Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyu.
Iska ta yi ta tura mu cikin teku da sauri. Yunwa da kishirwa suka taso mana, ba maganar gajiya da rashin barci ake yi ba. Haka dai muka daure iska ta yi ta tura gadonmu cikin ruwa.
Can bayan gari ya waye, rana ta fito ta baje haskenta bisa ruwa sai muka hangi wani tsibiri can nesa gare mu. Sai muka karkata gadon da muke kansa, wanda yake shi ne tamkar jirgin ruwa a gare mu, muka nufi wannan tsibiri.
Muka isa bakin gaba muka sauka cikin tsibirin, muka iske shi cike da itatuwa masu 'ya'ya, da tsuntsaye iri-iri suna shwagi bisa itatuwan. Ga kuma ruwan koramu suna gudana ko'ina. Muka debi 'ya'yan itace muka ci muka koshi, muka sha ruwa, karfin jikinmu ya dan dawo kadan.
Muka zauna karkashin inuwar wata bishiya muna hutawa. Muka gode wa Allah da ya tsirar da mu daga tsibirin bakaken dodanni da kuma hadarin teku. Muka ci gaba da zama karkashin wannan itaciya har dare ya soma yi.
Daga nan sai muka share wuri muka kwanta, abinka da gajiyayyu nan take sai barci mai nauyi ya dauke mu. Ba mu yi nisa cikin barcin ba sai wata iska mai karfi ta tayar da mu, muka yi zazzaune muna neman dalilin wannan iska.
Sai muka ji wani irin huci mai karfi kamar ana watsa wa wutar gobara ruwa. Mu duba haka sai muka ga wani irin katon maciji shimil. Wannan maciji girmansa ba ya misaltuwa, ba don yana motsi ba sai mutum ya ce iccen rimi ne ya fadi kasa aka sassare rassan aka bar gangar jikin. Wanna iska da ta tayar da mu daga barci duk ta hucinsa ce.
Kafin mu ankara har macijin nan ya zagaye mu da jikinsa, ya sanya mu tsakiya kamar an zagaye mu da katanga. Sai ya sa bakinsa ya cafko mutum daya daga cikinmu, ya hadiye shi iya kafada. Muka ga kafafun dan uwanmu na wutsil-wutsil kamar dai yadda kafafun kwado kan yi idan babba-da-jaka ko zalbe zai hadiye shi. Daga nan sai macijin ya karasa hadiye falken nan gaba daya. Sai muka rika jin wata kara rugugugu a cikin cikin macijin nan yayin da kasusuwan dan uwanmu ke karairayewa.
Daga nan sai maciji ya tafi ya bar mu nan cikin tsananin tsoro da tashin hankalin wannan irin mutuwa ta dan uwanmu.
Sanarwa Haryanzu Ba.a samun
Comments dinku danake buqata Please inkasan baza
ka'iya comments ba tokayi share ko like domin waensu su gani nagode @Smarteey
Muka fashe da kuka muna cewa, "Wallahi wannan abin firgici ne da tashin hankali! Duk lokacin da muka kubuta daga halaka sai mu afka cikin wata wadda ta fi ta."
Da muna murna mun kubuta daga bakin dodo da hatsarin teku, ga shi yanzu mun fada cikin wata musibar da ta fi ta baya ban tsoro. Babu tsimi babu dabara face daga Allah Madaukakin Sarki. Idan da fari mun tsere wa bakin dodo yanzu yaya za a yi mu tsere wa wannan maciji?
Daga nan sai maganar barci ta kare, muka tashi muna zagaya tsibirin har muka iso ga wata doguwar bishiya, muka yanke shawarar mu hau samanta mu kwana saboda tsoron kada macijin nan ya dawo. Muka haye saman bishiya muka sami rassa masu fadi muka kwanta, ni ina daga kololuwar bishiyar abokina yana daga kasana. Ba maganar barci ake yi ba, ban da zulumi babu abin da ke cikin ranmu.
Zuwa goshin asuba sai ga macijin nan ya zo wajen itaciyar nan da muke kanta. Ashe ya tafi inda muka fara kwantawa bai ganmu ba, sai ya biyo warinmu har zuwa wurin bishiyar. Yana zuwa kuwa sai ya yi rimi ya cafko abokin nan nawa. Ya hadiye shi zuwa kafada, da ya gama shure-shure sai ya iyar da hadiye shi.
Idanuna suka fito kwala-kwala kamar za su fadi kasa don tsoro, ina kallon abin da ke faruwa. Na ji kasusuwan abokina na karairayewa a cikin cikin maciji. Da ya gama hadiye shi sai ya juya ya tafi abinsa. Aka bar ni saura ni kadai a cikin wannan tsibiri.
Bayan gari ya waye ina kan bishiya, na duba ko'ina amma ban ga alamun macijin nan ba. Da na tabbar ba ya kusa sai na sauko daga itaciya, jikina a sanyaye kamar mara laka saboda tsananin tsoro. Na tabbata babu abin da zai kubutar da ni daga wannan maciji. Kafin gobe war haka, ko shakka babu, na zama tarihi. Wata zuciya ta ce in fada cikin teku mana in mutu da maciji ya hadiye ni, amma sai na kasa aikata haka, kun san rayuwa da dadi.
.
Nidinne dai
Al amin Ahmed
Guyson nake cewa
Sai Allah Ya kaimu
Gobe Zamu ci gaba
NO: 08064594218
June 20, 2017 at 8:18
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
9-HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO
Al amin Ahmed guyson Nake Magana
.
Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce, bayan gari ya waye ina kan bishiya, na duba ko'ina amma ban ga alamun macijin nan ba. Da na tabbar ba ya kusa sai na sauko daga itaciya, jikina a sanyaye kamar mara laka saboda tsananin tsoro. Na tabbata babu abin da zai kubutar da ni daga wannan maciji. Kafin gobe war haka, ko shakka babu, na zama tarihi. Wata zuciya ta ce in fada cikin teku mana in mutu da maciji ya hadiye ni, amma sai na kasa aikata haka, kun san rayuwa da dadi.
Daga nan sai wata dabara ta fado mini a cikin rai. Na je na karyo rassan itatuwa dogaye guda biyar, kowane daya ya fi ni tsayi sau uku, na ciri ciyawa na tufka igiyoyi, na ajiye su inda zan kwana karkashin wata bishiya. Da na ga marece ya fara shigowa sai na zauna karkashin itaciyar nan. Na dauko itatuwa guda hudu na daure su da kusurwowin juna, daya a kasa, daya a sama, daya a gefen dama, daya a gefen hagu, kamar dai an shata kofar wani babban daki. Icce na biyar kuma na daura shi a tsakiya daidai tsawona. Na shiga tsakiyar itacen na daure tafin kafafuna ga icce na kasa, na yi rawani da iccen tsakiya wanda ya taba kaina, na kwanta rigingine a tsakanin itatuwan nan, sun killace ni ta ko'ina.
Can da dare ya yi, sai ga macijin nan sa-ka-ka-ka ya biyo warina, ya zo inda nake. Ya yi niyyar hadiye ni amma babu dama saboda itatuwa sun tsare ni ko'ina. Ya juya ko wane bangare yana neman makamata amma bai samu ba. Ni kuwa na yi zurui da ido ko kiftawa ba na yi saboda tsoro. Macijin nan sai ya tafi sai ya dawo har asuba ta matso, da dai ya ga babu yadda zai yi ya hadiye ni kuma ga gari na shirin wayewa, sai ya hadiyi miyau ya yi tafiyarsa. Da gari ya waye sai na kwance kaina, hannuwana na rawa kamar tsohuwar da sanyi zai halaka. Na nufi bakin gaba da sauri ko na sami hanyar fita daga cikin wannan tsibiri. Domin na san idan dare ya yi macijin nan zai dawo da tasa dabarar, don haka ba lalle ba ne dabarar da na yi jiya ta fisshe ni yau ba. Ina nan tsaye bakin gaba ina addu'a ga Allah da ya koro mini da mafita, sai na hangi wani abu can daga nesa cikin teku kamar jirgin ruwa. Na murje idanuna na kara hangawa, babu shakka jirgin ruwa ne, kuma babba irin na fatake. Sai dai jirgin ba tsibirin da nake ya nufo ba, yana shirin gilmawa ne ya wuce. Nan da nan na karyo ganye bishiya, na yi ta daga shi sama ina kadawa cikin iska, ina kira da karfi domin masu jirgin su ji. Allah da ikonsa kuwa sai suka hango ni, sai na ga jirgin ya karkato zuwa inda nake.
Da suka zo sai na kwashe labarina duka na gaya musu, suka tausaya mini, suka saka ni cikin jirginsu muka tafi. Na gode wa Allah da ya kubutar da ni daga sharrin maciji na tausaya wa abokaina da suka halaka, na yi musu addu'a. Masu jirgi suka kawo mini abinci da ruwan sha mai sanyi, na ci na koshi, na gode wa Allah na gode musu bisa wannan karimci nasu. Hankalina ya kwanta, karfin jikina ya dawo, na kara yin godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya kubutar da ni daga halaka, sai na ga abubuwan da suka faru sun zama tamkar a mafarki. Ba mu gushe ba muna tafiya, iska kuwa ta yi wa jirginmu dadi, har muka iso ga wani tsibiri mai suna Assalahidati, wannan tsibiri kuwa cike yake da itatuwan sandal, Madugu ya ce a yada zango a cikinsa.
Aka daure jirgi a bakin gaba, fatake suka fita da hajarsu domin yin ciniki. Sai Madugu ya juyo gare ni ya ce, "Bawan Allah, ga shi kai bako ne, ka gaya mana cewa kai falke ne wanda ya hadu da hadarurruka iri-iri har ka rasa hajarka. Ina so in taimake ka ka koma gida da dan abin hannunka, kada ka koma hannu rabbana. Kasan an ce alheri ba ya da kadan, masu hikimar magana ma suna cewa, ya da alheri a baya ka tsince shi a gaba."
Allah yasaka muku da alkhari
Gaskiya yanzukam kuna yin comments kuma Abokin hira na godiy da hakan..ba lallai saikayi
Comments mai yawaba ko tnx ka rubuta tofa ka qara mana qwarin gwuiwane..Nine naku
Smarteey
"Wane irin taimako kake so ka yi mini?" Na tambaye shi.
Madugu ya ce, "Ka sani cewa mun fito gida da wani falke, tun da muka sauka a wani tsibiri muka huta ba mu kara ganin shi ba, ba mu sani ba ko yana raye ko ya mutu, har yanzu dai ba mu ji duriyarsa ba. Da na so sai mun koma gida in nemi iyalinsa in aika musu da hajar. Amma yanzu ina so in ba ka wannan haja ka yi kasuwanci da ita a cikin wannan tsibiri, ribar duk da aka samu, idan muka koma Bagadada, sai a raba ta biyu ka dauki rabi a ajiye wa mai kayan rabi. Ka yarda da haka in dauko maka hajar ka tafi tare da sauran fatake?"
Yayin da na ji ya ambaci Bagadada sai na ji kamar ya tsire ni da allura, ashe ma wadannan fatake na wajenmu ne. Na amsa masa da sauri, "Na yarda da wannan sharadi." Na yi ta gode masa har babu adadi. Madugu ya ce a fito mini da hajar falken nan da ya bace.
Mai kula da kayan jirgi ya tambayi Madugu, "Wane suna aka rubuta a jikin hajar?"
Madugu ya ce, "Wadda aka rubuta wa sunan Sindibad mai teku. Wanda ya bata a tsibirin tsuntsayen Rukki. Wannan bako za mu ba kayan ya yi fatauci da su, ribar duk da aka samu sai a raba biyu ya dauki kashi daya."
Mai kula da kaya ya ce, "Ai kuwa hakan da ka yi ya yi daidai ya Ra'isu."
Yayin da na ji Madugu ya ambaci sunana, ban san lokacin da bakina ya subuce ba don murna na ce, "Wallahi ni ne Sindibad mai teku."
Suka kalle ni haka galalala kamar masu kallon motsattse. Da na ga dai alamun ba su yarda da zancena ba sai na tambayi Madugu, "Yalla ka san Sindibad din ne?"
"Ni ban san shi ba," in ji Madugu, "amma shi mutumin Bagadada ne, ana yi masa lakabi da Sindibad mai teku. Da shi muka baro kasar Iraki har muka iso wani tsibiri na manyan tsuntsaye, tun daga nan sai ya yi mana batan dabo. Muna kyautaata zaton wata dabba ta cinye shi a cikin tsibirin."
Daga nan sai na fashe da kuka, kuka mai tsanani, na ce, "Ya kai wannan Madugu amintacce! Wallahi ni ne Sindibad mai teku. Bari ka ji yadda abin ya kasance haka. Yayin da muka sauka a cikin wancan tsibiri da kake magana, mun tafi tare da wasu fatake domin mu zagaya cikinsa. Sai na zauna a gindin wata bishiya mai sanyin inuwa, na ci abinci na sha ruwa, daga nan sai na kishingida domin in huta sai barci ya kwashe ni. Yayin da na farka sai na ga kun tafi kun bar ni. Wallahi wannan hajar tawa ce, da a ce za mu hadu da tajirai masu dibar lu'ulu'u a kwarin macizai da sun shaida ni, domin na shaida musu labarin yadda aka yi jirgi ya bar ni a tsibirin Rukki, da yadda aka yi na baro tsibirin na fada cikin kwarin macizai inda tajirai ke dibar lu'ulu'u ta dabarar jefa danyen nama."
Lokacin da fatake suka ji jawabina sai suka kewaye ni suna kallo, wasu suka yarda da maganata wasu kuwa suka ce karya nake yi. Amma yayin da wani daga cikin fataken nan ya ji na ambaci kwarin macizai mai lu'ulu'u sai ya kara dubana tun daga kasa har sama, ya juya ga fatake ya ce musu, "Ku saurari zancena ya ku 'yan uwana. Idan ba ku manta ba lokacin da ina ba ku labarin tafiye-tafiyen da na yi da abubuwan ban mamaki da na gano, na gaya muku cewa akwai wani kwarin macizai wanda yake cike da lu'ulu'u, babu mai iya shigarsa balla ya kwaso wannan dukiya. Na gaya muku cewa sai dai mu rika yanka dabba muna fede ta, sai mu jefa naman a cikin kwarin, lu'ulu'u mai yawa zai lillike a jikin naman. Idan tsuntsaye masu farauta sun shiga kwarin za su dauko naman su fito da shi, sai mu kore su mu cire lu'ulu'un. Kamar yadda na gaya muku wata rana na jefa dabbata a cikin kwarin, yayin da tsuntsu ya fito da ita sai na ga mutum a tsaye kusa gare ta. To, kun dai san sauran labarin da na fada muku, daga karshe dai kuka ce labarina zuki-ta-malli ne, wai babu wani kwarin lu'ulu'u a duniya."
Fatake suka amsa gaba daya, "An yi haka kuwa, ka gaya mana wannan labari amma daga karshe muka karyata ka."
Falke ya nuna Sindibad ya ce, "To, wannan shi ne mutumin da ya fito tare da dabbar da na jefa, kuma ya ba ni dukiya mai yawa wadda tamaninta ba ya misaltuwa, ya gaya mini sunansa Sindibad mai teku. Daga nan muka tafi tare da shi har birnin Basara, a can muka rabu ya ce zai nufi Bagadada, mu kuma muka nufi tamu kasa. Na gode wa Allah da ya turo shi nan, domin ya gasgata labarin da na ba ku kuka karyata ni. Kuna nan zaune kifin rijiya kawai, ba ku san kome ba sai mutum ya kawo muku labari ku karyata shi. Ni na yarda da shi, babu shakka wannan hajarsa ce."
Yayin da Madugun jirgi ya ji zancen tajiri, sai ya matso kusa gare ni, ya dube ni da kyau ya ce, "Yaya yanayin hajarka take, idan har gaskiya kake fada?"
"Abu kaza da abu kaza ne a ciki," na amsa masa. Na kuma kara tuna masa wasu abubuwa da suka faru yayin tafiyarmu a cikin jirgi daga Basara zuwa tsibirin da suka bar ni. Daga nan sai ya yarda lalle dai ni ne Sindibad. Ya rungume ni cikin kirjinsa yana cewa, "Wallahi ya shugabana, labarinka abin mamaki ne da ban tausayi. Godiya ta tabbata ga Allah da ya kubutar da kai daga halaka ya kuma sake sada ka da hajarka."
.
Nidinne dai
Al amin Ahmed
First admin
Na zauran labarai page
Guyson nake cewa
Sai Allah Ya kaimu
Gobe Zamu ci gaba
08064594218
June 21, 2017 at 7:08 AM ยท Public
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
10. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO
.
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
.
Sabuwar Fassarar: Ibrahim Malumfashi, Danladi Haruna, Bukar Mada.
.
Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce, Madugun jirgi ya yi godiya ga Allah da ya kubutar da ni daga halaka ya kuma sake sada ni da kayana. Na karbi hajata na shiga ciniki, in sayar in saya, na sami riba mai tsananin yawa. Muka ci gaba da zagaya tsibirai muna saye muna sayarwa har Allah ya kawo mu kasar Hindu. Muka sayi kayan yaji masu yawa irinsu citta da tafarnuwa, saboda suna da riba sosai a Birnin Bagadada. Daga Hindu kuma sai muka ci gaba da tafiya har muka dangana da kasar Sin, muna saye muna sayarwa. A cikin tekun Hindu na ga abubuwan mamaki wadanda ba su ko kidayuwa. Kadan daga cikinsu su ne, na ga wani irin katon kifi kamar saniya, sai ya fito da 'ya'yansa bisa ruwa yana ba su nono suna sha, kamar yadda 'yan Adam ke shayar da 'ya'yansu. Saboda tauri da karfin fatar wannan kifi, da ita ake yin sulke ko garkuwa wadanda ake amfani da su wurin yaki. Haka kuma na ga wasu kifayen, wasu siffar jakai wasu siffar dawaki. Na ga kuma kunkuru wanda girmansa ya kai kafa ashirin, wannan kunkuru zai iya daukar kato kome girmansa, ya yi tafiya da shi bisa bayansa. Na kuma ga wani tsuntsu wanda idan ya yi kwai ba ya kyankyashe shi sai bisa ruwa. Ba mu gushe ba muna tafiya cikin teku, cikin kyakkyawan yanayin iska da tsarewar Ubangiji har Allah ya nufe mu da dawowa Birnin Basara. Na huta kwana biyu a Basara, daga nan sai na dunkule kayana na nufi Birnin Bagadada, birnin aminci. Na isa gidana lafiya, na tarar da 'yan uwa da abokan arziki lafiya. A wannan tafiya na sami riba bisa riba har abin ba ya kidayuwa. Na bayar da sadaka ga mabukata, na ciyar da marayu, na rarraba wa abokaina kyaututtuka iri daban-daban.
.
Na ci gaba da rayuwata kamar da, in ci mai kyau in sha mai kyau. In sanya sutura ta alfarma in harde bisa karaga ina hura hanci kamar wani sarki. Wannan shi ne labarin tafiyata ta uku a cikin teku. Idan Allah ya kai mu gobe lafiya, zan gaya muku labarin tafiyata ta hudu a cikin teku wadda ta fi sauran tafiye-tafiyen da na ba ku labari ban mamaki. Bayan Sindibad mai teku ya gama wannan labari sai ya ba Sindibad dan dako dinari dari ya kuma ce a kawo musu abinci da abin sha. Aka jera akussan abinci da nama, Sindibad mai teku ya ci tare da Sindibad dan dako a akushi daya, sauran tajirar duka suka ci daga nasu akussan. Bayan sun gama cin abinci, sun sallaci sallar isha'i sai suka yi sallama da mai gida suka watse, kowa ya nufi gidansa yana mamakin labarin mai gida. Dan dako ya nufi gida zuciyarsa cike da mamakin labarin da takwaransa mai teku ya bayar. Ya kwanta barci yana alla-alla gari ya waye ya koma gidan mai gida domin ya ji labarin tafiyarsa ta hudu a cikin teku. Tun da assalatu dan dako ya farka, bayan ya yi sallar asuba sai ya zauna yana wuridi har gari ya yi sha. Da ya ga rana ta kunno kai haskenta ya sauka bisa jigayi da rufin gidaje, sai ya kimtsa ya nufi gidan Sindibad mai teku. Ya isa gidan, bayi suka shigar da shi dakin mai gida, ya zauna yana jiran fitowarsa. Bai dade da zama ba sai ga sauran tajirai suna shigowa daya bayan daya. Bayan sun hadu gaba daya, can sai ga mai gida ya fito cikin sutura ta alfarma, yana takawa dai- dai kamar dawisu. Suka gaisa da sauran abokansa tajirai, ya harde bisa karagarsa kusa ga Sindibad dan dako. Aka kawo musu abinci suka ci suka koshi, suka yi barkwanci a tsakaninsu cikin annushuwa da farin ciki. Daga nan sai Sindibad mai teku ya fara bayar da labarin tafiyarsa ta hudu: TAFIYAR SINDIBAD TA HUDU A CIKIN TEKU. Ku sani ya ku abokaina, bayan na dawo gida daga tafiyata ta uku da dimbin dukiya wadda ba ta misaltuwa.
.
Na zauna cikin farin ciki, ba ni da wani aiki sai dai kullum in gayyato abokaina mu wanke goma mu tsoma biyar. Ina nan kan haka sai ran nan wasu attajiran fatake, abokaina daga Basara, suka kawo mini ziyara. Bayan mun gama kwasar gara sai muka shiga hirar duniya da labarin tafiye-tafiye. Nan fa zuciyata ta motsa, suka takalo mini sha'awar sake fita cikin duniya, na manta kwata-kwata da wahalhalun da na sha a baya. Na yi sha'awar ganin al'ummomin wasu kasashe da al'adunsu. Nan take na yanke shawarar sake fita cikin duniya domin yin fatauci. Tun daga wannan rana na fara shirye-shiryen tafiya, na sayi kayayyakin zuwa fatauci masu yawa da tsada fiye da wadanda na taba tafiya da su a baya. Da lokacin tafiya ya yi sai na yi sallama da 'yan uwa da abokai, na kwashi kayana sai Birnin Basara, inda zan hadu da abokan tafiyata, wadanda suke su ne manya-manyan attajiran birnin. Muka shiga jirgi muka fada teku. Iska ta yi wa jirginmu dadi, muka yi ta tafiya daga wannan tsibiri zuwa wancan, muna saye muna sayarwa. Ran nan muna tafiya cikin dadin rai, kwatsam sai teku ta canja mana hali. Guguwar ruwa ta taso, rakuman ruwa kuwa suka yi ta kwallo da jirginmu kamar zai kife. Da saboda ban yarda na ci abincinsu ba, duk kuwa da cewa kullum sai sun kawo mini abincin wai in ci.
.
Da suka ga dai na ki kula abincinsu, kuma ga shi duk na rame, daga fata sai kashi, sai suka yi watsi da ni suka ma daina kula ni. Ni kuwa da na ga haka sai na saci jiki wata rana na sulale daga gidan nan na gudu. Bayan na yi nisa da gidan zindirawa sai na tasar wa bakin gabar teku, wadda take da nisa kwarai daga gidan zindirawa. Na kusa isa bakin gaba ke nan, sai na hangi wani tsoho daga cikin zindirawan nan. Ina ganinsa na shaida shi, shi ne wanda ke kiwon mutanen da suka kama.
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
11. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce,
bayan na yi nisa da gidan zindirawa sai na tasar
wa bakin gabar teku, wadda take da nisa kwarai
daga gidan zindirawa. Na kusa isa bakin gaba ke
nan, sai na hangi wani tsoho daga cikin
zindirawan nan. Ina ganinsa na shaida shi, shi ne
wanda ke kiwon mutanen da suka kama. Yayin
da tsohon nan ya gan ni sai ya shaida ni, ya san
cewa kuma ina cikin hankalina ba kamar sauran
da yake kiwo ba, don haka sai ya tabbatar da
cewa ina shirin tserewa ne. Ga mamakina sai na
ga yana daga mini hannu yana yi mini ishara da
in koma da baya in bi ta hanyar da ta yi hannun
dama. Na ga yana nuna mini cewa wannan
hanyar da na biyo mai hatsari ce. Don haka ban
yi gardama ba, sai na juya da baya na nufi
hanyar da ta yi hannun dama. Na rika gudu don
tsoron kada a kama ni, idan kuma na gaji da gudu
sai in yi tafiya, har na bace wa tsohon nan.
Yayin da rana ta fadi duhun dare ya fara
mamaye tsibirin nan, sai na sami wuri na zauna.
Na yi niyyar in kwanta in yi barci saboda gajiya,
sai wata zuciya ta ce ahir! Don haka na yi zaune
ina ta karanto duk wata addu'a da ta fado mini
cikin zuciya. Can da dare ya raba sai na tashi na
ci gaba da tafiya. Ban gushe ba ina tafiya har
hasken safiya ya keto sararin samaniya, wuri ya
yi sha da hasken safiya gwanin ban kaye. Rana
ta dago sama, haskenta ya haske duwatsu da
ciyawa da jigayi. Daga nan fa sai cikina ya fara
kiran ciroma, na duka na ci ciyawa da hakukuwa
gudun kada in halaka da yunwa. Na lasa dan
danshi-danshin raba da ke jikin ciyayi a matsayin
ruwa, daga nan sai na ji karfin jikina ya dan
dawo. Na ci gaba da tafiya tsawon wannan rana,
ban gushe ba har sai da dare ya yi. Na zauna na
huta, bayan dare ya raba na ci gaba da tafiya har
zuwa wayewar gari. Na ci ciyawa, na sha ruwan
rabar da ke jikin ciyawa. Ban gushe ba cikin
wannan hali har tsawon kwana bakwai. A cikin
kwana na takwas ne na hangi wani abu can daga
nesa kwarai, ban gane ko menene ba.
Na nufi wannan abu ina cewa a cikin raina ko ma
menene ya kashe ni in huta da wannnan bakar
wahala. Yayin da na yi kusa da abun sai na ga
ashe gungun mutane ne suna dibar goran yaji. Da
suka hango ni sai suka taso mini, suka zagaye ni
suna kallo, kamar masu kallon wata bakuwar
dabbar da ba su taba gani ba. Suka tambaye ni,
"Mutum ko aljani? Daga ina ka fito cikin wannan
tsibiri."
Na amsa musu, "Ni mutum ne dan uwanku." Na
ba su labarin abin da ya faru gare ni duka, da
wahalhalun da na sha. Na

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment