Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da murya ya ce "Kinsan bazan tab'a kinkiba saboda wannan Amera ina sonki har gobe kawai d'abi'unkine basamun Haihuwa kuma da kike magana Ai dukanmu ba asan mai matsala ba Dan haka karna karajin Kin fad'a haka"


Mikewa tayi tare da zuwa Inda yake ta zauna ta d'ora Kanta bisa kafadarsa ta ce "Thnks mijina insha Allah zanyi kokari wajen ganin na sauya dabi'u na please ka cigaba da rik'emun Amanata honey nima inason haihuear nan nasan yanda kakeji Saboda nima irin haka nakeji a cikin raina dan Allah kada Rashin haihuwa ya sanya ka ce zaka.Kara Aure wlh ina tsananin sonka mijina"

" ina tsananin kishinka akanka zan iya komai please karkace zaka k'aramun kishiya Dan na tsaneta bana kaunarta wlh duk ranar da ka k'ara Aure Saidai nima a kasheni amma saina kashe ko wacece.........โœ๐Ÿฟ

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ๐Ÿ‘ฏโ€โ™€๏ธ๐Ÿ‘Ž๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*


1, *MU GANI A ฦ˜ASA...*๐Ÿ”ฅ
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ฦ˜WAI..*๐Ÿฅš
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*๐Ÿ’ฅ
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*๐ŸŒŽ
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huษ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ษ—aya N300

*DOMIN TURA KUฦŠIN KAI TSAYE*๐Ÿ‘‡

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya๐Ÿ‘‡

0810 433 5144

Masu tura katin MTN๐Ÿ‘‡

0814 179 9224

ฦณan ฦ˜asar Niger zasu tura nasu anan.๐Ÿ‘‡

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huษ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ษ—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ๐Ÿ”ฅ๐Ÿฅš๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŽ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ



_*Miss Hajo ce*_๐Ÿค™๐Ÿฟ
[8/26, 17:07] โค๏ธโค๏ธโค๏ธ: ๐Ÿ’‘ *AUREN WATA TARA* ๐Ÿ‘จโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

MALLAKAR

*Hajara L Sadeq*

*_TEAM GAWURTATTU BIYAR_*๐Ÿ’ƒ

๐Ÿ…ฟ๏ธ.........*13 & 14*


Da mamaki MD yake kallonta jin kalamanta na karshe ya ce "

"Kina nufin zaki iya kisa kenan Amera"
Tana narke masa ta ce.

"Banajin zan iya kisa amma akanka zan iya kashe duk wacce tace zatayi kokarin rabani dakai ko ta shigo rayuwarka saboda ba k'aramun so nake maka ba "

"Girgiza kai kawai yayi batare da yace uffan Dan wannan haukan kishin na Amera ya fara mata uzuri idan tana wasu kalaman har mamaki take basa"


Sai yamma ya samu ya lek'a gidansu zaune yayi kan sopa tare da Kallon Chuchu dake gefen Ammy tana Danna waya ya ce.

"sis jeki had'amun kayan bud'a baki" Aje wayar tayi tare da mikewa ta ce"to babban yaya"

"Bayan barin Chuchu d'akin Ammy ta watsa masa harara ta ce

" ita Matar Mata aikinme take da bazata hada maka kayan bud'a baki ba "

"Jan numfashi yayi ya ce " Ammey Kenan "


"Kamarya Ammey Kenan Gaskiya Ce bakwaso daga kai har ita kaidai wannan Auren bai amsheka ba dashi da babu a wajena duk d'aya tunda banga wani banbanci ko cigaba da aka samu ba ace kana da mata amma bata isa ta shiga kitchen ta girka maka abinci ba ita ga shafaffiya da mai d'iyar Donald thrump ko?.


" sannan Dan tsabar fin arziki ni ban kai matsayin da zatazo Ta gaishe ni ba Dan na fad'a Gaskiya takemun gaba ai wlh nasan da da ran Alhaji da bazai barka haka baka Kara Aure ba Allah jikan dai Abbanku da Rahama amma rashinsa abubuwa da dama sun dagule"


" Duk fad'an ta Ammey take baisaka baki ba saida ta kawo zancen Abba tukwana ya ce "Ameeen " yana jin kewar Abban nashi harta gama fadanta yanajinta yayi shiru.


Washe gari saida ya nunawa Amera b'acin ranshi tukwana ta shirya ta je gaishe da Ammey sosai Ammey ta tarbeta faram faram dukda murtukewar da take irin ala dole tazo hakan bai sanya Ammey ta nuna mata komai ba.

batayi awa guda ba tayi musu bankwana tare da wucewa gidansu Dan ta tsani surukar tata tunda ta ce ayi mata kishiya.

Sosai nayi mamakin ganin girman gidansu Amera ashe dai suma masu kudi ne koda ta shiga gidan cikin shagwaba ta Ruga tare da Rungume Mummyn ta Cikin farinciki sukantarbi juna.


Daddyntama ya fito Suka Rungume juna a yanda naga yanayin mu'amularta da Iyayenta na tabbatar da ba k'aramun so sukeyiwa Amera ba sai nan nan suke da ita kodan kasancewar ta tilon y'arsu.


Da dare MD yayi ta jirayan dawowar Amera amma shiru kakeji Kamar bazai kirata ba saikuma ya Danna mata kira .
Bayan ta d'auka ya ce.


"Baki ganin dare yayi ki duba agogo har karfe 11 fa"

Haba honey a gida fa zan kwana shekara biyu banga iyayena ba Saina kwana biyu tukwana zan dawo ai daman Dan muga gida Mukazo"

Ran MD ne yayi mugun b'aci katse kiran yayi tare da Jan tsaki "Amera ko turo baki tayi daga Inda ta ke ta ce.

" badai zandawo ba kaje Chan kaji da jarabarka aini ba baiwarka bace ayi mutum kamar doki ai wlh saina kwana biyu ko kana gani na ".


Washegari tunda sassafe MD ana gama Sallar asuba ya shirya tare da kiran Jabir a waya Bayan yazo sunyi musabaha Jabir ya ce.

"Bloddy lafiya kira da sassafen nan" lafiya gombe zamu"yana fad'ar haka ya gane Inda zasu.

"ya ce okay bari a shirya tafiyar " Cikin kankanin lokaci aka shirya musu tafiyar cikin sirri kamar ko yaushe duk sanda zasuje a sirrance suke tafiya har suka isa gombe fuskarsa sanye da facemask ba kowa ya gane saba Jabir ma haka.



Kasancewar Tafiyarsu makaranta na tunkarowa ya sanyasu shiga busy

sosai Hafiz yake taka rawar gani a tafiyar da su Zarah zasuyi makaranta A yanzu sun gama Shirya koma yau Jabir ya kaisu Shopping mall Wanda shi ya biya musu kudin sayayyar komai itadai Zarah a sanyaye take yayinda Asma'u ke d'aukar musu komai da zasu buk'ata.


Bayan sun gama ya biya kudin suka kama hanyar gida Bayan shigar Asma'u gidan sun tab'a Hira sosai tsakanin Zarah da Hafiz Bayan nan tayi mishi Godiya akan irin hidimar da yake mata murmushi ya sakar mata ya ce.

"Komai nayi miki ban fad'i ba matata har na k'agara ranar nan tazo bansan wani irin farinciki zan shiga ba ranar da muka zama mata da miji"

Murmushi Zarah tayi tare da rufe fuska kunya ta baibayeta.

"Cikin Sauri ta bud'e murfin motar tare da fita "

Dariya yayi tare da girgiza kai Dan kunyar ta Zarahn tashi ba k'aramun burgesa take ba yanason mace mai kunya a rayuwa(exectly wlh kunya ado ce ga y'a mace maza da dama suna son mace mai kunya Rashin kunyar y'a mace ba wayewa bace Allahsa mu dace")


yaune tafiyar su Zarah makaranta tunda suka tashi cikin farinciki suke su dukansu Bayan sungama Parking d'in komai d'insu an saka a boot din motar hafiz .

nasiha sosai mai shiga jiki Malam ya dinga musu Bayan suma su maman su Asmy sunyi musu nasiha Mama Rabi ko ko Allah ya kiyaye batace ba sai bak'inciki take dubu goma Malam ya basu tare da cewa sunyi wani abun dashi.


Dukansu sosai sukayi kyau cikin manyan hijabai Asmy ma tayi kyau Dan itama masha Allah badai kyauba a hanya Hafiz sai satar kallon Zarah yake har suka isa Zaria kai tsaye cikin Makarantar A B U suka nufa.


Asmy ita ta dinga shigar musu da kayansu hostel din da aka kama musu Zarah ko tana gaban motar Hafiz ne ya mik'o mata kwalin waya biyu Duka iri d'aya Tare da cewa .

"ga wayarki keda Asmy please dia karkice bazaki amsa ba saboda bazan juri Rashin jin muryarki a kusa dani ba Kuma hasalima An sanya mana Aure ina da hakkin da zan d'auki hidimarki"


Amsar kwalin wayar Zarah tare da cewa "Hakane ya Hafiz nagode Hakika kaid'in ka taka rawar gani a cikin rayuwa ta babu abunda zance dakai Sai fatan alkhairi da nasara a rayuwa mungode"


Murmushi yayi najin dadi tare da mik'a mata 20k yace gashi ba yawa ku fara chachaftawa da wannan"


"girgiza kai tayi tare d'ago da dara daran idanuwanta "a a a ya Hafiz wlh bazan amsa ba hidimar tayi yawa."


"kamo lallausan hannunta yayi tare da damk'a mata kudin a hannu Wanda tunda ya tab'a hannun Zarah taji wani irin shock saida ta rumtse ido kafin ta daidaita nutsuwarta tayi saurin kwace hannunta Tare da b'ata fuska ta ce "

"Meyasa zaka rik'emun hannu ya Hafiz Bayan ni ba maharramarka bace"hade hannayenshi waje biyu Alamun rok'o ya ce "am sorry my Zarah by mistake ne bansan nayi ba"

" Uhm" kawai tace tare da bude motar ta ce "Ka tafi karkayi dare fa kaga hanya ba kyau"

"korata ake kenan"cikin murmushi ta bashi amsa da "Nina isa Banki mu shekara haka ba"

'ta fad'a ta na rufe fuska " murmushin jin dad'i yayi cike da kewarta Hafiz ya juya yabar makaranta Inda Zarah ta kama hanyar hostel d'insu.

ta na shiga ta samu Asmy Harta cire hijab din ta na shirya musu kaya "Kallon d'akin tayi ta ce.

" wai nufinki mu kadai ne kenan a dakin"

"Wlhko Nima haka nagani naga duk ba a fara zuwa ba Kinsan Monday ake fara lectures ba kowa zai zo kamar haka ba"

"Kice mu iyayen azarb'ab'i mune farko farko ta fad'a tana cire hijab din jikinta "

Dariya asmy tayi ta ce "Keko abunka ga farin shiga Dariya Itama Zarah tayi tare suka kimtsa komai kafin Zarah ta mik'awa Asmy wayar da ya Hafiz ya saya musu zo kuga murna wajen Asmy hada tsalle ta Rungume Zarah.

" itama Zarah cikin farincikin take bud'e wayar suka ga iPhone 6+ ce Duka iri daya dubawa sukayi kowacce Duka an sanya sim ganin ba chaji gashi ba wuta ya sanyasu ajewa sai Chan wajen 8 aka kawo wuta nan suka sanya wawowin chaji salla Zarah tayi tare tare da hayewa kan bed tace.

"nikam bacci zanyi wlh nagaji" Asmy ce ta ce "Chab aini nan inkinga na kwanta to wayar nan ta cika Na duddura abubuwa a ciki har what's app saina bud'e komin dare.

" Dariya Zarah tayi ta ce "aifa abun nema ya samu nikam bacci ma zanyi waya bata dameniba sosai Idan kin d'auko abubuwan nima ki daukoman amma what's app kadai zaki budemun sannan kiyimun down load din Qur'an na ji da na karantawa"

" To" Asmy ta fad'a ta ce "Mu sarakan zumudi Allah sama akwai data a sim din " Juyawa Zarah tayi tare da kwanciya ta ce .


"Allahsa ma babu muga ta tsiya kiyi ,zaman hofi"

"Insha Allahu ma akwai muguwa Asmy ta fad'a tana Mikewa itama tare da Fara Sallar bacci ne ya kwashe Zarah cike da gajiya.

Ranar Monday suka fara Lectures Sosai Dukansu suka maida hankalinsu ga karatunsu Zarah suna waya da Hafiz Sosai Kuma suna chat dukda ba Sosai take hawaba saboda ba wasu mutanen chat gareta ba.

danma Asmy tayiwa wata kawarsu da sukayi sec magana ta bada number su aka sanyasu grp din makaranta anan ne ma wasu ke binsu PC har suke chat amma dukda haka Zarah saita yini bata hau online ba.

Karatu suke sosai ba kama hannun yaro yanzu hostel din ya fara cika da mutane Dakinsu ma sunsamu Karin wata Mutum guda zaituna.



Cikin marairaicewa ta ce "Yaya Dan Allah ka bari na tafi A B U din wlh yaya banason karatu a America plx harfa sun bani admissions kuma ma har anfara lectures yaya Dan Allah"

"Chuchu bazan barki kiyi karatu anan k'asar ba fa Ga yanda na tsara tare zamu tafi america a gidana zakiyi karatunki amma ban lamunce na barki ki tafi Zaria karatu ba Nafison kiyi a gaba na na sanya miki ido saboda wannan rawar kan naki Dan kiyi abunda kikeso shiyasa ai kikak'i cike KASU kika zab'i ki tafi Zaria sannan banason kiyi karatu a kasar nan sanin kanki ne to bazaki ba A B U din ba na gama magana"

"kuka Chuchu ta sanya tare da Fara birgima ta sangarta sosai ta ke kuka da diddira kafa Ammy ce ta shigo ta ce .

" Subhanalla Me akayiwa Auta ta ke wannan kukan "MD dake zauna baice uffan ba sai maida hankalinshi ga kallon da yake yayi"

Chuchu ce cikin sangarta ta ce"Ammy yaya ne ya ce "Wai bazan tafi Zaria karatu ba dole sai dai mu tafi america tare Bayan ni banason nesa dake Ammy plx ki ce ya barni "


"Kallon MD Ammy ta yi ta ce " me yasa bazaka barta ba babana tunda harta samu kuma ta nuna Chan din take so ka barta ta tafi kawai nima banason tayi nesa dani saboda kaga gidan kadaici zaiyimun yawane ba Abbanku Zainab na gidan mijinta kaima ka tafi sai anganka please Babban yaya ka barmun ita "


Jan numfashi Yayi tare Dagowa ya harari Chuchu dake Kuka jikin Ammy ya ce.

"Allah Ammy kin sangarta Yarinyar nan jifa irin tabarar da takeyiwa mutane"

Dariya Ammy tayi ta ce "Ah muka sangarta ta dai duk gidan nan wa ya fi sangarta Maryam sama da kai "

"Ummmm to Taci arzikinki Ammy na yarda Tayi Chan d'in Allah kiyaye Amma Tana cigaba da irin wannan shigar Saidai taga na cireta Nayi mata Aure "

ya fad'a yana kallon matsatsun Riga da wandon dake jikinta Tsallen murna Chuchu ta buga tare da rugawa ta Rungumeshi ta ce.

"Thnks Babban Yaya Uba Allah ya k'ara girma bazan sake ba sannan tayi Dariya ta ce hhh yaya Ai ko kayimun Auren bazan zaunaba y'ar k'arama dani kuna kaini kafin ku dawo ma na rigaku gudowa "


Duk miskilancin MD saida ya d'an dara tare da Kai mata "Dukan wasa a baya ya ce.

" Kin rainani ko chuchun yaya shiyasa kika fad'amun haka"

"Ammey ma tayi Dariya tare da girgiza kai ta ce "Allah shiryaki Auta"

Dariya Chuchu tayi tare da mik'ewa ta Ruga cikin tana tsallan murna nan ta kira Aunty Zey ta mata albishir yaya Ya amince..

A nan take MD ya kira Wani Abokinshi dayake lecturar makarantar ta Cikin waya yayi mishi bayanin komai take ya ce Ai ba matsala tunda ta samu registration Banki kawai za Aje ayi"

PA d'inshi Ya kira Tare da sanyashi yaje yayiwa Chuchu registration saida yaga ya gama yi mata komai tukwana Ammy ce ta Kalleshi da damuwa a fuskarta ta ce.

"Baba na wai ya maganar bincike game da kisan mahaifinku naga Har yanzu bakayi wani Abu ba yaci ace angano kowaye yayi mana Wannan d'anyen Aikin"

"numfashi Ya fesar tare da cewa " Insha Allahu Mamy Gaskiya zatayi halinta inaji a jikina nan kusa akwai abun al'ajabin da zaizo bada jimawa ba akwai shirin da nake akan Lamarin "

Goge hawayen da ya zubo mata Ammy tayi tare da cewa"Allah dai ya Toni.Asirin ko suwaye sukayi mana wannan d'anyen aikin insha Allahu bazasu gama da duniya lafiya ba Sannan asirinsu saiya tono"

"Ameeeen MD ya fad'a tare da mik'ewa zai shiga Bedroom d'inshi dake gidan " da mamaki ammy ta Kalleshi ta ce "Ina kuma zaka Bayan Matarka na gari"......โœ๐Ÿฟ

*Domin magana da marubuciyar 07026166536*

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ๐Ÿ‘ฏโ€โ™€๏ธ๐Ÿ‘Ž๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡*


1, *MU GANI A ฦ˜ASA...*๐Ÿ”ฅ
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ฦ˜WAI..*๐Ÿฅš
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*๐Ÿ’ฅ
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*๐ŸŒŽ
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huษ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ษ—aya N300

*DOMIN TURA KUฦŠIN KAI TSAYE*๐Ÿ‘‡

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya๐Ÿ‘‡

0810 433 5144

Masu tura katin MTN๐Ÿ‘‡

0814 179 9224

ฦณan ฦ˜asar Niger zasu tura nasu anan.๐Ÿ‘‡

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huษ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ษ—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ๐Ÿ”ฅ๐Ÿฅš๐Ÿ’ฅ๐ŸŒŽ๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ



_*Miss Hajo ce*_๐Ÿค™๐Ÿฟ
[8/26, 20:35] โค๏ธโค๏ธโค๏ธ: ๐Ÿ’‘ *AUREN WATA TARA* ๐Ÿ‘จโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ

MALLAKAR

*Hajara L Sadeq*

*_TEAM GAWURTATTU BIYAR_*

๐Ÿ…ฟ๏ธ.........*15 & 16*


Ta na gidansu Ammy"tsaki Ammy taja tare da cewa "Allah ya kyauta " D'an murmushin gefen baki yayi tare da girgiza kai ya wuce ciki.



"Kwance take saman bed din Dakinsu ta na chat da Hafiz d'inta ya na bata labarin abun Dariya labarai masu sanya nishad'i sosai takejin dad'in chat d'in " Asmy ce da ke Dafa musu indomie a k'aramun gas d'insu ta ce "

"Uhm Manya chat yayi dad'i sai Murmushi ake "

"Kede bari wani labari ne ya Hafiz yake bani na ban Dariya" ta na sauke indomie d'in Asmy ta ce.

"Ai naga alama kam Sauko muci kafin ta huce "

kashe datar tayi tare da Saukowa nan suka faracin indomie d'in kasancewar dare ne.

"suna cikin ci y'ar d'akin su zaituna ta dawo K'arewa shigarta kallo Zarah tayi taci uban attachment ta sanya matsatsun kaya girgiza kai tayi tare da Cigaba da abunda take Dan ta lura yarinyar ba tarbiya gareta ba hakan yasa ko maganar kirki bata had'asu inba Sannu ba .


Sannu tayi musu Zarah ta amsa da yawwa " Asmy ce ma dayake suna Dan mutunci suka Dan tab'a Hira yayinda Zarah tayi kwanciyar ta dan gobe tun 8 suke da lectures .


Washegari tunda safe ta shirya 7:40 tayi mata a class saboda 8 suke da lectures Bayan lecturer d'insu ya fita Mikewa tayi tare da fitowa jikin wani block ta zauna tare da fiddo hand out d'inta ta fara Duba abubuwan da akayi musu sosai.

Sallama taji anyi mata batare da ta d'agoba ta amsa "zan iya zama Malama Zarah " Dagowa tayi tare da Kallonshi class mate d'insu ne amma tayi mamakin yanda yasan sunanta "

"Matsa masa tayi tare da cewa zaka iya zama mana" Bayan ya zauna Har lokacin karatunta take "cike da burgewa ya ce


" Gaskiya Malama Zarah kin burgeni wlh Tunda kika shigo makarantar nan na lura da kwazo da nutsuwarki Da yawan dalibai ba karatu ke.kawosu ba makaranta amma ke yanda kike dagewa yasanya nayi sha'awar Ko zakiyi abota dani Dan nima na k'aru saboda course d'inmu d'aya kuma math tana bani wahala sosai "

Murmushi Zarah tayi masa tare da kallonta ta lura yana da nutsuwa daga ganinsa kasan d'an Babban gidane ta ce "Badamuwa Allah sa mu karu da juna Saidai bansan sunan malamin nawa ba "

Cikin barkwanci ya ce "Ah dalibinki dai ai kece malamar sunana Yusuf muna zaune a garin Abuja tare da iyaye na karatu ya kawoni Zaria bansan kowaba"

"Ah kace Babana ne Saidai na kiraka da Baba " Dariya Yusuf yayi ya ce "Wow kice da y'ata nake tare Gaskiya nayi sa'ar haihuwar wannan santaleliyar d'iya Kinga dole ayimun biyayya Sannan Abban na zaki dinga Cemun ba Baba ba "

Duk yanda Zarah taso ta fusge saida ya sanyata Dariya ta ce "Eh Gaskiya ne Abba na Amma naga Abban nawa akwai iyayi da surutu fa "

Dariya yayi tare da bude book dinsa ya ce "Wlh daughter karatun da akayi yau kwata kwata bangane ba idan kin gane ki koyamun please"

โ€œbari na duba naga ko zan iya ta fad'a ta na amsa tare da Fara gwada masa dalla_dalla kamar ita ce lecturar sosai Yusuf ya gane fiye da yanda Malam ma ya koya a aji shi kanshi ya sake da baiwar kokari irin na Zarah gashi dai tare aka koya musu amma saika rantse malamin ma a Wajenta ya koya.


Saida ta gama koya masa komai "wow amma daughter nagode Wlh daga yau kinzama malamata ki godewa Allah yayi miki baiwar da ba kowa ya sameta ba Kyau Ilimi tarbiya uwa uba addini "

"Muje dai yanzu class za a shiga wata lectures ba surutun ba Abba na" ta fad'a tana Mikewa Shima Mikewa yayi yana Dariya tare da Amsar jakar dake hannunta "wara idanu tayi ta ce .


" so kake ace y'a ta sanya uba rik'e jaka ai sai a sanyamu a news "Shima dariyar yayi tare da amsar jakar ya ce " Kinga sai muyi suna yanda za ayi ta zancenmu muzama cele".

Har suka isa Class din suna Hirar barkwanci duk miskilancin Zarah har mamaki nayi yanda ta sakarwa Yusuf kodan ance Gamon jini daban yake.

Da suka gama lecture ma tare suka fito Inda sukaje capteria sukaci abinci kafin Zarah ta wuce hostel Bayan ya amshi numberta.

Shakuwa ce da abokantaka ta shiga tsakanin Zarah da Yusuf yazama closed fried d'inta Asmy har mamaki ta ke yanda Zarah ta sakarwa Yusuf fuska duk sanda bai gane wani Abu ba ita take zaunawa ta fahimtar dashi sosai yake amfanuwa da Zarah.

Cikin sati guda da Fara lecture a makarantar har amfara sanin Zarah saboda kokarinta Inda tayi wasu kawaye su biyu hibba da Jamila suma yabawa da tarbiyarsu ta sanya Zarah fara abuta dasu amma fa ba wai Chan ba saboda Har yanzu miskilancin ta ya na nan na Rashin son magana idan y'an maganar sukazo saikayi mamakin yanda take magana .

A yanzu Hankalinta kwance yake Hartama fara mancewa da su Mama Rabi Saidai tunanin babanta da take.

Suna waya da Hafiz Ya ce "Dear wai bazakije ku bud'e account ba Yaci ace kun bud'e ko Dan saboda scholarship sannan idan za ayi muku aike fa account yafi sauki akan Sai an Aiko muku"

"A rufda cikin da take a kwance ta ce " To ya Hafiz Insha Allahu gobe Monday sai muje mu bud'e ko"

"Yawwa matas Shiyasa nake sonki gobe kuje ku bud'e Ki bud'e a access "

"To ta fad'a tare da cewa gashi ba musan ko ina ba bamu tab'a fita ba "

"Ina abokin naki da kike bani labari Abba ko to shi zai iya sani kice ya rakaki "

"To " ta fad'a sun tab'a Hira Kad'an kafin ta kashe wayar a yanzu Hafiz ya Riga ya fara zama wani bangare na jikinta tun bata sonshi yanzu har taji ta fara sonshi saboda soyayya da kulawa da yake nuna mata.

Washegari Bayan fitowarsu daga lecture suka shirya Fita domin Suje su bud'e account around 1 suka tafi Yusuf yayi musu rakiya Napep suka hau su Ukku Inda shi Yusuf ya hau gaba.

Nan napep d'insu ta fara tafiya Yusuf ne ya jiyo cikin barkwanci ya ce "Daugher Kinga kuwa Yanda kikayi kyau na jima banga macen da hijab ke yiwa kyau kamarki ba ked'in ta musamman ce fa "

"Dariya tayi tare da cewa " baka rabo da barkwanci Abba na Kana uba amma ka maida y'ar jikarka"

"Y'ar Dariya yayi ya ce " Ai Gaskiya Ce dole a fad'a y'artawa ta daban ce Shiyasa idan na tashi Aurar da ita mutum na daban zan aurawa saboda ked'in Matar manya ce ba yara ba wlh daughter "


"Murmushi tayi tare da girgiza kai ta ce " kadai kalli gabanka karka fad'i kaja mana "

Bayan Asmy ta gama waya Ta ce "Ai Gaskiya ka fad'a ko Abbanmu"Dariya yayi tare da cewa " Eh mana Bestynmu "nan suka cigaba da hirarsu su Ukku yawaici duk ta barkwanci ce.

Sunzo daidai round din da zasubi ya kaisu Banki Sukaji mai napep d'in ya tsaya " Abun hankalinsu duk yana dumin da suke "Asmy ta ce Lafiya Malam yanaga ka tsaya"

Mai napep d'in ya ce "Kuyi hakuri Hajiya Inajin wani Babban mutum ne zai wuce a wajen shiyasa chunkoso yayi yawa sai motocinsu sun gama wucewa tukwana a bamu hanya".

Cikin jin Haushi Zarah ta ce " Yanzu haka zamuyi ta tsayuwa a titi saboda kawai wani zai wuce dan fin arziki za a tsaida mu".

"Kuyi hakuri Hajiya ya muka iya " Daidai lokacin da wulfa_wulfam motocin suka fara gittawa ta wajen "Kallon motocin da tunda uwarta ta haifeta Bata tab'a gani ba Asmy ta gani wara idanu tayi tare da cewa " Kan uban Chan waiko shugaban k'asane ya shigo garin?

Yusuf ne dake gaba ya ce "Kan ube Wlh MD ne ya shigo garin nan Chab dole a tsaida mutane Innalillahi inama zan gansa ido da ido MD a Zaria to me ya kawosa"


"Zarah ce ta ja tsaki Ta ce " Shi waye da za ace sabodashi za a tsaida mutane saboda shi yanzu fa Banki suna gab da tashi ta fad'a ta na duba Agogon hannunta "

"Yusuf ya jiwo ya ce "

"Wai kina nufin bakisan MD ba kina Nigeria Amma baki Kallon Television da labarai ko? "

Tab'e zarah tayi ta ce "nidai ban wani sansa ba Asmy ma ta ce nima kam "


Yusuf sarkin bada labari juyowa yayi yare da cewa aiko yau zan baku labarinshi saboda ni fans dinsa ne ina karanta tarihinshi sosai".

wani shahararren matashin mai kud'i ne iyayenshi suna zaune a garin Kaduna Mahaifiyarshi asalinta y'ar India ce a

2 Comments On AUREN WATA TARA
avatar
mubarak-nasir

11 months ago

Reply

Woow gaskiya yayi

avatar
mubarak-nasir

11 months ago

Reply

Abun yayi

Please Login or Register in order to submit comment