Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kallonta , na tanadar miki abubuwa kala kala agidana daidai nake da zamaninki tashi ki fita ki bani waje harta kai kofa yace saura kuma nagara ganin wannan mai wuya kamar zariyar wandon kiga abunda zan miki

Ta fice da gudu yace marar kunya na ɗauka zakimin ne wlh jikinki yabaki bayani yanzun nan


A hospital kuwa adeel ya hana shuhada saqat yau kwata kwata ma ya hanata mgn da likitoci maza har aka fara qananun mgn anya babu abinda yake tsakanin dr adeel da dr shuhada kuwa? Wasu suce anya kuwa kanwarsa ce kawai, wasu kuma suce soyayya suke kowa da abinda yke fadi



"""""""""""""Agurguje bayan sati biyu an tsaida bikinsu adeel
Binayya kuwa an tattarata ankaita niger acan za adaura nata auren sbd haukan da tadingayi harda bin shuhada da wuka ranar da kyar adeel ya murdeta ya kwace wukar shiyasa kawu baba yace a tattarata ta koma niger ayi bikinta acan

Shirya shirya akeyi sosai dan ba ataba aure dayawa haka ba abbu abbi abba sun tayarwa yaransu gidaje masu rai da lpy nagani na fada domin an zubar da wani abu mai suna kudi acan wajan zaria road kafin g,r,a


Adeel zaune shida fauzan yana basa lbrn yanda sukayi da shuhada ranar akan tanaso ayi asibiti a kauyensu adeel yace to ba damuwa nima abbi ya min mgn fauzan yace eh nina gayawa abbin ai adeel yace eh amma yace abari agama hidimar bikin nan tukunna fauzan yace to ba damuwa



Shuhada kwance suna waya da hindu sai zolayarta hindu keyi

Amarya amarya ba gashi ba dama ai na fada miki

Shuhada tace hummm hindu wlh har yau baice yana sona ba sai masifar bani umarni idan yaganni ina mgn da wani ko a asibiti ne sunana sorry hindu ta kwashe da dry tace shi kuma irin tasa salon soyayyar kenan amma dole ya furta damu yake zancan zai shigo hannunmu ke bari ma kiji yana fadi yana kuka
Shuhada ta kwashe da dry tace lallai ma hindu yaushe zakuzo hindu tace sai nan da sati daya
Ok Allah ya kaimu hira suka cigaba da yi hindu tana ɗaura shuhada akan network yadda zatayi da adeel


"""""""""


Har yau raeena batayiwa raeesa mgn
Raeena tadawo daga skll ta samu raeesa kwance dan bata zuwa ko ina jb ya hanata zuwa aikin ma duk ta zama wata shuru shuru da ita abin tausayi

Kallo daya raeena tayi mata ta kauda kanta gefe raeesa ta taso ta kama hannunta tace sister gaba kikeyi dani ?kiyi hakuri wlh banajin dadin shareni da kikeyi ta karasa hawaye na zuba a idonta
Itama raeenan hawaye ta share sannan ta rungumeta tace yawuce ni ba gaba nakeyi dake ba so nake ki fahimci gaskiya amma nima ba inajin dadin hakan bane


Tun daga lkc raeena suka dawo daidai da yar uwarta amma raeesa mgn ma yanzu wahala yake bata

Ammy ta dauko mai gyaran jiki daga maiduguri sosai ake musu gyara barin ma shuhada tawani qara kyau da qiba sai sheqi takeyi tana maiqo
Ranar zasuje asibiti burleey ganin irin kyawun da tayi yace mata ta koma tasa hijabi haka ta juya taje tasa hijab din ta fito yace ta koma tasa liqab tace bata dashi yace to daga yau babu ita babu zuwa aiki sannan ya fice yabarta tsaye anan kamar tayi kuka ko da ta koma cikin gida ammy tace ah baku tafin ba kuma ?shuhada ta sunkuyar da kai kasa dan yanzu kunyar ammy takeyi kamar me tace ammy yace bazanje ba
Ammy tace eh dama yakamata kam yanzu ki hkr da zuwa asibityn nan tunda amaryace likita matar likita
Shuhada tayi murmushi tana sosa ƙeya cike da kunya ta haura sama ammy ta girgiza kai tana dry dan ta fahimci yanzu shuhada bata sake da ita kamar da


********


Yau saura sati daya biki ayau ne kuma su anty haula da gwaggo mairo aminiyar kwarai hindu suka diro garin kaduna tun daga gate hindu take yaba gidan numfashinta bai tsaya ba saida suka shiga cikin gidan

Su gwaggo mairo da anty haula a family house aka tarbesu an karramasu sosai hajiya kaka sai jan gwaggo mairo takeyi da hira





*******


😞🤒🤒 kun matsa gashi nan to





Comments



An

Share


By mmn ahlan✍🏻[10/1, 6:18 AM] Zarahh: 🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠


*ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻

*ZAHRA ABDUL*( _momyn ahlan_)


( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

__________________
*masha Allah alhamdulillah ina tayaki murnan kammala book dinki _rasheedat usman (ummu nasma)_ wato _sara da sassaka_ darasin dake cknta Allah yabamu ikon amfani da ita kuskurenki kuma Allah ya yafe miki up up up aminiyata Allah yaqara basira da daukaka yasa kigama mn indo abirni lpy*
__________________
*_jinjina da gdy ga masoyana na nesa dana kusa da wanda na nasani da wanda bansani ba wannan pg din na kune kuyi yadda kukeso dashi ina muku ftn Alkhairi yan grp din SHUHADA FANS inayinku ina sonku barin ma masu suburbudomin cmmnts_*

Na gaisheku kamar haka

_DOTER SURAYYA_
_ANTYN AHLAN_
_TEEMAH FASHION_
_DR HERPSERT_
_UMMU FU'AD_
_MAMAN ABDUL🙊_
_ITZ DEEJEH_
_MOM TWINS_
_MRS FAROOQ_
_UMMU BILAL_
_MUNAYAH_
_HABIBTYNA احلم_
_MMN HAFSAT /BB_
_UMMYN FADEE_
_NAJA YARKWARAI_
_UMMAKULSUM_
_AMATULLAH_
_MAMANASMEE44_
_KHADIJA IBRAHIM_
_XEA SAEED_
_DEAR FATIMA BINTU SAGIR_
_CAPPA_
_MAMAN ISMAEEL_
_HIDAYA KABIR_
_MAMAN MUSHPIQ_
_NANAH XANNAH_
_Kanwata NAFEESAH_
_AYSHAT IBRAHIM_
"""""""""""""""
*mamies luv fans club wlh gabaki dayanku inayinku ina sonku ina qaunar ku*

*_MASOYANA ALLAH YABARMU TARE SON SO NAKE MUKU DOMIN ALLAH_*💘
__________________


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


*P*...3⃣5⃣↪3⃣6⃣


Family house ancika sosai ba ma tsaka tsinke sbd jama'a wasu ma kuma basu zo ba sun tsaya a niger tunda acan za ayi bikin binayya


Shuhada hindu raeena raeesa suna zaune adaki ammy ta shigo da babbar trey tace oya maza maza sauko kuzo ku cinyesa duka shuhada ce ta fara tashi kafin raeesa ,raeena tace ammy nifa wlh nagaji da cin wannan abun ta fada tana yatsine fuska ,ammy tace ungo nan naki maza zaune kafin na makeki hindu tayi dry tace ammy zataci ai dolenta ma, ammy itama dryn tayi tace yawwa hindu idan basu ciba ki ɗura musu ,hindu tace to ammy angama
Ammy ta fice suka zauna dukkansu suna ci suna dan taba hira sama sama amma banda raeesa dan ta koma silent kwata kwata bata son mgn yanzu


Bayan sun gama suna zaune shuhada ta tashi ta dauki hijabi,hindu tace ina zakije ?.
Tace zanje wajan zeeyadat ne akwai abinda nakeso ta turamin ne, nayi mata mgn ta whatsapp tun jiya bata cemin komai ba ,bari naje yanzu zan dawo ,hindu tace da dai kin hakura kinga fa waje akwai maza bai kamata ki fita ba wlh ,yatsine fuska tayi ta tabe baki kafin tace aidai naga ba a daura auren ba balle a qudunduneni ,eh amma ai za adaura tunda yau saura kwana biyar dan Allah shuhada karki fita ,hijab din tasa tace wlh saina fita harta kai bakin kofa hindu tace Allah yasa kina fita ki hadu da adeel, cikin gatse tace ameeen

Raeesa ta girgiza kai dan rabonta da fita idan bata manta ba tun ranar da aka daura mata wannan kaddararran auren
Raeena tace ai kuwa harna tausaya mata idan suka hadu hindu ta kwashe da dry, nan suka cigaba da hira da raeena ,raeesa kuma kwanciya tayi ta lumshe ido data fara tunanin khalid zatayi sauri ta bude ido tace astagfirullah


""""""""

Shuhada tana fita ta hango jama'a maza birjik gashi gabaki daya sai kallo ya koma ganta duk da hijabinta har kasa ne amma fuskarta tana haskawa
Ido yamata yawa hakan yasa jikinta fara bari da anganta za ace ga matar adeel can


tana zuwa bakin gate kenan ana budewa burleey gate ya danno motarsa ya hangota tana tafiya ahankali wani burki taci sakamakon tozali dashi da tayi yawani hade fuska tamau mazan wajan ya kalla duk da yan uwansa ne amma saida idonsa ta rufe har wani zufa yakeji amadadin yashiga yayi parking sai ya koma da baya da motar yayi parking dinta awaje ya fito yana taku cike da izza wanda dakagani kasan azuciye yake ranshi bace ko kunyar mutanen wajan baiji ba dan idonsa ya rufe so yake ya tambayeta uban abinda ya fito da ita mai gadi ya kalla yace rufe gate din nafasa shiga sannan ya fizgi hannun shuhada wacce take tsaye kamar bishiyar da aka dasata


Waje yayi da ita inda bar motarsa ya bude yasakata sannan ya zagaya shima ya shiga


_gidan uban wa zakije bance karna sake ganinki awaje ba dan iskanci da wulaqanci kin kama hanya kinfito sai kyetarawa kikeyi cikin maza suna binki da kallo suna qare miki kallo kema harda canza kalar tafiya sai kace tsutsa kina qara rausayawa agabansu ? Duk sauran suna daki a zaune amma shine ke kika fito dan kin rainani bakijin mgnta ban isa nace ga abunda nakeso kibi ba ko *Ashshuhada*,ina zakije nace ?ya fada afusace_

Shuhada da numfashinta ke barazanar barin gangar jikinta sbd tsoron daya dabaibaiyeta tace am..na..na..um...dama ...damaa. ...inaso ne naje..wajen..zeeyadat ta turamin abu ne, bansan da maza da yawa haka ba da ban fito ba kayi hakuri zan koma yanzu

_ok baki san da maza dayawa haka ba yayi kyau_

Motar ya figa da karfi basu zarce ko ina ba sai kasuwa yace ta zauna a mota karta sake ta fita tace to yadan jima kadan kafin yadawo da leda ahannunsa yabata yace gashi maza kisaka yanzun nan karba tayi ta bude ledar taga liqab da safa turo baki gaba tayi tace _haba dan Allah yaya burleey ina kuma zanje da liqab da safa_ taqara ashagwabe fuska

Da sauri ya juye yana kallonta yace what yaya wane kikace?

Da sauri itama ta riqe bakinta tashiga girgiza kai alamun ba haka take son fadi ba jikinta na rawa tace dan Allah yaya adeel kayi hakuri ba burleey nake son cewa ba subutar baki ne plss kamar zatayi kuka

Ya wani hade rai amma azahirin gaskiya sunan yamasa dadi abakinta kamar yace ta sake fadi amma kuma saiya fuske yaja motar suka koma gida saida tasa liqab da safan tukunna ya rakota har upstairs
Bai damu da mutanen wajan ba sai tsokanarsa sukeyi amma kasancewar sunsan halinsa na kyaliya da rashin son mgn shiyasa basu damu daya tanka ba


Ko da ya koma part dinsa yasamu su sadam fauzan jb da mashkur suna zaune suna tattaunawa amma banda jb dake amfanin da system
Fauzan yace yauwa adeel kawu baba yace babu wani bidi'ar da za'ayi da an daura aure za ayi walima shikenan ,adeel yayi tsaki to ina ruwana nifa duk wannan abun ba damuna yayi ba dama ni ba gayyar hayaniya nake so ba ,so that i don't care,

Nan suka cigaba da tattaunawar su


Shuhada tana shiga daki hindu ta hau dry tace Allah yaqara saida nace miki karki fita amma kikace sai kin fita gashi yanzu kindawo ninja raeena ma ta hau dry itama tace antynmu matar yayanmu gasky kalar love dinku yana burgeni ku naku daban ne dan Allah ku koyamin nadinga yiwa yaya sadam

Shuhada tace wlh wannan yayan naku au yayanmu karkije ki fada masa naboni gashi ni bai barni naje inda nake son zuwa ba yawani kaini kasuwa ya siyamin liqab ko waya nuna masa wajan oho ,hindu datake dry kamar ranta tace haba tunda yaje kasuwa ai zaiyi tambaya yasamu ta tabe baki ta dauki sha'ib tace ina shuhad? Hindu tace yana can family house dinku yasamu yara yan uwansa suna wasa

******
Duk wani shirye shirye da akeyiwa ya' idan za akaita gidan miji babu wanda ba ayiwa amaren nan ba, gida angama jere babu abinda ba asaka ba
Ammy momma mamy sun gyara yaransu ba kadan ba ayayinda akayi musu dinkin fitar biki
Tun ana saura kwana uku biki suka fara shan makeup
Jikinsu yayi bulbul barinma shuhada har wani maiqo maiqo takeyi


""""""""""""""""""


Ranar daurin aure masha Allah


Haka aka dinga daura aure dama shi jb an riga da an daura nasa dan haka yau saida aka daura na adeel shida shuhadarsa kafin aka daura na sadam da raeena sai fauzan da zeeyadat , haka aka dinga lissafin familyn jibril burka su goma sha uku jama'a sai barka ake musu ana tayasu murna da ganin kokarin wannan family dan sun nuna bajinta auren yara dayawa haka


Adeel yau ji yake babu wanda ya fisa duk da fuskarsa baya dry amma daka gansa kasan yana cikin farin ciki marar misaltuwa


Da yamma akayi walima inda aka gayyato malama juwairiyya isa tazo tayiwa su amare wa'azi akan haqqin miji akan matarsa da kuma haqqin mata akan miji


_yaku yan uwana mata idan har kukaji ance miji ana nufin majibancin lamarinki na rayuwa gabaki daya aljannarki tana ƙasar tafin kafarsa saiya ɗaga miki zaki samu dama wucewa mata muji tsoron Allah yar uwata aduk lkcn da miji yake miki mgn ki kasance mai duqar da kai agaresa karki daga masa murya ,yar uwa idan mijinki ya miki laifi ki kasance mai yafiya agaresa ki kasance mai yiwa mijinki adduah tare da taimakon sa yar uwa karki dinga yiwa mijinki rashin kunya yace kiyi kice bazakiyi ba sannan yace abari kice bazan bari ba hakan babban hatsarine ga neman aljannarki karku manta annabi S,A,W ) yamana bayani sosai akan babbar matsayin da miji yake dashi yamana bayani akan haqqin miji yan uwa muji tsoron Allah mudaina daukar aure abun wasa da kashe sha'awa aure rahma ce aure sunnar ma'aikin Allah ne aure kwanciyar hankali ne ,amma hakan bazata samu ba sai kin kasance mai hakuri ladabi da biyayya juriya da tawakkali tsabta iya girki iya kalamai masu dadi karki fiye yawan fushi_

Sosai malama juwairiyya ta sanyaya jikin amaren nan, ai kuwa suka dinga kuka barin ma raeesa lallai zataje tabawa yaya jb hakuri dan karta shiga wuta



Sai magriba aka watse

Da daddare aka kwashesu aka kaisu family house nan yan uwa da abokan arziki aka dinga yimusu nasiha
Kafin aka kaisu dakin kawu baba lkcn ya gama yiwa mazan nasiha nan yayiwa matan kafin yace afita abar masa shuhada

Bayan anfita kawu baba ya dafa kanta shuhada kuka takeyi sosai tarasa gane farinciki takeyi ne ko kuma akasin haka iyayenta kawai take tunawa ahalin yanzu addua take musu aranta

Shuhada !!! Kawu baba ya kirata a sanyaye ckn kuka ta amsa yace alhamdulillah haqiqanin gasky shuhada tun ranar da kika shigo familyna na maidake ckn ahalina fatan zaki zauna da adeel har abada sannan ban zaba miki abunda zai cutar dake ba?

Ckn kuka tace kunmin komai arayuwa kun maidani mutum yanzu kuma kun sake haɗani ackn ku ni kuwa me zance daku wanda yawuce Allah ya sanya ku agidan aljanna


Kawu baba yace masha Allah ,Allah yabaku zaman lpy da zuri'a dayyiba
Tana kuka a kunyace ta amsa da ameeen

Bayan ta fito adakin kawu baba gwaggo mairo da hajiya kaka ma suka yimata nasiha sosai anty haula ma ba abarta abaya ba

Wata yar uwarsu wacce tazo daga niyar mai suna anty suwaiba taja shuhada nan tadinga tsorata ta, kinga shuhada saikin daure gaki yarinya ce kuma wlh daga ganin adeel ba qaramin jarababbe bane zaki sha wuya maganganu sosai tadinga fada mata har saida aka fara kiran shuhadar kafin ta rakota hajiya kaka ta hau sababi tana cewa wananan wani irin iskaci ne duk antafi da sauran amaren amma anbarta burleey dallah azo afice ,suna fita kuwa hajiya kaka ta hau kuka dan tasan zasuyi kewarsu tunda ba unguwa daya bane




Masha Allah ko wacce an ajiyeta acikin gidanta

Hindu ta kalli shuhada tace dan Allah kibar wannan kukan ya isa haka yakamata ki godewa Allah lkc daya rayuwarki ta canza yanzu ki kalli wannan gdn duk girmanta da fadinta naki ne mai hakuri shike da riba kibi mijinki kiyi masa biyayya sosai hindu tadinga bawa shuhada shawara ,amma ina anty suwaiba ta dagula mata lissafi

Har wajen karfe goma suna tare hindu tana lallashinta dan jitake ma kamar ba itaba ,wayar hindu yayi ruri taga mijinta ne dauka tayi tace ok to gani nan fitowa , ta tashi ta dauki mayafinta da sha'ib wanda yayi bacci dama shi shuhad yana tare da gwaggo mairo

Shuhada ta riqe hindu tana kuka dan Allah hindu karki tafi kibarni,hindu ta hau dry tace eh lallaima kowa da haka aka tafi aka barsa yarinya sai hakuri dan yau inaji saki qara tabbatarwa eh lallai sunan mijinki burleey ta kwashe da dry tace saida safe ta fice abunta aka bar shuhada ita kadai sai tunane tunane takeyi
Yau itace tayi aure sannan acikin wannan gida tashi tayi sannan tayi alwala tayi sallah ta jima tana addua tare da gdy ga Allah da kuma iyayenta sannan ta canza kaya ta kwanta abunta

Can wajan karfe sha biyu saura taji motsinsa take gabanta ya fadi ta tashi da sauri ta diro daga gadon neman wajan boya take ,kafin ta hango ƙarƙashin gadonta wanda yaji flower ta shige. Da sallama dauke abakinsa ya shigo dakin amma wayam bai ganta baiyi tunanin komai ba ya ajiye ledojin da ya shigo dasu yafice dan a tunaninsa tana toilet

Saida yaje ya watsa ruwa ya canza kaya zuwa kayan bacci kafin yadawo dakin nan ma bai ganta ba toilet din yaje ya bude nan ma bata nan hankalinsa ne ya tashi yaje har wajen mai gadi yana tambayarsa dan ta duba duka dakunan bata nan ,mai gadi ya tabbatar masa eh lallai fa tana ciki bata fito ba ,ciki ya koma ya zauna adaki harya gaji ya tashi ya koma dakinsa ya kwanta yana tunanin inda ta boye
Shuhada kuwa yana fita ta dauki pillow ta koma ta kwanta akasan gadon


"""""""""""

Bangaren raeesa ma haka jb ya kawo mata ledojin kaza yasata agaba taci tadinga lallabata ita kuma ta kasa sakewa dashi gashi kunyarsa ma takeji tana so tabasa hkr amma takasa
Shi kuma jb umarnin mamy yake bi domin mamy tayi masa tatass akan raeesa shiyasa yayi alkawari zai kula da ita ko da tayi masa rashin kunya bazai mata komai ba sabanin da da yayi alkawarin saiya ballata idan tayi masa abun da ba haka ba


""""""""

Ta bangaren sauran amare kuwa komai yayi daidai

Allah ya qara bada zaman lpy

Da washe gari haka shuhada suka dinga wasan boya ita da adeel har ya fitan yabar gidan bai sakata a idonsa ba

Su hindu sunzo nan suke cemata sunzo mata sallamane ta hau kuka anty haula tace kee bana son shirme miye kuma abin kuka,hindu taja shuhada suka shiga bedroom dinta tace ke yanaga haka? Ckin rashin fahimta shuhada tace me fa me kika gani?
Hindu tace naga tafiyarki bai canza bane kodai baki bada kai bori yahau bane?
Mtswww wlh hindu bansan lkcn da kika zama marar kunya ba to ma ina ruwanki?
Hindu ta kyalkyale da dry tace to ai gwanda nasan dalili keda raeesa akwai ayar tambaya akanku domin duk saida muka biye gidajensu kafin mukazo nan raeena ma kam bata iya miqewa tana can zazzabi yakamata abin tausayi ,ai nan shuhada tasake tsorota, afili tace to al'mufuffuki ni jaruma ce shiyasa , anty haula tahau kiran hindu akan ta fito su kama hanya luqman yana jiransu
Har waje shuhada ta rakosu suna dan taba hira suna dry kamar daga sama ta hangosa saida gabanta ya fadi ganin kallon da yake mata ,yana qarasowa ya miqawa mijin hindu hannu suka gaisa ya gaishe da anty haula suka gaisa da hindu kafin ya kalleta yace koma kisa hijabi da liqabi anty haula da sauri ta shige mota tana cewa to suwaye agidan bayanku hindu tace haba ango kwantar da hankalinka yanzu zamu tafi , yadan saki murmushin gefen baki batare da yayi mgn ba hindu tace to amarya da ango mun wuce sai mun zo suna insha Allah adeel yace ok mun gode sosai Allah ya kiyaye hanya ,ya juya ya watse mata harara da gudu tayi ckn parlorn kafin ta haura sama tashiga daki harya shigo

Ganinsa yasa hanjin cikinta suka kaɗa ahankali ta juya zata hau saman ..yace ina abinci na ,juyowa tai tace yana kan dinning su hindu ne suka kawo daga family house ,,,,,ok ni kikeso nayi serving din kaina ?girgiza kai tayi sannan ta dawo ta wuce dinning area ta fara zuba masa abincin yana zaune a parlor bai taso ba harta gama haɗa masa komai tace nagama ,batare da ya ɗago ba yace kawo min nan daukowa tayi tazo ta jere masa agabansa ta tashi zata tafi....dawo ki zauna ,,abinda ya furta kenan ,dawowa tayi ta zauna tana turo baki ,kinci abincin ne ke? Tace aa ni sai anjima zanci
What sai anjima mtsww tashi yayi yaje ya dauko mata spoon yace maza zonan muci , babu yanda ta iya haka tazo ta zauna sukaci tare duk atakure take dan takasa sakewa dashi har suka gama

Ta koma dakinta shima bai damu daya bita ba tunda yaga gudunsa takeyi



Bayan biki da sati daya sukaje family house ranar wata jumma'a ai kuwa da suka hadu suka dinga murnan ganin juna hajiya kaka sai nan nan takeyi dasu sbd farincikin ganinsu kawu baba ma haka sai murna yakeyi babu wanda baya murna

Bayan sun gama hira a family house suka wuce gida shuhada sai kallon raeesa takeyi yadda tayi wani qiba da haske kasa hakuri raeeena tayi tace sister wannan qibar ina zaki kaita haka ? Zeeyadat tace wlh gata nan duk tafimu auki mihik tace dama mukam ba jikin garemu ba

Abin mamaki amadadin ta basu amsa saita fara kuka ,sosai hankalinsu ya tashi suka shiga tambayarta menene?
Saida ta tsagaita tukunna tafara mgn,,,, wlh sister's duk yadda nake tsoron auren nan ashe ba haka bane babu abinda yaya jb yakemin banda zallar. Kula dani dayakeyi idan banci abinci ba shima bazai ciba danayi motsi zai cemin me nakeso nan tadinga basu lbr abun kirki da yake mata zeeyadat ta kwashe da dry tace tofa to yanzu miye abun kuka? Kodai kin fara son yayanmu ne ?

Raeesa tace eh inajin wani abu ajikina dangane dashi idan na kwanta bacci yanzu mafarkinsa nakeyi sabanin da da nake mafarkin khalid

Shukra tace to ai mai sauki ne wannan soyayya ya kamaki,,,,, shikenan saiki rungumi mijinki ku zauna lpy

Raeesa ta girgiza kai tace baya shiga hidimata ,,shuhada tace kmr ya baya shiga hidimarki ?
Hawaye ta goge tace sbd ikirarin dana dingayi bana sonsa shiyasa yace babu ruwansa dani,,zeeyadat tace ai ga irinta nan duk kece kika jawo yaya jb yake miki abinda yake miki dabadin rainasa da kikayi ba wlh daba haka ba ,,,shukra tace haba zeeyadat yanzu gyara mukeso kidaina janyo abinda ya wuce mu fuskanci gaba ,,,kallo shuhada sukayi sannan raeena tace anty shuhada plss kinga ke matar yayanmu ce ki bata shawara ,,, shuhada azuciyarta tace tab wai nabata shawara nima akaran kaina ina bukatar shawaran da har gobe akasan gado nake kwana

Amma afili tace daki daya kuke kwana? Raeesa ta girgiza kai shuhada harda gyara zama ita gata adole matar yaya tace to yau ki je dakinsa ki kwana duk korar da zai miki karki tafi waima ke ba mace bace ai ba sai ance miki komai ba suka hau dry
Mihik tace anty shuhada anya ba ciki ne dake ba ?shuhada ta zare ido tace asati dayan?

Suka hau dry suna cewa ahto abu na Allah waya sani
Shuhadan ma dry tayi tace saidai ko ku ne kuke da cki amma bani ba hira sukayi sosai kamar karsu rabu


Sai bayan sallar isha'i ko wanne miji ya dauki matarsa suka kama hanyar gida




Da misalin karfe sha daya da rabi raeesa taci wanka na daukar hankali tasa wasu arnakun kayan bacci wando da riga

Wandon da kadan ya wuce cinyarta rigar kuwa iyakar cikinta ya tsaye turarukan da mai gyara jiki ta basu sai yau ta dauko nata ta mulke jikinta dasu ta daure kitson kanta da ribom ta fito gabanta na faduwa ta dauki hanyar dakinsa bisa shawarar anty zubaida wata yar uwarsu a family house


Ahankali ta tura kofar dakin tayi sallama ckn sanyin murya da sanyin jiki
Jb dake zaune kan gado da system acinyarsa yana kallon film take gabansa ya fadi sbd turaren da tasaka mai dauke wuta, hankalisa bai gama tashi ba saida ya hangota tsaye a kofar ita bata shigo ba ita bata koma ba
Harna tsawon minti10 aransa yace wannan yarinya yau me take nufi dani ne?

Ahankali ta qaraso garesa

Please Login or Register in order to submit comment