Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai kubutar dani!!
Shiru kawai nayi na zuba mata ido,lokaci guda naji wani tunani yazo min wanda na tabbata zai kubutar dani,ban jira ba kuwa na fara gabatar da shi kamar haka
"Kin san cewa a bincikena da nakeyi a kanki sai da na gano cewa ke........."Shiru nayi lokaci guda na kauda idona daga nata na 'kurama 'kofar dake bayanta ido. Idanuna na zazzaro cike da firgici kai kace wani dodo na gani wanda ke 'ko'karin kunno kai cikin 'dakin. Dagangan nayi hakan saboda burina ta kauda idonta daga gareni koda kuwa na 'yan sakanni ne,cikin sa'a kuwa ta fad'a tarkona. Juyawa tayi da niyyar duba abinda na gani a bayanta,cikin 'kiftawa kafin ta dawo da dubanta gareni na daka tsalle na fad'a ta tagar da ke kusa dani jikake timmm na fad'a waje. Ai kuwa ban jima da kaiwa 'kasa ta biyoni aguje tana harbi ba 'kak'kautawa. Da gaggawa na mike sannan na fake a jikin lungu na bangon dakin daga waje,bindigata na zaro nima na harba cikin dakin ba tare da sanin wajen da na harba ba.
Gaba 'daya dakinne ya kaure da duhu,ashe dai harbinda nayi ne na samu 'kwan lantarkin da ke ci a dakin. Karar takun sawunta naji alamar tana fitowa hakan tasa na arce a na kare,kwane-kwane na ringa yi a yayinda nake gudun daga wannan sashe zuwa wannan. Ganain haka yasa itama ta ringa aikomin da sakon harsashi kowanne bangare ba 'ka'k'kautawa. Banyi nisa ba cikin gudun da nakeyi naji saukar harsashi a kafata,hakan tasa na saki wani uban gunji mai 'karfi na fad'I kasa shame-shame a yayinda ita kuma ta tunkaro ni gadan-gadan.
Tsakaninta dani bai wuce taku hamsin ba najiyo wani sauti daga can nesa ana fadin "waye anan"da alama sautin ta microphone yake fitowa. Ai kuwa bata jira ba ta aika da sakon harbi daidai wajenda muka jiyo sautin muryar,faruwar hakan ke da wuya daga can bangarenma naji sun sako tasu wutar na dan wani lokaci kafin daga bisani a tsagaita. "Su waye kuma wadannan?Ko dai 'yan sanda ne?"Na tambayi kaina. Ni dai ina daga 'kasa kwance cikin jini sai naji dayan na cewa kofur ku 'karaso nan mun harbeshi,jira nake naji sun yanyameni amma ga mamakina sai naga dukansu sun nufi wajen gidan,sai a sannan na hango ta kwance a 'kasa sakamakon haskata da sukayi da fitulunsu masu tsananin haske.
"To amma me wannan mutumin ke harbi tun farko?"Naji dan sandan yace da 'yan uwannasa
"Gaskiya duk yadda akai yana da abokin karan battar"inji dayan
"Mu bincika ko zamu ganshi 'kila shima an kashe shi ko kuma ya buya a wani wajen"
"Gani nan anan"nace dasu da 'karfi a lokacinda naji sun fadi haka sannan na dora "kar ku harbeni,so take ta kasheni"
Shiru ne ya biyo baya,can sai dayansu yayi magana "waye kai,kuma me ke faruwa anan?"
"Sunana Haidar Ali ni dan jarida ne"
"Haidar kaine?"Aka ce dani,naso na shaida mai muryar amma na kasa
"Eh nine"
"Kana ina?"
"Gani nan anan"
"Fito fili mu ganka"
Dakyar cikin jan 'kafa na taso daga inda nake kwance,amma kafinnan sai da na boye bindigata a 'kuguna.
"Haidar me kakeyi anan?"
Daga kaina nayi na kalli mai tambayar tawa sai a sannan na ganeshi,abokinnannawa ne da ya aramin finger print gadget
"Ta mutu ne?"Nace dashi
"Wacece?"
"Matar dake kwance a 'kasa"
"Ai ba mace bace Haidar ko baka ga gemu ba a fuskarsa?"
"Ba namiji bane macece badda bami ne wannan gemun da kake gani"nace dasu
Sai da suka matsa har kusa da ita sannan suka fisge gemun da ta saka sannan suka tabbatar da abinda na fadamusu.
"Taya akai kuka san muna nan?"
"Mun dawo daga operation ne sai muka ga mota a gefen titi ganin haka yasa muka tsaya bincikawa sai kuma muka jiyo 'karar bindiga".
<<<<<<<<<<
Washe gari dana farka sai na tsinci kaina kwance a gadon asibiti gefena nurse ce a zaune.
"An ciremin harsashin?"
"A'a amma yanzu za'a cire ka huta tukun"
Bayan kamar awa guda da ciremin harsashin budurwata A'isha da abokin aikina Ibrahim suka shigo dakin da aka kwantar ni
"Ya jikin naka?"Tace dani
"Da sauki"
"Yanzu abokina sai da binciko wannan lamarin?"
Murmushi kawai namar bance 'kala ba sai a sannan na tuna wani abu yau ne daidai ya cika kwanaki goma sha hudun da Jaheed ya yanke min. Ina cikin wannan tunani kuma sai ga maigidanmu Ibrahim Atiku ya shigo shima yana ta washe baki
Cikin isa da gadara na dubeshi nace "Atiku so nake ka samomin lambar da zata sadani da Jaheed yanzu" "Ba damuwa"yace dani sannan ya fita.
.
KARSHEN TSEGUMIN KENAN.
.
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
.
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA DAYANSA TUN DAGA SHAFIN FARKO ZUWA NA KARSHEN GA KATAFANIN AL'UMMAR DAKE CIKIN WANNAN ZAURE NA.
"TASKAR GIDAN LITTAFI"
.

.
Mun jinjinawa
YARIMA A GANGARIYA Wanda shi ya bani COPY na wannan littafi kuma bisa taimakonshi wanga labari yazo ƙarshe Allah kuma ya saka masa da alkhairi
.
NI KUMA
SADEEQ SHEHU SHARIFF
( JARMAN TASKA )
Wanda na kawo muku wannan littafi nake muku fatan alkhairi game da addu'ar Allah ya sake sadamu a wani sabon littafin.
.
HAR KULLUM
MARUBUCIN LITTAFIN
TSEGUMI shine 👇
(BAMAI A. DABUWA KKM)
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment