Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawata? Don ni ma in zo in amshi rabona."
"Ke nawa kika samu jiya? " Rabi'at ta tambaye ta.
" Kwata - kwata dubu ashirin ya ba ni. Wani Alhaji na gamu da shi mai makon tsiya, da kyar ma ya kara mini goma, don da cewa ya yi goma zai ba ni, sai da na yi masa abin nan da na gaya miki. Kin san 'yan mazan nan... Kin dai gane ko?"
"Na gane mana kawalliya! " in ji Rabi'at.
Nusaiba ta ce," Af! Na ji kin ce kina gida. Me za ki ce da su?"
"Ahaf! Ke dai bar ni da su, ce musu zan yi, muna tafiya ne jiya a babur sai muka kade wani yaro, shi ne muka kai shi asibiti to a can na kwana muna jinya. Ba don zamanmu ba da yaron ya mutu. Kin san mamana da tausayi, shi kuma babana da ma ba ya nan."
"Fakat! " cewar Nusaiba,"to kuma ya ya za ki yi da kudin, in suka gani fa?"
Rabi'at ta dan yi shiru, "Gobe za ki raka ni na bude asusun ajiya a Unity Bank."
Nusaiba ta jinjina dabarun kawarta. Lallai ta yarda kowanne gauta ja ne, sai dai in bai sha rana ba.

Zan huta a nan. Lamba ta 4 kenan.KWANAN GIDA

MUHAMMAD LAWAN PRP

5.
BABI NA BIYU

Yau ma kamar kullum titin B.U.K. akwai karancin ababen hawa wanda ke sa ka ji shiru kamar mota ba ta wucewa, amma jefi - jefi kananan motoci kan gilma. Su kuwa 'yan bariki wadanda ke jiran abokan sana'a sun yi sahu suna iya yi da gwalli a kan titi, duk wanda ya kalle su sai ya sake kallon su. Wasu mutanen kan yi bakin ciki yayin da masu matacciyar zuciya kan yi fatan Allah Ya kai damo ga harawa.
A cikin matan barikin da suka yi sahu har da Rabi'at da kawarta Nusaiba, a yau sun sake shiga, ta yadda duk wanda ya kalle su zai yi wahala ya iya gane su, saboda sun fi kama da inyamurai maimakon hausawa. Sun yi wannan badda-bami ne saboda gudun haduwa da Alhaji Yunus dankwangila.
Cikin nutsuwa wata mota Prado, fara sol! Da ita ta taka birki a gabansu, da sauri suka fara rige-rigen lekawa motar.
Nusaiba ce ta fara magana, duk da fahimci saboda Rabi'at aka tsaya, a lokacin ta dan ji kishi amma sai ta dake.
Wanda ke cikin motar babban mutum ne amma fuskar yara gare shi. Tun kafin Rabi'at ta yi magana ya ce da ita, "Bude ki shigo mana, kin tsaya kina kallo na."
Gaban Rabi'at ya fadi, ba ta taba ganin mutum mai kwarjininsa ba.
Ta bude motar ta shiga. Bayan ya ja sun tafi ne wata karamar mota ta ja ta tsaya kusa da Nusaiba. Mutumin dake ciki ya fito, kai tsaye ya nufo Nusaiba.
In dai ba ta manta kamanninsa ba shi ya dauki Rabi'at jiya.
Kai tsaye ya tunkaro ta, wanda hakan ya sa gabanta dukan uku-uku, amma ta dake fuskarta ba ta nuna ba, za ta nuna bata san shi ba.
Ya tsaya cik! A gabanta bayan ya zare tabaran dake fuskarsa ya dube ta sama da kasa. Ta matsa gefe.
Malam idan ban yi maka ba ka nemi wata mana. Ya ya za ka saka ni a gaba kana kallo?"
Ya kawar da zancenta gefe, "Ina fata kin shaida ni?"
"Ni ban san ka ba," ta ce masa.
"Ina kawarki Usaina?" ya tambaye ta.
"Ni ban san wata Usaina ba," ta ba shi amsa cikin tsiwa, "ka je can ka neme ta a inda kuka hadu."
Ya fahimci yarinyar tana da tsiwa sai ya yi da gaske kafin ya shawo kanta ta gaya masa inda 'yar uwar yawonta a bariki take.
A bangaren Nusaiba, ta fahimci Usaina shi ne sunan da Rabi'at ta yi amfani da shi a wurin wannan mutumin, kuma ta yi imanin shi ne mutumin da Rabi'at ta satarwa kudi, amma mutumin nan shege ne duk da sauya kamar da suka yi sai da ya gano su, lallai tana bukatar ta bi a hankali, wannan Mutumin dake tsaye a gabanta yanayana da matsala. Lokaci guda ta ji tana fatan wani ya zo ya dauke ta don ta kubuta da take shirin afkawa ita da kawarta.
Tsawar da ta yi masa tun farko ta ja hankalin ragowar kilakan dake gefe, suka bi su da kallo.
Guda biyu suka tafa, daya ta ce, "Ahayye! Bariki gidan dadi, kowas so ki wata ran a bata. Kai Malam tun da ta ce ba ta yi ka rabu da ita mana. Wasu mazan ma wallahi nacin tsiya ne da su."
Alhaji Yunus bai koma ta kansu ba har zuwa lokacin da wata mota ta tsaya a kusa da Nusaiba. Na cikin motar ya leko. Nusaiba ta hanzarta da sauri ta bude motar ta shiga ta mayar ta rufe. Sauran matan suka sa ihu har da tafawa.
Alhaji Yunus ya yi murmushi yayin da ya bi motar da kallo, kafin ya koma cikin motarsa ya zauna. Wayarsa ya dauko ya nemo wata lamba ya kira, ba jimawa aka daga.
"Hello! Ku kula da wata mota baka da ta fito daga titin B.U.K yanzu. Matata ce a cikin motar wani ya dauke ta... "A'a ku datse ta kawai har na karaso," ya kashe wayar. Daga nan ya tuka matarsa ya rufa wa motar da ta dauki Nusaiba baya a fusace.

***
"Sunana Alhaji Sani," mutumin ya ce mata, bayan sun hau babban titi, "ina shigo da kayan gwala-gwalai daga Dubai."
"Ni kuma sunana Fatima. Ina zaune a unguwar Karkasara," Rabi'at ta fada masa sunanta na karya, duk da a zuciyarta, sonsa na neman shigarta. Kyakkyawa ne, kuma ta yi imanin ya fi Alhaji Yunus yarinta, har ma tana ji a ranta da zai amince za ta iya aurensa, duk da ba ta san ra'ayinsa na auren matan bariki ba, amma za ta jarraba sa'arta. Lokaci guda sai ta samu kanta da jin kunyarsa, da a ce ba a wannan harka suka hadu ba da babu abin da zai hana Rabi'at ta furta masa kalmar so.
"Fatima!" ta ji ya kira sunanta, "nice name, kin ga kuwa sunan mahaifiyata ne, Fatima kina kwana a wani wuri ne ban da otal?" ya tambaye ta.
"Me ya sa ka yi mini wannan tambayar?"
"Saboda babu wurin da na tsani kwana kamar otal, saboda wuri ne da kowa da kowa ke zuwa, ciki har da idon sani, ni kuma shaf-shaf nake al'amurana, shi ya sa na ware gida na musamman a Kundila inda nake saukar baki na musamman irinku."
Yanzu can muka nufa kenan? "
" Ko ba ki son ganin guest house dina ne?"
"Ba ka da matsala da ni in dai ta wannan ne. Matarka fa?"
"Ba ni da aure Fatima. Me ya sa kika tambaye ni? Kina Tsammanin zan yi aure ne in dauki nauyin wata mace ta hana ni sakewa da ku? Wannan ba ya tsarina. Ki saki jikinki, inda za mu je babu kowa."
Ya karya kwana suka shiga rukunin gidajen Kundila. Bayan 'yar tafiya kadan suka iso kofar wani gida tsararre mai katuwar kofa.
Alhaji Sani ya danna hon, wani dattijon maigadi ya taso ya bude kofar.
"Barka da zuwa Alhaji," ya dan rankwafa sannan ya bi motar da kallo cike da mamakin yadda maigidansa ke kawo mace gidan nan duk sati.

Zan ci gaba..KWANAN GIDA

MUHAMMAD LAWAN PRP

6.
Bayan Alhaji Sani ya ajiye motarsa a wurin ajiye motoci sai ya bude wa Rabi'at kofa ta fito, suka nufi kofar gidan ta ciki.
Ya sa mabudi ya bude suka shiga.
Tun da Rabi'at take ba ta taba ganin tsararre kuma katon falo kamar wannan ba. Ban da dumin na'urar dumama daki da ya yi mata maraba, da ta taka lallausan kafet din dakin sai ta ji kafarta na nutsewa, da kyar take ciro ta.
Alhaji Sani ya zarce da ita dakin kwanansa. A nan ta zama kamar wata 'yar kauye, tun daga kan gadon kwanciya zuwa ragowar kayan amfani na wuta dake dakin zuwa bandakin da ya nuna mata babu wanda Rabi'at ta taba gani. Lokaci guda ta tabbatar wa kanta fatsarta ta yi kamu.
Kai tsaye ta cire kayanta ta bar shimi da wani matsattsen wando, don ta nuna masa yadda yake ji da tsararren gida haka take ji da kyakkyawar surarta.
Ta yi sa'a kuwa ta fizgi hankalin gogan, wanda yake kallon ta daga sama har kasa yana hadiyar yawu. Zuwa can ya kauda kai kamar abin bai dame shi ba, yayin da ta kwanta a kan gadon ta yi dai-dai tana fadin, "Na gaji Alhaji."
"Ko dai kina son ki ce min yunwa kike ji? Ga shi dare ya fara yi. Ya ya kika ga gidan ya yi miki?"
Ta dube shi daga kwance, "Ya yi mana, kai dai kawai saki ingarmanka ka yi ta sukuwa sai inda mai ya kare maka, amma fa ka san mu pay before service ne. Me za ka bayar?" tana kashe masa idanu da fari.
"Kada wannan ya dame ki," ya baro inda yake zaune ya nufo wurinta, "ke din na na ga ta daban ce. Za ki iya karbar dubu hamsin a kwana daya?" ya zauna kusa da ita.
"Babu damuwa, kai nake saurare. Me kake nufi da kwana daya?" ta tambaye shi.
"Fatima ke nan, ina da ka'idoji, duk wadda na dauka kwana uku take yi a gidan nan, sannan duk zirga-zirgar da za ta yi a gidan kada ta wuce dakin Kwanan nan da falo. Akwai kayan abinci a kicin, akwai kayan shaye-shaye a firij masu sanyi. Za ki iya shiga ki zabi wanda ranki yake so. Sannan nakan fita duk safiya bana dawowa sai da yamma."
Rabi'at ta ji wani sanyi a ranta, "Shikenan ka'idojin naka? Ni na dauka ma wani abin ne mai wuya, ni na ji ka kwanta min a rai ma, zan so a ce mu kasance tare har abada."
Wani irin kallo ya yi mata mai wuyar fassarawa. Sannan ya mike ya nufi bandaki.
Ta biyo shi.
"Tare za mu yi wankan."
Dariya ya yi tare da kai mata duka.
Tare suka yi wanka, tare suka kwana, bayan ya ba ta kudinta a hannu. Haka nan da safe ya fita kamar yadda ya gaya mata.

Ina nan tafe..KWANAN GIDA

MUHAMMAD LAWAN PRP

7.
Tafiya suke a cikin motar ba tare da yi wa juna magana ba, Nusaiba na murnar ta kubuta daga sharrin Alhaji Yunus wanda ta fahimci yana farautar kawarta kamar yadda kyanwa ke farautar bera. Shi kuma dan barikin da ya dauke ta zuciyarsa cike da murnar yau ya yi babban kamu; ya samu irin macen da yake kwadayi, mai sura irin ta Nusaiba.
Iliya ya san ya samu kudin da zai hole kafin mahaifinsa ya dawo daga tafiyar da ya yi har ya gane yana kai mata guest house dinsa yana shanawa.
Iliya ya san halin babansa sarai! Kasancewar mahaifin nasa hamshakin dan siyasa ne a jihar, to kuma ya san a bangaren bariki uban nasa ba aljihun baya ba ne, musamman ya ware wannan gida da Iliya zai kai Nusaiba don ya yi Kwanan gida da ita.
In da a ce mahaifinsa Sanata Bara'u Madugu ya san Iliya ya gane gidan babu abin da zai hana shi fatattakar sa ya kore shi, amma ina! Shi kansa wani lokacin in ya sa kafarsa ya tsallake ya bar kasar sai ya share watanni uku bai dawo ba, ko tunanin mutanen da suka tura shi wakilci majalisa ba ya yi.
Don haka a wannan karon ma da mahaifin nasa ya bar kasar kullum sai Iliya ya dauki mota ya fita yawon bariki ya kai mace gidan babansa na shakatawa.
Duk da magriba ta yi kuma duhu ya fara shiga, hasken fitilar motarsa bai kasa hasko masa wasu mutane dake tsaye da motarsu a tsakiyar hanya suna dago masa hannu alamar ya tsaya ba.
Da fari Iliya ya yi Tsammanin ko 'yan sanda ne, amma cikin gaggawa sai ya sauya tunanin sa, ai' yan sanda babu abin da zai tsaida su a wannan titin a daidai wannan lokaci, kuma ma mutanen dake daga masa hannu ba su yi kama da ma'aikata ba, kawai dai wadansu 'yan rainin hankali ne.
Sai da Iliya ya zo dab da su kamar zai tsaya sai kuma ya kara wa motarsa wuta ya wuce a guje kamar an koro shi.
Mutanen suka tsaya sororo suna kallonsa. A lokaci guda Alhaji Yunus ya karaso wurin a fusace, ya bude kofar motar ya fito, ko kashe motar bai yi ba ya fara zaginsu.
"Ba ku da hankali ne? Me ya sa kuka bar shi ya wuce? Matata ce a ciki fa! " ya jaddada musu.
Sannan ya koma cikin motar ya sa giya ya rufa wa motar Iliya baya. Sauran kattin biyu dake tsaye su ma suka zabura suka fada motarsu, suka rufa wa motar Alhaji Yunus baya.
Iliya ya waiwaya baya, nan take ya fahimci ana bin sa, cike da zargi ya dubi Nusaiba da ke zaune kusa da shi.
Murmushi ya yi kawai sannan ya kashe fitila ya murza sitiyarin motar ya shiga wata kwana ya tsaya cik!
A lokacin da Alhaji Yunus ya iso kan kwanar sai suka yi kunnen doki da motar da ya qunsa sa su tare su Nusaiba. Don haka sai suka tsaida motocin suka fara waige-waige. Daga nan sai suka fara lababawa cikin duhu suna nufar inda suke Tsammanin nan motar Iliya ta shiga.
Shi kuwa da ya fuskanci sun fito daga motarsu sai ya juyo ya yi kwana.
Suna cikin leke a duhu sai tashin mota kawai suka ji. Alhaji Yunus ya ciro bindiga daga aljihun sa ya saita tayar motar, ya kuwa saki kunamar bindigar.
Tas! Karar harsashi ta cika kunnuwan mutanen dake wajen, sannu a hankali kuma motar da kanta ta nemi wuri ta tsaya, bayan ta yi 'yar gajeriyar tafiya.
Wani murmushin mugunta ya subuce daga bakinsa sannan cikin hanzari ya umarci yaransa biyu dake tsaye cewa su je su fito masa da matarsa.
Nusaiba da Iliya ba su taba zaton wasan kwaikwayon zai rikide ya koma yaki ba, don haka sai suka fito suka ranta a na kare, a tsammaninsu 'yan fashi ne.
Cikin xafin nama kuwa suka kure wa Nusaiba gudu suka kama ta, daya ya rufe mata baki suka cusa ta a motarsu da karfin tsiya.
"Ina za mu kai ta Oga?" daya mutumin ya tambayi Alhaji Yunus.
"Ku kai ta gidana da ke Ring road."
Daga nan ya shiga tasa motar ya rufa musu baya.

Babu jimawa motar 'yan sanda ta karaso wurin.

Cikin tafiyar da ba ta wuce rabin sa' a ba suka karasa gidan da ya ba su umarni su kai Nusaiba, babu dadewa shi ma ya karaso. Bayan sun fito ne sai suka shiga da Nusaiba wani daki.
Alhaji Yunus ya shigo, bayan ya kare mata kallo ya fahimci ba ta cikin hayyacinta sai ya ce mata.
"Ina 'yar uwarki Usaina?"
Ta dube shi kurum amma ta kasa cewa komai.
"Ki kwantar da hankalinki ni ba dan yankan kai ba ne, kawai labarin kawarki za ki ba ni da in da zan je na same ta, sai in kyale ki ki tafi."
Nusaiba ta dubi Alhaji Yunus, wanda duksa' adda ta kalle shi sai gabanta ya fadi, ta ce cike da tsoro da rudewa.
" Ni ban san wata Usaina ba."
"Kada ki bata mana lokaci kuma ki bata wa kanki akan abin da bai taka kara ya karya ba 'yan mata."
Daga nan ya yi shiru, ya tabbatar iyaka gaskiyarta ta fada, domin a yadda ya fahimci ta tsorata da su da irin aikinsu zai yi wahala ta iya yi masa karya, don haka sai ya canza dabara.
"A kawayenki ba wata mai suna Usaina?" Ya tambaye ta cike da zakuwa, don ya fahimci ta fara laushi.
Ta yi shiru kafin ta ce, "Gaskiya ba zan iya tuna wata mai wannan sunan ba, sai dai..."

"Sai dai me? Wadda na gan ku tare shekaranjiya ya ya sunanta?"
"Sai a sannan ta fahimci inda wannan mugun mutumin ya dosa da ta dada kallonsa, tabbas! Wannan shi ne mutumin da...
"Kin tuna da ni ko yarinya? Na yi miki uzuri, na san ba ki gane ni ba shi ya sa kika wulakanta ni, " ya yi dariya.
" Da ta satar mini kudi dubu dari biyu nawa ta ba ki? Ko dai rabawa kuka yi? Idan duk ba za ki ba a ni amsar tambayoyin nan ba zan kyale ki zuwa gobe da daddare don ki yi tunani, kin san komai yana bukatar nutsuwa."

Daga nan ya fita daga dakin bayan ya kulle kofar.

Zan Dakata a nan. Sai gobe..KWANAN GIDA

muhammad lawan prp

8.
Nusaiba ta yi zugum ! Tana tunanin halin da ta tsinci kanta, tana addu'ar Allah Ya sa mutumin nan ba dan yankan kai ba ne ya fake da neman kawarta. Zuciyarta ta tuno mata dalilanta na shiga bariki, a ciki har da Alhaji Ado Garabasa ; wani babban dan kasuwa kuma dan siyasa, shi ne ya fara bata mata rayuwa akan wata bukata ta kashin kanta, daga baya ya mayar da ita jujin zubawar shara yanzu dai ta yanke shawarar fada wa mutumin nan gaskiya idan ya dawo gobe, ko don ta tsira da rayuwarta, ta koma garinsu ta rayu kamar sauran mutanen kirki.
Da wannan tunanin bacci ya dauke ta. Sai ji ta yi ana taba ta, ta yi zumbur ta tashi zaune.
Daya daga cikin mutanen da suka kamo ta ne ya shigo rike da filet na abinci da murfinsa, da ruwan leda (pure water) guda daya.
Ya wage mummunan bakinsa yana yi mata dariya.
"Oga ne ya ce a kawo miki abinci, kuma ki daure ki ci, babu kyau kwana da yunwa," ya ajiye mata filet din a kasan kafet.
Ta bi shi da kallo kurum, bayan ta takure kanta a jikin bango, domin a yadda ta gan shi shi ma ba zai yi imani ba, kada ya cutar da rayuwarta.
Ya juya ya fita ba tare da ya sake magana ba.
Ta tashi da gudu ta sa sakata ta kulle ta koma ta zauna tana tunanin cin abincin don gudun ko an sa wani abu, amma da ta tuna yadda yunwa ke nukurkusar ta sai ta yi shahada ta bude filet din, shinkafa ce dafa - duka tana tiriri, har da naman kaza a kai, da cokalin roba.
Ta dade tana kallon abincin kafin ta fara ci. Bayan ta gamsu ba ta ga wani alamun an sa wani abu ba. Ta ci iya cin ta ta sha ruwa, ta koma ta kwanta tana nazarin makomarta.
***

BABI NA UKU
Bayan Kwana Biyu

Kwanan Rabi'at biyu a gidan Alhaji Sani, a bisa ka'idar da suka yi shi da ita, gobe ne za su rabu. Ta yi kokarin kiyaye ka'idoji da dokokin da ya shimfida mata.
Kamar yadda ya fada mata, haka ce ta kasance. Idan ya fita tun safe ba ya dawowa sai duhu ya shiga. Tana diban abinci da abin sha wanda ya kwanta mata a rai ta yi amfani da su.
Amma tana tambayar kanta, ko me ya sa ya iyakance mata wasu wurare a cikin gidan da cewa kada ta shiga?
Ba ta da amsa, face ta shiga da kanta ta gani, kuma tana bukatar yin haka kafin ya dawo su yi kwanan karshe shi da ita a tsarin kwanan gidan da ya dauke ta.
Rabi'atu ta yi amfani da safayar mabudin da ya bar mata ta dinga jarraba bude dakunan gidan, amma ba ta samu sa'ar bude su ba, ta sha wahala, ga shi duhu ya fara shigowa, a ka'ida lokacin dawowarsa ya yi kuma tana cike da mamakin abin da ya sa ya dade bai dawo ba.
Bayan ta zauna don ta huta ne abin kamar almara sai ta hango curin wasu mabudai a sakale a karkashin wani teburi na gilashi.
Da hanzari kamar wadda aka tsikara, ta mike zumbur! Ta ciro su ta kuma shiga jarraba su a dakunan da sauran sassan gidan. Duk wanda ta jarraba ta ga bai yi ba sai ta sake zura wani. Da haka ta samu nasarar bude dakuna uku.
Daki na farko, ba ta samu komai ba sai wata katuwar sif da ta yi kokarin bude ta da wani mabudi, babu komai a ciki sai kayan sawar Alhaji Sani, sun fi kala hamsin. Ta yi saurin mayarwa ta rufe ta fito daga dakin ta shiga wani.
A daki na biyu ne ta ga abin da ya ba ta mamaki, bayan ta balle wata kwaba, suturun mata ta gani kala-kala masu dan karen tsada, idan ba don tana cikin hadari ba da babu abin da zai hana ta dibar wasu daga ciki.
Ta baro wannan dakin bayan ta kulle shi, a lokacin duhu ya fara yi. Har zuwa wannan lokacin ba ta ji motsin dawowar Alhaji Sani ba. Ga alama tana da sauran lokaci, za ta karashe binciken kafin ta ji dirin motarsa.
Ta nufi daki na uku.
Sai a mabudi na goma sha uku cikin sha biyar din dake hannunsa ta samu damar bude dakin.
Dakin ya tsaru, shi ma dai kamar sauran dakunan, babu wani tarkacen kirki a ciki, in ka dauke wani lallausan jan kilishin da ya mamaye dakin sai kujerun zama manya-manya dake fiskantar juna a bangon Kudu da na arewa, akwai wani katon firij da Rabi'at ba ta taba ganin irinsa ba a tsarin yanayi, shi ya ja hankalinta, kuma shi ta nufa don ta bude.
Ta kama marikin firij din ta mirda amma sai ta ji gagau! Da ta kula sai ta ga ramin da ake zura mabudi a kasan mamurdin. Ta jarraba mabudan hannunta amma suka ki budewa, don haka sai ta sa karfin tsiya ta doki abin murdawar zuwa kasa sau biyu, nan take kuwa ya bude.
Kwakwalwarta ta hargitsa, zuciyarta ta tashi, hankalinta ya dugunzuma. Ta fi mintuna biyar kafin ta dawo hankalinta a bisa abin da ta gani.
A jere reras! Bisa farantai masu tsada kuma a gashe, naman sassan jikin mata ne.
Sai a sannan ta ji dirin dawowar motar Alhaji.

Zan ci gaba..KWANAN GIDA

MUHAMAD LAWAN PRP

9.
Lokaci guda al'amura suka cabe mata, tunaninta ya kasu kashi daban - dabam. Shin kulle firjin za ta yi ta fita ta kulle dakin, ko kuwa sulalewa za ta yi ta gudu? Ta tabbata rutsa ta a dakin nan da Alhaji ke shirin yi na nufin kawo karshen rayuwarta. Za ta tsaya sakatoto ne har a zo a same ta a yanka ta a yanke sassan je jikinta a gasa, ko kuwa za ta yi ta maza ta kwaci kanta.
Tana nan tsaye duk jikinta na rawa, kafafuwanta na neman gaza daukar ta, sai ta ji kamar motsi a bayan gidan.
Ta matsa jikin wata taga mai gilasai ababan zarewa ta janye labulen tagar ta leka.
Abin da gani ya dugunzuma hankalinta, har ta dinga addu'ar ina ma mafarki take yi ba gaske ba, ina ma ta hakura ta ci gaba da zama da talaucinta har abada. Amma ina! Kwadayi ba zai bari ba.
Alhaji Sani na tsaye tare da wasu karti guda biyu suna magana a cikin duhun dare.
Rabi'at ba ta jin me suke fada, amma ta tabbatar suna shawarwarin irin kisan da za su yi mata ne, abin da take ganin ko sama da kasa za su hade ba za ta ba su dama ba.
Ta hangi Alhaji Sani ya dauko waya daga aljihunsa. Kai tsaye ya sa a kunnensa wanda ya tabbatar mata kiran sa aka yi.
Ya koma gefe yana magana.
Tun kafin ya gama ya yi wa mutanen biyu inkiya da su bar wurin, suka kuwa bace cikin abin da bai wuce dakiku uku ba.
Alhaji Sani ya kashe ya kashe wayar, daga nan ya zagayo ya nufo babbar kofar shigowa falon.
Da sauri ta saki labulen tagar, zuciyarta na dukan tara-tara, gabadaya duniyar ta yi mata kunci, ta rasa gane bambancinta da wanda ke cikin kabari. Ta dawo tsakiyar dakin tana tunanin mafita.
"Fatima!" ta ji sautin muryar Alhaji Sani yana kiran ta sautin da ya yi kama da saukar aradu a tsakiyar kwakwalwarta. A hankali ta ji sautin yana matsowa dakin da take.
Ta dubi dakin ta kowanne bangare don

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

2 Comments On KWANAN GIDA
avatar
hassan-5-6

1 year ago

Reply

godiya Allah biya

avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Kash

Please Login or Register in order to submit comment