Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

batare da ta tuna kowa nata ba ga kuma karfaffar soyayyar da ta shiga tsakanin ta da Malam sosai suke San junansu Wanda lura da hakan ya sanya Baffa jin dad'i kanin mahaifinshi kenan Wanda shi ya tsaye musu har aka daura musu Aure.


ranar wannan masoyan sun shiga farincikin marar musaltuwa A funtua suka tare sabon gidan Malam da ke jabiri zamansu yaci gaba da wakana cikin soyayya da k'aunar juna saboda Zarah macece mai biyayya hakuri uwa uba Kirki Dan a zamanta da mutanen unguwar sai dai Sam barka Dan kowa Santa yake da kaunarta



aminiyarta d'aya a unguwar Saratu watau maman su Asmy a lokacin yarinyarsu d'aya Hauwa'u a lokacin suna cikin halin talauci Wanda hakan sosai ke damun Zarah hakan yasa bata iyacin Abu bata bata ba sunyi zama cikin mutunci da amintaka dukda Saratu ta girmi Zarah amma haka take girmamata kuma suke girmama juna.

"ana haka ne Zarah ta samu ciki Wanda tunda ta samu cikin takeshan wahala ta ke jin a jikinta cikin kamar shine ajalinta A tattare suka samu ciki da Saratu Inda lokacin mijinta ya samu warwara saboda daman yayi karatu Inda ya samu aiki a Bangaren agric saboda daman karatun malamin gona yayi .


kwana a tashi ba wuya wajen Allah a yanzu cikin Zarah ya shiga wata Tara Inda ranar wata Juma a ta tashi da nakuda kai tsaye Asibiti aka wuce da ita sosai take shan wahala tasan rayuwarta tazo karshe a lokacin ne kuma ta tuno da rayuwarta Ta baya Tana cikin halin nakuda ta ce " .

a kira mata Malam "haka ko akayi shigowarshi d'akin tayi daidai da haifo santaleliyar y'arta sak mai kama da Ita kamar an tsaga Kara an karya.

Ajiyar zuciya Ta sauke Kallon nurse tayi dake shirin Tafiya don a shirya d'iyar tayi cikin k'arfin ta ce " mik'omun naga kyautar da Allah yayi mun"

mik'a mata y'ar akayi Inda ta tsaya tana kallonta hawayen tausayin y'ar na zubo mata shafa kanta Tayi Tare da kissing din goshinta ta ce "Allah yayi maki Albarka Zarah ya sa mai taimakon Addini ce Ina sonki Sosai y'ata saidai Allah bai nufa Ba zamu rayu tare Allah ya shirya munke yayi miki albarka Albarkata taci gaba da bibiyarki har k'arshen rayuwarki "

tari ne yaci karfinta Mik'awa Malam y'ar tayi tuni harta fara fita daga hayyacinta Tare da cewa " ga Amanar y'ata na a hannunka Malam ka kula mun da ita ka bata tarbiya ka zame mata uwa da uba ka bata duk kulawar da zan bata ka bata tarbiya harka Aurar da ita Malam ga Amanar yata nan "


a lokacin ne maman asmy ta shigo ita ma cikin kid'imewa ta nufi gadon tana hawaye ta ce "me kike cewa haka Zarah ai cuta ba mutuwa bace haka haihuwar take kowa haka yakeji"


Murmushin yake tayi tare da girgiza kai ta ce "bakisan irin abunda nakejiba shiyasa wannan ba zafin nakuda bane sannan ta kamo hannunta tana hawaye ta ce "Ga Amanar y'ata nan A hannunku ku rik'emun ita amana sannan ku bata tarbiya nasan zaku iya ".


" Malam ne da har zuciyarshi ta karye Ya fara hawaye ya ce "Bazaki mutu ba Zarah ta Insha Allah muna nan tare Harsaikinga auran Zarah da kanki zaki Riki y'arki" .


Kallon y'ar kawai take tana tari cikin k'arfin hali ta Ciro wata zoben gold dake hannunta Tare da awarwaron zinaren da dukansu tare aka tsinceta da su ta mik'awa Malam ta ce .


"idan y'ata ta girma har lokacin Aurenta ku bata wannan shine Babban abunda zai taimaka mata wajen gano Dangina lokacin da zan maku Bayani ya K'ure sannan ku sanya mata suna na Fatima Zarah sosai tarinta ya k'ara tsananta kafin kuma daga karshe suji ta fara Salati ta na Salati har ta cika.

Allahsrk mutuwa kenan mutuwar zarah ba Malam kadaiba hatta mutanen dake unguwar ta Girgiza su Malam ko Kullum kamar ba namiji ba haka zai zauna yayi ta kukan mutuwar zarah danma idan ya kalli y'arta sai yaji wani sanyi a ranshi tunda bata mutu ba har saida ta bar masa Jininta kuma photocopy d'inta Dan sak Zarah mahaifiyarta ce har dimple dinta sai kyau ma da tafi mahaifiyarta.


Kasancewar maman asmy itama ranar ta haihu saboda tashin hankalin mutuwar aminiyarta itama nakudar tazo mata Tasha kukan wannan Babban Rashin da sukayi ita ta Shayar da Zarah tare da y'arta da taci suna Asma'u ita kuma Zarah daman tun ranar da aka haifeta kamar yanda mahaifiyarta ta fad'a haka Baba ya sanya mata sunan mahaifiyarta Zarah ".


kulawa ta musamman maman asmy ta dinga bawa Zarah tare da Asma'u ta had'u ta dinga renonsu Malam ko yanzu baida wata jinjinar sana a saboda tundaga mutuwar zarah komai ya tsaya masa baya iya Zuwa ko ina koda akayi shekara biyu da mutuwan da zai koma harkar nomansa Ya samu Mai gonar har ya bawa wani haya nan ya dawo gida yaci gaba da tawakkali da Allah harya samu Aikin bakanikanci a wani garrage gyaran mashina da motoci Inda ya fara aikin A lokacin ne kuma danginshi suka fara korafin akan baiyi Aure ba yaci yayi Aure yanzu.


Inda ya hadu da Wata zawara rabi'atu da yaranta biyu a lokacin kamar mutuniyar kirki haka ya aureta tare da yaranta duk yanda zaiyi saiya ciyar dasu Inda Ya maido da Zarah gidan Wanda a lokacin ta nuna Duk d'aya ne a gaban idonshi zata nuna tafi kowa son Zarah Inda Bayan idonshi irin azabar da take gana mata kare baici Malam bai tab'a ganewa ba saboda Zarah ta tashi da wani irin hakuri kome za a mata bata tab'a fada masa ba.

ta haifi yaranta Biyu da Malam Safiya sai kuma khairat Azaba sosai take ganawa Zarah kasancewar ta sameta yarinya mai hakuri Wanda Malam baisan da hakan ba saidaga baya ya fahimta A unguwar ba Wanda baisan irin wahalar da rabi keba Zarah ba.


Malam ya tsayewa Zarah Karatun boko da na arabi Zarah yarinya ce mai baiwar kokari Dan kokarinta saidai a kirashi na baiwa saboda yanzu za a ayi yanzu za a kwashe duk karatun da tayi tare sukayi da Asmy Dan sun zama kamar y'an biyu kuma maman asmy ta rik'e Amanar da aminiyarta ta bata danma Mama Rabi dake azabtar da ita Yaran Mama Rabi duk sun lalace saboda Rashin tarbiya da bata basu ba khairat ce cikinsu kawai ta fita zakka zarah tunda ta taso ta fara perioud take shan wahala dan duk wata saidai akaita ayi mata allura irin fita daga hayyacinta da take har suma take sannan tana da larurar tsananin sha'awa mai karfi wanda wani lokacin abun ya taso mata saidai a bata maganin bacci wanda shawarar dr din da aka taba kaita wajenshi ne dan ya bata magani ya basu hakan .
wannan kenan.

*FCT ABUJA*


Manyan motoci ne na gani na fad'a Sunkai Sha biyar jere suke suna tafiya cikin gudu saboda bikin da za a gudanar na bud'e shahararren sabon shopping mall d'in da ya amsa sunansa.


Wajen shake yake da manyan mutane tun daga kan y'an kasuwa "shahararrun masu kudi da sauransu *MD SHOPPING MALL*naga an rubuta a saman ginin yanayin yanda akayi rubutunma kad'ai ya isa ya sanyaka Yin k'auyanci.


Waje ne da ya tsaru da kyau saika rantse ba k'asa Nigeria kake ba saboda yanda zakayi mamakin irin dukiyar da aka zuba a ginin ma b'ata lokaci ne.

Nan aka fara gudanar da bikin bud'e Wajen Bayan jawabai daga bakin manya da shahararrun y'an kasuwa Inda akazo ga jawabi wajen mai gayya mai aiki wato mamallakin wannan shahararren wajen watau Mustapha Dikko *MD* .


"hamshak'e ya ke a wajen banyi Tunanin yana jin hausa ba saboda kwata_kwata baiyi kama da hausawa ba Fari ne sosai kamar bature ko kuma ba indiye Sanye yake cikin bak'ar coated wacce ta amshesa ta kara fito masa da kyau da kuma hasken fatar sa kallo d'aya zakayi masa kaga asalin ba india


sanye ya ke cikin siririn farin glass sumar kan nan nasa lufluf gwanin sha'awa da burgewa ga kuma sajenshi Dake zagaye da kyakyawar fuskarsa daya kara kayatar da tsananin kyaun da Allah yayi mishi.


a gaskiya ni kaina saida na rude da ganin zubi da kyau irin na wannnan bawan Allah zan iya cewa tsawon rayuwa ta ko a film bantaba ga namiji da kyau irin haka ba duk inda karshe da baiwar kyau take tofa Yakai a kirasa da komai Dan guy din ya had'u karshen had'uwa (lol).

Daga zaunen da yake batare da ya mik'e ba ya amshi abun maganar tare da Fara jawabi cikin zazzak'ar muryarsa Yanayin yanda yake.maganar saika d'auka wani sautin wak'a ne mai ratsa zuciya ke tashi.


baiyi wata magana mai tsayi ba saboda shi daman Chan ba mutum bane mai fiya son magana da yawa ba Hasalima yanzu a k'agare yake A gama taron nan ya tafi dukda dalilinshi kowa yazo wajen amma ya k'agu saboda hayaniyar da ake a wajen dan shi ba mutum bane mai son hayaniya .


camera ce A kansa ta gidajen television da dama kowa so yake ya d'auka jawabin harya gama ana haskasa da camerori.


"Tsaki yaja yana kauda kai Dan ba abunda ya tsana irin taron jama a "

jabir ne dake kusa dashi ya rad'a masa a kunne"Sorry bloody Dan Allah yau karkayi mana halin naga ka fara tsaki ka.daure har a gama bikin nan kasandai duk Wanda yazo wajen nan kai yazo tayawa farinciki".

Lumshe ido MD yayi tare da bud'esu a hankali batare da yace uffan ba kamarma ba dashi jabir yake magana ba hakan bai damesaba saboda idan da sabo ya saba da halin aminin nasa Shidai burinshi Indai bazai kwafsa musu ba ya jira har agama falilllahil hamdu".


Ba aja wani lokaci ba aka gama komai Inda MD ya Mike Security na take masa baya Sunkai su 30 yanda kasan wani president .

security gabansa haka bayansa ma sai kakkaresa ake nan fa y'an jaridu suka shiga d'aukar rahoto har ya isa motarsa Inda suma suka shiga motocinsu A motar ma tunda ya shiga Danna waya ya ke

"Jabir ne dake gaban motar da juyo tare da tambayarsa ya ce " Ranka ya dad'e ina muka nufa"Kamar baya da shirin magana Ya ce "Airport" Ya fad'a yana cigaba da latsa waya kamar bashi yayi maganar ba "Jin haka ya sanya jabir ganowa Kaduna Zasuje kenan ".

Ko a Airport d'inma saida nayi mamakin irin yanda mutane ke kallonsa y'an mata har Tuntube suke suna cewa.

" wlh shine MD ne "wata har tsuma take tare da Rungume y'ar uwarta ta ce " Alhmdllh Gaskiya yau rakiyar nan munzo a sa'a ganin mutumin Dan ban tab'a tunanin tab'a gani ba a rayuwa yau nagansa karkiga yanda nake da muradin ganin guy d'innan cikin Sauri ta d'auko wayarta tare da shiga snap daga nesa ta dinga daukoshi Dan tasan ko giyar wake ta sha bata isa ta tunkari wajenba yanda security d'inshi ke zagaye dashi.


Ba b'ata lokaci jirginsu ya d'aga Kaduna koda ya isa Kaduna Chan dinma haka ne Tsaki ya dinga ja shi d'aya saboda a Rayuwarshi ba abunda ya tsana sama da Kallo da kuma yanda y'an mata ke rudewa idan suka gansa Har suka isa Unguwarsu da ke G R A ya na Jan tsaki .

Horn biyu sukayi mai gadi ya Wangale musu Get d'in Aljannar duniya kenan gidane katoton gida mai girman gaske fad'ar kuma kyau da tsaruwar gidan ma b'ata baki ne Dan saimu cinye page Ukku zaku iya kwatanta gidan da gidan indimi.(lol)

Motoci biyar Duka suka danno gidan kai tsaye Ta tsakiyar ita ce tashi A hankali yake fitowa daga motar bayan ya fara ziro kafufuwanshi dake shanye da hadadden cover shoes koda ganin takalmin kasan ba na kananan mutane bane a haka harya karasa fitowa daga motar.


kamar Wanda baison taka k'asa ya fara tafiya securities d'insa ne suka biyo shi da hannu ya musu nuni da su dakata Kai tsaye hanyar Part d'in mahaifiyarsa Ya nufa Kafin ya k'arasa shiga Yaga fitowar Chuchu da gudu Tare da rugowa ta fad'a Jikinshi Sosai nayi mamakin yanda Ya sakar mata murmushi Wanda Ya Kara fito masa da baiwar kyawun da Allah yayi mishi ashe daman idan yayi fara'a yafi kyau yake tamke fuska.

"Shima Rungumeta yayi Tare da shafa bayanta ya ce " I'm very glad to see you my Beloved sister "Cikin farinciki da muryarta Mai kama da ta masu iyayi ta ce " me too yaya nafi kowa farincikin ganinka tunda akace ka taho nake ta zumudi" Ta fad'a ta na kama hannunsa Tare da janshi Dan su shiga ciki ta ce "Yaya muje kaga irin abubuwan da na shirya maka Dafota yayi kamar dafayya tun a hanya ta shiga fara zuba masa surutu Wanda har ya fara isarsa har suka isa tafkeken palourn ta na zuba masa surutu.......โœ๐Ÿฟ
*07026166536*


*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ๐Ÿ‘ฏโ€โ™€๏ธ๐Ÿ‘Ž๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*


1, *MU GANI A ฦ˜ASA...*๐Ÿ”ฅ
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ฦ˜WAI..*๐Ÿฅš
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*๐Ÿ’ฅ
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*๐ŸŒŽ
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huษ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ษ—aya N300

*DOMIN TURA KUฦŠIN KAI TSAYE*๐Ÿ‘‡

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya๐Ÿ‘‡

0810 433 5144

Masu tura katin MTN๐Ÿ‘‡

0814 179 9224

ฦณan ฦ˜asar Niger zasu tura nasu anan.๐Ÿ‘‡

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huษ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ษ—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ๐Ÿ”ฅ๐Ÿฅš๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŽ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ



~share please ~

*_Miss Hajo ce_*๐Ÿค™๐Ÿฟ
[8/26, 16:46] โค๏ธโค๏ธโค๏ธ: ๐Ÿ’‘ *AUREN WATA TARA* ๐Ÿ‘จโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

MALLAKAR

*Hajara L Sadeq*


๐Ÿ…ฟ๏ธ.........*11 & 12*


A palour ya tarar da mahaifiyarsa abar kaunarsa matashiyar mata da bazata wuce 55 years ba Amma Hutu da gayu ya boye shekarun.

sanye take cikin shigarta ta alfarma ta manyan mutane Idanunta sanye cikin farin glass Saida na K'are mata kallo naga sak kamarsu d'aya da MD har farin wacce daga ka ganta kaga Ba India Cikin farinciki ta tari Dan nata hug din juna sukayi suna farincikin ganin juna ta ce "Sannu da zuwa Baba na kazo lafiya"


"Alhmdllh Ammy na sameku lafiya" Alhmdllh ta fad'a ta na kama.hannunshi kamar wani yaro kan sopar da take suka zauna Kallonshi ta yi tare da kama hab'arsa ta na duban fuskansa ta ce "Baba na ya naga ka d'an rame".


kanshi ya d'ora bisa kan kafad'arta ya ce "Ammy idonki bai gane maki daidai ba ba wata rama fa da nayi"

Chuchu ce ta shigo da tilin kuloli a hannunta mai aikinsu na biye da ita da sauran Ajewa tayi gabanshi ta ce .

"Yaya na kazo kaga irin delisiou din da na shirya maka" Ammy ce ta ce "iyye to Auta bakin bari ya huta ba sai yazo ya ci"

Diddira kafa ta fara cikin muryar shagwaba da sangarta ta ce "umm umm ni dai wlh yanzu nakeson yaci basaiya huta ba "

Kamo hannunta yayi tare da zaunar da ita gefenshi ya ce "Caml down chuchun yaya bud'e naga abubuwan da aka shiryamun"

Cikin murna ta mik'e tare da bude masa d'aya Bayan daya Abinciccika da snack Sunkai kala goma shi abunma saida ya so bashi Dariya "Ya ce.

" Auta yanzu duk ina zankai wannan ai saikuma cikin Yayan naki ya fashe"Cikin shagwaba ta ce "Nidai yaya saikaci Duka "

Yasan halin y'ar rigimar Autar tasu hakan ya sanyashi d'aukar spoon Duka abincin yabi ya d'andana lumshe ido yayi Dan taji dad'i tare da jinjina mata good da hannu ya ce .

"Muje ki amshi tukuicinki Auta abinci yayi dadi" Tsalle ta daka tare da cewa "yeyeye yaya na muje Daman nasan zakaji dad'in abincin " .

Ammy Ce ta ce "Daman nasan ba banza ba wannan rid'in da kike "

Juyowa tayi tare da yiwa Ammy gwalo ta Ce "Aidai yaya ne " Dariya Ammy tayi tare da girgiza kai Had'in kan na yaran nata sosai yake yi mata dad'i A daki MD ya yiwa Chuchu kyautar had'ad'd'iyar Zoben gold mai matuk'ar tsada tare da turarruka masu k'amshi da tsada daman ita ya sayowa Sannan ya bata Rafar y'an dubu dubu zo kuga murna wajen Chuchu sai sanyawa Yayan nata albarka ta ke ta na "tsallan murna "

dak'yal ta samu ta bar Yayan nata ya huta Bayan Ya fito daga wanka Wanda saida ya d'auki dogon lokaci jikin mirror yaje Wanda shake yake da mayuyyuka da turarruka kamar mace

"nan ya shiga shafa mayuyyuka yanda yake shafa man kamar mace "

K'ank'anin kaya ya sanya Tare da hayewa Gado Dan yana buk'atar hutawa Tunda ya dawo daga America bai huta ba lumshe idonshi Yayi yanayin sanyin AC da K'amshin turarenshi ya kauraye d'akin ya bada wata irin sayayyar ni'ima.


Wayarshi ce tayi ringing Kallon screen d'in wayar yayi "Amera " Naga an rubuta "Saida ta karashe ringing d'inta batare da ya d'aga ba a jin kira na biyu ya sanyashi d'auka tare da Kara wayar a kunnansa.

" Cikin muryarta mai kama da mai shirin yi kuka ta ce "Honey Shine tunda ka taho baka kirani ba ina nan kewarki duk ta isheni please honey karkayi jimawar da kace zakayi"


"cikin muryarshi mai dad'in sauraro ya fara magana kamar haka " Da kina buk'ata ta a kusa dake da bazaki bari na taho ni kadaiba Ba kince ke bazakizo Nigeria ba To saikiyi ta zama a American tunda garinku ne"


"Cikin kwantar da murya ta ce " Uhm to kayi hakuri honey karkayi fushi da ni gobe gani nan tahowa"uhm "kawai ya ce " Dan haushinta yakeji na k'in biyosa da tayi Bayan tasan yanayinshi.


Bai jima yana bacci ba ya tashi mikewa yayi tare da sake wani wankan ya shirya cikin wasu kayan tare da fitowa palourn .

"Kanwarsa Zey ya tarar tare da yaranta " da gudu Suka Rugo ganinshi tare da Rungumeshi "mima " ta ce "oyoyoy uncle " Shima Daddy Ya ce "Oyoyo uncle Nayi murnar ganinka " Cikin farincikin ganin yaran sister tashi ya d'agasu sama tare da yi musu murmushi ya ce .

"welcome yaran uncle " Dak'yal suka barsa ya karaso palourn yanda suka bibiyeshi Zey ce ta kalli Yayan nata ta ce "Ina yini Yaya anzo lafiya"

Cikin kulawa da nuna soyayya ta y'an uwantaka ya ce "Alhamdulilla maman mima na sameku lfy" Lafiya qalau yaya Ya Aunty Amera ta na lfy ko ba tare kuke ba "Ta na lfy gobe ita zatashigo "

Ammy Ce ta ce "Ai nazata tare kuke ta tsaya Abuja" Nan suka shiga hirar Shopping mall dinshi da aka bude yau a abuja yayinda yaran Zey suka dabaibayeshi ya biyesu sai wasa yake musu saboda a duniya babu abunda MD yakeso sama da yara yana matuk'ar son Yara a rayuwarshi .

Ammy ko kullum ganin yanda yake da Yaran Zey saiya bata tausayi tasan yanda d'an nata yakeson yara Saidai Allah bai nufeshi da samunsu ba shekara ta Tara kenan da aurensa amma har yanzu ko b'atan wata matarsa bata tab'a yiba gashi yak'i kwata k'ara Aure ko angane cikinsu wake da matsalar.


"baiwani jima a palour ba ya mike saboda kiran sallar da ake masallacin gidan ya wuce dan ya gabatar da sallarsa bayan fitarsa zey ta kalli Ammy ta ce " yanzu ammy haka zaki zuba ido kibar yaya wlh tausayi yake bani me zai hana ki tirsasa masa ya kara aure dan a san inda matsalar take nifa jikina na bani yayana baida wata matsala".


numfashi ammy taja tare da cewa "to ya kike so nayi zey Wani irin Yi ne banyi da Baba na akan ya kara aure ba yaki kina ganin dalilin haka matarsa Har gaba takemun bata son zuwa gida na yakike nayi Nabarsu kawai "

Tana cika zey ta ce "Wlh ammy laifinkine tun farko da kika barsa ya auri yarinyar nan jifa duk ta shanyesa " mubar wannan zancen zey "Ammy ta fada.

Da daddare ko da ya kwanta wani felling na bijiro masa runtse idonsa kawai yake tare da matse cinyoyinsa Sosai mararsa ke murda masa dukda sanyin ac amma bai hanasa zufa ba dakyal ya lalubo warasa tare da dannawa chuchu kira ta na dauka ya ce


" ki hadomun ruwan lipton ki sanya lemon tsami kamar sha biyar a ciki ki kawoman yanxu "to ta amsa a lokacin tana jikin ammy kuma taji abunda akace "

mikewa tayi tare da nufar kitchen dan tayi abunda ya sanyata Ammy ko girgiza kai kawai tayi dan tasan har yanzu a rayuwar d'an nata akwai gyara Tasan ba wani dad'in matarsa yakejiba ita bataga wani banbanci ba da aurensa da lokacin da baya dashi dan duk sanda yazo cikin shan tea da lemon tsami yake.


Bayan chuchu ta kai masa ta fita Yunkurawa yayi tare da fara kurbar tea din haka har ya shanye sai chan dare ya samu relief har bacci ya daukesa.


Washegari Amera ta shigo k'asar ta na isowa ta kirasa ta ce "ta na gidansu dake nan Kaduna A lokacin har anyi isha 'i ina zuwa ya bata amsa tare da Katse kiran.

Daman duk a matse yake cikin Sauri ya Mike tare yiwa Ammy bankwana ya ce " zan wuce gida ammiy saida safe "Allah tashemu lafiya ta fad'a tare shigewa ciki ".

Kai tsaye MD katafaren gidansa na gani na fada dake nan Kaduna cikin g r a din ya nufa Bayan driver ya daukesa a palour ya tarar da ita cikin shigar K'ananan kaya Riga da jiens matsatsu Da gudu ta rugo tare da rungumesa ta ce .


" A Gaskiya Daga jiya zuwa yau ba k'aramar kewarka ba nayi miji na "Shafa bayanta yayi Cikin kasalalliyar muryarsa ya ce "

nima nayi kewarki matata "a palour suka fara yada zango Inda Amera sai narke masa take saida na K'are mata kallo naga doguwa Ce fara Sosai ta na da kyawun fuska ba laifi amma haskene ya k'ara fito da ita .


siririyace kamar ka hure ta fad'i a tsaye take bata da wani shape daga fuska zata gane ta na da shekaru Dan zatakai 28 haka Dan k'aramun jiki ne gareta.

Tun a palour ya fara nanikarta kafin Su wuce Bedroom duk yanda Amera taso nuna masa dauriyarta yau ma kasawa tayi ganin awa biyu ana Abu d'aya batare da yana shirin tsagaitawa ba Dan yau ba k'aramun dauriya tayi ba tun abun nayi mata dadi har yazo baya mata ihu ta fasa mata tare da Fara masa jaraba ta ce.

" ka tadani MD kai baka iya cin kwan makauniya ba kasheni kakeso kayi ka rabu dani Na shiga ukku ni Sadiya"ta fad'a tana kuka "

Jin hakan ya sanya MD tashi daga kanta Sosai wannan iskancin da take masa yake jin Haushi har tsoron tab'ata yake gashi saiyayi mata zuciya ta dawo tana mashi magiya da bashi hakuri

Ba karamun bata masa rai tayi ba tsaki yaja tare da mik'ewa a daddafe yaje yayi wanka tare da fitowa nan ya sameta ta na maida numfashi tsaki yaja tare da barin d'akin ya koma d'ayan bedroom d'in Ya jima kafin bacci ya daukeshi shi kanshi ji yake da da yanda zaiyi ya sauya irin yanayin halittarshi da ya sauya magani da kudi ko ba irin Wanda bai kashe ba akan matsalar Amma bai samuba harya kwanta ya na Jan tsakin haushin Amera.


washe gari da azumi ya tashi kasancewar Alhamis kuma daman Chan azumin Alhamis da Litinin baya wucesa ".

yana zaune ta fito Cikin shigar Kanunun kaya tare da hand bag a hannunta ta yafa gyale wani banzan kallo ya watsa mata tare da cewa .

"Gidanwa zaki da wannan arniyar shigar" Cikin marairaicewa ta ce "Honey gida zani kasan tunda nazo banje ba " Tsaki yaja tare da cewa "wuce ki koma bazaki ba" .


zata sake magana ya daka mata Tsawa tare da cewa "bazaki wuce ba nace ko saina tattakaki" .


Kuka Amera ta sanya kamar wata yarinya tare da durkushewa ta ce .

"MD wai meye haka ka daina sona ne ko me ka fad'amun Abu Kad'an zan maka ka hauni da fad'a Bayan da ba haka kakemun ba kodai ka fara gajiya dani ne Dan bana haihuwa".


ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka"Md sai yaji ta basa Tausayi Cikin k'asa

2 Comments On AUREN WATA TARA
avatar
mubarak-nasir

11 months ago

Reply

Woow gaskiya yayi

avatar
mubarak-nasir

11 months ago

Reply

Abun yayi

Please Login or Register in order to submit comment