Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san danginsu ba. Nayi 'ko'karin jure munanan halayen Hadiza lokacin da muke tare amma dare 'daya na wayi gari na nemesu na rasa har yau ta gudu da 'yar uwaratata."
"Amma dai Zainab bata kyauta ba gaskiya,duk irin kyautatwar da kike musu sai da gudu da 'yar uwartata"
"Ba Zainab ce ta gudu da Hadiza ba,Hadizan ce ta gudu da Zainab duk da kasancewar Zainab d'in ce babba amma tanayin duk abinda Hadizan ta sata. Ko kad'an halayen Hadiza ba masu kyau bane idan ka 'dauke sha'awarta na shuke-shuke. Tana matukar son aikin gona tasha fad'amin idan tayi 'kud'I zata gina gidan gona (lambu). Amma ita 'Abu' ba ruwanta bata damu da komai ba"
"Wacece kuma Abu?"
"Zainab kenan,inkiyar tace"
"Amma Hadiza ma tana da wani sunan?"
"Eh 'Mangu'shine iyayenta ke kiranta dashi"
"Kina da hotonsu?"
"Eh akwai hoton da muka d'auka dasu bari na 'dauko ma"
"To"nace da ita lokacinda ta shige cikin d'aki. Bayan kamar minti goma sha biyar ta dawo
"Wallahi kaga na rasa wajenda na saka hoton,amma dai tabbas yana nan me zai hana ka dawo gobe kafinnan na duba ma."
Tunanin abubuwan da suka faru da Auwal ne ya fad'omin sanadiyyar hoton shi yasani mata 'karyar ni ba dan garin bane yau nake son komawa Kaduna
"Me zai hana na tayaki dubawa ko zamu ganshi"
"Kawai ka bari duk sanda ka dawo garin wataran na nuna ma"
"To kawai zan jira goben na dawo"
"To Allah ya kaimu"
Ina 'ko'karin fita ne na tuna wata tambaya "Hajiya shin Zainab da Hadiza kuwa na kama da juna?"
"Ai kamarsu ta wuce yadda kake zato!basu da wani bambanci"
A mota wani tunani ya fad'omin Duk yadda akayi Jamila tana da dangata da 'yan biyun nan,kodai Zainab ce ta canja sunanta zuwa Jamilar? Amma kuma ai ance ita Zainab ba mai fad'a bace sabanin Jamila wacce ta nuna tsabar fushinta don kawai na dauketa a hoto,to idan ma itace me yasa zata canja sunanta? Yanzu a 'dauka Fatima Jaheed itace Hadiza to wacece Zainab kuma tana ina?
jinjina ga marubucin wannan littafi
.
Washe gari bayan na kimtsa da misalin 'karfe goma na nufi gidan Hajiya Jummai gameda hoton. Wani wari ne ya daki hancina a lokacinda na isa kofar gidan,na jima ina buga kofar amma ba'a bude ba hakanne ya sani mur'da mabudin kofar. A ciki ne na kasa jure warinda ke shiga hancina dole tasa na dauko hankici na toshe hancina. Kirjina ne ke bugawa ina ta zulumin kar fa itama an kasheta amma ban ga gawarta a falon ba. Dakinta na nufa kai tsaye na shiga anan na iske ta kwance shame-shame a 'kasa babu sauran rai a jikinta. Tausayinta ne ya kamani sannan naji na tsani Jaheed Auwal a zuciyata fiye da komai saboda nafi zarginsa akan kisan.
Naso naci gaba da bincike amma tunanin Hajiya jummai da kuma mutumin da ke bibiyata ya hanani babu shakka nima zai yi yun'kurin kasheni a duk lokacinda ya samu dama. Ya kamata nima na ri'ki wani abu da zan kare kaina saboda gudun 'bacin rana. Gidansu abokina na wuce wanda babansa babba ne a sojojin 'kasar nan,nasha wahala sosai sannan na jima ina shirga masa 'karya kafin daga bisani ya yarda ya bani aron bindigarsa. Bayan na karbi bindigar ne na wuce police station wajen wani abokina da mukayi makaranta d'aya dashi anan shima ya shigemin gaba aka aramin Finger prints gadget.
Tunanin ta inda zan fara bincike akan Zainab Abdullahi Adamri ne ya fad'omin amma na rasa ta inda zan fara hakan tasani watsar da lamarinta izuwa kan Abubakar Garba ( wanda yace ma abokinsa ya koma Khairat Night Club da aiki,dayaje kuma aka ce babu wani Abubakar dake aiki agun) me yasa akace masa baya aiki agun alhalin shine mamallakin gidan,ko dai shine yasa ace mar hakan don baya son ganinsa? Dole sai na koma Khairat Night Club anjima.
Kofin takardar Hadiza Abdullahi Adamri dana karbo a ministry na dauko nake dubawa,anan naga adreshin 'dinda take zaune (contact adress)lokacin da take aiki. A unguwar karkasara gidan yake ba mamaki tare suka zauna da 'yar uwaratata acan. Ban 'bata wani lokaci ba na isa unguwar anan nake tambayar wani mai shayi
"Malam don Allah ina tambayar wasu 'yan mata 'yan biyu ne?"
"Gaskiya babu wasu 'yan biyu a unguwarnan"
"Ina nufin sun ta'ba zama anan"
"Kai Gaskiya ban sansu ba,amma ka tambayi waccan inyamurar ta jima anan zata iya saninsu"
Bayan mun gaisa da ita a lokacinda na 'karasa shagonnata nake tambayarta
"Madam ina tambayar wasu twins sisters ('yan biyu) da suka ta'ba zama anan ko kin san su?"
"Sun juma da beri nan"
"Ko kinsan inda suka koma?"
"Ben seni ba"
"Amma kinsan wajenda suke aiki kafin su bar nan?"
"Eh daya yana aiki a Ministry ne dayan kuma yana aiki a wani gida nan kusa"
"Wanne gida kenan?"
"Wani ferin gidane mai lamba arba'in a wannan layin"
"Ya sunan megidann da take aikin?"
"Ben seni ba"
"Nagode madam"nace da ita sannan na nufi gidan da ta kwatantamin. Wani saurayi na iske a 'kofar.
"Malan don Allah ina tambayar wata Zainab ance ta taba aiki a gidannan"
"Ba 'dan gidan bane ni gaskiya sai dai ko na maka iso ciki. Bayan ya sanar da masu gidan aka ce na shiga,a ciki na iske wata gabjejiyar mata.
"Zainab nake tambaya ance ta ta'ba aiki anan"
"Wannan karuwar da ta kusan 'kwacemin miji shegiya, au yi ha'kuri ban san 'yar uwarka bace"
"Babu komai ba 'yar uwata bace,ni d'an jarida ne muna neman wasu bayanai ne dai gameda ita"
"To karuwace"tace dani tana zazzare idanu
"Ina zaman-zamana tsautsayi yasa na 'dauketa aiki ashe shegiyar miji zata 'kwacen. Wani lokaci mijina ya samu hutu a wajen aiki,yarinyar nan ba sai ta fara canja shiga ba ta fara saka wasu matsatststun kaya masu bayyana sirrin jikinta kuma gata kyakkyawa. Kasan ya takeyi idan ta saka irin wad'annan kayan?"
"A'a"
"Sai ta daidaici mijina yana 'daki kawai sai ta shiga wai tazo shara ko goge-goge"
"Kai!"
"Allah kuwa"
"Lalle shigiyace"
"Hmm ai bazan ta'ba mantawa da ita ba,sa'ar da nayi mijinnawa mai tsoron Allah ne shine yake fad'amin abubuwan da take mar na jan hankali sai na d'ana mata tarko nace mata zanyi bulaguro bayan kamar na tafi sai na dawo a 'boye na shige dakin mijinawa. Muna zaune ni da shi sai mukaji an 'kwan'kwasa 'kofa kafin ni ko shi ya amsa ta bud'e ta shigo kai kaga shigar da tayi kuwa? Hmm daganan na koreta ta bar gidan"
"Kin sake jin labarinta kuwa bayan kin koreta?"
"Eh lokacin bata jima da barin gidana ba ta samu aiki a wani restaurant nesa damu,anan ma aka kamata suna iskanci da wani ni kuwa da TSEGUMINA sai da naje har wajen na tamabaya aka tabbatar min"
"Anya kuwa itace?"
"Itace man sai da na tambayi sunanta aka cemin Zainab Abdullahi Adamri"
"Kwatantamin restaurant din man"
"To amma don Allah ka buga duk abubuwannan dana fadama gameda ita kaji"
"Babu damuwa zan buga"nace da ita bayan tamin kwatancen restaurant d'in
A nan ma da naje babu wani bayani dana samu gameda ita ko wajen da ta koma da aiki sai akan halayyarta na bin maza da take. To amma me yasa a bayanin da Hajiya Jummai tamin tace yarinyar mai hankali ce sa'banin Hadiza? Ko dan a lokacin tana 'karama ne? Ko dai Jamila itace Zainab? Babu shakka zata iya canja sunanta ko dan wannan halinnata da kowa ya sanshi . . .TSEGUMI-12
.
Daga alƙalamin

BAMAI DABUWA
.
Tunanin bincika gidajen karuwai dake garin (kano) ne ya zomin ko zan dace na sameta. Ni kaina nasan ban isa na gama gewaye gidajen karuwan da ke fadin garin ba ko da tsawon shekara zan shafe inayi amma duk da haka ban karaya ba na fara bi daga nan zuwa can amma ban dace ba. Na zaga gidajen karuwai a 'kalla sama da 'dari biyu sai a wanine na samu wata nake tambayarta.
"Kinga tambayarki kawai zanyi sannan na biyaki ba wani abu ne ya kawo ni ba"
"Tambaya?"
"Eh"
"To ina jinka"
"Wata yarinya Zainab Abdullahi Adamri nake tambaya ko kin santa?"
"Zainab ta bar nan"
"Kika ce me?"
"Nace ta bar nan"
"Kin santa?"
"Eh sosai ma"
"Ya kuke da ita?"
"'Kawata ce"
"Kenan bazaki rasa hotonta ba ko?"
"A'a amma dai mun ta'ba dauka sai dai har yanzu bamu karbo ba agun mai hoton"
"Ina wajen hoton?"
"Anan unguwar ne"
"Ya sunan wajen"
"Al'ameen professional photos"
"Amma kinsan inda ta koma"
"A'a"
"Kika ce 'kawarki ce?"
"Eh,lokacinda ta tafi bana nan da na dawo ban ganta ba nake tambayar 'kawayena suka cemin ai wata tazo ta tafi da ita. Sun ce suna matu'kar kama da juna 'kila ko 'yar uwarta ce"
"Tun yaushe ne hakan ya faru?"
"Shekaru uku kenan yanzu"
Bayan na sallameta na koma mota. Na 'dan 'dauki lokaci ina zazzagawa kafin daga bisani naga shagon mai hoton amma a rufe. Washe gari da safe na koma shagon wannan karon a bud'e na samehi,kutsa kaina nayi ciki
"Malam barka da aiki"nace da saurayin da na iske a shagon
"Yauwa,sannu da zuwa"
"Akwai wata yarinya da ta'ba daukar hoto anan"
"Wacce yarinya fa?"
"Sunanta Zainab Abdullahi Adamri"
"Zainab ? Kai na mantata gaskiya"
"Karuwa ce anan kusa da ku take ta jima da 'daukan hoton"
"Ok ! Na tuna kuma"
"Hotunan da ka 'dauketa nake so zan siya"
"Hhhh ai ta had'u yarinyar bari na 'dubosu"yace dani yana dariya a lokacinda ya shiga wani daki. Bayan wasu 'yan dakikai ya dawo rike da hotunan a hannu
"Yauwa gasu ko,sai ka zaba"
Basu da wani bambanci da Fatima Jaheed haka Jamila ma. Yanzu kam na fara warware abubuwan amma matsalar wajenda zan had'u da Zainab 'din. Ko dai Jamilar ce ta canja sunanta daga Zainab zuwa jamila? Amma kuma banajin Jamilar itace Zainab saboda bambancin halinsu halayenta yafi kama dana Hadiza kamar yadda bincikena ya nuna min. Idan kuma Jamilar itace Zainab a ina ta samu ku'din da zata gina kanta haka sai sannan kuma na tuna ashe fa tace dukiyar mijinta ta gada. Shi kuma a ina ya tara wannan dukiyar? Shima ai bincikena sun nuna matsiyaci ne. Dole shima na zurafafa bincikena a kansa,wannan dalilin ne ya sani ci gaba da ziyartar sauran mutanen da ke jikin takardar da na samo a kamfanin takalma.
"Abubakar abokina ne sai dai mun daina ganin juna tun shekaru uku da suka wuce"wani abokinsa dana kaiwa ziyara yace dani wanda shima sunansa na jikin takardar
"To lokacin a ina yake da zama?"
"A gyadi-gyadi yake"
"Amma me yasa kuka daina ganin juna?"
"Haka kawai na daina ganinsa"
"Nagode"nace dashi sannan na nufi gyadi-gyadi har gidan da ya kwatantamin amma sai na iskeshi a rushe. Wajen wani mai shago na 'karasa kusa da gidan nake tambayarsa
"Malam yaushe ginin nan ya rushe?"
"Yau shekara uku kenan"
"Nagode"nace dashi sannan na koma mota. Har na tayar da ita ina shirin tafiya na tuno da wani abu. Rusasshen ginin na nufa,anan na sunkuya ina binciken abubuwa da ni kaina ban san me nake nema ba sai kace mahaukaci. Wata tsohuwar dirowa na gani bayan na jawo ta kusa dani ne na fara binciken abubuwan da ke ciki. A ciki ne naga wata 'yar 'karamar takarda da rubutu a jikinta kamar haka
Zuwa ga Abubakar
Na rubuto na sanar dakai cewa abubuwa sun daidaita kuma zan so na sani ko ka bincika wannan abun kamar yadda na fadama idan bakayi ba don Allah kayi 'kokari kayi kaga lokaci na 'kuratowa kuma abin nada muhimmanci. Ashirin ga wannan watan zan taho saboda zai fita kasuwanci na 'yan wasu kwanaki. Amma ba zanzo wajenka ba saboda bana so mutane su ganeni mu had'u a can wajen gari hanyar kazaure gaba da bandirawo city. Sai anjima
Daga masoyiyarka
Hadiza.
PLS!!! Kar ka kuskura kace zaka kirani ko kace zaka zo ko ka rubutomin wasika. Ka bari ni zan shirya komai.!!!!
.
Nannad'e takardar nayi na totsata a gaban aljihun rigata sannan naci gaba da bincika sauran takarcen dake rusashshen gidan amma ban samu wani abu mai muhimmanci ba. Hakan ta sani dawowa cikin mota sannan na nufi gida da niyyar hutawa kafin dare yayi na le'ka Khairat Night Club.
Misalin takwas daidai na dare (08:00pm) na kama hanyar Khairat,nesa dani daga baya na hango wasu motoci guda biyu na taxi na biye dani a raina ina tunanin yaran Jaheed ne dake biye dani,wannan karon ban damu da duba lambar motocin ba domin nasan su 'dinma na haya ne. Fakin 'din motar nayi a wajen da aka tanada saboda ajiye motoci a club 'din sannan na shige ciki. Wannan saurayin ne ya sake tarbata wannan karonma.
"Sannu da dawowa yallabai"yace dani
"Yauwa"
"Wannan karon me kake da bukata ko giyar?"
"A'a Maltina nake so"bayan ya kawomin ya juya da niyyar komawa na sake kiransa
"Don Allah inaso zan maka wasu tambayoyi idan bazaka damu ba"
"Ba matsala amma sai dai zuwa anjima misalin sha biyu (12:00pm) kafinnan aiki yayi sau'ki"
"Ba damuwa ina nan har zuwa lokacin"nace dashi. Tashi nayi ina 'dan zazzagawa har wajen matar da min iso wajen Jamila kwanaki.
"Sannunki da aiki"
"Waye kai?"Tace dani a fusace
"Nine 'dan jaridannan na kwanaki da yazo wajen Hajiya!baki ganeni ba?"
"Me kuma kake so yanzu agunta?"Wannan karonma babu annuri a fuskarta
"Dama tambayarta nake so nayi ko taga Jaridar tattaunawar da mukayi"
"Bata nan"
Ganin ban samu fuska ba a wajenta ya sa ni fita daga sashennata,a hanya ne na kusa kici'bis da ita
"Kaine Haidar Ali dan jaridar nan ko?"Tace dani
"Eh nine Hajiya ya aiki?"
"Da godiya,naga jaridar da ka buga"tace dani tana murmusawa cikin wani salo mai kashe zuciya.
"Yauwa dafatan kinji dadinsa?"
"Sosai ma kuwa"
"Yauwa haka nake so naji dama"nace da ita a lokacinda nake 'kare mata kallo daga sama zuwa 'kasa.
"Bari na wuce office"tace dani sannan ta shige.
Sha 'daya da hamsin (11:50pm) matashin ya dawo ya sameni
"Wato akwai abubuwanda nake so na tambayeka"
"Me dame kake son ka sani?"
"Da farko ina so na san wanene Abubakar Garba?"
"Abubakar shine mijin Hajiya amma ya rasu"
"Tun yaushe ya rasu?"
"Ya 'dan jima gaskiya,tun farko-farkon bud'e wannan gidan"
"Amma kasan ta yadda akai ya mutu?"
"Eh to Hajiya tace mana dai wai jirginsu ne ya nutse a ruwa a hanyarsa ta dawowa daga garinsu"
"Amma ya kake ganin sha'kuwarsu da Hajiya kafin ya rasu,sun ta'ba samun sa'bani?"
"Eh to ba sosai ba,amma dai suna zaune lafiya"
"A irin sa'banin da suke samu ko ka ta'bajin wata kalma da suke furtawa?"
"A'a"
"Ka tuna dai"
shiru yayi na 'yan wasu da'ki'kai da alama tunanin yake sannan ya 'dago kansa
"Eh to akwai lokacin da naji Hajiya tana cemasa wai yana kawo tsoffin abokansa. Shi kuma sai yake ce mata shine fa silar samun komai nasu idan ta matsa mar zai fasa 'kwai kowa yaji"
"Ka tabbata kaji haka da kunnenka?"
"Eh na tabbata"
"To amma wanne 'kwai zai fasa?"
"Ban sani ba"
"To me Hajiyan tace daya fad'I hakan?"
"Shiru kawai tayi batace 'kala ba"
"Tun daga wannan ranar daya fadamata haka sun sake samun sa'bani?"
"Basu sake ba,sai dai ko a gida ban sani ba"
"Bayan wannan gidan sha'katawar akwai wani kasuwanci da Hajiyar ke yi?"
"A'a sai dai tana da gidan gona a hanyar Zaria"
"Wajen ina ne?"
"Da ka kama hanyar a bangaren hannunka na hagu zaka ganshi a ciki da wani gida anan Hajiya take hutawa"
Sai a sannan na tuna tattaunawarmu da ita tace tana sha'awar noma. "Yanzu kasan me zakamin?"Nace dashi
"A'a"
"So nake ka sa mata ido ka lura da duk wasu shiga da ficenta,sai kana fadamin ni kuma zan biya ka kullum idan ka samo min wani bayani kaji"
"Ba matsala"
<<<<<
Tayar motata na tarar a sace,sai da na matsa daf da ita na hangi wata zungureriyar 'kusa cake a gefen tayar rabinta ya nutse a ciki. A fusace na juyo na sami masu gadin ina fad'a akan sakacinsu da har zasu bari wani ya shigo ya huda min taya suna gani amma ga mamakina ko ci kanka basu ce ba sai ma zubamin ido da sukayi hakan kuwa ba 'karamin fusatani yayi ba. Ci gaba nayi da yi musu fad'a a fusace sai kace ni na 'daukesu aiki.
"Haidar"naji an kirani a bayana. Juyawar da zanyi muka had'a ido Hajiya ce
"Me ke faruwa ne?"
"Hava ! Wadannan sokayen masu gadin naki ne man,suna gani wani yazo ya fasa min taya zo fa ki ga yadda aka mata"
"Kayi hakuri don Allah,amma nasan ba laifinsu bane sai dai ko a hanya ka taka 'kusar baka sani ba. Amma na tabbata babu wanda zai shigo nan suna gani"
Ko kad'an ban saurari abinda take fad'a ba gaba d'aya hankalina yana kan kamshin turaren da ke fitowa daga jikinta!!!!TSEGUMI-13
.
Daga alƙalamin

BAMAI DABUWA
.
"Kayi hakuri zan turo wani yanzu ya tayaka canja wata tayar"
"Babu komai,nagode"
"Sai da safe"
"Allah ya tashemu lafiya"nace daita. Har tayi nisa ta dawo "Dan Allah idan bazaka damuba mu had'u a gidana mana gobe"
"Ba damuwa Allah ya kaimu goben"bayan ta ban adreshin gidan ta juya taci gaba da tafiya. Ranar ban isa gida ba sai misalin 'karfe daya da rabi na dare (01:30am).
Washe gari a zuciyata na yanke shawarar zuwa kaduna gidan Jaheed Auwal bayan na biya ta gidan Jamila kamar yadda ta nemi naje. A hanya nake ta nazarin dalilin da zai sa tace nazo gidanta. 'Kwan'kwasa 'kofar gidan da ta kwatantamin nayi ina jiran a bud'e amma sai naji ance shigo. A ciki na isketa da 'kananan kaya na training tana faman press up. Bata ko kalleni ba taci gaba da abinta,nima ban kulata ba sai ma 'karewa 'dakin kallo da nake a lokacin da na rufe kofar. 'Katoto ne 'dakin wanda girmansa zai linka girman normal daki sau biyu,a can wani lungu irin 'katon table "dinnan ne na snooker a 'daya sashen kuma makekiyar rediyo ce a jingine da bango. Idan ka 'dauke wa'dannan abubuwan to babu komai a ciki. Bayan na gama 'karewa 'dakin kallo ne na dawo da hankalina gareta na fara 'kirga press up 'din da take,sai da na 'kirga arba'in sannan ta tashi.
"Dakyau! Kina 'ko'kari fa,kinyi ya kai arba'in"
"Saba'in nayi"tace dani tana haki
"Ya kake?"
"Lafiya lau"
"Kullum kike wannan press up d'in?"
"A'a ina yi sau biyu a sati,ka iya snooker?"Tace dani lokacinda ta nufi wajen snooker
"A'a ban iya ba,sai dai in zaki koyamin"
Nan fa ta fara tarwatsa balabalannan tana jefasu a rami,babu shakka ta 'kware a wannan fannin ma. Bayan ta gama jefasu ne ta duba agogon hannunta "La'ila" kaga har na kusan makara ma akan abinda nake so zamuyi dakai. "Biyoni"tace dani
"Ina so ne kaban shawara akan fara kasuwancin Jarida"tace dani a lokacinda muka shigo wani 'daki mai kama da dressing room. "Ina so ne nima na bud'e ma'aikata tawa ta jarida"
"Me da me kike son sani gameda harkar?"
Dutsin guga ta 'dauka ta jona a jikin socket sannan ta fara goge kayanta a kan wani benci mai fad'I lullu'be da yadi. "Komai ma"
Nan na fara mata bayanin ta yadda zata fara da irin aubuwan da zata tanada har ta gama goge rigar sannan ta 'dauko skirt zata goge
"Don Allah taimaka ka gogemin skirt 'dinnan man zan shiga wanka,idan na dawo maci gaba"
Kafin na bud'e bakina har ta fice daga 'dakin. Wuta ce ta jani a lokacinda na kama iron (dutsin guga) 'din sai a sannan na lura da wayar jikin iron 'din ta sille kamar wacce 'bera yaci. Ajiye dutsin da kayan nayi na koma gefe na tsaya. Bayan wasu 'yan mintina sai gata ta dawo
"'Kin gogemin kayi ko?"
"Tarko ne wannan"nace da ita
"Tarko !Kamar ya tarko me kake nufi?"Tace dani a lokacinda take 'ko'karin kama iron 'din
"Dakata"
"Me ya faru?"
A hankali na dauki iron 'din na nuna mata wajenda wayar ya sille
"Tab! Allah ya taimakeni,kai amma nagode da ka ceci rayuwata Haidar"
"Babu komai,mu ci gaba da tattaunawarmu kawai"
"Mu bari sai wani lokacin maci gaba wallahi gaba daya na tsorata"
"Kar ki damu lokacinki baiyi ba tukun,zan wuce ni saboda ina so zanje kaduna yau"
"To shikenan nagode"
"Amma akwai 'bera a nan ne?"
"Akwai su"
"Ya kamata ki nemi maganinsu"
"Zanyi 'ko'karin hakan".
A hanya nake ta tunanin yadda akai ta goge rigar ba tare da iron 'din ya ja ta ba a karo na farko. Na tabbata yadda na kama dutsin gugar haka kowanne irin mutum zai yi idan ya tashi guga. Ya kamata ace itama dutsen ya ja ta a karo na farko.
Misalin sha 'daya na isa garin,kai tsaye wajen abokina daya gayyaceni auren Jaheed na wuce. Bayan mun gaisa na 'dan huta nake tambayarsa gameda Jaheed
"Wai ya labarin kawunnannaka yana nan?"
"Yana nan,gobe ma zamuje 'kauye ta'aziyya nida shi"
"Ok! A goben kuma zaku dawo?"
"A'a sai mun kwana biyu gaskiya"
Naji da'din haka domin ina son le'kawa gidannasa don 'karasa wasu bincike sai dai na yanke shawarar komawa kano yau don gudanar da wani aiki a Khairat Night Club kafin goben na dawo. Ban kama hanyar dawowa gida ba sai misalin shida na yamma,na isa kano da daddare misalin karfe tara. Kai tsaye Khairat na wuce sai dai wannan karon shiru na iske wajen sa'banin sauran lokuta da zakaji ki'de-'kide na tashi da tulin mutanen na 'dud'd'ukuwa ciki,a hanakali na'karasa wajen masu gadin zuciyata na bugawa.
"Barkanku da yamma"
"Yauw barka dai"
"Meke faruwa anan ne?"
"Yau bama aiki,mun rufe sakamakon bige wani abokin aikinmu da akayi yau a mota"
"Wanene?"
"Ba zaka sanshi ba"
"Kwatantamin yanayinsa"
A irin yadda ya siffantamin shi na tabbatarwa kaina cewa saurayinda nasa ya kula da shiga da ficen Jamila ne aka kad'e.
"Amma taya har aka buge shi?"
"Yau ne da safe zai koma gida a kan hanya"
"To yazo tsallaka titi ne ko ya?"
"Ko 'daya a gefen titi ma yake tafiya"
"Ina Jamila?"
"Kana nufin Hajiya?"
"Eh"
"Ta koma gida"
Haka nima na koma gida zuciyata cike da takaici da tunani!!!
.
Ban kama hanyar kaduna ba sai da la'asar sakaliyarta,wannan karon na yanke shawarar tunkarar maigadin kai tsaye yayin shiga gidan saboda zanfi samun nutsuwa da kwanciyar hankali wajen gudanar da abinda nake son aiwatarwa a gidan kasancewar maigidan baya nan kamar yadda abokina ya fad'amin,yau ne zasuyi tafiya,na tabbata yanzu kam sun bar garin. Bayan sallar magriba na isa kofar gidan kai tsaye wajen maigadin na nufa na masa sallama sannan na fara tambayarsa.
"Ka gane ni kuwa baba?"
'Kuramin ido kawai yayi yana nazarin fuskata a 'ko'karinsa na gano wajenda ya sanni na 'yan wasu dakikai kana ya numfasa hade da cewa
"Eh to kamar dai na shaida ka,amma ban wayeka ba sosai"
"Ka tuna kwanakinnan da suka shu'de da daddare maigidanka ya saka ka fita dani zuwa 'kofar gida?"
"Ok ! Na ganoka kuma"
"Yauwa !Ya fadama abinda ya kawoni kuwa waccan lokacin?"
"A'a bai fadamin ba,me ya faru?"
"Wato abinda ya kawoni waccan lokacin shine wata mata na gani da sukai matu'kar kama da matarsa da aka kashe,tsantsar kamannin da sukayi ne ya sani yanke shawarar zuwa naga gawar matar tasa ko itace ta rayo shine ya kamani. kaji dalilin zuwana waccan lokacin"
"Dama ana mutuwa a dawo?"
"Eh to ance dai wai wasu suna yin fatalwa su dawo"
"Amma yanzun dai ina fata ba wajen gawar ka sake dawowa ba?"
"Wajenta nazo"
"Ba zai yoyu ba gaskiya"
"Saboda me?"Nace dashi a lokacinda na zaro dubu 'daya na dam'ka masa a hannun
"Saboda babu mukullin gidan a wajena"
"Kar ka damu zan san yadda zanyi na shiga"
"Amma ina fata bazaka jima ba?"
"Minti goma sha biyar ma ya isheni zan gama abinda zanyi na fito"
"To yanzu yadda za'ayi ka koma wani wajen ni kuma zan je na kashe fitulun gidan sai ka dawo"
"To ba damuwa"
Bayan naga ya kashe gaba d'aya fitulun gidannane na shigo,kai tsaye 'dakin da gawar take na nufa. Bayan na bud'e gilashin da take ciki na 'dauko camerar da na aro agun abokin aikina na fara daukarta a hoto. A hankali na maida na rufe gilas 'din kamar yadda yake da sannan na shige 'daya daga cikin sauran 'dakuna ukun dake gidan,ina shiga na tabbatar ba shine 'dakin da nake nema ba don haka na fito daga ciki na fad'a 'daya 'dakin. Babu shakka wannan shine 'dakin Fatima sakamakon tulin kayan matan dana gani a cikin wani wardrobe dana bude,sai kuma jibgin turararruka da na gani da sauran kayan shafe-shafe na mata akan dressing mirror. Wata 'yar 'karamar leda na zaro daga aljihuna na 'dure wasu daga cikin kwalaben turaren ta hanyar amfani da hankici sannan na zurasu cikin aljihuna na wando. Ci gaba nayi da bincika 'dakin anan naga wani photo album na bikinnasu cikin wata loka dake jikin dressing mirror 'din. Sai da na zabi hotonta da nake ganin shine yafi miin sannan zai taimakamin wajen gudanar da bincikena shima na cusashi a aljihun wandona na 'daya 'bangaren sannan na fito daga cikin gida.
"Baba kaga ban jima ba ko?"Nace da maigadin a lokacin da na fito daga cikin gidan
"Eh baka jima ba kam"
"Yauwa nagode ni zan koma"
"To madallah, Allah ya kiyaye hanya"
"Ameen"
A gida ne na 'dauko hotuna biyun ina nazarinsu. Na jima ina kallonsu irin kallonnan da ake kira na 'kurilla amma ban ga wani bambanci ba tsakaninsu. Tabbas da ace zasu saka kaya iri 'daya to bazaka iya bambancesu da juna ba. Sake dawo da dubana nayi jikin hoton daga sama zuwa 'kasa a karo na ashirin sai a sannanne naga wani abu daya ja hankalina,akwai'dison ba'ki 'dan 'karami jikin kunnen

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment