Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yai wanka sai yaji an kiran sallar magrib, dan haka sai kawai yashiga toilet yadauro alwala yafito yadauki farar jallabiyya yasaka ba tare da yasa hulaba saidai kawai yadauki tasbi yafita zuwa masallacin da sauri domin ko kad'an bayaso yarasa jam'i.


*TASLEEM* kuwa da bataga *TAUFIQ* ba sai kawai ta zauna gefen gado tana turo baki tareda yin surutai tana kalle-kall can dai da tagaji da zaman saikawai ta kwanta inda barci yadauketa.


********
                                    "Abangaran *TAUFIQ* kuwa dama a'ka'idarsa idan yaje sallar magrib baya fitowa daga masallacin sai yayi sallar isha'i sannan, dan haka ko a wannan lokacin saida yai isha'in sannan yafito daga masallacin kai tsaye part dinsa yanufa domin yai wanka, yana shiga sai kawai yaga *TASLEEM* kwance akan bed dinsa tana barcinta hankali kwance.


Cike da bacin rai yafurta kai! wannan yarinya akwai mayyar yanzu saboda Allah, har nan tabiyo kenan yarinyar nan bazata barni nahutaba ko?..., tsaki yaja mtsww! tareda bud'e d'an karamin firizan dayake nan cikin bedroom din, yadauko goron ruwa Mr.V me sanyi sosai, yanufi gurinta yana murmushi mugunta sannan yabud'e goran tareda d'aga bakin goron sama yazuba mata ruwan afuska har zuwa kirjinta, aikam tafarka igigice tamike zumbur cike da mugun firgici da tsoro tako kwakumesa da dukkan karbin ta rungume, domin kuwa jin saukar ruwan tayi bazato ba tsammani. cikin firgici take fadin wayyo sanyi! yayana sanyi!! tana fadin tana sake cukuikuyasa cike da tsakanin tsoro.

Yayinda *TAUFIQ* kam tuni yai suman tsaye sakamakon jin taushin dukiyar fulanin *TASLEEM* din akan faffad'an kirjinshi, tuni yasaki goron inda ruwan yake gangarawa takasan tafin kafarta ihun fadin yayana kafata shima sanyi!!! yanazuba aciki, shine yadawo dashi daga suman wucin gadin dayai, da sauri yatureta daga jikinsa tafadi kasa kallonta yai kirjinsa yana wani irin bugawa, cikin fada yace ke! dalla gafara can meye haka zaki wani ma'kaleni kamar kaska eye?....


cikin turo baki tace yayana naji sanyi ne akafata da nan tafadi tareda nuna kirjinta da yajike sharkaf daruwan da yazuba mata.


Kallon kirjin yai sai kuma yai sauri yadauke kai tareda banka mata harara, still zuciyarsa tana cigaba da halbawa yace ba sanyi ba sanyo kinji ko?..wai matsaya uban me ki kazoyi part dina kika shigo mun har cikin bedroom dina saboda bakida kunya har da kwanciya akan bed din ko?...


Halan anfada maki cewa nidi tsaranki ne dazakiyi mun kwance akan bed ko?...

cikin turo baki tace to a ah! sorry ido yarintse tareda shafa lallausan gashin kansa cike da takaici yadaka mata tsawa dacewa soro mata, nace uban me yakawoki part dina eye?..cike da tsoronsa murya na rawa tace to! to!! ai chocolates da sweets dina za kabani, cike da matsifa yace kai! wannan akwai mayya idan ba nabata wayan nan tarkace zakin ba bazata barni nahuta ba.


Da sauri yabud'e dirowar jikin bed dinsa yadebo chocolates da sweets yawatsa mata, tareda cewa gashi nan mayya kwashi! kwashi!! kifitar mun d'akina ko yanzu nakarya ki kinji ko?...


yakarasa fadi da tsawa aikam cikin rawar jiki takwashe da sauri tamike tanufi hanyar fita tana waigensa hartana buga uban tuntu'be.


Tana fita yaja uban tsaki mtsww! kokarin takawa yake sai yakasa sakamakon jida yai kafafunsa suna neman kayar dashi kasa, hakan ne yasashi fadawa kan bed din da sauri yana me sauke numfashin tamkar wanda yai tsere,


yayinda hajiyarsa tayi wani uban tsalle ta halbi iska, ido yazaro tareda kai hannu yadafeta dakarfi cike da mamaki yace kut! ke! dalla gafara meye haka?...


No! ba dai daga kin d'anji taushin wayan can kananan abin shine zaki wani halban iska ba?....humm! aiko dai kinada aiki domin nikam banji komai ba dan haka bai kata kema kiji wani abuba, so kitsu aha!,


yadauki tsawon yan minutes akwance sannan yatashi yanufi toilet dan yin wanka saidai kuma zuciyarsa cike da mamakin halbawan da hajiyan satayi
tareda tambayar kanshi meye hakan yake nufi?...


To *TAUFIQ* nima dai ban saniba🤷🏻‍♀️


Muje dai zuwa


Assalamu'alaikum masoyana BARKAMU da wannan lokacin dafatan kuna lafiya, dan Allah ina me baku haka hukuri dajina shuru dakukai wlh har nayi nisa ada typing sai nabari, sakamakon "kanina da aka kawo daga sokoto bayada lafiya seriously, sannan diyar "yayata tarasu pls kusakasu acikin  addu'ar ku nagode.

          ~Note~

Kardai kumanta *KYANDIR ME HASKEN BANZA book 2* nakudine akan farashi me sauki wato 300, duk me bukata zaya iya turawa ta wannan acc no 0047769671 Amina Abdullahi gt bank saika turo shaidar biyanka ta hanyar yin screen shot sai katuro ma wannan lambar 08161850024 sai najiku nagode.



_Ya Allah kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_
[11/09, 10:54 pm] Amina Umar Faruq Writer: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
     🕯️🌹🕯️🌹
        🕯️🌹🕯️
              🕯️
  
  🕯️ *KYANDIR*🕯️
      ( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_

(It's all about hatred so much Love and so much caring)

*Book 2* Pay

Free Page 7️⃣8️⃣9️⃣

WRITTEN BY

🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
     _Kwantagora_

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR*
( _Mai Hasken banza_)

*GODIYA*
Ta tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.

    *_TSOKACI_*
     Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.

*_GARGAD'I_*
   Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.
 

✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_

""""""""Fuska cike da mamaki *Mamma* take kallon jikin *TASLEEM* dayake jikeda ruwa, yayinda ita kam sai washe baki take tana dariya tareda kokarin bude chocolate, zama tayi kusada kafar *Mamma* tareda kallonta tace *Mammana* yayana yabani chocolates da sweets, dayawa kingani?...


"Cike da takaici tace "eh fa gashi nan nagani saidai nace Allah yawadaran rashin zuciya, saboda Allah idan ba rashin zuciya ba, ya za'ai yanzu nanfa "mutumin nan yagama koranki amma saboda rashin zuciya irin taki daga idar da sallah ko addu'ar danace kiringa tsayawa kinayima kanki Allah yabaki lafiya tunaninki yadawo baki tsaya kinyin ba, kawai kika tashi somai-somai kika bishi saboda wannan tarkacen zakin adole ke ga shazumame bizaki  ko?....


tace eh *Mamma* kali yabani, cikin fad'a tace eh aina gani nasanma saida yajikaki sannan yabaki ko?... tunda ga gaban rigarki nan jiki sharkaf da ruwa.


fuska takwa'be tareda turo baki tana nuna gaban rigarta tace *Mamma* ruwa ne adakin yayana, cike da takaicinta tace "eh ko kogiba ni dalla rufe mun baki da kayan haushi kona mangareki awurin nan kinji ko?....


"Hakan yasa *TASLEEM* din tayi sauri yinshuru tana sake turo bakin...sosai *Mamma* take fad'a har tana cewa nidai ina roko Allah yasa dakike cikin hayyacinki bahaka kike da rashin zuciya ba, da sauri tace ameen ba tareda ta fahimci inda zancan *Mamman* yadosaba.


"Yayinda *Mamma* take kallonta tareda girgiza kai! sai kuma taji tausayin *TASLEEM* din yasake nikuwa mata acikin rai fiye da kullum, cikin sanyi jiki tace Allah yasawake yakuma baki lafiya tasake cewa ameen tana murmushi nan nata me kara mata kyau.


Sai kuma shuru yaratsa falon can sai *Mamma* tace taso zonan kizauna kusada ni kinji yarinyar kirki, hakan yasa *TASLEEM* tashi tanufeta fuskarta dauke da murmushi tace gani *Mammana* inda *Mamman* tajata jikinta tarungume ta yayinda ita kuma tayi lafe kamar jaririya, dama gata da san jiki kamar mage. Sannan cikin magana me kaman rad'a *Mamman* tace kinajina ko?..kai! ta gyad'a mata sannan tacigaba da fadin abinda nakeso dake shine, kiringa share wancan "yayan naki bakigani sai yayita maki fad'a ni haushi fad'an dayake maki nakeji, dan haka ki rigayin zuciya kinji *TASLEEMATA*.


kai ta gyad'a mata alamar to tace yauwa yar albarka, yanzu tashi muje muci abinci idan muka gama sai nakira aunty su Hussy mu gaisa kinji?....kasan cewa duk sunsan komai game da'ita kuma tuni sun saba awaya musamman Hussy, duk da bata ganta ba tana sonta sosai. dan haka cike da murna tace to tareda mikewa itama *Mamman* tamike suka shiga ciki.


*******
*TAUFQ* kam akasale yake wanka yayinda tsikar jikinsa take tashi aduk lokacin da yatuna rungumar da *TASLEEM* tayi masa, wanda ko kad'an bayyi tsammani hakan ba domin kuwa inda yasan haka zata kasance da bai zuba mata ruwan ba.


tsaki yaja mtsww! tareda furta wai meye haka ne?...sai faman tambayar kanshi yake amma yarasa bakanshi amsa, ahaka dai har yagama wankan sabulu sai kuma naga yayi wankan tsarki nikam nace tofa badai yar rungumar da *TASLEEM* tayi mashi baye yasashi yin wankan tsarki hhhh.


Bayan yafito daga toilet wani lotion me kamshi yasafa ajikisa bayan yagama shafa lotion din, sai yashafa man gashin nidai inata kallonsa sai faman kakale kamar mace sannan yayi kum din lallausan gashin kashi bayan yagama sai yafeshe jikinsa da body sprim me matukar kamshin gaske.


Sannan yabud'e wadrof yadauko boxes sannan yadauko wata rigar  barci me igiyoyi yasaka tareda kama igiyoyin yadaure,sannan yasake fesa turaruka masu asalin kamshin bayan yagama sannan yasaka silifas yafito, ahankali yake tafiya kamar mara lakka inda kai tsaye yanufi teburin cin abinci sai babu komai akan teburin din hakan yasa yanufi part din *Mamma*.


********
*Mamma* da *TASLEEM* kuwa
kai tsaye teburin cin abinci suka nufa, inda suka iske inna talatuwa sabuwar me aikin da *Mamma* tasa akasamo mata saboda ta ringayin akin gida ita kuma tayata kulada *TASLEEM*, Inna talatuwa takasance mutumiyar kirki sosai duk dacewa tagirmi *Mamma* amma hakan take makukar girmama *Mamman*, amatsayinta nawacce take karkashinta yayinda itama *Mamma* take matukar girmama inna talatuwa gashi tayi matukar iya girki kala-kala kamar *Mamma* dagana hausa har na larabawa, ga d'an karan tsafta wanda hakan bakaramin burger *Mamma* yayi ba dan haka nema tasakar mata ragamar girkin har dana *TAUFIQ*, sai kawa tanayi tana dubata.


"Dan haka komai yake tafiya dai-dai kamar yanzu duk tagama jera masu abinci cikin girmamawa tagaida *Mamma*, ta amsa tanayima inna talatuwan sannu da aiki bayan sun zauna saita zuzzuba masu abincin har sun faraci kenan sai *TASLEEM* tayi saurin ajiye spoon din hannunta, takalli inna talatuwan tace Inna talatuwa shima "yayana kizuba mashi abincin yanakai mashi, yayinda *Mamma* ta harareta tareda cewa dayake "kece kika saba kai mashi ko?...

Oh!..ni *Saudatu* d'iyar mutum biyu jikar mutum hudu, wai yarinya anarabata da kiwon kyalla tana fadin ai tunkiya tahaihu, ke! mutumin nan sai yakiceki yake amma sai sake likimasa" kike saboda Allah fa inna talatuwa ana haka?...


cikin dariya tace hajiya anayi mana, tace "eh agurin marasa zuciya irinta" ba cikin turo baki *TASLEEM* tace *Mamma* "yayana yafa jiya yasiyo mun kaya dayawa kuma yanzu yabani sweets har da chocolates, kai! *Mamma* ta girgiza tareda cewa kai! Allah dai wadara naka yalalace kinji inda yake samunta yana garawa, inna talatuwan dariya tayi tareda cewa Allah sarki *TASLEEM* yar gidan "yayanta kinadai yin Yayan nan naki" sosai, *Mamma* tace gashi shikuma yayan bayayinta ba.


"Cikin dariya Inna talatuwa tasake cewa ai in sha Allahu "shima watarana zayayita ne har sai anyi mamaki", tace humm! Allah yasa inna talatuwa ankaima shi nasa abincin kuwa?..tace a ah! bankai ba, tukun na dama natsaya ne idan nagama zuba maku, sai nadauka nakai "mashi tace to! akai masa" yanan part dinsa yadawo tun d'azu, cikin  girmamawa fuska d'auke da fara'a tace "eh ai naji diramansu" da mutuwar tasa.


*Mamma* tace humm! ai diraman nasu bata karewa kullum cikin yinta suke kala-kala, "ke dai je ki kawai kikai mashi abincin, tace to hajiya tareda nufar kichin su kuma suka cigaba da cin abinkinsu yayinda *Mamma* ke cigaba dayima *TASLEEM* mitan fadan tadaina likema ,*TAUFIQ*.


*******

Sunyi nisa acin abincin sai sukaji sallamar *TAUFIQ* wanda shine yasa dukkansu d'ago dakai, *Mamma* ta amsa dai-dai lokacin da inna talatuwa tafito daga kichin hannunta dauke da wasu manyan kyawawan kulolin, adai-dai lokacin ne kuma *TASLEEM* fuska cike da fara'a tace yayana Oyoyo sannu, yayinda shikuma yabanka mata harara.


Kujeran kusada *Mamma* yaja yazauna yana kallonta itama shitake Kallon me cike da tambaya?... fuska cike da shagwa'ba yace *Mamma* banga abinci na akan dinning table ba, kuwa inaji yinwa sosai yana fadine tareda kokarin daukar filat hadeda spoon, tace uhum! to acici gashinan inna talatuwa zata kai maku, dai-dai lokacin da inna talatuwan takaraso gurinsu fuska dauke da murmushi tace afuwan maigidana gashi nan dama zankai maka yanzun nan, yau nad'anso nataushe hannu ne gurin aikin abinci. 


"Fuska sake yace babu damu inna talatuwa yau da gobe ne, tace gaskiya ne to ga abinci yace a ah! kikai ki ajiye securitys zasuci ni zanci anan gurin *Mamma* tace to shikenan tareda fita tanufi part dinsa, yayinda shikuma yabude babban kula yazuba farar shinkafa sannan yarufe, yabud'e wani farin robo me marfi wanda salar ne da kabej da kwa yaji bama shanana shima yadiba yazuba sannan yarufe, yasake bude wani, kulan inda miyar kazane aciki wanda zallar nama ne bakashi nan ma yadiba yazuba yarufe sannan yai bismillahi! yafara ci duk suna kallonsa.


*TASLEEM* kam ganin yanda yashake filat da uban abinci yasata zaro ido cike da tsoron, tace wayyo yayana idan yau kacinye wannan food din duka cikinka zaya fashe ne, batareda yakalletaba yace cikin kine dai zaya fashe banawa ba, *Mamma* kam kai! ta girgiza tareda cewa kayya yarna yadai kamata ki koyi yanda ake zuciya, cikin murmushi yace ai dazata iya datuni takoya to bazata iyaba.


*Mamma* tace to Allah yakiyaye yace nagaba yana me maida hankalinsa gurin cin abinci, *TASLEEM* sai tafaman yimasa surutu take, yayinda*Mamma* sai hararanta take wanda batama san tanayi ba.


Shikam *TAUFIQ* gaba daya surutun nata yadameshi, wanda inda yasan haka ne da bai zauna gurinsu" cikin abinci ba domin idan yana cin abinci ko kad'an bayasan magana, dan haka yaketa faman sauri yagama yatashi saboda har wani yam-yam yakejin kansa nayi, tsabar surutunta.


******
*T J Turaki* ne tsaye ababban falon *TAUFQ* sai safa da marwa yake hannunsa rikeda waya, ga dukkan alamu lambar *TAUFIQ* din yake nema sai ga d'aya daga cikin security yashigo, idansa akan dinning table da alama yazo dubawa ne yagani ko ankawo abinci aiko yahango, murmushi yayi sai kuma yaga *T J Turaki* tsaye cikin girnamawa yace ranka yadad'e yallaban baya ciki ne?...


yace "eh naduba shi ciki har toilet ban ganshiba, nakuma kira wayarsa tana ringing but bai dauka ba yace sir kila yana ciki bari naduba maka "shi yace yes I tink so bari nashiga dakai na, ok sir sai kafito yace ok tareda nufar hanyan part din *Mamma*.


******
Saida *TAUFIQ* yakoshi sai addu'ar kammala cin abincin sannan yamike tareda d'aukar tissue yana goge baki, sai kuma yalumshe ido can yabud'e yazuba su akan *Mamma* cike da kasala yace *Mamma* inajin barci zanje nakwanta, tace to Allah yatashe mu lafiya yace ameen tareda bita kusada *TASLEEM* zaya wuce.


"Aiko da sauri tamike tareda cewa yayana zanje, da sauri yatsaya yatalli 'keyarta tareda cewa aiharma kinje me kafar yawo dalla koma zauna kona karya maki kashin baya, da sauri tazauna tana turo baki yayinda yakama kunnanta yace idan har nasake jin zanfita kika sake cewa wani yayana zanje, sai nakarya maki kafar nan me shegen san sawo kinji ko?...kai! tagyad'a da sauri sai da yamurd'a kunnan cike da mugunta sannan yasaki yana dariyar mugunta.


Aiko tasaki kukan shagwa'ba tareda Kallon *Mamma* wacce duk tana kallonsu hakan yasata cika 'bam da takaici *TASLEEM* din.


Sai kuma tace *Mamma* kinga yayana zaya cire mun kunne nako, cikin jin haushinta tace eh Allah yakara aigarama yacire kunnan tunda bayaji maganar da duk nake fada mashi, sannan tamaida kallonta kan *TAUFIQ* wanda yake dariya tareda kokarin wucewa, fuska had'e tace kai! kuma zonan tanuna gabanta cike da shagwa'ba yace eyya *Mamma* sorry nadaina, cikin fad'a tace soro banaaan kadaina kazo nan nace ko?...kai! ya gyad'a tareda matsawa kusada ita yaduka cike da ladabi yace *Mamma* gani kunnansa takama tamurd'a cike da shagwa'ba yace auchhhhh! *Mamma* akai zafi fa, tace Oho! ashe badad'i to "itama haka taji zafin daka murd'a mata kunne, kuma idan kasake murd'e mata kunne kamar haka sai nakarya maka kashin baya takarasa fadi da d'oma mashi dundu abaya.


********
Aiko me *TASLEEM* zatayi ba dariya ba tana fadin yehhhh! *Mamma na* tarama mun, shikam gantsarewa yai tareda mikewa da sauri yana fadin haba *Mamma* irin wannan dundu aisai bayana yakarye, tace "eh gara yakarye kafin ka karya mun na yarinyata yayinda *TASLEEM* sai dariyar jin dad'in take anrama mata, wanda har saida *Mamma* tayi murmushi domin sosai taji dadin gani farin cikin akan fuskar *TASLEEM* din, wacce kuma ta tsagaita dayin dariyar ganin yahade fuska yana hararanta cikin turo baki tace sorry yayana, kanta yasake dungurewa yace soro *Mamma* gud night kai! ta girgiza cikin murmushi tace Oh! ni *Saudatu* Allah dai yashirya munka d'anlele, to Allah yatashi mu lafiya, shima cikin murmushi yace ameen my first love tareda wucewa.


********
Dai-dai lokacin da *T J Turaki* yashgo aiko sukai kare, da sauri *TAUFIQ* yakomo baya yana cewa auchhhhh! tareda dafa goshinsa cikin fada yace d'an iska kafara makanta ne?...cikin dariya *T J Turakin* yace sorry my man is just accident ne fa haba wani irin fara makanta kuma ana zaune 'kalau eye?...



tsaki *TAUFIQ* yaja tareda cewa nasani ko kafara, yace no my man makanta babu dadi so Allah yarabamu da'ita yace gaskiya ne ameen.


To ya akai?...lafiya lau badai har kayi shirin barci ba?...yace gashi nan kagani, ahab dai sai kace wani mace na shiga part dinka har cikin toilet, da sauri yace saboda kana d'an iska har toilet dina kashiga nemana to idan tsirara nakefa?...cikin dariya yace eh to meye naduba bakanan shine nace bari nashigo nan tunda nakira wayarka baka d'aga ba, yace ina nan wlh ya akai ne?...



Ok! bari nagaida *Mamma* nazo akwai magana yace ok dai-dai lokacin da *Mamma* tace muryar wanakeji kamar na *Ahamad tijjani*, cikin dariya yace *Mamma* nine gani nan karasowa salamu'alaikum!, wa'alaikassalam!,


*Ahamad tijjani* idonka kenan?...cikin dariya yaduka cike da girnamawa yace "eh *Mamma* nine ina yini yakwana biyu, tace hum! lafiya lau anya *Ahamad tijjani* kanada kirkikuwa?...yaushe rabon dakazo mugaisa eye?...cikin dariya yace andad'e *Mamma* kiyi hakuri wlh bana zamane shiyasa.


kwanakima *TAFIDA* yace mun kina kwanace da marar lafiya asibiti naso naje gaidake to sai kuma muka tafi Germany da Dad, yakarasa fadi gaba daya attention dinsa yana kan *TASLEEM*, wacce batama san Allah yai ruwan tsiyarsa agurinba sha'anin gabanta kawai take, *Mamma* tace Allah sarki to ya "hajiyarka dashi Dad naka" duk suna lafiya dai ko?...eh *Mamma* lafiya lau suke, tace masha'allah!, yace to *Mamma* yame jikin dafatan taji sauki?...tace hum! me jiki kam taji sauki gatanan saidai har yanzu tunaninta bai dawoba.


Mikewa yai ba tareda yaji karshe maganar da *Mamman* tayiba ya karasa gurin *TASLEEM* yana kallonta wacce gaba d'aya yarikice daganin kyanta, dan haka cikin firgici da rawar baki w...o...w...*Ma..m..ma* wannan sarauniyar kyawun duniyar ce marar lafiyan taki?....


cikin murmushi tace kai! *Ahamad tijjani* duniya gaba d'aya?...cikin tsabar rud'ewa dayai da kyanta yace "eh aina fadi hakan kawai amma ita din tafi hakan, tafi kama da hurul'aini wato matan aljana dariya *Mamma* tayi tareda fadin kai! *Ahamad tijjani* kanada abin dariya,


*TASLEEM* dintawace take kama da hurul'aini?....yace "eh dan Allah *Mamma* kibani auran kyakkawar nan kinji?..
tace Allah sarkin ai anyi mata miji, cikin bugawar zuciya wanda *TAUFIQ* baisan dalilinsa najin haka ba saidai kawai yatsinci kansa da cewa miji fa kikace *Mamma*?...
yayinda shikuma *T J Turaki* da sauri yace.....



Ahaaaaaa


Mudai je zuwa



_ Assalamu'alaikum_
*Dan Allah ina bukatar addu'ar ku wallahi kanina bayada lafiya seriously kusaka shi cikin addu'o'i ku*


~NOTE~

Kardai amanta KYADIR ME HASKEN BANZA book 2 na kudi ne akan farashi me sauki 300 kacal, idan free pages yakare wanda yake bukata zaya iya turo kudinsa ta wannan acc no 0047769671 Amina Abdullahi gt bank ne sai katuro shaidar biyanka ta hanyar yin screen shot sai katurama wannan no 08161850024.




_Yah Allah kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu mu_
[11/09, 10:54 pm] Amina Umar Faruq Writer: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
     🕯️🌹🕯️🌹
        🕯️🌹🕯️
              🕯️
  
  🕯️ *KYANDIR*🕯️
      ( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_

( It's all about hatred so much Love and so much caring)

*BOOK 2*

PAY ne 300 naira idan kana bukata katura kudin ta wannan 0047769671 Amina Abdullahi gt bank ne, sai katura shaidar biyan ta hanyar yin screen shot sai katurama wannan no 08161850024.


Page 1️⃣0️⃣-1️⃣1️⃣-1️⃣2️⃣

WRITTEN BY

🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
     _Kwantagora_

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR 1- 2*
( _Mai Hasken banza_)

*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.

    *_TSOKACI_*
     Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.

*_GARGAD'I_*
   Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.
 

✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_


"""""""" *Mamma* anyi mata miji fa kikace?...tace "eh kaidai ayi mata miji, wayyo *Mamma* amma dai wasa kikeyi ko?..fuska had'e tace a ah! *Ahamad tijjani* ina wasa dakai ne?...


da sauri yace a ah! *Mamma*, cike da tashin hankali yai zaman yan bori dabas akasa cikin firgici yace yah salam kai! amma ko wanene "mijin nan yazo duniya da matukar sa'a, tace aiko dai shidin me" sa'ane nakwarai arayuwa sai kumayi sa'ar mata domin *TASLEEM* yarinyar kirkice gata da natsuwa da ladabi da biyayya, yanzu ana jiran ne taji sauki sai ayi bukin nasu.


                 "Cike da tashin hankali yasake cewa wayyo *Mamma* dan Allah ki taimaka amayar da auran kaina wallahi sonta yakamani sosai, tace haba *Ahamad tijjani* aiba ahaka da sauri yace afara haka akaina dan Allah *Mamma* kinji?...cikin murmushi tace a ah! baza'ai hakaba kadaiyi hakuri zanyi maka addu'a Allah yabaka wacce tafita.


Cikin firgici yace a ah! wallahi *Mamma* bazan taba samun wacce tafi wannan kyakkawar ba, tace a ah! kasan gaibi ne?...yace a ah ban sani ba tace to zaka samu idan Allah ya yarda, har zayasake magana tace ya isa hakan *Ahamad tijjani* nace maka zaka samu dan haka tashi katafi.


Hakan yasa yai shuru batare da yasake cewa komai ba sannan be tashin ba kamar yanda *Mamman* ta umarce shi, saidai yaima *TASLEEM* zuru da ido yanaji aransa tamkar yadauketa yagudu domin gaba daya ta tafida imaninsa.


*TAUFIQ* kam yana can tsaye rungume da hannu tunda yai maganar nan, wacce yake tunanin subul da bakane be sake cewa komai ba saidai zuciyarsa datake aikin bugawa, yayinda yacika 'bam da haushi *T J Turaki* nayanda duk  yarikice daga ganin *TASLEEM* din.


                "Wacce duk da bata cikin hayyacinta kallo daya zakai mata kafahimci cewa *T J Turaki* beyi mata ba kwata-kwata domin kuwa sai hararansa" take tareda turo baki.


**********
Jama'a mutumin T J Turaki* fa yana nan zaune bayada niyyan tashi, cike da mamakinsa *Mamma* tace a ah! *Ahamad tijjani* tashi mana kutafi ga d'an uwanka can yana jiranka.


cikin sanyi murya yace to *Mamma* tareda kokarin mikewa jiki bakwari still idon shi yana kan *TASLEEM*, sai kuma yakoma yazauna yana me cigaba da kallon *TASLEEM* din tamkar tsohon maye har wani lasan le'be

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment