Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Chan mahaifinshi ya ganta ya auro ta shiyasa da kin gansa zakiga asalin ba indiye kannansa biyu mata sosai yake sonsu da ji dasu na manta sunansu , Compononyn da gayen nan ya mallaka nan Nigeria da ma k'asashen k'etare da kadarori gidajen mai kudade na ban mamaki ke kanki saikinyi mamaki gashi matashi Dan bazai wuce 38 years ba Amma wlh Inajin gayen nan shi yazo na biyu a kudi a negeria su kansu manyan durkusa masa suke Dan wasu Mahaukatan kud'ine ke garesa duk wajen Da kikaje kikaga an rubuta MD to mallakinsa ne wajen Shopping mall ko da park_park babu jahar da baya dasu a wannan k'asar tamu Ga shi ya had'u Iya had'uwa y'an mata da dama karkiga yanda suke rudewa a kansa Kwanaki a labarai da nagani Wata tana shirin kashe kanta saboda iyayenta zasu aura mata wani Dan uwanta shegiyar yarinyar nan wai MD takeson mutumin da baisan da zaman ta ba Mutum ne mai matuk'ar ji da kansa d'an gayu ne na Bugawa a jarida miskili ne na karshe Dan Ance a waje saiya yini baiyiwa mutane magana ba Amma ance yana magana da family dinsa sosai nidai tunda nake bantaba ga dariyar MD ba a hotunan da nake gani nasa Dan bantaba ganinsa ido da ido ba yana da manyan company a Abuja Amma ance mafi yawan harkokinsa a America ya ke yinsu yanzu haka a Chan yake da zama Saidai Naji ance Allah yayiwa mahaifinshi rasuwa shekaruun baya sosai Wanda ake zargin kashesa akayi to kunji takaitaccen Tarihin MD matashi da kudi Wannan shine kirarinsa".


Tunda ya fara maganar Zarah take Jan tsaki Inda yana gamawa ta kuma Jan wani tsakin tare da cewa "To waya tambayeka Tarihinsa ina ruwanmu dashi ka zauna sai zuba kake mana akan wani chan banza "


wara idanu Yusuf yayi ya ce "MD dinne banza Zarah"

Tsaki taja Dan sosai takejin zafin tsayuwar nan tasu ta ce.

"To me zankirashi dashi Bayan ya tsaida mu a titi yanzu haka Ina tunanin Banki sun tashi"

ta fad'a ta na Jan tsaki tare da kauda kai tanajin haushin wannan banzan MD din da aka fad'a Wanda ya tsaida su kusan Awa guda a titi"

"Chab ba ruwana wlh security dinsa suka jiki Saidai kiji ina cewa A mota muka hadu "

"Asmy ce ta kwashe da Dariya tare da cewa " lallai Abbanmu kace duk uba da d'iyar da ake ajesa za ayi"

"Chab ina ake ta uba idan ta fito lafiya sai acigaba da ubantakan"

"Dariya Asmy tayi ta ce " Kaidai anyi matsoraci wlh nima saida ka fad'a na tuna da shopping mall d'insa da na tab'a gani a kano sannan a funtua ma ai akwai gidajen mansa har biyu Saida ka fad'a nagesu"

"Chab ai yana da Mahaukatan gidajen mai kalli Chan ya fad'a yana nuna mata wani had'adden gidan mai sabo mai d'aukar kai Ashirin Ya ce " Karanta Chan ma me aka rubuta wancen ma nasa ne"dagawa Asmy tayi ta Kalla ta ce "Aikuwa wlh amma dai nima nayi mamakin Mahaukatan kudin matashin nan ya na da mata amma?

" Wara hannu Yusuf yayi ya ce "wannanne dai bansaniba Anya ya rasa mata ma kuwa Amma dai ko wacece Matar zatasha miskilanci"

Dariya asmy tayi ta ce "Gaskiya kam " sai sannan motocin MD suka gama wucewa Mai napep d'insu ya tada suka isa Zarah ta cika tayi Fam Asmy na mata Dariya ta ce.

"Ran manya ya b'aci ayi hakuri ya muka iya k'asar nan Indai kai talaka ne Ai saida kayi hakuri"

"koda suka isa Banki harsun tashi sosai Zarah ta k'ara k'uluwa tana tsinewa wannan shegen MD din da ya tsaidasu ji take kamar ta kurma ihu Dan Haushi

Wata napep din suka Tara tare da komawa Zarah sai cika take batsewa Dan taji haushin b'ata lokaci ta da sukayi a banza a hofi.


Dan ita tana daraja lokaci da ace tsawon lokacin da suka 'bata a tsaye da ko karatu ta tsaya tayi bata amfana ba.

saida suka tsaya kasuwa sukayi sayayyar kayan miya da Abubuwan da zasu buk'ata Dan karsuyi fitowar banza sune basu koma makaranta ba sai wajen magriba .


Koda isarsu makaranta sosai sukayi mamakin chinchirindon student wasu ana wawwatsewa ita dai Zarah bata tsaya ma kallonsu ba .

Cikin jin Haushi ta isa hostel d'insu Asmy na mata fad'an akan ita da ta sani da hakuri yanzu kuma itace take mita akan Abunda baikai ya kawoba Ta ce " gobe ba saimuje mu bud'e ba Tunda safe ba"


"Zarah bata kula taba saboda ita kanta batasan ya akayi ba takejin haushin b'ata lokacin da sukayi suna isa hostel sunyi mamaki ganin bak'in kaya a Bangaren da ba kowa Uban jibgin kaya akwatuna kamar Lefe banda uban provison Kallon juna sukayi da mamaki Asmy ta ce " to fa ko bakuwa muka samu a d'akin namu '".

Basu k'arasa magana ba sukaji shigowarta dukansu Juyawa sukayi tare da Kallon matashiyar budurwar da baza wuce sa'anninsuba sanye da Doguwar Riga mai shegen tsada da kyau sai fara'a take sosai daga ganinta kasan tana da tsananin fara'a Murmushi ta sakar musu tare da karasa shigowa d'akin saurin fusgewa sukayi da Kallon da suke mata suka zauna bakin gadon su suna huta gajiyar da suka kwaso cikin girmamawa ta ce sannunku ko kune Wanda muke d'aki d'aya"......โœ๐Ÿฟ


*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ๐Ÿ‘ฏโ€โ™€๏ธ๐Ÿ‘Ž๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*


1, *MU GANI A ฦ˜ASA...*๐Ÿ”ฅ
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ฦ˜WAI..*๐Ÿฅš
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*๐Ÿ’ฅ
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*๐ŸŒŽ
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huษ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ษ—aya N300

*DOMIN TURA KUฦŠIN KAI TSAYE*๐Ÿ‘‡

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya๐Ÿ‘‡

0810 433 5144

Masu tura katin MTN๐Ÿ‘‡

0814 179 9224

ฦณan ฦ˜asar Niger zasu tura nasu anan.๐Ÿ‘‡

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huษ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ษ—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ๐Ÿ”ฅ๐Ÿฅš๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŽ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ



_*Miss Hajo ce*_๐Ÿค™๐Ÿฟ
[8/29, 14:32] โค๏ธโค๏ธโค๏ธ: ๐Ÿ‘จโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ *AUREN WATA TARA* ๐Ÿ‘จโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

```MALLAKAR```

*Hajara L Sadeq*


๐Ÿ…ฟ๏ธ............*17 & 18*


Murmushin suka mayar mata Asmy ta ce "Eh mune Sannu da zuwa" Yawwa Chuchu ta fad'a tare da cewa.

"suna na Maryam Dikko ana cemun Chuchu ko kuma ku kirani da chuchun yaya dan nafison a kirani da haka kufa".


"Ni suna nan Asma'u ana Cemun Asmy ita kuma wannan " Zarah y'ar uwata ce"Asmy ta fad'a ta na nuna Zarah

"Wow nice name Sunan Ammy na ne Fatima Zarah" Saidai na kirata da momcy "Chuchu ta fad'a cikin iyayinta da ya zame mata jiki.

" Murmushin da batayi niya ba Zarah ta sakar mata tare da cire hijab Dan taje tayi sallah "Asmy ta ce " Wow kice ke y'ar gata ce Gaki ga mom d'inki"

"Ah sosai ma a gatana nazo school d'innan Saidai naga momcyn nawa kamar batason magana dani?

"An d'an bata mata rai ne shiyasa " cewar Asmy Zarah ko Smile ta sakar mata tare da cewa"Ba haka bane Daughter Ykk anzo lafiya "

"Alhmdllh momcy sorry ko Naji ance an bata maki rai ko waye dai Wanda ko wacce ta bata miki ran nan bata kyauta ba gsky kiyi hakuri ko"

"Dariyar da bata shirya ba Zarah tayi Dan ta lura akwaita da surutu ta ce " shikenan na hakura daughter sunci arzikinki"

"Wayar Chuchu ce ta yi ringing Cikin Sauri ta d'aga kiran Ganin ammynta ce ya sanyata " murna ta ce.

"Hello my Ammy na " Daga bangaren Ammy ta ce "Na am Autar Ammy kinganni nan daga tafiyarki har na fara kewa"

"Dariya Chuchu tayi tare da cewa" Wayyo Ammy na tun ba Aje ko ina ba har kin fara missing Nima da banjima ba Amma kadaicinki duk ya isheni "ta fad'a ta na turo baki.


Sun tab'a Hira da Ammy cikin so da k'aunar juna Daga nan kuma ta kira Yayanta Bayan ya d'auka ta ce " yaya Ya hanya kunkoma lfy"

"Alhmdllh ya fad'a tare da cewa " ki tsaya kiyi karatun kirki karki sake na kamaki da matsala na sanya a sa miki ido sosai banda biyewa kawayen banza da samarin banza na sameki da haka cireki zanyi"

"toh yaya bazanyi ko d'aya ba daga ciki "

Shima sun tab'a Hira tukwana ta kashe.

Washe gari tare da Asmy suka wuce lectures saboda course d'insu d'aya itakuma Zarah ta tsaya tayi musu girki saboda sai 10 take da lectures.

Cikin k'ank'anin lokaci Su Asmy suka saba da Chuchu Wanda duk ita Chuchu din take shishige musu ita dai tunda taga Zarah taji ta kwanta mata a rai.

Itama Zarah din Chuchu ta kwanta mata a rai Saidai Abunda ke bata Haushi game da ita irin shigar da take kullum da k'aramun gyle bata tab'a ganinta da hijab ba sannan bata tab'a ganin ta dauki Alquran da sunan wai tayi karatu kullum cikin jin kid'a take ta lura yarinyar sangartattace ta Bugawa a jarida Saidai Inda take burge ta ta na da kamun kai sosai.


Sosai y'an mata keson abokantaka da Chuchu saboda lokacin da MD ya kawota sunsan Kanwarsa ce ta bangarenta ko bata kula kowa saboda ita daman haka take bata fiya mu amula da mutane ba sai Wanda jininsu ya zo d'aya.


Da Yamma suna zaune a Harabar hostel din suna shan daddad'an iskan dake kadawa Yayinda Alquran ke hannun Zarah cikin zazzak'ar muryarta Mai dadin sauraro ta ke rerawa ".

" Chuchu ce dake sauraronta sosai ta burgeta yanda take zuba kiri'a shiru tayi ta na sauraronta wayarta ce Tayi ringing saurin dubawa tayi ta ga yaya MD aiko cikin farinciki ta daga tare da cewa.


"Yaya na I really miss you so much yaya " Daga bangaren MD yaja numfashi tare da cewa "miss you too chuchun yaya Ya kike ya school d'in kina dai maida hankali kuma ba wata matsala ba abunda kike bukata"

"alhmdllh yaya na ba wata matsala kuma ina maida hankali sosai " good girl haka nakesonji wani karatu nake ji daga gefenki ko?

"Eh yaya momcy ce Ke yin karatu sunan Ammy gareta yaya karka ganta ta had'u da kyau Ga Ilimi Ko na baka ku gaisa" Tsaki yaja daga bangarensa tare da cewa "kin fara rainani ko ni zaki cewa zaki bawa wata mu gaisa " yana gama fad'ar haka ya kashe wayar .


Chuchu ko Dariya tayi ta ce "Allah barmun kai yaya na " Asmy ce ta ce "Na lura dai kina ji da wannan Yayan naki sosai fa"


"Kamar mai jira Chuchu ta gyara zama tare da cewa .

" kaiii ai fin sosai ma ina son yaya sosai shidin ba matsayin yaya kadai yake a wajena ba shi din uba ne ya na sona da kaunata sosai nima ina sonshi sosai matsayi biyu yake a wajena yaya kuma uba Dan tun wata na biyu a ciki mahaifina ya rasu bansansa ba yaya na kadai ya mayemun gurbinshi shidin na musamman ne a cikin mutane"


"Allahsrk Allah ya jikan Baba ya mishi Rahama Gaskiya dole kiso Yayan nan naki da yawa Allah ya k'ara had'a kanku" Cewar Asmy "

"amen Chuchu ta amsa ta na cigaba da sauraron karatun Zarah"

Dukda karatu ta ke amma Zarah na sauraronsu Taji abunda Suke fad'a saida takai daidai Inda takeson tsayawa tukwana ta ninke Alk'uran din Chuchu jira ta ke ta gama daman cewa ta yi"

"Gaskiya momcy kin hadu ta ko ina wlh bantaba Jin kiri'ar karatu mai dad'in wannan ba kina da murya mai zaki Dan Allah Ko zaki dinga yimun k'arin karatu Dan wlh hizif d'ina ko Talatin bankai ba "

"Da murmushi a fuskar Zarah ta ce " me zai hana daughter insha Allahu indai kina so daga yanzu ma saimu fara"

Cikin farinciki Chuchu ta ce "Wow ngd momcy a shirye nake yanzu ma mu fara"

Daga yasin suka fara Dan karatun ya tafi yanda suke so.

Washegari a tare sukaje suka bud'e account Inda ita Chuchu rakiya ce kawai tayi musu.

Tun daga ranar Zarah ta zama Malamar Chuchu kullum rabin shafi take Kara mata kuma sosai take fahimta idan ta bata hadda sai ta d'ora mata wani shakuwa Ce da abokantaka ta k'ara shiga tsakaninsu ta musamman hatta lecture din da bata ganeba wajen Zarah take zaunawa tayi mata bayani"


Sannan yanzu Chuchu ta nutsu ta koyi wasu daga dabi'un Zarah yanzu itama hijab take sanyawa dukda ba Koda yaushe ba da wasu kide kide duk ta rage ji



Zaune yake a garden d'in gidansa ya na shakar daddad'an iskan dake kadawa cike da ni'ima.

lilo din da yake kai ya na jujjuyasa har wani lumshe ido yake zazzak'ar muryarta Take dawo masa a kwalwa hatta karatun da yaji tanayi yaji ya na masa gizau ya rasa ya akayi ba tunda yaji muryar mai karatun nan take dawo masa ba a kwalwa Tsaki ya ja a ransa tare da saurin barin tunanin da yake.


Ya na nan zaune Jabir yazo yayi mamakin yau yanda fuskar abokin nasa a warware "Zaunawa yayi Inda suka shiga d'an hirar Kasuwancinsu"


"MD ne ya ce " Ina son a shiryamun tafiya America gobe "okay Kai d'aya za ashirya maka ko tare da Amera "

Sai sannan MD ya tuna da Amira tsaki yaja saboda haushinta da yakeji tunda ta tafi gidansu bata leko ba ya ce "

"Ni d'aya zaka shiryamun ta na gidansu"

da mamaki jaber ya ce.

"Wai kana nufin tun sanda ta tafi bata dawo ba kusan two weeks lallai Abokina ka na hakuri wlh wai meyasa ba zaka bi shawarar Ammy ba akan ka k'ara Aure Kaga dai na farko Auren nan naka da Amera shekara Tara kenan bata tab'a d'ora girki ba da niyyar wai ta girkawa mijinta abinci ba Sannan ita ba haihuwa ta tab'ayi ba bare ka ce zaka zauna da ita Dan d'iyanta sanin kanka ne kunje Asibiti yafi sau nawa ance matsalar daga gareta ne dukda kana boye mata why zaka zauna mace d'aya ta dinga baka wahala tunda ka Aure ta Banbancinka da gwouro Kad'an ne kana da kudi da komai da zaka mori rayuwarka da su MD kayi tunani"

"Nauyayyar Ajiyar zuciya MD ya sauke ya ce.

" bazaka gane bane Jabir bazan tab'a yiwa Amera kishiya ba Dan bata haihuwa da misalin ace nine bana haihuwar itama haka zata zauna dani sannan har yanzu banga wace macen da zance wai ina da ra ayin aura ba"

Numfasawa yayi saboda doguwar magana da bai saba ba sannan ya ce .

"Amera na da kishi sosai bazata iya zama da kishiya ba sannan ina son matata bazanso abunda zai b'ata mata rai ba hasalima ni a tsarin rayuwata ban tsara auran macen da ta wuce d'aya ba mace d'aya nake da ra'ayin zama da ita kuma Babu saki a tsari na karma ka k'ara zomun da irin wannan maganar"


"Shidai Jabir mamaki yaki barin fuskarsa zai d'aga baki yayi magana MD ya d'aga masa hannu dage kafada yayi tare da tashi Dan takaicin abokin nashi ya zauna mace d'aya na wahalsheshi.

Washe gari MD ya bar k'asar Bayan Yaje yayiwa Ammynsa bankwana ya wuce america.

Amera ko jin shiru mijin nata bai kirataba saida ta gama shiriritarta da yawonta iyayenta ko y'an komai kayi daidai ne cikinsu ba Wanda zaice shirya ki koma gidan mijinki.


kiranshi tayi a waya taji layinshi na k'asar baya shiga Ta na kiran na America taga ya shiga amma baya d'auka sai sannan ta gane ya tafi america kenan .

Aiko cikin rana tsaka ta d'auko akwatin kayanta cikin K'ananan kayan da ke jikinta ta d'ora mayafi tare da fitowa cikin Sauri iyayen da ke palour duk kallonta sukayi dadynta ya ce "

" ina zuwa da tsakar ranar nan my merah"Tana Sauri ta bar palourn ya ce "Dad America na tafi gidan mijina bye saimun dawo " .

ta na gama fad'ar haka tabar palour ta na fita ta kwalawa driver kira cikin Masifa da bala i ta rufeshi da fada akan zai bata mata lokaci shidai hakuri ya dinga bata Dan tun tana gidan ba mutunci garetaba ka tab'ata yanzu kayi ta aikinka Kai tsaye Airport ya wuce da ita.

Koda ta isa America sosai Tasha fama kafin ta shawo kan mijin nata Dan ya nuna mata b'acin ranshi a fili kuma yayi zuciya da jikinta sosai hakan ya dinga damun Amera saida kyal ta samu ta na kuka ya hakura Dan tasan logar mijin nata ba abunda ya tsana sama da kukan mace .


ranar dai amera ta d'an daure ba raki ba komai har Dan kanshi ya rabu da ita ya rasa wani irin mutum ne shi shekara Tara da Aure amma har yanzu baitab'a sanin gamsuwar da maza kecewa sunayi ba a tattare da matan su.



Karatun su Zarah sosai yake gudu Dan yanzu haka harsun fara exam sosai suka maida hankalinsu ga karatunsu Masha Allah sun gama Exams lafiya sai kuma jiran result Inda kowa ya tafi gidansu dominyi Hutu dazasu rabu su Ukku saida sukaji ba dadi Chuchu hada hawaye A haka dai suka rabu akan zasu dinga waya Bayan sunyi musayar number"


Chuchu tunda ta koma sosai Ammy taji dad'in irin shigar data ganta da ita ta hijab sosai taji dad'in sauyawar dabi'un na y'artata Wanda tun farko tasan sakacinta ne .


Tunda Chuchu tazo bata da labari sai na Zarah nan Tabawa Ammy labarin karatun da Zarah ke koya mata yanzu har sunyi hizif Talatin sosai Ammy tayi murnar Haduwar y'artata da mutanen kwarai Itama har cikin ranta taji wannan zarar ta kwanta mata a rai sanyawa tayi ta kira mata ita Aiko cikin Sauri Chuchu ta kira mata ita Zarah na d'auka cikin d'oki Chuchu ta ce.


"Momcy ga Ammy na zakuyi magana" ta fad'a ta na bawa Ammy wayar ".

cikin nutsuwa Zarah ta gaishe da Ammy'inda Ammy ta amsa mata cikin Fara'a tare da yi mata Godiya akan Karatun da take koyawa Chuchu"

cewa tayi" ba komai Ammy Ai anzama d'aya "sosai Ammy taji Zarah ta kwanta a ranta Dukda bata ganta a fili ba Amma a d'abi'unta da yanayin yanda taji muryarta sai taji ta na sha'awar Had'a zuri'a da ita a ranta ta ce "

"inama ina da wani d'an da zai sota Bayan MD da na had'asu da ita Dan tasan MD kam yayi nisa ta ma hakura da masa maganar Karin Aure Dan tasan ba yi ba zaiyi.

A haka har lokacin hutunsu ya k'are suka koma makaranta sai farincikin ganin juna suke nan aka d'ora daga Inda aka tsaya har suka cinye second semister Bayan sun koma wani hutun suna dawowa suka shiga aji biyu

a lokacin ne kuma Hafiz zai tafi karo karatu England ranar da yazo mata bankwana school duk yayi sanyi Kallonshi tayi ta ce .

"ya Hafiz naga duk kayi sanyi" Dagowa yayi tare da kallonta ya ce"kawai tafiyar nan da zanyi sainakejin gabana na fad'uwa kamar bazan dawo na taddaki ba sai nakejin kamar wani Abu zai shiga tsakaninmu ko wani zai raba mu Wanda bazan tab'a iya jurewa hakan ba"

"Cikin tausasa murya Zarah ta ce " ka daina wannan tunanin ya Hafiz babu Wanda ya isa ya shiga tsakaninmu kaid'in ka zamemun wani bangare na jikina kayimun abunda ba kowa yayimun a rayuwa ba ka tsayemun a karatu na ni d'in y'ar halak ce ba butulu ba ya Hafiz bazan tab'a butulce maka ba insha Allahu zaka dawo muyi auranmu ta fad'a ta na rufe fuska"


Sai sannan Hafiz ya sauke ajiyar zuciya Tare da sakin rai sunjima suna Hira kafin yayi mata bankwana cike da kewar juna suka rabu "


Koda ta koma hostel duk tayi sanyi Samun Chuchu tayi ta na cika ta na batsewa tare da Harararta.

"d'an murmushi Zarah tayi ta ce " yau kuma wa ya tab'o mana chuchun yaya"

tana cigaba da turo baki ta ce "Ke ce mana momcy" wara idanu tayi ta ce.

"Ni kuma to me nayi" Wancen mutumin mana da kika tsaya dashi kwata_kwata ba class d'inki bane yanzu asmy ke Cemun wai dashi aka sanya miki Aure kinji yanda Naji wlh kwata_kwata bakuyi match ba momcy ke Matar manya ce Wlh Harna fara kishi Dan da yaya na kika dace ba wancen bak'in ba....โœ๐Ÿฟ

_07026166536_

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ๐Ÿ‘ฏโ€โ™€๏ธ๐Ÿ‘Ž๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*


1, *MU GANI A ฦ˜ASA...*๐Ÿ”ฅ
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ฦ˜WAI..*๐Ÿฅš
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*๐Ÿ’ฅ
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*๐ŸŒŽ
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huษ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ษ—aya N300

*DOMIN TURA KUฦŠIN KAI TSAYE*๐Ÿ‘‡

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya๐Ÿ‘‡

0810 433 5144

Masu tura katin MTN๐Ÿ‘‡

0814 179 9224

ฦณan ฦ˜asar Niger zasu tura nasu anan.๐Ÿ‘‡

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huษ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ษ—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ๐Ÿ”ฅ๐Ÿฅš๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŽ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ









_*Miss Hajo*_๐Ÿค™๐Ÿฟ
[8/29, 14:32] โค๏ธโค๏ธโค๏ธ: ๐Ÿ‘จโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ *AUREN WATA TARA* ๐Ÿ‘จโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

```MALLAKAR```

*Hajara L Sadeq*


๐Ÿ…ฟ๏ธ............*19 & 20*


"Bata fuska Zarah tayi Jin shirmen da Chuchu take Dan a shirme ta dauki maganar wata maganar ta kawo musu Dan son barin zancen.

Tunda Hafiz ya tafi kullum cikin waya suke da Zarah tare da video call

Yau Zarah ta tashi da ciwon ciki hakan ya nuna mata zuwan perioud dintane sosai take murkashi akan Gado Dan su Asmy suna lecture Duk ta had'a zufa a haka har suka dawo suka sameta sosai suka shiga tashin hankali musamman Chuchu da batasan da larurar Zarah ba Dan kwanakin baya ciwon ya d'an lafa.


Da damuwa ta ce " subhanallahi me yake damunki momcy"Asmy ce dake mikar da Zarah ta ce perioud dintane yazo mu maza mu kaita Asibiti bari na taro napep "


Da mamaki Chuchu ta ce " Daman haka yake yi mata?

"Eh haka take Asmy ta fad'a tare da saurin fita Dan ta taro napep inda Chuchu ta shiga Jerawa Zarah Sannu.

Asibiti mafi kusa suka nufa Inda Asmy tayiwa Dr d'in bayanin abunda ke damun Zarah allura akayi mata Bayan Bacci ya kwasheta ta na tashi taji da sauki haka suka koma hostel Chuchu dukda tsorata Dan ita duk perioud din da take bata tabajin ciwon ciki ba Saidai taji kasala.


Tundaga lokacin abun Zarah ya k'ara worse a halin yanzu har suma ta ke Asibitin da suke zuwa Dr d'in harya ganesu wani zuwa da sukayi ya cewa Asmy .

"a Gaskiya ko yarinyar nan ta na samun sauki tofa dole sai wani Abu ya shiga tsakanin ta da wani?wara idanu Asmy tayi ta ce.

" What Dr kenan yanzu ba maganin da za a bata"Babu maganin ciwon nan kamar yanda na fad'a hakan ne kawai maganin da zan baku shawara tayi Aure zata daina "


"Ajiyar zuciya Asmy ta sauke ta ce " mungode dr"Ranar sun koma hostel Asmy ta kalli Zarah lokacin ta na kurbar tea ta ce.

"Sis waikinsan me dr ya ce Ko kina daina ciwon cikin nan sai kiyi Aure sainakejin inama saida akayi aurenki da Hafiz kafin ki fara makaranta Dan wlh ciwon nan naki ya fara bani tsoro da safe fa har suma kikayi"

"Cike da damuwa Zarah ta ce " Ni kaina ciwon nan ya na damuna karkiga idan perioud d'ina ya matso irin fad'uwar gaban da nakeji Asmy Aikin gama ya Riga ya gama dole ne nayi hakuri har na k'arasa karatu na Shima ya k'arasa nasa"




Tsaye ya ke waya na K'are a kunnansa daga ka gansa ka San ranshi a matuk'ar b'ace yake tashin hankali k'arara a fuskarsa ya ce.

"what ka na nufin an sanya an kashe Alh sammani?banji me akace daga d'ayan b'angaren ba saiji nayi cikin Sauri ya ce.

" gani nan zuwa k'asar yanzunnan ka sanar da DPO abunda ke faruwa a maza a tari abun da wuri kafin Su gudu a tabbatar an kama su"

Ya na Gama fad'ar haka ya katse kiran Tare kiran PA dinsa ya ce a shirya masa tafiyar gaggawa daga Inda yake tare da Escort dinsa suka wuce Aiport ba tare da ya koma ma gida ba yayi wa Amera bankwana Dan Zuwan emergency ne.



Kasancewar kwazo da dagewa da kuma ilimin addini ya sanya aka bawa Zarah Amera ta makarantar Sauri take sosai Dan zasuje wata musabaqa ta students din makarantu a Polytechnic Kaduna Sosai tayi kyau cikin Zumbuleliyar Hijab d'inta har k'asa

2 Comments On AUREN WATA TARA
avatar
mubarak-nasir

11 months ago

Reply

Woow gaskiya yayi

avatar
mubarak-nasir

11 months ago

Reply

Abun yayi

Please Login or Register in order to submit comment