Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE



You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[8/4, 19:30] +234 913 133 0334: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺
*KYAUTAR ALLAH*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺🌺


Alhamdulillahi am back


SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏽 (Marubuciyar boyeyyen al'amari)

Dedicated to hauwa'u mmn little saudiya and mom amatullahi.

Inama kowa barkada sallah.💃🏽


Page 1

A garin katsina safana lacal government, a wani dan madaidaicin kauye, me dauke da gidaje ginin kasa. Sede wani gini dankarere, wanda ya amsa sunansa gini bulo na gugar bulo, a gaskia ginin ya tsaru, kai inkaga ginin ka rantse da Allah a birni yake, duk garin babu gini dayakaishi kyau, da tsaruwa, domin kuwa kofar gidan dankareren getne me mugun kyau, yayinda a saman get din gidan aka rubuta *SAFANA HOUSE* da Ruwan gold Kai tsaye na dannakai cikin gidan, ma aikatane taf a bakin get din gidan masu sanye da kakin sojoji.

Ginine hawa biyu sama da kasa, a farfajiyar gidan akwai motoci biyar na alfarma, DUK CIKI BABU MOTAR MILIYON, sede zillions.

A falon kasa naga wata tsohuwa zaune a kan lallausar kujera, hutu da kwanciyr hnkli ya rasata.Farace Sol tsohuwar kai daganinta kasan bafullatanace dukda ta tsufa tukuf amma hkn be hana kyawunta ya boyuba, hajiya Annah kenan ikon allah. Benu, baki tsufa sede ki sake sabon gashi. Shine kirarin da Jikanta *muhammadu raslan* yakeyi mata.
Daga gefen Annah wata kyakyawar yarinya na hango kwance a kn cinyarta, idanuwanta a rufe, yyinda tunanin abbahnta fall ranta, dukda kuwa jiya ya tafi amma sam se takejin kmr tayi shekara bata ganshiba. yatsu ne ke bakinta tana tsotso, hutu ya ratsa yarinyar dagani. Sanye take da riga da wando kalar peach irin na yan hutunnan, luf kyn suka kwanta a kn kalar fatar yarinyar, wato ita kalar chocolate ce irin me shining dinnan.a kallah yarinyar batafi 12yrs ba.


A gaskia kujerun falon sun tsaru, sunyi kyau ainun tsayawa fadar kyaun falon is a west of time fans. Amma komi yaji. Hotunane manne a duk inda na wurga idona a falon hoton wani saurayi da wannan yarinyar dana gani a kwance, saurayin dasuke hoton matashine fari sol dashi, kmr ka taba jini ya fito. Saurayin nada cikar kamala da zati da haiba. ita kuma yarinyar kalar chocolate ce irin kalarnan me mugun sheki, yayinda duk suna dariya a hoton, hannunshi cikin nata, tanada wushirya sama da kasa, yayin kyaunta ya gigita lissafina, tuni tunanina ya dauke na wasu yan dakiku. Shikam matashin dimples garesa gefe da gefe, a gaskia ya hadu, kmr balarabe.

A wasu hotunan kuma tana karama, wani kuma tana jaririya wani kuma tanada girmanta amma da yatsa a bakinta tana tsotso, se abin ya daureminkai, wai yar 12yrs ce ke tsotson yatsu biyu, ammafa se naga tsotson yatsar ya kara mata kyau ainun. Wani hotone yafi daukar hankalina wanda take kwance a kn kirjinsa, da yatsa a bakinta, a jikin hoton an rubuta *KYAUTAR ALLAH* da mnyan harufa kalar gold, sanye take da riga da skeet na lace a hoton.

Zaune suke sanyin ac na ratsasu. dayake akwai wuta a kauyen dalilin hajiya aisha har yan kauyen suka samu wuta, domin kuwa Yayanta duk sunada budi, musamman ma Alhaji umar safana.

A duniya yara hudu Allah ya mallakawa aisha da jibril sudin haifaffun garin katsinane (Katsina ta dikko dakin kara) cikakkum fulanine na ainihi, auren zumunci aka yima jibril da shatu. Jibril a jeji suke a wancan lokacin, kowade yasan sana'arh fulani kiwon shanu domin shanaye sune dukiyar fulani.

Da mahaifin jibril da mahaifiyar shatu yanwa da yan kani suke, a haka akayi musu aure, jibril nada 15yrs shatu nada 7yrs, tinde ba asan inda rayuwa takeba' ba amasan meye aurenba har Allah yasa akazo aka fahimci meke tafiya a duniyar. Allah ya azurta jibril da shatu da yara hudu, uku maza se autarce mace, wadda seda suka cire rai da haihuwa,se kuma allah ya basu ita. Domin kuwa har shatu ta cire ran samun diya mace , don ada anama tunanin haihuwar tata ta tsayane. Se gashi allah yayi ikonsa.

aikou nan ta dauki son duniya ta dora mata, haka shima jibril a bangaren kakanninsuma sunfison auta rukayyah wadda taci sunan mahaifiyar jibril ake kiranta da *KYAUTAR ALLAH*.

Dukda a kauye suke hakan be hana jibril tsayawa yaransa mazaba sukayi karatuba sosai, domin kuwa a cikin gari suke fita karatunsu, su mazan kenan. Na farkon sunansa harun se na biyun musa sena ukun umar. Yaran sun tashi da hazaka kan kace kwabo Allah yasa musu hannu, yayinda umar ke karantar harkar kasuwanci, shi kuma harun acouting ya karanta shikam musa, harkar siyasa ya karanta.

Auta rukayyah wato *KYAUTAR ALLAH* itama daidai gwargwado tayi iya nata karatun.wato Allah yasa mata wani irin kyaune na mamaki, itadin yar madaidaiciyace, tin tana 7yrs maza ke kawo hari amma ina ainan shatu ta tsaya tsayin daka kan ba wanda ya isa yayima yarso dinta abinda akayi mata wato auren wuri.

Yayinda dukkanin mazan kowa ya kama ma tsaya Allah ya daukakasu fiyeda tunanin me karatu, amma Allah yafi daukaka alhaji umar wato na ukun. Allah ya azirtasa da dukiya taban mamaki, dominshi dan kasuwane, ya shahara kwarai da aniya, duk fadin nigeria da niger da ghana babu wanda besan da *Alhaji umar jibril safana* ba.

Alhaji harun yayi aure ya aura fulani, ta haifa da daya namiji wanda yaci sunan jibril. Wato mahaifin harun.

Musa kam tini ya samu mukamin govenor a garin kaduna a ynzu hk. Yanada mata biyu dayace ta haihu yara uku duka maza amma dayar sam bata haihuba.

Toufa Annah shatu da anyi haihuwa taji ance namiji, se murna ta koma ciki. itakam Allah yasa mata son mace, gashima yarannata basuda yawan haihuwa abunna damunta, Annah macece me fada fada ga surukanta musammanma in bata sonka toufa ka bani, jika kuwa sam bayashan ruwa a gabanta, Dan ita tafison danta bawai jikaba.

Nanfa ta matsawa umar kan dole shima yayi aure kou Allah zesa shidin ta hanyarsa tasamu jika mace. Ai data tasa sa agaba dole tasa ya aura wata shuwa'arab dasuka hadu a garin barno yaje business dinsa. Mace me natsuwa ya aura me suna zainab, zainab tanada kyau domin kuwa duk a cikin matan babu macen data kaita kyau da haduwa, farace soll. Amma kuma se akayi rashin sa'arh sam Annah bata kaunarta. Hakan yasamu nasabane da yadda, zainab ta iya rike mijinta, kunsande yadda matan shuwa suke da iya rike miji ladabi da biyayyah etc.

Duk wannan labarin danake muku ita KYAUTAR ALLAH batafi 15yrsba a lokacin domin kuwa tsakaninta da wanda takebi shekara Goma sha biyarne ne.

Ana haka, zainab tasamu ciki. Ainan Annah ta fara sonta da tattalinta a tunaninta, kou mace zata haifa. Amma kashe ranar haihuwa ta santalo santalelen danta namiji me kyau. wanda yaci sunan mahaifin Annah wato, Muhammad ake kiransa da *Raslan* tou yaronde yaci darajar dande kawai yanada sunan mahaifintane yasa Annah ke daga masa kafa. Amma kullum adduarh Annah daya Allah yasa tasamu jika mace.

Ana haka dukkaninsu kowa ya koma inda yake aiki dazama harun ya koma garin kano, yayinda musa ke garin kaduna, shikam goga alhaji umar da matarsa zainab suna garin abuja.

Annah da alhaji jibril sun more yaya, domin duk shekara se sunje hajji da umra, a kallah bazasu iya kirga adadin, sau nawa sukaje, dakin allah ba.


Ana hk Allah yayima, mahaifinsu alhaji jibril rasuwa bayan yayi doguwar jinya, a china. na ciwon sugar, tou a nan se muce Allah ya jikansa mukuma Allah yasa mucika dakyau da imani. Annah tayi kuka ta gaji *KYAUTAR ALLAH* kan seda ta kwanta asibiti domin har lokacin batayi aureba, dan Annah tace sam aure ba ynzuba ita indama son samuntane kada KYAUTAR ALLAH ta matsa daga inda take, bakaramin so Annah keyi mataba, haka suma yayyun nata ji suke kmr zasu lasheta, yar gatace gaba da baya.

Daman alhaji jibril ke takawa Annah burki tou ynzu babu shi dan haka duk yadda ta tsara hakanne ke faruwa a family din, dukda basa kusa amma Annah tasa musu ido a hkma dan KYAUTAR ALLAH na taka mata burki shiyasa abubuwan ke sauki. Daman tin kafin mutuwar malam jibril yarannasa sukayi sukayi su dawo birni amma Annah tayi fir tace aah dayake jibril mutumne me hkri dan hk duk abinda Annah tace kouda yakeda rai sede yabita da tom. Dole sede Suka siya gabaki daya anguwar suka graya musu, sukayi musu ginin zamani me hawa biyu nanma Annah nata fada wai almubazzarancine, tin kafin mutuwar jibril akayi hkn, a ynzu hk kullum cikin gyaran gidan suke.

Autan family's din shine *MOHAMMED RASLAN* seda yakai shekara sha biyar , duk jikokinma sun tasa yayinda babban jikanma keda matarsa nanma Annah tasa ido taga tattaba kunne mace, amma ina se maza biyu itama ta haifa. Jikokinma sun samu ilmi sosai. Yayinda *RASLAN* ya tashi da kwanya taban mamaki, shima burinshi ya gaji mahaifinsa wato fannin kasuwanci. Nan da nan arziki ya habbaka a family din jikokima arziki,tom daman ai cikin arzikin suka taso.

Ana hk KYAUTAR ALLAH tasamu miji dan niger buzune, alhaji Abdallah yanada rufin asiri, yana kasuwancinsa, da kyar Annah ta bari akayi auren a lokacin KYAUTAR ALLAH nada 25yrs, a garin katsina nan KYAUTAR ALLAH take zaune daman nan kasuwancin mijinnata yake. Nanfa hajiya aishatu wato Annah ta zuba ido tana jiran ganin cikin diyar tata kullum cikin adduarh take Allah yasa KYAUTAR ALLAH ta haifa mata diya mace. A hakade aka kwashe shekaru uku KYAUTAR ALLAH kou bari bata tabayiba,

Duk a family din jinin KYAUTAR ALLAH yafi haduwa da Dan yayanta RASLAN domin RASLAN yana respecting dinta, ta dauki son duniya ta dora masa tin yna qarami harya girma,shima ya dora mataso fiyema da iyayensa hk yakesonta dukda tayi aure kullum yna hnyar zuwa katsina duk weekend a gidan KYAUTAR ALLAH yakeyinsa. A haka yazo yabar kasar zuwa ingland Dan Karo karatu a fannin kasuwanci, a lokacin ynada 20yrs.

Bayan tafiyar *RASLAN* da shekaru biyar Allah ya bawa KYAUTAR ALLAH ciki, aikou zokaga murna gun Annah rnr ai batayi bacciba kwana tayi tna ibada tana godewa ubangiji da fatan Allah yasa a haifa mata mace me albarka wadda zatayi alfahari da ita dama duniya gabaki daya. Washe gari kuwa ta fara shela ga iyalan nata babu wanda bata gaya mawaba hatta Raslan da baya kasar seda ta kirasa ta gaya masa, shima yayi murna sosai, harda azumi yayi na godiyar ubangiji shima adduarh dayace Allah yasa macece me albarka kuma Allah yasa tayi kma da KYAUTAR ALLAH.

Annah tasa anyi sadaka da dukiya ta fitar hankali duk dan saboda samun cikin KYAUTAR ALLAH ji takeyi kmr rnr ne zata fara samun jika.

Family kam wasu na murna wasu na bakin ciki wasukam adduarh sukeyi Allah yasa a haifa namiji suga ta tsiyar Annah, kou ince suga iyakarta.

A bangaren KYAUTAR ALLAH Kam tinda tasamu cikinnan shikenan tayi bye bye da lafia, kou ruwa tasha seya dawo duniya babuci babusha wani irin laulayine Allah ya jarabceta dashi me mugun azaba, ji takeyi kmr ta cireshi ta huta, bata kara tabbatr dacewar uwa mace nada darajaba seda tasamu wannan cikin, kullum cikin kuka take, ganin hkn yasa Annah taje da knta ta daukota ta dawo da ita gidanta, toufa nanmadin kullum suna hnyar zuwa asibiti kullum hannun KYAUTAR ALLAH na daure da drib domin shine abincinta shine abinshanta don bataci batasha. A haka cikin yakai wata biyar ana tsammanin chanji amma ina kullum se cigabama whlar keyi Annah dukta sare dabadan tasarai da cikinnanba data haqura a zubar kawai domin autar ta KYAUTAR ALLAH ta huta, ji takeyi daman ana amsa ta amsar mata ta huta, domin wata rana ita da knta Annah tasa KYAUTAR ALLAH takeyi a gaba tayita kuka, gabaki daya rayuwarsu tass takoma a asibiti, KYAUTAR ALLAH dukta lalace ta kode ta canza kamanni setayi wani irin fari, kuma ita ba fara bace chocolate colour ce,irin kalarnan me shekin tsiya baka ganin komi a jikinta se karan hanci da dara daran idanuwanta, dukta koma kashi.

A haka wata rna Raslan yazo hutu yaje ya ganta, yna ganinta ya fasheda kuka, dukse yaji murnarsa ta koma ciki, yazo ya rungumeta yna kuka Annah Kam ta zabga uban tagumi.

KYAUTAR ALLAH tayi murmurshi ta shafa kan Mohammed Raslan din cikin sanyin muryarta tace, "My son...kaga yadda kanwarka ke wahalar dani kou..."

Wani irin hawaye me zafi yashiga bin kuncin Raslan ya shafa cikinta daya dan tasa, se kuma yaji sanyi a rnsa, yace" am sowie sweet mother a gaskia kanwarnan tawa bata kyautaminba...kiyi hkri pls mother zaki samu sauki very soon..."

Smiling kawai KYAUTAR ALLAH tayi ta zubawa Raslan ido tana masa wani irin kallo, shima dago kai yayi yna kallonta.

Rnr daze koma ingland haka ya dawo asibitin domin yayi mata sallamah domin yna tunanin inya tafi baze dawoba har zuwa lokacin dazata haihu. Kwance yasameta,tna sanye da riga doguwa maroon domin daman duk a kala tafison maroon kowa yasani a family,. Lokacin Annah na toilet tana wanka.

Ido KYAUTAR ALLAH ta zuba masa, kna tasakar masa murmurshi naso da kaunah, matsowa yayi yaja kujera ya zauna daf da gadonta, ya dora hannu a cikinta, haka kawai yakejin wani irin matsifaffen so da kaunarh yna ratsa bargon jikinsa da jijiyoyinsa yayinda zuciyarsa ke amsar sakon kaunar cikin dake jikinnata, ji yakeyi duk duniya be tabason wani halittaba kmr yadda yakeson cikin dake jikinnata. "Allah yasa ki sauka lafia mother in dawo in ga kanwata..." Ya krshe mgnr da murmurshi.

Itama murmurshi tyi ta damke hannunsa cikinnata, tace "Hmmm son inajin wani abu a game da rayuwata..."

Dam yaji gabanshi ya fadi, yynda jikinsa yayi sanyi, yace "kmrya mother.." Ya fara a firgice.

Murmurshi tasakar masa na kwantrda hnkli tace. "Dan Allah zan baka amana zaka amsa..."

Cikin hanzari yace "ki bani amana kota menene wallahi nayi alqawarin zan riqe miki kouda hkn ze zama silar rayuwatane..."

"Na baka amanar abinda zan haifa walau mace kou namiji..."

Be dauki komi a rnsaba yy murmurshi yace"na dauka..."

Dam ta kara rike hannunta cikin nasa, ta maimaita masa amanar har sau uku yace ya amsa, kna sukayi sallamah ya tafi yna waiwayenta,hk kawai yakejin jijiyoyinsa duksun sage.

Cikin *KYAUTAR ALLAH* yacika watannin haihuwarsa Seda tajera sati biyu tana labour se haihuwa tazo gadan gadan se kuma tayi shiru dif, hankalin iyalan safana dukya tashi. Ana shirin shiga dakin tiyata da ita allah yasa ta sauka ta sambalo diyarta katuwa wadda taci ta koshi bul bul da ita kamarta sak kmr uwarta harma tafi uwar tata kyau, dukkanin jikinta gashine, gashi dukya baibaye fuskarta yayindaya kwanta luf a fatar jikin jaririyar tinda nake ban taba ganin jaririya me gashiba kamar yarinyar domin tsaf za a iya kitsa sumar dake kanta, ga kyau, ga farin jini dashiga zuciya.

Toufa ga murna ga bakin ciki. Yayinda iyalan safana suka samu labarin haihuwar diya macen murna fal cikinsu annah kam baki har kunne, hatta raslan da bayanan ana haihuwar aka sanar dashi lokacin yna masallaci yanata ibada a kan nakudar da aka sanar dashi KYAUTAR ALLAH tanayi. A lokaci daya yaji labarin haihuwar da rasuwar KYAUTAR ALLAH bayan haihuwar kou second daya bata karaba tace ga garinku nan. Hmmm jimami da bakin ciki baya misaltuwa, Annah kam har suma tayi dakyar aka samu kanta, raslan da bayananma seda yayi qaramin hauka. Aka yima KYAUTAR ALLAH wanka aka kaita gidanta na gaskia. Yayinda akabar zuciyoyi da kewarta da kaunarta mijintama mutuwar ta tabashi amma haquri yazama dole, tsakanin mamaci dame rai adduarh ce babbar soyayya se muce allah yajikan rai mukuma allah yasa mucika da imani.

Allah sarki, duk wanda yaji mutuwar seya tausayawa jaririyar.

Washe gari raslan ya iso nigeria a hargitse kai tsaye ya nufo gidan Annah nan ake zaman makoki yayinda annah ke rungume da Jaririya ta hana kowa ganinta ballan tanama a dauketa, babban danta wato harun na gefenta yna bata baki yana mata natsiha,amma ina hawaye be dena zuba daga idanuwantaba, wai a hkma dan tna ganin jaririyarne har takejin sanyi ga rayuwarta, yayin data dauki son KYAUTAR ALLAH ta dorashi cas a kan jaririyar da tini tayi mata lakabi da *KYAUTAR ALLAH* itama.

Bayan anyi arba'in uban yarinya yaso amsar diyarsa yakaiwa kanwarsa tacigaba da shayar da ita, amma ina beda dmr magana dole ya haqura, ya barma Annah KYAUTAR ALLAH wadda taci sunan Rukayya wato sunan mahaifiyarta, dukda ana jimamin mutuwa amma byn arba'in da kwana hudu Annah tasa aka kawo kosassun marikan shanaye har guda hudu aka yanka a cewarta na sunan KYAUTAR ALLAH ne, a halin yanzu babu wadda Annah keso fadin duniyarnan kmr jaririyarnan *KYAUTAR ALLAH* wai ance abun cikin kwai yafi kwan dadih.

Jaririyar nada hakuri, madara ake bata, yayinda tinda tadiro duniya daman tana tsotson hannu, annah tayi tayi ta rabata da tsotson hannun amma ina da an cire seta fasa ihu, inkouda hannun a bakinta kou kuka batayi, yunwama bataji, sannan sam batada rigima.

Raslan kam ai nan ya tattaro ya dawo gidan Annah, da kyar yasamu annah ta fara bashi KYAUTAR ALLAH, domin annah bata yarda da kowaba a kn kyauta allah.a hnkli, ragamar rainon KYAUTAR ALLAH ya dawo hannun raslan, shike ciyarda ita ya shayar da ita yaci kashinta yasha fitsarinta, shike mata komi, har goyata yakeyi yayita jijjigarta, in KYAUTAR ALLAH batayi bacciba, tou shima raslan rnr baze rintsaba. A lokaci kankani wani irin so da kauna yashiga tsakanin raslan da jaririya KYAUTAR ALLAH, yayin dashi ke kiranta da Jaririyar, itama yarinyar tini ta ganeshi.

Saboda Kyautar allah raslan ya haqura daci gaba da karatunsa a Ingland saboda bayason nesa da ita daidai da bacci bayayi se in kyautar allah tayi bacci, shima a kn cikinsa take bacci, wani abunma sede annah tazuba musu ido, domin kou ita bata tunanin son datakewa kyautar allah yakai rabin wanda raslan keyi mata, kwata kwata baya bari masu aiki su tabata har nanny aka daukar mata amma ya sallameta.

Wata rana Cikin dare KYAUTAR ALLAH ta rinka kuka, raslan yayi rarrashin amma takiyin shiru Annah ma tayi rarrashin amma takiyin shiru, Raslan ya rasa ina zesa rayuwarsa kukan yarinyar na taba masa zuciya ji yakeyi kmr zuciyarsa zata tarwatse, shima kawai seya fasheda kuka me tsanani Annah ta zuba musu ido tana kallon ikon allah a nan ta kara tabbatr dacewar Raslan nason KYAUTAR ALLAH fiyeda tunaninta. Tin daga rnr inde knaso kaga hawayen raslan tou KYAUTAR ALLAH na kuka nanne shima zakaga nasa kukan.

KYAUTAR ALLAH ta taso batasan kowaba se Raslan, da bakinta ya fara budewa da sunansa ya bude yayin datake kiransa da Abbah. Hartakai shekara daya batabar tsotson hannuba, amma ita nata tsotson hannun kyau yake kara mata ainun. Yayin da tana girma tana kara kyau kamanninta da mahaifiyarta nata kara bayyana a tare da ita.

Hajiya Rukayyat amaryar alhaji musa wadda bata haihuwa, allah ya dora mata son KYAUTAR ALLAH,don hk duk inda taga kyale kyale seta siya, ta kaima KYAUTAR ALLAH ji takeyi, daman Annah ta bata KYAUTAR ALLAH, Amma so ba samu bane, sede da soyayyar kyautar allah a zuciyarta. Hknne yasa suke shiri ita da raslan. KYAUTAR ALLAH ma tana kaunar takwarar tata.

Wannan tarewar da raslan yayi a gidan Annah abin naciwa Hajiya zainab tuwo a kwarya,
musammanma data lura da jarabar son dayakewa KYAUTAR ALLAH, ita bawai tana bakin ciki bane, amma jikinta na bata wani abu i mean something bad. Duba da yadda Annah ta tsaneta, aikou ba dadinta bane ita kuma jininta yaje ya manne da jinin wadda ta tsaneta, dukdade bata da yadda zatayi ta raba hanta da jini.

Kwanci tashi ba wuya, game rai da lafia. Yayinda kyautar allah takai shekara biyqr, ga kyau gata bulbul da ita sam maraici be tabataba, ragamar rayuwarta na hannun raslan, hatta kitso shi yakeyi mata, a knta ya koyi kitso, dayakema ita kyautar allah akwai gashi domin kuwa sumarta har baya, jefi jefi yake mata kitso, wata rana yakaita, gun saloon. Komi da komi shi yakeyi mata hatta pant shi yake siya mata, kuma sam batasa kayan nigeria sede na Dubai.

Shaguwa daso da kaunar raslan dashi KYAUTAR ALLAH ke girma batasan komiba se raslan ita duk a tunaninta da yadda ta daukeshi shine mahaifinta.

Duk bayan kwana biyu se safana family's na nesa dana kusa sunzo ganin KYAUTAR ALLAH, allah yasa sonta a zuciyoyin duk wani dan safana family.

Haka mahaifintama duk byn kwana daya yna hnyar zirya domin ya dobu diyar tasa har zuwa lokacin, ya gazayin aure don gani yakeyi baze taba samun kmr marigayiyyar matarsaba.

KYAUTAR ALLAH nada 7yrs mahaifiyar raslan ta matsa dole ya dawo gida ya kama tasa sana"arh dukda lokacinmashi yna business dinsa don be yadda ya zauna se an basaba. Tinda hajiya zainab ta matsa dole raslan ya koma abuja yacigaba da kasuwancinsa yayin dayakeda hannun jari a kasace daban da ban a hnklifa ya zamana duk safana family babu me arzikinsa, alhmdllh arziki kullum kara habbaka yakeyi. Dukda raslan ya koma garin abuja amma duk byn kwana biyu yna hnyar zirya zuwa katsina don duba farin cikin rayuwarsa KYAUTAR ALLAH. Inkou byanan kullum suna manne a waya, ta video call, raslan ne yase mata iphone 12.

KYAUTAR ALLAH tnada miskilanci donse ta wuni batayi mgnaba, daga uhm se okay se tom, don ita Akwai miskilanci fiyeda tunanin me karatu, da ita da raslan bnsan wanda yafi wani miskilanciba.

Dukkanin companonin Raslan sunan KYAUTAR ALLAH ne, itace kan gaba a komi nasa, hajiya zainab wani lokaci sede ta zubawa sarautar allah ido, don lamarin na nemar fin karfin tunaninta.

Hajiya zainab tnada kawa daya tilo hajiya hadiza, hajiya hadiza shu'umar macece, domin kalarta kalan yan bariki, itacema ta zuga zainab kan

2 Comments On KYAUTAR ALLAH
avatar
maryam-8-8-3

10 months ago

Reply

Aslm

avatar
taskar

10 months ago

Reply

Replying to maryam-8-8-3

Wslm

Please Login or Register in order to submit comment