Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kuma nan ne dakin kwananki idan kin dawo, ni daga can zan wuce kasuwa," bai jira ta yi magana ba ya wuce fuu!
Rabi'at ba ta da zabi sai kawai ta mike ta biyo shi, Alamomin tambaya cike taf! A fuskarta, zuciyarta na yi mata lissafin dawakan rano.
Zulai ta bi ta da kallo, "Allah Ya kiyaye. Sai kun dawo."
Tun da suka fara tafiya ba wanda ya yi magana, har zuwa sadda Malam Ya'u ya tare mai kabu-kabun babur kafa uku.
"Asibitin Murtala,"ya ce da shi.
'Me za mu yi a asibiti kuma?' Rabi'at ta tambayi kanta.
Ba ta san lokacin da suka gama ciniki da Malam Ya'u ba sai ji ta yi yana ce mata.
"Shiga mutafi Rabin Mama."
Ba ta tsaya gardama ba ta shiga babur din suka kama hanya.

Mhm!KWANAN GIDA

Muhammad Lawan Prp

15.
Ilyasu na zaune gaban DPO Rabe yana yi masa bayanin abin da ya faru a daren jiya, lokacin da wadansu suka tare shi shi da budurwarsa suka harbi tayar motarsa suka kuma gudu da budurwar tasa, yayin da shi kuma ya sha da kyar.
DPO Rabe ya yi shiru yana mamakin yadda a wannan lokaci da ake fama da tashe-tashen hankula a wannan gari, amma har wasu ke da karfin halin aikata wani laifi makamancin wanda ake fama da shi a garin. Tun daren jiya da yaransa suka kawo masa rahoton sun ji karar bindiga a wani lungu a cikin garin sun kuma je, amma sun tarar da babu kowa a wurin sai wani saurayi dake amsa sunan Ilyasu, kuma sun tambaye shi abin da ya faru ya yi musu bayani filla-filla, don haka suka dauki bayanin nasa tare da cewa ya koma da safe ya zo ya yi musu bayani, DPO yake faman nazari.
A yanzu da Ilyasu ke gabansa ya kammala bayanin.
"Za ka iya shaida motocin?" DPO ya tambaye shi.
"Duk da dai da dare ne amma na shaida su, don kuwa dayar fara ce kirar Henensi, yayin da dayar ko dai baka ce ko launin shanshambale."
"Lambobinsu fa?"
Ya yi shiru, "Nan fa daya! Ba zan iya tunawa ba. Illa dai kawai na gane su uku ne mutanen, kuma shi wannan na cikin farar motar shi ne babbansu, don kuwa na saci jin abin da yake fada musu sama - sama."
"Me ka ji yana cewa?" DPO yana cizon biron da ke hannunsa.
"Ai sama - sama na ce, domin bana gane abin da yake fada saboda yana da saurin baki."
"DPO ya yi shiru yana hada biyu da biyu ko zai samu hudu, amma mafi girman tunaninsa na ga yadda zai samu wani abu daga wannan saurayin da ya yi imanin ubansa daya daga cikin manyan kusoshi ne a jihar. Ko ma dai me ake ciki yana ganin wannan ba wani kes ba ne da za a daga hankali a kansa.
"Budurwarka ce ka tabbata?"
Ran Ilyasu ya fara baci, "Budurwata ce mana, duk da dai yau muka hadu da ita, amma ina tausaya wa hannun da ta fada, domin a yadda na fahimci mutanen nan ba su da imani."
DPO ya yi shiru yana mamakin yadda kes irin wannan yake yawan shigo musu, duk da halin da ake ciki.
Ya sosa sankonsa da biro, "Yanzu me kake so a yi?"
"Ku kuke da hakkin ku binciko wadanda suka sace ta, domin a gaskiya ina son aurenta."
DPO ya jawo wani fayil ya yi 'yan rubuce - rubuce, daga nan ya kira wani sajen, wanda kes din ke hannunsa ya hada shi da Ilyasun.
"Nura ku je ya ba ka kamannin yarinyar da kuma titin da yake zargin an bi da ita."
Sajen Nura ya kame bayan ya sara. Daga nan suka fita waje shi da Iliya
Na gaji.KWANAN GIDA

Muhammad Lawan Prp

16.
Ba su dade da fita ba ya ji karar waya daga can dakin da Rabi'at ke kwana.
Gabansa ya fadi, domin yana cikin damuwar da ba ya bukatar sabon al'amarin da zai dagula masa lissafi.
Ya yi iyaka tunaninsa, daga can ya samu amsa, samun amsar da ya yi dai-dai da samuwar wani sanyi a zuciyarsa, babu shakka Rabi'atu ta gudu ta bar wayarta a dakin kwanansu, in haka ne kuwa to ta bar wani wagegen gibin da zai yi amfani da shi wajen samo ta.
Da sauri ya nufi dakin nasa ya daga wayar.
"Hello! Tun dazu nake jira a bugo. Wane ne?"
Daga can vangaren aka yi shiru ba a amsa ba, ya kuma duban wayar, har yanzu ba a kashe ba. Ya kula da sunan da ke kai, 'My friend,' namiji ne ko mace?
Ya yi saurin mayar da wayar kunnensa.
"Hello! Wane ne?" ya kuma tambaya, gabansa sai faman faduwa yake, yana ganin ga hanyar da zai bi ya samu abin da yake so amma an ki a yi magana.
"Idan ba za a yi magana ba zan kashe. Wane irin iskanci ne wannan?"
"Ni ce!" ya ji an fada.
"Ke ce wa? Me za ki tambaya?"
A halin yanzu ya nutsu, kwakwalwarsa tana lissafo masa abubuwa da yawa, kamar yadda zuciyarsa ke azarbabin sanin alakar wanda ya bugo wayar da Rabi'at, wadda ya fi sani da suna Fatima.
"Ina son yin magana da Rabi'at ne, idan tana kusa ka ba ta wayar."
"Rabi'at ko Fatima?" ya tambaya, "ta fita dazu, ke daga ina kike waya in ta dawo sai a gaya mata, kuma wa za a ce ya bugo?"
"A ina take yanzu? Wacce unguwa kenan? Kai kuma wane ne?"
Daga can bangaren Alhaji Yunus ya kura wa Nusaiba ido, bindigarsa tana fuskantar ta yayin da ita kuma take ta faman zuba uban surutu ya daka mata tsawa.
"Ki bude hands-free mana wawiya kawai! "
Hannunta na rawa ta danna sifiikar wayar waje. Alhaji Yunus ya fara jin abin da ake fada garai-garai.
" Duk wadannan tambayoyin kike sa ran zan amsa miki?" aka fada daga daya bangaren, "me kike nema da ita, kuma me ye alakanta?"
A rude ta dubi Alhaji Yunus, shi kuma ya yi mata inkiya da ta fadi sunanta.
"Ni kawarta ce. Sunana Nusaiba."
"Ah! Nusaiba? Kin ga kuwa tana ba ni labarinki sosai. Allah Sarki! Ai sunan ne ban gane ba, na ga an sa 'my friend' kin ga kuwa friend ai suna da yawa. Malama Nusaiba kina ina ne yanzu?"
Nusaiba ta ji sanyi a ranta, domin ta fara jiyo kamshin Rabi'at, abin da ta tabbatar in dai Alhaji Yunus ya samu tabbacin samun ta to kuwa zai bar ta ta tafi, don haka sai ta dubi Alhaji Yunus dake tsaye shi ma yana murmushi, ya yi mata inkiya da shi ma ta tambaye shi inda yake don ta zo ta same shi.
"Kai ma kana ina yanzu? Domin ina son ba ta kudinta da ta ba ni Ajiya ne kwana uku da suka wuce, saboda gobe nake son barin garin ni ma."
Ta fada da kwarin gwiwa.
Alhaji Sani ya kwatanta wa Nusaiba inda gidansa yake a Kundila, kwatancen da za ta gane. Tuni Alhaji Yunus ya haddace kwatancen, ya fara tunanin yadda zai yi da Nusaiba, duk da haka ba ya son ya sake ta da wuri, ya fi so sai ya yi kwalli da Rabi'at ido da ido.
Maganar Alhaji Sani ta cikin waya ta katse masa tunaninsa.
"Ina jiran ki fa!" Alhaji Sani ya fada.
'Za ka ci ubanka ne kai ma,' Alhaji Yunus ya fada a zuciyarsa.
"To shikenan sai kin iso," daga nan ya kashe wayar.
Alhaji Yunusa ya warce wayar daga Hannunta tun kafin ta mika masa, sannan ya mayar da bindigarsa aljihu.
"Kin tsallake wannan siradin yarinya, saura ki kai mu gidan, ki shiga don mu tabbatar tana gurinsa daga nan sai mu kyale ki ki tafi. Ki yi hakuri, kawarki ce ta ja miki. Shi ya sa aka ce ka yi abota da kowa amma banda munafuki da barawo, nan gaba ki san da wanda za ki yi abota kin ji yarinya."
Nusaiba ta gyada kai, ga alama ta dauki nasihar da ya yi mata.
Ta wuce gaba suka nufi kofar fita.
"Ina za mu je?" ta waiwayo ta tambaye shi.
"Dakina za mu je ki ba ni wani labari a takaice, kafin mu wuce wurin ja'irar kawarki."
Nusaiba ta saki baki tana kallonsa.
"Wanne labari kuma zan ba ka?"
"Labarin Alhaji Ado Garabasa mana."

Zan ci gaba.KWANAN GIDA

Muhammad Lawan Prp
with me
Yusuf Ilyasu Abdulkadir

17.
Sun zauna a dakinsa kamar yadda ya umarce ta. Babu komai a dakin sai wani gadon kwanciya da dima-diman kujeru na zama guda biyu, akwai tebur a tsakiyar dakin, banda makeken kilishin da ya mamaye dakin, kore da shi shar! Alhaji Yunusa ya umarci Nusaiba da ta zauna a daya daga cikin kujerun, shi kuma ya tsaya a bakin kofar ya tokare hannun hagunsa da kugunsa.
"A ina kika san Alhaji Ado?"
Ba ta yi gardama ba wannan karon, babbar bukatar ta ta bi umarninsa don ya sake ta.
"Dadirona ne, ya sha ajiye ni a wani gida yana daukar nauyina," ta ba shi amsa cike da damuwa.
"Har yanzu, ko kuwa ba ki tare da shi?"
"A'a yanzu ba ma tare, rabona da ganinsa ma shekaru biyu kenan," tana yatsina fuska.
"Kada ki damu Nusaiba, labarinsa kawai nake so, domin na ga kin fara gajiya da kasancewa tare da ni, ga kuma yawan tambaya ko?"
Ba ta ce komai ba wannan karon illa bin sa kawai da ta yi da kallo.
"Kada ki daga hankalinki ki dauka ko shi ma laifi ya yi min nake so ki nemo min shi. Ina son sanin yadda yake gudanar da harkokinsa na yau da kullum ne, guraren shakatawarsa, abincin da ya fi so da sauransu... Ko ya taba yi miki wani abu ne?" ya tambaye ta, domin ya fahimci kamar ba ta son maganar mutumin.
Ta daga kai sama, alamar 'E'.
"Me ya yi miki?"
"Shi ne ya saka ni a wannan harkar, shi ne ya fara bata mini rayuwata, tun lokacin da na je neman aiki kamfaninsa da takarduna na Diploma, ya ce ba zai ba ni aiki ba har sai na amince da shi. Ni kuma a lokacin ina cikin matsanancin hali; domin iyayena da aikin da zan samu suka dogara, ga babana na fama da ciwon asma. Da kyar Ado ya ba ni kudin da na saya masa magani, a ranar da ya fara sanina 'ya mace ke nan.
Tun daga ranar muka kulla huldar banza da shi bayan ya samar mini aikin.
Bayan wasu shekaru jarinsa ya karye, ya cefanar da kamfanin nasa, dole na rasa aiki na koma bin titi. Daga baya da aka buga kugen siyasa ban san ya ya aka yi ba sai na ga ya tsaKWANAN GIDA

Muhammad Lawan Prp

with
Yusuf Ilyasu Abdulkadir

18.
Ya yi shiru kafin ya ci gaba, "Tun lokacin siyasa a tenuwa ta farko a shekarun baya ni ne sarkin yakin neman zabensa (Chief campaign) a lokacin ba shi da wani aboki fiye da Alhaji Madugu, wanda jam'iyyarsu daya, shi yana takarar dan majalisar jiha yayin da Alhaji Madugu ke takarar sanata a arewacin jihar nan. A cikin wannan hali na sha wahala don ganin sun kai gaci, mu ne zuwa kauyuka muna kwana, mu ne karade lunguna da sakuna ba dare ba rana muna yawo, wani lokacin da kudin aljihuna nake yin yakin. Sai da ta kai na kwashe duk wani jarina na kasuwanci na zuba a harkar, kudina kuwa da nake ajiyewa a banki sai da na tatike lalitar tawa, in kika dauke dubu dari da na tsira da ita a karshe. Duk ina yin wannan ne da nufin idan mun samu gwamnati a hannu mu fanshe a dukiyar talakawa.
A lokacin da zabe ya karato ne aka bukaci kudin da za a raba wa 'yan jagaliya su tada hargitsi ranar zabe da kuma wadanda za mu ba aikin sace akwatuna idan muka ga za mu sha kaye aka rasa, ya nuna min ba shi da kudi, a dole na lalube ragowar kudin muka zuba a kamfen. Ganin haka sai ya shawarce ni da na shiga wata kungiya ta manyan 'yan siyasa da wasu gwasake a manyan kasar nan, na kuwa amince na biye masa. A nan na hadu da manyan mutane da suka shahara a fagen siyasa."
Ya dakata ya ajiye numfashi sannan ya ce, "Lokacin da zabe ya zo suka yi sa'a suka lashe kujeru talatin da takwas daga cikin arba'in da hudu da ake da su a jihar nan, sannan da magudi da komai suka lashe kujera lamba daya (ta gwanna).
Alhaji Ado garabasa da Alhaji Madugu su ma sun tsallake zaben, bayan tafka mummunan magudi.
Hm! Kin san me ya faru a karshe?"
Kallonsa kawai take yi tana mamakin yadda ya balle da surutu kamar rediyo.
"Bana son fada, domin zuciyata tafarfasa take yi. A karshe dai da na matsa da tuhumar matsayina sai ya turo 'yan jagaliyarsa su kaddamar mini. Ganin haka sai na tsallake na koma legas, har sai da kura ta lafa sannan na dKWANAN GIDA

Muhammad Lawan Prp

WITH

Yusuf Ilyasu Abdulkadir

19.
Shiru ta yi babu amsa, wanda ya tabbatar masa yarinyar ta tsane shi, amma wannan bai dame shi ba, duk da ya fi ganin laifin Rabi'at, don ita ta ja mata. Da a ce bai gan su tare ba babu abin da zai sa ya kama ta ya yi garkuwa da ita.
"Za ki ci abinci?" ya tambaye ta, a yayin da ya kakaro wani murmushi mai kama da yake.
Ta girgiza kai, "A'a bana jin yunwa."
"Kada ki cuci kanki. Ko kunya ta kike ji na ba ki wuri?" ya mike tsaye.
Bin sa kurum ta yi da kallo.
"Bari in sa a kawo miki."
"A'a ka bar shi. Na koshi."
Ya dube ta kawai, shi ma ya san ba za ta ci ba, domin tun da ya kawo ta gidan ya lura hankalinta bai kwanta ba. Yana son lallaba ta ne kawai ta saki jiki da shi don ya yi amfani da ita wajen kafa wa Alhaji Ado tarkon da zai kama shi. Ya koma ya zauna.
"Hm! Nusaiba ke nan. Ki saki jikinki, ba wani abu da zai same ki a nan, matukar dai kin yi min biyayya. Tashi mu je gun Rabi'at kin ga dare yana dada yi, kada mu samu matsala."
Nusaiba ta mike tsaye cike da fargaba. Ko shakka babu in Allah Ya sa ta kubuta hannun wannan azzalumin, tana sa ran za ta yi bankwana da bariki. Domin duk dadewarta a bariki ba ta taba shiga hadari makamancin wannan ba. Tana dai taba shaye-shaye na miyagun kwayoyi da kuma benelin, emzolyn da roci da sauransu. Sai kuma yaudarar samari da alhazan birni da take dan yi tana amshe musu kudi, amma ba a taba hada baki da ita an ji wa wani ciwo ba, ballantana a kai ga kisa. Tana tunanin abin da zai samu aminiyarta in dai har wannan mugun mutumin ya hada ido da ita, tana fatan kafin su je gidan Rabi'at ta gudu...'
Ta yi maza ta sauya tunani, ai kuwa gudun Rabi'atu na nufin ci gaba da zama da Alhaji Yunus, wanda take kallonsa tamkar wani mala'ikan mutuwa da zai iya daukar ran kowane mutum a kowane lokaci.
Me yake nufi ma da bayyana mata sirrinsa a yanzu?
Wannan wani abu ne da lokaci zai nuna.

Lokacin da suka fito daga gidan goma na dare ta yi. Alhaji Yunus ya kira yaransa biyu suka yi kus-kus, kafin daga bisani su shiga motarsa shi da Nusaiba su kama hanya.
Babu wanda ya yi magana a cikin motar, har suka isa Kundila. Suka bi kwatancen da Alhaji Sani ya yi musu. Suka iske gidan yadda ya fada, suka danna ham sau biyu.
Alhaji Yunus ya shafa bindigarsa.

Allah Ya ara mana lokaci.KWANAN GIDA

Muhammad Lawan Prp

20.
Rabi'atu ta yi kasake tana duban mahaifinta cike da damuwa, ta kasa magana sai hawaye da ya fara zubo mata ba tare da ta sani ba. Duk duniya babu wanda ta fi kauna fiye da mahaifinta, haka kuma da a ce sa'adda ta fara bariki ya gan ta ya tsawatar mata ta tabbata da sai ta bari, saboda tana gudun bacin ransa.
"Kukan me kike yi kuma?" mahaifiyarta ta katse ta, sai a sannan ta dubi fuskar 'yar tata.
"Daga ina ki ke ma tukuna, na gan ki kozai-kozai haka?"
Rabi'atu ta share kwalla. Yanzu ba lokacin bada labari ba ne, ballantana ta gaya wa wani halin da take ciki. Abu daya take bukata; ta samu ta nutsu sannan ta canza kayan dake jikinta, don haka sai kawai ta dubi mahaifiyarta.
"Me ya samu Alhaji?"
"Hawan jininsa ne ya tashi, sakamakon azabar da kika gaba masa."
"Ni Mama, me na yi wa Alhaji? Ina cikin damuwa ku taimake ni Mama."
Da mahaifiyarta da Malam Ya'u suka zura mata ido saboda jin abin da ke fitowa daga bakinta.
"Mene ne kuma ya faru Rabin Mama?" cewar Malam Ya'u. Tun da safe yake so ya tambaye ta saboda raunin da ya gani a jikinta, amma yake tunanin tun da Allah Ya sa ya gan ta da ranta da lafiyarta, to girman al'amarin rashin lafiyar mahaifinta shi ya zama ahammu da fara gani, ko da akwai abin da za ta iya yi a kai, domin tun da aka kwantar da shi jiya yake ta faman kiran sunanta.
Daga nan Malam Ya'u ya juya ga mahaifiyarta.
"Ni zan wuce kasuwa Binta, babu abin da kuke bukata?"
"Babu komai Malam. Mun gode Allah Ya saka da alkhairi bisa wannan dawainiya da kake yi da mu, Allah Ya ba ka mai yi maka kai ma."
"Babu komai," daga nan ya juya ga Rabi'at, "ba kuka za ki yi ba Rabin Mama, addu'a za ki yi; Allah Ya ba shi lafiya," ya juya ya fita.
Gyada kai kawai ta iya yi, daga nan ta zauna a kan wata kujera da aka tanadar don masu ziyara.
Shiru babu wanda ya yi magana, har zuwa lokacin da mahaifinta ya yi tari sau biyu sannan ya bude ido.
Tun sadda Rabi'at ta hangi ana ba shi abinci, ta kula idonsa a rufe yake, ko dai bacci ne ya dauke shi ko kuma zafin ciwo ne.
"Sannu Alhaji. Ka tashi?" in ji mahaifiyarta.
"Sannu Baba," cewar Rabi'at.
Ya juya ya kalle ta a hankali kawai bai ce komai ba, ya kauda kansa.
'Hawan jininsa ne ya tashi sakamakon azabar da kika gana masa.'
'wacce azaba na gana wa babana?' ta tambayi kanta.
'ko wani ya gaya masa ina kwana a waje ne?'
Babu amsa, don haka sai ta mayar da tunaninta baya ta debo abubuwa masu yawa ta zo da su zuciyarta. A da, mahaifinta yana fama da ciwon zuciya ne, tun bayan da karyewar arziki ta same shi. Haka kuma yana kwantawa jefi-jefi, kuma ta sha ji yana gaya wa mahaifiyarta ta kula da Rabi'at, ita kadai ce za ta share masa hawaye da damuwar da ta haddasa masa ciwon zuciyar dake damunsa, in dai har Allah Ya shirye ta ta hau turba madaidaiciya (kafin ta lalace ke nan) har zuwa yanzu da take tunani, ba ta san dalilin mahaifinta na fadin haka ba. Abu daya ta fahimta, shi ne yana kaunar ta fiye da mahaifiyarta.
Tana bukatar shiga bandaki, haka nan kuma in da hali ta samu ganin likita domin ya duba mata jikinta, saboda damuwar da ta shiga daga jiya zuwa yau sun sa ta manta da tata matsalar.
Don haka sai ta dubi mahaifiyarta.
"Akwai bandaki a kusa ko?"
Mahaifiyarta ta nuna mata.
Rabi'atu ta shiga. Jimawa kadan ta fito.
"Ina likitan yake?" ta tambayi mahaifiyarta.
"Ina ji yana ofishinsa."
Rabi'at ta mike. Tana iya jin mahaifinta sadda ya fara magana da mahaifiyarta kasa-kasa. Kamar za ta tsaya sai kawai ta ci gaba da tafiya.
Da tambaya ta isa ofishin likitan dake lura da mahaifinta.
Ta dade tana jira kafin a ba ta iznin ganin sa.
Ta wuce wani korido da aka kebe don marasa lafiya masu ido da kwalli.

Ofishin madaidaici ne, haka kuma teburin likitan faffada ne, yayin da likitan ya kasance siriri.
Ya ba ta umarni ta zauna.
"Any problem?" ya tambaye ta.
Ta yi masa bayanin mahaifinta, ta kuma ce masa ita 'yarsa ce. Daga karshe ta tambaye shi, ko nawa ake bukata kafin mahaifinta ya samu sauki.
Likitan ya bude wani fayil, "A zahirin gaskiya yana cikin matsanancin halin da yake bukatar kudi masu yawa don sayen magungunan da zai dinga amfani da su muddin ransa. Kuma in so samu ne ya fara amfani da magungunan nan da sa'a arba'in da takwas. In ba haka ba komai na iya faruwa."
Abubuwa biyu ne suka doki zuciyar Rabi'at a lokacin; na farko dai maganar da likitan ya fada, 'komai na iya faruwa' shin yana nufin mahaifinta zai iya mutuwa?
Abu na biyu kuma, tunanin a inda za ta samu kudin, duk da ba ta ji yawansu ba.
"To likita nawa ne kudin?" ta tambaya.
Ya dube ta sosai, idonsa boye cikin tabarau, "Dubu dari biyu da hamsin har da 'yan kwabbai," ya ce mata.
Ta dafe kirji, "Na shiga uku! A ina zan samu wannan kudin?"
"Za ki iya yin kokari a kai, matsalar ma ba mu da maganin a nan, da na yi wani abu."
Ba ta ji me likitan yake fada ba, illa kawai mikewa tsaye da ta yi ta kama hanyar fita. Amma da ta je harabar asibitin sai ta yi tsaye ta rike wani dogon karfe ta shiga sabon karatu.
***
Kwanan gida

Muhammad Lawan Prp

21.
Alhaji Sani ya ajiye wayar Rabi'at dake hannunsa
a kan gadon, tare da yin kwana, lokaci guda
kuma ya zauna.
'Yarinya za ki gane shayi ruwa ne, ba irinmu ake
yi wa bankada da tonon silili ba,' ya fada a ransa.
Daga nan ya waiga dama da shi, 'ai kuwa Rabi'at
sadda ta shigo gidan nan da jaka ta shigo, kuma
yana da tabbacin haka ta fita hannu ba komai.
Ya kamata ya duba jakarta ko zai samu karin
bayani game da ita.
Da sauri ya mike ya fita kamar wanda aka
zungura, ya fara laluben jakar a cikin falon gidan
amma bai samu komai ba, don haka da sauri ya
ci gaba da bincike dakunan gidan, amma shiru.
Sai bayan da ya gaji ne ya hangi jakar a gaban
madubin da ya tanada don duba kwalliyarsa, ya
dauke ta.
Bai yi mamaki ba da ya ji ba ta da nauyi sosai,
domin mafi yawanci jakunkunan mata babu
komai a ciki sai su jagira, hoda da jambaki. Ilai
kuwa, da ya bude su ya gani ; kayan kwalliyar
mata ne a ciki, duk da girman jakar, sai hoda
kala-kala da wani madubi mai siffar da'ira. A can
kasan jakar hannunsa ya tabo wani kati tare da
wasu abubuwa masu kama da takardu, ya yiwo
waje da su.
Shaf! Ya manta da kudin da ya ba ta kafin su
fara harka. Sai yanzu ya ga dubu dari biyu da
hamsin ('yan dubu-dubu) ya ajiye su a kan
teburin. Ya kwakulo daya abin mai kama da kati,
ba kama ba ce, katin cirar kudi a banki (ATM
card) ne mai dauke da sunan Rabi'atu, wanda
yake nuna ana ajiyar ne a bankin hada kan
al'umma (Unity bank).
"A hankali dabaru za su dinga zo min," Alhaji
Sani ya ce da kansa.
Tabbas! Duk inda yarinyar nan ta je tana bukatar
kudin kashewa, kuma ya tabbata iyakacin kudin
da ta mallaka ke nan (a tsammaninsa) don haka
in dai har ta cika makwadaiciya kuma kwararriyar
'yar bariki, to ya kamata ta dawo ta dauki katinta
na cirar kudi.
Dariya ya yi shi kadai, yayin da wata dabara ta
fado masa sai dai ba ya tsammanin za ta iya ci
wajen kama Rabi'atu, amma zai jarraba sa' arsa,
mai yiwuwa tarkonsa ya kama kurciya.
Zai ba wani daga cikin yaransa ya kai cigiyar
wannan jakar gidan rediyo da cewa tsintar ta aka
yi a kan hanya. Daga nan zai sa yaransa su sa
ido sosai a gidan, ko shi da kansa. Idan Allah Ya
kawo Rabi'at karbar kayanta sai ya yi amfani da
wannan damar ya bi ta don ya gano
makwancinta.
Amma fa duk zai jarraba wannan hikimar ne idan
har yarinyar da ta kira kanta Nusaiba ba ta zo
don bai wa Rabi'at kudinta ba. A yanzu kam ita
yake jira, kuma da zarar ta zo zai rarrashe ta ta
gaya masa inda zai samu Rabi'at, domin ya
tabbata lokaci dada kure masa yake yi. Har
yanzu yana fargabar idan Rabi'at ba ta gaya wa
'yan sanda abin da ya faru ba.' in ma za ta fada
sai da safe,' domin a yadda ya fahimci ta tsorata
zai yi wuya ta iya kwana biyu ba tare da ta fada
wa kowa wannan labarin ba.
'Kafin kwana biyun zan kama ta,

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

2 Comments On KWANAN GIDA
avatar
hassan-5-6

1 year ago

Reply

godiya Allah biya

avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Kash

Please Login or Register in order to submit comment