Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai hannu maroon"

Tare da daura Nik'ab tare da Asmy suka tafi Dan tayi mata rakiya Chuchu ko ta na gida Dan weekend ne kuma yawaici a kd takeyinsa.

Kasancewar a motar makaranta suka tafi cikin k'ank'anin lokaci suka isa Inda aka fara gudanar da Musabaqa ko wasu makarantu har akazo kan makarantar su Zarah Inda Zarah ta wakilcesu cikin muryarta mai dad'in sauraro tare da qiri'arta ta fara karatun da aka tambayeta duk Inda aka janyo saita k'arasa batare da gargadaba ba Kuma zallar tajwid take fitarwa Sosai ta burge mutane da dama dake wajen.

Motocin Escord dinsa Guda goma suka sanya motar da yake ciki tsakiya shi kadai ne a motar sai driver .


sunzo daidai zasu gitta ta poly MD yajiyo karatun muryar da ta kasa barin kwalwarsa cikin Sauri ya cewa "Driver ya tsaya"


tsayawar yayi yayinda sauran motocin ma suka tsaya gabaki d'aya ya mayar da hankalinsa ga zazzak'ar muryarta karatun da yake jiyowa har wani lumshe ido yake Sosai muryar ke shiga ta na ratsa duk wani sassa na jikinsa suna nan tsaye ya na sauraronta muryar da tabbas ya San muryar da yaji ce a lokacin da yake waya da Chuchu.


sosai yaji ya na son cigaba da sauraron karatun daga mamallakiyar wannan zazzakar muryar saida suka kwashe minti Talatin tsaye kafin ta gama karatun sai sannan MD ya dawo hankalinsa.

ji yake kamar ya dawwama cikin sauraron muryar ta Cikin Sauri kuma ya tuno da abunda ya kawosa Umartar driver yayi da yaja su tafi.

Zarah ko Bayan ta gama karatu kabbara kawai ake daga karshe dai ita ta ciyo musu na d'aya Wanda hakan yasa makarantar suka kara alfaharin da ita Dan sannan ne karo na farko a Musabakar makarantu state din da aka fara ciwo musu na d'aya Zarah ta samu kyautoci da dama daga wajen manyan da suka halacci wajen.

Koda za a koma A motar makaranta kin shiga sukayi Dan suna son su biya gidan su chuchu Dan tun d'azu ta ke kiransu akan d'an Allah Ammy tace suzo Mai napep suka Tara Inda sukayi ciniki da shi akan ya kaisu G R A.


Gudu sosai suke shararawa a titi yayinda waya na K'are a kunnansa DPO ne ya ce .

"Ranka ya dad'e sun Kufce mana Yanzu haka Suna Hanyar da kake bi karka yarda su tsere zaka gansu a mashin sun rufe fuska su biyu suka rage sauran sun gudu"


Cikin masifa MD ya Ce "Aikinme kuke har zaku kasa kama k'ananan y'an iskan da basu da aiki sai kashe jinin y'an uwanmu musulmi bil'adama ".

tsaki yaja tare da katse kiran yace driver Kara gudu "Sunzo daidai Wani round about MD ta Cikin glass ya Hango su cikin Sauri ya zage glass din tare da fiddo bindigarsa Ya saitasu ji kake tassss ya harbesu a gefen hannu d'ayanma haka Shi kanshi MD rumtse ido yayi Dan wannan ne karo na farko da ya tab'a harbi a rasuwarsa.


Hakan yayi daidai da isowar su Zarah wajen Akan idonsu Harbin ya afku saida basuga mai Harbin ba Sosai suka rude Zarah ta kankame Asmy tare da fasa Kara Dan iya tsawon rayuwarta bata tab'a ganin irin wannan ba Mutane filis a kasa jina jina akan idonsu aka harbesu.


Ita kanta saida Asmy ta girgiza karkame juna sukayi tare da karanto duk addu'ar da tazo bakinsu dan basu tabajin anyi harbi a gabansu ba lura da hakan mai napep din ya juyo ya ce

"Ku nutsu Wannan abun ba Bak'on Abu bane a Saidai kawai Allah kyauta"

Asmy ce tayi k'arfin halin cewa "da gangan fa aka harbesu suna Tafiyarsu Dan zalinci ,"

girgiza kai napep din yayi ya ce " a Lamarin k'asar nan sai dai addua MD ne a cikin motar kuma ina kallonsa ta cikin glass shi yayi harbin Kunga ko a kudin sa ba abunda aka isa ayi hatta gwamnatin a hannunsu ta ke Saidai hakuri kawai "


MD Zarah ta maimaita a cikin zuciyarta lokaci guda taji wata irin matsanancin tsanar mai sunan a rayuwarta ta tsani mutumin da baisan darajar d'an adam ba bazata tab'a mance da sunan ba mutumin da ya tsaidasu a Zaria da zasuje Banki.


Sosai taji wata irin tsanarsa dukda bata sansa ba a fuska Amma taji a duniya babu mahalukin da ta tsana sama dashi cikin rud'u ta ce "mai Napep juya damu ka maidamu tashar motar Zaria"


Juyasu mai napep din yayi har lokacin Zarah A rude ta ke Har suka isa Tasha Inda suka hau motar Zaria Dan komawa school jikinta bai bar kyarma ba


"Ajiyar zuciya ya sauke daga zaunen da yake tare da maida bindigar ma ajinta a take nan motar y'an sanda suka ido DPO da kanshi ya lek'a ta glass tare da sarawa MD ya ce.


" da ana samun irinka a cikin k'asar nan da an zauna lafiya Allah ya k'ara tsarewa sannan ya k'ara girma yanzu zamu wuce dasu police station ko asibiti bazamu kaisu ba harsai azaba ta ishesu sun fad'a ogansu dake sanyasu wannan aikin".


"Jinjina kai MD yayi tare da cewa " kar ayi Sakaci dasu a matsesu har saisun fad'a ko waye duk bayanin da aka samu a kirayeni "



Har suka isa hostel Zarah na kyarma Inda suna isa ta lulluba saboda zazzabin tsorata da ya zubar mata Asmy ta dinga Lallashinta akan karta sanya abun a ranta ya hanata bacci "Zarah na hawaye ta ce

" dole na damu Asmy Jinin musulmi fa aka kashe a gaba na Asmy bantabajin tsanar wani d'an adam ba a rayuwata sama da MD d'innan da aka fad'a na tsanesa na tsana jininsa na tsani Wanda ya shafesa saboda duk mutumin da zai iya kashe jinin musulmi ya chancahnci tsana mai muni daga wajena "ta fad'a ta na rumtse ido.

Ta na ganin abunda ya faru na dawo mata a cikin kwalwarta.



Lumshe ido yayi jikin Ammynsa ya na jin dad'in zama kusa da mahaifiyar tasa Albarka Sosai Ammy ta shiga sanyawa d'an nata a bisa Namijin kokarin da yayi Dan kafin ya Iso ma Har sungani a television live Chuchu ma sosai tayi alfaharin da irin taimakon da yayan nata yake bayarwa ta fannin Yak'i da y'an ta'addan da suka hana k'asarmu zaman lafiya.


Ammy ce ta kalli chuchu ta ce " Wai har yanzu su momcyn taki Basu iso ba lafiya".


Lalubo wayarta Chuchu tayi cikin damuwa tare da cewa"nima tun d'azu jiransu nake jira Bayan na shirya musu abubuwa ta fad'a ta na kiran Zarah"

Asmy ce ta d'auka dan zarah duk ta rikice mata cikin shagwaba Chuchu ta ce


"Wai me ya tsaidaku nasanfa tun d'azu aka gama Musabaqa kufa kawai nake jira " cikin sanyi Asmy ta ce "am so sorry sis wlh matsala aka samu wani Abu ne ya firgitar damu yanzu haka muna Zaria Kinga Zarah nan ma bata lafiya zazzabi ke damunta"

Cikin tsananin damuwa Chuchu ta ce "Subhanallahi me ya faru ya jikin momcy din " da sauki Haba ai yau munga tashin hankali maganar bata fad'uwa a waya bace saidai kindawo"Cewar Asmy .


Sosai Chuchu ta rude "Ammy ce ta ce " Lafiya Kuwa"wlh Ammy wai wani Abu ya rud'ar dasu suka koma yanzu haka momcy ba lafiya bari kawai na wuce school din yanzu hankali na bai nutsu ba "

Ta fad'a tare da saurin Rugawa ta sanyo k'atuwar hijab din da suka dinka tare da Zarah tundaga Fitowarta MD ya bita da Kallon mamaki Kasa shiru yayi ya ce .

"Ammy yau Chuchu ce da hijab " Dariya Ammy tayi ta ce "Au ashe ban baka labari ba Ai yanzu Chuchu an nutsu kawa tayi Malama Yanzu haka ta tafi hizif arba'in Karin karatu takeyi mata wannan shigar banza da kide kide da raye raye duk ta dainasu "

"wow but Gaskiya Naji dadi ko wacece wannan Malamar ta chanchanci tukuci daga gareni".


Cikin farinciki Chuchu ta ce "Wlh yaya danma baka ganta ba ta had'u Ga kyau Ga addini ga Ilimi itace amera d'in school d'inmu yanzu haka musabak'a ce sukazo ita ta wakilce y'an makarantarmu zancen da nake maka Yanzu haka ita ta ciyo musu na daya barima ka gani sunna sun dora Yanzunnan ta fad'a ta na kamo sunna daidai Inda Zarah ke karatu sanye cikin niqab ".



Maida hankalinshi MD yayi ga television d'in sosai gabansa ya tsananta fad'uwa jin muryar da yajiyo dazu d'ince


gabaki d'aya hankalinsa ya maida ga sauraron daddad'an karatun da baitab'a sauraron karatun da ya bashi nutsuwa da annashuwa irinsa ba Sannan ya kafa mata idany


Sanye take cikin Zumbuleliyar hijab fuskarta ba abunda kake gani hatta kwayar idanunta wannan Karin a rufe suke cikin nikab nauyayyar Ajiyar zuciya ya sauke tare da Kallon Chuchu ya ce .


" ko ita ce muryar da najiwo Daga gefenki kwanaki"Cikin murna Chuchu ta ce "Eh itace yaya Zarah kenan kawata ce sunan ammy gareta yaya Ai saima ka ganta ido da ido nasan saita tafi da imaninka ta had'u sosai yayana ka ganta saika rude Dan da kai tayi match tafi Aunty Amera komai"

Wani banzan kallo ya watsa na kin rainamun wayau tare da janyo kunnanta ya murde da karfi ya ce......✍🏿


*hmmm muje zuwa Fans ba a fara komai ba yanzu salon wasan zai fara Kudai kawai Karku gaji da comment sharhi tare da sharing akwai daddadar tafiya nan gaba*


*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. πŸ‘―β€β™€οΈπŸ‘ŽπŸ‘‡πŸ‘‡*


1, *MU GANI A ƘASA...*πŸ”₯
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*πŸ₯š
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*πŸ’₯
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huΙ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda Ι—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*πŸ‘‡

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biyaπŸ‘‡

0810 433 5144

Masu tura katin MTNπŸ‘‡

0814 179 9224

Ζ³an Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.πŸ‘‡

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huΙ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda Ι—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* πŸ”₯πŸ₯šπŸ’₯πŸŒŽπŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨


_*Miss Hajo ce*_πŸ€™πŸΏ
[8/29, 15:11] ❀️❀️❀️: πŸ‘¨β€β€οΈβ€πŸ‘¨ *AUREN WATA TARA* πŸ‘¨β€β€οΈβ€πŸ‘¨

```MALLAKAR```

*Hajara L Sadeq*
_*TEAM GAWURTATTU BIYAR*_πŸ’ƒ

*SHAFIN NAN NA SADAUKAR DASHI GA DAUKAKIN MASOYA A DUK INDA SUKE NAJI DADI KWARAI DA YANDA KUKE NUNAWA LITTATAFAINA SOYAYYA KUSANI NIMA INAYIMUKU SON FISABILILLAHI MASOYAN ASALI WANNAN PAGE DIN NAKU NE KYAUTA*😝

πŸ…ΏοΈ............*21 & 22*

"Ina wasa dake Chuchu ni kike fad'awa haka na k'arajin maganar nan bakinki zan zaneki"

D'an Kara Ta saki tare da cewa "Auch sorry Babban yaya bazan sake ba" Kafin ya sakar mata kunnen ya ce .

"Bazaki koma ba Yau sai jibi week end ya k'are badan Chuchu ba taso ta zauna Dan bazata musawa Yayan nata ba Amma gabak'i d'aya hankalinta ya tafi wajensu Zarah.


suna nan zaune a palour suna y'ar tab'a Hira Har aka k'are nuno Musabakar A television Knoking da suka jiyone ya sanya Chuchu saurin Mikewa tare da zuwa ta bude.


Wani wawan tsalle ta daka ganin Hajiya kaka tare da su Adil da Ruky " dakyal ta Bari suka karaso palourn saboda d'oki MD ko gabanshi ne ya fad'i ganin zuwan Hajiya kaka gidan yasan shikenan yanzu kuma zata addabeshi akan Maganar k'ara Aure.


Sosai Ammy tayi murnar ganinsu nan ta shiga musu lale marhaban Bayan sun gaisa an cika musu gabansu da abubuwan makuleshe Chuchu suna mak'ale ita da Ruky da bazata wuce sa anninta ba suna Hirar yaushe gamo.

MD ne ya kalli Hajiya fuska ba walwala ya ce "Sannu da zuwa Hajiya anzo lafiya".


tab'e baki tayi tare da k'are masa kallo ta ce "Lafiya salamamme ina ita gimbiyar taka ko har yanzu bata haihu ba "


"Ya na had'e fuska ya ce " Daga zuwanki ba ko gaisawar kirki Hajiya "


"eh ba gaisuwar ai wannan zuwan da kaga nayi zuwan Kane na kashin kanka tunda ita Fatima ta kasa tab'uka komai ta na tsoranka karka tsireta to ni bazanji tsoronka ba idan kaga na bar nan garin nan tofa sai naga haihuwar shegiyar yarinyar nan idan ba haka ba Da Rukayya zan hadaka Auren zumunci sai Inga ta tsiya.


" Ba MD ba hatta ruky saida ta d'ago jin maganar Hajiya kasa tayi da kanta Dan Ita kanta tasan karya take tace batason MD amma kuma tasan MD bazai tab'a sonta ba yafi karfinta kuma ma ita tana da Wanda takeso "


"Shiko gogan Mikewa yayi ba tare da ya nuna Alamun damuwa a fuskarsa ba ya haye stairs da Kallo Hajiya ta bishi ta na Jan tsaki" Chuchu ko Dariya tayi kasa kasa tare da tsunkunin Ruky ta ce "Kaji amarya a gidan yaya MD" .


harara ta maka mata Arif ko Tunda ya shigo ya ke kallon sahibar ta sa Chuchu ta message yayi mata magana da su kebe Dagowa tayi suka hada ido tare da sakarwa juna murmushi Ya Mike ya fita Ta na ganin haka itama ta bisa "tab'e baki Hajiya tayi ta ce.


" kuma Kunzo ku fad'amun abunda ke tsakaninku Dan na gaji duk Aurar da ku zanyi yara sun girma sun bunkasa a gida Suna gogayya da iyayensu"cewar Hajiya ta na Jan tsaki Ammy dai murmushi kawai take.


Washegari asubanci MD yayi yabar garin daga shi sai Jabir kamar koda yaushe tafiyar sirri sukayi har suka isa garin gombe.

Daga gombe ma nayi mamaki irin dajin da suka Yanka kafin Su isa wani k'aramun kauye karshen kauyen naga tafkeken gida flat da ya tsaru Inda suka kutsa motarsu cikin gidan


Zaune yake gaban wani dattijon mutum Wanda bazai haura shekaru 65 ba ko fi a kwance ya ke yayinda idanunsa suke a bud'e Babu abunda yake motsi a cikin jikinsa sai y'ar yatsarsa Gadon da yake MD ya hau tare da kamo hannun dattijon ya rike gam gam ya na murzawa Shima shi yake kallon dattijon ba abunda yake sakar masa sai Murmushi ".

Muryarshi na rawa Alamun damuwa k'arara a fuskarsa ya ce" Allah ya baka lafiya Insha Allahu Inajin a jikina wahalar nan taka ta kusa zuwa karshe da izinin ubangiji "

"Lumshe ido yayi tare da budesu Alamun yaji dadin abunda ya fada " wani Dattijon ne ya shigo Shima da bazai wuce sa'annin na kwancen ba .

"Kallonshi MD yayi ya ce " Sannu Baba A Gaskiya ba abunda zance da ku sai Godiya Allah ya saka da alkhairi jikin nashi na ga ya fara sauki masha Allah".

Da Fara a tsohon ya ce "muke da Godiya a wajenka ranka ya dad'e kai ka gama yi mana komai Allah dai ya basa lfy yanzu kam ana samun cigaba sosai Dan jiya har hannunshi saida ya motsa "


"Nauyayyar Ajiyar zuciya MD ya sauke ya ce " Baba inason a ninka akan saukar da ake masa Ya tashi daga duk sati ya koma duk kwana biyu "sannan ya mik'a masa mak'udan kudi ya ce " gashi a k'ara rabawa malamai da kuma makarantu a ninka sadakokin da ake ".

***
Tsaye yake sai safa da marwa yake waya na K'are a kunnashi cikin tsananin tashin hankali ya ke cewa " garinya har aka bari aka kama su baushe Aiko muddin suna hannun hukuma akwai babbar matsala sannan shi MD din zanyi maganinsa ina zuwa karka damu bazasu tab'a Tuna Wanda ya sanyasu aikinba ko za a kashesu".


Ya na Gama wayar cikin Sauri ya bar gidan tare da wucewa wajen tsafinsu Dan a rufewa su baushe baki.

Da dare aka kirasa akace aiki ya gama ranka ya dad'e sunkasa fad'a "Dariyar mugunta ya kwashe da ita ya ce " suna wasa dani basu San waye Alhaji mudan ba manya ma mun gagara baresu kanana kanana sannan shi MD zaisan ya shiga gonata ubanshi ma na gama dashi bare shi darajar soyayyar da y'ata kawai take masa yake ci nasan muddin na kashesa zata shiga mugun hali wanda bazan juri hakan ba saboda soyayyar da nakeyiwa Amera y'a daya tilo amma badan haka ba Da na jima da shafe Tarihinsa a cikin rayuwa k'aramun kwari"ya k'arasa fad'a ya na kecewa da wata dariyar irin ta su ta mugaye.



Ran Monday Chuchu ta koma school koda ta je a lokacin Zarah taji sauk'i da damuwa ta ce " wlh hankali na duk a tashe yake me ya ke faruwa?

"Haba daughter Ai zuwanmu kadunar nan munga tashin hankali nan suka bata labarin abunda suka gani sannan Zarah ta d'ora da cewa .

" wlh Chuchu bantaba Jin tsanar wani mahaluki ba sama da MD d'innan na tsanesa na tsani duk Wanda ya shafesa zubar da jinin mumuni guda d'aya wasane Chuchu yaza ayi k'asarmu ta zauna lafiya ana zubar da jinin musulmai a gabanmufa mugun mutumin nan ya harbe bayin Allah suna Tafiyarsu basuji ba basu gani ba "


.rumtse idonta Chuchu tayi Jin Yanda Zarah ke aibanta Yayan nata mafi soyuwa a gareta Cike da damuwa ta ce "Amma bai kamata ace kin yanke hukunci batare da kin bincika ba kika sani ko masu laifi ne "


Wani banzan kallo Zarah ta watsa mata tare da cewa "Ai daman haka za ace tunda Mai kud'ine komai yayi daidaine Ta haka aka karesa kenan to ai idan duniya ta karesa zaiyi bayani a lahira mugu azzalumi macuci makashin mutane ko kema kina goyon bayansa ne"


Kara rumtse idonta Chuchu tayi Jin bazata iya d'aukar wannan mugayen kalaman ga yayantaba ya sanya ta tashi tashi tare da komawa gadonta ta kwanta tare da rumtse ido Tanajin zafin maganganun da Zara ke yi akan Yayan nata .


Tabbas inko hakane dole ta boyewa Zarah cewar ita kanwar MD ce Dan yanda taga tsanarsa k'arara a idonta tasan Kanwarsa ce Zata iya rabuwa da ita Wanda bazata juri hakan ba Dan a tarenta da Zarah ta koyi abubuwa da dama na karuwa


A halin yanzu su Zara sun gama Exams Inda sukayi hutun second semester da sun dawo level3 zasu shiga.

Koda ta koma gida a kofar gida ta tarar da Baba cikin farinciki ta je ta gaishe da mahaifin nata ya amsa mata ya na sanya mata Albarka sun tab'a Hira sosai ta y’a da uba kafin ta wuce cikin gidan


Ta na shiga khairat ta rugo da gudu tare da Rungume ta ta ce "oyoyoy Aunty Zarah Sannu da zuwa" itama Rungume y'ar uwar tata tayi ta ce "Sannu my khairat ykk ya makarantar kina dai zuwa ko" gyada mata kai tayi tare da Amsar akwatinta ta shigar mata dashi ciki.


Mama rabi ce ta lek'o daga daki jiyo Zarah da tayi da Fara a Zarah ta ce "Mama ina yini" tsaki taja tare da cewa "da baki ganni lfy ba andawo daga yawon katuwancin ko Har wani kiba da kyau aka k'ara hmm muna nan dai muna jiran kishin dan abun nan ba banza ba akwai lauje cikin nad'i".


Girgiza kai kawai Zarah tayi Dan tasaba da kalaman nan ta na shiga daki Nan ta fitowa da khairat tsarabarta Godiya tayi mata jin bataji Safiya ba a gidan ya sanyata cewa " waini ina Safiya tunda na shigo banjitaba"tab'e baki khairat tayi ta ce .


"Baba ya maida ita Batsari gidan Bappa samari ke zuwa Wajenta har a soro suke zance rannan Baba ya kamata wani na rungumarta ranar Tasha Duka a ranar ya kaita Batsari ya barota ya ce bazata k'ara dawowa garin nan ba ".


Ajiyar zuciya Zarah ta sauke ta ce " Allah ya kyauta kedai Dan Allah khairat ki nutsu karki Shiga rayuwar nan marar kyau"murmushi tayi ta ce "Insha Allahu Aunty itama safiyar ai su Aunty Habiba ta ke biyawa"

Bayan ta huta Corn flask ta jika tare da madara ta sha ta kwanta ba b'ata lokaci baccin gajiya ya kwasheta saboda akwai tsananin gajiya tattare da ita.



Duka zazzaune suke a palourn hajiya,Ammy ,Adil,Chuchu,sai Ruky MD dake Danna waya Hajiya ta Kalla ta ce.

"Wannan karin maganar da nazo da ita ba wasa Mustapha wlh wlh kaji na rantse shekara guda na baka idan Matar ka bata haihu ba ko bata samu ciki ba ko a kauye ne sai na nemo maka mata na aura maka ko ka fito mun da wacce kakeso amma Bazan juri cigaba da ganin wannan kayan takaicin ba Mace d'aya ta zauna ta na Juyaka macen ma ba y'ar arziki ba to wlh baka isa ba ni ba tsohuwar banza ba ce Na baka shekara guda idan ba haka ba zakaga irin hukuncin da zan yanke maka salamamme a haka kamar zai tab'uka abun kirki a ido kamar mai jarumta nanko solo ne fanko kawai Me Auren ya amfaneka dashi aikin banza aikin hofi "


MD cikin tashin hankali ya ce "Haba Hajiya wai meyasa kike haka Haihuwa fa ta Allah ce Sannan Shekara guda fa Haba hajiya ke da kinzo saikin tayarmun da hankali"

Ammy ce ta ce "karna karajin bakinka babana ba kaiba ko ni Hajiya ta na ikon yanke hukunci akaina Dan haka abunda ta fad'a Gaskiya ne ko ni kaina Dan ba yanda zanyi ne na kyaleka Dan haka karna karajin bakinka shekara guda aka baka ba wata guda ba duk wani adalcin da zamuyi munyi maka amma baka gani ba Dan haka Ina Bayan hukuncin da Hajiya ta yanke"

Amma Ammy.."yimun shiru karka sake magana"Kallon Ammy kawai MD yake Dan Gaskiya hukuncin nan yayi masa tsauri ta ya ma za ace wai nanda shekara idan Amera ba ta haihu ba zaiyi Aure shi har akwaima macen da ta isa ya so ta har ya aure ta Bayan Amira ga kuma tashin hankalinshi na halin da Amira zata shiga ta samu labarin nan Dan ba abunda ya tsana sama da b'acin ran amirar sa ".


Chuchu ko hukuncin nan yayi mata dadi hamdala ta sauke cikin d'oki ta ce " yo Hajiya wlh danma bakisani ba Aunty Amera fa Bata tab'a girki ba a gidan yaya Saidai su suyo abincin restaurant ga bata da aiki sai waya da Abokai da yawo kasash.....kasa k'arasa maganar tayi sakamakon tsawar da ya daka mata cikin tsananin Zafin rai ya ce "get out kafin na tattakaki ni sa ankine Ana magana ta kina sa baki Dan baki da tarbiya"

Cikin Sauri Chuchu ta mik'e tare da saurin barin d'akin Dan ta tsorata da yanda Yayan nata yayi mata

"ohh dan ta fada gaskiya shine zakayi mata tsawa to Komai dai me zakayi Saidai kayi amma hukuncin da na yanke banga ubanda ya isa ya take sa ba mu zuba mu gani mu da kai d'an halak ka fasa shege sai yanka sototon wofi salamamme bawan mace"......✍🏿

*07026166536 hanya a bud'e take domin neman Karin bayani sharhi ko tambaya*

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. πŸ‘―β€β™€οΈπŸ‘ŽπŸ‘‡πŸ‘‡*


1, *MU GANI A ƘASA...*πŸ”₯
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*πŸ₯š
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*πŸ’₯
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*πŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huΙ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda Ι—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*πŸ‘‡

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biyaπŸ‘‡

0810 433 5144

Masu tura katin MTNπŸ‘‡

0814 179 9224

Ζ³an Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.πŸ‘‡

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huΙ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda Ι—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* πŸ”₯πŸ₯šπŸ’₯πŸŒŽπŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨


_*Miss Hajo ce*_πŸ€™πŸΏ
[8/30, 17:38] ❀️❀️❀️: πŸ‘¨β€β€οΈβ€πŸ‘¨ *AUREN WATA TARA* πŸ‘¨β€β€οΈβ€πŸ‘¨

```MALLAKAR```

*Hajara L Sadeq*

*_TEAM GAWURTATTU BIYAR_*πŸ’ƒ

πŸ…ΏοΈ............*23 & 24*


Sosai Hajiya ta shiga f'ada Inda ta shiga ba tanan take fita ba Ganin haka ya sanya MD barin palour ya ma bar gidan gabak'i d'aya ya koma gidansa.


Tunda yaje ba tunanin da ya ke sai maganganun Hajiya baijin zaiyi abunda Hajiya take so Amma kuma Tabbas yasan.muddin Amira bata haihu ba da gaske Hajiya Aure zatayi masa Dan ta isa da su hatta mahaifinsu da yana raye ita ke ikonshi bare shi sosai ya shiga kogin tunani sai Jan tsaki ya ke ya Ma rasa mafutar da zai samu.


Jabir ne ya fad'o masa a rai Dan ba abunda ya ke boyewa aminin nasa tun pri sch ya na Danna masa kira ya ce ya na buk'atar ganinsa ya ce gasanan.

Minti ashirin mai kyau jabir ya Iso cike da damuwa ya kalli abokin nasa ya ce.

"Yadai Bloody akwai matsala ne naganka haka?" Numfashi MD yaja ya ce.

"babba ma kuwa Jaber old woman d'in chan Ce tazo wai dole ta bani nan da shekara idan Amera bata samu ciki ba ko bata haihu ba

2 Comments On AUREN WATA TARA
avatar
mubarak-nasir

11 months ago

Reply

Woow gaskiya yayi

avatar
mubarak-nasir

11 months ago

Reply

Abun yayi

Please Login or Register in order to submit comment