Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake, ciki da takaici had'e da tsananin bacin rai *TAUFIQ yazo yada'ga shi ciki masifar fad'a yace dalla gafara can malam wai meye haka kakeyi ne eye?...cikin firgita yace  eye?...


harara yawatsa mashi tareda cewa wai bakaji abinda *Mamma* tace" bane anyi mata miji ba?...cike da gigita yace me "tace ma?....cikin jin haushin yace ban saniba banza, kaga malam idan zaka tashi muje katashi muje idan kuma bazaka tashiba zan wuce kanaji ko?...da sauri yace to muje amma dan Allah kace da *Mamma* ta taimaka tabani auran  kyakkawar yarinyan nan kaji mutumina?...


cikin masifar fad'a tamkar zaya had'iyasa yace dalla gafara wai kai wani irin mayan mutum ne eye?...,in bandama kazama namamajo sarkin mata me zakai da me ciwon mantau eye?....Da sauri yace wallahi inasonta ahaka ko ciwon hauka gareta yayinda cikin bacin rai *Mamma* tace danlele *TASLEEM* din tawace me ciwon mantau?...da sauri yace a ah!  *Mamma* kiyi hakuri banufina kenan ba raina ne yabaci yasa nace haka tace to yayi kyau sai  kutafi.


            Cike da bacin rai *TAUFIQ* yaja *T J Turaki* 'keeeeeee! kamar kayan wanki suka nufi part dinsa, suna shiga babban falo yature shi yafadi tareda kaimashi shuri dakafa har sai da *T J Turakin* yace washhhh! haba my man zakaji mun ciwo fa, yakasa fadi fuskarshi d'auke da murmushi.


           Cikin masifar fad'a yace banza kawai aigara naji maka ciwon tunda kai! mayan mata ne inbanda kazama jarababbe ba me zakai da wacce batama san kanta ba eye?....mikewa yai yana dariya "yace kasan Allah ko yaya take" indai "zasu bani ita na aura inasonta", domin nidai tayimun wallahi saboda duk abinda d'a namiji yake nema agurin mace tana dashi.


Da sauri *TAUFIQ* yarintse ido zuciyarsa tana bugawa yato she kunnasa cikin tsawa yace dalla malam ya'isheni hakan, basai kafasa mun dodon kunne ba da mugun surutun ka nabala'i kaga idan zakai maganar dakazo muyi to bismillahi!, idan kuma bazakayi ba to ni barci nakeji dan haka kaga tafiyata naje nakwanta yakarasa fadi da nufar hanyan hawa benan,


da sauri yarike shi tareda fadin yi hakuri my man zauna muyi maganar wallahi tanada mutukar mahimmanci.


                "Fuska had'e yabanka masa harara yace d'an iska kawai namamajon banza da wofi daga ganin "yarinya bakasan halinta ba bakasan danginta ba, in part bakasan komai agame da'ita ba amma saboda tsabar jaraba irin taka duk kawani burkicema mutane.


Cikin dariyar sha'kiyanci dayasaba yimasa, yace mutumina bazaka gane bane, domin ni naga abinda nagani ajikinta 'yarinya nan, yace dama yaza'ai nagane tunda ni ba mayan mata bane irinka.


            "Yace naji ni mayansu ne" kuma aiba haram bane sannan ba bid'a bane sunnace, tunda annabin mu (S A W) yana matukar san mata dan haka nima nake sansu, kaima kuma nasani kanasan su" fiyeda ni kawai dai baka bayyanawa ne, saboda kai! hakan nan ne tsarinka.


Kunne *TAUFIQ* yasame toshewa da hannuwansa duk biyu idan ransa yakai dubu to gaba d'aya sungama 'baci, da surutun da *T J Turaki* yake zuba mashi akai!, kasan cewar shidin mutum ne da bayasan hayaniyar magana da yawa, musamman ma idan akansa akeyi.


Yayinda shikuma *T J Turakin* yakasance maganan nan mutum ne nagasken gaske, dan haka yaketa zubawa bakwama balle ful stop yayinda shikuma *TAUFIQ* har wanin yama-yama yakejin kwakwalwarsa tanayi, tsabar magana daman lokuta da dama abinda yake saurin had'asu fad'a kenan wato yawan magamarsa.


Cikin tsawa yace dalla gafara malam kadameni da ihu, idan baka tashi yin abinda yakawo ka ba ni zanje nakwanta kuma billahillazi! duk "ubanda yaimaka tsaye bazan tsaya na saurare kaba kaji ko?...da sauri yace sorry to zauna, muyi maganar saida yaja tsaki tareda hararansa yace banza parrot kawai.


Cikin dariya yace nadaiji zauna danlele *Mamma* aminin kwarai na * T J Turaki*, kyakkawa mijin mace me sa'a, kai! ni wallahi dama dai *Mamma* tasa amaida auran kyakkawar can akanka, danaji matukar dadi saboda zakuyi matukar dacewa, domin naga alamar "itama miskilace irin ka yakarasa fadi dayin dariya.

       Sai kallonshi *TAUFIQ* yake me had'eda harara har saida yakai aya sannan ya girgiza, cike da takaici yace wai kai! dan girman Allah bakinka baya ciwo ne?....cikin murmushi yace a ah! bayayi, to dan Allah karinga saka kwad'o da mukulli kana rufe bakinka kaji?....da sauri yace kuttttttt! lallaima my man wallahi bazansa kwad'o harda makulli narufe baki naba.

          Kanagani ahakama yana bud'e yana motsi amma kullum sau uku zuwa hudu nake masa brosh dan karda yayi wari, to kuma yanzu idan nasa mashi padlock natufe ruf baya motsi ai warin dunge zayayi ko na mushe, yakarasa fadi dakashe masa ido d'aya aihaka ne ko nawa?...

tsaki *TAUFIQ* yaja mtsww! tareda fadin kaidai kasani, yace "eh kaima kasan haka! to zauna mana gashi kayi tsaye kikam kamar wani trapic man, saida ya hararansa sannan yazauna suka fara tattaunawa akan wani muhimmin al'amari.


*Bayan sati daya*
********

Haka sai rayuwa take cigaba da tafiya har yanzu dai shuru tunanin *TASLEEM*, be dawo gareta ba kuma sosai *Mamma* take kulawa da'ita tareda baga magungunan akan 'ka'idan yanda likita Lamir yabayar.


Kasan cewar har yanzu dai shine likitan dayake kulawa da'ita, tunda *Mamma* taso *TAUFIQ* yai masu biza afitar da'ita waje dan aduba kwakwalwarta da kyau, to amma sai likita Lamir din yahanasu ta hanyar cewa aiko sunje waje magungunan dayake bata irinsu za'a basu.

Dan haka dole *Mamma* ta hakura ba dan taso ba, abinda bata saniba duk *TAUFIQ* yatsarama likita Lamir din cewa yacema *Mamman*, haka domin yace shi bazaya kashe kudinsa abanza ga marar kunya yar talakawa ba, yayinda shikuma likinta Lamir hakan bakarin yimasa dadi yayiba, ko bakomai yakara samun kusanci da *TASLEEM* din dama sunyi matukar shakuwa, gashi Allah yazuba mashi masifar kaunarta aransa wannan kenan.


Yau asabar kuma ayau ne su *Mamma* zasu kaimasu Hassy da Hussy ziyara makarantarsu, *G G S U C K* wato _government girls science unity college Kontagora_.


Wanda harda *TASLEEM* din za'aje kai ziyaran wanda ko kad'an bada san ran *TAUFIQ* za'atafi da'ita ba,yayinda *Mamma* ta tuma kasa tace idan har bada ita za'atafi ba to itama bazataje ba hakan yasa dole akashirya tafiyar da'ita.


Da misalin karfe goma saura yan mintuna *Mamma* da *TASLEEM* suka fito cikin shirinsu tsaf sai kamshin turare suke, inda *Mamma* take sanye da wani tamfatsetsan less me ruwan toka dake da ratsin marron, dinkin doguwar rigane na saura kiris wuyata da hannuwa sanye da diamond tayi daurin d'akwali irin na manyan mata, fuskarta sauke da light make up tayi kyau sosai musamman data yafa babban gyale marron color, sai tafito chas abinta babbar mace me matukar haiba da kamala idan ka kalleta bazaka ta'ba cewa ita ce tahaifi zabgegen saurayi *TAUFIQ RASHID TAFADI* ba.


           "Yayinda itama *TASLEEM* sanye take da abaya ba'ka da ratsin marron tanada duwatsu a gaban rigar tundaga sama harkasa, abayar irin me igiyar daurawan nance dan haka da tadaura igiyar sai yafito mata da shape dinta sosai especially kirjinta, itama wuyanta sanye da sarkar diamond dan siriri hannunta daya kuma daure da agogo tsayarta d'aya sanye da zobe na sarkar, itama *Mamma* tayi mata light make up sannan tayi mata rolling kanta da gyalan abayar, gaskiya tayi matukar kyau tamkar balarabiyar kasan masar  kamar kasaceta kaboye dan kyau.

        Tsaye suke *TASLEEM* narike da wayar *Mamma* tana buga game tana dariya abinda hankali kwance, suna jiran fitowar *TAUFIQ* ne sutafi suna nan tsaye sai ga inna talatuwa tashigo cikin girmamawa tace hajiya angama saka komai aboot din, tace ansaka duka harda su cincin da cake din?..tace "eh ansa, to  masha'allah! sannu da kokari da aiki inna talatuwa tace yauwa.


*Mamma* tace yanzu megidanki kawai muke jira, tace ai in sha Allahu yanzun nan zaya fito tace to Allah yasa karya shanya mu kamar kayan wanki, cikin dariya tace to ameen sunkai kusan fiye da mintuna shabiyar atsaye shuru be fitoba.


Kai! *Mamma* ta girgiza tareda kallon inna talatuwa tace kinga  munata jiran mutuminki har yanzu Allah bai bashi ikon fitowa ba ko?...cikin murmushi tace ayi hakuri hajiya aiyana nan zuwa.

Dai-dai lokacin da *TAUFIQ* yashigo wanda tunkafin yakaraso masifaffam kamshin turaransa yagama cika hancinsa, cikin takun kasaita yakaraso gurinsu fuska d'auke da fara'a Inna talatuwa tace to shikenan ma ga megidan nawa nan yafito.


Murmushi yai datake karama fuskarsa kwarjini da haiba tareda cewa inna talatuwa tasamu kenan?...,cikin dariya tace eh kai kad'ai ake jira yace to gani inna talatuwa yakika ganni nayi kuwa?.


Ahankali take kallonsa yana sanye cikin wani dakakken yadi baki me sheki wanda kallo d'ay zakai mayadin kagane me tsada ne yanada matukar kyau da daukan ido, anyi masa dinki zamani inda aka ratsa wani yadi marron dinkin yai kyau sosai kansa ba hula dan haka gashin sai sheki yake, hannunsa daure da agogon diamond da kafarsa sanye da takalmi half cover marron kai! gaskiya yayi matukar kyau tsarin shirin nashi sai yai kamar anko sukai da *TASLEEM* tayi.


Saida ta gama kare mashi kallo sannan tace tubarakallah! masha'allahu! megidana kayi kafito tsaf kad'and'asa kyau Allah yasa kar wata takwace mun kai, murmushi yai tareda fadin godiya nake karki damu daga ke! bakari tace to shikenan hajiya ga megidana nanfa yafito.


tace "eh da yagama isaba dariya yai me kayatarwa tareda cewa kai! *Mamma* wani irin isa kuma?...tace wanda kasaba mana dai-dai lokacin da *TASLEEM* tace yayana mutafi?...kallonta yayi danufin yagwasaleta kamar yanda yasaba, sai yafasa sakamakon jidayai gabansa yai mugun fad'uwa saboda ganin tsananin kyau datayi irin wanda bai taba ganiba arayuwarsa, aiko take yarikice har baisan lokacin da yace *Mamma* amma dai ba haka zamu tafi da ita tsirara bako?... ido tazaro😳cike da tsoro tace....


 


Muje zuwa


Kardai ashagala KYANDIR book 2 nakudi ne akan farashi me sauci 300 naira after free pages sun kare, idan kana bukatar cigaba  za iya biya ta wannan acc no 0047769671 Amina Abdullahi gt bank ne idan katura sai kayi screen shot katura shaidar biyan ta wannan no 08161850024 sai najiku nagode.

Kuyi hakuri jiya nasa nayi posting sai Allah bai bani ikon yi ba, saboda condition din da kanina yake ciki so karda ku gaji dani har yanzu ina bukarta addu'ar akan kanina da bayada lafiya nagode.





*ALLAH kasa mucika da imani Ameen ya hayyu ya kayyuu*
[11/09, 10:54 pm] Amina Umar Faruq Writer: 🕯️🌹🕯️🌹🕯️🌹
     🕯️🌹🕯️🌹
        🕯️🌹🕯️
              🕯️
  
  🕯️ *KYANDIR*🕯️
      ( _Mai Hasken banza_)
_A Romance love story_

( It's all about hatred so much Love and so much caring)

        *BOOK 2* 

PAY ne 300 naira idan kana bukata katura kudin ta wannan 0047769671 Amina Abdullahi gt bank ne, sai katura shaidar biyan ta hanyar yin screen shot sai katurama wannan no 08161850024.

Page 1️⃣3️⃣-1️⃣4️⃣-1️⃣5️⃣

WRITTEN BY

🌹 *AMINA UMAR FARUQ*🕯️
     _Kwantagora_

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*ZAUJUN MAJNUN part 2*
*TASEERI*
and now
*KYANDIR 1- 2*
( _Mai Hasken banza_)

*GODIYA*
Tabbata ga Allah ubangiji madaukakin sarki me kowa me komai, wanda yabani ikon rubuta wannan littafin, tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S A W), da iyalainsa da sahabbansa da wayanda suka yarda dashi har zuwa ranan kiyama, ina rokonka Allah kabani ikon gama wannan littafin lafiya ameen.

    *_TSOKACI_*
     Wannan labarin 'Kir'kirarran ne banyishi dan cin zarafin "wani ko wata" ba, dan haka dukkan wandan yaga hali yazo d'aya danashi, to bashi nakeba arashi ne.

*_GARGAD'I_*
   Bayarda wani yasauya mun labarina, ta wata siga ba tareda sani na ba, yin hakan babban kuskure ne, dan haka sai akiyaye.
 

✍🏼
_Bismillahirrahamanirraheem!_

""""""""Subhanallahi! danlele tsirara fa kace take?...cikin bugawar zuciya yace "eh mana, tace innalillahi! shin d'anlele kafara makanta ne kome?....ga sutura ajikin yarinya amma kace tsirara take.

Yace *Mamman* wannan kayan dashi da babu duk d'aya tunda batasaka hijab da niqaf ba to tamkar tsirara take, hararansa tayi tare da fadin oh! wato tunda batasaka hijab da niqaf ba shine take tsirara?...da sauri yace "eh.

                      "Cikin fad'a tace to nidai "banganta tsirara ba saidai idan kaine kaganta" haka nan, fuska murtik yace to *Mamma* gaskiya bazata bimu haka ba, dan haka taje tasaka hijab da niqaf wanda ai dama tasaba sakawa ko?...tace "eh tabbas datake cikin tunaninta tana sakawa, amma yanzu tunda bata cikin tunaninta bazata saka ba kuma dole sai anje da'ita idan kuma baza'aje da'ita ba saidai afasa zuwa ziyar eheee takarasa fadi da zama akan kushin tare da daukar kafa d'aya ta d'ora akan d'aya tana girgizawa.

Kallonta yai cike da mamaki inda yahango tsantsan rigima kwance akan fuskarta har be san lokacin da yad'an murmusaba, yace  *Mamma* maganar afasa zuwa ziyarama bata taso ba, domin idan har muka fasa zuwa to ko tabbas "su  twins bazasuji dadi ba sam, tace to atafi da'ita" yace *Mamma* ai duk yanda kikace" haka za'a.

                   "To amma meyasa *Mamma* zakice bazata saka hijab da niqaf ba eye?....alhali kuma tana sakawa, bayan haka kinfasan ace dukkan jikin mace al'aurane, da sauri tace "eh nasan da hakan tin ban haifeka ba, amma aibanda fuskarta da tafin hannuwanta dana kafa, kuma ka kalleta da kyau suka d'ai ne afili.

Sannan abinda yasa nace bazata saka hijab da niqaf ba, saboda ko Allah yasa muga "wani da yasanta", kaga sai yataimaka mana muhad'ata da *iyayanta, amma tasaka hijab da niqaf yaza'ai wani yaganta balle har aganeta eye?.

                         "Cikin kwantar mata da hankali yace haka ne *Mamma* to tashi mutafi, sannan tamike tareda kama hannun *TASLEEM* tana cewa muje kinji yarinyar kirki, fuska dauke da murmushi tace to *Mammana* suka nufi hanyar fita.

Yayinda *TAUFIQ* yabi bayansu yana girgiza kai! yana me sake jinjina girman kaunar dake tsakaninsu, wanda har yau yana mamakin karbin wannan kaunarta su yayinda inna talatuwa ma take biye dasu domin tayi masu rakiya.

                    Matoci uku ne wato *TAFADI 1* TAFADI 2 TAFADI 3*. Motar farko security ne aciki yayinda mota tabiyun ne suka shiga *Mamma* da *TASLEEM* abaya *TAUFIQ* nagaba shida driver, mota ta uku kuma wasu secuirity ne aciki inna talatuwa tanan tsaye harsuka tashi tareda barin harbar gidan, sannan takoma cikin tana meyi masu fatan dawowa lafiya.

********

Cikin nitsuwa direbobin ke tuki akan kwalta tamkar basu san tafiya, wanda ogansune yabasu umarni yin tukin cikin nitsuwa saboda yasan *Mamma* batasan ana gudu da'ita. .

                    "Ahankali kira'a ketashi acikin motar su *Mamma*, hakan yasa duk sukayi tsit suna sauraran kira'ar yayinda sanyi ac motar had'eda sanyayyan turaran mota, wanda yagauraye da kamshi turarukan jikinsu, sai yahadu yabada wani irin ni'imantaccan kamshi me saukar da kasala da kashe jikin d'an adam.

     Sosai *TASLEEM* ta nitsu tana sauraran karatun wanda yaimata dad'i sosai, tanasan tabi karatun amma takasa sai kawai ta kwantar da kanta akafad'ar *Mamma*, tareda lumshe ido ba abuga me son jiki murmushi kawai *Mamman* tayi tareda girgiza kai tana me cigaba da sauraran kira'ar tareda bi.

    "Aban garan *TAUFIQ* kam sanyin ac da kamshin turaransu yasaukar masa wani irin kasala, hakan yasa lafe akan kujera tareda lumshe ido yanutsu sosai yana me sauraran kira'ar, karantun ahankali yayinda duk wani motsin *TASLEEM* akan idonsa kasan cewar lokaci-lokaci yakan bude idon ahaka har suka isa school din su twins, basu wani shan wuyaba gurin ganinsu.

******

Cikin tsananin farin ciki suka rungume *Mamman* har suna kokarin kayarda ita, saida *TAUFIQ* yadaka masu tsawa tareda fadin bakuda hankali ne kayarda ita zakuyi ne?...da sauri suka saketa suna dariya sukace no bros munyi miss dinta ne over, sai kuma shima sukaje da sauri suka rungume shi suna bros kaima munyi miss naka sosai shima kamar zasu kadashi, amma ko gezau beyi ba kasan cewar sa namijin gaskiya.

        
                   Cikin dariya yace nima nayi miss "naku irin sosai din na rigimanmu kannai na, sannan yarabasu" da jikinsa yana kare masu kallo duk sun fad'a saboda karatun dasukeyi kasan cewar sun kusa fara rubuta wayak da naiko.

           "Amma cikin zolaya yace kai! yaran nan anya kuna karatu kuwa?...naga kumatunku sunyi su'bu-su'bu ne kamar banke,yakarasa fadi da kallon *Mamma* yana kifta mata ido wacce keta dariyar farin cikin ganin 'yan biyunta, itama cikin zolaya tace gaskiya kam da alama basuyin karatun nan domin gasunan sunyi lukuta-lukuta abinsu harda gurun wuya sukai.

            Cikin shagwa'ba suka fara bubbuga kafa suna fadin wallahi suna karatu ba'aga duk sun rameba, suka karasa fadi tareda sake zuwa suka rungume *Mamman* cikin dariya tace gaskiya ne na yarda da yarana suna maida hankali da karatu sosai.

Sai kuma suka saketa suna kallon *TASLEEM* wacce ke tsaye tanata murmushi, Hussy ce tace *Mamma* wacece wannan?...cikin murmushi tace baku ganeta ba?....dukkansu sukace a ah wacece ita?...,Hussy ta sake cewa kai amma gaskiya tanada kyau kamar yar indiyawa takarasa fadi tareda karasawa gurinta ta kamo hannunta wanda yaji jan lalle, tace wow! gaskiya lallenki yayi kyau sosai pls tumara name kiyahe atunaninta *TASLEEM* yar indiyace😂.

            "Cikin rashin fahimtar abinda Hussy take nufi tace me kikace?.., ido Hussy tazaro tareda fadin wow! ashe kinajin hausa nace ne yasunanki?...cikin kayataccan murmushinta me kara mata kyau da kwarjini, tace sunana  *TASLEEM*.

                Wani irin uban tsalle Hussy tayi tareda rungume *TASLEEM* din aiko tuni sukai kasa zasu zube, da sauri *TAUFIQ* yatare Hussy cikin fad'a yace ke! Hussy meye haka idan takaryaki fa baki ganta bane buhu guda.

                Ido tazaro cikin dariya tace kai! bros T ai ita din bakatuwa bace, kawai dai tanada hips sosai ne, baki yata'be tareda yima *TASLEEM* din kallon kasan idon, sannan yai kasa-kasa da muryar dai-dai kunnan Hussy yace aikam gashi nan sai fama take da gidan kashi ko sha'awa babu.

Cikin dariya Hussy tace kai! bros ai hips yana karama mace kyau, yace hum!, tareda hararan *TASLEEM* wacce ke ta murmushi sai kuma da sauri Hussy tasake cewa bros wallahi ban san ita ce 6ter *TASLEEM* ba, cike da mamaki yace dama kin santa ne?....tace eh mana idan muka kira *Mamma* tana bata waya mu gaisa da'ita,


aitama fad'a mana duk abinda yafaru da'ita Allah sarki na tausayamata, da sauri yace ke! dalla batada matausaya saboda bata da kunya, tace eyya kilan dan bata cikin tunaninta ne, amma batayi kalar rashin kunya ba hararanta yayi tare da cewa ke! dallah har wani kalane da mara kunya?...tace eh mana daga yanayin da d'a bi'ar mutum za'a gane.


             Fuska had'e yace to secological har anfara nazarin sanin halayyar d'an adam din kenan ne?....cikin dariya tace kai! bros, yace eh mana, cikin murmushi tace a ah bros yanzu dai muyi mata addu'a Allah yabata lafiya baki yata'be batare da yace ameen ba.


Itakam Hussy cike da farin ciki ta kalli Hassy wacce taketa kallon *TASLEEM* da kyanta yadauki hankalinta, amma bata nunaba kasan cewarta miskila irin *TAUFIQ*.


   ******
Tace Hassy ga *TASLEEM* fa cikin basarwa tace naganta tareda nufar gurin *TAUFIQ*, wanda dad'i duk yarufe shi naganin yanda Hassy tanuna halin ko in kula ga, *TASLEEM* din aiko take aransa yafara rokon Allah yasa Hassy tana side dinsa wato itama na tsanar *TASLEEM* din kamar yanda yatsanet.

  
             Tana karasawa gurinsa takama hannusa tarike tareda jansa suka fara tafiya tana cewa bros T muje chan karkashi bishiyar mango muzauna, yace Ok.


Yayinda su *Mamma* ke biye dasuna abaya, suna cikin tafiya sai *TAUFIQ* yace da Hassy ashe kun dad'e da sanin wancan aljanar yarinyar, tace 'eh duk lokacin da muka kira *Mamma* tana bata waya muna gaisawa aitama fad'a mana komai game da'ita, baki yata'be tareda fadin ok amma bros meyasa naji kace mata aljana?...yace bakiga tafaye kyau ba aijinsi aljanuce, cike da tsoro tace gaskiya kam nina na tsorota da kyanta.


             Amma kema naga kamar "bakiyi farin ciki da ganinta" ba kome yasa?...tace nima ban sani, yace ko dai kema kin tsaneta ne kamar yanda na tsaneta?...da sauri tace bros ka tsaneta yace sosai ma kuwa, murmushi tayi tareda cewa bros nima na tsaneta yace da gaske? my lovely 6ter, tace Allah tunda baka santa nima bana santa hannu yabata tareda fadin kashe mun nan cikin dariya ta tafa hannunsa.


Dai-dai lokacin da suka karasa karkashin bishiyar mangon, inda *Mamma* tasa  Hussy taje cikin boot tadauko musu darduma suka shinfida duk suka zazzauna, sannan sukaje ita da *TASLEEM* sukayi tadauko tarkacan dasu *Mamman* suka kawo musu.


Nan dai sukaita cin wasu daga cikin tarkacan suna fira inda firan yakasu kashi biyu, *TAUFIQ* shida Hassy suketasu firan sunata dariya, yayinda *Mamma* Hussy da *TASLEEM* suke tasu firan suma suna dariya abinsu inda cikin lokacin kan-kani, *TASLEEM* da Hussy suka shaku tamkar sun kai shekara da sanin juna, atakaice dai nan su *Mamma* suka yini sai misalin karfe biyar na yamma sannan suka tafi *TASLEEM* da Hussy da kyar suka rabu harda kuka saida *TAUFIQ* yaimasu tsawa tukun na.


********
Aban garen su *inna* da *Abba* kam haka nan suke cigaba da gudanar da rayuwarsu cike da tawakkalin, inda yanzu sun rage damuwa sosai suka mikama Allah lamarinsu suna kai kukansu agareshi kullum, ta hanyar rokonsa idan har yar tilon yarsu *TASLEEM* tana raye Allah yadawo masu da'ita garesu idan kuma bata raye, to Ubangijin Allah yajikanta yaimata rahama
yasa aljannar firdausi ce makomarta, wannan addu'ar ita ne sukeyi ba dare ba rana.


*Bayan kwana biyu*

*********
Ranan jumma'a da misalin karfe shidda na yamma *TAUFIQ* ne yake kokarin fitowa daga mota da direba yabud'e mashi da alama dawowarsa kenan daga gurin aiki, sanye yake cikin wani farin yadi me santsi dinkin dai irin nazamani ne wanda ake ratsa wani yadi da alama dai yana matukar son dinki, kasan cewar yadin farine sai aka ratsa bakin yadi dan haka yaikyau sosai musamman da yasaka bakin takalmi.


Sai yadaura agogo me bakin fata irin me shaini din nan, yayinda cukurkud'ad'd'an bakin gashin kasa yaketa sheki saboda gyara dayasha, sai zuba kamshin turare yake sosai shigar tayi masa kyau fuskarsa tayi fayau da alama agajiye yake, ahankali yake tafiya hannusa d'aya sanye cikin aljihun wando, d'ayan kuma rikeda wayoyinsa biyu.


Kallo daya zakai masa kagane tabbas amatukar gajiyen yake kai tsaye part din *Mamma* yanufa, bakinsa dauke da sallama *Mamma* datake zaune ta amsa tana Kallon tashar aljazir
zama yai kusada ita tareda fadin sannu *Mamma* da hutawa yagida?...tace yauwa sannu gida lafiya lau ya aiki yace alhamdulillahi!.


Sai kuma yakwantar da kansa akafadarta cike da shagwa'ba yace washhh! *Mammana* nagaji wallahi sosai tace sannun kaje kai wanka ko karage jin gajiyar, yace to *Mamma* tare da tashi har yafara tafiya sai yatsaya tare da juyowa cike da daukan magana yace a ah! *Mamma* ina?... aljanar yarki ne yau banganta ba, yakarasa fadi fuskarsa dauke da murmushi.


Hararansa tayi tace anya d'anlele bazaka daina kiranmun "yarinya aljana ba ko?...,cikin dariya yace yi hakuri *Mamma* nadaina tace hum! ai kullum haka kake cewa amma gobe kuma sai kasake fad'a, cikin zolaya yace daga gobe zan daina oh! wato kamasan zaka kai goben kenan ko?...
yace kai! *Mamma* in sha Allahu zankai shekaru ma ba gobe ba, tace Allah yasa. 


Yace ameen yanzu dai ina "take nad'an rankwashi kan nan nata da bayaja yakarasa fadi dayin dariyar zolaya, kai! ta girgiza tareda fadin aikai naka kan yanaja hum! Allah dai yashirya munkai, tana can part dinka tin d'azu wai har yanzu baka dawoba bari taje part dinka tagani kila kadawo baka shigoba ne, nace ai sai tayita zuwa tunda ita bata zuciya.


Cikin dariyar mugunta yace yauwa dai-dai makenan yanda zanji dadin rankwashi kanta da kyau, yakarasa fadi dasake yin wata dariya tace kasan Allah idan ka ta'bata sai ranka ya'baci wucewa yai yana cigaba da murmushi.


Yana nufa hanyar part dinsa yaji gabansa yai mummunan bugawa, da sauri yatsaya tareda rintse ido yadaura hannunsa akan kirjinsa dayake bugawa cikin tsananin tsoro yace......
 


Muje zuwa


Ina godiya sosai da addu'o'in ku akan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment