Ta matsa can gefen bishiyar da Balarabe yake zaune. Hansatu mace ce mai matuƙar son kuɗi don duk abin da zai haɗa ku da ita muddin ka zo siyan abu wurinta bata zuciya. Tana da tsumulmula saboda ko ita bata iya zagewa ta ci ragadada idan ba mijinta Balabare da Allah ya jarrabeta da mutuwar sansa ba. Duk abin da Balarabe ya tambaya ba ta iya hana shi. Don haka a ƙa'ida kullin ta sauke tukunyar ragadada kwanonsa daban yake, kuma ko kara ya ajiye ba za ta iya tsallakawa ba.

Hansatu na ɗauko leda ta shiga wurgawa Dubu harara sanna ta fara zuba mata, za ta ƙulle ledar Balarabe ya ce, "Ke Hansatu ƙara mata ta hamsin." Ai kuwa kamar ya watsa mata ruwan zafi ta ɗago a zafafe ta ce, "A kan wane dalili za ka siya mata bayan ɗazun nan yarinyar nan ta gama ci mini mutumci..." Nan fa Hansatu ta zayyanewa Balarabe yanda suka yi, kamar ta rufe bakinsa shiru kake ji sai dai sam ba haka ya so ba, Dubu na karɓar ragadadarta ta nufi hanya za ta fita sai ga Ɗan'iya ya shiga gidan yana kwala ihu.

Da kallon mamaki ya bi Dubu har ta fice, Hansatu don sauri zaninta har faɗuwa yake. Ta fara jefo masa tambaya a hargitse, "Ɗan'iya ina bokitin ragadadar?" Tun bata rufe baki ba ya hau nuna ƙofa ya ce, "Dubu ce ta karɓe mini." Ai kuwa kamar wanda ya ɗanawa wuta haka Hansatu ta zabura tana cewa, "Buhun uban can, kai buɗe baki ka yi mini magana yanda zan fahimta." Dubu na jin haka ta fara zuba sauri bata tsaya ko'ina ba sai islamiyya.

Ɗan'iya ya zayyanewa Mahaifiyarsa abin da ya faru. Hansatu na jin ƙarashen labarin ta shuri takalma garin ɗaukan takalmi ƙafarta, ta shuri bokitin Ɗan'iya da ke cike da yashi. Hansatu ta nuna Bokitin tana faɗin, "Ɗan'iya ba wannan ba ne bakitin da ka fita da shi?" Nan take mamaki ya cika su. Hansatu ta suri bokitin ragadadar da ke cike da yashi, ko ta kan Balarabe bata bi ba ta wuce gidansu Dubu tana kumafar baki.

Lokacin da Yaya babba ta gama jin jawabinta, kallon sheƙeƙe ta yi wa Hansatu sannan ta ce, "Hansatu kura ko mayya kika mayar mini da Dubu da za ta iya cinye bokitin ragadada guda? Allah na tuba me ye ragadada abin da duk yaɗi da jijiya ne, me ye Dubu bata ci a gidan nan?" Takaici ya kama Hansatu ta yi ƙwafa sannan ta ce, "Dama ai sake ta samu shi ya sa take shuka tsiyar da take so, to wallahi daga kaina ba za ta sake yi wa wani haka ba." Tana gama masifar ta fice, Inna furai ta bita har soro tana mayar mata da martani.

"Aniyarki ta faɗa kanki, azzulama mai baƙin baki. Bayan zazzagar iya shegen da kika yi mata shi ne bai ishe ki ba za ki biyota har gida kenan." Sai da ta ga ficewar Hansatu ta juya ta samu Yaya tana faɗin, "Yaya an ya maganar yarinyar nan bata kan hanya, na san halin Dubu sarai za ta iya tare yaron nan ta karɓe bokitin ragadadar fa." Yaya babba ta yi ƙwafa cike da takaici ta ce, "Ai kuwa wallahi da na ɗebe mata falsafar albarka alƙur'an da babu ni babu ita."

Hansatu kai tsaye wurin mai unguwa ta wuce bayan ta kwashi gaisuwa ta zayyane masa abin da yake faruwa, ba shiri ya aika da kiran gaggawa gidan Marigayi mai carbi. Zuwan dogarawan ya yi daidai da zuwan Baba Abubakar shi da Aseem, wannan sammaci ba ƙaramin ɓata ran Baba Abubakar ya yi ba. Ya ci alwashin idan kuwa haka ta tabbata Dubu ce ta cinye ragadadar, tabbas ba ƙaramin hukunci zai ɗauka akanta ba don duk abin da Yaya babba za ta faɗa sai dai ya toshe kunnuwansa. Shi da Aseem suka wuce wurin mai unguwa ba tare da sun shiga cikin gidan ba. Suna zuwa aka aika kiran Dubu, tare da Dogarawan suka taho tana zuwa ta yi turus! Jiki a sanyaye ta zauna ta hangi Aseem na wurga mata harara sai Ɗan'iya da idanunsa suka yi wuri-wuri, saboda kukan da ya sha. Hansatu lokaci-lokaci take kallon Dubu tana ƙwafa cike da jin haushi.

Shiru wurin ya ɗauka Mai gari ya ƙurawa Dubu ido yana son gano gaskiyar lamari, don ya san sarai Dubu za ta yi abin da ya fi haka, bayan an gabatar da abin da ya tara su a wurin, Mai unguwa ya kalli Ɗan'iya ya ce, "Ɗan'iya ko za ka gaya mana yanda abin da ya kasance." Ɗan'iya ya fyace majina sannan ya zayyane duk abin da ya faru tsakaninsa da Dubu. Tun bai rufe baki ba Dubu ta yi caraf ta fara magana, "Alƙur'an ƙarya yake yi mini haka kawai zai yi mini sharri saboda ba ƙaunata ake..." Da sauri Baba Abubakar ya katse ta yana yi mata daƙuwa Hansatu ta tura ɗankwali gaba tana faɗin, "Allah ya taimakeka ka yi mini tsakani da Dubu wallahi muddin ta sake shiga gonata sai na yi ƙasa-ƙasa da ita. Ƙwaranƙwatsa kuma sai an biya ni kuɗin ragadadata." Mai unguwa zai yi magana Aseem ya zaro dubu biyar ya miƙawa Hansatu yana faɗin, "Shi kenan magana ta wuce." Dubu na gefe da ta ga maƙudan kuɗin da aka bawa Hansatu ta yi zaraf ta ce, "Wallahi ragadadarta bata kai da kuɗin nan bayan kafin na karɓi bokitin Ɗan'iya ya ce mini ta dubu ɗaya ce." Ta ƙarasa maganar za ta warci kuɗin da sauri Hansatu ta maƙe su tana cewa, "Ai irin wannan asara kullin ma Allah ya kawo ta." Baba Garba saboda ɓacin rai sallama ya yi wa Mai gari ya tafi ya tafi, shi kuwa Aseem hannun Dubu ya fisga suna tafe yana haɗa hannunsa da nashi yana murzawa. Ban da wash! Babu abin da take yi saboda yanda hannunta yake yi mata raɗaɗi.

Suna shiga cikin gidan suka wuce sashen su Yaya babba har lokacin hannun Aseem na riƙe da Dubu. Tun da Yaya babba ta hango su take sakin murmushi, don shi kansa Aseem har sai da ya saki murmushi saboda yanda ya ga kakar ta shi cikin farinciki. Tun kafin su zauna ta sake washe baki tana faɗin, "Allah ƙadiran alamanyasha'u. Ikon Allah! Allah mai sanin abin da yake cikin zuciya." Gabaɗaya ba su kawo komai a ransu ba sai ɗan murmushi da suka yi. Bayan sun gaisa cikin ɓacin rai Baba Abubakar ya fara yi wa Dubu faɗa, kasancewar mutum ne ba mai zafi ba ya sa bai cika faɗa ba, amma Dubu ba ƙaramin tsora ta yi ba. Saboda dama mai haƙuri bai iya faɗa ba. Yana gamawa Yaya babba ta dasa nata faɗan.

"Maganar gaskiya Dubu kin wulaƙanta ni ki rasa me za ki karɓarwa yaro sai ragadada?" Inna Furai ce ta shiga ɗakin tana girgiza kai ta ce, "Don Allah Garba ka ji wata muguwar ɗabi'a, ka gaya mana meye Dubu bata ci a gidan nan?" Yaya babba ta yi ƙwafa ta ce, "Gane mini hanya Furaira neman maganar fa. Garba ka rabani da Dubu tun takaicinta bai kashe ni ba, ba zan iya ba gaskiya ba za ta ƙara kwanar mini a ɗaki ba. Ina dalili ta kashe ni ta cuci iyalaina, ko da dai kun girama shi fa Maraici ba daɗi gare shi. Don Allah Garba idan babu ni ba kun zama marayu gaba da baya ba? Na gaji gaskiya, ka sa Dubu a gaba ka tafi da ita na bar maka ita halak malak."

Baba Abubakar ba ƙaramin daɗi ya ji ba, don dama ya jima yana san ɗaukan Dubu Yaya babba ce take hanawa. Ya gyara zama ya ce, "Dama Inno na daɗe ina yi miki maganar amma yanzu tun da kin amince zan tafi da ita." Madadin Yaya babba ta yi magana sai ta yi jim sannan ta ce, "Ni fa Garba ba raba ni da Dubu ne bana so ka yi ba, gaskiya a riƙa zalintar marainiyar Allah ne bana so. Wannan matar taka ba ƙaunar Dubu take ba, sai ta zo ta yi ta gallazawa marainiyar Allah, ina nan ban san halin da ake ciki ba. Kai kuma mutuwar sonta kake ballantana ka tsawatar mata. Gidan Ado kuma Fauziyya sai jaraba mace sai masifa ko ƴaƴan cikinta ba ƙaunarsu take ba bare kuma Dubu, raba ni da bawa Ado Dubu ana zaune ƙalau. Ita kuma waccan mai tausayin ƙasar komai nata ba kuzari ina dalili inkai Dubu ta riƙa barinta da yunwa? Ni inbawa Rahama Dubu ta kashe ta da yunwa Allah ya tsare ni. Don Allah Garba wacce riba suke ci wai Rahama basa karyawa sai goman safe, mu da anan ƙarfe goma an fara haramar na rana. A'a gara Dubu ta yi zamanta a nan ina ganinta ina jin daɗi." Baba Abubakar ya girgiza kai don dama sai da ya ayyana haka amma ya ci alwashin ko da dabara sai ya karɓi Dubu muddin ya dawo gidan da zama, don barinta a haka har girmanta akwai gagarumar matsala.

Yaya Babba ta kalli Inna Furai ta ce, "Furaira ki gaya masa mana ai kyayi mini kara dai ko?" Inna Furai ta washe baki ta ce, "Garba wani abin alkhairi muka hango kuma mun san da kai da kaya duk mallakar wuya ne. Mun yanke shawara ni da Yaya ya kamata a ci gaba da yaɗa zumunci." Gaban Baba Abubakar sai da ya faɗi don ya san wataƙila wani abin za su ɓallo masa.

Inna Furai ta karɓe zan cen da cewa, "Ka san dai bikin su Salisu da su Zulfa bayan babbar sallar nan ne kuma dududu bikin saura wata guda ina jin." Baba Abubakar ya gyaɗa kai ya ce, "Ai ina jin lokacinma mun dawo nan." Inna Furai ta yi dariya ta ce, "Ai za ku sha hidima tun da auren ƴaƴa shida ba wasa ba." Baba Abubakar ya yi murmushi don shi kansa idan ya tuna bikin har daɗi yake ji ace cikin gidansu za su aurar da ƴaƴa shida maza da mata kuma duk auren gida abin akwai farinciki.

Yaya babba ta katse masa tunani da cewar, "Ka ga da Zulfa da Bintu duka Dubu fa ta girme musu." Baba Abubakar ya gyaɗa kai ya ce, "Ai suma Yaya don kun matsa ne amma duka nawa yaran suke?"

Nan take Yaya babba ta ɓata fuska ta ce, "Yara dai Allah ya kawo musu mijin aure kar ka yi musu buƙulu, kai da ɗan'uwanka ba kun ɗorawa kanku bokon jaraba ba. To gaskiya bana son hassada Garba kuma na yanke shawarar haɗa Dubu da Soja don gaskiya ba za a zo ana yi mata gori ba tun da ƙawayenta kusan duka sun yi aure wasu ma sun haihu."
[7/23, 2:48 PM] Ameera Adam🌚: *DUBU JIKAR MAI CARBI*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*


FREE PAGE 10
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.


Baba Abubakar da Aseem lokaci guda suka ɗago suna kallon Yaya babba, da ta ci gaba da zayyano zance ko a

Please Login or Register in order to submit comment