Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ASSO...*

LAST FREE PAGES 10


Ilahirin jikin Mommy ban da karkarwa babu abin da yake yi saboda tsananin tsoro, firgici da tashin hankali. A takure take a ƙuryar gado ta sunkuyar da kanta ƙasa saboda tozali da ta yi wata shirgigegiyar mummunar hallita, girman hallitar ta zarce goggon biri ga wasu irin ƙwala-ƙwalan idanu da suka zazzago kamar za su faɗo ƙasa. Bakinta ban da fiƙoƙi babu komai a ciki sai ƙaton hancinta mai ƙofofi takwas, tare da manyan ƙahunhuna guda biyu. Sautin takun Hallitar kan iya nakasta dodon kunne don haka Mommy ta sa hannuwa biyu ta toshe kunnenta da take jin sa kamar zai tarwatse, Hannuwan hallitar kama suke da ƙafafuwan doki don haka a duƙushe take tafiya rafkeken kanta shi ne a gaba. Jin shirun takunta ya sa Mommy ta ɗago da kanta a zatonta ko hallitar ta ɓace daga wurinta, sai dai tana ɗagowa suka haɗa ido da hallitar nan take ta hango Raihan maƙale a hannun hallitar tana kuka tana miƙawa Mahaifiyarta hannu, jikin mommy har rawa yake yi ta yunƙura don zuwa wurin hallitar tana faɗin, "Don Allah ki bani ƴata ita kaɗai na mallaka karki hallakata, Hallitar ce ta fara ja da baya tare da Raihan ta fara yunƙurin kai kan Raihan zuwa bakinta don ta laƙumeta, da sauri Mommy ta yunƙura cikin tashin hankali ta furta, "Raaaaihaaaaan."

(Allah sarki Uwa kenan😰 Duk tsanani Mahaifiya ba za ta so ganin abin da zai cutar da Ƴarta/Ɗanta ba.)

Firgigita Mommy ta farka daga mummunan mafarkin da take yi, har lokacin da ta farka jikinta ban da rawa babu abin da yake yi. Da allon gado ta jingina a hankali bakinta na furta Ayatulkursiyyu don ba ƙaramin tsorata ta yi da mafarkin ba. Raihan na gabda da yankar ɗan yatsan mahaifiyarta ta ji wani irn turiri ya yo kanta da sauri ta ja da baya don kaɗan ya rage bata ƙone ba. Farkawar da Mommy ta yi ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba don ta yi bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta aiwatar da abin da yake tafe da ita. Daddy ne ya ajiye takardar hannunsa ya ɗago yana kallon wurin da Mommy take ya ce, "Lafiya dai Mommyn Raihan na ji kina ambatar sunan Raihan cikin dare." Mommy ta yunƙura da ƙyar jikinta gabaɗaya a sanyaye yake ta zauna a kujera mai kallon ta Daddy ta ce, "Daddyn Raihan wani mummunan mafarki na yi akan Raihan, ina jin tsoro matuƙa kar wani abu ya faru da ita. Maganar gaskiya ina tunanin babu shaiɗanu a lamarinta kuwa, kana gani ƙa'ida bana iya kwanciya ba tare da alwala ba kuma addu'a bakin gwargwado ina yi amma idan mummunan mafarki na tashi yi sai na da yarinyar nan a ciki..." Daddy ya yi murmushi sannan ya katseta da cewar, "Zainabu kenan, duk fa abin da kafi sawa zuciyarka yana tare da kai. Ba tun yau ba na sha gaya miki ki bar danganta ciwon yarinyar nan da wasu shaiɗanu, ki gaya min Raihan ina take zuwa da za ta kwashi shaiɗanu? Ƴarmu a killace take ban da makaranta tana zuwa wani wurin? Karki manta silar ciwon yarinyar nan tun bata fi shekara biyar a duniya ba muka wayi gari da shi, ta yaya za a ce wai wasu shaiɗanu suna bibiyarta kamar wacce take bin kwararo tana jari bola a kan sharar kasuwa." Mommy ta yi guntun tsaki tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Na rasa ya akayi idonka ya rufe haka, kana tunanin shaiɗanu sai a waje ake samun su Daddyn Raihan? Ganin su muke yi da za mu shaida kamanninsu? Idan a baya ta wayi ido da ciwo shin muna da lasisin da za mu tabbatar da cewar babu haɗin jinnu a jikinta..." Daddy ya ɗaga mata hannu da cewar, "Zainabu ni da ke muka haifi yarinyar nan, don haka ki nema mata maganin Aljanu tun da so kike ki jawo mana wata masifar muna fama da wannan, shi kenan ki sakar min mara na yi fitsari." Daddy ya ƙarasa maganar a fusace yana tattara kayan gabansa, ya miƙe ya wuce kan gado, jiki a sanyaye Mommy ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala sannan ta saka hijabinta ta nufi ɗakin Raihan don zuciyarta ta gara amincewa ta bari har gari ya waye, a hankali ta fara sauka daga bene sai dai duk taku ɗaya idan ta yi sai ta ji kamar ana bin ta a baya don sai ta ji takun tafiya, sai da ta kusa sauka daga bene ta yi ƙarfin halin juyawa amma wayam babu wanda ta gani. Idanunta ne suka sauka a kan agogon bangon da ke jikin bango wanda ya yi nuni da ƙarfe biyu da rabi na dare, wucewa ta yi hanyar da za ta sadata da ɓangaren su Raihan don gabaɗaya sashensu ɗaya idan aka cire sashen Daddy da yake ɓangarensa daban, a hankali wata sanyayyar iska ta fara kaɗawa mai haɗe da walƙiya tun iskar na kaɗawa kaɗan-kaɗan har ta fara ɗaga labulaye, ƙofofin ɗaki da na window suka fara rufewa da buɗewa a ƙarfi, da sauri Mommy ta fara waigawa don har lokacin bata daina jin alamun takun tafiyar da ake bin ta a baya ba. Tana cikin tafiya ta ga ƙwan fitilar ya fara ɗaukewa yana kawowa, ba shiri ta fara lalube har ta samu ta taɓa jikin bango ta ci gaba da tafiya a jikin bango. Daga bayanta ta ji ƙarar fashewar kwalba tuuuush, a firgice ta fara lalube tana ƙwalawa Daddy kira don iya tsoro ta gama tsorata uwa uba ga shi har lokacin bata daina jin takun tafiya a bayanta ba. Ƙwan fitilar ne ya tsaya cak ya daina ɗaukewa, mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da tafiya a gaggauce cikin sauri. Tana zuwa ta wurin windon da ya fita ta harabar gidan ta hango wata matashiyar budurwa a zaune ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta, da mamaki Mommy ta tsaya tana kallonta sai jikinta ya fara bata kamar Raihan ɗinta don kusan yanayin jikinsu ɗaya, hatta doguwar rigar baccin irinta Raihan ce. Gashin kan yarinyar a barbaje yake ya rufe fuskarta ta yadda ba kya iya ganin ainihin fuskarta.

Duk abin da yake faruwa tsakanin Raihan da Mommy Abar bauta tana kallo a cikin Kogon dutsen ƙungiya, ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi da ganin Mommy na son bata matsala ba. Abar bauta na ganin Mommy ta fito don zuwa ɗakin Raihan ta yi wa Raihan magana da cewa, "Ki hanzarta domin samun nasararki, a yanzu a wanni ne kaɗai suka rage miki don samun ci gabanki. Mahaifiyarki za ta fita ki yi ƙoƙari jan hankalinta zuwa harabar gidanku, sauran aikin ki bar min komai a hannuna ki dawo min da ƙashin bayan mahaifiyata don sauran aikin yana gare ni." Raihan da ke biye da a bayan Mahaifiyarta ta furta, "Biyayya gare ki ta zama wajibi fansar iyayena na gareki ya abar bauta." Raihan na rufe baki ta ci gaba da bin bayan Mommy, tana zuwa ta zauna a harabar gidan kamar yadda abar bauta ta tsara mata.

Alhaji ƙarami ba ƙaramar azaba ya ci a hannun kunamun nan ba, sai da suka ga ya daina motsi sannan suka dakata da azabtar da shi, sakamakon umarnin da uwar ɗakinsu ta basu. Daga wurin da yake Dodon tsafinsu ya ƙarasa cikin takaici don ba ƙaramin haushi ya ji ba ganin ƴan wata ƙungiyar sun azabtar da ta su ɗan ƙungiya ba. A fusace ya kafawa Alhaji Ƙarami haƙora tun yana masa magiya har rai ya yi halinsa, sai da ya tabbatar da baya numfashi ya ɗaga shi yana faɗin, "Da ka mutu ta sanadin wasunmu gara mu ƙarasaka da hannunmu." Kusan lokaci ɗaya Alhaji Ƙarami da matarsa suka Mutu, Likitoci na kan matarsa ta jima tana wani irin fisge-fisge daga ƙarshe ta ce ga garinku nan.

Kabiru yana tafe cikin zuciyarsa yana saƙa da warwara har ya ƙarasa cikin gidan, a lokacin da ya je ƙofar gidan a buɗe ya samu gate ɗin don haka yana turawa da ya shiga ya wuce ɗakinsa da yake a bakin ƙofa yake idan baka lura ba ma ba za ka san ya fita ba. Yana shiga ya ajiye buhun kayansa ya fito ya ɗaura alwala ya gabatar da sallar Isha'i ya yi shafa'i da wuturi . Ya jima yana addu'a da kaiwa Allah kukansa akan mummunar ƙaddarar da ta same shi daga ƙarshe bayan ya idar ya zauna ya fara tilawar alƙur'ani. Ya kusa awa guda yana karatu sai da ya gama sannan ya fito harabar gidan da babu mutane kowa ya kama gabansa, sai da ya kira Daddy a waya ya tambaye shi ko zai ƙara fita ya tabbatar masa da ya rufe gidan babu inda za shi kuma baƙi duk masu tafiya sun tafi.

Sama-sama Mommy ta fara jin kamar ana ambatar sunanta, har ta yi kamar ta wuce ta ji ba za ta iya giftawa ta bar yarinyar da take ji kamar Raihan ɗin ta ba, don tuni zuciyarta ta fara ayyana mata ko ciwon Raihan ne ya tashi ta buɗe ƙofa ta fita harabar gidan ta zauna. Kai tsaye ta nufi hanyar da za ta sada ta da ƙofar fita, sauri-sauri ta fara yi har ta samu nasarar zuwa barandar harabar waje. Kamar wacce ake fisga haka Mommy ta fara jin zuciya da gangar jikinta na azalzalarta zuwa wurin da wannan matashiyar budurwar take bakin ta na furta, "Hasbunallahu..." Ta fara tunkarar wurin gabanta na ci gaba da tsananta faɗuwa, lokaci ɗaya ta ji wani irin tsoro ya mamaye ta sakamakon jin kukan wasu irin tsuntsaye na tashi a saman kanta. Ta maza ta yi ta ci gaba da takawa har ta ƙarasa wurin da Raihan take zaune, Mommy ta fara ƙoƙarin kai hannu za ta taɓa gadon bayanta tana kiranta, "Raihan!" Shiru ne ya biyo baya ba tare da ta amsa ba, Mommy ta sake sunkunyawa ta ce, "Raihan." A haukace Raihan ta ɗago tana bin Mommy da kallo, da sauru Mommy ta yi baya sakamakon tozali da ta yi da mummunar hallita. A madadin da ga fuskar irin ta bil'adam kamar yadda gangar jikinta ya nuna sai gani ta yi ta yage mata baki mai kamar na kura, cike suke da manyan haƙora da fiƙoƙi ga hancinta tamkar na kare haɗe da idanu jawur kamar garwashi. Mommy da ta faɗi can gefe ta fara ja da baya jikinta na rawa, Gadan-gadan Raihan ta fara takawa gabanta don ta bawa Abar bauta damar aiwatar da abin da yake gabanta. Cikin gigita Mommy ta fara karanta duk wata addu'a da ta zo bakinta, tana yi tana kiran sunan Daddy don ya kawo mata ɗauki. Tana cikin wannan halin sai gani ta yi wannan hallitar da ɓace daga gabanta, da ƙarfin gaske ta ji ana fisgarta kamar za a yagi naman jikinta.

Kamar wanda aka tasa daga bacci haka fitsari ya farkar da shi, kasancewar ƙafa ta ɗauke ya sa Kabiru ya fito bakinsa ɗauke da addu'a don ya kewaya banɗaki. Bayan ya fito daga can bayan ɗakinsa ya fara jin motsi, har cikin zuciyarsa ya ji kamar ya leƙa ya ga abin da yake motsi amma sai ya yi tunanin dare ne ta yuwu ɓeraye ne suke dabdalarsu. Mommy na jin motsin Kabiru ta riƙa ƙwalla masa kira amma a banza ko kaɗan bai san ana yi ba, sai dai har lokacin bakinta yana ci gaba da karanta ayoyin Ubangiji, da abar bauta ta zo kawo mata cafka sai ta ga mommy ta zille mata kamar tarwaɗa. Kabiru na shiga ɗaki ya koma ya kwanta sai dai fir idanunsa sun bushe bacci ya ƙaurace masa, tashi ya ƙara yi ya fito a ƙofar ɗakinsa ya ɗaura alwala yana shirin shiga ɗaki ya ji ƙusur-ƙusur ɗin ya yi yawa. A hankali ya fara takawa yana haske-haske da ƙaramar fitilarsa, daga can bayan ɗakinsa ya hango Mommy a kwance sai shure-shure take yi tana motsa baki da alama magana take yi. Tsoro ne ya kama shi don ko a mafarki bai taɓa ɗauka mommy bace a wurin, a tsorace ya fara faɗin, "Hajiya lahiya kuwa?" Mommy hannu ta fara miƙa masa tana kiran sunansa, ganin haka ya sa Kabiru ya fara ƙoƙarin miƙa hannu don ya taimaka mata amma tunowa da abubuwan da suka faru da shi ya sa ya ja da baya yana karanto aytulkursiyyu ya fara tofa mata tare da falaƙi da nasi. Kamar wanda aka yi wa wankin kunne raɗau ya ji maganar Mommy a kunnensa saɓanin da; da baya jin abin da take faɗa, tsugunnawa ya yi a wurin yana faɗin, "Hajiya me ya fito da dake a tsakar daren nan?" Mommy da ta ji jikinta ya fara sarara mata ta ce, "Kabiru taimaka min ka kaini ciki kar su halaka ni." Kabiru ya zaro ido yana dube-dube yana shirin magana mommy ta dafo hannunsa da sauri ya yi baya yana kurma ihu don ya gama tsorata gabaɗaya. Abar bauta da take laɓe ta fara Allah-Allah akan Kabiru ya basu wuri don ta dawo ta ci gaba da abin da take niyyar aiwatarwa, donma ita kanta Mommy ba ƙaramar wahala suka sha akanta ba amma so take ko ta wanne hali ta samu ta lakuci jinin jikinta idan ya so ko da sihiri ne in sun kaiwa ɗakin arziƙi jininta magana ta ƙare. Kabiru har zai shige ɗaki da gudu sai wata zuciyar ta ayyana masa ta yuwu ita ma shaiɗanu sun yi mata abin da suka yi masa ne har suka tsorata ta fito. Bakinsa ɗauke da addu'a ya sake tunkararta Mommy ta dafa kafaɗarsa ta miƙe tsaye tana layi, da ƙyar ta iya tsayawa a kan ƙafarta ta fara takawa da ƙyar kanta na ci gaba da sara mata. Kabiru na raka ta bakin ƙofa zai juya fir mommy ta ƙi yarda don har sa da ta saka Kabiru ya rakata har ƙofar ɗakin Daddy sannan ya koma ɗakinsa, tana shiga ta zube a bakin ƙofa tana ci gana da karanta duk ayar da ta zo bakinta. A lokacin da ta koma ɗakin tuni Daddy ya yi bacci, da rarrafe ta fara rarrafawa zuwa bakin gadon tana kiran sunansa. Sai dai babban abin da ya sake firgitata yadda ta ji yana sauke wani irin munshari mai ban tsoro, ga ƙwan ɗakin da fara ɗaukewa yana kawowa.


Raihan da abar bauta kusan tare suka koma kogon dutsen ƙungiya kowannensu fuska babu walwala, abar bauta ta dubi Raihan rai a ɓace ta ce: "Mahaifiyarki za ta bamu matsala domin tana da riƙo da addini. Sannan wannan Bafulatanin yana ƙoƙarin wargaza shirinmu tabbas za mu ɗau mummunan mataki a kansa, amma fa duk da haka Mahaifiyarki bata sha ba domin za mu ɓullo mata ta sigar da ba za ta taɓa tsammani ba. A yau saura kwana biyar ta fara al'ada don haka zan yi amfani da wannan lokacin, domin alƙawarinta na yi ga ɗakin arziƙi." Raihan ta jinjina kai cikin girmamawa, abar bauta ta nuna wata ƙaramar ƙorama ta ce,: "Ki ɗebi ruwan wanke zunubi ki yi wanka domin kin karya ƙa'idoji da dokar ƙungiya." Raihan na yin wanka kamar yadda Abar bauta ta umarceta ta fice daga kogon dutsen.

Intisar ce ta ɓullo daga ƙarƙashin ƙasa ta yi gaisuwa ga abar bauta, kusan cikin haɗin baki suka furta, "Huzaifa zai aika da Raihan ƙasar India don bincike na musamman akan Raihan." Abar bauta ta yi murmushin takaici ta ce, "Na san da haka shi ya sa na nemo ki yanzu. Zai kaita India ne wurin Kakansa Jibbul-Ƙasi don ya yi mata bincike a kanta, ya ɗora zarge-zarge akanta ciki kuwa har da ke." Intisar ta jinjina kai sannan ta ce, "Tabbas na san za a yi haka domin na san wanenen Huzaifa da bin didiginsa." Abar bauta ta miƙe tsaye sai da ta yi zagaye wurin sau uku sannan ta ce, "Ba zai yi nasara a kanmu ba, domin za mu mallakawa Raihan duk wani ƙarfin iko, idan a da bata san wacece ita ba ya zama dole mu sanar da ita ta hanyar sakata a ɗakin arziƙi." Hankali a tashe Mugaza ta ɗago tana faɗin, "Kina nufin tun yanzu za ta mallaki shuɗaɗɗan ruhi ba sai nan gaba ba ya Abar bauta." Abar bauta ta ci gaba da tafiya tana jinjina kawunan jikinta ta ce, "Alƙawarin ƙungiya baya tashi, matsawar Huzaifa ya kaita wurin kakansa tabbas sai ya gane shirinmu kuma sai Kakansa ya wargatsa ƙungiyar nan. Idan kuwa muka saka mata shuɗaɗɗan ruhi dole zai zama garkuwa a gare ta, za ta gagari Jabbul-Ƙasi da dukkan wani shirinsa.

WASAN YA FARA ƊAUKAN ZAFI🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ RAIHAN TA KUSA ZAMA SHUGABA LIKAFA TA CI GABA😂😂 MENENE ALAƘAR SHUƊAƊƊAN RUHI DA RAIHAN, SHIN DAMA RAIHAN NA DA WANI A ƘUNGIYAR ASIRI NE DA HAR RUHINSA ZAI MAYE GURBINTA KO YAYA? WACCE ALAƘA CE TSAKANIN SHUƊAƊƊAN RUHI DA KAKAN HUZAIFA JUBBUL-ƘASI? CAKWAKIYAR ƘARA GABA TAKE🥵 MAZA HANZARTA KI BIYA DON JIN YADDA ZA TA KASANCE GARA KI BIYA 300 KI KARANTA AMMA IDAN NA KAMMALASHI SAI KIN SAKA 500 ZA KI SAME SHI🥱🥱🥱 WANNAN SHI NE SHAFIN ƘARSHE WATO SHAFIN ƘAUTA😎 MU JE ZUWA ƳAN GROUP ƊIN *ZAUJATU PAID* A CI GABA DA GASH SUYA SAI RANAR BIKIN NAƊIN 👸🏻 RAIHAN A ƘOGON DUTSEN ƘUNGIYA🤸🏻‍♀️💃🏼

SHARE HILIS🌚
[7/23, 2:48 PM] Ameera Adam🌚: *DUBU JIKAR MAI CARBI*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*


FREE PAGE 1

Babban gida ne mai ɗauke da ɓangare daban-daban har kusan sashen mutum goma sha biyu. A taƙaice za mu iya cewa gidan gandu ne da ya haɗa Kakanni, 'ya'yaye da jikoki. Garin Ɗangwauro yana ɗaya daga cikin ƙanana ƙauyukan da ke cikin ƙwaryar Kano, Allah ya azurta su da noma, kiwo da kasuwansu. Gidan Malam Muhammadu mai dogon Carbi sanannan gida ne a kaf cikin garin Ɗangwauro. Tun daga titi idan ka tambaya za a kai ka har cikin gidan, sakamakon gida ne gidan yawa don wani lokaci mutane na yi masa laƙabi da gidan 'Ya'ya da yawa.

Gidan Mai dogon Carbi cike yake da mutane sakamakom wayar gari da suka yi da rasuwar rashin wannan Dattijo mai yawan shekaru, ba iya gidan ba hatta garin Ɗangwauro ya girgiza da rashin wannan Dattijon mai dogon zamani. Yaya Babba da Inna Furai sune matan wannan Dattijo da ya rasu mutuwar ba ƙarmin taɓa su ta yi ba.

Bisa ga al'adar Malam bahaushe a ranar da aka yi mutuwa mutane sun fi nuna damuwarsu ta hanyar koke-koke, kukan ma yana taƙaita yawancin bayan ankai mammaci. Hakan ce ta faru a gidan Mai dogon carbi domin an fita da gawarsa a yi mata sallah yara da Manya sai kuka suke yi.

A gefe ɗaya Hali dubu na hango rakuɓe sai muzurai take lokaci-lokaci tana share hawaye, sai dai cikin zuciyarta haushin mutanen gidan take ji saboda ta lura babu wanda yake bi ta kanta don ya rarrasheta, duk kuwa da irin gursheƙen kukan da take yi. Kallonsu ta fara yi tana ayyana irin abin da za ta yi domin ta janyo hankulansu kanta. Tun da ai ita gani take kamar ta fi su jin mutuwar koda suna yawan faɗa da Mai dogon carbi amma kafin ya rasu, ai ita ma Kakanta ne.

Sumi sumi sumi ta tashi da yaƙunannan hijabinta ta bi hanyar soron gidan tana waiwaye, sai da ta je soron ƙarshe daga shi sai fita Hali dubu ta ɗora hannuwa biyu akanta ta dawo cikin gidan da gudu tana cewa, "Wayyo Allah! Wayyo ni na shiga uku na lalace." Lokaci ɗaya hankulan mutanen gidan ya dawo kanta, da sauri aka yi carko-carko a kanta masu jero tambaya na yi. Zuciyarta ƙal don ko ba komai ita ma za a rarrasheta kamar yanda aka saka su Yaya Babba ana basu haƙuri. A fakaice take satar kallonsu tana sake sharce hawaye amma ta yi biris babu wanda ta tankawa duk irin tambayoyin da mutane suke yi mata. Baba Munkaila ne ya shigo ya hango cincirindon mutane a tsaitsaye da sauri ya ƙarasa wurin, ganin Hali dubu a zaune ya sa ya ja guntun tsaki sannan ya buga mata tsawa, "Ke lafiya kike yi wa mutane ihu?" Kamar sabuwar Marainiya haka ta ɗago shanyayyin idanuwanta ta kalle shi sai kuma ta waiga ta saci kallon ƙofa ta kuma duƙunƙune kanta cikin alamun tsoro da firgici. Kamar haɗin baki dukansu suka kalli bakin ƙofar suna neman ƙarin bayani, babu abin da ta furta musu sai ma kuka da take yi tana nuna musu ƙofar da ɗan yatsanta. Baba Munkaila tsawa ya sake buga mata ya ce, "Me ye a cen ɗin?" Hali dubu ta kuma kallon ƙofar ta rushe da kuka tana cewa, "Baffa ne!" Cikin haɗin baki duka suka ce, "Baffa kuma? Wane Baffan?"

Bata bi ta kansu ba sai kawai ta baje a wurin ta fara wata irin birgima tana cewa, "Wayyo Baffa ne ya tafi ya barni!" Takaici ne ya rufe Baba Munkaila domin ya san za a rina don ya tabbata ganin Dubulliya tana wannan kukan ba banza ba. Cikin faɗa-faɗa ya fara yi mata magana amma ko gezau ba ta motsa ba. Can gefe ya hango wata igiyar dabbobi ai kuwa bai yi wata-wata ba ya fara tafka mata, tana jin shigar bulala ta tashi ta yi cikin gida ta gudu.

Can ɗakin Yaya Babba ta shiga ta haye ƙarshen gado tana kuka, ga haushin Baba Munkaila ya tsinkata a cikin mutane. Tambayar duniya Yaya Babba ta yi amma Dubuliyya kanzil! Bata ce da ita ba. Sai ma ta yi zamanta a nan domin duk duniya babu abin da tafi tsana kamar taron jama'a a gidansu. Domin ba ƙaramin takura take yi ba, dalilinta na haka kuwa ta yanda za ta ji mutane na bata ji ko kuma ta cika rashin ji kamar ƴar aljanu. Tana daga kwance dabara ta faɗo mata ta yanda za ta kore jama'ar gidan ta ruwan sanyi domin ta san yanda danginsu suke sai a kusa arba'in da mutuwar da sauran baƙi tsiraru. Saboda haka Baffa mai dogon Carbi ya saba musu tun yana raye, idan suka zo taro baya barin ƴan uwansa su koma a kwana kusa. Wannan dabara tata ba ƙaramin daɗinta ta ji ba don har sai da ta murmusa saboda farin ciki. Kamar wacce aka tsirawa allura haka ta zabura da sauri ta fice daga ɗakin Yaya Babba, ita kanta Yaya Babba ba ƙaramin daɗi ta ji ba kasancewar duk duniya babu Jikarta da take so kamar ita sakamakon Marainiya ce gaba da baya.

Dubu tana fita ta yi garau da ita kamar ba ita ta sharɓi kuka ba, nan fa mutane suka fara yi mata tsiya, har da masu cewa dama ita zuma ce sai da wuta. Wasu kuma su ce gara da ya yi mata haka ga shi ta ware ta fara harkokinta. Shiru ta yi babu wacce ta tankawa sai dai duk wacce ta yi magana tana auna maganar tata a mizani domin ta san irin hukuncin da za ta yi mata.

Tun da Magriba ta doso Dubulliya ta fara haɗa kayan aikinta a fakaice cikin hikima da basira, ba tare da wani ya fahimci halin da take ciki ba. Sakamakon babban gida ne kowa da wurin da yake nema ya kwanta saboda ko ina a wadace yake hakan ne ya sa Yaya Babba bata damu ba da Hali dubu ta ce za ta sashen Baba Munkaila ta kwana a cen.

DA DADDARE

Da daddare gidan ya yi tsit ban da kukan tsintsaye da ƙananan dabbobi babu abin da yake tashi, sai munsharin bacci da yake tashi daga ɗakunan daban-daban. Dubuliyya tana daga sashen Baba Rufa'i cikin ɗaya daga cikin ɗakunan

Please Login or Register in order to submit comment