Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta samu wata kafar tsira.
Zuwa can ta tuna da tagar da ta gama lekensu dazu. Da sauri ta karasa gindin tagar ta fizge labulen da ya yi wa tagar hijabi ta fara zare gilasan tana ajiye su a kasa a hankali, har ta samu kafar da kanta zai iya shiga, ta sunkuya jikinta na rawa ta tattare doguwar rigarta wadda ita kadai ce a jikinta, sannan ta kama tagar ta karfi da yaji ta cusa kanta, wata sassanyar iska ta bugi fuskarta, sannan kamar mage sai ta janyo uwar jikinta. Wani guntun gilas da ya maqale ya yi wa kafarta rauni, jini ya fara zuba, amma ba ta damu ba.
Tim! Ta fadi a kasa bayan ta dira, sai da ta yi katuwar ajiyar zuciya sannan ta mike ta fara waige-waige, gabadaya ta manta hanyar fita daga gidan, don gudun arangama da daya daga cikin mutanen nan ya sa ta fara sanda tana bin bango kamar kadangaruwa.
A can cikin daki Alhaji Sani ya karaso dakin da Rabi'at ta shiga, ya yi sa'a kuwa ba ta rufe kofar ba, ya tsaya yana kare wa falon kallo, nan take kuma ya fahimci abin da ya faru, in ransa yi dubu duka sun baci, wato yarinyar nan ta ci amanarsa ke nan? Ta tsallake iyaka da dokokin da ya shimfida mata, ta shiga guraren da ya ce kada ta shiga.
Ya zaro waya daga aljihunsa ya yi danne - danne sannan ya kara ta a kunnensa.
"Isuhu kada ku bar yarinyar nan ta fita, tana nan cikin gidan nan, ta bincike sirrina kaf! Mintuna biyar za su iya ba ta damar guduwa."
Daga nan ya koma falon da gudu ba tare da ya kulle kofar dakinsa ba, hankalinsa a tashe ya daga wani rami a jikin wata kujerar kushin ya dauko karamar bindiga sannan ya nufi kofar fita daga falon yana huci, ya bazama neman Rabi'at.
Ita kuwa, yayin da ta fahimci ta yi nisa da falon Gidan sai ta zunduma a guje ta nufi inda take jiyo karar motoci daga waje, don a zatonta nan ne hanyar fita. Ilai kuwa sai ta fara hango kyallin fitilunsu daga saman gidan, don haka sai ta nufi wurin kai tsaye.
Daya daga cikin mutanen da aka ce su kula da ita ya ga gilmawarta, don haka sai ya auno ta da sandar dake hannunsa, sandar ta taho da gudun tsiya kamar an wullo kibiya ta tade kafafuwan Rabi'at, ta wuntsila ta sake wuntsilawa tare da yin wata 'yar kara kamar an matsa bebin 'yartsana ta yara, sannan ta tumu da kasa.

Malam Audu maigadi ya mike firgigit! Daga gyangyadin da ya fara dibarsa yana zare idanuwa.
"Me ke faruwa a gidan nan ne yau?" ya tambayi kansa.
Rabi'at ta mike cikin wani zafin nama na ban mamaki, da ta lura sai ta ga kusa da katangar gidan take, don haka sai ta yi wani irin tsalle na kwatar rai ta kama katangar gidan, duk da hannunta ya damki wasu abubuwa masu tsini ba ta damu ba, har sai da ta tabbatar jikinta ya hau kan katangar, a lokacin ne harsashi ya yi shawagi ta gefen kunnenta.
Ta yi wata 'yar kara, da karfin hali ta wuntsila bayan gidan. Ba ta bata lokaci ba ta mike ta rufa a guje.
***KWANAN GIDA

MUHAMMAD LWAN PRP

10.
Alhaji Sani ya juyo a fusace ya dubi yaransa biyu dake tsaye suna jiran umarninsa.
"Ba ku da hankali," ya ce musu., ya nuna daya daga cikinsu, "Isuhu na rasa me yake damun Kwakwalwarka, sam! Ba ka da basira ko ta goga farce, hankalinka yana kan kudi, amma kullum ba ka da tunanin yadda za ka same su," ya nuna shi daga sama har kasa, "girmanka ya zama na banza, tun da har ka kasa kama karamar yarinya."
Isuhu ya bude baki, "Wallahi yallabai gudu ne da Yarinyar kamar..."
Gudu fa ka ce? "Alhaji Sani ya katse shi," yanzu a ce kamarka a ce ba za ka iya zagaye gidan nan a guje ba, duk gidan nan ai gudun nata ba zai wuce shi ba."
Ya juya ga daya yaron nasa, "Dangudulle!"
"Na'am yallabai," yaron nasa ya amsa.
"Akwai sauran aiki a gabanmu," cewar Alhaji Sani, "ya zama dole mu nemo inda yarinyar nan ta shiga, tun da muke harkar nan sama da shekaru biyar wata ba ta taba ba mu matsala ba sai wannan hatsabibiyar 'yar barikin, matsala daya da za mu fuskanta da ita ita ce, ta gaya wa 'yan sanda abin da ta gani. Saboda haka dabara daya ta rage a gare mu, wato mu tattara kayan dake cikin gidan nan kaf! Mu tashi nan da kwana biyu, ita kuma za mu san yadda za mu bullo mata."
A sannan ne suka ji motsi daga can waje, alhali suna cikin babban falon gidan.
Alhaji Sani ya matsa kusa da taga da sauri cike da damuwa ya zuge labulen taga ya leka waje. Maigadi ya hango, yayin da yake komawa bakin aikinsa.
Ya juyo, "In tambaye ku mana, maigadi ya ga lokacin da Fatima ta haura katangar?"
" Ya gani," Isuhu ya yi saurin bada amsa, "don na ga sa'adda ya taso da sanda ya biyo ta, duk da yana cikin magagin bacci."
Alhaji Sani ya yi shiru, "Mun dade da Baba Maigadi yana yi mini aiki, duk da bai san wani abu da ke faruwa a gidan nan ba, amma abin da ya faru yau zai iya dasa masa digon zargi a zuciyarsa," ya yi shiru yana tunani.
Dangudulle ya matso, "Yallabai ya ya kake ganin za a yi masa?"
Alhaji Sani ya ce, "Duk da ban yi tunanin zai ba mu matsala ba, ya kamata a sa masa ido sosai."
Ya daga kansa sama, "A yadda muka yi agreement (yarjejeniya) da shi, duk ranar Juma'a da yamma yana zuwa hutu gida kuma ba ya dawowa sai ranar Litinin da safe, idan kun tuna ai gobe ne Juma'a ko?" ya dube su daya bayan daya.
"Gobe ne Juma'a ko?"Isuhu ya tambayi Dangudulle.
"Ni ma ban sani ba." ya ba shi amsa.
Alhaji Sani ya yi banza da su domin ya san ba sallah suke yi ba.
"Idan Baba Maigadi ya tashi aiki gobe ina so ku bi shi gida ku gane makwancinsa kafin matsala ta biyo ta kansa, amma fa sai idan shi ya jawo wa kansa," daga nan sai ya zaro bindigarsa daga aljihu.
"Ban sani ba ko Baba ya san karar bindiga domin akan kunnuwansa na yi harbi..."
"To in mun gano makwancinsa me za mu yi masa?"
"Ban ce ku taba shi ba, kawai dai na ce ku lura da motsinsa, kana da saurin hannu Isuhu, ba ka da wata dabara sai ta yadda za a cuci wani, kawai duk abin da kuka ga ya yi duk bayan awa daya ku dinga sanar da ni, ya yi kwafa, "ita kuma Fatima za ta ci ubanta."
Daga nan ya sallami yaransa, "Ku je ku kwanta, ni zan zauna na yi karatun-ta-nutsu kafin safiya."
Ya nemi kujera ya zauna yana cika yana batsewa shi kadai.
***
KWANAN GIDA

MUHAMMAD LAWAN PRP

11.
Tun lokacin da Malam Audu Maigadi ya ga balahirar da ta faru a gidan maigidansa da yake yi wa gadi, hankalinsa ya kasa kwanciya, ya dinga zargin Maigidan nasa da laifuka daban - dabam, amma ba zai iya cewa ga laifin ba.
Ya dade yana ganin maigidansa yana shigo da mata gidan amma ba ya ganin fitarsu. Sai kuma yau kwatsam! Ba zato ya ga an biyo wata a guje ta haura katanga ta tsere. Da fari ya dauka 'yam fashi ne suka kawo wa Alhaji ziyara. Amma yanzu ya gamsar da kansa akwai wani abu da yake faruwa, kuma ko mene ne ba mai dadi ba ne. In da ba don halin Malam Audu Maigadi na shegen kwadayi da son abin duniya gami da burin ci a kwance ba, to da babu abin da zai sa ya yi gadi a wannan kadaitaccen gida, domin tun da farko lokacin da Alhaji Sani zai dauke shi aiki sai da ya ce masa.
"Ka yi a hankali Baba, ka ga kai tsoho ne. Na dauke ka aikin nan ne don ka samu rufin asiri kai da iyalanka. Babban abin da bana so shi ne shisshigi, kuma na tsani na kafa sharadi a karya min, zan dinga biyan ka dubu ashirin duk wata, duk abin da kake bukata zan tanadar maka shi a wancan dakin, kama tun daga kayan abinci da za ka dinga sallamar iyalanka zuwa sauran abubuwan kwana. Bana so ka dinga barin gidan nan dare da rana, sai dai na yarda duk ranar Juma'a da yamma za ka dinga zuwa gida kana hutun mako, ranar Litinin da safe bakwai ta yi maka a nan. Ba ruwanka da shiga cikin gidan nan balle har ka yi abin da ba a saka ba. Idan ka kiyaye wannan za ka ji dadin zama da ni.
Shikenan tashi ka je."
To tun daga wannan lokacin Malam Audu Maigadi ya fara aiki a gidan Alhaji Sani, yau kusan shekaru biyu, kuma yana kokarin kiyaye dokokin Alhaji mastada'a. Wani lokacin sai ya ji kamar ya yi karambani ya binciko wani abin, amma sai ya share, musamman idan ya tuna gargadin Alhaji.

A yanzu da yake kan hanyarsa ta komawa gida saboda yau Juma'a, tunanin al'amarin da ya faru jiya a kan idonsa yake, musamman bayan da ya nemi kattin da suka biyo 'yar budurwar nan ta jiya ya rasa, tausayinta yana damun sa.
Ya tuna lokacin da aka auna budurwar da bindiga kuma aka saki kunama, ya ga lokacin da ta fada baya, amma ba shi da tabbacin ko an same ta. Shi dai kawai ya koma daki ya labe, Yana so ya taimaki yarinyar amma yana jin tsoro.
Malam Audu Maigadi duk yana wannan tunani lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida.
Yana da mata daya da 'ya' ya uku. Babban dansa Rabi'u Mangyal takadari ne, ba shi da wata ta'ada sai neman mata da shaye-shaye. Tun Malam Audu yana yi masa nasiha har ya daina ya ce, 'ya je, duniya ce, wanda bai zo ba ma jiran sa take yi,' ya maida hankalinsa ga sauran kannen Rabi'un, wadanda dukkansu mata ne, Suwaiba da Hajara, su ma din kuma yana fatan aurar da su badi. In da matsalar take shi ne, babu wasu tsayayyun manema da suka fito sai dai 'yan shan minti. Ganin haka sai Malam Audu ya bullo da dabarar yi wa samarin kofar rago, duk wanda ya zo wurin' ya 'yansa sai ya tura a kira shi, sannan ya ce masa in da gaske yake ya fito. Daga rannan ba zai kara ganin keyarsa ba. Kafin a jima samarin suka yi laya aka neme su aka rasa.
Abin da Malam Audu bai sani ba shi ne, matsalar tana wurin yayansu Rabi'u. Da a ce zai daina bata 'ya' yan wasu to da babu wanda zai kara zuwa gidansa da sunan yaudara.
A yanzu kam tunanin Malam Audu ya sauya yana ta faman nazarin neman mafita akan hadarin da ya fada.
Da haka har ya karasa gidansa a kan farin kekensa mai kararrawa.
Malam Audu Maigadi ya yanke shawarar barin aikin da yake yi wa Alhaji Sani, domin ya ga kamar yana neman jefa rayuwarsa cikin hadari.

Zan dora idaan nasami lokaci
Na gode da bibiya.KWANAN GIDA

Muhammad Lawan Prp

12.
A gidan ta kwana ta wuni. Tun jiya lokacin da wani kato ya kawo mata abinci bai kara dawowa ba sai da safe ya kawo mata abin kari, sannan da ya fita kuma sai wajen karfe hudu ya kawo mata abinci, duk abincin da aka kawo mata kasa cinye shi take saboda tsabar zulumi, ta kula daga jiya zuwa yau ta dan fada saboda tsabar tunani.
Yanzu ma tunanin take yi lokacin da Alhaji Yunus ya shigo dakin yana damun ta da tambayoyi amma ta kasa ba shi amsa.
Karar wayar sadarwa da ke cikin jakar Nusaiba ta katse masa maganarsa, ya juyo ya kura wa jakar tata ido sannan ya matso kusa da ita.
"Ke da, da akwai waya a wurinki kike bata mana lokaci? "
Idanuwan Nusaiba suka zazzaro, domin tana ji da wayar nan kamar ranta, saboda ta saye ta har ajiya (account) ta bude a banki, ta yi ta tara kudi har ta sayi wayar, tun farkon shigowarta bariki.
Ya sa hannu ya dauki jakar ya zaro kwandaleliyar wayar wadda ta girmi tafin hannunsa.
"Iye! Babbar harka!" ya kura wa fuskar wayar ido 'ALH. ADO GARABASA' ya gani a kan gilas din wayar.
Gabansa ya fadi, ya san mutumin, maigidansa ne a siyasance, haka kuma shugaban kungiyarsu ta... Amma yanzu sun bata, haka kuma matsananciyar gabar dake tsakaninsu ta sa ba sa ga maciji da juna, lallai ya zama dole ya raba yarinyar nan da wayar nan don kada Alhaji Ado ya san inda yake, domin ya yi imanin Nusaiba yarinyarsa ce, amma kafin nan sai ya kashe bos da ita yanzu.
Yana cikin tunani har wayar ta katse bai sani ba.
Ya sa hannu a aljihu ya zaro bindigarsa ya nuna mata wayar hannunsa.
"Wace ce Usaina na ce!"
Nusaiba ta ga idon bindiga, ta kuma san halin wannan mutumin na gabanta, zai iya kashe mutum a yadda ta fahimce shi. Don haka sai ta yanke shawarar jefar da kwallon mangwaro ko ta huta da kuda.
"Ni wadda na sani ba sunanta Usaina ba, sai dai in karya ta yi maka, kuma ita ce wadda ka gan mu tare shekaranjiya."
"Yauwa 'yan mata, kin dauko tutar sulhu. Mene ne sunanta na gaskiya, kuma a ina zan same ta?"
"Jiya kafin ka zo wani mutum ya dauke ta a motarsa sun tafi kwanan gida."
"' Yan mata kamar ba kya gane hausata sosai, sunanta na tambaya da kuma inda zan same ta," yana murmushin nasara.
"Sai dai ka kira ta a waya," ta fada tana shesshekar kuka.
"Wanne suna kika sa mata?" ya fara duba fuskar wayar tata.
"Rabsy baby," ta fada tana kallon sa.
"Ok! " ya daddanna wayar.
" Mene ne sunanta na gaskiya?"
"Rabi'atu," ta ba shi amsa.
Idonsa na kan wayar yayin da ya ce mata.
"Nice, na ga sunan. Zan ba ki wayar nan ki yi magana da ita idan na kira ta. Ki tambaye ta inda take."
Daga nan ya dauko bindigarsa ya nuna mata.
"Kada ki bari ta gane kina hannunmu, idan kuma kika fada to..."
Daga nan ya mika mata wayar bayan ya kira lambar Rabi'at, ya ja baya ya auna ta da bindigarsa.
"Wannan ita ce damarki ta karshe ta ci gaba da rayuwa."
Nusaiba ta karbi wayar hannunta na rawa, ta kara a kunne.
Wayar ta dade tana kara kafin a daga.
Maimakon ta ji muryar Rabi'at sai ta ji muryar wani namiji yana cewa.
"Hello! Tun dazu nake jira a bugo. Wane ne?"
Gaban Nusaiba ya fadi, domin ta tabbatar ba Rabi'at ce ta daga wayar ba.
***

Zan Dakata A Nan.Kwanan gida

Muhammad Lawan Prp

13.
BABI NA UKU

Dare ya fara yin nisa. Haka nan ba a samun motoci masu wucewa ta titin sai tsalli-tsalli, haka nan kuma babu wadataccen hasken farin watan da zai fallasa duk wanda ya mayar da daren mafakar aikata laifi.
Samuwar duhun ya taimaka wa Rabi'at bin bango a nutse, bayan ta tabbatar ta yi nisa da gidan Alhaji Sani.
Ko kadan ba ta cikin hankalinta, domin tun da take ba ta taba ganin gawa kiri-kiri ba, amma sai ga shi yau ta ga wani sashe na jikin mutum a yanke, kuma wai har an gasa ana jiran mai ci. In dai haka rayuwar masu kudi take, Allah wadaran mutumin da zai tara dukiya irin ta su Alhaji Sani. Zuciyarta tashi take kamar za ta yi amai, idan ta tuna halittar kirjin mace da gabanta da ta gani a dakinsa. Ashe ita ma da ta tsaya da yanzu an yi layya da ita an yanke sassan jikinta an zuba a tangaran.
Tunanin haka ya sa ta waiwaya ta kuma hango gidan sannan ta kara sauri.
Ba ta san ko karfe nawa yanzu ba, domin ta baro wayarta a dakin da suka sha sha'aninsu da Alhaji Sani, haka kuma 'yan kudaden da suka ja ra'ayinta zuwa gidan su ma ta gudu ta bar su a dakin, ballantana ta tari mai mota ko baburin A-daidaita-sahu ta ce musu ga inda za ta.
Ta sha gudu har ta gaji, don haka tana bukatar ta huta. Ta waiga hagu da dama, ba ta san a inda take ba, haka kuma ba ta san inda za ta je ba in so samu ne ta gan ta a gida, amma ta ya ya?
Kyallin fitila ta hango a gabanta, ga dukkan alamu mutane ne a wajen.
Can ta nufa, domin jikinta ya ba ta, in dai ba mai shayi ba ne a wurin to mai tsire ne ko kuma dan tireda. Tana bukatar jama'a a kusa da ita, ko babu komai hankalinta zai kwanta. Don haka sai ta nufi wurinsu kai tsaye. Gefe ta samu, cikin wata duhuwa ta rabe, tana jiran mutane su ragu ta karasa wurin mutumin ta nemi taimakonsa. Sai a sannan ne ta ji radadi a kafarta ta dama ta duba. Duk da akwai duhu sai da ta ga shafcecen yankan da gilas ya yi mata lokacin da take yunkurin haurowa ta taga, ga kuma sauran wurare da ta kukkuje daban - dabam a jikinta. Tana bukatar ganin likita don ya duba ta, amma ya kamata ta yi wa kanta taimakon farko;wato ta daure wurin.
Ta kama kasan doguwar rigarta ta ja, sai ta ji rigar da kwarinta, amma tun da ba jini ne ke zuba sosai ba sai ta hakura ta ci gaba da kallon motoci masu tsada da ke gilmawa bisa titin.
Rayuwarta ta koma baya ta debo abubuwa masu yawa ta zo mata da su.
Lokacin da tana yarinya ba ta son kallon fina-finan ban tausayi da na tsoro domin suna saurin saka ta kuka, amma yanzu ga shi ta jefa kanta a cikin matsalar da ya kamata ta yi wa kanta kuka amma ta kasa. Ta tuna yadda ake son ta a gidansu, kasancewar ita ce 'ya ta farko a wurin mahaifanta, da yadda ake shagwaba ta a lokacin da mahaifinta ke da dukiya, mutanen unguwar ita suke son gani saboda kwalliyarta, nan take tunanin gida ya fado mata a rai, ta ji tana sha'awar ganin iyayenta bayan kwana biyu da ba su saka ta a ido ba.
Ta waiga ta dubi inda mai fitila yake, sai ta ga duk mutanen sun watse, sai mutum biyu kadai.
Ta mike tsaye ta taho wurin cikin wata malalaciyar tafiya.
Sauran mutane biyun dake zaune suka kura mata ido har ta karaso kusa da su.
"Barkanku dai. Don Allah tambaya nake," ta ce da su.
"Allah Ya sa mun sani," suka fada a tare.
"Nan ina ne? Ni bakuwa ce. Na bace hanya ne?"
Suka dubi kayanta da suka kudundune, sannan sai matashin ya ce, "Ina za ki je ne?"
"Tarauni zan je."
"Allah Sarki! Ai kin baro hanyar. Nan Zoo road kika nufa."
Daya dattijon da take tsammanin shi ne mai shayin ya ce mata bayan ya zauna.
"Suka kwatanta mata hanyar da za ta bi.
Har ta juya sai ta kuma dawowa.
"Don Allah ko yanzu karfe nawa?"
Saurayin ya duba wayarsa, "Sha daya saura kadan."
"Na gode," ta juya ta tafi.
Suka bi ta da kallo. Dattijon ya ce, "Tab! In dai kana raye babu abin da ba za ka gani ba. Yanzu wannan in ta gamu da marasa tausayi ai sai dai ta Allah."
Saurayin ya ce, "Kai don Allah rabu da ita! Yanzu haka irin 'yan matan nan ne' yan rage dare."
Dattijon ya ce, Rage dare kamar ya ya?"
"Yanzu wannan idan na ce zan yi mata masauki a dakina yarda za ta yi. Ai wannan tsintuwa ce babba a wurin gayu 'yan jiran tsuntsu daga sama gasasshe."
Dattijon ya yi tsaki, "Kai! Allah Ya sawwake wannan zamanin, ka ji Baballe."

Gobe zan ci gaba Insha'Allahu.KWANAN GIDA

Muhammad Lawan Prp

14.
Rabi'atu ba ta isa unguwarsu ba sai misalin daya na dare, kuma ta yi sa'a ba ta gamu da 'yan sanda ba.
Ta kwankwasa kofar gidansu ta ji ta a kulle. Ba ta bukatar tambayar kanta, domin ta san dare ya yi.
Tun tana buga kofar a hankali don kada makwabta su ji, har ta zage tsakani da Allah tana jibgar kofar.
Ba a jima ba ta ji ana zare sakata daga kofar wani gida da ke makwabtaka da su.
Wani mutum ya bude ya leko.
"Wane ne yake buga wa mutane kofa da wannan uban daren?"

"Ni ce," ta ba shi amsa.
Ya haske ta da tocilan, "Ke ce wa? Au! Rabi ce?" ya kashe tocilan din sannan ya fito sosai.
"Ba ki san abin da ya faru ba?"
Gabanta ya fadi, "Me ya faru kuma?"
"Sai dai ki shigo nan ki kwana, da safe a ba ki labari."

Ranar, a gidan makwabta ta kwana.

Tun da ta kwanta a gidan zuciyarta take yi mata wasu-wasi tana dawurwura ita kadai. Duk da cewa ba ta kwanta da wuri ba, amma bacci ya ki zuwa idanunta, duk da katin gayyata da take ta aika masa.
Abubuwa biyu ne suka hana ta bacci a daren; na farko dai, tunanin halin mahaifiyarta ke ciki. Me ya sa ta zo ba ta samu kowa a gidansu ba? Makwabcinsu ya ce mata wai wani abu ya faru, wanne abu ne wannan? Abu na biyu kuma tunanin abin da ta gani a gidan Alhaji Sani a wannan yammacin, wanda ya janyo mata cika wandonta da iska, ba don komai ba sai don ta tserar da rayuwarta. Daga zarar ta rufe idanunta sai ta dinga ganin abubuwan da ta gani a firij din Alhaji Sani.
Shin menene mafita?
'Yan sanda?
A'a, irin wadannan mutane suna da matsala bisa ga yadda kasar ta lalace. A karshe dai ta yanke shawarar yin shiru da bakinta, don kada kilu ta jawo bau!
Ita kadai a zaune a dakin, ba ta jin komai sai haushin karnuka da kukan gyare.
Sai can kusan asuba gajiya da ciwon jiki suka haddasa mata nannauyan bacci mai cike da mafarkai na ban tsoro.
Lokacin da Rabi'at ta farka rana ta fito, haka kuma mutanen gidan da ta kwana sun riga sun tashi, har sun fara karin kumallo.
Malam Ya'u ya yi sallama ya shigo dakin da Rabi'at ta kwana. Ya same ta a zaune ta yi tagumi. Haushinta ya kamata ya ji ko tausayinta?
Ya yi mata kallon 'ke kika ja wa kanki' ya ce mata.
"Kin tashi?"
Ta dube shi kurum, "Na tashi. Ina kwana?"
"Lafiya kalau," ya amsa mata.
"Bari a kawo miki abinci ki karya kafin mu tafi. Kin dai yi sallah ko?"
Ta dube shi cike da mamaki, "Ban yi sallah ba. Ina za mu je?" ta mike tsaye, "bari na yi sallar."
Ya bi ta da kallo kurum, kafin shi ma ya leka waje.
'Yarsa Baraka ya kira ya umarce ta ta samo wa Rabi'at ruwa kuma ta nuna mata bandaki.
Hakan ce ta kasance.

Jimawa kadan sai ga Rabi'at tsaye kan darduma tana ramuwar sallar asuba. Kafin ta gama Baraka ta shigo da kwanon sha karami da wata leda kunshe da wani abu a ciki. Ta ajiye ta fita.
Mintuna biyu ta idar da sallar ta bude kwanon Koko da kosai ta fara karyawa.
Gama karyawarta keda wuya Malam Ya'u da matarsa Zulai suka shigo dakin.
Zulai ce ta fara magana bayan sun zauna.
"Ina kika shiga tun jiya ana neman ki, kuma ga..."
"A'a Uwale, kar ki yi haka mana,"ya katse ta, "ki bari ta ga komai da idonta."
Daga nan ya juya ga Rabi'at, "Kin gama kintsawa ko?"
Rabi'at ta dube su kamar tana kallon wasu tababbu, domin ba ta gane inda maganarsu ta dosa ba, an ce ko me ye za ta ji in safiya ta yi, ga shi kuma safiyar ta yi ana ce mata za ta gani da idanunta.
Me za ta gani?

Ta dubi Malam Ya'u, "Na gama. Wai me ya faru ne?" a halin yanzu ta fara rudewa.
Malam Ya'u ya mike yana sabe malum-malum dinsa,
"Idan mun dawo ki samu Uwale ga ta nan,"ya nuna matarsa Zulai, "za ta yi miki bayanin komai.

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

2 Comments On KWANAN GIDA
avatar
hassan-5-6

1 year ago

Reply

godiya Allah biya

avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Kash

Please Login or Register in order to submit comment