Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

KURA DA KAN RAGO

1

(NAS)

Laraba janairu 10 2007

Tunda asuba hadari ya lullubr sararin saaniy baqinqirin yaqarawa garin duhu.wannan shi ya hana jamaa da dama samun sallar asuba musamman wadanda suke amfani da haske ko duhun gari.kowa ya gama yanke qauna da babu wani abu daxai hana marka marka amma cikin ikon Allah har qarfe takwas saura kwata na wannan ranar Allah bai kawo koda qwayar ruwa guda ba ikon sauka a doron qasa ba.maimakon haka sai wata sassanyar iska mai dauke da damshin ruwa ta fara hurowa cikin gari kadan kadan tana fifita bil'adama,tsirrai harda dabbobin gida dana daji.Abin gwanin ban shaawa domin hadarin ya dakushe hasken rana.

wannan kyakykyawan yanayi shiya bawa marasa lafiya waanda ke kwance a asibiti a karon farko cikin makwannin damar fitowa farfajiyar asibitin domin su sami damar shaqar tsagtatacciyar iskar tatacciya musamman a wadanda suka sami rangwamen lalurar dake damunsu.

Cikin sauri Ahmad ya ratso asibitin dauke da yan littatafansa yana tafe yana gaida marasa lafiya wadnda suke cikin bishiyoyin wasu a xaune wasu kuwa a tsaye suna qoqarin motsa jikinsu .yayin da wasu suke kwance basa ko iya qwaqwqwaran motsi an shanyasu kamar kayan wanki suna kallon gajimaren dayake tafiya a hankali akan sararin samaniya.

Ahmad ya kalli wata mace cikin tausayi saadda yaga tana ta qoqarin yiwa danta wasa wanda ke kwance a kusa da ita baima san abin datakeyi ba domin cuta ta gama cinyeshi ,duk ya rame ya motse ya koma kamar qwarangwal .Amma duk da haka bata haqura ba qoqari take wai dole saita shi koda murmushi ne don da tanji sanyi a ranta.Ahmad ya gigiza kansa cikin tausayi duk da shima mahaifinsa yana can a kwance rai a hannun Allah.

Cikin sauri ya nufi wani shago na lashe lashe da tande-tande wanda ke can jikin katangar asibitin daga bangaren gabasa. Mutum ukune kawai a cikin kantin. Biyu a xaune kan kujrar roba da teburi an ajiye kwalaben lemon fanta a gabasu. Sannan akan wani farin tangaren felele mai kamar marar kwason tuwon cincin ne guda huduKURA DA KAN RAGO

2

Mutanen biyu daya kakkaura ne mai qaton ciki wanda ya sami mazauni akan cinyarsa kamar ya rungumi kayan wanki.jifa-jifa sai mutumin ya gutsiri cincin yaciba bakinsasannan ya kurbi lemo yana ta muzurai,yayin da dan uwansa yake zaune.duk ya rame ya motse da alama mara lafiya ne da dan xaman jinyasa ko kuma dan dubiya.to koma dai menene mutumin mai qaton cikin da alama rashin lafiyar dayan bata dameshi ba.Duk wnnan Ahmad yalura dashi ne a kallo daya. A hankali ahmad ya matsa gurin mutum na ukun dake dakin.Dattijo ne xaune a gaban qaton firinji dake dauke da kayan sanye-sanye dangin zaqi iri daban daban.
"sannu bba ina kwana." Ahmad yace da tsohon. Dattijon ya dubi Ahmad cikin murmushiLafiya lau dana ,yaya jikin tsohon naka?"
"da sauqi" sannan yawuce kai tsaye xuwa gurin daya saba zama acan quryar kantin a gab da taga yaxauna sannan yadora littafinsa akan teburin dake gabansa kana ya zuba musu idanu kamar yanda yasaba tsawon kimanin kwanaki ashirin da suka gabata a tsawon wadannan kwankin kullu tare yakr kwana da mahaifinsa,kafin gari ya waye mahaifiyarsa taxo ta karbeshi. Ahamad yayi rashin sa'a domin rashin lafiyar mahaifinnasa yasameshi a lokacin dayake fama da jarrabawarsa ta qarshe a digirinda na biyu a jami'a . kullum da littafansa yake xuwa asibitin domin yin bitar dare.Hakanan ya wajabtawa kansa al adar kullum da sassafe xaixo wannan kantin yakoma can quryar yaci gaba da karatunsa har xuwa lokacin da mahaifiyarsa xataxo tare da qannensa su karveshi. wannn shiyasa Ahmad ya saba da wannan dattijon mai aron wannan kantin.

Ahmad yayi ajiyar xuciya sannn ya dada bude tagar datake kusa dashi domin bawa sassanyar iskar damunar sanyaya fuskarsa. Ahmad ya fara nazari sannu a hankali. lokaci-lokaci sai ya dago kai ya dinga kallon wani gajimare mai kyawun gani wanda ke tafe yana yiwa baqi gajimare ado da farinsa.

Lallai da wahala idan baayi ruwa ba . Ahmad ya fada a ransa. A daidai wannn lokacinne yaji kamar motsin ana tura gadon asibiti mai taya xuwa cikin kantin. Ahmad yayi duba ixuwa qofar dakin cikin mamaki.Ahmad ya dago a kansa a hankali. To adai dai lokacinne yafara yi mata kallon farko a duniya.Ganin farko ,ganin da baxai taba mantawa dashi ba. Farin gani baqin gani kuma ganin qaddara.

wata kakkaurar macece fara mai jiki sakwafskwaf kamar ruwa a cikin gugan fata tashigo tana tura kujera irin ta guragu mai tayoyi hudu. a zaune a cikin kujerar wata tauraruwace mai haske da qirar bil adama.

Tsarki ya tabbata ga ubangiji mai daidaita tsoka da qashin bil adama. Ahmad yafada a cikin ransa,saar dayaji numfashinsa ya dauke sannan xuciyarsa ta fara harbawa das-das ."meke damunane?" Ahmad ya tambayi kansa. Nan da nan sai yasami kansa yana mai nadamar da dama bai dago kansa ba don yasan bazai sake samun nutsuwa akan karatun dayakeyi ba.KURA DA KAN RAGO

3

Zan iya barinki anan naje nadawo ko kuwa najiraki? kakkaurar matar ta tambayi kyakykyawar.

ke ni nagaji da xaman daki jeki kidawo bayan minyi talatin.
"to" kakkaurar matar tajuya cikin gaggawa kamar dama Allah Allah take ta rabu da kyakykyawar matar.
"Kidawo bayan minto arbain ba talatin ba"
"To" kakkaurar matar takuma amsawa batare data juyo ba ,meyiyuwa batayi niyyar juyowar bane, ko kuma koda tayi niyyar juyowar bzata iyaba saboda girmanta.

Tun saar da Ahmad yayi mata kallon farko kallon daya ruwa duk tunanisa ,bai sake dago kaiba har saida kakkaurar matar tabar dakin.Jikinsa na rawa yasake dago kansa a wayance,.katsam sai suka hada idanu da ita.Cikin sauri saita dauke kai gefe guda.Ahmad yadawo da fuskarsa kan littafin dake gabansa ,duk kuwa dacewa tuni haruffan dake kan littafin sun bace baya iya ganin komai sai kyakykyawar fuskarta.mintuna biyu masu kama da shekara suka shude.Ahmad bai iya jurewa ba sai yasake dago kansa a karo na biyu .Suka sake hada idanu. Ahmad yana qoqarin wayancewa kenan da kallon wasu tarun kwalaben lemo dake can quryar dakin,sai matar tayi masa mirmushi sannn ta daga kyakykyawar girar idanunta baqa sidiq mai kyawun tsayuwa kamar wata tsaiwar dren farko tace:
"In bbu damuwa don Allah dan taimaka ka karbo min lemo acan mana." tanuna inda dattijon nn yake.

Ahmad yaji kamar ta jefeshi da sassanyar gudumr qanqara a xuciyarsa.. MAY BE SAI, ,,,,,, XAN DAWOKura da kan rago

4

Cikin sauri ahmad ya rufe littafin dake gabansa ya nufi inda take.Ahmad yaji wanu mai kmar mayan qarfe na fisgoshi da niyyar ya hadasu da juna .A lokacinnr ahmad yalura ashe qafarta ta hagu a nannade take da wani farin abu mai kamr sunduqin roba tun daga kan guwarta har xuwa tafin qafafunta.Hakanan ya lura cewa matar duk da a zaune take doguwa ce jaxur take kamar tsada. sanye take da doguwar riga baqa ,kanta lullube yake da dan wani sirirn gyale fari mai alamun santsi sai dai gyalen bai iya rufe gashin kanta mai sheqi kamar fasassun kwalabe a cikin rana . hancinta dogo daga qarshe mai tsini kamar fiqaqqen alqalami. fuskarta doguwa shan xuciya, ma abociya kunduquqi mai annuri.haqoranta fararr qal kamar garin alli.

matar tayi murmushi a karo na biyu
kyawun lebben bkinta su suka qafar ahmad ta hagu taci karo da kujera a yayin da murmushinata yakoma na mai shirin yi magana.

"sannu ,nasaka wahala ko?.
ah ah kada kidamu ,ya jikin naki.Ahmad ya furta yana mai nuna jimaminsa na halin datakr ciki.
"wanne iri kike so a lemon? Ahmad yace bakinsa a rawa saar daya dada matsawa kusa da ita.jiki da da sauqi tace dashi cikin murmushi lokaci guda kuma ta dubi nanadaddiyar qafarta cikin damuwa.
"kowane iri ma kana iya karbowa amma banda na kwlba a lokaci guda saita xaro sabuwar naira dari biyar ta miqa masa.. Ahmad baisan daga inda ta xarota ba shidai kawai yaga kudin a hannunta kamar aikin aljanu.
ah ah kibari kawai na karbo muki ahmad yajuya ba tare daya ji amsarta ba ya juya da sauri ya nufi gurin dattijonnan.

kyakykyawar matar ta dubeshi cikin mamaki.

Ba afi minti uku ba saiga ahmad yadawo dauke da wani lemo cikin kwali wanda shi kansa bai iya karanta sunansa ba domin da faransanci aka rubuta. ahmad ya ajiye lemon a gabanta tare da wani kofi na tangaran mai ruwan garai.

oh sannu bawan Allah ina tasaka wahala ko.

ah ah bbu komai wallahi Allah dai yabaki lfy..kura da kan rago

5

Ah ah babu komai Allah dai yabaki lfy.Ahmad yacr sannan cikin sauri ba tare da ya dubeta ba yajuya kai tsaye xuwa gurin da yake karunsa. shi kansa saar daya xauna yasan karatunsa ya qare bbu abin daxai qara fuskanta amma saboda tsabar qi fadi sai ya xurawa littafin idanu waishi a dole karatu yakeyi .

mintuna talatin suka wuce ,kamar wasa ahmad yana xaune ya xubawa littafin idanu ba tare daya fuskanci komai ba, san guntun ma daya karanta a daren jiya sun fara bin iska.

"sai mu tafi ko.
Ahmad ya dago kansa cikin sauri dayaji murayar.kakkaurar matar nan ce tadawo. kakaurar matar ta kama bayan kujerar kyakykyawar tafara turawa suka nufi qofa. Ahmad yadubeta lokaci guda kuma yafara tunanin daga mata hannu amma ga mamakinsa, sai yag ta hade rai ta kau da kai gefe guda bata yarda sun hada idanu ba. A haka suka fice daga kantin kamar yanfa suka shigo.

Ahmad yayi ajiyar zuciya kana ya share gumi. yadubi littafin dake gabansa ciki xuxxurfan tunani na dan lokaci.
"uhm"
yaji anyi gyaran murya koda yadago kai sai yaga dattijonnan mai tsaron kantin yana yi masa murmushi

"Gaskiya kyakykyawace. " dattijon yace sannan ya karya goro ya jefa a bakinsa.

********

washe gari tun fa duku duku Ahmad ya shirya ya tafi kantin xuciyarsa tana ta saqe saqe marasa amfani.Gashi jiya kwana yayi baiyi barci ba.

A da can kusan shekaru bakwai da suka gabata . yayi imani a xuciyarsa cewa duk duniya babu mai kyawun surar BADARIYYA. Tsohuwar budurwrsa ce da suka hadu tun a makarantarsu ta secondary

"Duk duniya babu mai kyawunki badariyya. yace da ita watrana suna hira a qarqashin bishiyar maina bayan an tashi daga makaranta.A lokacin tana jiran direban gidansu ne yazo ya dauketa.
"Haba duk duniya fa kace Ahmad ,ai ko a makarantar nan ma wadanda suka fini kyau ma bazasu qirgu ba" badariyya tace lokacin datake jifansa dawani tattausan murmushi.

"Ina laifin ma idan kacr a gurinka bbu wadda tafini kyau"

"eh to haka dinne"
yafada ba tare daya dubeta ba domin baiyi imani da abin data fada ba.kuma har wayewar garin jiya ,Ahmad bai taba yarda akwai mai kyawun badariyya ba. sai lokacin da aka turo tauraruwar kyawu mai haske akan kujera karyayyiya
Kura da kan Rago

6

Don haka saar da ahmad yashigo cikin kantin yaxauna a gurin daya saba zama sai yayi ajiyar xuciya ,kana ga mamakinsa sai yaji qwalla na qoqarin subucewa daga cikin idanunsa Rabuwansa da badariyya. mace daya dayafi qauna a duniya, macen da take qaunarsa fiye da yanda yake qaunarta ,macen da aka rabasu dare daya badon basa qaunar junansu ba sai don babu qaddarar aure a tsakaninsu.Rashinta shi ya dauke masa shauqin son kowacce mace a duniya, hakan shi yasashi har xuwa yanxu dayake karatun digirinsa nabiyu bai qara aure ba.

Ahmad ya gyara takardu da littafan dake gabansa ya fara qoqarin karantawa,amma abin ya faskara don ko motsin kujera yaji sai ya dago kansa yagani ko itace aka shigo da ita.

Yana nan xaune yana yan waige waigensa daga taga xuwa qofar kantin, babu kowa a ciki dagashi sai dattijon nan dayake jiran gurin.Jifa-jifa suna hada idanu da dattijon Ahmada yalura kamar akwai murmushi a gefen bakin tsohon amma bashi da tabbas.Saidai duk dahaka yafahimci cewa tsohon yaganr yau ba xaman karatu ne yakawoshiba,tunfa ya xauna bai kalli takarda daidai na minti guda ba. Sannu a hankali qarfe takwas nasafe suka gota shiru babu motsinta, sai tsoro ya mamaye xuciyar ahmad ,ko yau baxata zo bane? ya tambayi kansa. meyiwuwa ma tun asuba ta xo tafita.Cikin sauri ahmad ya kawar da wannan tunanin domin yasan ba abune mai yiwuwa ba.

Wani qaton agogo tun xamanin lokacin turawan mulkin mallaka dakr maqale a bango ya nuna qarfe takwas da minti uku.Ahmad yayi ajiyar xuciya ,ya gama yankr qauna katsam kuma sai qofar kantin tabude.

Wani abu mai kamar dutse ya tokare haqarqarinsa jikinda yafara rawa. saar daya hangota ana shigowa da ita.Zaune take kamar jiya sanye da doguwar riga launin rawaya mai santsi,to sai dai kuma yau abin mamaki wani qaton mutum ne dattijo mai kwarjini ya turo ta akan kujerar. Abin daya fara xuwa xuciyar ahmad shine dattijon mahaifinta ne domin ya isa ya haifeta kua qimarsa da kwarjinisa sun wuce ace yana tura wannan kyakykyawar akan kujera

mutumun ya gyara mata xama a gaban wani teburi na roba sannan shima yajawo kujera yaxauna yana fuskantarta.Daga inda ahmad yake yana iya jiyo kufin kujerar tana neman taimako saboda nauyin mutumin.

Ahmad ya xubawa mutumi idanu ,gani yake kamar yasanshi amma yakasa tuno a inda yasanshi.
mutumin dogone qaqqarfa sanye da babbar riga da jamfa da wandonta. farare qal suna ta sheqi, qafarsa sanye take cikin wani takalmi mai gashi gashi, hakanan wata farar hula tayi daram a kansa kai ka rantse da ita aka haifeshi,katon tabarau fari dayasa shiyasa yayi kama da minista kudi ko kuma ko kuma tsohon kwamishinan ilimi a jamhuriya tabiyu.

mutumi yacire tabaronsa sannan ya kalli kyakkyawar yace a tausashe.
"To gashi nakawoki shikenan? mutumin ya mayar da tabaron sannan yadubi qaton agogon dayake daure a dantsensa.

Ahmad yaci gaba da kallonsu cikin kaduwa domin tunda suka shigo babu wanda yayi wa wani murmushi a tsakaninsu . Hakanan ahmad yasan matar ta hangeshi tunda suka shigo amma bata nuna ma alamar taganshi ba ballantana ta dago masa hannu. Hakan ya dan sosawa ahmad rai.

"Kai shashashakura da kan rago

7

Kai shashasha da menene tsakaninka da ita ,ya fadawa kansa. hasali ma jiya jiyannan kafara ganinta, menene abin damuwa don ta nuna bata sanka ba ? tayiwu ma ta manta dakai.

kinga ni xan tafi baxaki xuramin idanu kiyi ta kallona ba babu magana kamar wani naan daji. katon mutumin yace yana kallon agogonsa lokaci guda kuma yamiqe.

"Nan da minti nawa xaa xo a koma dake?"
"talatin" tafada ba tare da tadubeshi ba.Ahmad ya lura akwai alamun bacin rai qarara a fuskarta . saar data fadi haka.

to shokenan, ah ni xan tafi xamu shiga meeting xan tafi dai dare xan dawo. yafada batara daya motsa ba.
"Ah ni na rasa abin dakike son a gani a cikin wannan tsohon kantin,haka kawai kishogo yanda jama suke taruwa. Ai gwara ma a fitar dake waje kyasha iska."
A karo na farko saita dago kai ta dubi ahmad ido da ido da dattijon.

"Ni a barni anan nafi jin dadin xma anan."

mutumin ya xunkuda kafada.A daidai lokacin wayar tafi da gidanka tadauki qra a cikin aljihunsa..cikin sauri ya xaro wayar yabudeta sannan yanufi kofar fita yana amsawa.
"ganinan xuwa plx"

kantin yayi shiru bayan fitarsa, bakajin motsin komai sai na takardun Ahmad wanda yake jujjuyasu akan teburin kamar waina ya rasa abin daxai karanta. Na farko dai yana son yayi mata magana amma takarya masa gwiwa Tunda tama nuna bata ma ganeshi ba . Ahmad ya dago kansa a hankali ga mamakinsa sai yaga itama idanunsa Amanda suke shi take kallo.Suna hada idanu saita haskeshi da murmushi .Ahmad yaji xuciyarsa ta dulmiya saar data waiga ta kalli qofar kantin sai ta yafitoshi da siraran yatsunta.
Jikinsa na rawa yatashi batare daya rufe takardun ba qafarsa tana harhardewa.
"Ranki yadade ina kwana ,ya jikinna naki"Ta dubeshi da tattausan murmushi "da sauqi ranks yadade"
tadanyi shiru tana duban karyayyiyar qafarta.
Gani nayi yau baka kawo min abin sha ba baka yi min magana ba shine nace bari ni nakiraka mugaisa"

bari akawo muki mana don dai abin sha ai kinfi qarfinda a gurina. Ahmad yafada cikin sauri,

jin haka keda wuya saita fashe da xaxxaqar dariya . laa wallahi da wasa nake maka bawan Allah yau cikina babu abin dayakr buqata. "
Ahmad bai taba jin murya mai xaqin tata ba.
"xauna mana ko tafiya xakayi?"
Ahmad yadubi agogo a yatsine wai shima a xuwan bai damu ba."eh badai jimawa xanyi ba" yace sannan yajanyo kujera yaxauna. wani qamshi yadaki hancinsa bai taba jin irin qamshin ba.

"Na dauka ma baxan sameka anan ba."Kura da kan rago

8
"eh nima din banyi niyyar zuwa ba", Allah ne dai yayi zamu hadu ahmad yafada. lokaci guda kuma yadago kai yadubeta ba kallon tsoro ba.
sai gabansa yafadi saar dayaga barin kumatunta na hagu duk yayi jazur hakanan akwai alamun kumburi sai dai idan mutum ba lura yayi ba dawuya yaga kumburin.
Ta lura da kallon dayake yi mata don haka sai ta shafi gurin da kyawawan hannunta tadubeshi tace .
" fuskata tayi muni ko?"
Ahmad ya girgixa kansa cikin sauri yace.
"kidaina fadar haka baiwar Allah ai bakima taba hada hanya da muni ba"
Haka dai kace don dai bka taba ganina bane kafin wannan marar imanin yayi min haka"
Ahmad yayi shiru don bai fahimci inda xancenta yadosa ba,don haka sai yacanxa maganar yace
"wannan qafar taki karyewa kikayi ne?"
Matar ta girgixa kai sannan tadauke kai lokaci guda.Ahmad yayi nadamar tambayar dayayi mata domin yalura da yanda fuskarta yacanxa lokaci guda kamar yandakalanxir yake canxa ruwa.
tsawon lokaci kanta yana gefe guda sai tayi ajiyar xuciya sannan tacire kanta tadubeshi ido da ido tace
"wani mara imanine yayi min haka har saida nafadi nakarya qafata ,bakaga yanda fuskata ta daddaje ba?"
Ahmad yayi shiru yana kallonta cikin kaduwa. bai iya cewa komai ba.
"kafishi kirki duk da jiya muka fara haduwa. Nasan da kaine da baxaka dokeni ba. tayi shiru sannan ba xato ba tsammani saita dubeshi tace.
"nagode kakoma gurin xamanka yanxu xaaxo daukata"
Ahmad yamiqe tsaye a hankali kamar kaxar da qwai yafashewa a ciki.
" har kin gaji danine?"
Tagirgixa kai.
"habadai yaya xakace nagaji dakai? tayi shiru tana dubansa kana tasunkuyar dakai tace a tausashe
"saboda kawai nasake ganinka nazo nan"
Ahmad yariqe numfashi cikin kaduwa domin bai taba tunanin abin daxai fita daga bakinta ba kenan.Rabonsa dajin dadin kalma mai dadi daga gurin macr tun lokacin dasuke tare da badariyya.
"kina nufin abin dakika fada har cikin xuciyarki?"
Ahmad ya tambaya bakinsa na rawa.
"koma gurin xamanka tace dashi cikin sauri, sannan tajuya tana kallon qofa akwai alamun kduwa a tattare da fuskarta.
Ahmad ya fahimci haka ,meyiwuwa tsoro takeyi agansu atare.Yafada a xuciyarsa, don haka cikin sauri sai ya miqe yakoma gurin xamansa.

"muhadu anan" tace dashi cikin tattausar muryakasa kasa.Ahmad bai ko gama xama ba saiga qatuwar matar nan tajiya tashigo kantin.A hankali tatura suka fita batare da kyakykywar ta waiwayo bare ma ta kalleshi.

washe gari kamar shkaranjiya da jiya Ahmad da sassafe ya shigo kantin xuciyarsa cike da tambayoyi akan wannan kyakykyawar matar ko shakka bayayi ida yabi a hankali yasai sauyin badariyya. shigowarsa kantin keda wuya sai dattijonnan mai jiran kantin ya yafutoshi ahmad yawuce kai tsye xuwa gurin dayake.
Dattijon ya miqa masa wata guntuwar takarda yace
"ga wannan yanxunnan wani yaro yashigo yace nabaka baka hadu dashi ba lokacin dakake shigowa ? Ahmad ya girgixa kansa"ban hadu da kowa ba wanne yaro ne?"
Nima ban taba ganinsa ba fari ne dai dogo kamar dan larabawa"
Ahmad yajo gabansa yafadi sannan yagodewa dattijon cikin sauri ya nufi gurin xamansa hannunsa na rawa ya bude takardar ya fara karantawaKura da kan Rago

9

kayi haquri naso musake haduwa ko don na sake ganin fuskarka mai kirki,amma Allah baiyi ba meyiwuwa kuma har abada bazamu sake ganin juna ba. amma duk da haka ga number wayata nan ko ma dinga gaisawa,amma banda doguwar magana domin wannan dakaga yakawoni jiya,mijina ne kuma tsohon dan giya ne,idan ta raya masa sai yayi ta dukana har sai na tsaneshi,bana qaunar ganinsa. amma da zarar ya sunkuya agabana yana bani haquri yana kuka sai naji bazan iya rabuwa dashi ba,Nice LAURIYYA"

kuhuta yan samari da yan mata naku a koyaushe yusuf Yusuf Ilyasu AbdulkadirKura da kan rago

10

Jumuah 9,maris 2007

Bala ya farka a gigice saar dayaji kamar wani abu yana taba masa qafafu,cikin sauri yatashi xaune sannan ya lalubi makunnin lantarki dake jikin bango fab da bango ya kunna.Didim dakin bai haskaka ba tabbas andauke wuta. Bala yayi tsaki lokacin ya lulubi qarqashin fulonsa ya dakko wata doguwar cocilan mai kamar karas ya kunnata. farin haske ya mamaye dakin.To adaidai lokacinne ya hangi baqar magen tana xaune kan gadontana ta muxurai tana lashe baki .bala yakai mafa duka da qafa, magrn tayi tsalle tasauka sannan taruga guje ta fice daga dakin.

Har yanxu xuciyarsa bugawa takeyi hakanan kansa yayi nauyi ga xufa duk ta mamaye jikinsa sai naso yakeyi kamar waina.Hannunsa na rawa bala yamiqe a dudduqe yabude tagar dakin, sassanyar iskar safiya tsaftatacciya ta banko dakin, bala yayi ajiyar xuciya sannan cikin kasala sai yajanyo matashin kansa yajinginashi a jikin bango sannan ya sanya bayansa a jikin Fulton yalumshe idanu.Jim kadan kuma sai ya miqe ya moqa hannunsa can qarshen gadon ya ya dakko kwalin sigari ya xaro daya sannan ya girgixa kwalin sai makunnin sigarin yafado hannunsa na rawa ya bankawa sigarin wuta sannan yaxuqa ya daga kansa sama ya qara sararin samabiyar dakin nasa hazo. lokaci guda kuma sai yakuma jingina da filon sannan yafara tunanin halin dayake ciki.
Mako guda kenan yana irin wannan mafarkin lokaci guda sai yaji ida nunsa sun bude yana cikin barci gabansa yayi ta faduwa wata saar idan yaduba agogo dai yaga
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment