Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka shigo nan?"
Bayan na fadamar ne ya umarceni dana bashi duk kayayyakin da nayi amfani dasu wajen shigowa.
"Ka saurareni dakyau"yace dani "na baka nan da kwanaki goma sha hu'du (sati biyu)ka tabbatar wa da duniya cewa matar da ka gani itace matata da aka kashe"
"Amma taya?"Nace dashi
"Kai ka sani,ni dai burina kenan. Idan kuwa ba haka ba rayuwarka tana cikin garari domin baka da bambanci da gawa"yace dani sannan ya umarceni dana fito waje a hankali har zuwa farfajiyar gidan. Anan ya kira maigadin gidan ya rakani waje.
.
Washe gari a hanyata ta dawowa gida zuciyata taci gaba da sake-saken da nasan ba fiddani zasuyi ba,babu ta yadda za'ai na tabbar wa da duniya cewa Jamila Abubakar itace Fatima Jaheed domin kuwa ko ni kaina nasan ba hakan bane. Sai dai har yanzu akwai wani abu da nake ji a jikina dake nusar dani hakan mai yiwuwa ne,babu shakka akwai wani abu 'boyayye game da Jamila Abubakar amma zuciyata ta gaza gano menene. Tunanin gano 'boyayyen al'amarinne ya fara zarya a 'kwa'kwalwata amma na rasa ta inda zan fara,"hava sai kace ba 'dan jarida ba"zuciyata tace dani. Tunanin wasu kyaututtuka da aka baiwa wasu 'yan jaridu shekarar da ta wuce saboda 'kwazonsu ne ya fa'do zuciyata,a waccan lokacin ina daga gefe ina kallon yadda ake kiran sunansu 'daya bayan 'daya ana dan'ka musu kyaututtukan. "Babu shakka zan jarraba ko dan NEMAN SUNA da kafa tarihi a duniyar binceke"da irin wa'dannan sa'ke-sa'ken na iso gida KANO.TSEGUMI-04
.

BAMAI DABUWA
.
Da misalin sha biyun rana na isa gida (12:00am),sai a sannan na lura da matsananciyar yunwar da ke damuna,kasancewar rabona da abinci tun yammacin jiya. Kitchen na fara wucewa anan na ha'da shayi da madara na kurba kafin daga bisani na wuce office cike da fargabar abin da zai biyo baya idan na sanar da maigida abinda ya faru dani. Kai tsaye ofishinnamu na fara shiga
"Kai! Haidar me ya faru dakai,sai kace wanda ya shafe shekaru ba bacci"abokin aikina yace dani a lokacinda na shigo
"Hmm abubuwa dayawa sun faru"nace dashi a lokacinda nake 'ko'karin zama a kujerata kana 'dora da cewa "ina cikin ru'du da tashin hankali"na sanar dashi duk abubuwan da suka faru dani
'Kuramin ido kawai yayi sannan ya fara magana "amma ya zakayi,kasan fa Maigida bayason gardama gashi kuma ka bijire umarninsa"
"Na sani shi yasa ma nazo da shirina domin nasan bazai barni ba,amma dai sai na fa'damar duk abubuwanda suka faru"
"Me kuma kake 'ko'karin yi gameda barazanar da Jaheed Auwal yama,kasan fa masu kudinnan suna da damar yin duk yadda suka so a 'kasarnan"
"Hakane,kamar yadda na fa'adama babu wata hanya da wannan matar zata kasance matarsa kamar yadda yake so nayi saboda ba ita 'din bace. Amma dai akwai wani 'boyayyen al'amari game da ita. Gameda barazanarsa kuma,akwai hanyoyi biyu da na samarwa kaina. Na farko shine zanyi 'ko'karin neman mutane da zasu taimakamin su ro'kamin afuwarsa,ko kuma dai nasan yadda zanyi na bar 'kasar gabaki 'daya".
"Amma baka tunanin yanzu haka yasa yaransa suna kula da duk wani motsinka?"
"Komai zai iya kasancewa kam"nace dashi a lokacinda na mi'ke tsaye."Bari naje naga maigida (Ibrahim Atiku)".
Waya yake lokacinda na shiga ofishinnasa,saidai hakan bai hanashi zubamin na mujiya ba lokacin da shigo
"Haidar me ya faru dakai"yace dani bayan ya ajiyae wayar
Ban tsaya wata-wata ba nan shima na kwashe labarin abinda ya faru dani na fadamar
"Kana nufin kace sai da kaje gidan Jaheed Auwal duk kuwa da cewa na hanaka"
Shiru kawai nayi bance dashi 'kala ba,hakanne ta sa yaci gaba "ka jefa kanka a matsala Haidar,sai dai ina so ka sani nima bazan iya ci gaba da zama dakai ba anan saboda zaka iya jazamin. Alfarma 'daya da zan ma itace idan har ka tabbatar da aikinda ya sa kan cikin kwanakin da ya 'kayyade to zaka iya dawowa kaci gaba da aiki,amma yanzu kam na koreka"
.
Na fusata ainun da kalamansa domin dai bai min adalci ba musamman idan yayi la'akari da cewa na fa'da wannan 'kangin ne sanadiyyyar 'daga sunan ma'aikatar
"Amma idan akamin haka ba a min adalci ba"
"Haka kace? To tunda kana ganin ba'a ma adalci ba me zai hana kaje ka tabbatarwa da duniya cewa Jamila Abubakar itace Fatima Jaheed sai ka buga jaridar 'kar'kashin ikonka na tabbata wannan labarin zai 'daukaka tattalin arzi'kinka,har ka kafa taka ma'aikatar"
"Amma ku'din sallamata fa"
"Wanne sallama kuma,ka tunamin ma. Duk wasu abubuwa da kasan ma'aikatar nan ce ta baka to ka dawo dasu,sannan gameda motarka kuma za'a dawo maka da ku'da'denka da aka yanka,itama zaka ajiye mana ita.
"Ban ta'ba zaton zakamin haka ba Maigida"
"Zan iya ma fiye da haka ma Haidar,sannan ina so in sanar dakai cewa ko da Jaheed Auwal zai zo nan nemanka zamu fa'damar bamu ma sanka ba"
Da wannan na fice daga office 'din cike da takaici izuwa office 'dinmu.
"Ibrahim ina so zakamin wani taimako don Allah"nace dashi a lokacinda nake tattara kayayyaki na
"Kamar name fa?"
"So nake ka buga tattaunawar da mukayi da Jamila Abubakar a jaridar da zaka fitar na wannan makon"
"Insha Allah ba matsala,sannan ka 'dauki abubuwan da suka faru a matsayin 'kaddara insha Allah,Allah zai fidda kai"
"Babu komai Insha Allah zanyi 'ko'kari. Nagode"nace da shi,kana na fito daga office 'din kaina a sunkuye kamar wani mai nazarin 'kasa.
A gida cikin 'dakina tunanin abinda ya kamata na farane ya ziyarci kaina. "Gaskiya aikinnan da zanyi yana bukatar kudi nace a raina,hakanne ta sani fita izuwa banki domin duba ragowar kud'ad'en da suka ragemi a account 'dina. Duka-duka naira dubu ashirin ne sukai saura,sai a sannan na lura da wautata na yin facaka da kisan kwaf 'daya da nake wa kud'i a duk lokacinda na samesu. "Babu shakka ina bu'katar 'kudi ko dan tserewa na bar 'kasar a lokacinda naga ba haza". A hanyata ta dawowa daga bankin ina nazarin inda zan samu 'kud'I ko da aro ne domin fara bincike amma na rasa,sai daga baya na tuno da budurwata AISHA BELLO kasancewarta ma'aikaciya. Ko kad'an na'ki jinin kar'bar kud'I daga wajen mace musamman ma budurwa domin ina ganin hakan kwafsi ne da zubdawa kai kima,shi yasama kawai na yanke 'kudurin fara aikin da abinda ya ragemin kafin su 'kare . . .TSEGUMI-05
.

BAMAI DABUWA
.
BUSUKU shine 'kauyen da ya kamata na fara kai ziyara domin nanne garinda Jamila Abubakar tace dani shine garinsu a tattaunawar da mukayi da ita a can jahar Jigawa,kirikasamma local Government. A gaggauce bayan na had'a kayana a jaka ina shirin tafiya naga dacewar sanar da Maryam gameda tafiyartawa saboda kada taga shiru kwana biyu,wayata na 'dauko na mammatsa lambobinta kasancewar tuni na haddacesu a kaina sannan na karata a kunnena ina jiran ta sadani da ita
"Hello"ta amsa
"Maryam"
"Sweetheart yau ba baby 'din da ka saba kirana dashi ma,kodai nai maka laifine?"
"Sorry,wallahi kan nawane sai a slow,yanzu hakama na bugone na sanar dake tafiya ta kamani zuwa Jigawa domin 'daukar wasu rohoto. Saboda kar kiga shiru kwana biyu.
"Amma yaushe zaka dawo"
"Inajin bazan wuce kwana biyu ba gaskiya"
"To!Allah ya kiyaye ya kuma dawomin dakai lafiya"
"Ameen"nace kana na kashe wayar.
Har na fito daga gidan na tuna dacewa ashe ina da tsohon I. D card 'dina wanda ya 'bata kwanaki,ban ganshi ba sai bayan na kar'bi sabo a office wanda yanzu haka yana hannun Alh. Jaheed Auwal. Bayan na 'dauka ne naci gaba da tafiya zuwa tashar 'yankaba anan na iske mota mai zuwa Hadejia ta kusan cika mutum 'daya ake jira lokacinda na isa. Bamu isa ba sai misalin 'karfe hud'u da rabi na yamma. Wani 'dan acaba na samu nake tambayarsa "Malan dan Allah tambaya nake"
"Allah yasa na sani"
"Wani 'kauye nake tamabya Busuku"
"Busuku,kai! Amma a wanne local government 'din aka ce ma garin yake"
"Kirikasamma"
"Gaskiya ban san garin ba,amma sai dai ko idan kaje can kirikasamman ba zaka rasa wanda yasan garin ba"
"To kai ni man tashar da zata kaini kirikasamman"
Bayan ya saukeni na sallameshi,na zauna zaman jiran mota ta cika. Na jima a zaune ina jira ta cikan amma shiru babu alamar mutane masu zuwa garin. "Direba ya kamata mu tafi,dare yana gabato mu fa"nace dashi a lokacinda na kasa jure jiran
"Mu tafi ina,ai sai motannan ta cika kafin mu barnan. Idan kuma kana saurine zaka iya 'daukata shata"
"Kamar ya shata"
"Ina nufin ka biya ku'din sauran kujerun da ba fasinja"
Dolena na hakura na koma na zauna zaman jira har na tsawon wasu lokuta sannan mutum uku suka zo,saura mutum 'daya. Ba a jima ba 'dayan shima yazo,anan mukashishshiga bayan sun karbi 'ku'da'denmu muka fara tafiya.
Mintuna ashirin da fara tafiyarmu muka iso garin,a bakin titin garin na had'u da wasu 'yan mata guda uku 'daya tana tallan pure water,dayar kuma goro ne a kanta a yayinda 'dayar ke 'dauke da tire cike da rogo. Matsawa nayi kusa dasu bayan na musu sallama"'yan mata sannunku"
"Yauwa"suka amsa a tare
"Dan Allah tambaya nake"
"Allah yasa mun sani"
"Wani 'kauye Busuku nake tambaya"
"Eh mun sanshi amma 'kauye ne mota bata zuwa sai dai a babur"
"Nagode"nace dasu a lokacinda na 'dagawa wani 'dan acaba a hannu,ya iso gareni "nawa zan baka ka kaini Busuku yanzu"
Ka kawo 'dari hudu maigida"
"A'a zan baka jaka dai"
Dakyar muka daidaita a dari uku. Har cikin garin ya saukenibakin wani shago na 'kasa,sai dai lokacin ana kiran sallar Isha'I. Anan nima nayi alwala na rama sallolin da banyi ba a masallaci kusa da shagon. Sannan na fito daga masallacin na isa wajen mai shagon "Mal barka dai,don Allah ni ba'ko ne ina neman inda za'a taimakamin na kwanta zuwa gobe"
"Allah sarki! Insha Allah ba matsala zaka samu" yace dani
"Yauwa nagode"
"Babu komai. Akwai 'dakina ni ka'dai ne a ciki ya ishemu"
»». »». »»
Washe gari na nemi yamin iso wajen dagacin garin don ganawa dashi. Bayan munje ne na gabatar da akaina a matsayin ma'akacin kamfanin sadarwa na MTN. Sannan nazo ne neman wata Jamila Abubakar domin 'danka mata hakkinta na tallar kamfaninmu da tayi.
"Kai!Gaskiya a kaf garinnan babu wata mai irin wannan sunan"dagacin yace dani. Jotter na 'dauko wacce na rubuta tattaunawarmu da ita,sai a sannan na lura da cewa Abubakar 'din sunan mijintane da ya rasu. Amma ainahin sunanta Jamila Abdullahi Adamri kamar yadda ta fadamin.
"Jamila Abdullahi Adamri nake nufi"nace da dagacin
"Adamri?"
"Eh"
"Tabbas akwai Adamri a garinnan sai dai ya rasu"
"Amma bashi da 'da?"
"'dansa 'daya ne sunansa Auduwa"
"Ko zan iya samun sa?"
"Ai ya jima rabonsa da garinnan,tun wani sa'bani da suka samu da mahaifinnasa ya fita ya bar garin bai sake dawowa ba har yanzu shekaru talatin kenan".
"Yanzu duk wannan tafiyar da wahalar da na sha nayi ta yita a banza kenan"nace a raina lokacinda muka dawo gida daga wajen dagacin. Jotter na 'dauko na sake dubawa a karo na biyu ina nazarinta,sai a sannan na lura da sunan garin mijinta da ta fadamin a tattaunawarmu. "Dole tunda ban samu yadda nake so ba anan,naje can kila na dace da wani abu.
Washe gari da misalin karfe 09:00am na isa kakori garinsu Abubakar dake jahar yobe bayan doguwar tafiya cikin kwale-kwale. Anan bayan na sau'ka a jirgin na ha'du da wata mata mai 'dan jiki ka'dan,kallo 'daya zaka mata ka tabbatar da cewa ba bahaushiya bace saboda irin yadda aka tsatstsaga mata fuska wato 11 11. Matsawa nayi kusa da ita muka gaisa sannan nake tambayarta ko ta san wani Abubakar Garba.
"Eh nasan gidansu dai"tace dani,anan tamin kwatancen gida na kama hanya har kofar. A daidai kofar gidanne na ha'du da wani tsoho yana fi'ke 'kaho a jikin wani dutse dake 'kofar gidan. Kai tsaye na tunkareshi muka gaisa sannan na tambayeshi ko yasan Abubakar Garba. Sai da ya 'karemin kallo sannan yace dani "akan me kake nemansa" anan shima na 'kir'kiri wata 'karyar na kifar dashi. Gamsuwar da yayi da 'karyar da na shirgamar ce tasa ya bani damar na biyoshi izuwa cikin gidannasa domin tattaunawa.
Da'alama shi ka'daine a gidan domin dai har ya shigar dani ciki banga kowa ba, a cikin 'dakinsa muka zauna sannan ya fara magana "tabbas na san Abubakar Garba hasalima nine mahaifinsa, a lokacinda Abubakar yake tare dani na sha fama dashi akan 'kwace da cin zalin mutanen garinnan da yake. Ko ka'dan halinsa ba mai kyau bane,nayi 'ko'karin ganar dashi amma Allah bai nufa ba. Ya jawomin abubuwan kunya da dama a wannan 'kauyen namu,wannan dalilinne ta sani na tsine mar sannan na koreshi daga gidana"cike da 'bacin rai yakemin wannan batun
"Wato baba sau tari dama ana samun haka,sai kaga yaro ya taso da wasu munanan 'dabi'u amma cikin ikon Allah sai ya shiryeshi,da ace kaga irin matar da 'danka ya aura tabbas zakayi mamaki. Saboda babu ta yadda za'ayi mai hali irin wannan ya samu mallakar mace mai hankali,nutsuwada kyau irin ta ba. Don haka kada kayi mamaki idan nace ma 'danka ya canja daga halayensa munana da ka sanshi dasu da. Yaanzu tambayar da zan ma shine yaushe rabonka da Abubakar?"
"Rabona dashi tun shekaru shida da suka wuce,naji labarin yaje wajen 'dan uwansa babban 'dana dake kano. Nan shima na aika masa da ya koreshi a gunsa"
"Ko zaka iya fa'damin adireshin babban 'dannaka?"
"Eh". Anan ya fa'damin ni kuma na rubuta a jotter. Bayan na masa godiya na mi'ke domin komawa gida (kano).
Ban isa kano ba sai da daddare misalin 'karfe goma sha 'daya (11:00). Naso na 'danyi nazarin abubuwan da ya kamata nayi amma ban samu dama ba sakamakon matsananciyar gajiyar da ke damuna,bisa dole na shiga 'daki na kwanta. Ban farka ba sai da gari ya waye rana ta fito,bayan nayi sallah na shiga kitchen domin kimtsa kaina sannan na wuce ban'daki watsa ruwa. Bayan na gama shiryawane na fito domin zuwa gidan yayan Abubakar kamar yadda tsohon ya kwatantamin. Ban sha wahala ba wajen samun gidan,sai dai banyi sa'ar samun maigidan ba sai matarsa kawai na iske. "Sunana Haidar Ali,ni 'dan Jarida ne daga Mikiya"nace da ita a lokacinda nake nuna mata I.D card 'dina
"Lafiya?"
"Lafiya kawai inason ganawa da maigidanne akan matar kaninsa Jamila Abubakar"
"Sai kuma gashi maigidan baya nan,kumama ko yana nan banajin zai taimakama domin dai ya jima rabonsa da 'dan'uwannasa sann....."Bata 'karasa zancentaba wata mota ta 'karaso izuwa kofar gidan "shikenan ma ga yayannasa yazo"tace dani a lokacinda motar ta tsaya a kofar gidan!
Bayan mun gaisa na sake gabatar da kaina a wajensa,anan yamin iso izuwa cikin gidannasa. "Shekara shida kenan yanzu rabona da shi, waccan lokacinda yazo hannu bibbiyu na kar'beshi ina tunanin ko zai canja halayensa. Nayi 'ko'karin sama masa aiki a wani kamafanin da abokina ke aiki a matsayin masinja,amma munanan halayensa yasa suka koreshi. Nima da naga ba mai canjawa bane na sallameshi kamar yadda mahaifinmu ya umarcen. Amma nayi mamakin yadda kace ya canja har da matarsa"yace dani bayan mun zauna a 'dan madaidaicin falonnasae
"Hakane kasan komai mai iya canjawa ne,a wanne kamfani ne kace ka sama masa aiki?"
"Kamfanin takalma ne anan Jogana"
"Kace kuma shekaru shida da suka wuce ko?"
"Eh"
"Ko abokinnaka daya 'daukeshi aiki har yanzu yana aiki a kamfanin?"
"A'a baya nan"
"Nagode,insha Allah zanyi 'ko'kari naga na sameshi domin ha'duwa da matar"nace dashi a lokacinda na mike tsaye ina 'ko'karin fita.
Kai tsaye kamfani takalmin na wuce..
Sai kuma da daddare!!!
TSEGUMI-06
.
Daga alƙalamin

BAMAI DABUWA
.
Isata daidai mashigar kamfanin na had'u da wani mutum cikin Uniform an rubuta security (maigadi). Bayan na masa sallama muka gaisa,nake tambayarsa "Mal. Don Allah tambaya nake"
"To Allah yasa na sani"
"Ina tambayar wanine Abubakar Garba,ya ta'ba aiki anan shekaru shida da suka wuce"
"Shekaru shida kace?"
"Eh"
"Kuma kazo nemansa nan"
"Eh nasan yanzu haka baya tare daku,ina nufin ko zan had'u da wani wanda ya sanshi"
"Gaskiya banajin akwai"
"Amma ai kuna da record book da kuke rubuta sunaye da adreshin masu kaiwa ma'aikatanku ziyara kafin su shiga"
"Eh muna dashi"
"To don Allah ko za'a bincikamin irin mutanen da ke zuwa masa ko Allah zaisa na samesu su sadani dashi"
"Gaskiya bazai yiwu ba saboda aiki nake"
"Kar ka damu nace dashi a lokacin da na zaro naira dari biyar na dam'ka masa a hannu"
"To shikenan ba matsala,amma ka dawo bayan Azahar zan bincika ma"
Da misalin 'karfe biyu na koma,ina zuwa ya taryeni hannunsa ri'ke da takarda. 'Damka min takardar yayi sannan ya juya a saye da alama baya so wani ya gani.Ina 'ko'karin bud'a takardar ya juyo yace dani "kaje can wani wurin sai ka duba". Da na tabbatar nayi nisa da wurin na fiddo da takardar na fara dubawa,sunayen mutanene birjik a jiki da adreshinsu.
Tun daga wannan lokacin na fara bin adreshin mutanen dake jikin takardar amma babu 'daya daga cikinsu da nayi sa'ar samu daga ace ya bar unguwar ko kuma kaji ance bamu sanshi ba. Misalin 'karfe biyar da rabi na isa rijiyar lemo daidai 'yan katako,don bibiyar wani mai suna Garba Hadi wanda shima sunansa na jikin takardar. A cikin lungu gidannasa yake,da alama gidan haya ne irin na yaku bayinnan. A daidai 'kofar na tsaya na 'kwan'kwasa,wani shirgegen 'kato ne ya fito daga gidan na tsorata ainun da siffarsa "wanene ke 'kwan'kwasa mana 'kofa"yace dani a fusace yana ta faman huci
"Nine"nace dashi cike da karaya
"Ya akayi to"
"Ina tambayar Garba Hadi ne"
"Lafiya kake nemansa?"
"Eh lafiya,ina so ne zai sadani da abokina wanda na samu labarin abokinsa ne shima kuma yana zuwa gunsa lokacinda yake aiki a kamfanin takalma na Jogana"
"Wanene abokinnaka"
"Abubakar garba"
"Garba Hadi baya gari amma gobe ko jibi zai dawo,sai dai ko ka leko goben idan ya dawo"
"To nagode"nace dashi sannan na dawo gida.
Na jima a zaune ina nazarin mafita,domin dai duk wahalhalun da nasha babu wanda na samu wani abu 'kwa'k'kwara da zai tabbatar da wani abu gameda ita. Hannuna na zura a aljihu na 'dauko takardar ina nazarin sunayen mutanen da ban samu zuwa wajensu ba. A can 'kasa 'karshen shafin farko idona suka hango min da sunanda yayi sanadiyyar katsewar bugun da zuciyata take na 'yan wasu dakikai. "Hadiza Abdullahi Adamri" na maimaita sunan a bakina,wacece kuma haka kodai sunan Abdulllahi Adamrinne yazo daidai dana Jamila Abdullahi Adamri? Ko kuma dai itama danginsu 'daya da Jamilar? Na tambayi kaina. "Amma kuma ai ita jamilar ta fadamin cewa bata da kowa,ita kadaice gun iyayenta. Hasalima tana da shekara goma sha biyar iyayenta suka rasu lokacin tana aji biyar na secondry. Wata makociyarsu ce ta riketa har ta gama kafin ta gudu ta barta saboda tsangwamarta da take kamar yadda ta fadamin a tattaunawarmu,amma itama tace min sun had'u da tsohon mijinnata shekaru shida da suka wuce itama kuma wannan ta had'u dashi shekaru shida da suka wuce. Wai yaya abin yake?"Na tambayi kaina.
.
Washe gari da misalin shida na yamma na koma neman Garba Hadi. "Wanene"aka ce dani daga ciki
"Nine wanda yazo neman Garba Hadi jiya"
Su biyu suka fito wannan karon shi da wani gajere "kai ne kake neman abubakar Garba"gajeren yace dani yana nazarin yanayina
"Eh nine"
"Amma kai abokinsa ne?
"Eh abokinsa ne ni,ban jima da dawowa daga America ba"na shirga masa 'karya
"Amma taya akai kasan na sanshi?"
"Acan kamfanin da yayi aiki aka kwatanta min wajenka,sunce kana zuwa gunsa"
"Hakane,amma gaskiya yanzu rabona dashi shekaru hudu kenan ban sake ganinsa ba. Tun wani sa'bani da muka samu dashi akan wata budurwarsa,saboda irin yadda take jefa rayuwarsa cikin garari domin biyan bukatarta yasa na bashi shawarar ya rabu da ita amma ya'ki. Tun daga nan muka raba gari"
"Ya sunan budurwar tasa kuwa"
"Sunanta Hadiza"
"Zaka iya ganeta idan kaga hotonta?"
"Sosai ma"
"To don Allah gobe zan dawo da hoton saboda yanzu bana tare dashi"
"Babu matsala"
Da alama zan warware rud'un da ke tsakanin Hadiza da Jamila. Tunanin zuwa gidan cinema ne ya fad'omin domin 'debe kewa ko na samu na sassauchi a kaina wanda tuni har na fara sabawa da ciwon da yakemin. Ban dawo gida sai misalin sha 'daya da rabi na dare a nan naga abinda ya matukar tayarmin da hankali. 'Kofar gidannawa na gani a bud'e alhalin ina da tabbacin sai da na kulleta kafin na fita. "Waye a ciki" na fad'a da karfi amma shiru babu wanda ya amsa. Sosai na tsorata,tuni gumi ya fara ji'kamin riga "kodai Jaheed ne ya aiko da yaransa su kashe ni,amma kuma ai kwanakin basu cika ba. A hanakali na 'karasa bakin 'kofar cikin sand'a na shiga cikin gidan . . .TSEGUMI-07
.
Daga alƙalamin

BAMAI DABUWA
.
Sai da na fara kunna wuta sannane tsorona ya dad'u saboda ganin irin yadda aka birkita komai na gidan. "Da alama 'barayi ne" nace a raina,nan na fara binciken abubuwan da aka 'dauka amma ga mamakina basu 'dauki wani abu mai muhimmanci ba idan banda rediyo ta tajin labarai sai dubu na 'daya dana ajiye cikin dirowa. Tunanin hotonne ya fadomin aguje na wuce 'dakina dubawa,'dakin ma an birkita. A 'kasa na tarar da littafin da na ajiye hoton amma ga mamakina sai banga hoton a ciki ba. Sai da na bincika ko ina na 'dakin amma banga alamar hoton ba. "To ko hotonma 'barayin sun 'dauka?Wanne amfani to zai musu idan suka dauka?
Nayi matu'kar ta'kaicin 'batan hoton,dashi ka'dai zan iya bambance tsakanin Hadiza da Jamila. Da ace na kai masa hoton ya tabbatar min da cewa Hadiza ita ce Jamila to da abubuwan zasu zomin da sauki. Sai dai har yanzu ina ji a jikina cewa Jamilar itace Hadiza,amma me yasa ta canja sunanta,tayaya mijinnata ya tara kud'in da zai gina irin wannan katafaren gidan sha'katawar da sauran kadarori a cikin shekaru shida kacal,alhali duk sana'o'insa ba wasu manya bane da zasu kawo masa kud'I. To ko dai safarar miyagun 'kwayoyi yake,da irin wad'annan tunane-tunanen na sake dawowa falo. Tunanin sanar da 'yan sanda abinda ya faru dani ne ya fad'omin,amma nayi fatali da ita kasancewar abubuwanda aka sacen ba wasu abubuwa ne masu tsada ba.
Bayan na zauna a 'daya daga cikin kujerun dakae falon tunanina ya fad'ad'a akan Fatima Jaheed. Ya kamata itama na binciko wani abu game da ita musamman danginta. Sai dai matsalar babu wani cikakken bayani gameda ita ko iyayenta a jaridar mu da ta watsa labarin sacewarta da kasheta da akayi.
Nayi 'ko'karin kai ziyara wasu daga cikin ma'aikatun jaridun dake garin (kano)amma babu 'daya daga cikinsu da na samu wani cikakken bayani gameda Fatima Jaheed ko na iyayenta. Hakanne ta sani yanke shawarar zuwa wajen Garba Hadi (wanda zan kawowa hoto). Bayan mun gaisa nake sanar dashi cewa na samu matsala gameda hotonnan amma zanci gaba da bincikawa idan na samu zan kawo ya dubamin ko ita ce. Sai dai kafinnan ina so zan tambayeshi inda Abubakar yake da zama shi da budurwar tasa Hadiza Abdullahi Adamri. Kai tsaye unguwar da ya kwatanta min na nufa,anan na iske wata mata a daidai layin da ya fad'amin.
"Malama barkanki dai"
"Yauwa"
"Don Allah tambaya nake"
"Allah yasa na sani"
"Ina tambayar wani Abubakar Garba da suka ta'ba zama anan shida wata Hadiza Abdullahi Adamri"
"Eh na sansu,amma sun jima da barin nan"
"Amma kin san ita Hadizan?"
"Eh na santa man,tare suke ai"
"Ko zaki iya kwatanta kamanninta"
"Gaskiya ban iya kwatanta kamannin mutane ba amma dai kyakkyawa ce"
"Fara ce ko ba'ka?"
"Tsaka-tsaki ce gaskiya"tace dani. Ai kuwa jamila ma tsaka-tsakin ce nace a raina
"Tana aiki?"
"Eh tana aiki a wani restaurant"
"To amma da zasu bar unguwarnan ko sun fad'a muku inda zasu koma?"
"A'a babu wanda suka fad'ama hasalima da bashin maigidan hayan suka gudu basu biya ba"
"Amma babu wasu muatane dake kawo musu ziyara?"
"Akwai su sosaima,sai dai bamu damu da sanin ko su wanene ba,saboda ko kad'an bamu saki jiki dasu ba"
Kwatancen restaurant 'dinda tamin na nufa,sai dai a hanya kafin na 'karasa titi nake ji a jikina kamar wani na biye dani. Bayan na waiga ban ga kowa ba naci gaba da tafiya har zuwa titin,anan na hau mota zuwa restaurant din. A cikin motar ne na lura da wata mota peugeot blue,sai dai bazan iya shaida matukin motar ba sakamakon tintin 'dinda ya lullu'be gilasan motar. Lambar motar na sake dubawa DCHA aka rubuta a jikin lambar.
Bayan na sau'ka a daidai wajen,kaina tsaye na isa restauranta 'din. Anan na had'u da wata mata nake tambayarta
"Don Allah ina tambayar wata Hadiza Abdullahi Adamri wacce ta ta'ba aiki anan shekaru shida da suka wuce"
"Wallahi ban jima anan ba nima,sai dai kaje wajen waccan ka tambayeshi zai iya saninta domin ya jima anan. Sunansa Auwal"
"Malam barka dai"
"Yauwa"
"Ina tambayar Hadiza Abdullahi Adamri ne"
"Tab! Hadiza ai ta jima da barin nan"
"Ko kasan wajenda ta koma da ta bar nan?"
"Eh na sani,Al-amir restauranta dake sharad'a phase1 ta koma da aiki"
"Amma me yasa kake nemanta?"Yace dani
"Babu komai kawai muna son biyanta ne akan wani talla na kamfaninmu da tayi"na kifar dashi
"Kamfanin sabulu kake aiki?"Yace dani
"A'a,amma me yasa ka tambaya?"
"Naga sune masu sa hotunan kyawawan 'yan mata,ganin itama kyakkyawar ce yasa na tambaya"
"Hmmm hakane,amma kana da hoton

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment