Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ne?"Nace dashi
"Ina dasu dayawa ma idan zaka siya,sai dai suna gida"
"Don Allah kwatantamin gidannaka zan dawo anjima"
"To amma kar ka haura 'karfe bakwai na dare"yace dani bayan ya rubutamin adreshinnasa a takarda.
Akan hanyata ta zuwa sharadan a cikin bus idanuna suka sake arba da blue peugeot d'innan. "Ko dai ni suke bi?"na tambayi kaina. Har na isa daidai wajen motar na biye dani sai dai nesa-nesa take da motar da nake ciki. Ban sha wahala ba wajen samun Al'amir restaurant din,ciki na shiga kai tsaye. Bayan mun gaisa da wata mata mai dan matsakaicin 'kiba ne nake tambayarta
"Malama ina tambayar wata Hadiza Abdullahi Adamria,ance ta ta'ba aiki anan"
"Eh amma gaskiya tunda ta bar nan ban sake ganinta ba"
"Ko kin san inda ta koma?"
"A'a amma dai akwai wata 'kawarta Laila wacce ke zuwa tana fita da ita"
"Ita Lailan kin santa ne?"
"Eh gidanta yana daidai layin freedom,amma dai 'yar gala ce"
"Menene kuma gala?"
"Irin masu rawar nan a gidajen cinema"
"Ok !Amma kina ganin itama Hadizan galar ta koma?"
"Eh zata iya kasancewa"
"Nagode"nace da ita a lokacinda na fito daga restauranta 'din. Ina 'ko'karin tafiya titin freedom radio ne na sake hango blue peugeot 'dinnan nesa dani . . .TSEGUMI-08
.
Daga alƙalamin

BAMAI DABUWA
.
Kai tsaye titin freedom 'din na nufa,sai dai kafin na isa a hanyata sai da na kira abokin aikina Ibrahim na sanar dashi game da motar da ke ta bina. Lambar wani abokinsa ya aikomin wanda ke aiki a Licence office,ban 'bata wani lokaci ba na kirashi aka sadani dashi.
"Hello"aka amsa
"Hello jabeer ne"nace dashi
"Eh shine"
"Ibrahim abokinka dake aiki a jaridar Mikiya ne ya ban lambarka,sabodaina so zaka taimakamin"
"To ina jinka"
"Ina so nasan mamallakin wannan motar"na karanto masa lambar.
Bayan kamar da'ki'ka goma ya kirani "motar haya ce"
"Kasan address 'dinsu?"
"Eh,Dauda car hire agency ofishinsu yana zoo road (DCHA)"
"Yauwa,nagode sosai"nace dashi sannan na katse wayar naci gaba da neman gidan Laila. Nasha wahala kafin na isa gidan,babban gidane hawa biyu da alama gidan haya ne a daidai mashigar na iske wani kul'be'ben mutum "malam don Allah ina tambayar Laila ne"
"Ka hau sama"yace dani. A can saman benen ne nake tambayar wata mata Laila,sai da ta kaini har 'kofar 'dakin tace min shine 'dakin Laila. Na 'dan 'dauki lokacin ina 'kwan'kwasawa kafin daga bisani wani matashi ya bud'e 'kofar a fusace. Daga shi sai gajeren wando da singileti ya dubeni sama da kasa sannan yace "ya akayi ne"
"Ina tambayar Laila ne"
"Waye kai?"
"Ni abokin Hadiza ne 'kawar Lailan" ya bud'e baki da niyyar sake min wata tambayar aka katse shi daga ciki "Babannan barshi ya shigo". Yanayinda na sameta a cikinne na tabbatarwa da kaina bata da wani bambanci da karuwa,a kan wata kujera na zauna irin ta katakonnan da alama ita kad'ai ce a dakin domin suma sai a kan katifa suka zauna idanunta 'kyar a kaina sai kace mujiya
"Hadiza ce ta aiko ka?"Tace dani
"A'a ina dai nemanta ne shine aka kwatantamin ke aka ce kinsan wajenda zan sameta"
"Amma kai waye?"
"Ni 'dan jarida ne,ina so zamu 'dan tattauna da ita ne akan wani abu sannan mu biyata"
"Malam dan Jarida kace kana neman Hadiza domin 'daukan wasu bayanai sannan ka biyata,to nawa ni kuma zaka biyani idan na kwatantama wajen da zaka sameta?"Tace dani cike gautsi
"Nawa kike so"
"Dubu 'daya"
"Kai ! Gaskiya bani da dubu yanzu,ina laifinma 'dari hud'u"
"mtswwww"taja wani dogon tsaki sannan ta dubi abokin holewarta tace dashi "babbannan bud'e masa 'kofa ya fita"
Dama bai so zuwana ba da 'karfi-'karfi ya kama hannun rigata yana 'ko'karin figata waje "dakata"nace dashi
"Zan bada 'dari bakwai
"Idan kuwa hakane to zan fa'dama wasu abubuwa gameda ita amma ba duka ba,saboda kasan Hadiza shegiyace tana da masifar wayo. Inaso nai maganintane kafin ta....ta katse abinda take son fad'a
"Kafin ta me?"Na tambaya cike da 'kaguwa
"Ina 'dari bakwai 'din"
Da gaggawa na cirosu daga walet na mika mata.
"Kaje Tahir guest palace sokoto road,nan ta koma da aiki lokacinda ta bar Al'amir restaurant. Amma bata jima da barinnan bama saboda wani 'kulli da ta taka. Babu wanda yasan wajenda ta koma ko kaje nan sai ni,ni kuma bazan fad'a ba sai ciko 'dari ukun"
Dubu da 'dari biyu ne kacal suka rage min a jikina,kuma dasu ne nake son nayi 'kud'in mota zuwa wajen Garba Hadi siyan hotunan Hadiza. "Yanzu haka babu kud-n a jikina,amma da wanne lokaci zan dawo na sameki?"
"Ka dawo gobe misalin sha 'daya na safe"
Wani mutum na gani yana sauka daga benin a daidai lokacinda nake fitowa daga 'dakin yayi shigar ba'ka'ken kaya over size kansa rufe da ba'kar hular sanyi ya zura hannayensa a aljihu da sauri ya sauka daga benen "kodai shine ke bina a mota"nace a raina a lokacinda na rufa masa baya. Ko alamarsa ban gani ba a farfajiya da wajen gidan. Wani na samu a waje nake tambayarsa ko yaga fitowar wani mai ba'ka'ken kaya
"Naga shigarsa dai,'kila ko ta 'kofar baya ya wuce"
"Akwai 'kofa daga baya?"
"Eh akwai"
Ganin 'kuratowar da lokaci yayi ne yasa na kama hanyar gidan Auwal kamar yadda yace nazo bakwai dot. Na isa unguwar da misalin shida da rabi,wajen wata mai saida a wara na zauna ina jiran cikar lokacin kafin na 'karasa. A raina ina ta sa'ke'ken Hadiza Abdullahi Adamri ko ita ya kamanninta suke yau dai zan gani. Bakwai saura minti biyar nabiyo kwararon har bakin 'kofar 'dakin kamar yadda ya kwatantamin. 'Kwan'kwasawa nayi hade da sallama amma shiru,agogon hannuna na duba naga bakwai daidai ban haura ba "kar ace bayanan,ai kuwa da bai kyautamin ba"nace a raina. Na 'dan 'dauki lokaci mai tsawo ina bugawa amma shiru,kofar 'dakin na kama da niyyar gwada bud'ewa amma ga mamakina sai naga ta bud'e. A zaune a kan kujera Auwal ne fuskarsa da alamun murmushi a fuskarsa "Auwal baka ji inata buga 'kofa bane amma ka......"Bakina
ne ya 'kafe harshena ya sar'ke a lokacinda idanuna sukayi arba da jinin da ke 'bul'bulowa daga 'kirjinsa saitin zuciya. Babu shakka ya mutu
Lura da yanayin gawar ne zai tabbatar maka da cewa ba'a jima da kashesi,amma waye ya kashe shi?
Sai a sannan na lura da irin yadda aka birkita komai na gidan,gaba-ki-'daya an warwatsa kayansa na sawa ko ina takardune zube a kowanne 'bangare na 'dakin. Lura da yanayin gawar ne zai tabbatar maka da cewa mai kisan ya 'kware wajen iya harbi,saboda harbi 'daya ya mar wanda yayi sa'ar samun sa a 'kahon zuciya. Duk yadda akayi wanda yayi kisannan ya biyo sawun hotunan Hadiza ne kuma da alama ya 'daukesu ya gudu. Gudun taka sawun 'barawo ya sani zaro hankici daga aljihuna na goggoge bakin 'kofar da na 'taba yayin shigowa da fita a tsorace na bar layin unguwar cike da tunani a raina. Cikin ikon Allah babu wanda yaga fitata
Zoo road na nufa domin binciko wani abu gameda motar da ke bina ina ji a jikina bazata rasa nasaba da kisannan ba, a hanya nake tamabayar kaina "an birkita gidana an dau'ke hoton Jamila gashi kuma nan ma an 'dauke na Hadiza shin suna da had'i ne? Amma kuma wanene zai sace hoton Hadiza? Wanne irin muhimmancine da hoton da har zai sa a kashe mutum saboda shi? To ko dai Hadiza abdullahi Adamri ita ce Fatima Jaheed? Idan kuwa har Hadiza itace Fatima Jaheed babu makawa Alh Jaheed Auwal ne ke turowa a kwashe hotunanta don kare mutuncin kansa na auren 'yar gala ko ince karuwa da yayi musamman kasancewarsa babban mutum na tabbata babu wani mutum da zai so ace matarsa da yake matu'kar so ta ta'ba yin karuwanci ko makamanci haka. 'Kila shi yasa ma babu wani cikakken bayani na tarihin rayuwarta a jaridar da ta buga kisanta. Haka a invitation card na aurensu ma kawai sawa akayi Jaheed weds Fatima babu wani sunan iyayenta da aka sa. "To amma idan Jaheed 'dinne taya akai yasan zamu ha'du da Auwal 'din misalin 'karfe bakwai? Da irin wa'dannan tunane-tunanen na isa Zoo road.
Ban sha wahala ba wajen gano wajen hayar motocin a ciki ne na had'u da wani saurayi da alama shima ma'aikacinsu ne "malan barka dai"nace dashi
"Yauwa"
"Don Allah tambaya nake"
"Ina jinka"
"Anan ne aka 'karbi hayar motar nan ko"nace dashi a lokacinda nake nuna masa lambar motar
"Eh nan ne,lafiya ko wani abu ne ya faru"
"A'a babu abinda ya faru,kawai ina so nasan wanda ya 'karbi hayarta ne"
"Ina zuwa"yace dani a yayinda ya koma ciki
"Basheer Shehu"yace dani bayan ya fito
"Ok ! Amma adireshinsa fa"
"A na'ibawa yake gida mai lamba 23 kusa da police station"
"Tun yaushe ne ya 'karbi hayar motar?"
"Jiya kamar yanzu" na duba agogo naga 'karfe takwas na dare
"Yaushe kuke rufewa?"
"Goma na dare"
"Amma ya dawo muku da motar ne?"
"Eh ya dawo da ita"
"Da wanne lokaci?"
"'Dazunnan da misalin 'karfe shida da rabi na"
"Ko zaka iya kwatanta kamanninsa?"
"Eh gajere ne baki mai jiki"
"Wad'anne kalan kaya ne a jikinsa?"
"Doguwar rigace fara da blue jeans"
Ko ka'dan baiyi kama da mutumin da na gani ba a gidan Laila domin waccan 'din dogo ne sanye da ba'ka'ken kaya sannan da gashin baki a fuskarsa. . .TSEGUMI-09
.
Daga alƙalamin

BAMAI DABUWA
.
Washe gari da misalin 'karfe tara na isa Tahir guest palace kamar yadda Laila ta fa'damin nan ne wajenda tayi kafin ta taka wani 'kulli. Anan na had'u da wata ma'aikaciyarsu nake tamabayarta bayan na dam'ka mata dari biyu a hannunta a matsayin cin hanci. "Wata nake tambaya Hadiza ance ta ta'ba aiki anan"
"Hadiza?"
"Eh"
"Eh ta ta'ba aiki anan amma ta bari"
"Ko zan iya sanin wajenda ta koma?"
"Gaskiya ban sani ba,amma dai ga wani shago can tsallaken titin ka tambayi mai shagon zai iya sani domin mutumiyarsa ce"tace dani.
"Malan barka dai"
"Yauwa"
"Ina tambayar Hadiza ne da ta ta'ba aiki anan tahir guest palace"
"Ai ta jima da barinnan"
"Eh na sani,ina son naji ko ka san wajenda ta koma da aiki"
"Amma lafiya kake nemanta?"
"Lafiya lau,ni 'kanin mahifiyarta ne daga 'kauye. Ta jima bata je gida bane shine akace na fito na nemeta"na shirga mar 'karya
"Gaskiya ta bar nan shekaru uku da suka wuce,akwai lokacinda naga an buga mutuwar wata mata a jarida na 'dauka ma ita ce sai naga sunan ya bambanta kuma ita Hadiza daga Jigawa take sa'banin ita waccan dake Kaduna"
"Ka santa ma kenan?"
"Sosai ma,ai mutuniyatace"
"Ta ta'ba fad'ama wani waje da ta ta'ba yin aiki kafin tazo nan?"
"Eh"
"Ina ne"
"Ta ta'ba aiki a Ministry for Education"
"Amma lokacinda zata bar nan,ko ta fad'ama wajen da zata koma?"
"Bata fa'damin ba saboda yanayin yadda ta bar nan 'din"
"Wanne yanayi kenan?"
"Ka duba kaga duk yadda muke da ita lokaci guda kawai naga tana kayakin a boot 'din wata farar mota babu ko sallama ta wuce"
"Wacce kalar motace?"
"B. M. W ce fara,motar ta burgeni matu'ka har sai da na rubuta lambarta a jikin bango ma"
"Yanzu haka kana da lambar?"
"Eh akwai bari na duba ma". Nan ya fara dube-dube na 'yan wasu lokuta
"Yauwa gata nan"bayan na rubuta lambar na masa godiya. A hanya na kira jabeer
"Kayi ha'kuri fa Jabeer zaka na dameka,wallahi wata lamba nake so ka 'kara bincikomin"
"Babu komai,fadamin lambar kawai"bayan kamar minti goma ya kirani
"Ina jinka"nace dashi
"Motar mallakin Jaheed Auwal ce" shiru nayi ina tunani bance 'kala ba
"Hello kana jina?"Yace dani
"Eh ina ji,kace ta Jaheed Auwal ce?"
"Eh"
Yanzu kuma na gane cewa Hadiza Abdullahi Adamri itace Fatima Jaheed shine aka canja mata suna daga hadiza zuwa Fatima duk dan a rufe sirrinta. To amma wacece Jamila ko duk ita ce Hadizan,babu ta yadda za'ayi ace Jamila itace Hadiza domin naga gawarta. To ko dai ita Hadizan a gidan marayu ta taso data girma shine ta gudu? Ko kuma guduwa tayi daga gun iyayenta? Tunanina ya tsaya a lokacinda na tuno da cewa ai ita ma Jamilar 'yar Jigawa ce (Busuku) amma ai ita tace a gaban iyayenta ta taso wa'danda suka mutu tana da shekara goma sha biyar daga nan ta dawo hannun ma'kociyarsu wacce ta gudu ta barta daga baya. Babu ta yadda za'ayi ace Jamila itace Hadiza na tabbatarwa da kaina haka.
Yanzu dai kam na gano cewa Hadiza Abdullahi Adamri ita ce Fatima Jaheed. Amma wacece ita? Su wanene iyayenta?Har yanzu suna da rai? Da ace zan ga hotonta to da duk abin zaizomin da sauki. Sai a sannan kuma na tuna Auwal da aka kashe ta dalilin hoton da kuma mutumin da ke bibiyata. Babu shakka sai na taka a sannu
Kai tsaye gidan Laila na nufa don cika mata 'dari ukun ta 'karasa fad'amin wajen da zanga Hadiza. Sai da na 'kwan'kwasa 'kofar a 'kalla sama da sau goma amma ba'a bude ba. Ga mamakina ina tura 'kofar naga ta bud'e kutsa kaina ciki kawai nayi. Tsulum naji na tsoma 'kafata a wani abu kwance a kan katifa Laila ce da Babannan idanunsu yana kallona. Sai a sannan na lura da 'dan 'karamin tafkin jinin da ke malalowa daga kan katifar zuwa inda na ajiye kafafuna. Suma an kashe su!!!!
Da gaggawa na fice a 'dakin na bar layin unguwar. A hanya nake ta nazarin mutumin dake wannan aika-aikar. Babu shakka 'yan sanda zasu iya nemana a matsayin primary suspect musamman idan akayi rashin sa'a suka had'u da matar da ta kaini har bakin 'kofar 'dakin Lailan jiya. Tunanin karbar hayar motane yazomin saboda irin yadda nake fama da jigila daga nan zuwa can amma bani da isassun kud'in da zan karbi hayar motar dashi dole na na biya wajen A'isha ta ara min dubu goma. Bayan na karbo hayar motar ne na wuce kai tsaye ma'aikatar ilmi (Ministry of Education). Ta cikin mirrow ina tafiya na hangi blue peugeot 'dinnan tana biye dani nesa kad'an daga wajen da nake. Isata ma'aikatar nayi fakin 'din motar a gefe sannan na fara dube-duben motar da ke biye dani amma ban ganta. Wajen maigadin wurin na nufa bayan mun gaisa nake tambayarsa gameda Hadiza Abdullahi Adamri amma yace bai santa ba sai dai ya kwatantamin office d'in wani clerk. A ciki ne na iske wani saurayi zaune a kan kujera yana ta faman dube-dube cikin wasu file,bayan mun gaisa ne yamin iso a 'daya daga cikin kujerun na zauna nima
"Yauwa lafiya?"Yace dani
"Wani taimako nake so zakamin idan da hali"
"Allah yasa zan iya"
"Ameen,akwai wata Hadiza Abdullahi Adamri wadda ta ta'ba aiki anan shekaru shida zuwa bakwai da suka wuce shine nake so ka taimaka ka binciko min file 'dinta"
"Gaskiya bama bada file 'din ma'aikatanmu"
"A'a ba wai ina nufin a ban ba,kawai inaso ne ka bincikomin makarantun da ta halarta adreshinta da kuma wakilanta (next of kin) idan da dama ma hotonta wadda nasan baza'a rasaa ba"
"Gaskiya bazai samu ba yanzu saboda yanzu haka akwai ayyuka a gabana,amma ka dawo gobe bayan 'karfe goma Insha Allah kafin lokacin zan binciko ma"
"Nagode"nace dashi sannan na fito daga office 'din . . .TSEGUMI-10
.
Daga alƙalamin

BAMAI DABUWA
.
"Sai ina kuma?"Na tambayi kaina a lokacinda na shigo mota. Gida ya kamata na koma 'dauko takardar da na samo a kamfanin takalma na Jogana domin bibiyar sauran mutanen da ban samu damar zuwa wajensu ba gameda Abubakar. Cinkoso da gosulon motocine ya dakatar dani a hanya,le'kawar da zanyi ta mirrow na hangi blue peugeot 'dinnan a bayana motoci uku a tsakaninmu. "Yau kam sai naga wanda ke bibiyata"nace a raina lokacinda na fito daga motar na tunkari blue peugeot d'in. Ban 'karasa isa ba mutumin da ke ciki ya bud'e 'kofar da gaggawa ya tsallake gefen titi sama ko 'kasa na nemeshi na rasa. Sai da na 'karasa har cikin motar cusa kan da zanyi ne wani dadda'dan 'kamshi ya daki hancina. Babu komai a motar sai wani 'dan 'karamin agogon hannu na mata a ciki. "Me kuma ya had'a namiji da agogon mata?"Na tambayi kaina.
Ban sha wahala ba wajen iske gidan mutumin da naga sunansa da adreshinsa a jikin takardar ba a unguwar Nasarawa yake.
"Malam barka dai"nace dashi bayan mun gaisa
"Yauwa"
"Don Allah ina tambayar wani abokinka ne Abubakar Garba"
"Waye kai?"
"Sunana Haidar"
"Taya akai kasan abokina ne?"
"Nasan hakane a kamfanin takalma na jogana kasancewar kan zuwa wajensa kuna gaisawa"
"Ok ! Gaskiya rabona Abubakar tun yana aikin kwandasta(karenmota) shekaru uku da suka wuce ban sake ganinsa ba"
"Kana nufin yana zuwa nan shekaru uku da suka wuce?"
"Eh"
"Amma a lokacin a ina yake da zama?"
"Tsamiyar boka nesa kad'an da police station"
"Amma direban da yakewa karen motar fa ka sanshi?"
"A'a ban sanshi ba gaskiy"
"Amma ka ta'ba ganinsa da wata yarinya ko ka ta'ba jin sunan Hadiza Abdullahi Adamri a bakinsa?"
"Eh to ina ganinsa da 'yan mata dai kam amma bansan wacece Hadizan ba cikinsu"
"Kace shekaru uku da suka wuce kuka daina had'uwa?"
"Eh amma akwai lokacin da na ta'ba ganinsa a gidan polo,yake fad'amin cewa yanzu ya koma Khairat Night Club da aiki"
"Yaushe ne?"
"Bara ne (shekara daya)"
"Amma ka ta'ba zuwa Khairat d'in gunsa?"
"Eh naje,amma da na tambayi masu gadin sai suka cemin babu wani Abubakar dake aiki agun"
"Lokacinda ka ganshi a filin polon ya kaga yanayinsa,irin na masu kud'ii ne?"
"Eh to gaskiya dai ya canja bai yi kama da mai aikin wahala ba"
"Nagode"nace dashi sannan na dawo mota. Hankalina ne ya rabu biyu a yayinda nake tunanin wajen zuwa "Khairat ya kamata naje ko kuma can Tsamiyar bokan wajen da aka ce ya zauna?" Daga 'karshe na yanke shawarar zuwa Tsamiyar bokan. Na tambayi mutane da dama amma babu wanda ya sanshi a layin dole na ha'kura na dawo gida lokacin dare yayi.
Washe gari da misalin goma da rabi na isa Ma'aikatar ilmi (Ministry of Education) tarun tulin 'yan sandan da na ganine da makamai a hannunsa ya tayar min da hankali mutane a gefe suna kallo a yayinda ake caje wasu. Matsawa nayi kusa da wani nake tambayarsa "Malan me ke faruwa anan ne?"
"Ina tunanin 'yan fashi ne suka kawo hari"
"Yan fashi !Me suka zo sata?"
"Ban sani ba"
Ana haka ne na hangi mutuminda yace na dawo yau bayanmun gaisa nake tambayarsa "wai 'yan fashi ne suka zo muku?"
"A'a ba 'yan fashi bane"
"Su wanene to?"
"Wanine yazo yake son sace mana files sai dai ya kashe d'aya daga cikin masu gadinmu a yayinda ya raunata 'dayan da harsashi a kafad'a"
"Amma taya akai kuka san file yazo sata?"
"Saboda a wajenda muke ajiye files 'din abun ya faru sannan an warwatsa file din zuwan 'yan sanda ne ya koreshi daga wurin"
"Yanzu kenan baku sani ba ko ya sace file d'in?"
"Shine binciken da mukeyi kenan"
"To ya maganarmu ta jiya?"
"Wallahi ban duba saboda faruwar wannan al'amari,amma me yasa kai kuwa kake son a binciko ma file dinta?"
"Wato wani 'dan uwana ne ya jima da barin gida bai dawo ba shine aka turoni nemansa na tattambayi mutane da dama sun fad'amini cewa suna tare da ita Hadiza Abdullahi Adamrin shi yasa nake son a bincikomin file d'inta ko zan ga adreshin gidan da suke zaune"na shimfid'da masa karya. Gyad'a kansa kawai yayi alamar ya gamsu kafin daga bisani yace "amma me yasa bazaku sanar ma 'yan sanda ba?"
"Eh muna 'ko'karin hakan,amma yanzun dai muna bukatar file d'in"
"To yadda za'ayi ka dawo anjima misalin 'karfe biyu (02:00pm) insha Allah zan bincika ma"
"Nagode"
Gida na nufa domin na huta kafin lokacin ya cika saboda matsananciyar gajiyar da ke damuna. Gumi ne ya fara ketowa daga kaina zuwa goshina a lokacin da na hango wasu 'yan sanda su biyu a unguwartamu kusa da gida. Naso na koma da baya saboda ina ji a jikina ni d'in mai laifi ne ko dan akan kisan Laila da saurayinta da akai amma na fasa. Haka nazo ta kusa dasu na nufi gidana a raina ina jira naji sunce you are under arrest amma shiru babu wanda yace ci kanka a cikinsu har na shiga gida. Hankalina bai kwanta ba kwata-kwata jira kawai naji an 'kwan'kwasa min 'kofa amma shiru can na leka da taga sai na hango suna wucewa zasu bar unguwar. Sai da na tabbatar sunyi nisa sannan na fito na samu wani ma'kocina nake tamnbayarsa abinda ya kawo su "wai neman wata yarinya suka zo,tace musu anan unguwar take"yace dani. Tsaki nayi gami da sau'ke wani nannauyen ajiyar zuciya sannan na dawo gida.
'Karfe biyu daidai na isa wurin,wannan karon akwai 'karancin mutane a wajen sannan 'yan sandan ma basa nan. Kai tsaye na shige ofishinnasa bai jira na zauna ba ya mi'kamin wata doguwar takarda fara cike da rubutu a 'bangare 'daya. "Hoton fa?"Nace dashi
"Babu hoto a file 'dinta"
"To nagode"
A mota nake nazarin takardar anan naga abinda yaja hankalina Busuku,kirikasamma Local Govt jigawa state shine garinsu ai kuwa Jamila ma can ne tace garinsu. Bayan na ci gaba da duba takardar ne naga makarantar da ta halarta private commercial college a birgade. Ban jira ba kawai na nufi makarantar ganin lokacin tashi yayi ko Allah zai sa na iske malaman. Office d'in principal na shige
Malam barka da aiki"nace dashi bayan nayi sallama
"Yauwa,ya akayi?"
"Ni d'an jarida ne daga mikiya,nazo inaso a bincikamikn file d'in wata d'alibarku saboda muna so zamu d'auki wasu bayanai ne game da ita"
"Ok! Amma taya zan san kai d'an jarida ne"
"Ga I D card d'ina"na mi'ka mar
Bayan 'yan wasu sakanni ya mi'ko min sannan yace "ya sunan yarinyar,kumna tun yaushe ta bar nan?"
"Sunanta Hadiza Abdullahi Adamri shekaru goma kenan rabonta da nan"nace dashi a lokacin da na duba takardar dana kar'bo a ministry. 'Kararrawa ya kad'a masinjan sa ya shigo
"'Dahiru kaje ka sami malam bala ku wuce store wajenda muke ajiye file na yara ku dubomin me wannan sunan ka kawo yanzu. Amma shekararta da goma da barinnan"yace masinjan bayan ya shigo
Surutai ya rufeni dasu na makarantar tun daga farkonta har zuwa yanzu,kamar yadda yake fad'amin ainahi mahaifinsa ne ya gina makarantar kafin ya gajeshi. Shigowar masinjan ce ta ceceni daga surutannasa da ba fahimtarsu nake
"Yallabai gashi"
"Yauwa"yace da maigadin a lokacin da yake kokarin karbar file din
"Zainab Abdullahi Adamri ! Wannan ai ba shi bane Hadiza Abdullahi Adamri na ce ma ba Zainab ba maida ka ku d'auko na Hadizan"yace da masinjan yana 'ko'karin mi'ka masa file d'in.
"Malam zanso na duba wannan d'inma kafin su binciko waccan"nace dashi
"Ba nata bane ba fa"
"Eh na sani amma ina jin kamar suna da ala'ka"
"Ok ! Gashi to"
A lokacinda nake bincika file d'inne masinjan ya shigo a karo na uku ri'ke da wani file 'din "yallabai gashi"ya mi'kawa principal 'din. Bayan na 'karba ne na fara dubasu. Babu wani ba$banci tsakanin file 'din biyu na daga adreshinsu komai 'daya ne hatta sunan mahaifiya (fatima). "Ko zan iya kwafar wasu abubuwa a jiki?"Nace da principal d'in
"Ba matsala"
A 'kasa ne na zo wajen halayya da d'abi'unsu ita Hadiza nutsatstsiyace sannan tana da haza'ka sai dai tana da saurin fushi ita kuma Zainab bagidajiyace sannan jaka ce.
"Malam ko kuna da hotonsu?"
"A'a bama ajiye hoto"
"To nagode malam zan koma"nace dashi na mi'ke tsaye bayan na gama kwafa.
Zama nayi a cikin mota ina nazari. Duk yadda akayi matar Jaheed Auwal 'yan biyu ne,amma wacece Jamila tunda ita tace ita kad'ai ce agun iyayenta????TSEGUMI-11
.
Daga alƙalamin

BAMAI DABUWA
.
Gidan Hajiya Jummai na nufa wacce suka bayyanata a matsayin wakiliyarsu (next of kin) ban tsaya a ko ina sai a 'kofar gidan a nan ne na iske wani zaune a kan benci bayan mun gaisa nake tambayarsa.
"Hajiya Jummai nake tambaya"
"Kai d'in wanene kake tambayarta?"
"Sunana Haidar Ali,ni d'an jarida ne muna bincike ne akan wata yarinya Hadiza Abdullahi Adamri. Ta ambaci sunantane a matsayin wakiliyarta lokacinda take aiki a ministry da kuma makaranta shine nake son zan mata wasu tambayoyi gameda yarinyar"
"Hadiza Abdullahi Adamri !Kana nufin 'yan biyun nan?"
"Eh ka san ta ne?"
"Na santa shegiya ce,bata da kirki duk irin kyautatawar da tshohuwar take musu lokacinda iyayenta suka rasu bata gani saboda zulamarta na son abin duniya da dogon buri ya sata ta gudu da 'yar uwarta Zainab suka barta."
"Yanzu dai ina Hajiya Jummai d'in take?"
"Ta tashi anan,'ya'yanta sun siya mata gida a zoo road ta koma can da zama"
"Ko kasan adreshin gidan?"
"Eh na sani,bari na rubuta ma"
Ban sha wahala ba wajen iske gidan a bakin 'kofa na 'kwan'kwasa.
"Ina wuni Hajiya"nace da ita bayan ta fito
"Lafiya"
"Sunana Haidar ina tambayar wata Hadiza Abdullahi Adamri"
"Shigo daga ciki man"tace dani
"Kace Hadiza Abdullahi Adamri?"
"Eh"nace da ita a lokacinda na zauna a 'daya daga cikin kujerun da ke falon.
"Kai me d'inta ne kake tambayarta?"
"Ni d'an jarida ne muna son 'daukar wasu bayanai ne game da ita"
"Ok"
"Ko zaki bamu d'an ta'kaitaccen tarihinta?"
"To babu matsala.""Da farko dai su biyu ne 'ya'ya agun iyayensu ita da Zainab sun kasance tagwaye.Kamar yadda mahaifinsu ya fadamin asalinsa dan jigawa ne shi da matarsa Fatima wacce ta rasu sanadiyyar hatsarin mota kafin daga baya shima mijinnata ya rasu. Tun da muke da iyayensu babu wani danginsu daya ta'ba kawo musu ziyara wannan dalilin yasa suka dawo hannuna da zama sakamakon bamu

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment