Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwashe labarina duka
na gaya musu, na kuma fada musu irin bakar
wahalar da na sha a cikin wannan tsibiri. Suka yi
mamaki matukar mamaki, suka ce, "Wallahi
labarika abin mamaki ne da tausayi matuka. To,
amma yaya aka yi har ka gudo daga al'ummar
zindirawa, wadanda babu wani mutum da zai
shiga hannunsu ya kuma tsere daga gare su?"
Na gaya musu ni ma ban sani ba. Allah dai ne ya
kubutar da ni daga hannunsu. Na gaya musu abin
da ya faru ga abokan tafiyata. Mutanen nan suka
zaunar da ni karkashin wata bishiya mai sanyin
inuwa, suka kawo mini abinci mai rai da lafiya
suka girke a gabana. Suka ce in ci abinci kafin
su gama dibar goran yaji. Na nade hannun rigata
na sa abincin nan gaba. Na yi ta wulka loma har
ina sarkewa, kamar wanda za a kwace wa
abincin. Ban cire hannuna daga cikin akushin
abinci ba har sai da na ji na kai masabar gatari.
Na yi hamdala ga Ubangiji da ya kubutar da ni
daga kabilar zindirawa.
Bayan mutanen nan sun cika kwandunansu da
goran yaji, sai suka sanya ni a cikin jirginsu suka
tafi da ni zuwa ga nasu tsibiri. Muna zuwa sai
suka kai ni ga sarkinsu. Sarkin nan kuwa
mutumin kirki ne, ya karbe ni da hannu biyu-biyu
cikin fara'a. Bayan mun gaisa sai ya tambayi
labarina. Na duka na kwance masa bakin jaka.
Sarki da fadawansa suka yi mamaki mai yawa da
jin wannan labari nawa, ya umurce ni da ina
zauna kusa gare shi. Ya sa aka kawo abinci da
nama, muka ci tare da shi. Bayan mun gama
muka wanke hannuwanmu da ruwan wardi muka
goge da adikon da aka yayyafa wa miski. Na yi
godiya ga Allah Madaukakin Sarki. Na kuma gode
wa wannan Sarki kwarai da gaske bisa ga
wannan irin karimci nasa.
Bayan an watse daga fada sai na shiga cikin gari
ina zagayawa domin ganin yanayin garin da
al'ummarsa. Garin cike yake da jama'a, kowa
yana harakar gabansa, babu ruwan wani da wani.
An bubbude rumfuna ana ta ciniki, kowace rumfa
cike da kayan masarufi. Na lura da cewa
mutanen garin mutane ne masu hannu da shuni,
kuma 'yan kasuwa ne sosai. Hankalina ya kwanta
da mutanen wannan gari. Kwanci tashi har na yi
abota da 'yan kasuwa masu yawa. Na kasance
abin girmamawa a cikin wannan gari kamar
wanda ya yi shekara da shekaru. Wani abu da ya
ba ni mamaki da mutanen wannan gari shi ne,
ban taba ganin sun hau doki da sirdi ba. Kome
tsadar doki haka za a hau shi babu sirdi babu
wata kwalliya. Hatta Sarki da fadawansa duk
haka suke hawan nasu dawakin.
daga TASKAR WAZIRI AKU
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
12. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Sabuwar Fassarar:
Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.
Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce, bayan an watse daga fada sai na shiga cikin gari ina zagayawa domin ganin yanayin garin da al'ummarsa. Garin cike yake da jama'a, kowa yana harakar gabansa, babu ruwan wani da wani. An bubbude rumfuna ana ta ciniki, kowace rumfa cike da kayan masarufi. Na lura da cewa mutanen garin mutane ne masu hannu da shuni, kuma 'yan kasuwa ne sosai. Hankalina ya kwanta da mutanen wannan gari. Kwanci tashi har na yi abota da 'yan kasuwa masu yawa. Na kasance abin girmamawa a cikin wannan gari kamar wanda ya yi shekara da shekaru. Wani abu da ya ba ni mamaki da mutanen wannan gari shi ne, ban taba ganin sun hau doki da sirdi ba. Kome tsadar doki haka za a hau shi babu sirdi babu wata kwalliya. Hatta Sarki da fadawansa duk haka suke hawan nasu dawakin.
Ran nan dai sai na kasa hakuri, da aka tashi daga fadanci sai na tambayi Sarki, "Allah ya ba ka nasara, me ya sa ba ku hawan doki da sirdi? Na ga cewa sirdi yana sa mahayi ya ji dadin zama bisa doki, kuma yakan kara wa doki karfi da kuzari."
Sarki ya dube ni cike da mamaki, "Menene kuma sirdi? Ban taba jin wannan abu ba tun da nake."
"Allah ya ba ka nasara, idan ka yarda zan yi wa dokinka sirdi, ka hau shi ka ji yadda ake ji."
Cikin doki, Sarki ya ce ya amince. Na ce a sassako mini itace. Nan take Sarki ya sa aka sassako mini itace irin wanda nake so. Na nemo wani kwararren masassaki, na kwatanta masa yadda zai sassaka sirdi da wannan itace. Na sami tawada na zana masa, a kan itacen, siffar yadda nake so sirdin ya kasance. Masassakin nan gwani ne, nan da nan ya yi kamar yadda nake so. Na samo fata na lullbe sirdin da ita na dinke. Na sami wani masaki ya saka mini rigar sirdin da gashi mai taushi da laushi, kamar yadda na kwatanta masa, na shimfida rigar gashin bisa ga sirdi na dinke ta tare da fatar.
Bayan sirdi ya hadu yadda nake sonsa, sai na je ga wani makeri na kwatanta masa yadda zai kera mini likkafu da ragama. Ya aikata yadda na umurce shi. Ya goge su suka yi fari tas, ya shafa musu bulari, suka yi ta daukar ido kamar azurfa. Na sami wani mai tufkar igiya ya tufka mini linzami na alharini. Na hada kayan nan wuri guda. Na tafi bargar Sarki na zabo wani ingarma cikin wadanda Sarki ke hawa. Na daura masa sirdi da likkafu da ragama, na jawo linzami na aza bisa ga sirdi, na ja ragamar doki na nufi wurin Sarki da shi.
Sarki ya dubi doki ya cika da mamaki, ko ba kome dokin ya kara kyau. Na nuna masa yadda zai taka likkafa ya hau. Ya taka ya haye bisa doki, na mika masa linzami na fada masa amfaninsa. Ya yi tafiya da doki kamar taki hamsin, ya juyo ya dawo. Nan fa ya shiga gode mini kamar ya dauke ni ya goya. Ya kawo dukiya mai tarin yawa ya ba ni ladar wannan aiki da na yi. Yayin da Wazirin Sarki ya ga sirdi ga dokin Sarki sai ya ce lalle in yi masa irinsa. Nan da nan na hado masa nasa sirdin, shi ma ya yi mini kyautar dukiya mai yawa.
Daga nan fa sai fadawa da attajiran gari kowa ya taso yana so a yi masa sirdi. Na hada abokan aikina muka yi ta sassaka siradda muna sayarwa, kasuwa ta bude gare mu. Muka sami dukiya mai yawa wadda ba ta kidayuwa. Na zama hamshakin attajiri cikin kankanen lokaci. Sai ya kasance har daga makwabtan wannan birni ana zuwa sayen sirdin doki gare ni. Na kara samun daukaka ga Sarki, ya rike ni tamkar dansa, barci kadai ke raba ni da shi.
Ina nan cikin wannan birni cikin kwanciyar hankali da jin dadi, ran nan ina tare da Sarki muna hirar duniya sai ya takale ni da wata magana, ya ce, "Ka sani ya kai Sindibad, yanzu ka zama daya daga cikinmu, kuma na dauke ka a matsayin dana, har ba na so in rabu da kai. Ina so ka bi umurnina a cikin wannan magana da zan gaya maka yanzu?"
Na dukar da kaina kasa cikin ladabi na ce, "Allah ya ba ka nasara, ai yadda ka dauke ni a matsayin danka haka na dauke ka a matsayin ubana. Babu wani abu da za ka umurce ni da shi, face na aikata shi. Menene wannan abu da kake so ka umurce ni da shi?"
"Ina so in aura maka kyakkyawar budurwa daga cikin 'ya'yan manyan mutane, mai ladabi da ilmi da biyayya. Ka sani mutum duka bai cika mutum sai fa in yana da mata. Ina so ka yi mini biyayya a kan wannan bukata tawa."
Na sunkuyar da kaina kasa cikin tsananin jin kunya, na yi shiru ban ce kome ba.
"Ya na ji ka yi shiru ba ka amsa mini ba?" Sarki ya tambaya.
Na amsa masa, "Allah ya ba ka nasara, ai don wannan ba sai ka tambaye ni ba. Na amince ka aura mini duk wadda ka ga dama."
Sarki ya ce, "To, madalla." Ya sa aka tara alkalai da malamai da shaidu. Aka daura mini aure da wata kyakkyawar budurwa 'yar manyan mutane, wadda mahaifinta ya mutu ya bar mata dukiya mai yawa ta kudi da dabbobi da gidaje da gonaki. Bayan ubanta ya mutu sai Sarki ya dauki nauyin kula da ita. Yarinya ce kyakkyawa tamkar wata dan daren goma sha hudu.
Sarki ya aurar da ni ga wata budurwa kykkyawa wacce ta gaji dukiya mai yawa daga mahaifinta. Sarki kuma ya ba ni kerarren gida, na-gani-na-fada, kusa da fadarsa, na tare da amaryata a ciki. Ban da wannan gida kuma Sarki ya ba ni bayi da kuyangi farare da bakake, ya kuma nada ni daya daga cikin waziransa, ya yanka mini albashi da ake biyana kullum. Na zauna cikin dadin rai, na manta da duk wata wahala da na sha tun daga kifewar jirginmu a cikin teku da kuma wahalar da na sha a cikin tsibirin zindirawa. Na zauna tare da matata wadda nake matukar kauna, ita ma tana matukar sona kamar ta hadiye ni. Har na rika cewa a cikin raina, "Babu makawa idan zan koma gida Bagadaza in tafi tare da ita." Sai dai kamar yadda masu iya magana ne ke cewa, kana taka Allah na tasa. Bari ku ji abin mamakin da zai faru.
Ina nan zaune da matata cikin tsananin soyayya, sai ran nan matar makwabcina ta mutu. Na zagaya domin in yi masa ta'aziyya sai na same shi cikin tashin hankali da tsananin tsoro. Na yi masa gaisuwar rashin matarsa ina rarrashinsa, "Ka yi hakuri haka Allah ya kaddara. Allan da ya dauke matarka shi za ya kara ba ka wata wadda ta fi ta, ku ci gaba da rayuwarku cikin dankon soyayya."
Yayin da makwabcina ya ji zancena sai na ga ya kara fashewa da kuka, ya ce, "Ya kai abokina, ta yaya zan sake auren wata mace bayan saura kwana daya ya rage mini a cikin duniya."
Na dafa kafadarsa na ce, "Subhanalillahi! Don me kake yi wa kanka fatar mutuwa ga ka da lafiyarka?"
Ya ce mini, "Ai iyakacinka da ni yau, gobe war haka ni ma na kwana kiyama."
"Saboda me?" Na tambaye shi cikin mamaki.
Ya gaya mini cewa, al'adar wannan birni ce idan daya daga cikin ma'aurata ya mutu, mata ko miji, tare za a rufe su duka biyun da mataccen da mai rai a kabari daya. Wai don kada daya ya ci gaba da rayuwa ba tare da dan uwansa ba, wai soyayyar da aka yi a nan duniya ta dore har can. Ko ya gaya musu ana soyayya a barzahu. Wannan kuwa ko Sarki ne haka za a yi masa. Da na ji haka sai na yi sallallami na ce, "Wannan abu ai bai dace ba, don me za a rufe mutum da ransa tare da gawa? Ya kamata a watsar da wannan mummunar al'ada."
Ina nan zaune gidan wannan makwabci nawa ina taya shi jaje, sai mutanen gari ke zuwa kungiya-kungiya suna yi masa ta'aziyyar rasuwar matarsa suna kuma yi masa ban kwana. Daga nan sai ga masu binne gawa sun shigo da sunduki. Suka saka gawar matar a cikin sunduki suka tafi da ita tare da mijinta zuwa bayan gari. Suka isa ga wani tsauni kusa ga gabar teku. Suka share kasar wurin sai ga wani katon dutse mai fadi kamar marufi ya bayyana, suka ciccibi dutsen nan suka dauke shi da kyar suka ajiye gefe daya, ashe rijiya ce aka rufe da dutsen. Da na leka rijiyar nan ban ga iyakar zurfinta ba. Suka dauki sundukin nan wanda gawar matar take ciki suka ingiza cikin wannan rijiya. Daga nan sai suka kama mijin suka daura masa doguwar igiyar kaba mai kwari ga hakarkari. Suka rataya masa gora cike da ruwa, da gurasa kwara bakwai a cikin jaka. Suka rika zura shi cikin rijiyar nan a hankali har ya kai kasan rijiyar, ya kwance igiya daga jikinsa. Mutanen nan suka fitar da igiyar, suka mayar da katon dutsen nan suka toshe bakin rijiyar kamar yadda muka same ta da farko, suka mayar da kasa saman dutsen. Muka tafi muka bar abokina da gawar matarsa a cikin rijiyar.
Yayin da na ga abin da ya faru ga makwabcina sai na ce a cikin raina, "Wallahi wannan mutuwa har ta fi ta farko zafi. Gwamma mutum ya mutu bisa gadonsa da a kashe shi da yunwa da kishirwa." Na nufi wurin Sarki na ce masa, "Allah ya ba ka nasara, me ya sa ake rufe mai rai tare da matacce a cikin rami guda?"
Sarki ya ce mini ai al'adarsu ke nan kaka da kakanni. Muddin miji ya mutu to za a rufe shi tare da matarsa, haka kuma idan matar ce ta mutu za a rufe ta tare da mijinta. Na tambaye shi, to na ji ku al'adarku ce. Idan irina wanda yake bako matarsa ta mutu, ko ni na mutu fa? Sarki ya ce ai babu banbanci ga kowa. Da na ji haka sai na ji hantata ta dauki rawa, tsoro ya kama ni. Na ji kamar an sanya ni cikin wani irin kurkuku mai kunci, nan take duk sai na tsani wannan birni da al'ummarsa. Na ce a cikin raina, yanzu idan matata ta riga ni mutuwa shi ke nan ni ma na mutu, lalle da sake wai an ba mai kaza kai.
Daga nan sai na fara shawarar in rabu da matata ko kuma in tsere daga wannan birni, duk da dai Allah kadai ya san gawar fari tsakanin ni da ita. Na yi iyakar kokarina in kawar da wannan tunani a cikin raina amma na kasa. Inan nan zaune da matata lafiya, sai ran nan ta ce mini kanta na ciwo. Wasa-wasa dai har rashin lafiya ya kai ta kwance. Bayan 'yan kwanaki kadan sai ta ce ga garinku nan. Mutane suka yi ta zuwa suna yi mini ta'aziyya, suna kuma yi mini ban kwana, kamar dai yadda suka yi wa makwabcina.
Aka yi wa matata sutura, aka sanya mata tufafi masu tsadar gaske. Aka sanya mata sarka da awarwaro na zinariya. Sai ka rantse da Allah idan ka ce mata sannu za ta ce maka, "mhm!" Aka dauke ta tare da ni aka nufi bayan gari wurin rijiyar nan da aka rufe makwabcina tare da matarsa. Da zuwa sai aka bude bakin rijiyar nan aka jefa matata a ciki. Abokaina kuma suka zagaye ni suna yi mini ban kwana, wasu daga cikinsu har suna zubar da hawaye. Ni kuwa sai na rika kururuwa ina cewa, "Wallahi Allah ya haramta wannan danyen aiki da kuke shirin aikatawa. Ba ku ganin ni bako ne, ba al'adarmu daya da ku ba. Don me za ku rufe ni da raina? Wallahi da na san haka al'adarku take da ban yarda na yi aure ba."
Af, babu wanda ya kula da hargowata, suka kama ni da karfi suka daure da igiya, suka zuba mini ruwa a cikin gora da 'yar gurasa guda bakwai, suka zura ni cikin rami kamar dai yadda al'adarsu ta tanada. Da suka ji na sauka kasan ramin sai suka yi mini magana da karfi, wai in kwance igiyar da aka zuro ni da ita cikin ramin daga jikina, ni kuwa sai na ki. Da suka ga ba ni da niyyar kwance igiyar sai suka jeho mini ita cikin ramin suna cewa, tafi da ita idan igiya na amfani a lahira. Suka ja dutse suka rufe bakin rami gam, suka tafi abinsu.
Na sami kaina a cikin wani irin rami mai duhu, sai kasusuwan mutane ko'ina bargaja kamar an watse kara. Ga wani irin doyi da hamami na tashi, cikin dan kankanin lokaci sai na ji iska na gagara ta shaka. Na zargi kaina da kaina, na ce a cikin raina, "Wace wauta ta sa na yi aure a cikin wannan birni? Babu shakka duk abin da ya same ni ba ni da kaico."
Na ci gaba da cewa, babu tsimi babu dabara face daga Allah Madaukakin Sarki. Duk lokacin da na kubuta daga halaka sai in kara fadawa cikin wadda ta fi ta. Wallahi mutuwa a cikin ruwa ta fi wannan mummunar mutuwa da zan yi. Ina ma a ce na mutu a cikin teku lokacin da jirginmu ya kife, ko kuma yunwa ta kashe ni a cikin tsibirin zindirawa.
Na ci gaba da zama cikin wannan rami, ba na iya banbance dare balle rana, bakina kuwa ba ya rufuwa, kodayaushe ina karanta duk addu'ar da ta fado mini cikin rai.
Na jefa kaina bisa kasusuwan matattu na yi kwance, hawaye na zuba daga idanuna. Na ci gaba da rokon Allah ya kubutar da ni daga wannan hali da nake ciki. Na yi ta jiran mutuwa ta zo ta dauke ni, amma ba ta zo ba.
A nan asuba ta riski Shaharuzad, a karshen dare na dari biyar da hamsin da uku (553), ta katse zancenta mai dadin saurare.
(c) 2015 Taskar Bukar Mada
http://bukarmada.com/
Bukarmada@gmail.com
Twitter: @bukarmada
Whatsapp: +2348021218337
PIN: 2BDDD505
To, an ce kyawun alkawari cikawa. Na yi muku alkawari zan kawo muku labarin tafiye-tafiyen Sindibad hudu daga cikin bakwai, ga shi na kawo. Labarin sauran tafiye-tafiyen uku (wadanda sun fi wadanda muka kawo dadi da ban mamaki), da kuma karshen wannan tafiya, da yadda zai fito cikin rami, sai ku nemi littafin idan ya fito ku karanta.
Idan Allah ya kai mu ranar Laraba mai zuwa, da karfe tara na dare (9:00PM), zan kawo muku wata sabuwar hikayar mai dadi da armashi, watakila ma ta fi wannan da muka gama dadi.
Allah ya kai mu!


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment