Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a ranar kuma
zan bar gidan nan.'
Allah Ya ara mana lokaci mu dora.KWANAN GIDA

Muhammad Lawan Prp

22.
Tunaninsa ya koma baya ya tariyo masa
abubuwan da suka faru da shi tun yana yaro; irin
rayuwar da ya yi, zuwa mutanen da ya hadu da
su, da yadda aka yi ya san wannan harka ta
sayar da sassan jikin mata ga wasu manyan
mutane. Ya tuna babban maigidansa Alhaji Ado
garabasa, wanda ya sha masa alwashin duk
rintsin da zai shiga za su yi kokarin ganin bai
kwana a ciki ba.
Saboda a cewar Alhaji Ado, su ne garin, kuma
duk wani shege sai dai ya bi bayansu. Shi ne ma
ya hada shi da wadansu mutane, wadanda da
ganin su manyan gwasake (manyan masu kudi)
ne, kuma ya san sanannun mutane ne a kasar, ba
ma a jihar ba. Sai dai ba zai iya fadin inda suke
ba, domin sau daya ya taba ganin su. Har zuwa
lokacin da ya samu yaransa na kansa, su Isuhu
da Dangudulle, yau shekaru kusan ashirin ke nan
suna tare, kuma bai taba barin su san wani wuri
da zai dinga haduwa da su in ba a nan gidan ba.
Illa dai idan ya samo mace sai ya yi musu
magana ta waya da irin zaurancensu. Idan sun
zo kuwa sun san ta inda za su fara aika-aikarsu.
Alhaji Ado ya taba gaya masa ya bi a hankali,
domin wannan harkar babu amana a cikinta, balle
batun yarda da amincewa, don haka tun da suka
yi sakaci har aka samu baraka to su ma suna
cikin matsala.
Ya sa hannu a aljihu ya ciro wayarsa ya kira
wani yaronsa da shi ne gidigad.
Kara daya wayar ta yi aka daga.
"Basasa kana ina ne" Alhaji Sani ya tambaya.
"Ina kusa da kai ranka ya dade," wata murya
maras dadin ji ko a tarho ta amsa. Alhaji Sani ya
mike ya fito falon yana leke-leke, don ya
tabbatar ba mai jin sa.
Kullum amsar Basasa idan aka tambaye shi yana
ina, amsar ita ce, 'Ina kusa da kai...'
"Ok ka yi sauri ka bi yaran da suka bi Baba
Maigadi gida yau, kada ka bari gari ya waye ba
ka..."
"Na sani Alhaji," ya katsi maigidan nasa, "su ma
yadda suke yi za a yi musu ko?"
"Yauwa danhausa," cewar Alhaji. Daga nan ya
kashe wayar.
Har zai koma sai ya jiyo kugin mota a kofar
gidansa, ga alama Maigadi ake yi wa ham ya zo
ya bude.
Alhaji Sani ya tabbatar Nusaiba ce ta karaso don
ta kawo wa Rabi'at kawarta kudin da take ba ta
ajiya. Tuni kuma ya shirya dabarar da zai yi
mata. Don haka cikin sauri ya koma don ya
dauko bindigarsa.
***
Zan Dakata a nan sai kuma gobe, in Maiduka ya
yarda.kwanan gida
Muhammad Lawan Prp

23.
Dare ya tsala sosai. Haka kuma babu gizagizai a
sama, matashin farin watan da bai fi kwana
goma ba ya gaza samar da wadataccen hasken
da zai sa ka gane fuskar na kusa da kai idan ka
kalle shi.
Isuhu ya dubi fuskar Dangudulle, duk da ba ya
shaida ta sosai saboda dalilai biyu; na farko dai
rashin haske, na biyu kuma wiwin da ya yi wa
mugun sha tuni ta fara aiki a kwakwalwarsa,
domin idan ya sha ba sosai yake gane mutane
ba, ya ce masa.
"Ni fa motsi nake ji. Kada fa wani ya lababo ya
kawo mana wasa a nan."
Abokinsa Dangudulle ya tashi zaune, domin tun
dazu yake so ya yi bacci ya kasa.
Tun da suka yi shawarar neman wurin kwana
Isuhu ya lalubo musu wannan kangon da hankalin
Dangudulle bai kwanta da shi ba, abu na biyu
kuma ba sosai yake iya bacci ba idan ya yi wa
wiwi shan Allah-tsine-uwar-mai-karya.
"Kana da matsala Isuhu. Kai duk sadda ka sha
sai ka dinga jin ana motsi a cikin kanka. Ka dai
san babu abin da zai kawo 'yan sanda gurin nan
in da ba..."
Motsin da suka ji shi ya katse wa Dangudulle
maganarsa har ya kasa karasawa, baki bude ya
kama kallon mai shigowar.
Kai tsaye wurinsu ya nufo. Tocilan ya sa ya
haske fuskokinsu dai-dai.
Suka sa tafukan hannayensu suna karewa.
"Wanne dan iska ne wannan?" Isuhu ya fada a
fusace.
"Ubanka ne," aka ba shi amsa, "me kuke yi a
cikin kangon nan da wannan tsohon daren?"
Dukkansu su biyun mamakin abin da suka ji ya
fito daga bakin mutumin da ba su san ko wanene
ba suke yi, amma an rasa wanda zai mayar masa
da zagin a tsakaninsu.
Mutumin ya kara matsowa kusa da su, hakan ya
sa suka mike tsaye su duka.
"Wai wane ne?" suka tambaya, a halin yanzu
wiwin da suka gama zuzzuka ta fara aiki a
kwakwalwarsu.
"Ubanku ne!" aka kuma maimaita musu zagin kai
tsaye. A halin yanzu mutumin ya matso dab da
su.
Kowannensu ya dan ja baya ya buda da shirin
fada.
Kamar ya san sun shirya wa arangama, bai tsaya
bata lokaci ba ya sunkuya ya kinkimo wani katon
bulo ya maka wa daya a fuska.
Isuhu ya kwalla kara lokacin da bulon ya same
shi a fuska, ya yi taga-taga ya ja baya sannan ya
jingina da bango tare da yin wani kakkarfan nishi.
Jini ya wanke masa fuska.
Dangudulle ya antayo a guje ya rumbaci mutumin
ya tura shi baya da karfin tsiya, suka fada waje a
cikin wata kwata, tocilar din hannun mutumin ta
fadi gefe.
Suka mike cikin zafin nama na ban mamaki
rungume da juna tare da yin musayar naushi,
mutumin ya rarumi kan Dangudulle ya yi masa
gware. Dangudulle ya juya kamar zai fadi, katon
mutumin ya yi masa rakiya da bahaguwarsa, a
kokarinsa na kai shi kasa. Da kyar Dangudulle ya
shanye naushin tare da yin wani nishi da yake
nuna jin jiki.
Ya daure bai kai kasa ba, a lokaci guda ya samu
harba kafarsa a marainan mutumin da karfin
tsiya, mutumin ya ji zafin dukan kuma nan take
ya gigice tare da yin karar wahala sannan ya yi
kasa kusa da kwatar, ya sa hannu ya dafa wani
rubabben bulo, take kuwa ya balgace ya fada
kwatar, wanda hakan ya tilasta masa ci da baki.
Kafin ya gama shanye wannan zafin faduwar
Dangudulle ya bi shi ya turmushe suka fara
mirgin-mirgin daga kwance suna neman inda za
su rike a matsayin makasa don kassara abokin
rigima.
Ga alama mutumin ya fi Dangudulle kumari da
karfin damtse, nan take ya danne shi ya dinga
kai masa naushi dama da hagu a fuskarsa,
bakinsa da hancinsa.
Suka yi kace-kace da jini. Da ya tabbatar ya
gama galabaitar da shi, sai ya dauko wata wuka
daga kubakar wandonsa da nufin yi masa yankan
rago.
Sannan ne to al'amarin ya faru; da fari ya dauka
duniya ce taruguzo masa a ka, amma jin wani
abin ya kuma tarwatse masa a ka, ya tabbata
bulo ne.
Bai kara ganin komai ba ya kife a wurin, bayan
ya yi sallama da duniya.
A tsaye a bayansa rike da wani bulon yana shirin
kara masa, Isuhu ne, fuskarsa jike sharkaf! Da
jini.
Ya jefar da bulon gefe, ganin kamar mutumin ba
ya motsi ya kama hannun dan uwansa
Dangudulle ya tashe shi. A lokacin ne kuma suka
hangi wani saurayi tsaye a gefe ya zuro musu
idanuwa yana kallon su.
In dai ba sun manta ba shi ne bugaggen saurayin
da ya wuce su dazu yana wake-wake kafin dare
ya tsala. Nan suka sha jinin jikinsu kuma suka yi
imanin wannan saurayi ya ballo wa kansa ruwa
tun da har ya ga aikin da suka yi.
Rabi'u Mangyal ya dubi fuskokinsu, duk da sun
cudanye da jini ga kuma dare, amma shaye-
shayen da ya yi yana gaya masa zai iya gane su
ko da rana ne.
Don haka sai ya zaro idanuwa yana kallon su
cike da tsoro, saboda duk yawace-yawacensa da
kwana a kulab da otal da yake yi bai taba ganin
an make mutum a gabansa ba sai yau.
Haka kawai yana kwance a dakinsa yana zukar
sigari sama-sama sai ya dinga jin buge-buge a
kusa da gidansu, wanda daga shi sai wani fili sai
kuma kangon da su Dangudulle suka kwanta, da
ma ba bacci yake ji sosai ba, domin an dade da
ma a unguwar ana so a kama masu yin bahaya a
kangon. Tuni Alhaji Labaran (mai kangon) ya
bada cigiyar duk wanda ya kama mai yi masa
bahaya a kangonsa to zai ba shi wani abu.
Tun daga wannan lokacin Rabi'u da abokansa
suka sha alwashin kama masu kewayawa kangon
da daddare, don kawai su samu na kashewa.
Rabi'u bai san ba shi kadai ba ne ya ji hayaniyar,
sauran mutanen dake makwabtaka da kangon
sun gane rigima ake yi a wurin, amma sun kasa
fitowa su raba fadan, saboda ba su san dalilinsa
ba, don kuwa ba su ji wani musu ko tankiya ba,
duk da ce wa wani lokacin samari kan taru a
wurin su yi ta hayaniya..
Rabi'u Mangyal ya waiga dama da shi ya dauko
wani katako siriri, ya yi hakan ne don saboda
ganin sun dumfaro shi kai tsaye.
***
Zan dakata a nan. Sai wani lokacin.Kwanan gida

muhammad lawan prp

24.
BABI NA HUDU

Makeken gida ne wanda aka kawata shi da ado na kece-raini, tun daga katangar gidan zuwa kofofi da tayel masu shekin dauke ido dake malale a filin tsakar gidan zuwa dan karamin shatale-talen da aka kawata da siririn famfo mai zubar da ruwa a tsakiyarsa zuwa bangwayen gidan da suka sha zane da fulawoyi na dauke hankali, babu wani abu da za ka gani ka raina.
Motocin da suke ajiye a gefe sun fi talatin, kuma babu wadda kudinta yake kasa da miliyan biyar. Idan ka yi duba izuwa hadiman gidan kuwa, to kwanciyar hankalinsu daidai yake da na ma'aikacin gwamnatin dake daukar albashi mai tsoka.
Duk wanda ya shigo wannan gida zai dauka wani muhimmin taro na siyasa ake yi ko kuma wata walima ko biki, saboda tarin motocin da za ka samu a farfajiyar filin gidan.
Amma a zahiri a can falon gidan, mutane biyu ne rak! Suke wata ganawa ta sirri a tsakaninsu, sakamakon wata matsala da suke fuskanta.
Daya daga cikinsu kakkaura ne fari, yana da siririyar fuska wadda ta wadata da kasumba buyu-buyu, yana sanye da shakwara da jamfa ta shudiyar shadda mai haske, ya dora hularsa minista a kan teburin gilashin dake gabansa, wadda ke dakon lemukan sha kala-kala.
Sanata ne mai ci a karo na biyu. Sunansa Alhaji Bara'u Madugu.
Dayan kuma fari ne, madaidaici a kiba, ba shi da kasumba, sai dai yana da tarin gashin baki, sanye yake da farin boyel da hula damanga a hannunsa, yayin da daya hannun ke dauke da kofin gilas mai kunshe da sassanyar madara, akwai kwalin sigari ('yar waje) a gabansa.
Tsohon danmajalisar jiha ne wanda ya wakilci mazabu guda biyu a jihar. Sunansa Alhaji Ado garabasa.
Alhaji Bara'u ya tsiyayi lemon kwali a cikin kofin gilas siriri, ya dubi abokinsa.
"Kamar ba ka gane karatun da nake biya maka, barin wani dan shiyyarmu ya tsaya takara a wannan lokacin babban gibi ne a wurinmu. Ka dai san yadda mutanen kudancin kasar nan musamman shiyyar yamma suka kware da munafunci, idan muka yi wasa kaye za mu sha. Ka ga kenan shugaban kasa mai hawa zai yi wahala ya tafi da mu a gwamnatinsa. Ka ga ta bare da mu ke nan."
Alhaji Ado ya numfasa, "Duk na fahimce ka mutumina, amma fa ka san wannan zai ja mana bakin jini a gun talakawa, musamman ma ni da nake son neman takarar gwamna a jam'iyyarmu idan talakawa suka san ina goyon bayan wani dan kudu ba abin da zai sa su dangwala min kuri'unsu."
"Wannan duk mai sauki ne," cewar Alhaji Bara'u, "idan laila ta kiya sai a koma fasha, ai kawai idan muka ga haka za ta faru sai mu koma sabuwar jam'iyya mu dana tarkonmu a nan, ka san fa mutane na yi wa shugabannin sabuwar jam'iyya kallon waliyyan Allah, ka ga kuwa babu yadda' yan adawa za su iya da mu, ka ga daga nan..."
Burarin da daya daga cikin wayoyinsa da ke kan tebur ta fara ne ya katse masa zancensa. Ya manta bai kashe wayarsa ba kamar yadda ya saba idan za su yi irin wannan zaman.
Ya kai hannu ya dauke ta, duk da bai san lambar ba, hakan bai hana shi dagawa ba, domin tuni ya raba lambobin wayoyinsa ga talakawa wai don su kawo kokensu, tare da cewa bai taba yunkurin biya wa wasu bukatunsu ba saboda tsabar yaudara.
"Honorabil barka da dare," aka fada daga cikin wayar.
"Wa ke magana?" ya fada cikin tausasa murya irin ta kwararrun 'yan siyasa.
"DPO Rabe Mustafa ne, daga ofishin' yan sanda shiyyar Hotoro."
"Ok me ya faru kuma? Ba mun kashe wannan kes din ba?"
"A'a wani sabo ne kuma."
"Ina jin ka," ya fada cikin kosawa, domin ya fara gajiya da belin 'yan jagaliya dake ta faman fadace-fadace a tsakaninsu.
DPO ya katse masa tunaninsa da cewa, "Wani yaro ne ya kawo wata rigima gabanmu kuma ya ce danka ne, shi ne muke so mu samu tabbaci."
"Mts!" Alhaji Bara'u ya ja tsaki, kamar zai ajiye wayar sai kuma ya fasa.
"Wane ne?"
Yana jin sadda aka yi ajiyar zuciya, "Ya ce sunansa Ilyasu, kuma ya kawo kes din ne akan wata yarinya da ya ce 'yam fashi sun tare su sun auna shi da bindiga ya sha da kyar, amma sun tafi da yarinyar. Shi ne muke son samun tabbaci daga gare ka. Kamar yadda ya gaya mana cewa auren yarinyar zai yi, kuma da saninka, to za mu yi kokarin ganin mun yi wani abu akai, domin 'yan jarida na damu na akan maganar, har sai da ta kai na kashe waya."
Alhaji Bara'u ya yi tunani a ransa, ya dade yana zargin dansa na mu'amala da mata. A yadda ya san Iliya kuwa zai yi wahala idan aurensu zai yi, domin ya dade da gaya masa ba zai yi masa aure ba har sai ya gama mastas dinsa.
"E dana ne mana, amma..." ya kashe wayar tare da ajiye ta a kan tebur.
Tun kafin ya yi magana wayar Alhaji Ado garabasa ita ma ta fara ruri. Ya dubi abokinsa. Sai da ta kusa katsewa sannan ya daga.
"Hello! Wane ne?" ya tambaya.
"Alhaji Yunusa ne," aka ba shi amsa.
Gabansa ya bada das! Amma sai ya ce, "Alhaji Yunusa? Wanne ke nan?"
"Alhaji Yunusa Dankwangila mana. Ya ya na ji duk ka tsorata? Ziyara kawai zan kawo maka nan da sa'a arba'in da takwas. Ina fata za ka tanadar mini masauki domin da kayan aikina zan zo."
Alhaji Ado ya zazzaro idanuwa yana kallon abokinsa, amma a zahiri hankalinsa ba ya kansa.

Mu tara a gaba in Maiduka Ya yarda.Kwanan gida

25.
Ba su dade suna danna ham ba aka wangale katuwar kofar gidan. Alhaji Yunusa ya danna hancin motarsa cikin gidan, ya mike sambal! Har zuwa gurbin da aka tanada don ajiye motoci. Tun a hanya ya gaya wa Nusaiba yadda al'amarin zai kasance har ya yi sa'ar kama Rabi'at, don haka da kanta ta dube kofar motar ta zuro kafarta waje. Akwai hasken fitilu tarwai! A tsakar gidan, wadanda suka kara fito da komai sarari.
A tsaye a can kofar shiga babban falon gidan, Alhaji Sani ne a tsaye rike da kugunsa yana yi wa Nusaiba murmushi. Bai yi garajen matsowa kusa da ita ba, tun da har Allah Ya sa ta kawo kanta, to kuwa tabbas! Ya samu kugiyar da zai kama Rabi'at.
Lokacin da ta fito daga motar ne Alhaji Yunus ya ce mata, "Ki kula da komai kamar yadda na gaya miki ki lallaba shi ya gaya miki inda take, domin jikina yana ba ni kamar wancan mutumin shi ma ba shi da gaskiya."
Abin da ya fada ya fadar mata da gaba akan faduwar gaban da take fama da ita tun da ta shigo hannunsa. Kawai dai ta fito daga motar ne ta nufi inda Alhaji Sani ke tsaye yana dakon ta.
Gaba daya su biyun kowanne ya tsura mata ido yana jiran ta samo masa labarin da ba ta da makamar ta inda za ta fara bada shi, wato labarin kawarta Rabi'at. Sai dai matsowarta kusa da Alhaji Sani ya sa shi ma ta shaida shi, kuma ta ji kamar karshen rigimar ta zo, amma fa ta bangarenta. Shi ne ya dauki Rabi'at tun kafin Alhaji Yunus ya zo neman ta a titin Bayero, haka kuma tun daga lokacin ba ta san ina ya yi da ita ba. Idan kuwa haka ne, ba ta bukatar boye-boye, za ta gaya wa Alhaji Yunus cewa, wannan ne ya dauki kawarta. Ta san dai a yadda ta fuskanci zafin rai irin nasa zai yi wahala ya bar wannan mutumin da rai. A yanzu kam ta gano inda Rabi'at take; tana cikin gidan nan.
Ba ta san ta matso dab da shi ba sai da ta ji yana cewa.
"Ga ni nan. Ina za ki je kuma?"
Ta yi turus! Ta tsaya tana dubansa, "Ina Rabi'atun?"
"Saurin me kike yi ne?" ya ce mata, "ai duk abinki kya tsaya ki sha ruwan sanyi dai ko?"
"A'a babu komai wallahi. Ba ka gani mu biyu ne, kuma za mu wuce unguwa ne," ta fada cike da damuwa, don ta fuskanci yana son bata musu lokaci ne.
"Tana ciki ne?" ta tambaye shi yayin da ta nufi kofar falon kai tsaye.
"Ke da waye ne?" shi ma ya tambaye ta yayin da yake duban motar da ta kawo ta, saboda bai san alakarta da abokin rakiyar tata ba. Yana bukatar sanin ko waye, don ya san yadda zai bullo masa, domin ba kowa ne abin yarda ba.
"Saurayina ne, tare muka zo da shi kuma tare za mu bar garin gobe," ta ba shi amsa, a daidai lokacin da ta rike mamurdin kofar ta juyo tana kallon sa.
Ta fadi haka ne saboda dalilai guda biyu; na farko dai ba ta son ya kawo mata wani abu mai kama da wasa, ko ya tilasta mata kwana a gidan, na biyu kuma kada ya janyo abin da zai bata musu lokaci.
"Ok saurayinki ne? No problem," ya gyada kafada, don nuna halin ko in kula, "anyway! Mu je ciki. Allah Ya sa ba ta yi bacci ba."
Suka kama mamurdin kofar a tare suka murda tare da dannawa lokaci guda.
Kofar ta bude suka shiga ciki, kafadunsu na gogar juna. Alhaji Sani ya sa kafarsa dake kunshe cikin wani takalmi sau ciki mai kwarin tsiya ya yi wa kofar wani wawan duka ta kulle da karfi, ya zaro mabudai daga aljihunsa ya kulle kofar, sannan ya juya da murmushi ya dubi Nusaiba.
"Mu karasa ciki ko?"
Ta tsaya turus! Da farko, "Ah! Ban gane ba. Ya ya kuma na ga ka kulle kofar?"
Ya dube ta, har yanzu murmushin muguntar na nan a manne a fuskarsa.
"Ba Rabi'at kike nema ba? Ko Fatima sunanta ko? Ai ni ma neman ta nake."

Alhaji Yunusa ya yi firgigit! Ya daki kofar motarsa da kafarsa, ta kara budewa. Ya fito a razane, kana ya kura wa kofar shiga falon gidan idanu a fusace. Ba mamakin shigar Nusaiba falon Gidan yake ba, domin da ma sun shirya hakan tuntuni, sannan sun shirya idan ta ga za a ba su matsala, ya ba ta lamba da wayar da za ta yi masa dan kira (flashing) idan ya gani shi kuma zai fado daki ko falon da suke ciki don yin barazanar karshe, a'a yana mamakinmamakin yadda ya ji an rufe kofar falon kusan da karfi. To wannan ne ya sa shi mikewa daga cikin motar a razane.
Ya cire bakin kwabcecen tabaran dake idonsa ya kura wa fadin tsakar gidan idanu, Yana duba gurin da zai labe idan aka samu akasi abin ya zo da musayar wuta.
Bayan ya yi nazarin tsakar gidan sai ya kwabe takalmansa sau ciki ya zaro karamar libarbarsa ya tura kofar motar a hankali sannan ya nufi kofar falon. Ya tabbata Nusaiba da wannan mutumin suna ciki, kuma yana bukatar ya san me yake faruwa a tsakaninsu. Ba zai yarda a kuma yaudarar sa ba. Idan Rabi'atu ba ta fito daga gidan nan ba, to lallai kuwa za a yi dan karamin yaki.
Duk da ba shi da takamaiman masaniyar abin da ya sa aka kulle kofar, hasashensa na gaya masa akwai Lauje cikin nadi a al'amarin Nusaiba.
Da haka ya karasa kofar falon ya kama ya murda, don dada samun tabbacin a kulle take. Ya ji ta gamgam! Ya zagaya bayan gidan, inda ya hango wata taga.
***

Mhm!.

Fatan alkyri gareku gabaki daya masu bibiyar wannan labari, Zanyi amfani da wannan damar domin sanar daku cewa marubucin yakai shekara kusan uku kenan yana rubuta wannan labarin kuma haryanxu bai samu damar qarasawa ba,sbd abubuwan dasyke gabansa. muna nan muna jiran lokacin da zai ci gaba nikuma nayi muku alqawarin xan turo muku shi,
Jinjina ga marubucin wannan labarin watau muhammad lawan prp. Sakamakon namijin qoqari dayayi. Ni da na kwafo nakawo muku nake cewa sai haduwa tagaba tx to u all
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

2 Comments On KWANAN GIDA
avatar
hassan-5-6

1 year ago

Reply

godiya Allah biya

avatar
mustapha-6-6

1 month ago

Reply

Kash

Please Login or Register in order to submit comment