Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk ranar da taje karyewar asirin su yadiko. Yazo to abun yakenan?

Wannan amsa duk sai mun hadu a next page

_______________




Comments


And

Share
[10/1, 6:18 AM] Zarahh: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠

*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻

*ZAHRA ABDUL* ( *m͞͞o͞͞m͞͞y͞͞n͞͞ a͞͞h͞͞l͞͞a͞͞n͞͞*)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻
*sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

*S̶O̶N̶ S̶O̶ N̶A̶K̶E̶ M̶U̶K̶U̶ M̶A̶H̶ P̶P̶L̶S̶ S̶H̶A̶R̶H̶I̶N̶ K̶U̶ Y̶A̶N̶A̶ S̶A̶N̶Y̶A̶N̶I̶ N̶I̶S̶H̶A̶D̶I̶*😘


*بسم ا لله ا لر حمن ا لر حيم*
*_________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________*


*P* ..2⃣9⃣↪3⃣0⃣


Ta kira sa ya kai sau biyar amma bai ɗaga ba har suka isa hospital tana kan kira amma yaqi ɗagawa bawai kuma bai ga kiran bane aa dan bai san number bane shiyasa yaƙi ɗagawa

Fauzan yayi parking ya juya ya kalleta yace yadai? hawaye ne ya zubo mata tace yaƙi ya ɗauki wayar fauzan ya girgiza kai ya ɗauki wayarsa ya kira sa ringing huɗu adeel ya ɗaga yasa akunne kafin fauzan yayi magana adeel yace ammy ta fada maka sako na?

Fauzan ya numfasa yace aa wani sako kuma ?ammy bata cemin komai ba, na kira ka ne nace maka shuhada tana son magana da kai tanata kiran ka baka ɗaga ba
Bai jira amsar sa ba ya miqawa shuhada wayar ya fice a motar yabata key din yace idan kun gama kika fito ki kulle motar ta ki sameni aciki , gyada masa kai tayi ba tare da tayi mgn ba sbd hawaye takeyi
Fauzan ya juya da sauri yayi cikin asibiti domin akwai abinda zaiyi

Wayar ta kara akunne tayi shuru shima yayi shuru bata san me zata ce masa ba sai ajiyar zuciya kawai take saukewa

To ma me za tace ? wannan ai rashin kirki yake son mata wai kar taje maganar ma ko tsari babu sai kace mijina ko ubana

Da kyar tayi sallama cikin zazzaƙar muryarta

_Assalamu alaykum_
Ajiyar zuciya ya sauke domin sallamar ta daki kwakwalwarsa ya kai minti uku yana jan iska kafin ya amsa
_wa'alaykissalam_
_ina wuni_
_lafiya_
Shuru ta kumayi tana zare ido shi kuma yana jira yaji me zata ce masa da kyar dai ta tattaro jarumta tace
_zanje ƙauye na harna fadawa ammy amma kace bazan je ba meyasa_?
_mtswww keee ina wasa dake ne da zan fadi umarni har zaki kirani kina tambayar ba'asi to banyi niyyar kije bane fauzan yaje yataho dasu gwaggon sai a nema musu gida a azaren amma karki sake kije_,
kamar zatayi kuka tace
_yaya fauzan bai san ƙauyen ba fa_,
_okay naji bai san ƙauyen ba amma ai ana iya masa kwatance idan kuma kin dage sai kinje to kibari kawai ku dawo sai muje tare karki kuskure kije nadai gaya miki_

Kasa magana shuhada tayi kawai ta saka masa kuka runtse idon sa burleey yayi domin yanda sautin kukan nata ya daki dodon kunnensa da kwakwalwarsa da zuciyarsa shuru yayi yana sauraron kukan nata da yaji bazai iya jurewa bane yaja dogon tsaki ya kashe wayar yana busar da iska mai zafi abakinsa tunani kuma yafara ya kirata ya lallasheta amma kuma karta gane sonta yakeyi nan ma yasake jan tsaki domin ya rasa mafita baya son kukan ta sannan kuma baya so taje

Shuhada kuwa kuka taci sosai daga baya ta share hawayenta tana cewa wlh saina tafi saidai duk abinda zai faru ya faru amma tafiya dole dan ni banga dalilin ka na cewa karna je gida ba fitowa tayi a motar ta kulle ta shige asibitin suka haɗu da sauran likitoci yan uwanta suka cigaba da aikin su na taimakon jama'a




**********

Da washe gari bayan fauzan ya gama abinda yakeyi a asibiti ya shirya zuwa kauyen tanko domin ya tambayi mijin hindu yayi masa kwatance
Shi kadai zai tafi domin burleey ya kirasa yamasa gargadin akam karya sake shuhada tabisa ko tace zata je karya tafi da ita fauzan yadinga dry yace ba damuwa yanda kace haka za ayi



Hindu ta shirya tsaf zasuyi tafiya harta fadawa mijinta kuma ya amince yace amma fa kuma fauzan yace banda shuhada hindu ta kwashe da dry tace nasani ta fadamin jiya brothern sa ne yace kar taje amma ni banga dalilinsa na hanata zuwa ba dan haka kawai ka bamu kudin mota ka kaimu tasha
Luqman yace ke momyn shuhad banson irin haka fa tunda yace kar taje to ta hakura mana
Kar yazamo matsala

Hindu tace aa wlh nidai muje kaimu tunda ai ba mijinta bane bata aure sa ba tukunna balle harta taka masa umarni ta shiga wuta kishi yakeyi tun bai furta mn kalmar so ba, ai ba haka akeyi ba
Luqman yace to maganau naji muje na kaiku amma nikam ba ruwana hindu tana dry ta kama hannun mijinta da ɗanta tace eh munji ba ruwanka


A hanya suka ɗauki shuhada luqman ya kaisu har tasha yabasu kudin mota yamusu Allah ya kiyaye hanya ya juya ya tafi

Bangaren fauzan kuwa ya nemi shuhada harya gaji bai ganta ba ya kira wayarta a kashe haka shima ya juya ya kama hanya sai kauyen tanko tunda baiyi tunanin zata tafi ba ya ɗauka tana gidan hindu ne



*********** *ƘAUYEN TANKO*



Tunda suka fara shigowa gaban shuhada ke tsananta bugawa hindu tace ina zamu tsaya gidan gwaggo mairo ko gidan anty haula ko kuma mu wuce faɗar mai gari shuhada tace duk inda muka sauka ma daidai ne

Shuhada tace amma fa har yanzu ba asami wata cigaba ba a kauyen tanko ,hindu tace gsky kam ba asamu wata cigaba ba

Ko da suka sauka a mota shuhada ta ɗauki sha'ib hindu kuma taja hannun shuhad suna tafiya jama'ar kauyen tanko kallon shuhada kawai sukeyi sun shaida hindu amma basu shaida shuhada ba samari sai lashe baki sukeyi, ita kuma yar'gidan mai gari ina ta samo balarabiya haka cewan wasu samari da yan'mata

Shuhada tsaki tayi tacewa hindu har yau dai samarin kauyen nan basu daina yiwa yan mata kallon qurillah ba
Hindu tayi dry tace yo ina kuwa zasu daina barin ma ke ai dole akalle ki

Harta yan mata ma sai sun kalli shuhada bama samari ba yadda take tafiya tana haskawa ga kyau ga ilmi

Sunata tafiya abubuwa dayawa take tunawa ji take kamar bata taba rayuwa anan ba gabaki daya komai na kanta jitake ya tsaya mata tsak, a ƙauyen tanko aka binne cibiyarta aƙauyen tanko aka binne uwa da ubanta amma sai gashi rana daya tazo tabarta wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata ,
Hindu tace shuhada dan Allah ki manta da komai ki dubi gaba, murmushi shuhada tayi tace hindu wahalar dana sha nake tunowa ni ake aikawa rafi tsakar dare ni ake kamawa a jibgeni kamar jaka hummm Allah sarki rayuwa duniya kenan mahaƙurci mawadaci ne , shakka babu ba gashi ba yanzu kinyiwa jama'ar kauyen nan zarra dan ba mai ilmi ki
Karki damu komai zaizo karshe wani abu kuma sai ranar da muka kai ki dakin burleey ta qarasa da dry

Shuhada kuwa tsoro ne ya kamata dan ita harta ma manta da yace mata wai kar taje ajiyar zuciya tayi aranta tace am so sorry burleey bazan iya jurewa ba
Saina zo hankalina zai kwanta tayi murmushi

Hindu tace inyee wato na kira sunan masoyi shiyasa haƙorin ki suka qi rufuwa ?

Shuhada zatayi magana kenan suka iso fada hindu ta duqa ta gaishe da mahaifinta da jama'ar wajen sannan. Shuhada ta gaishesu suka amsa sunawa hindu kallon tuhuma

Hindu tace baba baka gane ta ba ko ko kuma nace baku gane ta ba ko?
Aka haɗa baki akace eh , hindu ta kalli mahaifinta tace baba dan Allah ka aika akira gwaggo mairo da anty haula
Umarnin da mai gari yabayar kenan yace aje akirawo gwaggo mairo da matar mansur

Ba ajima ba suka taho tare suna isowa shuhada ta miqe tsaye tafara ambaliyar kuka anty haula sumar tsaye tayi tace ..shu..shuhaa..shu..ha..da... Rungume anty haula tayi ta fashe da matsinacin kuka tuni al'ajabi ya ƙauraye fadar mai gari sun sha kuka kafin shuhada tazo takama kafaɗar gwaggo mairo tana kuka gwaggo mairo itama kuka hindu tana tayasu saiga innar hindu domin tuni shuhad ya shiga gidan ya fadawa kakarsa sunzo da wata kyakkyawar momy
Innar hindu ma tayi farin cikin ganin yanda shuhada tadawo bayan angama koke koke mai gari yabada umarnin a zauna

Bayan an zazzauna aka fara tambayar shuhada inda taje tsawon lkc haka
Nan ta shiga basu lbr jama'a sai tausaya mata sukeyi ga mutane ancika maqil a fadar mai gari wasu shuhadar kawai suke kallo ai da suka gane shuhada ce nan lbr yadinga zagaye ƙauyen tanko shuhada tadawo

Labarin har kunnan talatu shuhada ta dawo cikin tashin hankali talatu ta fita taje gidan yadiko tana kwance tana bacci yaran sale sunyi kace kace da gidan yaran nuratu kuwa dambe sukeyi
Talatu ta kallesu tace dan ubanku da uwarku ku baku iya komai bane sai bar'na ku kuma baku iya komai bane sai dambe ?
Daya daga ckin ɗan sale ne ya durqusa yaja kafar talatu ta fadi timmm da ƙasa
Suka kwashe da dry suka fita da gudu aka bar talatu zaune sai ruwan ashariya takeyi sai kace tanayi da babban mutum

Tashi tayi fuuuu ta shiga dakin yadikko zarnin fitsari ya daki hancinta har saida cikinta ya juya da iya karfinta ta ɗakawa yadiko duka afirgice yadiko ta miqe zata fita da gudu talatu tace ina zakije? Wannan daki ai bazan iya bacci ba wannan zarnin fitsari haka ,
Yadiko tace wlh shegun yaran nan ne da rana suka tashi iskancin su haka zasuzo su tsula fitsari atsaye su ruga da gudu yanzu dai meya kawoki naganki wujiga wujiga haka tafada tana sosai kai hannu bibbiyu dan Jitake kamar an zuba mata ƙarara akan sbd ƙaiƙayi


Talatu tace shahashar banza ba dole ki ganni haka ba kina nan kin kwanta kin sake baki kamar injin patari kina bacci
To *SHUHADA* tadawo kauyen tanko

Tsallen yan bori yadiko tayi ta zube daf da ƙasa wata sharab tace ni laure kai talatu ban son irin wannan wasan
Talatu tace tashi muje fada ba shiri yadiko ta zari mayafinta suka fice

Duk inda suka gitta sai anbisu da kallo ana musu kallon mahaukata

Suna zuwa fadar mai gari sukaga jama'a ancika sai kace ana rabon kudi daidai nan fauzan ya iso yace dan Allah yana neman fadar mai garin tanko nan aka masa kwatance yace ya gode sai kallon kauyen yakeyi ai ko amafarki aka ce masa anan kauyen aka haifi shuhada zaice karya ne


Atare suka isa yadiko tayi kukan kura tayi kan shuhada da sauri fauzan ya fito a mota ya shiga tsakani nan jama'a aka hau tare tare ana tare yadiko

Wani irin ihu gwaggo mairo ta saki ta zube ƙasa tana murza idonta da sauri jama'a akayi kan gwaggo mairo yadikko tahau cewa nice ajalinki mayyar yarinya shikenan zata karya min asiri kizo kibar kauyen nan dan uwarki da ubanki shegiya yar kutumar uba ta karya min asiri boka yace duk ranar da kika dawo asirina ya karye to saina kashe ki ta sake yin kan shuhada fauzan da ransa ya gama baci yaɗaga hannu ya wanke yadiko da maruka biyar masu rai da lafiya saida taci ƙasa network dinta ya ɗauke na wucin gadi talatu kuwa ta hau dry tana nanaye awajan tana tafa hannuwa tacire ɗan kwalinta ta jefar dashi mayafinta kuma ta ɗauresa a kugunta tana ta shewa tana cewa yau ranar tonon asiri ne
Hahahahha nice nan na batar da innar garba shekaru goma shabiyar da suka wuce nice na asirce mijina na hanasa katabus
Nice na raka laure wajen boka aka makantar da mairo nice nayi kaza nayi kaza faɗe faɗe tayike tare da sambatu kala kala

Banda salati babu abinda ke tashi afada anayiwa su talatu da laure Allah wadai da halinsu

Nuratu ce tazo da gudu tasamu yadiko tana fizge fizge itama da sauri shuhada tazo ta rungumeta tana kuka nuratu ta tureta tace wacece ke? Shuhada tace nice fa yar uwarki antynki shuhada ,sun kuyar da kai kasa nuratu tayi tana kuka

Malam liman ne yasa aka kawo masa ruwa yayi tofi aciki yabawa gwaggo mairo tasha tayi ajiyar zuciya ahankali tafara bude idanunta da suka rufe kimanin shekaru kusan goma tar ta budesu tana kallon jama'ar dake faɗa

Wani kururuwa yadiko tasa ta zunduma da gudu talatu tabi bayanta shuhada zata bisu fauzan ya riqota yace karki bisu duk wanda yayi nagari zaiga da kyau idan kuma kayi akasin haka zaka gani atafin hannunka kuka nuratu takeyi ta juya tayi hanyar gida


Shuhada kukan tausayin nuratu takeyi da yaya sale da yaransu

Bayan yan nasihan da mai gari yayi da kuma bada umarni da doka agarin sa daga nan aka rufe fada da adduah

Fauzan yayiwa mai gari jawabin zai tafi dasu gwaggo mairo cikin garin azare bisa tallafin yayansa zasu zauna acan garin azare nan yayiwa mijin anty haula mgn akan ya maida Sana'arsa azare tunda dama shago suke dashi murna sosai yaya mansur yayi yadinga zubawa adeel albarka

Mai gari yace amma su bari sai gobe su kama hanya fauzanu sai akaika gidan saukan bakina fauzan yayi murmushi yace ba damuwa gdy nake


Haka suka wuni suna yawo akauyen shuhada tana nunnuna masa kauyen ta yace waima yaushe kika taho burleey yace karkizo shine kika rigani tahowa to wlh nikam ba ruwana domin yace zaki koma ki samesa ne ,murguda baki shuhada tayi itakam abarta ma da abinda ya dameta

Haka suka wuni suna yawo sosai yan mata kauye sai yabawa da kyawun fauzan sukeyi

Shuhada tace yan matan garinmu fa kai suke kallo fauzan yace idan sukaga burleey zasu suma kenan shuhada tayi dry fauzan yace kema gashi sai haɗa go'slow kikeyi nan ma dry tayi


"""""""""
Da daddare taje gidansu ta samu nuratu da sale abun duniya ya musu yawa ga yara suna ihun yunwa masu dambe sunayi

Shuhada kuka sosai tayi amma nuratu da sale sun kasa kallonta da kyar sale ya nemi ya fiyanta nuratu ma haka
Shuhada tace najima da yafe muku ko.ba komai ku din jinina ne Allah ya yafe mana gabaki daya ta ciro dubu goma ta miqa musu gamida alƙawarin zata dawo domin harta yanke wata shawara azuciyarta


Da washe gari da safe suka bar kauyen tanko sai cikin garin azare

Fauzan yayi dukkan abunda burleey ya umurce sa da yayi, dan ya tura masa kudi masu yawa ya budewa mijin anty haula shago ya nema musu gida sosai shuhada taji dadi.tadinga zubawa yaya fauzan gdy yace bawani zakiyiwa gdy ba wa burleey zakiyiwa gdy kuma yana nan yana jiranki ki koma tunda yace karkiyi kikayi itadai bata ce komai ba dan burleey yasake samun babbar fada azuciyarta

Sosai yanzu hankalin shuhada ya kwanta duk abinda yake faruwa su ammy suna sane kullum kuma sai sunyi waya dasu..hardasu kawu baba da hajiya kaka

Satin su 2 suka shirya zasu koma kaduna shuhada tasha kuka kamar karta koma haka suka kama hanya sai yamma suka isa fauzan yayi horn ana wangale musu gate suka yi ido hudu da burleey ya hade rai fauzan yana parking ta fito kamar wanda kwai ya fashe mata aciki domin tagama tsorata da kallon da burleey yake mata

Afusace ya tashi yayo kansu ba shuhada ba harta fauzan ya tsorata fizgo hannunta yayi sukayi part dinsa .....



*******tofa
sai mun haɗu a next pg



Cmmnts


An


Share


By mmn ahlan✍🏻
[
[10/1, 6:18 AM] Zarahh: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠

*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻

*ZAHRA ABDUL* ( *m͞͞o͞͞m͞͞y͞͞n͞͞ a͞͞h͞͞l͞͞a͞͞n͞͞*)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻
*sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

Dedicated to my bestie
*UMMA MUHAMMAD NAJAMAGA* _luv u kace kace_😘
___________________
🤦🏻‍♀ *kash bana kashe waya matsala sim card din yasamu but now alhamdulillah yadawo nml duk wanda ya kirani zai shiga*


*بسم ا لله ا لر حمن ا لر حيم*
*_________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*__________________*


*P*...3⃣1⃣↪3⃣2⃣


Shuhada a tsorace take dashi ganin yanayin sa gashi sai fizganta yake sai kace ya samu kaza ,suna shiga parlornsa ya haɗeta da bango idonsa yayi ja

_mene ce miki ? Cikin daga murya ,banace karkije ba shine dan kin rainani kika kama hanya kika tafi sannan ko ki kira ni sbd kin mai dani abokin wasan ki_?

Ƙiris ya rage shuhada tasaki fitsari tsananin tsoro

_Muryan ta na rawa tace kayi hakuri bazan iya jurewa bane saina je naga ƙauye na shiyasa na tafi amma kayi hakuri ngd sosai da taimakon ka agareni harna mutu bazan manta ba Allah yasaka maka da mafificin Alkhairi_

Sosai yaji dadin adduarta ,
Zamewa tayi ta gefensa ta raba zata wuce

Yace ina...tsayawa tsak shuhada tayi naji gabanta ya fadi juyowa tayi suka haɗa ido suna kallo juna

_ina....inaa...ina..dafe goshin sa yayi sannan yace ina...so daga yau idan nace bana son abu kidinga kiyayewa kinji ko_?

Asanyaye ta amsa da to sannan ta fice, tabbas ba abinda yayi niyyar fadi ba kenan yaso ya fada mata yana sonta ne zubewa yayi akan kujera ya lumshe ido oh Allah ka kawo min agaji nida nake fari bazan so yarinya ba sai gashi son shuhada yana neman zautar dani ya dafe qirjinsa dake harbawa da sauri sauri


Tana shiga parlor ta samu ammy atsaye tana ta mita fauzan yana zaune yana dry raeena raeesa zeeyadat shukra mihik sabah duk suna zaune
, haba wannan wani irin abu ne daga dawowarta saiya wani jata bari abbinku yadawo yaxo ya fadi menene matsalar sa da shuhada daya takurata haka bari naje na dubota dan naga alama wani lkc ba imani yacika ba yanzu sai yace zai daketa

Shuhada tace ammyna gani fa ,
Juyowa ammy tayi tace my Doter, da gudu shuhada taje ta rungumeta ta saki kuka ammy tace badai dukan ki yayi ba raeesa ta yatsine fuska tace indai yaya burleey ne zai aika ,yaya fauzan yace ki iya bakin ki dan yau naga a wuya yake yanzu zakiji yamiki rubdugu, su zeeyadat suka kwashe da dry

Ammy ta shiga lallashin shuhada tana bubbuga bayanta a hankali ,ammy ta kuma tambayarta adeel ya dakeki ne?
Girgiza kai shuhada tayi taɗago fuskarta tana share hawayenta da bayan hannu tace ammy babu abinda yamin nayi kewarki ne kawai ,ammy tayi murmushi ta shafo fuskarta tace nima nayi kewar yarinyata jeki watsa ruwa kizo kici abinci


Shuhada ta juya ta kallesu tace sister's nayi missing dinku wlh tashi sukayi suka rungumeta duka, sabah tace anty shuhada wlh kin ƙara kyau dry shuhada tayi tace ngd , juyawa tayi ta kalli yaya fauzan tace ahuta gajiya saurayi mijin yan matan kauyenmu su zeeyadat me zasuyi inba dry ba fauzan ya miqe afusace ta haura sama da gudu tana dry ta juyo tamasa kwalo yayi kwafa ya fice domin yaje ya samu ya watsa ruwa shima
Gabaki daya suka haura sama shuhada ta shiga wanka

Ta fito ta shafa lotion tasa dogowar abaya marar nauyi raeena taje ta kawo mata abinci taci ,suka kafa dandalin hira shuhada tana basu lbr sai mamaki sukeyi daga karshe kuma sukace Allah ya rabamu da son zuciya suka amsa da ameen raeena tace dan Allah kujifa wani abun kamar a shirin film mihik tace shuhada kefa kawai an haifeki ne acan amma mune familynki shuhada tace kamar ya? Shukra tace haka kawu baba ya fada ranar ,
Zeeyadat tace kawu baba yana can yana jiranki yayi kewarki harta hajiya kaka kullum saita addabemu yaushe zaki dawo shuhada tayi murmushi tace Allah sarki mijin da kishiyar bari muyi sallar isha'i sai mutafi family house din


Zeeyadat tace naji kawu baba yace akwai mgn bansan wani mgn bane yace abari yaya fauzan ku dawo tukunna ,shuhada tace to Allah yasa muji alkhairi suka amsa da ameen

Shuhada tace raeesa yanaga kin rame haka? Murmushi tayi batare da tace komai ba tausayinta ne ya kama shuhada aranta tace nidai wlh raeesa banga wani abun so ba awajan khalid duk da ya hadu so kenan mai sa mutum yafita daga kamannin sa da da akwai yanda zanyi danayi kin auri khalid amma bani da wannan ikon Allah dai ya zaba mana abinda yafi Alkhairi

Mihik tace ai yanzu raeesa an koma salihatu suka kwashe da dry ta bude baki zatayi mgn wayarta ya ɗauki ruri tana dubawa taga my lyf ɗaukawa tayi ta fice daga dakin dan idan ba haka ba yanzu zasuyi fada dasu zeeyadat da shukra

Hira sosai sukayi bayan sallar magriba suka fita sukaje gidan momma shuhada ta gaisheta momma da fara'anta tace doter ina tsaraba shuhada tace kwantar da hnklinki mommana zan kawo miki gobe ,momma tace to shikenan doter inajiranki fa suka yi dry suka fice suna cewa zasuje wajen mamy daga can zasu wuce big house momma tace adawo lpy sai munzo ,
Gidan mamy suka shiga mamy tayiwa shuhada sannu da dawowa tace dazu fauzan yazo ai nake cemasa ina yabaro min ke wai yabarki a azare nace masa ashe zai koma yanzu da dogoyen kafafunsa kenan , shuhada tayi dry tace yaya fauzan da zolaya nadawo mamyna ,mamy tace ai da kuwa da gske ne bama niba kawu baba zaisa shi ya koma suka sa dry

Saida sukayi sallar isha'i kafin suka fito duka zasuje family house har sun kai gate raeesa tace wayyo nayi mantuwa kuje zanzo suka ce to ita kuma ta juya da gudu bata lura ba taji ta bangaje mutum da sauri taja burki tana kallonsa haɗe rai yayi ,keee ba ki ganin gabanki ne murguda baki tayi tace sai fa hakuri domin idanuwana abayan ƙeyata suke kaga kuwa ai bazan iya kallon gabana ba kai da kake da ido agaba aida saika matsa ka bani hanya na wuce

Cikin bacin rai jb yasa hannu zai kaiwa bakinta kopɗa da sauri ta matsa sannan tayi cikin gidan da gudu mamy tace ah ke baki tafin bane waya koro ki da gudu kuma,? Eh mamy na manta da waya nane ɗauka tayi ta fice tana cewa mamy kinsan akwai horror agidan ,a gate din taga su shuhada suna tsaye dasu yaya anwar yaya mashkur yaya rayyan da kuma yaya fauzan tace au baku tafin ba shukra tace brother's ne suka tsaida mu

Yaya mashkur yace matar tsoho aka akwashe da dry shuhada tace eh naji nice nan ku faɗi da ihu ku kara da wayyo sai kawu baba hira sukeyi abin sha'awa atsaye awajan

Yaya anwar yace mutafin ku mana, dukan su suka ɗunguma family house


Sallama sukayi yawanci jama'ar gidan suna. Zaune parlorn kawu baba da gudu hajiya kaka ta tashi tana cewa oyoyo shuhada rungume juna sukayi suna dry

Hajiya kaka tace wlh bansan haka nake sonki ba saida kikayi tafiya shuhada tana dry tace wlh nima nayi kewarku sosai
Gaban kawu baba taje tana cewa hajiya kaka dan Allah kishiyar karki sakeyin gudu kamar haka kinga dai ni ba likitar ƙashi bace balle idan kika karye na gyaraki

Riqe baki hajiya kaka tayi tace eh ba dole ba ja'irar yarinya tunda kinga nayi miki oyoyo daban rakaki da sanda ba akasa dry

Kawu baba yayi murmushi ya shafi kan shuhada yace sannu da dawowa matar gaishesa tayi ya amsa yana fara'a sannan ta gaida kowa na gida nan aka hau hira zuwa can anjima burleey sadam jb suka shigo aka ɗaura dasu amma burleey da jb basu mgn dan sune yan'shan kamshi


Kawu baba yayi gyaran murya yace masha Allah isyaku hafeezu ismaeel ina alfahari daku amatsayinku na ya'ya'na sannan ga jikokina masha Allah

Sannan duka nan ba bare gabaki dayan mu family ne kum....kawu baba bai gama mgnr sa ba wuf binayya tace aa fa tsoho kadinga cire harafi daya akwai bare mutum daya

Kawu baba yace eh tabbas akwai bare kuma inaga nin ba kowa bace face keee domin duk familyn mu babu marar kunya sama dake ina magana da ubannin ku ne wanda na haifesu suke ganin girmana wanda zansa suyi sannan suyi nace abari sannan subari
Idan kuma shuhada ce kike kiranta da bare to shuhada ta sha gaban bare kiji na fada miki tun ranar da shuhada ta taka gidan nan na maida ita ahalina shuhada bazata auri bare awaje ba *SHUHADA ƊAN GIDA ZATA AURE ACIKIN FAMILYN JIBRIL BURKA*
Binayya ki kiyayeni zanyi mugu mugun saba' miki ran kawu baba yabaci sosai domin azuciye yake magana

Ahankali binayya ta tashi tana qunquni har tana buga cinye daga gani kasan alwashi take

Please Login or Register in order to submit comment