Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanina da bayada lafiya, karku gaji dani har yanzu ina sake baran addu'o'in ku agareshi nagode Allah yabar zumunci ameen.



*ALLAH kasa mucika da imani Ameen ya hayyu ya kayyuu*
[11/09, 10:54 pm] Amina Umar Faruq Writer: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
     🕯️🌹🕯️🌹
        🕯️🌹🕯️
              🕯️
  
  🕯️ *KYANDIR*🕯️
      ( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_

( It's all about hatred so much Love and so much caring)

        *BOOK 2* 

PAY ne 300 naira idan kana bukata katura kudin ta wannan 0047769671 Amina Abdullahi gt bank ne, sai katura shaidar biyan ta hanyar yin screen shot sai katurama wannan no 08161850024.

Page 1️⃣6️⃣-1️⃣7️⃣-1️⃣8️⃣

WRITTEN BY

🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
     _Kwantagora_

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR 1- 2*
( _Mai Hasken banza_)

*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.

    *_TSOKACI_*
     Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.

*_GARGAD'I_*
   Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.
 

✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_

""""""""Innalillahi'wa'inna'ilaihirraju'un!hasbiyallahu wani'imal'wakil!la'ilaha'illa'antasubahanaka innikuntu'minazzalumin!, saida yamaimata haka har sau uku sannan yad'anji nitsuwa tazo mashi amma har alokacin kirjinsa be daina bugawa ba, haka dai yaja kafafunsa da babu kwari atare dasu yafara tafiya ahankali yanufi part din.


              "Aban garan *TASLEEM*
lokacin da tabar part din *Mamma* tanufi part din *TAUFIQ* tun daga babban falon take sallama tareda kiran sunan yayanta, har takai karamin falo bataji ya amsa ba kai tsaye tanufi benen cikin nutsuwa take matakalar bene still bakinta yana kiran yayana.


                       Bakinta dauke da sallama ta tura kofar d'akin tashiga nanma bata ganshiba saidai daddad'a kamshin turaransa da yahade da sanyi air condition sai yake fitar da wani sanyayyan kamshi me sanya nutsuwa sai kuma t-v dake kunne yanata aiki da alama yamanta shine akunne.


                   "Zama tayi gefen gado tare da daukan remote dake kan drower gefen gadon ta" danno tashar katun, kasan cewar tuni *Mamma* takoya mata dan haka tasan yanda ake kamowa, cike da zumud'i tahaye kan gadon tayi zaman cin tuwo wato talankwashe kafafunta, cike da farin ciki yafara kallon tana murmushin dayake kara mata kyau.


Sanye take da wando da riga top fara me dogon hannu wacce tad'an kamata kad'an inda kirjinta yafito, gaban rigar yanada hoton filawa ja yayinda wandon kuma falazo ne baki me layi-layin fari da ja, kanta sanye da hula ja irin me tuntu agaba sosai shirin yai mata kyau kamar yar turawa.


  Gashi tayi kiba abinta dubul-dubul harda gurun wuya, sannu ahankali take kallon katun din tana cigaba da murmushi hardai tafara kyalkyata dariyar, harda rike ciki can kuma tafara hamma! daga nan ta'bin gire akan gadon sai barci.
   


********

Hon ne keta faman tashi abakin get din gidansu *TAUFIQ* da sauri me gadi yazo yabud'e, inda wata bakar mota takunno kai direct gurin ajiye motoci yanufa yai fakin tareda kashe motar yafita, *T J Turaki* ne sanye yakeda riga da wando rigar t-shirt ce dark blue gaban rigar an rubuta THANK U da manyan haruffa,


wandon kuma na jeans fari sai yasaka takalmi half cove fari sai kamshi turare yake zubawa gashin kanshi yasha kum, yayi kyau sosai kasan cewar shima kyakkawan ne, yanada innocent fice da kaganshi azahiri kaga kamilin mutum, saidai kuma abad'ili shid'in KYANDIR ne wato me kyan banza.


Cikin d'an sauri yake tafiya hannusa tarike da waya yana dannawa, kai tsaye yashiga part din *TAUFIQ* still yana cigaba da kiran wayar yanayi yaka kaiwa kunnansa, hannunsa rike da waya yana dannawa ga dukkan alama *TAUFIQ* yake kira koda yashiga babban falon babu kowa, dan haka nan ma kai tsaye yanufi karamin falon.


Still yana sake cigaba da kiran wayar zama yai ad'aya daga cikin kushin din falon yana jan tsaki mtsww! tareda fadin, ban san me yasa kwanan nan sai nayita kiran wayar *TAFADI* tana kara amma sai yaki d'agawa.


Jibi dan Allah yanzuma sai kara wayar take amma saboda tsabar walakanci irin nasa yaki d'agawa, sai kuma yamike da sauri yanufi sama domin yaji kamar motsi cikin sauri yake taka matakalar benan still wayan na manne akunna shi, kwankwasa kofar d'akin yayi tareda fadin excuse me jinshuru ba'a amsa mashiba, hakan yasa shi tura kofar ahankali bakinsa dauke da sallama inda yaci karo da *TASLEEM* kwance tana sharar barci abinta cikin nitsuwa.


Kallon d'akin yayi inda yaga t-v nata aiki sai kuma cike da mamaki yakai kallonsa kan *TASLEEM*, tareda katse kiran dayake yace a ah me kuma  yakawo mai kyau din nan d'akin *TAFADI* ko dama tasaba zuwa ne?...harda kwanciya akan gadonshi.


A ah! to ko dai yana cikin toilet ne?..yafadi yaname nufar toilet din yatura kofar toilet din bakowa ciki, yace a ah baya ciki to kodai be dawo bane?...bari dai nasake kiransa yana kiran layin *TAUFIQ* idon shi yana kan *TASLEEM*, wacce har hulan kanta yacire gurin barci inda lafiyyayan gashin kanta yazubo gefen fuskarta, wanda yakara mata kyau aransa kuwa fadi yake kai! gaskiya yarinyar na Allah yayi mata mugun kyau da diri duk namijin da yasameta yagama more rayuwar duniya.


Koda yasake kiran wayar *TAUFIQ* still wayar tana kara amma har alokacin*TAUFIQ* din be d'agaba, hakan yasa yaja tsaki tareda katse kiran yana fadin d'an iskan har yanzu yaki d'agamun waya.



Hanyar fita yanufi har yakaima bakin kofa yariko marikar kofar, sai kuma yayi tsaye nayan wasu mintuna kamar me tunani can kuma sai yasaki kofar, tareda juyawa da sauri yakoma cikin d'akin.



*******

Gaban  *TASLEEM* yaje yai tsaye yana kare mata kallo tsawon lokaci, kafin sannu ahankali shed'an yafara yimasa hud'uba cewa yahai'ke mata kawai, tunda baza abashi auran taba aikam take yadauki hud'ubar shed'an inda yasaki wani irin murmushin mugunta.


Kallo daya zakai masa kagane imaninsa yaikaura acikin lokaci kan-kani, rigar jikinsa yacire yai wurgi da'ita chan gefe har zaya cire farar singlet din ciki sai yafasa, sai yazare belat din wando yacire still yana cigaba da kallonta yana murmushin narashin imani, yahaye gadon tareda saka hannun yafara shafar kyakkawan fuskarta, aikam da sauri tabud'e ido inda suka sauka akanshi, kasan cewar duk yanda barcinta yai nauyi dazaran anta'bata zata farka.


********
Aikam cike da tsoro tayinkura zata mike yai saurin maida ita zaya danneta tasake yinkurawa tamike, nan dai kokawa yakaure tsakaninsu domin kuwa duk yanda yaso danneta taki yarda, kuka tasaki tareda girgiza kai duk da cewa bata san manufarsa akanta ba hakan be hanata fadin a ah! kabari banaso! banaso!! tana turesa da iyakacin karfinta, hada kaimasa duka da yakushi duk dan tahanashi cutar da'ita.


Kasan cewar karfin mace dana namiji ba d'aya ba dan haka duk abinda take masa ko kad'an beyi tasiri akanshi ba, saima kara mashi kaimi yake akan mugun nufinsa akanta yana fadin haba me kyau aitunda baza abani auranki ba sai nad'and'ani zumarki, nakuma tabbatar zakiyi matukar dad'i domin naga alamar ni'ima atare dake, baiwar Allah itako sai kuka take sosai tana kiran *Mamma* da yayanta.


Wani uban cizo ta gatsa masa ahannu aiko yasaki kara tareda fisge hannunsa, yace kai! kai!! kai!!! kika cijeni?....tab aiko tunda kika cijeni yau ko zaki mutu sai nayi sex dake, wani cizon tasake kai mashi da sauri yajanye hannusa tareda shara mata lafiyyayan marin da saida taga taurari, yayinda jinta da gani yadauke na wucin gadi.


Hakan yabashi damar kokarin cire mata wando saidai kuma kafin yakai ga nasaran yin haka, tafarfad'o inda tafara turesa cikin tsananin kuka da karfin gaske take fadin kabari banaso!z, tareda rintse idonta wanda yake nuna cewa ranta yakai kololuwa gurin 'baci aikam take 'kwan'kwaman kanta suka tashi, wani irin mugun turi takaimashi sai gashi akasa timmm!.


amma dayake zuciyarsa tagama kwad'aituwa dasan kasan cewa da'ita, mikewa yai zumbur cikin karfin hali yasake nufarta inda suka kicime da wani kokawan, dai-dai lokacin da *TAUFIQ* yabanko kofar da karfin gaske.


Kasan cewar tunda yadoso karamin falon yakejin kukanta tareda kiran sunansa, kai tsaye  kan *T J Turakin* yayi tareda chakumoshi yashara masa maruka har biyu cikin masifar fad'a yace wai!kai wani irin mugun d'an iska ne eye?...kenan iskancin naka har akan nagida saboda kai! gizago ne bakada sabo ko?..


to bari kaji nagaya maka billahillazi! idan kace zaka ketama wannan "yarinyar haddi, al'qur'anin Allah kan ubanka *Mamma* zatasa aci la'ada waje d'an iska bunzuru kawai, kabar ganin kai aminina ne tuni zata manta da alakar dake tsakani na dakai tasa aladaftar mata dakai wallah, idan baka sani ba to yau kasani tanada alaka me karfi da human right, ido *T J Turakin* yazaro cike da tsoro da alama yasan ko su wanene human right.


Cikin rawar murya me had'e da mugun tsoro yace human right fa kace?....tamkar zaya sake zabga masa mari domin saida yachakumo rigar singlet din dake jikinsa, tukun na yahayayyako masada masifar fada yace bansaniba banza bunsuru kawai wannan ko kad'an baya iya control din kanshi, sannan yahanka d'ashi da karfi yai baya cike da takaicinsa.


Dai-dai lokacin da *TASLEEM* taduro daga kan gadon, idonta rufe tayi kukan kura tayi cikin *T J Turaki* tasha'ke masa wuya, *TAUFIQ* nakokarin riketa tasa hannu ta turashi dakarfi yai baya inda yai taga-taga zaya fadi amma sai yai saurin dafe bango, tareda kallonta cike da mugun mamaki
jin yanda ta turesa tamkar wani katon namijine yature shi.


Yayinda da karfin gaske take tura *T J Turakin* baya wanda gaba d'aya tsoro yagama cika shi sai zaran ido yake tamkar mazuru, turashi take sosai har sai data danganashi da jikin bango, sannan tad'aga shi sama da hannu d'aya inda gaba d'aya idanunsa suka sake firfito waje saboda tsabar sha'kan datayi masa wanda shakane bana wasa ba, kallo daya zakai mata kagane bata cikin hayyacinta.


*TAUFIQ* kam tsaye yai yana kallonta rai bace yafurta no wander, dama wannan mugun kyau dole sai ansamu bataliyar 'kwan'kwaman aljannu akan nan.


Shuru yai yana tunanin abinyi da sauri yamatsa gurinta ganin yanda take kokarin kashe *T J Turakin*, hakan yasa yafara karanto addu'a yana tofa mata wani irin kara tayi tareda sake turasa yai baya, cikin wata irin murya wacce kanaji zakasan bana *TASLEEM* bane.


tace wannan abun da kanayi bazaya hana mu abinda mukayi niyya akanshi ba, tunda yata'ba mana god'iyar mu yau sai mun kashe! shi sai mun kashe shi! haka take nanatawa da iyakacin karfinta.


Cikin jarumta yasake matsawa kusada ita, ya kallonli fuskarta datayi jajir still har yanzu idonta rufe yake yace kuyi hakuri shid'in mahaukaci ne bayada hankali, shiyasa yai kokarin haikema god'iyar "ku.


Cikin karaji tace karyane d'an iska ne mazinaci yau zamuyi maganin iskancinshi, aikam tasa d'ayan hannunta nahagu ta chafko mazakutanshi.


"Wani irin gigitaccan kara *T J Turakin* yasaki saboda tsabar azaban dayaji ,yayinda *TAUFIQ* yai saurin rintse idon sai kuma yai saurin bud'e idon domin ayanda tasha'ke masa wuya, tareda rikemasa mazakutanshi tabbas tsaf zata kashe sa.



Cikin matukar tashin hankali yace tabbas zaku iya abinda kuka fad'a, amma dan girman Allah kuyi masa afuwa karku kashesa
kunji?...wani irin kara tayi sannan tarad'a *T J Turakin*
kasa jikake rifffff!. Aikam tuni yasume harda sakin fitsari awando saboda tsabar wahala, yayinda ita kuma ta tafi luuuuu! zata fad'i cikin sauri *TAUFIQ* yarikota tafad'a jikinsa, ido yarintse ciki bugawar zuciya shinkam zaya iya cewa tunda yake be ta'ba ganin tashin hankali irin yauba.


Kuri yai mata da ido gashin kanta duk yarufe mata fuskarta ahankali tad'ago hannunta da kyar tamaida gashin baya, still idonta rufe sai yamutsa fuska take cikin wani irin murya me nuna cewa amatukar galabaice take, tafurta washhh! kai! kaina! can 'kasan makoshi yafurta mata SANNU, wanda balallai banema idan tajishi.


Domin tamkar dole akai masa kuma wannan ne karo nafarko da yata'ba furta mata kalmar SANNU tsawon zamanta cikin laluran gushewar tunani.


Sai kuma jikinta yasaki domin kuwa wani irin nauyayyan barcine yadauketa, tsaki yaja mtsww! tareda mikewa dauke da'ita inda yakwantar da'ita akan gado.


Da sauri yabud'e firjin yadauko goran ruwa me sanyi yanufi gurin *T J Turaki* wanda yake yashe kasa tamkar matacce, cikin sauri yabud'e marfin yazuba masa afuska firgigit! yafarka bakinsa dauke da fadin wayyo! wayyo!! kutai makeni zata kasheni, wallahi ba mutum bace aljanace wayyooo!!! ni Ahmad zata kashe ni wani, ku taimake ni! mugun tsawa *TAUFIQ* yadaka masa, tahanyar cewa dallah gafara malam rufe mani baki hakan yasa shi yatsu.


Yanata wuri-wuri da ido yana Kallon d'akin cike da mugun tsoro, yayinda *TAUFIQ* yabanka masa harara cikin masifa yace "d'an iska dama barinta nayi takasheka", kowama yahuta da shegen jarabar nan naka kaga idan kaje lahira sai kayima ubangijinka bayani abinda yakasheka, cikin rawar murya yace my man dama yarinyar nan ba mutum bace?...cike da mugun jin haushinsa yace.....





Muje zuwa



_Kuyi hakuri dajina shuru wayar ba chaji gashi nepa suna yajin aiki😩_




*ALLAH kasa mucika da imani Ameen ya hayyu ya kayyuu*
[11/09, 10:54 pm] Amina Umar Faruq Writer: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
     🕯️🌹🕯️🌹
        🕯️🌹🕯️
              🕯️
  
  🕯️ *KYANDIR*🕯️
      ( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_

( It's all about hatred so much Love and so much caring)

        *BOOK 2* 

PAY ne 300 naira idan kana bukata katura kudin ta wannan 0047769671 Amina Abdullahi gt bank ne, sai katura shaidar biyan ta hanyar yin screen shot sai katurama wannan no 08161850024.

Last Free Page1️⃣9️⃣2️⃣0️⃣

WRITTEN BY

🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
     _Kwantagora_

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR 1- 2*
( _Mai Hasken banza_)

*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.

    *_TSOKACI_*
     Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.

*_GARGAD'I_*
   Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.
 

✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_

""""""""Ban saniba d'an raini hankali kawai idan ba mutum bace ita to wacece?...da sauri yace aljanace mana,

yace dan iska kai! ne kamai da'ita aljanar ko?...yace a ah! dama can din aljanace, cike da fada yace dallah gafara can yanda kake takama kai mutum ne to itama mutumce.

                 Nisawa yayi tareda cewa tab!, aiko dai tana dauke da guma-guman aljanu akanta masu d'an banzan karfi kamar shari'a, kai! kaji yanda aka dam'keni kuwa?... humm! tamkar yanda kuka yake kamun kaza, kai! dagajin wannan dam'kam kasan ba mutum baye yayishi.

Duk dacewa ran *TAUFIQ* amatukar bace yake dashi hakan be hana maganar *T J Turakin* bashi dariya ba, amma sai beyiba asalima sake tamke fuska yayi  yace hum! aibaka dam'kuba wallahi, tunda gashinan har yanzu wannan d'an iskan bakin naka marar control be rufuba, da sauri yace billahillazi! na dam'ku matuka,

yace d'an iska kaidai kasani oh! aisai yanzuma nafahimceka dakai kayi zaton zallar mutumce ita kazo kayi mata fyad'e kaci banza katafi ko?..., kai ya gyad'a cikin wani irin yanayi me kama da nadama yace tabbas haka ne amma wallahi bisa kuskure ne, cike da 'bacin rai yace to tunda baka samu cin banzan ba sai katashi kaje gida marar mutunci kawai.

                  "Aini wallahi *T J Turaki* kayi matukar bani mamaki, kenan ma zaka iya haikema su "twins ko?...ido yazaro da sauri yace haba my man aiko hauka nayi, bazan ta'ba haikema su twins 6ter ba har gaban abada,

Allah bazaya ta'ba samun kwad'ayinsu araina ba, sudin fa tamkar kannai na najini su Naja'at da Sarat haka nasauke su twins 6ter.

"Yace oho! to meyasa "ita din bazaka dauketa tamkarsu" ba?.., idan bakasani ba to yau kasani wallahi daka 'batama yarinyar can rai to gara ka'bata mana rai nida su" twins 6ters sai dubu, domin *Mamma* tadauketa fiyeda mu.

Ni har mamakin yanda takeji da yarinyar can nakeyi wallahi, dan haka kasani akanta komai *Mamma* tana iyayi saboda  haka katashi sahunka alifafa, katafi tin kafin taji abinda kayi kokarin aikatawa akan yarinyarta.

            "Cikin tsananin galabaita yace nayi kuskure my man dan girman Allah karufa mun asiri, karka bari *Mamma* taji wannan abin kunyar dana aikata kaji?...wallahi *Mamma* tana matukar ganina da mutunci, kuma idan har taji nasan tuni zata daina ganina da mutunci nikuma bana fatan hakan kaji?....yakarasa fada fuskarsa cike da tsantsan nadama.

"Fuska had'e *TAUFIQ* yace naji tashi katafi banasan ganinka, ido yazaro yace haba my man ninefa *T J* dinka cikin b'acin rai yace aini daga yau mun raba gari dakai, tunda baka da mutunci wai! da ad'akina zaka aikata fasi'kanci saboda kai! din d'an akuya ne.

Cikin mugun tashin hankali *T J Turakin* yace kayiwa girman Allah karufa mun asiri, karka rabuda ni domin duk duniya banida abokin kwarai irinka idan karabu dani naboni na lalace, babu wanda zaya ringa fad'a mun gaskiya tareda gyara mun kuskure na.

Tabbas nasan nayi babban kuskure amma wallahi nayi nadama dan Allah kayi mun afuwa kaji mutumina?...cikin d'an sassauta murya me nuna alamar yad'an yarda da abinda yafad'a, yace nace naji to tashi katafi.

Yace to amma sai ka taimaka mun natashi wallahi gaba d'aya jikina ciwo yake especially guri ukku nan, yafadi tareda nunawa kaga "kaina wuyana and than my manhood dina" wallahi kamar zaya tsinke haka nakeji.

Saida yabari yakai karshe amaganarsa sannan fuska had'e yabashi amsa da cewa malam idan zaka tashi katafi katashi katafi, idan har kuma saina taimaka maka sannan katashi to ko zaka dauwama anan gurin zaune, da sauri yace haba nawa duk fushin ne haka?....

cikin b'acin rai yace fiyeda hakama dan raini hankalin kawai, kuma wallahi idan har baka fitaba har tafarka tasake sha'karka billahillazi! bazan sake kwatarka daga hannunta ba kaji nagaya maka.

Yanufi hanyar shiga toilet da sauri yace wait chak! yatsaya batareda yajuyoba, yace naji zan tashi nafi amma dan girman Allah kayi hakuri ka taimaka kamiko mun rigana da wandona nasaka gasu can kusada "ita, kuma wallahi bazan iya zuwa kusada itaba domin yanzu kam mugun tsoronta nakeji.

         Tsaki yayi tareda matsawa inda kayan suke watse yaje yawatsa mashi akan fuska, tareda fadin dan iska kasunan sai katashi kasa katafi da sauri yacha'be kayan yace godiya nake aminin kwarai, batare dayace komai ba yashige toilet bakinsa dauke da addu'a saidai har alokacin yanajin yanda kirjinsa ya cigaba da bugawa

Yayinda zuciyarsa take cunkushe saboda wannan abun da *T J Turaki*, ya'aikata ma *TASLEEM* gaba d'aya yahaifar masa da matsakancin 'bacin rai marar musaltuwa, wanda yarasa meyasa shi jin hakan d'an guntu tsaki yaja mtsww!. tareda tu'be kayan jikinsa yasakarma kanshi ruwan sanyi, ahankali yake sauke ajiyar zuciya jin yanda ruwan yaratsa kwakwalwarsa har zuwa tafin kafarsa, sannun ahankali sanyin ruwan yashiga ratsa har cikin bargonshi yad'an jima ruwan nasauka ajikisa kafin yadauki sabulu yafara wankan ahankali kamar bayaso.

*********
*T J Turaki* kam yana ganin *TAUFIQ* yashige toilet cikin sauri yasaka kayan yanayi yana Kallon *TASLEEM*, har yagama sakawa inda tsabar sauri tabaibai yasaka rigar sannan yamike dakyar duk idonsa yana kanta, wacce ita batama san wainar dayake toyawa ba domin kuwa tayi matukar nisa abarcinta dajan kafa yafita bata saniba.

*TAUFIQ* kam bayan yai wanka saida yad'auro alwar magrib sannan yafito, dan haka be iske *T J Turaki* ba tsaki yaja tareda kai kallonsa kan *TASLEEM* wacce keta sharar barcinta me d'an karan nauyi.

 
                "Duk dacewa barci take hakan be hana agane amatukar galabaice take ba, domin ayanda take sauke numfashi tareda ajiyar zuciya kawai zaka fahimci hakan yadad'e tsaye yana kallonta, aransa yanad'anjin wani abu me  kama da tausayinta kafinan yanufi gaban merro, body sprim kawai yafeshe jikinsa sannan yabud'e wadrof yadauko boxe da jallabiyya sky blue tareda hula taba kaji hadisi bayan yasa yadauki farin tasbi, yasa wani silifas me taushi yasa yasake feshe jikinsa da turare sannan yafita zuwa masallacin.

*********
Saida yai sallar isha'i sannan yafito kai tsaye part din *Mamma* yanufa, bakinsa dauke da sallama yashiga *Mamman* ce ta amsa wacce fitowar kenan daga d'aki tana sanye da hijab milk hannunta rikeda tasbi fari tanaja da alamar idar da sallar isha'inta kenan.

Kallonsa tayi tareda cewa daga masallaci kafito ne?...yace eh *Mamma* dama nazone nasake tambayarki, da sauri tace akanme fa?...yace *Mamma* akan yarinyar can mana me ciwon mantuwa, da sauri tace  zaka fara ko?...danlele wai meyasa bakajin maganata ne?....

cikin murmushi yace yi hakuri *Mamma* nadaina, tace hum! aiko abakinka aka halicci kalmar nadaina iyaka kenan amma kuma baka martabata tunda baka dainawar.

Ina jinka menene tambayar?...yace *Mamma* dama cewa nayi wai "ita dillaliyar nan data kawo maki waccan yarinyar aiki, dama bakisan komai agame da'ita ba ne?....

Cikin sanyin murya tace kaidai bari aiba karamin kuskure nayi ba wallahi bansan komai ba, agame da'ita damafa bamuyi wani dad'ewa ba da'ita tunda duka-duka bamu fi sati biyu ba, da had'uwa kawai dai taji "nace inason yar aiki shine tace" zata samo mun.

Ranan nan kawai sai gashi takawo mun wannan yarinyar *TASLEEMA*, itama kuma bamufi sati biyu ba sai wannan tsautsayin yafaru da'ita  kuma cikin hukunci Allah, sai ban ta'ba tambayarta komai game da'ita ba, saidai kamar na ta'bajin tace ko unguwar tudun wada ko nasarawa nadai manta inda tace.

Kai yagyad'a alamar gamsuwa da maganarta sannan yace shikenan*Mamma* in sha Allahu gobe zansake kaiwa Landmark asake yin sanarwa ko Allah yasa agane yan uwanta, sannan zansa aje unguwan tunda wada da nasarawa nanma ayi sanarwar kila asamu yan uwanta, domin gaskiya yakamata ace takoma gurin su ko yakika gani?...

Tace tabbas haka ne to Allah yakaimu goben lafiya sai kasa ayi din yace to ameen, har zaya wuce tace   kai! ina "yarinyar tawa take ne?...ban ganta ba cike da mamaki yace ah! har yanzu tana can tana barcin kenan?..
cike da mamaki itama tace barci kuma?...

Saida ya zauna sannan yace "eh aiko da naje na isketa tanata barci, "nikuma ban tada'ita" ba nasan shine har yanzun tana can tana barci bata tashi ba.

Tace ikon Allah *TASLEEM* barci har yanzu?....gashi anyi magrib har anyi sallar isha'i amma bata tashiba, to lafiya?...yace to wayasani amma dai *Mamma* anya "yarinyar nan batada ciwon barci?...yakarasa fada yana kunshe dariya, hararansa tayi tace eh tana dashi sai kasamo mata magani kaji?.., cikin murmushi yace yi hakuri *Mamma* wasa nake.

   Amma dai gaskiya barcinta yai yawa cikin sanyi jiki ta zauna tare dacewa "eh gaskiya kwanan nan tana yauwan barci sosai kome yasa?...yace uhum!, tace kaga tashi kaje katarmun da'ita tayi sallah, ahankali yamike tareda cewa to har zaya wuce da sauri tace kai! tsaya aina manta sabon magani da likita yakawo matane take sha, shine yakesata barci kuma yace idan tayi barcin kar atasheta domin ba mamaki cikin barcin tunaninta yadawo.

Dan haka jekawai ka dauko mun ita cike da mamaki yace haba *Mamma* wani irin dauka kuma sai kace wata jaririya?..., tace to ai jaririyarce wacce bata da lafiya kuma kaga likinta yace" aringa lallashinta dan haka jeka dauko mun ita, dan Allah kar kabari ta tashi kaji?..

Rai ad'an 'bace yace haba *Mamma* yanda nagajin nan yaza'a na iya daukar wannan katuwar yarinyar me kamada buhu, yakarasa fada daturo baki.

Hararan shi tayi tareda fadin buhunce kuma sai ka daukota, domin sai kasan bazan barta takwana d'akinka ba tunda ita din ba muharramarka bace, da sauri yace haba "ainima ya za'ai nakwana da'ita" ad'akina salon tahanani barci da wannan fuskar nata me kalan ta aljanu, yakarasa fadi dayin dariyar zolayar dayasa ba.

Har *Mamma* zatayi magana sai ga *TASLEEM* tashigo tana faman murzan ido, fuska dauke da fara'a *Mamma* tace yauwa alhamdulillahi! kaga shikenan ma ga yar albarka nan ta taso, sannu  *TASLEEM* kin taso...?

kai

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment