Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dan Adam, da ya farfado daga mutuwar tsayen da ya yi, sai na ga ya duka wurin dabbar nan yana duba karkashinta. Ya juya ta gaba daya bai sami lu'ulu'u ko daya ba. Sai ya buga sallallami yana cewa, "Babu sarki sai Allah mai girma da daukaka, wanda muke neman kariyarsa daga sharrin Shaidan jefaffe!"
Ya yi ta tafa hannuwa yana salati cike da jimami yana cewa, "Ya aka yi wannan abu ya faru? Shike nan na yi asarar dabbata?"
Na matsa kusa gare shi. Yana ganina sai hankalinsa ya komo gare ni. Ya tambaye ni, "Wanene kai, mutum ko aljan? Ya aka yi ka zo nan?"
Na amsa masa, "Kada ka ji tsoro. Ni mutum ne, falke. Labarina yana da ban mamaki. Yadda na shiga cikin wannan kwari kuma na fito abu ne mai matukar daure kai. Ina so ka kwantar da hankalinka, idan dai don lu'ulu'un da ake samu ne a cikin wannan kwari zan ba ka wanda zai ishe ka har tsawon rayuwarka."
Sai na ga fuskar tajirin nan ta washe da farin ciki. Ya duka ya yi ta gode mini kamar wanda aka ba duniya duka. Muka yi ta mayar da zance, ni da shi, har 'yan uwansa suka jiyo mu, suka fito daga inda suke labe suka zo wurin mu. Kowanensu kuwa ya jefa dabbarsa a cikin kwarin nan. Muka gaisa da juna.
Suka ja ni muka nufi cikin gari, muna tafe ina gaya musu labarina. Na gaya musu yadda muka shigo cikin teku tare da 'yan uwana fatake, da yadda muka yada zango a cikin tsibirin da barci ya dauke ni, aka bar ni can. Na fada musu dabarar da na yi na daure jikina a kafar Rukki har ya kawo ni cikin kwarin lu'ulu'u, da irin macizan da na gani a cikin kwarin. Na gaya musu dabarar da na yi na fito daga cikin kwarin.
Da suka ji wannan labari sai na ga suna ta kada kai don mamaki. Na debo lu'ulu'u mai yawa na ba mai dabbar da tsuntsu ya fito da ita. Su ma sauran tajiran na 'yan musu wani abu. Suka yi ta godiya suna murna. Suka yi ta yi mini addu'a suka ce, "Mun rantse da Allah ka zama dashi mai yawancin rai. Ai babu mahalukin da ya taba shiga wannan kwari ya fito da rai sai kai. Tajirai da yawa sun gwada shiga da kwanduna wajen dibar lu'ulu'u amma babu wanda aka kara jin duriyarsa. Godiya ta tabbata ga Allah da ya kubutar da kai."
Da dare ya yi ba mu isa gari ba sai muka sami wuri muka kwanta. Ina cike da farin cikin kubuta daga kwarin macizai da kuma tsibirin tsakiyar teku da babu dan Adam ko daya. Yanzu kuwa ga ni cikin karkara tare da mutane 'yan uwana. Na kara gode wa Allah.
Bayan gari ya waye, rana ta fito ta watsa haskenta bisa kasa da duwatsu, muka ci gaba da tafiya tare da tajirai. Wannan kasa cike take da duwatsu da kwazazzabai. Kowane kwari kuwa cike yake da macizai.
Muna cikin tafiya muka iso ga wani tsibiri mai cike da bishiyoyin kafur. Kowace bishiya daya mutum dari na iya zaunawa karkashinta ya sha inuwa saboda girmanta.
Tajirai suka gaya mini cewa daga jikin wadannan bishiyoyi ake fitar da kafur. Yadda ake dibar sa kuwa shi ne, sai a soka wa itacen wani karfe mai hanya a tsakiyarsa, a sa karfen cikin gora. Ruwan itacen zai ta biyowa ta cikin karfen yana shiga cikin goran, da haka sai a cika goruna masu yawa daga bishiya guda. Idan ruwan ya taru da yawa sai ya daskare kamar danko. Shi ke nan kafur ya samu. Sai dai daga nan kuma itacen zai mutu, ya zama kwaure. Sai a sare shi a yi icen wuta.
Haka kuma a cikin wannan tsibiri na itacen kafur na ga wasu dabbobi tika-tika suna kiwo. Tajirai suka ce mini dabbobin nan su ake kira karkanda. Suna da girma sosai jikinsu kamar na rakumi, amma sun fi rakumi girma nesa ba kusa ba. Kafafunsu gajeru ne kwarai. A tsakiyar kansu daga can gaba suna da kaho guda daya tal, mai kauri da tsini, ya dan lankwaso baya kadan, amma ba ya da tsayi sosai. Suna cin ciyawa da ganyen itatuwa kamar bauna da saniya. Na taba ji fatake da alhazai na cewa, wannan dabba mai suna karkanda tana iya tsire babbar giwa da kahon nan nata, ta yi ta yawo da ita bisa kanta tana kiwo ba tare da ta damu da nauyinta ba. Har sai giwar nan ta mutu ta fara rubewa, idan rana ta narka kitsen giwar sai ya dararo ya shiga cikin idon karkanda, wannan shi zai yi sanadiyyar makancewarsa. Sai ya yi kwance a bakin teku. Daga nan kuma idan tsuntsun nan mai suna Rukki ya fito farauta ya ga wannan makahon karkanda a kwance, sai ya fyauce shi duk da giwar da ke bisa kansa ya kai wa 'ya'yansa su yi kalaci. Hmh! Kun fa ji ikon Allah.
Duk dai a cikin tsibirin kuma na ga wasu irin shanu da babu kamarsu a wannan kasa tamu. Da muka iso cikin gari na sayar da wani abu daga cikin lu'ulu'un da na samo, na sayi irin hajar kasar, wadda na tabbata idan na dawo da ita gida zan sami riba mai yawa. Na sayi dabbobi na lafta musu hajata, na bi ayarin fataken wannan kasa. Muka rika bin kasashe muna saye muna sayarwa. Na ga abubuwan mamaki iri-iri, na ga kasashe daban-daban da al'adunsu. Kwanci tashi har Allah ya kawo mu Birnin Basara. Bayan na huta kwana biyu, sai na bi wasu fatake muka nufi Bagadada gidan aminci.
Na sadu da 'yan uwa da abokan arziki. Na rarraba sadaka da kyaututtuka ga mabukata. Na rarraba wa abokaina dukiya mai yawa. Na koma ga dabi'ata ta cin abinci mai kyau da abin sha. Na rika sanya tufafi na alfarma ina kece raini. Na manta da duk wasu wahalhalu da na sha a baya. Na kasance babu wata damuwa a cikin raina. Mutane kuwa suka yi ta zuwa suna yi mini barka. Ni kuwa na yi ta ba su labarin abubuwan mamakin da na gano a cikin wannan tafiya tawa. Suka yi ta mamaki da jin wannan labari.
"Wannan shi ne karshen labarin tafiyata ta biyu a teku," in ji mai gida. "In Sha Allahu gobe zan gaya muku labarin tafiyata ta uku a cikin teku, wadda tafi wannan hatsari da ban mamaki."
Sindibad dan dako da sauran tajirai suka yi mamakin wannan labari na Sindibad mai teku. Daga nan aka kawo musu abinci da abin sha, suka ci suka koshi. Mai gida ya kawo dinari dari ya ba dan dako, ya sallame shi. Dan dako ya karbi kudi ya yi godiya, ya nufi gida cike da mamakin labarin da takwaransa ya bayar.
Koda ya isa gida dare ya yi, bayan ya yi sallah sai ya kwanta yana alla-alla gari ya waye ya koma gidan tajirin nan domin ya ji labarin tafiyarsa ta uku.
Gari na wayewa kuwa bayan Sindibad dan dako ya yi sallar safe sai ya nufi gidan Sindibad mai teku. Aka yi masa iso, ya shiga ya zauna a dakin shakatawar mai gida. Can jimawa kadan sai ga shi ya fito. Bayan ya zauna sai suka gaisa da juna, suka jira kadan har sauran tajirai suka iso. Bayan an kawo musu abinci sun nada, sun kora da abin sha mai dadi. Zuciyoyinsu suka yi fari, fuskokinsu cike da annushuwa. Mai gida ya dube su ya ce, "Ya ku abokaina, ku saurari labarin da zan ba ku, domin ku tabbatar da cewa ikon Ubangiji shi ne iko. Kuma Ubangiji shi kadai ya san adadin abubuwan mamakin da ya boye a cikin wannan duniya tamu." Mai gida ya ci gaba da labarinsa:
TAFIYAR SINDIBAD TA UKU A CIKIN TEKU
Kamar yadda na fada muku jiya, na dawo gida daga tafiyata ta biyu da dimbin dukiya, fiye da tafiyar farko da na yi. Allah ya kara wadata ni da dukiya fiye da wadda mahaifina ya bar mini gado, wadda na barnatar da farko. Na zauna cikin dadin rai da kwanciyar hankali, na manta dukan wahalhalun da na sha a baya.
Ina nan zaune kan haka, kun san zuciya da debe-debe, ran nan sai na ji babu abin da nake sha'awa irin na sake shiga cikin duniya. In ga kasashe da al'adunsu daga nan in dan taba fatauci.
Na sayi kayayyakin da zan yi wannan tafiya da su, na kulle su wuri guda. Na yi ban kwana da 'yan uwa da abokai, na nufi Birnin Basara. A can na sami wani babban jirgin ruwa zai tashi da fatake. Na yi wa Madugu magana, na biya kudi aka saka kayana. Na shiga jirgi tare da sauran fatake, kowa ya zauna bisa kayansa.
Jirginmu ya tsunduma cikin teku, bayan mun yi addu'o'in neman kariya da neman sa'ar wannan tafiya daga Allah Madaukakin Sarki. Muka yi ta keta ruwa, daga wannan teku zuwa waccan teku. Daga wannan tsibiri zuwa wancan. Daga wannan birni zuwa wancan. Babu hadari daya da ya same mu, muka ci gaba da saye muna sayarwa a duk birnin da muka sauka.
Wata rana muna cikin tafiya a teku ashe ba mu sani ba, iska ta kwashi jirginmu ta canja masa hanya. Ba mu ankara ba sai muka ganmu cikin wata teku mahaukaciya. Rakuman ruwa na ta toroko kamar jirginmu zai kife. Sai muka ga Madugu yana ta nazarin wannan teku da muka shiga. Ya duba dama ya duba hagu. Ya tada kansa ya yi duba nesa. Sai muka ga ya fara sallallami yana tafa hannuwa. Daga nan sai ya fashe da kuka, ya tube rawaninsa ya jefar a cikin ruwa. Ya rika marin fuskarsa yana tsige gemanya tasa.
Da ganin haka sai hankulanmu suka tashi, muka tambaye shi, "Ya Ra'isu, me yake faruwa ne?"
"Ku sani ya ku 'yan uwana, iska ta canja mana tafarki. Mun bar teku mai lafiya mun fada cikin teku mai hatsari. Gaba kadan za mu isa ga dutsen da ake kira Zugibu. Yana bisa wani tsibiri wanda babu kome a cikinsa sai wadansu irin manya-manyan halittu masu gashi kamar birai. Babu wani mutum da ya taba zuwa wannan wuri ya tsira da ransa. Ni kam tuni na yi ban kwana da rayuwata." Sai ya ci gaba da kuka, kamar dan yaro.
Madugu na gama mayar da jawabi sai jirginmu ya tsaya a bakin gabar wannan tsibiri. Kafin ayi haka sai muka ga birai sun kewaye jirginmu kamar kuda. Wadannan birai abin tsoro ne. Dukan jikinsu lullube yake da bakin gashi, baki kirin kamar gawayi. Idanunsu launin rawaya, da matsattsar fuska mara kyan gani, baki wuluk. Ga su 'yan kanana kamar 'ya'yan karnuka. Suna ta wata irin magana da junansu, Allah kadai ya san abin da suke cewa.
Muka ji tsoron mu far musu da kisa, domin idan muka fara kisan su, to, kuwa za su yi mana taron dangi, don kuwa an ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi. Muka yi tsuru-tsuru muna jiran mu ga yadda biran nan za su yi da mu.
Bayan sun gama magana da junansu, sai suka taru, kamar birai dari, sai su ciccibi mutum guda daga cikinmu su fitar da shi daga cikin jirgi su ajiye shi bisa tsibiri. Haka suka yi duk suka fitar da mu daga cikin jirgin. Daga nan sai suka fada cikin jirgin gaba dayansu, suka tuka suka tafi duk da kayanmu, ba mu san inda suka nufa ba. Suka bar mu nan tsaye muna karanta wasikar jaki.
Muka kasance cikin tsibiri muna ci daga 'ya'yan itatuwa muna sha daga ruwan koramu. Wata rana muna yawo cikin wannan tsibiri sai muka hango wani gini daga can nesa kamar gida. Sai murna ta kama mu, watakila mu iske mutane a cikin wancan gida da muka hango. Muka nufi wurin da sauri har muna tuntube, ashe ba mu sani ba, za mu kai kanmu ne ga halaka. Da muka isa kusa ga wannan gini sai muka ga ashe duk girmansa daki ne daya kwal.
Wannan daki ba irin dakunan da muka saba gani ba ne, daki ne babba mai tsayi. An gina shi da dutse, an zagaye shi da dogayen katangu. Yana da wata babbar kofa wadda sai rakumi ya shiga da mutum yana tsaye bisa bayansa, ba tare da mutumin ya sunkuyar da kansa ba don tsawonta. Kofar na da gambu daya da aka yi da iccen marke, an raba gambun biyu daga tsakiya ya zama marufi biyu.
Muka je bakin kofar muka tura gambun sai muka ga ya bude. Ba mu yi wata-wata ba sai muka kutsa kai cikin dakin. Wannan daki babba ne, don girmansa rakuma kamar hamsin na iya kwanciya cikinsa ba tare da wani ya taba jikin dan uwansa ba. A cikin dakin muka tarar da wani dogon dakali mai fadi na dutse. Sa'annan kuma a bangayen dakin an sassargafe kayan girki da na cin abinci, irinsu tukwane da akussa da goruna. Ga kuma murhun wuta, kusa ga murhun duk kasusuwan dabbobi ne bargaja. Amma ba mu ga wani mahaluki ba a cikin wannan daki, muka cika da mamakin wannan abu, matukar mamaki.
Muka zauna bisa dandamalin nan na dutse, da yake a gajiye muke tibis sai muka dan kwanta domin mu huta, sai kuwa barci mai nauyi ya dauke mu. Muka yi ta sharar barci tun da rana har marece ya yi ba mu farka ba. Muna cikin barci sai muka ji kamar kasa na girgiza, muka farka a firgice, muka yi zaune zuru-zuru.
Kasa kuwa ta ci gaba da girgiza kamar za ta tsage, muka rika jin hayaniya da hargowa da tankiya ta nufo dakin da muke ciki.
Ba zato ba tsammani sai muka ga wani irin mutum, shirgegen kato mai tsawo kamar iccen dabino ya shigo dakin. Jikinsa baki kirin da gashi ko'ina ya rufe jikin. Idonsa daya a tsakiyar goshi, ja jawur kamar garwashin wuta. Bakinsa wagege kamar bakin rijiya. Fatun lebbansa kuwa kamar na rakumi sun sauko har bisa kirjinsa, da hakori zaro-zaro kamar kasusuwa. Kunnuwansa kamar na giwa don girmansu, sun sauko har bisa kafadunsa. Ya shigo rike da wani busasshen iccen wuta, kumbunan hannunsa kamar na zaki. Da ya shigo sai ya mayar da kofa ya rufe garam.
Yayin da muka ga wannan shirgegiyar halitta, don mun tabbata ba mutum ba ne, sai hankalinmu ya tashi. Saboda tsananin tsoro da firgita sai muka zama kamar matattu.
(c) 2015 Taskar Bukar Mada
http://bukarmada.com/
bukarmada@gmail.com
Twitter: @bukarmada
Whatsapp: +2348021218337
...
Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, da karfe tara na dare (9:00PM). In sha Allah.
Allah ya kai mu!
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
7. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO
***guyson Ke Magana
Sindibad bahariyi ya ci gaba da labarinsa ya ce, yayin da muka ga wannan shirgegiyar halitta mai kama da mutum sai muka rude don tsoro, muka zama kamar matattu.
Da ya shigo cikin dakin sai ya zauna bisa dogon dakalin nan na dutse. Ya dube mu da idonsa daya mai kama da idon Dujjal, sai ya miko hannunsa ya rumke ni cikin tafin hannunsa kamar ya rumke kaza. Ya rika mammatsa jikina wai ya ji ko ina da maiko, kamar yadda rundawa kan yi idan za su yanka tinkiya.
To, ni kuwa da ma haka nake dan kyamas, duk dadin nan da nake ci a gida ba ni da kiba, balle kuma ga wahalar tafiya ta kara ramar da ni. Da ya ji jikina duk kasusuwa ne sai fata, sai ya jefar da ni gefe daya.
Ya mika hannunsa ya kara cafko wani falke, ya mammatsa shi ya jujjuya a cikin hannunsa, sai ya sake shi. Haka dai ya yi ta daukar mu daya bayan daya yana latsawa cikin hannunsa har ya dauki madugunmu. Madugun nan kuwa mutum ne lukuti mai kiba sosai.
Da katon nan ya latsa shi ya ji shi kiba-kiba kamar yadda yake so, sai ya fyada shi da kasa kamar yadda ake fyada kwado a kasa. Nan take Madugu ya mimmike bai ko shura ba.
Sai katon nan nan ya jawo wani dogon tsinke, ya tsire shi kamar yadda ake tsire kaza idan za a gasa ta. Ya hura wuta ga murhu, ya aza madugu saman murhun yana jujjuya tsinke har ya gasu ram, mai sai tsiyaya yake yi.
Da Madugu ya gasu sai dodon nan ya dauke shi daga kan murhu. Ya rika yago namansa guntu-guntu yana ci kamar mai cin kaza har ya cinye shi duka ya watsar da kasusuwan gefen murhu. Ya dauki ruwa ya kwankwada, ya zauna sa'a kadan sa'annan ya kwanta bisa dakalin nan ya mimmike, barci mai nauyi ya dauke shi.
Ya rika minshari da gwarti mai karfi kamar an yanke bijimin sa. Bai farka ba sai da gari ya waye, ya tashi ya fita wurin nasa harkoki, ya mayar da kofar daki ya rufe.
Bayan mun tabbatar da tafiyarsa sai muka zauna muna kuka saboda abin da muka gani na tashin hankali. Muka ce da junanmu, "Ina ma a ce jirgi ya kife da mu cikin teku duk mun halaka, ko kuma a ce biran da suka dauke jirginmu sun halaka mu da ya fi sauki da a gasa mutum bisa wuta a cinye. Wannan wace irin mutuwa ce? Amma abin duk da Allah ya kaddara zai sami bawansa babu mai iya karkare shi sai ya same shi. Babu tsimi babu dabara face ga Ubangiji Madaukakin Sarki."
Mukasakankance ga halaka. Muka yi ta yawo cikin dakin nan muna neman wani dan sako da za mu boye kafin dodon nan ya dawo ya ce zai gasa wani daga cikinmu. Muka zagaye dakin nan kaf babu wurin boyew, kuma mun yi dabarar duniyar nan domin bude kofar nan, amma abu ya gagara.
Da muka ga alamun maraice ya yi sai hankulanmu suka tashi, muka yi zaune muna jiran dawowarsa.
Can sai muka ji kasa na girgiza kamar za ta tsage, daga nan sai muka ga an bude kofar daki shirgegen dodon nan ya shigo, ya mayar da kofa ya rufe. Ya zauna bisa dakali, ya rika daukar mu daya bayan daya yana latsawa cikin hannunsa har ya dauki wanda ransa ke so. Ya aikata masa kamar yadda ya aikata wa Madugu. Ya gasa ci, ya cinye ya watsar da kasusuwa, ya daga tulun ruwa ya kyankyama. Daga nan sai ya kwanta barci ya yi ta gwarti kamar yankakken bijimi har gari ya waye. Ya tashi ya fita ya mayar da kofa ya rufe.
Muka hadu wuri guda muka ce wa juna, "Wallahi gwamma a ce jirgi ya kife da mu mun mutu a cikin ruwa da a gasa mu a cinye."
Sai wani falke daga cikinmu ya ce, "Ya ku jama'ar fatake ku saurari zancena. Mu hada kanmu mu san dabarar da za mu yi mu kashe wannan dodon banza mu tsirar da kanmu daga halaka da kuma sauran musulmi da kaddara ka iya korowa wannan tsibiri. Allah ya hore mana hankali da dabara fiye da dukkan sauran halittu."
Sai na ce da su, "Ku saurari zancena ya ku fatake. Idan har za mu jaraba kashe wannan dodo ne, to mu fara daura 'yan gadaje da wadancan tulin itacen da dodo ya tara kusa ga murhu, mu yi su kamar jirgin ruwa. Ya kasance kowane gado daya zai iya daukar mutum biyu ko uku. Idan muka yi nasarar kashe dodon sai mu yi amfani da gadajen a matsayin jiragen ruwa watakila Allah ya nufa mu fita daga wannan tsibiri. Idan kuma ba mu yi nasarar kashe shi ba sai mu fada cikin teku bisa wadannan gadaje, idan Allah ya kaddara za mu tsira shi ke nan, idan kuwa mun nutse cikin ruwa sai mu yi mutuwar shahada, domin an ce duk wanda ya mutu cikin ruwa, to ya yi shahada. Kuma ma ai gwamma mu mutu cikin ruwa da mu tsaya ana gasa mu da ranmu."
"Mun rantse da Allah," fatake suka amsa gaba daya, "Wannan shawara taka ita ce daidai." Dukanmu muka yarda da haka. Muka yi ta jido itace muna daura 'yan gadaje da su. Muka yi gadajen da za su ishe mu hawa dukanmu. Bayan mun gama wannan aiki sai muka zauna zaman jiran dawowar dodo.
Can bayan rana ta fadi, maraice ya fara yi sai muka ji kasa tana girgiza. Ba a dade ba sai muka ga an bude kofar daki, dodo ya shigo da itacen wuta rungume ga hannunsa, yana huci kamar karen da zai yi cizo. Ya watsar da da itace sharaf a gindin murhu, ya mayar da kofa ya kargame. Ya zauna bisa dakali ya sa hannunsa ya cafko daya daga cikinmu, ya mammatsa jikinsa. Da ya ji ya yi masa yadda yake so sai ya fyada shi da kasa, ya soke shi ga tsinke kamar an soke kifi. Ya hura wuta ya aza falken nan bisa, ya rika jujjuya shi har ya gasu. Ya cinye tsokar ya watsar da kasusuwan. Bayan ya kwankwadi ruwa sai ya mimmike bisa dakalin nan ya fara barci yana minshari kamar an yanke sa.
Da muka tabbatar da cewa barci mai nauyi ya dauke shi, sai muka dauki tsinken nan da yake tsire 'yan uwanmu da shi yana gasawa, girmansa kamar shinshiniyar rumfa. Muka dora shi bisa garwashin wuta, muka yi ta iza wutar har sai da tsinke ya yi jawur kamar garwashin wutar, muka dauke shi muka nufi inda dodo ke barci.
Da isarmu kusa ga kansa sai muka dubi idon nan nasa daya muka caka masa tsinken da iyakar karfinmu a tsakiyar idon, ji kake cus kamar an jefa garwashi a cikin ruwa. Nan take muka mayar da shi makaho.
Dodo ya farka a gigice ya dafe idonsa da hannu ya yi wani irin ruri mai karfin gaske har sai da bangayen daki suka motsa kamar dakin zai rushe. Muka tsorata tsoro mai tsanani. Don tsananin tsoro ma sai muka fadi kasa kamar matattu.
Dodo ya ci gaba da kara yana lalube-lalube ko zai kama daya daga cikinmu. Da muka ga haka sai muka fara zagaye-zagaye da shi a cikin dakin, zukatanmu cike da firgici, tuni mun sakankance da halaka.
Da ya ga dai bai kama mutum ko daya ba daga cikinmu sai ya fara laluben bango har ya tarar da kofar dakin ya bude ta. Ya fita waje yana kururuwa mai karfi, kasa kuwa ta rika girgiza kamar za ta tsage don karfin wannan kururuwa tasa.
Da muka ga ya fita ya bar kofar dakin a bude sai muka kwashi gadajen nan muka fita da sauri, muka bazama da gudu muka nufi bakin teku, ana kuwa kwala farin wata kamar rana, muka rika ce wa juna, "Watakila wannan rauni da muka yi masa ya zamanto sanadiyyar mutuwarsa."
Muna gab da isa bakin teku kamar an ce mu waiwaya, sai muka hango wasu dodannin guda biyu 'yan uwan wannan da muka soke wa ido sun nufo wurinmu da sauri. Idandunan nan nasu jawur a cikin farin wata kamar borkono, har ma sun fi wanda muka raunata ban tsoro.
Nidinne dai
Al amin Ahmed
Guyson nake cewa sai Allah Ya kaimu gobe Zamu ci gaba
Ebook created by Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng
8. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO
Al amin Ahmed guyson Nake Magana
.
Sindibad Mai teku ya ci gaba da labari ya ce, muna gab da isa bakin teku kamar an ce mu waiwaya, sai muka hango wasu dodannin guda biyu 'yan uwan wannan da muka soke wa ido sun nufo wurinmu da sauri. Idandunan nan nasu jawur a cikin farin wata kamar borkono, har ma sun fi wanda muka raunata ban tsoro.
Da ganinsu sai muka kara azama muka isa bakin teku, muka jefa gadajen nan bisa ruwa muka haye, muna tura ruwa da hannuwanmu. Ko da dodannin nan suka iso bakin gaba mun yi nisa cikin teku, da suka ga babu yadda za a yi su kama mu sai suka rika daukar manyan duwatsu suna jifar mu da su.
Suka sami wadansu daga cikinmu, 'yan gadajen suka kife da su cikin teku suka halaka. Ni kuwa da wasu fatake kadan muka tsira daga jifar da wadannan dodanni.
Iska ta yi ta tura gadajenmu da sauri a cikin teku har muka ba tsibirin dodanni baya muka kasance a tsakiyar teku, rakuman ruwa suka rika yin sama da kasa da gadajenmu kamar za a kifar da mu. Haka dai iska ta ci gaba da tura mu cikin teku ba mu san inda muka nufa ba. Abokan tafiyata suka rika mutuwa daya bayan daya, muka rage saura mu uku, ni da wasu mutum

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment