Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

 Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Novels villa
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
07039625239

MAYA’UDARA-Page-1-
to-end
OCTOBER 20, 2016 | RASHIDATKARDAM | 3
COMMENTS
[10:14PM, 9/21/2016] Rash Kardam:
[6/5/6:30pm]
RASH KARDAM
&
SADEEY S ADAM
WITH
BEEBAH LUV
YAUDARA
( Bismillahir Rahmani Rahim)
{Allahumma Salli Ala Muhammadin
Wa Sallim}
Ranshi a bace yake sosai, ya rasa
meke masa dadi,, duniar tayi masa zafi,,
ya ciji lebe, ya ciji yatsa, duk shi kadai,
yayi zagayen a daki ya koma Parlour, sai
gumi ke keto masa duk da sanyin Ac,,
kamar wani zautacce.
Ba kowa bane illa “”AREEF””
Daukan waya yayi ya kirata yafi sau
20 amman bata dauka ba,, wai me yasa
Teemahluff ke mishi haka,, Kodan taga
yana bala’ in sonta ne??
Ya kuma dialing wayar frnd dinsa
farouk,,bugu daya ya dauka, bayan sun
gaisa ne yake ce masa, ya akai ne
abokina ya gidan ya akwai labari ne?
Yayi tsaki tare da cewa whl kasan
matsala ta guda daya ce akan teemah,,
nayi kiranta but she refused to answer
my calls..
Farouk ne ya girgiza kan shi, tare da
tausaya wa aminin nashi, don kuwa
yasan yana cikin matsala,,, baisan me
zaice mishi ba wanda ya wuce ya bashi
hakuri,, tun farkon soyayyar su da
yarinyar shi daman batai masa ba,,
kuma yasha bashi shawara akanta,
amman yaki ji, har fada sunyi akan
teemah.
So daga baya sai ya yanke shawarar
zuba mashi ido akanta, inya kawo masa
kukanta sai dai kawai ya bashi hkr ya
kwantar masa da hankali,, amman yasan
yarinyar kawai cheating take ma
abokinsa, yasan ba son shi take ba, sai
dai yace Allah ya ganar dashi gaskia..
Kamar kullum yanda ya saba bashi
hakuri yau ma hakan ce ta faru, yace ya
sake kiranta may be, bata kusa da phone
din ne,, haba farouk I called her more
than 20 tyms fa..
Bari kawai naje gidan su,, yanzu. Ya
dire wayar yana ajiyewa ya sake kiranta
still no answer,, ya dauki key din motar
sa ya fice daga gidan..
A bangaren Teemah kuwa,, tana
ganin calls din sa taki dauka, don kuwa
yau batai niyar ganin shi ba,, kuma
tasan shi da dan karan naci zai iya ce
mata zai zo..
Mstwww tayi tsaki aikin banza
kawai, sai shegen nacin tsiya.
Hmmm masu karatu last week fah ta
gama tarairayar shi, ta amshe masa yan
kwabban sa, wai za ai bikin kawarta nxt
week,,,
Yanxu haka wani take jira, zai zo yau
kuma shi zata wanka.
Areef bai zame ko ina ba sai kofar
gidan su teemah, nan ma yayi kiran
dunia taki dauka, ya kira wani yaro ya
aike shi cikin gidan, ya kira mashi ita,,
ai kuwa yana zuwa ta balbale shi da
masifa, dallah je kace mishi bana nan na
fita unguwa,, yace toh har kama hanyar
tafia tace zo nan, ya dawo ta kama
kunnen sa kuma sauran in kaje kace
nice nace bana nan,,, whl sai nayi maka
dukan tsiya in muka gamu,, kuma in ya
tafi ka dawo ka gayan,, yace toh daman
yasan hali.
Bayan fitar shi ummanta tace,, anya
teemah baza kima kanki fada ba ko?,,
whl duk ranar da Allah ya tashi kamaki
baza kiji da dadi ba.
Bata ce komai ba tayi wucewar ta
daki, tana kunkuni,, uwar tace hmmm
ayi dai mu gani..
Bayan an gaya masa bata nan,, ya
dauko naira 100 yaba dan Aiken,,
sannan ya zauna cikin motar yayi
tagumi, ya kulla wancan ya kunce
wancan duk shi kadai,, yakai har kusan
10 to 15 mins bai tafi ba,, sai can ya tada
motar shi ya tafi…
Har yanzu bai ji ya tsaneta ba,har
yanzu ji yayi kamar kara rura mashi
wutar son ta ake a cikin zuciyar shi,,
Allah sarki daman ance so hana ganin
laifi..
After tafian shi da 10 minute kuwa
sai ga wanda take jira yazo me suna
Haydar, daman tana ta Allah2 Areef ya
tafin kar su hadu…
Nan aka chanchada kwalliya,, me jan
hankali aka fito ana yatsina ita a lallai
ga me saurayi..
Teemah fara ce doguwa, amman
bata da wani kyau,, tana da dukiyar
fulani daidai gwargwado,, amman kuma
kasan sha6al yake don kuwa sungul ta
tafi,, abinda ya Cece ta farin da take
dashi,, don ko gashi bata dashi, ita dai
wannan farin da iya kwalliya da kwalisa
da kuma shagwa6a da kwarkwasa,, shine
yake jawo mata samarin, har take samun
damar yaudarar su..
Tasan duk wata salon hanya ta
yaudara da iya kwacewa samari abin
hannun su,, don kuwa indai har Allah ya
hada ku, toh ka shiga uku a wurinta sai
tasan duk wata hanya data amshe maka
kudin ka sannan ta rabu dakai….
Toh masu karatu ga dai Haydar nan a
gaban teemah,,, bamu san ta yanda zata
bullo masa ba don shima wankar sa take
son yi…
Ku biyo mu don jin yanda zata
karshe,,, don yanzu aka fara yanzu aka
diga damba a wannan lbrn me suna
YAUDARA don kuwa akwai
gwagwarmaya a cikin sa sai kun jimu…
Daga masu kaunar ku. S B
R
Marubuta Uku
[truncated by WhatsApp]
[10:14PM, 9/21/2016] Rash Kardam:
[7/5/6:47am]
RASH KARDAM
&
SADEEY S ADAM
WITH
BEEBAH LUV
YAUDARA
Pg
Hydar tunda ya hango ta yake
smiling,ita kuwa sai gwargwasa take a
hankali take tafiyar kamar mai tausayin
k’asa haka dai ta k’araso gurinsa cikin
kisisina irin ta mayaudaran Mata.
Jingina tayi da motar sannan tad’an
had’e rai ba tare da ta kalli hydar d’in
ba.
Murmushi yayi sannan ya rage glass d’in
motar ya kuma bud’e Mata “Allah yasa
dai banyi laifi ba”,murmushin makirci
tayi Wanda shikesa samarin nata su
rud’e suna kallon duk duniya ba Wanda
yakai teemaluf iya soyayya da kuma
kyau.
“laifi ai ka gama yinsa my D kasan
awowin da na d’auka ina jiranka kuwa?
amma kak’i xuwa a lokacin da kace
zakazo” tad’an k’ara b’ata rai “ka koma
wajen wacce kake so tunda yanzu ni
baka sona”, a gigice ya kalleta “haba
teemah kinsan kuwa duk duniya ba
wacce nake so kamar ki,wlh bani da
wadda ta fiki,na b’ata lkci ne wajen siyo
Miki kayan da kika buk’ata pardon me
pls ”
“murmushi tayi najin dad’i “dan kasan
baka laifi a guna shiyasa kake min haka
but next tym in ka kuma I wl punish u”,
bazan kuma bama” tayi dariya sannan
ta Shiga cikin motar ta zauna, ya kake
ya mummyna(mamanshi)?”, lafiyanta
k’alau tace a gaida surukarta kuma Yana
son ganinki yaushe zakije mata?” ,
hmmm “zan duba ko da week-end ne Sai
naje kasan yanzu Ina busy ga bikin
bestyna ga kuma skul”, ok Allah kaimu”
“Ameen my D”.
Sunyi hira sosai yasha kisisina da iyayyi
da shagwab’a shi kuma hakan ke
burgesa ga teemah
Ta wankensa sosai d’an kuwa Sai da ya
rubuta mata cheque na 50k sannan ya
mik’o mata Manya manyan leda guda 2
sukayi sallama ta fito daga motar
sannan ta juyo ta kalleshi
“Am vry proud of u my D,Allah barmu
tare har k’arshen rayuwarmu”, “Ameen
teemah” ya amsa a tak’aice.
“to ni zan shiga gida sbda magrib tayi ya
kamata muje muyi sallah ko?” murmushi
kawai yayi baya gajiya dajin zazzak’ar
muryar teemah da kallon kyakkyawar
fuskarta”(hmmm mukuwa SBR cewa
mukai “kallon kitse akewa rogo “)
“My D ya kayi shiru?”, hmmm “nothing”,
hmm badai zaka fad’a ba nizan shiga
gida my regards 2 mumcyna”Tana Gama
fad’a ta shige gida, yad’an jima dan har
Saida yaji an fara Kiran sallah sannan
ya ja motarsa ya tafi cike da kewar
teemahluff d’insa.
********
Misalin k’arfe 02:30am Areef ne keta
juyi kan makeken gadonsa ya rasa me
keyi masa dad’i anya kuwa teemah
unguwa taje? Ya tambayi kansa
To kodai bata da lafiya ne shiyasa tak’i
d’aga wayar kuma basa so su tada mai
hankali suka k’i fad’amai gaskiya da
yaje?, amma yasan teemansa bata tab’a
k’in d’aga wayarsa ba saidai in Bata
gurin ko a silent ta saka wayar kuma
data ga missed call d’insa take kiransa
Gskya ba lafiya ba dole gobe na koma
gidan dan ganin meke faruwa Allah yasa
dai lafiya duk a zuciyarsa yake tunanin
Tashi yayi ya Shiga toilet ya d’auro
Alwallah yayi ta jero nafiloli tare da
yiwa teemansa addu’a,sai da yayi sallar
subhi sannan bacci mai nauyi ya
d’aukeshi.
********** Tun k’arfe 11:00am
teemah tayiwa bestynta waya tace dan
Allah tazo yanzu2 akwai Magana
Futha na break fast taji Kiran bestynta
dan haka ko gamawa batayi ba taje ta
watso ruwa,tayi sauri tad’anyi makeup
taja hijab tace wa mamanta tayi gidansu
teemah yanzu zata dawo
“Karki dad’e Futha saboda d’aura
abincin rana”, “insha Allahu baxan
dad’e ba” ta fad’a tare dayin waje har
tuntub’e take don son zuwa taji gulma
dan kuwa tunda taji teemah tayi Mata
Kiran sassafe tasan da Magana.
Tana Shiga gidan teemah taja Futha d’aki
ta d’ebo ledojin ta juye a
gabanta,atamfofi guda 4 da Swiss lace
guda 3 sai veils da kayan makeup da
kuma turaruka masu sanyin k’amshi
Futha ta saki baki tana kallon kayan cike
da mamaki tace “kina cutar Areef da
yawa teemah ko wlh kiji tsoron Allah
bafa sonshi kike ba amma kike Yi masa
muguwar YAUDARA ina tausayinki
Randa Allah ya tashi kamaki”
Hmmm “ya tashi kama mu dai kema ai
kina YAUDARAr samarin,samarinki
nawa, dariya Futha tayi sannan tace
“dama in kanayin Abu sai kayi tunanin
kowa ma nayi to wlh k’arya kike min
besty Samarina biyu kacal kuma in
kinga sun yimin kyauta su suka Sa kansu
ni bana YAUDARA Kawai dai duk Wanda
Allah ya zab’amin a cikinsu zan aura”
“sai kiyi tayi kuma in fad’a Miki yanxu
duniya ta canza ni samarina basa
k’irguwa uncountable ne wasu ban sansu
ba sai recharge card ake watso
min,Areef kuma tuni na gama yayinsa
na wankesa sosai na yadda shi, yanxu
wani hydar ne on top,in fad’a Miki
bayan kayannan har cheque ya rubuta
min na 50k kuma da sunanki na
wankesa nace bikin bestyna za’ayi,futha
wayake tausayin maza yanxu ca6 wlh
wankar banxaye zanyi
dariya Futha tayi “ba dama teemah
yanxu dai a karb’o kud’in a bani kaso
na tunda da sunana aka wankesa”,
“kinma Isa keda kikace ina YAUDARAr
samari to bazan bada ba” “wlh dole na
fad’a Miki gskya besty ko xaki
mutu,kuma sai kin bani Swiss d’aya da
5k”
Dariya sukayi su duka teemah tace “kin
manta sunana TEEMAHLUFF tun muna
sec skul kuka samin sunan shiyasa LUV
d’in ya bini har girmana dashi na samu
damar wankar samari”
“hakane kam k’awata nima dazan samu
damar wanka da na wanka saboda ba
kyaune dake ba makeup ke taimakonki
ni kuma ga kyau ga makeup but ban iya
YAUDARA ba amma nima zan Maida
sunana FUTHA LURV dan na d’an
wankesu kad’an ba kamar naki ba”.
dariya sukai sosai teemah tace “Ashe
kema kinason wankar samarin dama ce
baki samu ba” futha tayi dariya sosai
sannan tace ” am joking fa wlh ban tab’a
Jin son inyi yaudara ba” teemah tace
“ohh kenan ni mayaudariya ce?”, “oho
Miki” suka sake yin dariya sannan suka
ci gaba da hirarsu.
Urs… S B R
(Triple Writer’s)
[[truncated by WhatsApp]
[10:14PM, 9/21/2016] Rash Kardam:
[8/5/2:19pm]
RASH KARDAM
&
SADEEY S ADAM
WITH
BEEBAH LUV
YAUDARA
Pg 3⃣
Sunyi hira sosai da Futha, can Teemaluff
Tace”ke yar gari, tsaya muga miye a
cikin laidan nan da ya kawo, suka
zazzage kayan ciki, Riga da skirt ne,
masu ‘kyan gaske, sai dogayen riguna,
masu duwatsu, ajiki, sunji ado sosai, sai
wasu takalma da turaruka masu kyan
gaske designers.
Shewa sukayi tare da tafawa Futha
Tace”Teema kinyi wuta fa, Teema ta
rausaya idonta, tare da juyasu, hmm ke
ae bamuyi komai ba. Yanzu nafara
wankan garori. Futha ta kaleta
Tace”Allah yasa ki gane ki dawo hanya.
Dariya sukayi dukansu, sai dab magriba
Futha tayi shirin tafiya, Teema ta d’eba
mata, turare da su powder, da su lip
gloss, masu kyau ta bata. Sai da tayi
make-up kafin ta rako Futha, tafiya
takeyi, kamar bazata taka kasa ba, tana
karairaya, wanda duk d’a namiji in ya
ganta, sai ya kyasa.
Sun fito bakin titi, suna jiran mai Napep
ke nan, wata katuwar jeep ce tazo
wucewa, har ya tafi ya dawo, dai-dai
inda suke ya rage glass d’in motarsa,
yana kalon Teema da ke kwar-kwasa,
tana juyi tamkar sarauniyar kyau. Cikin
sanyin murya Yace”Hajiya ya kk? Ina
zuwa haka?.
Sai da ta rausaya ido ta jujjuya jiki, ta
bud’e baki, ta fara magana cikin salon
YAUDARA da kisisina irin na wayyayun
mata, kawar da fiskanta gefe tayi, kafin
Tace”k’awata ce mai tafiyar, shikam
baki yasake yana kalonta, don ta
matukar tafiya da tunaninsa. “Ok! To
kefa? Sai da ta d’anyi fari da ido, Tace”
tazo gaidani ne, na mata rakiya.
Futha da ke gefe, saki baki tana kalon
ikon Allah. Teema lokaci d’aya, ta sauya
salo, kamar ita bace suka fito tare ba, a
zuciyarta, Tace”eh! Tabbas Teema ta
‘kware taci sunanta Teema lurv.
Mai mota ya kali Teema Yace” Hajiya
zan iya samun phone number ki? Sai da
ta fari da ido, cikin da barata boye
babban wayarta, ta ciro ‘karaman ta
mika masa, yana karba ya juya wayar a
hannunsa,Yace” kina babban Yarinsa
kamar ki ace wannan
ne wayarki?. Wani murmushin
YAUDARA Tace”ya zanyi wayar tawa
kenan, tana kwarkwasa.
Kansa ya gir-giza, Yace” dole na san
abinyi, kamarki ace kina rike wannan
wayar, ba girmaki bane. Murmushi ta
masa, Tace” Ranka shidad’e ayi haka?.
Murmushi ya mayar mata, “karki damu
ae kinfi haka a gurina. Futha da ta tsaya
tana kalo, Yace” ko zan sauke k’awar
taki a gida, “ok! ba matsala da ka
kyauta. Da ‘kyar Futha ta, tashiga
motarsa ya kaita gida.
Wa she gari da yamma, “Khalid ne ya
wayar Teema, ya sanar mata yana zuwa,
yau da daddare. Cike da murna da
rawan kai, ta shirya, cikin kayan da
Haiydar ya kawo mata, riga da wando
tayi kyau sosai, tayi zaman jiran
zuwansa.
Sai da karfe ta’kwas da rabi ya iso k’ofar
gidandu Teema cikin motarsa mai glass
baki. Wayarta ya kira ya saida mata,
yana ‘kofar gida, Tace” gani fitowa My
Sweet Heart.
Sai da ta ‘kara yin ‘kwaliya kafin ta fito,
cikin yanga da kwar-kwasa, Khalid tun
daga nesa, ya zuba ma ‘kirjinta ido,
wanda suke tsatsaye kamar biro,
fiskanta nan ya sha make-up. Har ta
k’araso gurin bai san ta iso ba, sai da ta
zo dai-dai fiskansa, ta hura masa iska,
wani sassayan ajiyar zuciya ya saki, tare
da bud’e mata ‘kofar motar ta shiga ya
zagaya shima ya shiga.
Zama yayi, ya k’ura mata ido, tare da
sunkuyo da fuskan sa dab nata, yayi
‘kasa da murya Yace”Beb kinyi kyau
sosai, har kinfi kulum. Rausayar da da
ido tayi Tace”nagode amma kafi ni kyau.
Haccinta ya lakace, Beb baki da dama
fa.murmushi tayi mai k’ayatarwa.
Hannuta ya kalla, ya sha lale, Yace”
Teema inga hannu ki?, ‘boye hannu tayi,
ni bazaka gani ba. Haka kika ce ko? Ni
kuma yau sai na gani. Ta
‘boye hannu tayi, yayi ya gani ya kasa,
ya kaleta Yace”dole na miki hukunci
tunda kika hanani gani, kafin tace
komai, sai ji tayi ya gantsara mata cizon
wasa a kunneta.
‘Kara tayi irin na shagwab’a, ta
murgud’a masa baki, lah! lah!, lalle yau
kin tsokanoni, sai nayi maganin bakin,
da kike murgud’awan, kama hab’arta
yayi, yasoma shan janbakin, har sai da
ya shanye duka, ya riko hannunta, mai
da numfashi suka rinka yi, hirarsu da
Khalid yawanci shafe-shafe ne saida
suka gaji dan kansu, yari ko hannuta
don ya mata rakiya.
Wayar ta ne tasoma k’ara, sunan Areef
ta gani, sai da ta faki, idon Khalid taga
baya kalonta, da sauri tasaka wayar a
silent, don yanzu Areef baya gabanta, ta
gama da shi.
Duk ta shagwab’e masa a jikinsa, sai
shafa ta yakeyi, yana zuwa kan k’irjinta
ya kira sunanta a hankali, Teema!, ta
amsa a kasalance, Yace”ina son nan gun,
k’irjita a shafa, yana birgeni sosai.
murmushi tayi Tace” Allah ko? Ya
gyad’a mata kai alamar eh!.(Yan matan
Zamani, mafi yawanci yanzu irin
soyayyan da kukeyi kenan, na tab’e
tab’e, kusani namiji yana gama latsaki,
daga lokacin darajanki, ya ragu a gunsa.
Ina mai shawartan ku, da ku kiyaye,
guys abunda suke so kenan, ba soyayyan
gaskiya, suke maki ba).
Urs…
S B R.
(Triple Writer’s).
[[truncated by WhatsApp]

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Novels villa
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
07039625239


[10:14PM, 9/21/2016] Rash Kardam:
[16/5/8:30pm.]
BEEBAH LUV
&
RASH KARDAM
WITH
SADEEY S ADAM
MA’ YAUDARAH
06~10
Note: Pls fans, sakamakon jin da
mukai anyi novel me suna YAUDARAH,
shi yasa muka chanxa ma namu suna ya
koma MAYAUDARAH,. Tnx
Sun isa babu dadewa, don daukan
Futha, su tafi batai tunanin wani ne zai
kai su ba, tayi tunanin a keke napep
zasu tafi, daman bata shiga ba a kofa ta
tsaya tayi mata waya, futha tayi ma
ummanta waya sallama, tace sai sun
dawo Allah ya kiyaye hanya, su gaishe
da Amaryar tace toh.
Bayan ta futa ne ta gansu a cikin
mota, ta shiga da sallamar ta, ta gaisar
dashi daga nan bata sake cewa komai ba,
sai dai in teemah tayi mata magana
takan bata amsa a takaice, don Futha
akwai kamun kai.
Bayan sun isa shima da zata futa
tace mashi sai anjima, kai wannan
kawar taki akwai ta da girman kai, sai
wani shan kanshi take,, ayya whl baka
fahimceta bane haka take bata fiya
magana ba,,, ok sai yaushe zanzo daukar
ki, tace zadai muyi waya ok sai ltr din
kenan, ok bye.
Hmmmm kedai teemah bazaki
taba jin magana ba, kullum cikin kula
samari kike, wannan kuma daga ina
kika kwaso shi,, daga ganinshi ba
mutumin kirki bane,, don Allah teemah
ki ringa tunani whl wannan rayuwar ba
mai bullewa bace, ki nitsu kiyiwa kanki
fada pls kinji kawata, ta kama hannunta,
toh naji matar liman zanyi, ni muje
dallah.
Matar soja kam ba karamin dadi taji
ba,, tayi masu tarba me kyau,, sunci sun
sha, sunyi hani’an.
Nan kuma aka dosa hirar school,
after nan kuma aka fara ta samari,
kowacce na bada nata lbrn, da irin
yaudarar da take ma samari,, hmm nan
fah teemah aka soma fede biri harda
wutsiyar sa, ai duk naku wasa in gaya
muku, nifa yanzu indai zan fita unguwa
to alkawari ne sai nayi saurayi, kuma
daman in naga kalar ka batai mun ba ko
sauraranka bazan yiba, don kunsan ni
sai mai kudi,, gwara wanda zan wanke
shi, ba wanda zaizo yana mun karyar
baya dashi ba.
Heeeeh whl kuwa yar uwa kinmin
daidai, don kuwa yanzu sai da hakan
inji Sumayya Gireii, don kunsan suma fa
mazan yanzu dan karan yaudara ce
dasu, yo kun manta ni da Ahmad ya
yaudaran yazo ya kawo kudin aurena,
ashe ba iyayen shine na kwarai ba, na
karya ne tsabar yaudara ce irin ta
maza,, ai shiyasa yanzu na Daura
damarar yaudarar maza son raina, don
nama daina tunanin aure yanzu, sai na
gama cin dunia ta da tsinke tukunna.
Futha ce da ummilele suka gyara
zama, hmm yanzu kukam kuna ganin
hakan yafi maku ko? Whl kuyi ma kanku
fada yaudara babu kyau, gwara ku
tsaida guda daya nagari, yanzu dunia ta
lalace, wasu samarin fa ba sonku suke
tsakani da Allah ba, sai dai su zo su
kashe muku kudi, in sun samu abinda
suke so a gurin ku su gudu su barku, ai
kuwa sun cuci rayuwar ku.. Whl kuwa
fada musu ummi don kullum sai na
gayawa teemah ta daina amman gani
take burgewa ne, whl ba abin burgewa
bane kuna cutan kanmu ne…
Can kuma rash ta amshe chab wai
wa’azi zukuyi mana?? Ai gwara ma ku
daina, don yanzu kam bazai shige mu
ba, yanda ake yaudarar mu, muma sai
mun dana, donni inda aure kazo mun
ma tuni nike korar ka don ban shirya
ba, sai na tatsi na tatsa son raina, in
baka red card,, dakyau kawata ban mu
kashe,,, inji sadeey, ai sai da hakan, don
ni yanzu akwai me sanya mun credit,
akwai me siyan kayan make up,, akwai
me sai mun anko, akwai kuma driver na
wanda duk inda zanje shi yake kaini,,
kuma duk yanda nace ana yi mun, koya
kika ce kawas,, kwarai kuwa,,
Matar soja tace ayi dai a hankali
don kuwa a wannan zamanin ba kasa
fai samari ke bama yan mata kudi haka
kawai ba, sai kema in kina bada
gudummuwa,,
To ai ba wani abu bane baya wuce
shan minti, kawai meye a ciki don an
dan sha minti ai ba wani abu bane inji
teemah duk teemah tafi zaqalqalewa a
cikin su don kuwa idon ta ya bude sosai
sai dai gyaran Allah kawai…
Ai kuwa whl wani abu ne babba ma
kuwa don kuwa kunsan babu kyau Allah
ya haramta hakan,, kuma sai sun gama
shafe ku sannan su arce su barku anan,
su kara wuta, wani ma daman da matar
shi, wani kuwa da wadda aka sa musu
rana, tunda yaga kin sakar mashi sai
yazo yayi abinda zai yi ya gudu, Allah
dai ya kara shirya mana zuri’ a amin..
Ohoo sudai ina ai wanda yayi nisa
yayi nisa, sai dai gyaran Allah kawai
Allah ya gyara amin.
Sai dab da maghrib suka tafi ansha
hirarraki kala kala..
Wacece Teemah
Teemahluff diya ce ga Alh Rislan da
Haj Raudha, Alh rislan haifaffan garin
kano ne a wata unguwa da ake kira
Hotoro Dan Marke,,, malamin makaranta
ne govt, sec, school dake hotoro, ya dade
yana teaching, har ya samu mukamin
principal a makarantar.
Alh rislan mutum ne me kirki da
kawai ci, da rikon a mana, da sanin ya
kamata,, baya karbar cin hanci, yana da
bala in kirki da rikon addini..
Matar shi daya, raudha me bala’in
hakuri da addini, yayan su uku Fauzan,
shine babba sai Teemah itane ta biyu,
sai kuma mukhtar shine autan su.
Sun taso cikin gata da tarbiyya, don
kuwa Alh rislan yana kokari Sosai wurin
basu tarbiyya da ilimi, both side,
islamiyya da boko, yana son yaga sunyi
karatu me taho, farko sun fara govt
school daga baya ya cire su ya saka su a
private school tun suna primary 4 suke
Private school har secondary school.
Yana bala’in kokari duk abinda ya
samo akan iyalin shi suke tafia, ba wani
me kudi bane rufin asiri ne kawai da
zuciyar nema.
Akwai wani makwocinsa Alh Faisal
yana da kudi sosai,, kuma suna shiri da
Alh rislan don kuwa shike bashi
shawara, ya zama kamar dan uwan sa,,
yakan taimaka mashi sosai bawai don ya
gaza bane a ah yana dai taimakon shine
tunda ya fishi kudi nesa ba kusa ba.
Akwai wata shekara ya hada da nashi
iyalin da Alh rislan da raudha ya kai su
aikin hajji,, shi yasa ake kiransu Alh
rislan da haj raudha..
Alhamdulillah komai yana tafia
daidai a rayuwar gidan Alh rislan, su
teemah da Fauzan har sun sauke Qur’an
don ba wani tazara ke tsakanin su ba,
shekara daya ne tsakanin su.don haka
komai tare suke yi, hatta a school ma aji
daya ya bata, kuma shi baya da jikin
girma, ita kuwa tana da tsaho ana
yawan cewa ita ce babba akan shi..
Teemah ta tashi cikin tarbiyya da
nitsuwa tun tana Karama amman tana
shiga SS1 a school ta zama fitinanniya
kamar ba ita ba,
Don kuwa yan mazan ajin su da yan
matan ma yawancin su duk kangararru
ne yayan masu kudi, shi yasa fitinar tayi
yawa, su suka bata tarbiyya teemah,, tun
tana kin biye musu har dai ta fara shiga
layi.
A lokacin bata wani kware ba,
kuma bata kula samari don bata fara
zuwa zance ba, babanta yace karatu
zatai har sai ta fara higher institution
sannan zai aurar da ita don yana son
yaga sunyi karatu, tunda sun sauke na
muhammadiyya, kuma yasan yarsa tana
da tarbiyya zata rike mutuncinta a duk
inda take.
Ayyah baba rislan kayi kuskure don
kuwa,, abokai da kawaye sun lalata
maka tarbiyyar da ka dade kana yi tun
fil’azal, teemah kam ta fara nisa yanzu
sai dai gyaran Allah.
A kwana a tashi ba wuya wurin
Allah su teemah har an gama secondary
school, kuma Alhamdulillah tayi passing
exams din ta gaba daya, a waec neck ne
tayi losing subject biyu. Tana da kokari
sosai da maida hankali sai dai kawai
rashin jin da ta zunduma kanta yanzu a
ciki,,.
Bai wani bata Lokaci ba ya samar
mata admission a Bayero university,
kuma ta samu a fannin sociology, yayi
mata fada sosai akan ta maida hankali
akan abinda ya kaita baya son kula
yayan banza, tayi abinda ya kaita tace
to kamar da gaske..
Shi kuwa fauzaan yana ABU ZARIA
can ya sami admission shi kuma
mukhtar Auta yana JS one don akwai
tazara tsakanin shi da
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment