Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayinda Salma yake da shekara bakwai a duniya, Fulani Maryama babu wani abu da yake damunta a yanzu saboda bata da wani abu da zai ɗaga mata hankali, tun da ba ita kaɗai ba hatta sauran mutanen da ke cikin masarautar sun san fifikon da Sarki Aminullah yake yi tsakanin Saif da Salman.

Lokacin da Saif ya kai shekara goma lokacin ya ƙara girma sosai kammaninsa dana Sarki Aminullah ba ƙaramin ƙara fitowa sukeyi ba, a wannan lokacin cikin ikon Allah ya fara jan ciki a haka yake zuwa duk inda yake san zuwa a sashen mahaifiyarsa, dan ma ta hanashi fita saboda bakin mutane da ƴan tsegumi yana fita ake dandazon zuwa kallansa, da ƙyar Fulani Zaliha ta shawo kan Mai martaba aka samo me koya masa karatu, da farko Sarki Aminullah faɗa ya rufe ta da shi lokacin da ta sameshi da magananar. Sai da ya gama sauraronta yace.
"Haba Zaliha ke meyasa kin fiye fitina yaron da yake a nakashe ta yaya zai iya koyan karatu?" Fulani Zaliha ta ce. "Allah ya taimakeka hakan ba yana nufin zamu barshi haka babu ilimi ba tunda yaron nan ba ciwon hauka yake yi ba kuma babu abinda ya samu ƙwaƙwalwarsa, Allah ne ya hallitoshi haka ba dan baya ƙaunarsa ba, yaron nan ba kurma bane duk abinda nake faɗa yana jina kuma wata baiwa da yake da ita duk inda na aikeshi a ɗakina kome nace ya ɗauko min zaije ya ɗauko min, kana ganin idan muka barshi babu ilimi Allah bazai tuhumemu ba Mai martaba? Dan Allah idan ma bazaka ja shi a jikinka ba saboda nakasarshi ka taimaka masa ya samu ilimin bautawa Ubangijinsa, Amma ina tuba gurinka bansani ba ko kalamaina sunyi ƙushi" ta ƙarasa maganar tana zubda ruwan hawaye. Mai martaba shiru yayi yana jin tausayinta cikin zuciyarsa yake ayyana tabbas yasan abinda ta faɗa gaskiya ne sai yaji gabaɗaya bai kyautawa kansa ba, janyota yayi jikinsa ya rungume ya fara lallashinta ya ce. "Ina ji a jikina sam ina aiwatar da rashin adalci amma ni kaina bansan me yake damuna ba, na rasa sanda na zama haka dan Allah ki dinga taimaka mun da addu'a kinsan mijinki da ba haka yake ba, Dan Allah idan ina cutar da ku ki yafe karki bari Ubangiji ya kamani da laifin da bansan ina aiwatar da shi ba." Ɗagowa tayi ta kalli ƙwayar idanunsa tabbas tasan da ba haka yake musu ba ita da ɗanta, idan batasa son zuciya ba zata iya cewa duk cikin matasan yafi ƙaunarta, idanunta ne suka cigaba da kawo ƙwalla murya a sanyaye ta ce. "Ina yi maka addu'a a duk lokacin da na sanya goshina a ƙasa nayi imani da Allah addu'a ta bazata taɓa faɗuwa a banza ba, Allah zai kawo mana mafita kuma nida ɗana bamu taɓa ƙullatakar a zuciyarmu ba" Lumshe idanunsa yayi cikin jindaɗin kalamanta yace. "Insha Allah zan sa a kawo Malami ya dinga koya masa karatu shikenan" murmushi tayi tana gyaɗa masa kai sannan suka cigaba da hira.

Tun daga ranar aka samowa Saif Malamin da yake zuwa yana koya masa karatun addini dana boko, kuma sosai yake ganewa dan dai bashi da baki da yake mayar da karatun da aka biyasa ne, Saif Allah ya bashi basira ita kanta Mahaifiyarsa har mamaki takeyi idan yaji muryarka sau ɗaya ya gane ka, kuma yana daga kwancen nan yake taya mahaifiyarsa wasu ayyukan, ya lura Mahaifinsa bayasan ya dinga ganinsa a fada hakan ne yasa ya ganje jikinsa sai ya shafe wata guda bai halarci fada ba idan yaje ma Salman ya dinga hantararsa kenan yana ƙyararsa daga ƙarshe ma har suna ya sa masa kwantaccen. A haka rayuwa ta cigaba da gangarawa da daɗi babu daɗi har aka shafe wasu shekaru masu yawa.

BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYU

Wata rana Sarki Aminullah ya tafi ɗaurin aure ƙasar Adamawa a hanyarsa ta dawowa suna tafe a mota shida dogarawa uku tayar motarsau ɗaya ta fita, duk yadda direban motar yaso dakatar da motar hakan bai yuwu ba saboda kan motar ya kwace masa, da sauri motar bayansu tayi parking wacce sauran dogarawansa ne a ciki, Motar su Mai martaba cikin daji ta shiga bisa tsautsayi ta dinga bi ta kan wasu masu Fulani sai da ta kai ga wata bishiya sannan motar ta mutu, wani ikon Allah Sarki buguwa kawai yayi a kafaɗa sai gocewar ƙashi da yayi a ƙafarsa, Direban motarsa ne suka ya samu karaya sauran mutanen motar kuma duk buguwa ce. A hankali ya buɗe motar ya fito kasancewar jin koke-koken yaran da motarsu ta bige.

Kafin ya ƙarasa tuni Dogarawan ɗayar motar sun nufo gurin da suke da sauri suka kama Sarki Aminullah suna masa sannu, cikin galabaita yace. "Ku ƙyaleni kuje ku duba bayin Allahn cen" da sauri suka ƙarasa gurin suka samu mata Huɗu a akwance sai ƴaƴayensu uku da suke kuka Cen gefe suka hango wani bafulani da alama iyalansa ne jini na zuba ta kansa, Sarki Aminullah ne ya kira jami'an tsaro na garin Kano ya sanar dasu halin da ake ciki, ba'a ɗauki Jami'an tsaro na garin da suke suka ƙaraso tare da motar asibit suka kwashe su gabaɗaya zuwa asibiti.

A cikin mutanen da motar Mai Martaba ta bige mace ɗaya ce ta rayu, sai ƴaƴansu biyu suma kuma basu ji wani ciwo sosai ba, Mai martaba ya bada umarnin a wuce dasu gida a haɗasu da uwar bayi. Su kuma sauran gawarwakin tare aka yi musu suturu Mai martaba da kansa ya sallace su aka kai su makwancinsu.

Daga cikin Waɗanda aka wuce da su gida Akwai Inna Habi sai Maryu da Abu, tunda aka doshi shiga gidan sarautar Maryu ta fara ganin wata irin walƙiya na hasawa tana giftawa har tana neman kashe idonta, kanta ne yayi mata wani dummmm ga jiri da yake neman ɗaukanta, suna shiga cikin gidan kanta ya hau sarawa nan take zazzaɓi ya rufeta, sama-sama take jin kamar hayaniya akanta amma tana waigawa babu waɗanda suka hayaniyar babu alamarsu.


😄😄TO FA YANZU WANSAN ZAI FARA ƊAUKAN ZAFI😄😄


_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[3/8, 5:46 PM] AU MARYAM: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️


*ANYA BAIWA CE?*

Na

*AMEERA ADAM*


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._


FREE PAGE 8


Abu ce ta dafata ta ce, "Maryo lafiya kuwa" Maryo lumshe idanu tayi tana jin kanta yana daɗa sara mata ta ce. "Abu wallahi kaina ne yake juya mun ji nake juwa na ɗiba na" Inna Habi ta ce. Sannu Maryo kinji? Bayan shi ko wani abun yana damunki?" Uwar bayi cikin masifa ta ce. "Kai dallah kuyi ku ɗaga ƙafa sai tafe kuke kamar masu tausayin ƙasa haba, banda ma ku baƙin takawa ne kwa tsaya kuna mun tafiyar rangwaɗa wallahi sai kun fanshe wannan rangajin da aikin wahala" Gabaɗaya babu wanda ya kula ta har suka ƙarasa sashen bayi Uwar bayi na zuwa da ƙwalawa Zainu kira da sauri ta fito cikin girmamawa ta ce. "Gani uwar bayi" a yatsine Uwar bayi ta ce. "Ga baƙin takawa ne ki kaisu ɗakinku" tana gama faɗar haka ta juya ta fice.

Zainu ce ta musu jagora zuwa cikin ɗakinsu, a gajiye su Inna Habi suka zauna a fakaice suke bin cikin ɗakin da kallo, sauran bayin da ke sanye da kayan bayi sai binsu suke da kallo jin ance baƙin Mai Martaba ne, suna nan zaune Jakadiya ta shigo cikin gidan kamar wacce aka jefo haka ta tsaya daga bakin ƙofar ɗakin tana binsu da kallo, Inna Habi ce ta russuna ta ce. "Ina wuni Inna" Jakadiya ya mutsa fuska tayi ta ce. "Kar dai kune baƙin takawa?" Murmushi Inna Habi tayi ta ce. "Eh mune" Jakadiya ta taɓe baki ta ce. "Ai naga alama to amma ba Inna sunana ba, ni da kika ganni Jakadiya ce babu wanda bai san matsayina ba a gidan na" Inna Habi ta gyaɗa cikin ladabi ta ce. "Zamu kiyaye" Maryo tunda ta zaune ta dafe kanta sama-sama take jin maganganunsu kuma har zuwa wannan lokacin bata daina jin maganganun farkon shigowarta masarautar ba, Jakadiya ta gyara tsayiwa tana gyara ɗaurin zaninta ta ce. "Yaya sunanku kun zuba mun na mujiya sai kallona kuke" Inna Habi ta ce. "Ni sunana Habiba wannan kuma Zainabu Abu ga Maryo duka ƴaƴana ne" Jakadiya ta ce. "Yayi kyau zan wuce sai na ƙara zagayowa" Jakadiya na wuce Inna Habi tabi Jakadiya da kallo lokaci ɗaya suka haɗa ido da Abu, ita kuwa Maryo duk budurin da akeyi kanta na ƙasa saboda sarawar da yake mata. Inna Habi ce ta ce. "Maryo lafiya kuwa ko jikin ne?" Maryo ta ce. "Inna wallahi har yanzu kaina sarawa yake ga wata irin hayaniya da nake ji" Inna Habi ta ce. "Kinsan gidan sarakai na'a rabasu da jama'a dole kiji hayaniya" Maryo taja ta jingina da bango tana runtse idonta.

Bayan kwana su Inna Habi na zaune Mai martba ya aika kiransu da a wannan ranar har sun fara sakin jikinsu da waɗanda suke kwana ɗaki ɗaya, sai dai alhinin rashin da sukayi da ƴan uwansu. Gabaɗaya suka ƙara gurin Mai Martaba a fada yana zaune da shi da Galadinma sai Waziri, Cikin girmamawa suka gaishe sa Sarki Aminullah bayan ya amsa ya ƙara da cewa. "Ya baƙunta" Inna Habi ta amsa da, "Alhamdulillah ranka shi daɗe" Sarki Aminullahi yace. "Masha Allah, maƙasudin kiranku na kira ku ne domin naji tarinku da ainihin garinku da inda zamu je mu sadu da ƴan uwanku, dan mu jajanta musu da rashi ƴan uwa su da sukayi" Inna Habi hawaye ta goge murya na rawa ta ce.

"Allah ya taimake ka a yanzu dai maganar da nake maka bani da kowa kaine uwata kaine ubana, Mutumin da ya rasu lokacin da kukayi hatsari Mahaifina ne" Inno ta tsagaita da maganar tana share ƙwallah ta ci gaba da cewa. "Mahaifina ne shi kaɗai ya rage mun kuma shima Allah ya karɓi rayuwarsa." Sarki Aminullah ya ce. "Baki da dangim mahaifi ko mahaifiya" Inna Habi ta ce. "Bansan dangin Mahaifi da mahaifiyata ba, sai dai wata rana Mahaifiyata kafin ta rasu ta taɓa bani labari cewar ita da Mahaifina ƴan ƙasar Agadaz ne wani daliline ya rabosu daga garin sakamakon rashin amincewa da Iyayensu sukayi da aurensu, tun da suka baro garinsu basu ƙara komawa ba wannan dalilin yasan nida ƴan uwana muka tashi bamusan kowa daga danginsu ba, na taɓa aure da ƴaƴa uku sai mijin ya rasu lokacin da ciwon baƙwan dauro yazo yarana suka kamu da ciwon ta sanadin haka na rasa ɗaya daga ciki, sai biyu ne Allah ya barmun su gasu nan har sun fara girma, dangin Mahaifinsu tun bayan rasuwarsa suka gujeni da yake fulanin tashi ne tun daga lokacin bamu ƙara sa kowanne daga cikinsu ba. Daga cikin waɗanda suka rasu akwai Mahaifina, Mahaifiya sai ƴan uwana guda biyu wannan shine tarihina." Cikin tausaya Sarki Aminullah yace. "Allah ya jiƙansu ya gafarta musu.'" Inna Habi ta ce. "Amin ya rabbi" Sarki ya ci gaba da cewa. "Zamu ci gaba da riƙe ku a ƙarƙashinmu Allah ya albarkaci rayuwarsu" Gabaɗaya suka amsa da Amin. Maryo tun da ta zauna take ƙurawa Sarki Aminullah ido har sai da shi kansa ya lura da irin kallon da Maryo take masa, mamaki ne ya kamashi saboda yasan duk cikin talakawa da fadawansa da sauran masu sarauta da suke ƙarƙashinsa basa iya haɗa ƙwayar idonsu da nashi, sai gashi ya haɗa idanu da Maryo yafi a irga amma ta kasa ɗauke ƙwayar idonta a kansa, Waziri da Galadima ba ƙaramin mamaki sukayi da ganin haka, har sai da Sarki Aminullah ya kalli Inna Habi yace. "Ya sunan yaran naki" Inna Habi ta ce. "Wannan Zainabu ce muna kiranta da Abu ita kuma wannan Maryama ce muna kiranta da Maryo" Inna Habi ta ƙarasa faɗa tana nuna Maryo da har lokacin ƙwayar idonta na kan Mai Martaba, Muryar Sarki Aminullah ce ta katseta ta sunyar da kai ƙasa taji yace. "Allah yayi musu albarka, zaku iya tafiya" Cikin ladabi suka russuna suna godiya gai Mai Martaba sanannan suka fice.

Tun kafin su fice daga farfajiyar Sarki Aminullah Maryo ta tirje a gurin ta ce. "Inna wallahi nasan wannan Sarkin kuma ko jiya a tsakiyar dare sai da ya zo gurina yace inbishi mu tafi..." da sauri Inna Habi ta sa hannu ta toshewa Maryo baki tana waigawa gefe da gefe muryan cen ƙasa ta ce. "Ke Maryo ahir na ƙarajin makamanciyar wannan maganar sai ranki ya ɓaci, so kike wani yaji ya kai ƙararmu a koremu bayan Allah ya rufa mana asiri? Idan aka koremu ina muka kama ki rufa mana koda wasa karna ƙara jin haka" A dai-dai wannan lolacin Fulani Maryama ta ƙaraso cikin soron da alama wucewa zata yi, binsu tayi da kallo daga ƙasa har sama har ta wuce su taga babu wanda ya tanka mata sai ma binta suke yi da kallo. A wulaƙance Fulani Maryama ta dawo ta ce. "Ku ƴaƴan gidan uban waye, waye Ubanku a garin nan da me kuke taƙama da har zanzo wuce wa baku gaisheni ba" da sauri Baiwar dake biye da ita a baya ta ce. "Ƙarya kuke ƴaƴan talakawa Fulani Maryama tafi ƙarfin wargi" Jiki na rawa Inna Habi da Abu suka tsugunna suka fara kwasar gaisuwa, Maryo ido ta ƙurawa Fulani Maryama babu ƙiftawa, a hankali Fulani Maryama ta fara takowa har gaban Maryo tana yi mata wani irin kallo mai wuyar fasaltuwa.

KUYI HAƘURI DA SHORT TYPING BANYI EDITING BA KUNSAN ƳAU WEEKEND OGA NA GIDA😉


_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️


*ANYA BAIWA CE?*

Na

*AMEERA ADAM*


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._


FREE PAGE 9



Fulani Maryama ta jima a tsaya tana ƙarewa Maryo kallo itama kuma Maryo bata ɗauke idanunta daga kan Fulani Maryama ba, wani murmushin gefen baki tayi nan take ta ɗauke Maryo da wani gigitaccen mari, nan take kanta ya sara ɗagowarta yayi dai-dai da ɗigar jini daga hancinta. Da sauri Inna Habi ta sha gaban Fulani Maryama ta ce. "Ranki shi daɗe Allah ya huci zuciyarki dan Allah ki yafe ta tayi kuskure, yarinyar nan ba lafiyayyi bace tana da matsalar ƙwaƙwalwa ne haka take yi tun kafin muzo nan" Fulani Maryama da fuskarta tayi murtuk ta ce. "Nan gaba sai ta banbance gidan da kuka baro da inda kuke yanzu, ƙarshen hauka idan a turu take a cikin gidan nan za'a saita mata zama Ni Fulani Maryama nafi ƙarfin kallon ƙasƙanci, me mulki ma a gidan nan bai isa zura mun ido ba bare ku ƙasƙantattun bayi" Fulani Maryama ba gama faɗa ta wuce fuuuu baiwarta na take mata baya.

Inna Habi da sauri ta fisgo Maryo da har lokacin jini na fita daga hancinta ta ce. "Maryo meye haka kike yi ne meyasa kike so ki jaza mana masifa Allah ya rufa mana asiri, anya Maryo wannan taurin kan naki zai barmu mu zauna lafiya a gidan nan" Idanun Maryo da suka rine jawur ta ce. "Inna akanme zatayi mana wulaƙanci to idan so take mu gaishe ta basai ta faɗa ba?" da sauri Inna Habi ta janye hannun Maryo suka wuce cen sashensu, sai da suka ƙure a ɗaki lokacin ta wanke jini hancinta Inna Habi ta ce. "Maryo ita rayuwar duniya ƴar haƙuri ce kinga nan gidan sarauta ne kuma a ƙarƙashin wasu muke, bamu da kowa sai Allah sai waɗannan bayin Allahn komai zaku gani a gidan kuyi haƙuri ku kauda kawunanku. Mai haƙuri shi zai dafa dutse har ya sha romo" Maryo ta ce. "Inna gaskiya wannan karan bazan yi haƙuri ba a irin haƙurin da nayi a baya ne aka cutar dani, yanzu haka zan ci gaba da haƙuri na kuma ƙare rayuwata babu jindaɗi?" tana ƙarasa faɗa hawaye ya fara zuba a idanuwanta. Inna Habi ta kalleta sosai ta ce. "Waye ya cutar da ke Maryo yaushe muka zo gidan shin tunda kika zo gidan nan wani yayi miki wani abu ne ban sani ba? Idan ma ancutar dake haƙurin dai dana baki shi zaki yi mahaƙurci mawadaci" Maryo ta ce. "Maganar gaskiya Inna wannan karan bazan zura ido ba" tana gama faɗa ta kwanta tana juya bayanta.

Bayan kwana biyu da yamma liƙis Bayan su Maryo sun kammala sirfen gero suna zaune suna hira ita da Abu da wata baiwa Dije, Abu ta ce. "Dije wai a gidan nan babu inda kuke zuwa ne wallahi ni ƙafa gabaɗaya ƙaiƙayi take a cen rugarmu mun saba da yawace-yawace, Abu ta ce. "Muna ai muna fita amma ba ko ina ba sai guri mai muhimmanci, kuma ai cikin gidan nan ma ya isheki yawo tunda babban gida ne, Maryo tayi murmushi ta ce. "Gaskiya ku zo mu shiga mu wasa idanu dan wallahi ni kaina na gaji da zama" miƙewa suka yi Dije tayi musu jagora suka dinga zaga gurare, sun jima suna kewaye-kewaye har magriba ta fara kawo kai lokacin sun shiga cen wajen gari banda bishiyoyi da sauran tsintsaye babu abinda yake tashi a gurin.

Suna tafe a hanyar su ta dawowa suka ƙaraso wajen wata murgujejiyar bishiyar kuka gida biyu da suke gefe da gefe reshensu ne ya yiwa hanyar rumfa, wajen babu komai sai kukan tsuntsaye ga wata iska me sanyi da take tashi a gurin.

Tunda suka tunkaro gurin Maryo ta hango wata kyakykywar fada a gurim me ɗauke da ado kala-kala masu ƙayatarwa da wata ƙayatacciyar kujera a gurin babu kowa akanta, wasu mutane ta gani kewaye a gurin suna ƙarasowa suka fara russunawa wasu kuma suna kiranta suna nuna mata karagar kujerar. Banda waige babu abinda take yi har suka so gota gurin ganin haka yasa Abu ta ce. "Maryo lafiyarki me kike kallo ne haka" Juyawa tayi suka ci gaba da tafiya batare da tace komai ba, shiru ne ya biyo baya har suka wuce.

Suna gabda ƙarasowa cikin Mutane suka bi ta wajen bishiyar tsamiya har sun kusa gota wajen ta ja tunga ta tsaya, Dije ce ta kalleta ta ce. "Maryo kiyo sauri kinga magriba ta kawo kai kizo mu wuce ciki" nan take kanta ya sara a hankali ta fara kallan mutanen dake kan bishiyar ta gyaɗa kai sannan suka wuce.

Da daddare misalin ƙarfe goma dare gidan yayi tsit yawancin bayim sunyi bacci idan da waɗanda basuyi ba ma kaɗan ne, cikin mafarki ta ganshi ya ƙaraso gurinta da hawaye fal idanunsa yana zuwa gurinta ya ce. "Sun cutar da Mahaifina a wancen karon dan ALLAH karki bari wannan karanma su cutar da shi, bani da ikon aikata komai kiyi wani abu dan Allah ki ceto rayuwar mahaifina bazan iya jure rashinsa a wannan karan ba" zumbur Maryo ta miƙe tana faɗa gumi sai kuma ta tuno da abinda ta ji, kamar wacce aka zabura da sauri ta miƙe ta fice daga ɗakin lokacin ƙafa ta fara ɗaukewa.

Tana fita kai tsaye sashen Mai martaba ta nufa a lokacin Sarki Aminullah na zaune yana hutawa ga damammiyar fula da taji zuma a ƙwarya, kai tsaye Maryo sashen ta nufa duk yadda dogarawa suka so hanata abun ya gagara, da sun zo riƙeta tana hankaɗe su suke faɗuwa a gurin, haka tayi ta kutsawa har sai da ta shiga cikin turakarsa tana zuwa ta ɗauke ƙwaryar furar har taje bakin ƙofa sarki Aminullah ya ce. "Wacece ke" kamar bazata juyo ba ta jima a tsaye har sai da ya fara takowa cikin wata irin murya ta ce. "RAYZUTA ce" tana gama faɗa ta fice daga ɗakin, da sauri sarki ya bita amma ga mamaki tuni ta wuce ya nemeta sama ko ƙasa ya rasa, abu ɗaya ya riƙe ya ganta sanye da kayan bayi."


KUYI HAƘURI DUK WEEK END BAZAN DINGA POSTING DA YAWA BA SABODA BANDA TYM SOSAI. KWANA BIYU ZAKU JINI SHIRU SABODA WANI UZURI BABBA IDAN KUMA NA SAMU DAMA ZAN MUKU TYPING. FATAN ALHERI🥰

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️


*ANYA BAIWA CE?*

Na

*AMEERA ADAM*


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._


LAST FREE PAGE 10


Jiki a sanyaye Sarki Aminullah ya ƙara leƙawa harabar gurin amma babu ita babu alamarta, gyara tsayuwa ya yi ya furta, "Rayzuta? Wace me tsaurin idon Baiwa ce har za ta shigo cikin fadata ta ɗauke abinda zansa a baki na, ina masu gadin bakin ƙofar?" Sai a lokacin ya tuno da dogarawan gurin yana dubawa gefe da gefe ya hangosu a kwkkwance da alama babu me motsi a cikinsu. Tsoro ne ya fara kama shi da sauri ya ƙarasa gurin ya fara tattaɓasu yana kiran sunayensu, daga cen gefe Harisu ne ya fara motsawa yana jin muryar Mai Martaba ya miƙe a zabure yana rissina masa. Sarki Aminullah ya taka a hankali ya matsa gurin Harisu yace.

"Harisu me ya faru daku haka? Harisu ɗan jim yayi kamar me nazari sannan yace. "Allah ya taimakeka na tuna, muna tsaye wata Baiwa me sanye da kayan bayi ta ƙaraso gurinmu kai tsaye ta tunkari ƙofar shiga turakarta, muna ƙoƙarin hanata ta hankaɗe mu gefe nidai daga haka ban ƙara sanin abinda yake faruwa ba." Ajiyar zuciya Sarki Aminullah ya sauke ya waiga gefe da gefe sannan ya ƙarasa gurin Harisu har sai da ya kai dabda kunnensa sannan yace. "Harisu ka bamu hankalinka nan bama san shiririta ko shirme, musan ka bincika muna a cikin bayi mata wacece RAYZUTA? musa san ayi binciken cikin sirri ko ƴan uwanka dogarawa banasan su samu wannnan labarin, idan har labarin ya fita ranka zaiyi mummunan ɓaci" Harisu cikin girmamawa ya rissina yace. "In sha Allah zan ayi yadda kace Mai martaba Allah ya ƙara nisan kwana da jinkiri mai amfani" Sarki Aminullah takawa yayi ya koma cikin turakarsa. Harisu ne ya dinga bin ƴan uwansa yana yayyafa musu ruwa sannan suka miƙe kowanne yana mamakin abin da ya faru.

Rayzuta kai tsaye tana barin gurin bata tsaya ko ina ba sai hanyar dajin nan wajen bishiyoyin kukar nan guda biyu, tana zuwa ta nemi guri ta zauna tana ƙarewa ƙwaryar fura da nonon kallo. A hankali ta dinga sa ɗan yatsanta tana tsince gubar da ke cikin furar, tana nan zaune ta hanyo wasu ayarin mutane suna tunkaro ta a hankali ta fara ja da baya suna ƙara tunkarota, tana niyyar yunƙurin guduwa suka cimmata da sauri suka fara zagaye suna faɗin wasu irin kalmomi da bata fahimtarsu, russunawa suke alamun girmamawa suna ci gaba da zagaye ta wani namiji ta gani ya ƙaraso gurinta har lokacin bata

Please Login or Register in order to submit comment