Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gane fuskar ko waye ba, zuwa yayi ya tsaya a kusa da ita yana murmushi tare da shafa fuskarta bata yi aune ba taji ya haɗa bakinta na shi sai a lokacin ta ga fuskarsa, suna cikin wannan yanayin taji an fisgi hannunta da ƙarfin gaske. A tsorace suka juya ita da matashin da ke rungume da ita cikin mamaki haɗe da tsoro, cikin izza ya ƙarasa gurin ta ya fisgi hannunta ya fara ƙoƙarin rungumeta da ƙarfin tsiya tana gocewa. Matashin yana ganin haka ya ƙaraso da gudu zai janyeta da sauri wancen matashin ya zaro wuƙa ya yanke shi a hannu. Hannu ta fara miƙa masa alamar ya ceci rayuwarta shima ya fara ƙoƙarin miƙa mata hannu dukda jinin da ke zuba a hannunsa. Ɗagowa tayi cikin kukan ta ce. "Furzan karka bari yayi nasara akanka kafin sanin ko waye shi dan Allah ka ceceni daga gurinsa, idan ba haka ba zan kashe kaina gwara na mutu da rayuwa da wannan" da sauri matashin ya miƙa hannunsa da niyyar cetonta amma wancen ya ƙara saka masa wuƙa a tafin hannunsa, a hankali ya sulale ƙasa ya faɗi jini na fita daga jikinsa.

Ana cikin haka Suka hango wani ya ƙaraso gurin ya fisgi hannunta ta ƙarfin tsiya ya wuce da ita cen cikin surƙuƙin dajin ba tare da waɗancen samarin sun iya aiwatar da wani abu ba, sai ma ganin wani ayarin tayi sun rufe Furzan da duka, tana riƙe a hannunsa ta fara ƙwala ihu tana cewa. "Furzaaaaan! Furzaaaaan dan Allah kazo ka ceci rayuwa ta."

Juye-juyen take yi tana mutsu-mutsu har sai da ta fara birgima a cikin ɗakin, idanunta a rufe suke bakinta na ambatar sunan "Furzaaan" Inna Habi ce ta farka ganin abin da Maryo take yi yasa ta fara tashinta a hankali. Firgigit ta miƙe jikinta ya jiƙe sharkaf da gumi, da sauri ta rungume Inna Habi ta fashe da kuka har lokacin jikinta na karkarwa kamar mazari. Inna Habi rungume ta tayi tsam tana karanto mata addu'o'in da ta iya na bakinta har sai da ta lura da Maryo ta fara dawowa nutsuwarta. Kallan Inna Habi tayi idanunta cike da hawaye ta ce. "Inna wallahi tsoro nake ji na rasa me yake damuna ina jin tsoro wallahi kar su cutar da shi" A hankali Inna Habi ta ce. "Waye" Maryo ta fara girgiza kai tana hawaye ta ce. "Wallahi bansan shi ba Inna, ni banma taɓa ganinsa ba kawai dai ni inajin kamar yana da muhimmanci a rayuwata, ina jin kamar ma na taɓa saninsa a rayuwata, amma Inna ina jin tsoron waɗannan abubuwan da suke faruwa da ni. Inna wannan mafarkan suna bani tsoro..." da sauri Inna Habi ta rufe mata baki ta ce. "Ki daina faɗa Maryo babu abin da zai faru da ke sai alkairi, rashin addu'a ne da bakwa yawan yinta akai-akai ki kwanta insha Allahu bazaki ƙara irin wannan mafarkin ba"

Maryo har zata kwanta ta kalli Inna Habi ta ce. "Inna har wani suna naji suna ambatona da shi amma na manta shi" Inna Habi ta ce. "Karki damu wannan yana daga cikin shirmen mafarki, bari na tofa miki addu'a babu abinda zai faru da ke" Maryo ta koma gurin kwanciyarta ta kwanta Inna Habi ta fara karanto mata ayoyin tsari, Maryo sai kusan asuba bacci yayi awon gaba da ita.


Washe gari Dogarin Sarki Harisu ya dinga shige da fice yana bugar cikin bayi mata tare da tambayar wata baiwa me suna Rayzuta amma bai samu nasarar amsar tambayarsa ba, sai da ya kwana bakwai cir yana bibiyar me wannan sunan a ɓoye amma babu wata baiwa me irin wannan sunan, hasalima yawanci duka ya san sunayensu dama waɗanda suke bakin fuska su Maryo ne kuma dama waɗannan kusan kowa yasan baƙin sarki ne. Da daddare bayan ƙafa ta ɗauke Harisu ya samu Sarki Aminullah ya sanar dashi duk abinda yake faruwa, bayan ya gama sauraron Mai Martaba yace. "Harisa mun saurareka dan haka wannan maganar a binne ta bana buƙatar jin ta a bakin wani ko wata a gidan nan" cikin girmamawa Harisu yace. "Da kai da kaya duk mallakar wuya ne, idan har kaji wannan maganar ta fita to ka yanke mun hukunci me tsanani Ranka shi daɗe." Jinjina kai Sarki Aminullah yayi sannan ya sallami Harisu.

Sarki Aminullah ya jima yana nazarin abin da ya faru amma ya rasa wacece ta aikata haka, daga ƙarshe ya watsar da lamarin yana addu'a a ransa akan Allah ya yi masa tsari da duk wani mai nufinsa da sharri.

Maryo washe garin ranar haka ta tashi sukuku da ita bata da wata walwala, Inna Habi ta lura da haka kuma hakan ba ƙaramin sa ta yayi cikin damuwa ba, sai bayan Azahar Maryo ta ɗan saki jikinta har suka fita ita da su Abu suka gudanar da ayyukan da suke yi duk yammaci.

Fulani Maryama ce ɗurƙushe gaban Boka Marduska gabaɗaya yanayinta tana cikin damuwa, Ɗagowa yayi da jajayen idanunsa masu kama da gauta sannan ya bushe fa wata irin dariya yace. "Zina bata cikin tsarin aikina ba da ɗana dake Maryama tunda na lura kin zama haja kowa baje kolinsa yake akanki, idan angirma ya kamata ace angirma amma da alama kin zama holoko haɗarin kaka." Fulani Maryama ta ɓata fuska ta ce. "Haba sarkin bokayen duniya ya nazo ka share mun hawaye na amma kuma kana gaya mini maganganu marada daɗi" Boka Marduska ya kuma bushewa da dariya sannan ya murtuke fuska yace. "Bani na kar zomon ba ko ratayar ma ba'a bani ba, karfa wani narkeken ƙaton banzan ya shirga miki ciki ki zo ki sauke ɓacin ranki a kaina" Fulani Maryama fuska cikin damuwa ta ce. "Marduska ka taimaka mini bansan ya zanyi ba wallahi idan cikin jikina ya fito bansan ya zamu kwasheta da Mai martaba ba, tunda na gaya maka wancen karon Mai Martaba ya samu lalura yanzu babu wata mu'amalar aure da muke gudanarwa mu da shi." Boka Marduska ya zura hannunsa a cikin waka ƴar siriyar rijiya ya zaro wani garin magani ya miƙa mata yace. "Ungo wannan ki kaɗa shi a ruwa ki sha cikin zai ɓare sai kuma ki kiyaye gaba" Fulani Maryama tayi masa godiya ta ce.

"Marduska amma bazan iya jure rashin haka ba kuma antabbatar mana da Mai martaba bazai samu lafiya ba" Boka Marduska ya zurawa Fulani Maryama Idanu sannan ya ce. "Maryama karki fake da guzuma ki harbi karsana dama cen halinki ne, ko kin manta Salman ba jinin Sarki Aminullah bane? Gwara kiya taka tsantsan dan daga wannan bazan ƙara baki maganin zubda ciki ba mata ƴar firit da ke sai jarabar tsiya, ki tashi ki bani guri sakamakon mu zai biyo baya da daddare zamu ɗauki ɗaya daga cikin bayin ku"Boka Marduska yana faɗa ya ɓace daga gurin, Fulani Maryama da yake ita kaɗai ta kai wannan ziyarar ta miƙe ya fice daga cikin kogon dutsen.

Washe gari tun safe Fulani Maryama ta aiwatar da abinda ta karɓo daga hannun Boka kuma ba'a ɗauki lokaci ba ta fara zubar da jini, bayan wani lokaci cikin ya zube gabaɗaya.
Tun safiyar ranar ta fara kasa kunne taji anyi shelar mutuwa, amma taji shiru sai kusan Azahar labari ya isar mata na rashin lafiyar Baiwarta Bintu, wai tunda gari ya waye take ta aman jini labarin na zuwa gurin Sarki Aminulllah ya sa aka ɗauke ta aka wuce da ita asibiti.

Fulani Maryama taji ba daɗi sosai saboda sunyi sabo da Bintu a ƙalla sun kusa sheka goma tare kuma ba ƙaramin biyayya take mata ba. Sakamakon haka yasa Fulani Maryama ta sa aka tara mata bayi dan ta zaɓi wacce zata maye gurin Bintu, dan ta tabbatar Bintu dai bazata tashi ba da alama Aljanun Boka Marduska sun jinkirta kashe ta. Tara mata su akayi gabaɗaya ta fara zagaya su ɗaya bayan ɗaya tana zuwa kan Maryo ta zaɓe ta. Haka sauran suka tarkata suka wuce suna jin inama ace sune suka samu aka zaɓe su. Inna Habi Addu'a ta dinga yi a zuciyarta kar Maryo ta nuna irin halin da ta nunawa Fulani Maryama rannan, cikin sa'a kuwa Maryo ta russuna da girmamawa ta yi wa Fulani Maryama godiya sannan ta fara takewa Fulani Maryama baya har suka shige sashen matan Sarki.

Kamar almara suna shiga a mararrabar sashen matan Sarki ta Hango Saif ya tako da ƙafafuwansa yana tafe yana laluben bango, yana wani irin baƙin amai mai warin gaske, A zabure Fulani Maryama ta ce. "Saif kaine kake tafiya da ƙafafuwanka?" juyawa tayi ta kalli Maryo ta ce. "Maza jeki zan neme ki anjima." Maryo ta juya ta tafi tana waigen Saif da ya haɗa uban gumi har lokacin bai daina aman ba, kafin ta fita Fulani Zaliha ta shigo tana salati ganin halin da Saif yake ciki." Fulani Maryama har harɗewa take saboda sauri tana shiga ɗakinta ta ɗebo wuri ta fara karanta kalmomin da Boka ya bata, nan take ta bayyana a bakin kogonsa hankali a tashe ta shiga ta fara ƙwalla masa kira.

Dukda a lokacin rana ta buɗe amma kogon nasa da ɗan duhu saboda idanuta sun rufe bata hangoshi ba, har sai da ta kusa taka shi tana ganinsa ta ce. "Marduska kamun rai yaron nan Saif ya fara takawa wallahi da matsala" Boka ya yi mata wani irin kallo yace. "Maryama ke me yasa kanki kamar na tinkiya haka yake? Kin shafe sama da shekara ashirin kina zuwa gurin nan kuma duk zuwan da zakiyi sai kun wayi gari da mutuwar Bawa ko Baiwa a masarautarku, amma wannan zuwan da kikayi kinji shelar mutuwa ne?" Fulani Maryama da ta kasa zama saboda tashin hankali ta ce. "A'a Marduska sai dai baiwata Bintu ba lafiya tana asibiti" Boka Marduska yace. "To idan ke me hankali ce yaci ace ki fahimci akwai babbar matsala, idan kin tuna shekarun baya na gaya miki Rayzuta zata shigo gidanku kuma yanzu haka ta shigo dan haka dabara ta ragewa me shiga rijiya."


INASHA ALLAH TUN DA NA SAUKE FREE PAGES ZAN DINGA POSTING SAU BIYI SABODA LABARIN DA TSAYI IDAN NACE ZAN DINGA SAU ƊAYA ZAN DAƊE INA TYPING, AMMA FA BANYI ALƘAWARIN KULLIN BA LOKACI-LOKACI HAKA.

YESSSSOOOO💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 YANZU WASAN ZAI FARA FA SHIN FULANI MARYAMA ZATA GANO WACECE RAYZUTA IDAN TA GANOTA WACE CAKWAKIYAR ZA'A YI? HAUSAWA SUKA CE FAƊA DA ALJANI FA BA RIBA😂😂😂 TO WAI SHIMMA MARYO MUTUMCE KO ALJAN IDAN MUTUM CE ME YE ALAƘARTA DA RAYZUTA IDAN KUMA ALJANA CE YA AKAYI TA ZO DA SIFFAR MUTANE. TO WAI MA MEYE ALAƘAR MARYO DA MAFARKIN SAMARIN NAN DA TAKEYI SHIN DAMA TA TAƁA RAYUWA DA SU NE KO YAYA???? 🤣😂😂

GABAƊAYA AMSOSHIN TAMBAYOYIN NA GARENI KU DAI KARKU BARI A BARKU A BAYA DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI TUN DAGA FARKO HAR ƘARSHE, NASAN KUN KARANTA LITTAFAN SARAUTA DABAN-DABAN AMMA BA INA YABON KAINA BA WANNAN LABARIN SALONSA DABAN YAKE 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️


_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉


An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment