Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

boye, kowane rike da dogon
mashi. Suka tsorata dokin ruwan nan, ya fada
cikin teku kamar dorina ya bace.
Bayan wasu 'yan kwanaki sai ga dukkan 'yan
barga sun hadu wuri guda, kowane jaye da
godiya. Da suka gan ni tare da dan uwansu sai
suka tambayi labarina. Na kwashe na fada musu
kamar yadda na fada wa dan uwansu. Muka ci
abinci tare da su, bayan sun gama kimtsawa
suka daura mini sirdi ga wata godiya na haye.
Muka yi ta tafiya a cikin wannan tsibiri, kwana da
kwanaki, ba dare ba rana, har muka iso birnin
Sarki Mihirjanu. Suka tafi ga Sarki suka gaya
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
masa labarina.
Sarki ya sa aka kai ni gabansa. Da na shiga
wurinsa na fadi kasa na yi gaisuwa, ya yi mini
sallama irin ta addinin musulunci, na mayar masa
da sallama. Bayan na zauna sai ya tambayi
labarina. Na kwashe duka na gaya masa. Ya yi
mamaki matukar mamaki, sa'annan ya ce mini,
"Wallahi ka yi awon arziki! Ba don Allah ya sa
kwananka na gaba ba ai da tuni ka halaka." Na
zauna muka yi ta hira da shi kamar wadanda
suka dade da sanin juna.
Sarki Mihirjanu ya karrama ni matukar
karramawa, ya girmamani matuka har ma ya
nada ni mai kula da gabar ruwan teku inda
jiragen fatake ke shigowa birnin da hajarsu. Aka
ba ni gida da bayi masu kula da ni. Aka ba ni
suturu na alfarma. Kullum nakan je bakin teku da
yarana muna duba jiragen da suka shigo birnin,
mu dauki rahotonsu mu kai wa Sarki. Kullum
farin jinina sai karuwa yake yi wurin Sarki, na
zama dan gaban goshinsa, duk abin da na ce ba
ya tashi a fadar nan. Da yawa mutane a wurina
suke kamun kafa idan suna neman wata bukata
ga Sarki.
Na zauna a wannan birni cikin dadin rai da
kwanciyar hankali. Sai dai abu daya kawai ke
tayar mini da hankali. Wannan abu kuwa shi ne,
na sha tambayar mutanen wannan birni labarin
Bagadada har na gaji, amma ban samu wanda ko
ya ce ya taba jin sunan birnin ba. Wannan shi ne
kawai damuwata. Domin duk wannan daula da
nake ciki ina matukar son in koma kasarmu, cikin
'yan uwana da abokai.
Wata rana na shiga wurin Sarki Mihirjanu sai na
same shi tare da wasu baki 'yan kasar Hindu. Na
yi musu sallama, suka mayar mini da sallamata.
Bayan mun gaisa sai suka tambayi labarina da
kuma kasar da na fito. Ni kuwa na ce musu ku
fara gaya mini labarinku. Suka ce mini su 'yan
asalin kasar Hindu ne, amma ba kabilarsu daya
ba. Akwai 'yan kabilar Shakiriya daga cikinsu,
wadda kabila ce mai son zama lafiya, ba ta
takalar kowa kuma ba ta yaki da kowace kabila.
Akwai kuma 'yan kabilar Burahamiya, wadanda
babu ruwan su da shan giya, sai dai masu arziki
ne sosai a kasar Hindu, sun mallaki shanu da
rakuma da tumaki da awaki. Haka kuma suka ce
mini akwai kananan kabilu a kasar Hindu har
guda saba'in da biyu. Na yi mamaki da jin
wannan labari nasu.
Ni kuma na duka na kwashe nawa labari na gaya
musu, na kuma gaya musu na fito ne daga kasar
Bagadada.
A cikin abubuwan mamaki da na gani, wadanda
ba zan manta da su ba, a dan zaman da na yi a
tsibirin Sarki Mihirjanu, akwai wani dan karamin
tsibiri mai suna Kasilu, wanda ke makwabtaka da
na Sarki Mihirjanu. Kullum sai dare ya yi tsaka
sai a yi ta jiyo ganguna da algaitu na tashi kamar
ana biki, duk da cewa babu dan Adam ko daya a
cikin wannan tsibiri. Sai dai ana jita-jitar wai
mutanen boye ne ke wannan shagali da dare.
Haka kuma na taba ganin wani kifi mai tsawon
zira'i metan a cikin teku, inda masunta ke su.
Girman wannan kifi sai da ya tsorata kowa.
Masunta suka hadu suka dauko itace suka kore
shi ya gudu cikin ruwa.
Na taba ganin kuma wani kifi mai kai irin na
mujiya a cikin wannan tsibiri. Kai, abubuwan
mamaki da na gani suna da yawa a wannan
tsibiri.
Na ci gaba da zama tare da Sarki Mihirjanu,
kullum ina zuwa bakin teku domin daukar rahoton
jiragen da ke shigowa da kuma masu fita.
Wata rana ina bakin teku kamar yadda na saba
ina jiran isowar jigi. Na yi tsaye na dogara ga
wata sanda ina kallon ruwa. Can sai na hangi
wani babban jirgi yana nufo gabar ruwa inda nake
tsaye. Da jirgi ya iso bakin gaba sai ya tsaya.
Aka daure shi da igiya, aka aza itatuwa masu
fadi daga cikin jirgin zuwa ga saman kasa, inda
mutane za su taka su fito. Fataken dake cikin
jirgin suka yi ta fito da hajojinsu daga cikin jirgi.
Ni kuwa ina tsaye ina daukar lissafin kayansu.
Bayan sun fito da kayansu duka sai na tambayi
madugun jirgin, "Iyakacin kayan da kuka zo da su
ke nan?"
Ya amsa mini, "Ya shugabana, akwai 'yan
uwanmu da suka halaka a cikin wannan tafiya,
mun sayar da kayansu duka, saura na mutum
daya daga cikinsu muka zo da shi wannan birni.
Idan mun sayar da kayan za mu kai wa iyalansu
kudin a Birnin Bagadada, Gidan Aminci."
Yayin da na ji ya ambaci Bagadada sai gabana
ya fadi, na tambaye shi, "Menene sunan falken
da kuka zo da kayansa?"
Ya amsa mini, "Sunansa Sindibad."
Da na ji haka sai na kalli madugun nan da kyau
sai na gane ashe dai madugun jirginmu ne da
muka fito gida tare. Saboda saje da gemun da
suka fito masa ne buzu-buzu a fuska ya hana in
shaida shi da farko. Na yi wata irin kara don
murna, har sai da ya tsorata.
Na dube shi na ce, "Ya madugu, shin ba ka
shaida ni ba? Ai ni ne Sindibad da muka fito tare
da kai da sauran fatake daga Bagadada. Lokacin
da ka yi kiran mu da mu koma cikin jirgi kafin
katon kifin nan ya nutse da mu, muna nesa da
jirgi. Kafin mu yi taku daya har ya nutse da mu
cikin ruwa, sauran wadanda muka nutse tare duk
sun halaka. Amma ni sai Allah mai girma da
daukaka ya jeho mini wani gungumen itace na
haye bisa gare shi. Iska ta yi ta tura ni har ta
kawo ni cikin wannan tsibiri. Ina yawo cikin
tsibirin na hadu da 'yan bargar Sarki Mihirjanu,
suka kawo ni gaban Sarki. Na gaya masa
labarina, ya tausaya mini har ma ya nada ni mai
kula da gabar teku inda jiragen ruwa ke sauka.
Don haka wadannan kaya da ke cikin jirgi nawa
ne da na fito da su daga gida domin yin fatauci."
Da madugu ya gama jin zancena sai na ga ya
rike baki cikin mamaki yana yi mini wani irin
kallo na rashin yarda. Ya rika tafa hannu yana
sallallami, "Babu Sarki sai Allah. Mhm! Lallai
zamani ya lalace, mutane ba su tsoron Allah!
Sun mayar da yin karya kamar a sha ruwa a tafi."
.
Za mu ci gaba
4. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU
DA SINDIBAD DAN DAKO
Daga littafin LABARUN DARE
DUBU DA DAYA
Sabuwar Fassarar:
0 ...
Sindibad mai teku ya ci gaba da
labari ya ce, na ce wa madugu
hajar da ke cikin jirgi tawa ce
wadda na zo da ita daga gida
domin yin fatauci.Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
Da madugu ya gama jin zancena
sai na ga ya rike baki cikin
mamaki yana yi mini wani irin
kallo na rashin yarda. Ya rika
tafa hannu yana sallallami, "Babu
Sarki sai Allah. Mhm! Lallai
zamani ya lalace, mutane ba su
tsoron Allah! Sun mayar da yin
karya kamar a sha ruwa a tafi."
Da na ga dai madugu bai yarda
da zancena ba sai na ce masa,
"Ya Ra'isu, Wallahi gaskiya nake
gaya maka. Shin ba ka gane ni
ba ne?" sai na rika duba kaina
wai ko wani abu ya canja ne a
jikina.
Madugu ya amsa mini, "Watau
don ka ji na ambaci haja wadda
mai ita ya mutu a cikin ruwa,
kake so ka yi mini karya don
kawai in ba ka hajar. Hala
kurege ya cije ni da zan yarda
da maganarka? Muna kallo da
idanunmu duk mutanen da suka
nutse cikin teku suka mutu.
Babu daya daga cikinsu da ya
tsira."
Na kara maraairaice masa,
"Haba Ra'isu! Don me zan yi
maka karya gemai-gemai da ni.
Ai karya na daya daga cikin
alamomin munafuki. Saurari
labarina da kunnen basira." Na
kara gaya masa labarina, tun
fitowar mu daga Birnin
Bagadada da biranen da muka
ya da zango muka taba ciniki. Da
yadda muka sauka bisa bayan
kifi muna tsammanin tsibiri ne,
da yadda kifin ya nutse da mu
cikin ruwa. Na gaya masa yadda
aka yi na tsira har na zo wannan
tsibiri. Na dai gaya masa kome
tun daga farko har karshe.
Yayin da sauran fatake suka ji
labarina sai suka ce lallai
wannan Sindibad ne, babu
shakka.
Madugu ya yarda da labarin da
na gaya masa. Suka yi mini
barka da arziki da na kubuta
daga halaka. Suka ce, "Wallahi
mun dauka dukanku kun mutu."
Madugu ya ba ni hajata, na
kuwa gan ta yadda take, ko
allura ba a taba ba. Lalle wannan
madugu da amana yake.
Na debi kayayyaki masu daraja
da ke cikin hajar na kai wa Sarki
Mihirjanu kyauta. Na gaya masa
abin da ya faru, na ce masa
masu wannan jirgi abokan
tafiyata ne da muka fito gida
tare.
Ya yi mamaki matukar mamaki,
ga shi kuma gaskiyata ta fito ta
labarin da na gaya wa Sarki tun
farkon zuwana gare shi. Sarki ya
kara girmama ni. Ya kara mini
kyaututtukan kaya ninkin
wadanda na ba shi sau goma.
Na sayar da hajata a wannan
tsibiri, na sami riba mai yawa.
Na sayi wasu kayayyakin da na
san za su yi tsada a Birnin
Bagadada.
Bayan 'yan kwanaki kadan duka
sauran fatake suka sayar da
hajarsu suka sayi wasu kayan
da za su koma da su. Da suka
gama shirin tafiya na sa kayana
a cikin jirgi. Na tafi wurin Sarki
na yi ban kwana da shi. Ya kara
mini wata kyautar fiye da
wadda ya ba ni a baya. Na bar
wurinsa yana kuka ina yi don
sabo.
Muka shiga jirgi muka fada teku.
Iska kuwa ta yi mana dadin
sha'ani. Muka yi ta tafiya kwana
da kwanaki ba tare da wani
hatsari ba. Allah da ikonsa ya
kaddare mu da isowa birnin
Basara lami lafiya.
Bayan mun huta a birnin Basara
mun kuma taba ciniki, sai muka
yi gaba zuwa gida Bagadada,
gidan aminci. Kwanci tashi
muka iso bakin gabar tekun
birnin Bagadada. Kowane falke
ya rungumi kayansa ya nufi
gida. Ni kuwa sai da na bidi
masu rakuma suka yi mini
labtun kayana zuwa gida.
'Yan uwa da abokan arziki suka
yi ta zuwa suna yi mini barka da
dawowa. Bayan kwana biyu na
sake sayen kayayyakin da na
sayar a gidana, na kawata shi
fiye da yadda yake da farko. Na
sayi bayi da kuyangi masu yi
mini hidima. Na sayi gonaki da
gidaje da filaye. Na bude
rumfuna a cikin babbar
kasuwar Bagadada ina ciniki a
cikin su. Na zama dai hamshakin
mai arziki fiye da da.
Da yake an ce mai hali ba ya
barin halinsa, sai na koma wa
halina na da, na rika tara abokai
ina kashe musu gara suna
kwasa. Na manta da wahalar da
na sha a baya. Amma da yake
ina saye da sayarwa ina samun
riba, dukiyata ba ta ja baya ba.
Wannan shi ne labarin tafiyata
ta farko. Idan Allah ya kai mu
gobe zan gaya muku labarin
tafiyata ta biyu, wadda ta fi
wannan hatsari da ban mamaki.
Yayin da Sindibad mai teku ya
gama ba da wannan labari, sai
ya sa aka sake fito da akussan
abinci da abin sha. Aka aza wa
kowane tajiri akushin abinci da
abin sha a gabansa. Shi kuma ya
ci tare da Sindibad dan dako.
Bayan sun gama cin abinci ya
kawo dinari dari ya ba dan
dako, ya ce, "Karbi wannan kudi
ladar tsayawa da ka yi tare da
mu. Mun hana ka zuwa neman
kudi."
Dan dako ya karbi kudi ya yi
godiya, ya tafi yana mamakin
irin wahalhalun da mutane ke
fadawa garin neman kudi. Ya
kwana yana tunanin wannan
labari.
Da gari ya waye, tun da safe ya
shirya ya nufi gidan Sindibad
bahariyi. Yana zuwa aka karbe
shi hannu bibbiyu, mai gida ya
zaunar da shi kusa gare shi.
Jimawa kadan sauran abokan
Sindibad mai teku suka iso
gidan. Kuyangi suka yi ta fitowa
da akussan abinci da nama da
gorunan ababen sha. Bayan sun
ci sun koshi, sai mai gida ya fara
ba da labarin tafiyarsa ta biyu a
cikin teku:
TAFIYAR SINDIBAD TA BIYU A
CIKIN TEKU
Ku sani ya ku abokaina, bayan
na dawo daga tafiyata ta farko
na samo dukiya mai dimbin
yawa. Na zauna cikin jin dadi da
kece raini, kamar yadda na gaya
muku jiya.
Ran nan sai zuciyata ta karkata
ga son shiga duniya domin
ganin kasashe da tsibirai. Na yi
sha'awar kara fita zuwa fatauci.
Na kwashi kudi masu yawa na
sayi hajar da zan tafi da ita.
Na yi sa'a kuwa wani sabon jirgi
mai kyau, wanda aka kawata da
kyallaye masu ban sha'awa zai
fita da fatake. Na biya kudi na
shiga tare da kayana da sauran
fatake. Jirgi ya motsa, muka
nausa cikin teku.
Muka dace da yanayin teku mai
dadi, muka yi ta tafiya daga
wannan tsibiri zuwa wancan
tsibiri, daga wannan gari zuwa
wancan gari. Duk garin da muka
je mukan tsaya mu yi ciniki, mu
sayar da kayan da muka zo da
su mu kuma sayi wadanda za
mu ci riba a gaba.
Haka muka ci gaba da zagaya
garuruwa da tsibirai har wata
rana Allah Madaukakin Sarki ya
kawo mu ga wani babban tsibiri
a tsakiyar teku. Tsibiri ne mai
cike da bishiyoyi da nunannun
'ya'yan itace. Ga furanni launi
daban-daban kowace tana fitar
da irin kamshin da Allah ya hore
mata. Tsuntsaye na ta rera
wakoki iri-iri, suna tashi daga
wannan bishiya zuwa waccan.
Ga koramu ko'ina na gudana,
ruwansu garai-garai kamar
mudubi. Amma duk kyawun
tsibirin nan ba mu ga alamun
dan Adam ba a cikinsa.
Madugu ya ce mu sauka nan mu
huta. Aka daure jirgi a bakin
gaba, dukkan fatake muka
sauka daga cikin jirgi, muka
fantsama cikin wannan tsibiri
domin kashe kwarkwatar ido,
muna tu'ajjibin ikon Ubangiji,
Buwayi gagara misali.
Na zo ga wata korama mai ruwa
gawanin dadi, na zauna
karkashin wata babbar itaciya
da ta saki inuwarta ko'ina. Na
zaro 'yar gurasa daga cikin
jakata na ci, na sha ruwan
koramar nan na zauna ina
hutawa ni kadai.
Wanna wuri da dadin zama
yake, ga sassanyar iska na
kadawa gami da kamshin
furanni, kukan tsuntsaye ya
hadu ya kara wa wurin armashi.
Nan da nan sai na ji wata kasala
ta rufe ni, na dan kishingida wai
in huta. Barci mai nauyi ya
dauke ni.
Bayan na shafe lokaci mai tsawo
ina barci sai na farka. Na nufi
inda jirginmu yake da sauri,
amma ina, ashe na makara. Jirgi
ya tafi ya bar ni a cikin wannan
tsibiri da ke tsakiyar teku, fatake
na tsammani ina cikinsu.
Na yi yawo cikin tsibirin nan
amma ban ga mutum ko aljani
ba. Hankalina ya tashi, zuciyata
kuma kamar za ta fashe saboda
fargaba. Ga shi dai an bar ni ni
kadai babu abinci babu kuma
wani dan Adam da zan gani. Na
sakankance da halaka, na ce a
cikin raina, "Lalle ba kullum
safiya take Jumu'a ba. Idan da
farko na tsira daga halaka a
tafiyata ta farko, yanzu ba lalle
ba ne in tsira."
Hawaye suka yi ta zuba daga
idanuna, na yi da-na-sanin sake
fitowa daga gida domin
kwadayin fatauci. Na tuna irin
jin dadin da nake yi a gida, ga
nama ga abinci iri-iri sai wanda
raina ke so nake ci, ga sutura. In
kwanta wuri mai kyau, duk
wani aiki kuma sai dai in sa bayi
su yi mini. To, amma yanzu fa?
Kwayar abincin ma da zan ci sai
na nema. Da ma an ce garin
tone-tone zakara ke tono wukar
yanka shi.
Na yi nadamar fitowa daga
Bagadada, bayan duk wahalar
da na sha a tafiyata ta farko. Na
yi ta tafiya cikin wannan tsibiri
ina cewa,"Daga Allah muke, gare
shi muke komawa."
Ina tafiya ina tangadi ina surutai
ni kadai kamar sabon
mahaukaci ko wanda aljani ya
shafa. Bayan na yi tafiya mai
nisa, babu alamun gari ko kauye
ko gida sai na yanke shawarar
hawa wata doguwar bishiya
domin hango abin da ke nesa.
Na hau bishiyar na duba ko'ina,
Gabas da Yamma, Kudu da
Arewa, ban ga kome ba sai
itatuwa, can gaba kuma ruwan
teku ne iyakar ganin ido. Har
zan sauko daga kan bishiyar
nan sai na hangi wani abu fari
tas can da nisa daga shiyar
Kudu. Na sauko na nufi inda
wannan abu yake.
Da na zo kusa gare shi sai na
gan shi kamar dutse, ga shi dai
fari tas, girmansa kamar daki,
amma kuma siffar kwai. Na
zagaya wannan dutse amma
ban ga kofar shiga ba ko wata
matakala da zan hau samansa.
Wannan irin dutse ya ba ni
mamaki, sai na yi wata 'yar
alama daidai inda nake tsaye a
gindin dutsen. Na rika tsagaya
shi ina kidaya takun kafar da na
yi, da na zagayo inda na yi
alamar nan sai na ga na kidaya
takun kafa hamsin daidai.
Na tsaya ina tunanin yadda zan
hau wannan dutse mai santsi,
lokacin kuwa rana ta yi tsakiya.
Kwatsam sai na ga hasken rana
ya gushe wuri ya yi duhu. Sai na
yi tsammani ko gajimare ne ya
rufe rana, amma da na tuna ai
wanna lokacin rani ne, sai
tunanina ya canja.
Na daga kaina sama da sauri
domin ganin abin da ya rufe
hasken rana, sai na hangi wani
irin tsuntsu mai girman gaske a
cikin sararin samaniya, ashe
fika-fikansa ne suka rufe hasken
rana.
Na yi mamaki da girman
wannan tsuntsu, gayar mamaki,
sai na tuna da wani labari da na
taba ji fatake da alhazai na
bayarwa. Wai a wani tsibiri da
ke tsakiyar teku ana samun
wasu irin manya-manyan
tsuntsaye wadanda ake kira
Rukki.
Wai wadannan tsuntsaye sukan
fyauce giwa idan tana kiwo,
kamar yadda shaho ke fyauce
dan tsako, su kawo wa dan
jinjirinsu wannan giwa ya cinye
ta shi kadai. Nan da nan na gane
ashe dutsen nan fari mai santsi
dake gabana shirim kamar daki,
ba dutse ba ne face kwan
wannan tsuntsu, Rukki.
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
5. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU
DA SINDIBAD DAN DAKO
Daga Littafin LABARUN DARE
DUBU DA DAYA
Sabuwar Fassarar Kabir Umar Sulaiman ...
Sindibad mai tekui ya ci gaba da
labarinsa ya ce, yayin da na daga
kaina sama domin in ga abin da
ya rufe hasken rana sai na ga
wani katon tsuntsu, wanda
girmansa ba ya misaltuwa, ashe
fika-fikansa ne suka rufe hasken
ranar.
Na yi mamaki gayar mamaki, sai
na tuna da wani labari da na
taba ji fatake da alhazai na
bayarwa.
Wai a wani tsibiri da ke tsakiyar
teku ana samun wasu irin
manya-manyan tsuntsaye
wadanda ake kira Rukki. Wai
wadannan tsuntsaye sukan
fyauce giwa idan tana kiwo,
kamar yadda shaho ke fyauce
dan tsako, su kawo wa dan
jinjirinsu wannan giwa ya cinye
ta shi kadai.
Nan da nan na gane ashe
dutsen nan fari mai santsi dake
gabana shirim kamar daki, ba
dutse ba ne face kwan wannan
tsuntsu, Rukki.
Ina nan tsaye kusa da kwan nan
ina mamakin sarautar Ubangiji
har tsuntsun nan ya sauko kasa.
Ya lullube ni tare da kwansa, ya
yi kwance, nan take barci ya
dauke shi.
Tsarki ya tabbata ga Ubangiji
wanda ba ya gyangyadi balle
barci.
Yayin da na ga tsuntsun nan ya
yi barci, sai wata dabara ta zo
mini. Na tube rawanina na yaga
shi, na murda shi ya zama
kamar igiya. Na yi damara da shi
sa'annan na daure kaina ga
kafar Rukki mai kama da jikin
bishiya don girma.
Nufina idan ya farka daga barci
zai tafi neman abinci ya tafi da
ni. Ta haka zan sami damar fita
daga wannan tsibiri ke nan,
watakila ya kai ni kusa ga wani
birni ko kauye.
Haka na kasance daure ga kafar
wannan tsuntsu tun da rana har
gari ya kusa wayewa ban runtsa
ba, gudun kada ina cikin barci
ya tashi da ni ban shirya ba.
Da gari ya waye sai Rukki ya
farka daga barci, ya yi kuka da
karfi ya kada fika-fikansa ya
tashi sama da ni daure a jikin
kafarsa.
Ya yi ta yin sama har sai da na
zaci ya kai kololuwar sama ta
farko sa'annan sai ya yiwo kasa-
kasa a hankali ya sauka cikin
wani kwari.
Lokacin da na ga tsuntsu ya
sauka cikin kwari sai na yi sauri
na kwance kaina daga kafarsa.
Na fita daga karkashinsa ina
neman inda zan boye don kada
ya gan ni, watakila ya hadiye ni.
Amma sai na ga bai ma lura da
akwai wata halitta kusa gare shi
ba, saboda kankantata gare shi.
Daga nan sai na ga ya tura
kafarsa cikin wani katon kogo
ya kamo wani abu ya tashi sama
da shi. Da na lura da kyau sai na
ga wani irin maciji ne mai
girman gaske ya kama, yana ta
wutsilniya. Ya tafi da shi tun ina
kallonsa har ya bace mini. Na yi
mamaki matukar mamaki.
Ashe ni ban sani ba, a cikin wani
irin kwari nake mai fadi da
zurfin gaske. Ban gane haka ba
sai da na daga kai na sama, sai
na gan ni kamar ina cikin rijiya.
Yayin da na ga haka sai
hankalina ya tashi, na zargi
kaina bisa wannan halin da
nake ciki. Da ban baro gida ba
da duk wannan wahala ba ta
same ni ba. Tsibirin da na baro
ma ya fi wannan rami kwanciyar
hankali. A can ina samun 'ya'yan
itace da ruwa, amma nan ban
da duwatsu da rairayi babu
kome.
Babu tsimi babu dabara face
daga Allah Madaukakin Sarki!
Duk lokacin da na kubuta daga
wata halaka sai kuma in kara
fadawa cikin wata halakar.
Na ci gaba da tafiya a cikin
wannan kwari ina tunanin
yadda zan fita daga cikinsa. Da
na lura da kyau sai na ga ashe
rairayin wannan kwari duk
lu'ulu'u ne. Da na isa ga bangon
da dutse ya yi wa kwarin sai na
ga dutsen na jauhari ne mai
daraja. Na daga kaina sama
amma ban ga wata matakala da
zan hau ba da za ta fitar da ni
daga cikin wanna kwari.
Wannan shi ake kira ga koshi ga
kwanan yunwa! Ga dukiya nan
ko'ina a cikin kwarin, amma ni
da nake neman hanyar fita daga
cikinsa ba ta dukiya nake yi ba.
Ban da wannan kuma kwarin
cike yake da wasu irin macizai
masu girman gaske. Kowane
maciji girmansa kamar iccen
dabino, idan ya bude baki kuwa
sai ya hadiye doki. Wadannan
macizai sukan boye da rana
saboda tsoron tsuntsayen da ke
farautarsu irinsu Rukki da
mikiya. Sai cikin dare macizan
suke fitowa su nemi na su
abinci.
Yayin da rana ta fara yin ja za ta
fadi, sai na fara neman inda zan
boye wa wadannan macizai
kafin rana ta sake fitowa.
Yunwa da kishirwa duk sai suka
bace saboda tsananin tsoro.
Ina nan ina dube-dube sai na
hango wani kogo mai kofa
matsattsiya. Na yi sauri na shige
cikin wannan kogo, na jawo
wani dutse mai fadi na rufe
kofar, na ce a cikin raina, "Zan
kwana a nan, idan rana ta fito
sai in fita in ci gaba da neman
hanyar da zan fita cikin wannan
rami."
Na jujjuya idanuna ko'ina a cikin
kogon domin ganin abin da ke
ciki. Numfashina ya dauke
lokacin da na ga wata macijiya
daga can saman wani dutse a
cikin kogon da nake, tana
kwance bisa kwayayenta tana
barci. Nan take jikina ya dauki
rawa, gashin jikina ya mimmike,
na daga hannuwana sama na
fara addu'a ga Ubangijin
talikkai.
A wannan dare dai ban runtsa
ba har gari ya waye. Da na ga
hasken rana ya ratso ta cikin
kwarin sai na janye dutsen da
na rufe bakin kogon na fito
waje. Na ci gaba da tafiya ina
tangadi kamar mai maye, yunwa
kuwa sai dafa ni take yi, ga
tsoro cike fal a cikin raina.
Ina cikin tafiya ina jan kafafu sai
na ga an jeho wani abu daga
sama ya fado kusa gare ni, tim.
Na yi tsalle gefe guda don tsoro.
Da na duba abin da aka jeho sai
na ga kamar alfadari ne aka
yanka, aka fede fatar, aka cire
kai da kafafu aka jeho naman.
Na daga kaina sama, amma
saboda zurfin kwarin ba zan iya
ganin wanda ke bisansa ba. Na
yi mamakin abin da ya sa aka
jeho wannan nama. Daga nan
sai wani labari ya fado mini a
rai.
Na taba jin fatake na cewa, a
wata kasa akwai wani kwari
wanda rairayinsa na lu'ulu'u ne,
duwatsunsa na zinariya. Wai
mutanen kasar kan yanka wata
dabba sai su jefa namanta a
cikin kwarin. Lu'ulu'un zai lillike
naman da aka jefa. Shi kuwa
wanda ya jefa dabbar sai ya
koma wani wuri ya make yana
kallo. Akwai wasu tsuntsaye
dake shiga cikin kwarin neman
abinci, idan suka ga naman sai
su dauko shi su fito cikin kwarin
da shi, su sauka bisa wani dutse
suna ci. Idan mai dabbar ya ga
haka sai ya fito ya kori tsuntsun,
ya cire lu'ulu'un da ke jikin
naman ya koma gida. Ta haka
suke tara dukiya mai yawa. Idan
ba ta wannan hanyar ba babu
mai iya shiga cikin kwarin balle
har ya kwaso abin da ke cikinsa
na dukiya.
Yayin da na ga an jeho wannan
dabba cikin kwari ta fado kusa
gare ni, sai labarin fatake ya
fado mini ga rai. Nan take sai
wata dabara ta zo mini. Ban yi
wata-wata ba sai na cika
aljihuna da lu'ulu'u na kuma
kumsa wani mai yawa a cikin
rawanina. Ina cikin dibar
lu'ulu'u sai na ga an sake jeho
wata dabbar jif, kusa gare ni.
Da na gama kwasar abin da
nake iya dauka na lu'ulu'u sai na
kwanta kasa rigingine. Na dauki
dabbabr nan na aza bisa kirjina,
ta rufe ni ruf, ba a iya gani na.
Na kama wani wuri a jikin
dabbar na rike gam.
Ina nan kwance karkashin
dabbar nan, kamar yadda na
zata, sai ga wani katon tsuntsu,
mikiya, ta diro bisa naman nan.
Ta dauke shi da kafafunta ta
tashi sama, ina rike da dabbar,
ta fito daga cikin kwarin ta
sauka bisa wani dutse mai fadi
domin yin kalaci da abin da ta
farauto.
Tun kafin ta fara cin naman nan
sai na ji ana tsawa da kururuwa
ana buga itace ga kasa domin
dai a tsoratar da ita. Tsuntsuwa
ta firgita ta tashi sama ta bar
dabbar a nan. Ni kuma sai na
ture dabbar daga kaina na mike
tsaye.
Tufafina duk sun rine da jinin
dabbar. Attajirin da ya kori
tsuntsuwar nan bai ko kula da
ni ba, hankalinsa na ga lu'ulu'un
da zai cire daga jikin dabbar. Sai
da ya zo kusa ga dabbar sai ya
gan ni tsaye kamar gawar da ta
tashi. Saboda tsananin tsoro sai
ya yi mutuwar tsaye, ya kasa yin
gaba balle baya. Ko bakinsa ma
ya kasa motsawa balle ya yi mini
magana. Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
6. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO
Sindibad ya ci gaba da labari ya ce, tun kafin tsuntsuwa ta fara cin naman nan sai na ji ana tsawa da kururuwa ana buga itace ga kasa domin dai a tsoratar da ita. Tsuntsuwa ta firgita ta tashi sama ta bar dabbar a nan. Ni kuma sai na ture dabbar daga kaina na mike tsaye. Tufafina duk sun rine da jinin dabbar.
Attajirin da ya kori tsuntsuwar nan bai ko kula da ni ba, hankalinsa na ga lu'ulu'un da zai cire daga jikin dabbar. Sai da ya zo kusa ga dabbar sai ya gan ni tsaye kamar gawar da ta tashi. Saboda tsananin tsoro sai ya yi mutuwar tsaye, ya kasa yin gaba balle baya. Ko bakinsa ma ya kasa motsawa balle ya yi mini magana.
Amma saboda son dukiya irin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment