Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma dai duk anan cikin unguwan ne nasan gobe idan anzo dole ne asan abinda ya faru sannan asan wacece ke

Cikin matsinacin kuka shuhada ta fara mgn muryarta harya dashe ta hau bawa ammi labarinta tunda ga haihuwarta rayuwarta a kauyen su da mutuwar mamarta da babanta da wahalar da tasha wajan yadiko har izuwa barinta kauyen su da taimakon da bala yamata ba don Allah ba yaso bata mata rayuwa da haduwa da hajiya kila da tayi da siyar da ita da tayi wa alh tukur duk bata boyewa ammy komai ba sannan tace wlh bansan dalilin dayasa nabaro kauye na ba nabar gwaggo mairo na da anty haula da aminiyata hindu

Hawaye ammy keyi tana jinjina karfin halin wasu wanda basu tunanin zasu mutu sai kace duniyar nan baza abarta ba da kyar ammi ta tsaida hawayenta tafara lallashin shuhada da ra'eena harda ra'eesa ammy tasha mamakin ganin ra'eesa tana kuka dan ita ba komai bane na tausayi awajanta tafi kwarewa tayiwa mutum mugunta ta koma gefe tana kyalkyala dry

Ammy tace kiyi hakuri kibar kuka insha Allah yadiko zata ga iyakarta ni kuma ki ɗaukeni amatsayin mahaifiya domin ya'ya' na kowa ne idan kaki ɗan wani kai bakasan wa zaiqi naka ba harka zalika idan kaso na wani kaima baka san wanda zai so naka nan gaba ba

Shi kuma wannan tsohon banza Alhamdulillah da Allah bai basa nasara akanki ba shi da bala
ita kuma kila idan halinta kenan Allah ya ganar da ita da gaggawa ta tuba

Yanzu dare yayi sosae muje ki kwanta ki huta tunda baki da lpy ku ma ra'eena ra'eesa kuje ku kwanta kwabe fuska ra'eesa tayi tace ammy adakina zata kwanta ko
Ra'eena tace ammy adakina zata kwana ai kawata ce ra'eesa tace nima ai ina sonta da kawa ammy tace duk ku gama hayagagan ku adakina zata kwana

Dan haka ku tashi kuje ku kwanta tashi sukayi amma ahanya saida ra'eesa ta tsokani ra'eena duk da dakinsu yanzu ba daya ba sbd rigima irinta ra'eesa yasa abbi raba musu daki amma ga daki ga daki



***************
Su waye abbi da ammi wanda shuhada zatayi rayuwa tare dasu

*ALHAJI ISYAKU JIBRIL BURKA*


Su ba yan kaduna bane amma yawancin yan uwansu da abokan arziki suna kaduna
Asalinsu buzaye ne acan cikin niger

Isyaku yayi karatun sa a niger kafin ya baro niger yazo kaduna domin neman aiki amma bai samu ba da haka ne yafara kasuwanci
Cikin ikon Allah da rahmarsa kuwa Allah ya buɗa masa a kasuwancin sa
Yana da qanne maza uku shine babba sai mai binsa isma'il sai hafeezu
Ganin kasuwacin da yakeyi Allah yasa masa albarka da haka yajawo ƙannansa suka hada hannu tare har suka gida babbar gida acikin garin kaduna a unguwar malali ya zama kamar family house sannan isyaku ma ya gina nasa domin a lkcn anfara mgnr aurensa da ramlatu (AMMY)
Abisa ƙa'idar familyn basu yarda ɗan gida ya auri bare ba sam saidai ya dubo acikin ya'ya'n yan uwa ya aura ramlatu yar' gidan bappan su ne wato yar'qanin mahaifinsu


Bayan anyi auren isyaku da wata biyar akayi na su is'mail da hafeezu
Yayinda suma suka tada gininsu duk a unguwar malali kusa da familyn house din da suka haɗa hannu suka gina sannan dukkansu yan uwa ne suka aura babu wanda ya auri bare wa haka ne duk suka tare a unguwar malali saidai kawai banbancin tsakanin gidajen


Ammy tana da shekara biyu agidan miji kafin Allah yabata ciki

Cikin ammy yana da wata bakwai matar hafeezu sajida ta haihu ta samu ɗanta namiji
Wannan family sunyi murna sosae haka ranar suna yaro yaci sunan kakarsa wato mahaifinsu isyaku alh jibril yaji dadi sosae da ɗansa hafeezu ya masa takwara hakan ne yasa ba akiransa kan tsaye da sunan ake ce masa kawu karami wasu kuma daga cikin family suke kiransa da JB domin takwaran sa yace kar a boye masa sunan sa
Bayan sunan jb da wata uku ammi ta haifi ɗanta itama namiji fari sol dashi mai kama da mahaifinsu isyaku wanda suke kiransa da kawu baba
Anyi farin ciki sosae kawu baba da kansa yace asa masa suna abdulrahman
Haka kuwa akayi domin sunan da aka samasa kenan amma mahaifiyarsa ta boye sunan domin sunan babanta ne shiyasa aka masa inkiya da suna (adeel)

Adeel yana da wata biyar matar isma'il badiya ta haife ɗanta itama mai suna sadam
Masha Allah haka akayi suna lpy aka gama lpy
Yayinda family sai hayayyafa akeyi ana qara cika

Ammy bayan adeel ta sake haihuwar namiji mai suna fauzan sai mashkur kafin twins dinta ra'eena da ra'eesa sai ƙaramar kanwarsu auta sabah yar shekara 7

Hakama mamy
( sajida) matar abbu hafeezu bayan jb akwai anwar sai zeeyadat da shukra

Momma (badiya)ma haka matar abba isma'il bayan sadam akwai rayyan da maryama wanda suke kiranta da (mihik) sbd sunan kakarsu ce da ita wato mahaifiyar baban su

Wannan kenan shine takaiceccan tarihin wannan family

*************

Wa she gari.
Da misalin karfe 11 tana kwance a dakin ammy ra'eena tana zaune agefenta tana bata lbr hayaniya sukaji an doso dakin ammy ra'eena tace wata kila su zeedi ne da shuk...bata qarasa ba kuwa suka turo kofar suna dry suka zazzauna suna kallon shuhada
Kafin suka yimata ya jiki tace Alhamdulillah aranta tace wai wannan family akwai kyau gasu farare

Mihik tace sis yama sunan ki?
Murmushi shuhada tayi
Kafin tace sunana *shuhada*

Wow nyc name cewar ziyadat
Amma fa gaskiya kina da kyau sosae

Shuhada tayi murmushi tace kuma ai kuna da kyau mihik tace ai bamu kai ki ba
Duk family dinmu yaya burleey ya fimu kyau da hasken fata domin yana kama da kawu baba sosae
hasken fatar ku daya dashi
Ra'eena tace haka jiya ra'eesa ta fada wai suna kama da yaya burleey
Shuru shuhada tayi tace wannan wani irin suna ne kuma burleey bayan a tarihin da ra'eena ta bani banji mai sunan burleey ba

Kyalkyalewa da dry mihik tayi tace yaya burleey shine *yaya adeel* afirgice shuhada ta ɗago idonta tana kallon mihik dan bata san mgnr ya fito fili ba
Zeeyadat tace ra'eesa ce ta saka masa suna burleey tun muna qanana sbd baya da wasa ko dry balle mgn gashi baya da sassauci idan kayi laifi jibgarka yake kamar ba gobe ra'eesa kuwa humm duk yadda za a gaya miki halinta bazaki gane ba sai kin zauna da ita ba kina tare damu ba ai zaki gani da idonki halin ra'eesa yaya burleey casata yakeyi shiyasa tasa masa suna burleey har sunan ya bisa amma fa agabansa bamu isa mu fadi haka ba dan sunan mu sorry yaya burleey da yaya jb da yaya sadam sam basuyi mana wasa idan kinga muna wasa da dry to ko yaya fauzan ko yaya mashkur ko su yaya anwar da yaya rayyan amma su ukun nan kam sai a hankali shukra tace amma dai gwanda yaya sadam ra'eena tace ai yaya sadam baya da hayaniya ko ɗaure fuska kamar yaya burleey da yaya jb

Mihik tace da rabon ba zaku hadu da yaya burleey ba ya tafi Indonesia kuma bazai dawo ba sai nan da 5years shima yaya jb da yaya sadam zasu tafi jibi domin komai tare sukeyi su uku

Nan da nan shuhada taji familyn sunyi matukar burgeta sosae suka dinga hira tun shuhada bata sake ba harta sake sosae
Duk wannan bidirin da sukeyi yau kwata kwata bata ga ra'eesa ba tun tana shuru harta tambaya ina ra'eesa
Ne yau ban ganta ba ? ra'eena tace waya san mata ko tana family house ne ko tana gidan abba ko gidan abbu ne oho Mata
Gyada kai shuhada tayi batare da tayi magana ba

Yan'family house yawanci sunzo sun duba shuhada abin mamaki kuma babu wanda ya gwada rashin amincewa da riqonta a family dinsu sai wata budurwa ita kadai wacce tun shigowarta take watsawa shuhada kallon banza akalla zata kai shekara 19 ganin kallon banzan takeyiwa shuhada yayiwa ne yasa shuhada ta ɗauke kanta itama

Ra'eesa kuwa tana gidan abbu a part din jb kayansa daya shirya zaiyi tafia dasu ra'eesa tasa su agaba da almakashi duk ta yan yanka su sbd dama tanajin haushin sa sannan da ammy taje family house dinsu ta basu lbrn shuhada ammy take cewa ra'eesa ce tasa garba fita wai akaisu shan ice cream da daddare har abin ya faru shine jb yana tashi ya ƙwaɗa mata rankwashe akai shine taje yimasa wannan aika aikan


Bata koma gida ba saida aka shiga sallar magriba ta fito tayi gida a parlorn ammy tasamu su shuhada da ra'eena suna zaune suna hira sallama tayi sai murmushi takeyi tazo ta zauna kusa dasu ra'eena ta kalleta da kyau tace sis anya bakiyi wani abun ba kuwa naga sai fara'a kikeyi ?

Mtssww oho karki dameni malama ban sani ba
Shuhada tace yau ina kika shiga ne ra'eesa tun safe
Dryn ƙeta tayi sannan tace wlh naɗan je wani aiki ne tana fadin haka ta tashi tayi hanyar dakinta



Kwanan shuhada biyu
Su jb da sadam suma suka shirya tafiyarsu har airport aka rakasu ra'eesa sai zubawa jb Allah ya kiyaye hanya takeyi cije baki kawai yayi ya shige yaja akwatynsa wanda ra'eesa ta yage kayan ciki kaf tana kallon yaja akwatyn ta sake kwashewa da dry ra'eena tace ina fatan dai lpyr ki kalau yaya mashkur yace tayi miki kama da mai lpy ne ku shige muje gida motar su suka shiga sai gida


Ban garen jb kuwa da suka isa Indonesia burleey ne yazo ya ɗaukesu bayan sunyi wanka jb yaja akwatynsa zai sa kaya amma mai yana ɗauka yagansu pieces pieces mamaki ne ya kamasu duka kafin sadam yafara dry ahankali ɗago zara zara idanunsa adeel yayi ya busa iska yace wannan aikin saidai ra'eesa kwata kwata bansan wace irin yarinya bace jb dai ya kasa magana sbd bacin rai gashi yabar ƙasar ma gabaki daya idan ba haka ba baisan kalar dukan da zaiyiwa ra'eesa ba
Tagumi yayi idanunsa sunyi jajur gashi course din da sukazo yi sai sun shekara biyar kafin su koma gida amma insha Allah duk ranar da suka koma saiya koyawa ra'eesa hankali



Bayan sati daya

Alhamdulillah jikin shuhada yayi kyau sosae kuma ta saba dasu dan ammy ta fara mgnr nema mata admission

Wani lkc haka zataje family house suyita hira ana dry amma banda wannan budurwar



Agurguje shuhada ta fara zuwa makaranta sosae rayuwarta ta sauya
Masha Allah

****************


Fans Dan Allah saidai kudinga hadamin da hakuri yanxu wlh sbd skll

______



Comments

And

Share

*_by Mmn ahlan_*✍🏻
[10/1, 6:18 AM] Zarahh: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠

*ᔕTOᖇY ᗯᖇITTEᑎ ᗷY*

*z̸a̸h̸r̸a̸ a̸b̸d̸u̸l̸* ( *m̸o̸m̸y̸n̸ a̸h̸l̸a̸n̸*)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

__________________
_sadauƙarwa gareku_

*mrs farouq* _ta group din Ummu Nasmah_
&
*Dr herpsert*
&
*_dearie na fatima bintu sagir_

_nayin ku irin totally din nan_💓
__________________

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


*P*...1⃣9⃣↪2⃣0⃣

Yau ta kama weekend dukkan su suna family house zaune suke a parlorn hajiya kaka sai hira sukeyi ra'eena ra'eesa shuhada zeeyadat shukra mihik

Ra'eesa tace hajiya kaka ki bamu labarin yanda soyayyarku ta fara tsakanin ki da kawu baba dry suka kwashe dashi hajiya kaka ta dunqula hannu tace ungo naki ja'iran yarinya kawai mihik tace aa fa hajiya kaka kawai ki fada mana
Hajiya kaka tace wai yau baku da islamiyya ne kam ku tashi ku tafi gidan ubannin ku amma kunzo kun cikani da surutu
Shukra tace hajiya kaka yau fa saura mana wata daya muyi sauƙa insha Allah

Ah masha Allah abu yayi kyau Allah ya kaimu ashe dai muna da walima
Zeeyadat tace sosai ma aini harda party saina yi ra'eesa tace kice zamuyi dai ba zakiyi ba riqe baki hajiya kaka tayi tace yau najini da yaran zamani saukan al'qur'ani mai girman ne za ayiwa party ? Shuhada kina jinsu fa sai alkcn shuhada tayi mgn sbd suna cikin hiran su mai dadi amma daga shigowar wannan budurwan ta kasa sakewa sbd kallon da tasaba mata wato kallon wulaqanci da ƙasƙanci gashi har yau bata san sunanta ba kuma tunda ta shigo parlorn ko uhum bata ce ba illa ma kwanciya da tayi akan dogon kujera


Shuhada tace kai zeeyadat kai ra'eesa walima fa kawai akeyi wlh duk wannan party partyn babu kyau a musulunci saidai kawai Allah ya kyauta

Hajiya kaka tace yauwa faɗa musu dai ko zasuji
Shukra tace ke kam kinji dadi tun kina shekara 11 kikayi sauka amma muma Alhamdulillah yanzu muna 13to14 zamuyi sauka
Murmushi shuhada tayi tace ai kuma kunyi da wuri Allah dai yabamu ikon amfani da ilmin mu suka amsa da ameeen nan dai suka cigaba da hira kawu baba ne yayi sallama ya shigo yace ah yau matan nawa ne duka anan yatsina fuska ra'eesa tayi tace haba kawu baba ai kai kam kariga da kagama saidai hajiya kaka amma banda mu zeeyadat ma tace wlh nima dai bandani shukra ma tace nima dai banda ni gasky mihik itama saida ta yatsine fuska kafin tace kawu baba ai kai na hajiya kaka ne wai ma meyasa bakayi mata kishiya a gaske ba ?
Kawu baba yayi dry ai ku nake jira ku girma saina aura daya daga cikin ku nan ma dry suka kwashe dashi ra'eesa tace kawu baba amma fa idan ka caskare kafita baza ayi tunanin ka girma kana da jikoki kamar su yaya burleey damu bafa hajiya kaka tace nikam bazaku kasheni da mgna ba bari na tashi mihik tace hajiya kaka kodai kishi kikeyi ne ta qarasa da dry
Kawu baba yace tunda baku so na shuhada ai tana sona ko ba haka bane ? Murmushi shuhada tayi cikin wasa tace sosae ma ina sonka son so ma kuwa dry ra'eena tayi tace ke kuma sis me zakiyi da kawu baba ?
Zeeyadat tace ashe dai ke kam sai tsoho kawu baba yayi dry yace karki yarda su zugamin ke kinji ko
Shuhada tace ai bazanji zugan su ba
Hajiya kaka tace to kwalelen ki bake ba mijina cikin dry shuhada tace ai kuwa hakuri zakiyi hajiya kaka amma daga yau mun zama kishiya

Tsaki sukaji anyi kawu baba ya juya ya ganta kwance ta wani haɗe rai yace ah matan dama kina parlorn nan
Uhum kawai tace ta rufe ido kamar mai jin bacci amma azahirin gasky ba baccin takeyi ba yadda lkc daya shuhada ta sace zuciyar familynsu ne abin ke bata haushi gashi ita kwata kwata batajin son shuhada haka kawai ma idan ta kalli shuhada sai taji gabanta ya fadi


Basu da barin gidan ba kuwa har yamma tukunna su ra'eena sukayi shirin islamiyya suka tafi shuhada kuma ta koma gida a parlor ta samu yaya fauzan na zaune gaishesa tayi ya ɗago kai ya kalleta yayi murmushin gefen baki ya amsa yace ke bakije islamiyyar bane?

Sun kuyar da kai kasa tayi tace ni nayi sauƙa tun tuni
Da mamaki ya ɗago yana kallonta yace kinyi sauƙa kika ce
Ta gyada masa kai
Jinjina kai yayi yace da kyau ashe dai malama ce murmushi tayi yace zo ki zauna mu dan yi hira

Bata so hakan ba amma babu yanda ta iya haka tazo ta zauna suna hira sama sama take basa amsa yawanci yana mata tmbayoyi ne akan abinda take karanta domin shima likita ne sosae ya yaba da kwazonta da baiwarta da kwakwalwarta suna cikin hiran nan wayarsa ya ɗauki ruri yana dubawa yaga sunan *broz* annurin fuskarsa ƙaruwa tayi kafin ya ɗaga wayar yasa akunnan sa yace hlo ɗan uwa rabin jiki
Saida aka ɗauki kusan minti3 kafin yace wato rabin jiki ba ma gudan jiki ba ko dry fauzan yayi yace tunda aka fara da rabi ai zaka zama guda dinma
Yace karka cikani da surutu tambayarka zanyi fauzan yace to adeel inajin ka ko kuma nace burleey

Gaban shuhada ne ya buga har sau uku
Duk lkcn da za akira sunan adeel ko ace burleey sai zuciyarta ta tsinke ta rasa dalilin hakan

Tashi tayi ahankali zata haura upstairs fauzan yace shuhada ina zakije kuma?
Gaban adeel ne shima yaji ya buga ya sake maimaita sunan aransa shuhada!shuhada!shuhada!

Murmushi ta kwaqulo tace zan ɗan duba littafina ne kafin anjima nazo sai kamin bayani akan wannan abun ok kawai yace sannan ya juya ita kuma ta haura sama

Adeel yayi ajiyar zuciya yace wacece kuma shuhada?
Fauzan yace ok baka santa ba ko yarinyar da ammy ta riqeta ne wanda garba ya bugeta da mota ko kana nufin baka san labarin ba

Mtsww ok nasani mantawa nayi da shike ma bansan sunanta ba that's why
Ok ayya ai sunan ta kenan *shuhada*

Ok yayi dama so nake na tambaye ka abbi yadawo kuwa ?

Aa bai dawo ba sai nan da sati daya abbu ne kawai yadawo amma ko abba ma bai dawo ba
Adeel yace ok to shikenan sai munyi magana yana fadin haka ya katse wayar


Da daddare suna zaune su uku a parlor suna hira shuhada tace ra'eesa ke me kike karanta ne ? Saida ta juya ido kafin tace *Jounalist*
Shuhada tace nikam gaskiya inaso naga yawanci Mata suna aikin likitanci SBD yanzu wlh ana wahala barin ma asibityn kauye ra'eena tace sis shuhada waya gaya miki ra'eesa zata iya aikin asibity ai inaji kafin ta duba marar lpy ya mutu

Afusace ra'eesa tace kinga malama. Ki kiyayeni fa ban gane ba kafin na duba marar lpy ya mutu ba

Ra'eena tace ai kinfi dacewa da yar jaridan kam dan idan aka kawo miki marar lpy zaki tsaya rigima ne ko kuma surutu kinga kuwa kafin ki waiwayi marar lpy ai ya mutu tashi ra'eesa tayi zata shaqo ra'eena

Shuhada ta riqeta tace kai ra'eesa meyasa da anyi magana zaki ɗauki zafi ? kidinga hakuri dan Allah kidaina abubuwan da kikeyi nan gaba kadan fa zaki zama big girl hararan ra'eena tayi tace sis shuhada da take cewa kafin na duba marar lpy ya mutu itama da take karantan doctor din kafin ta duba marar lpy ya mutu sbd zata sashi agaba ne tayita kuka


Dry shuhada tayi tace kuma fa gskyr kine ra'eesa sbd akwaita da saurin kuka kuma nima haka nake fa
Ra'eena tace wlh bana sanin lkcn da zuciyata take tsinkewa banson ganin abin tausayi

Shuhada tace yauwa dama inaso na tambye ku
Hankalin su gabaki daya suka bata tace laahh ba wani abu bane bafa wannan wanda kuke kiranta da sistern nan ya sunanta ??

Ra'eena ta zare ido tace baki san sunanta ba duk zamanki a family house murmushi shuhada tayi tace ai kinsan ba mgn muke da ita ba
Ra'eesa ta yatsine fuska tace ai girman kai ne da ita harda na siyarwa
Sunanta *_binayya_*
Yar gidan kanwar hajiya kaka ce itama duk a family dinmu take

Tabe baki shuhada tayi aranta ta sake maimaita sunan binayya humm

Hankalinta ta maida kan tv din da suke kallo wani hausa film aka saka mai suna *hindu* wanda
*jamila nagudu* tayi
Ba qaramin tashin hankali ta shiga ba ahankali ta tashi ta shige dakinsu taci kuka tana son zuwa kauyen su amma tarasa dalilin dayasa da tayi yunkurin zuwa saitaji wata azababbiyar ciwon kai dole take hakura ranar dai haka ta kwana da zazzabi


Masha Allah haka rayuwa take ta tafiya shuhada ta zama yar familyn alh kawu baba da kowa ta saba dashi saidai har kwanan gobe basu ga maciji da binayya abbi ma daya dawo daga tafiya sosae ya yaba da shuhada tsaraba ya musu sosae
Hakama abba wannan family dai rayuwarsu sukeyi cike da farin ciki da walwala kullum sai sunje family house sudinga barkwanci
Kawu baba yace mata ai kuwa zai bata mamaki tunda tace tana sonsa saita auri mai kama dashi shuhada tayi ta dry dan bata san me yake nufi ba suyita sababi da hajiya kaka

A kwana atashi
Yau saura kwana biyu su ra'eena ra'eesa zeeyadat shukra mihik suyi sauƙa shirye shirye akeyi sosae ammy momma da mamy sunyi musu shiri sosae sannan sun dinka musu kaya sunyi anko hajiya kaka ma ba abarta abaya ba haka ma kawu baba yaya fauzan cikin wasa yace wato mu dan ba ason mu lkcn da zamuyi namu sauƙan ba ayimana wannan shagalin ba
Kawu baba yayi dry yace to ina kuwa ku za amuku ai saidai matana fauzan yayi dry yaya rayyan yace ah kawai dai anyi son kai anwar yace wlh kam anyi son kai amma ba komai nan suka dinga hirar su da raha tare da barkwanci

Ranar walima kuwa bayan anyi a islamiyya suka gayyato kawayensu akayi acikin gida anci ansha anyisu pics

Mashkur ne ya turawa jb pics din yana buɗewa yafara tozali da ra'eesa tayi matuƙar kyau cikin wata tsadaddan net tana dry wani ƙololon baqin ciki ya hadiye ya juya ya kalli akwatyn kayan sa wanda tayi musu yagun rashin mutunci ya cije baki yana aiyana kalar ɗibar albarkan dukan da zaiyi mata duk ranar daya koma 9ja kalleta kamar ta Allah ya fada a zuciyarsa

Ko da fauzan ya turawa adeel pics din yagani kam amma bai bude ba

Agajiye suka tashi awajan walimar tasu shuhada hannun saba taja sukayi cikin gida sun samu kyaututtuka sosae

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya duniya tana gudu kwanaki suna qarewa


Agurguje

*AFTER 5YEARS*......


_______________



Sai a next page😜 zamuji mai yafaru awannan tsawon lkcn sannan musan mai zai faru nan gaba



*****



Comments


And


Share


*_by mmn ahlan_*✍🏻
[10/1, 6:18 AM] Zarahh: 🌠🌠🌠🌠🌠🌠
🎇🎇🎇
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
🎇🎇🎇
🌠🌠🌠🌠🌠🌠

*ᔕTOᖇY ᗯᖇITTEᑎ ᗷY*

*z̸a̸h̸r̸a̸ a̸b̸d̸u̸l̸* ( *m̸o̸m̸y̸n̸ a̸h̸l̸a̸n̸*)

( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*)
👸🏻 *sᎪhᎥbᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻

__________________
*_nidai kullum bani da bakin magana agareku saidai nace Allah yabar qauna masoya littafin SHUHADA da wanda nasani da wanda ban sani ba ina gaisheku ina muku fatan alkhairi aduk inda kuke_*
Gada
_mmn ahlan_
____________________
_yau dai inaji idan har banyi typing din book din nan ba akwai wanda zasu cinyeni ɗanya 😟 bazasu bari saina gasu ba kowa *shuhada shuhada* 😟 to gata nan tunda ni baku nemana sai shuhada😪_
____________________
_amma fa gsky ina shan dariya wlh 🤣🤣🤣 sbd wasu basu iya kiran sunan ba yan'group din mamies luv fans yau inaji zanyi muku voice note na fada muku🤣🤣_
____________________

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*P*...2⃣1⃣↪2⃣2⃣


Wata budurwa ce tsaye a parking space na hospital fuskarta ɗauke da murmushi
Bazata wuce 19years ba sanye take da atampa riga da siket wanda dinki ya karbi jikinta kaman dama ajikinta aka dinka kayan
ta naɗa veil akanta asaman atampar lobcourt ne na likitoci tym to tym takan duba agogon dake ɗaure ahannunta zuwa can anjima wani saurayi ya fito da sauri shima hannunsa ɗauke da labcourt din kallon sa tayi tace yaya fauzan sai yanzu

Murmushi yayi yace eh *shuhada* muje mu ɗauko su mihik da shukra a skull
Mota ya shiga itama ta shiga ya tada suka ɗauki hanyar *nadabo university Kaduna* fauzan yace gsky yau kinyi matukar kokari ko da yake ma kullum kinayi kinsan wannan doctorn dayazo daga Dubai dinnan wlh saida yasha mamaki wai shekarun ki 19 amma wai kina da degree sbd bai taba tunanin yan' nigeria suna da wannan hazaƙan ba

Murmushi kawai shuhada keyi tana tuna baya lumshe ido tayi tace yaya fauzan turawan nan sun raina mu dayawa wlh

Yace haka suke ai hira suke danyi sama sama dan shima fauzan din bawani magananne bane har suka isa waya fauzan ya ɗaga ya kira mihik yace sufito ko minti uku basuyi ba suka fito duk sun zama big girls jida kansu kawai sukeyi suma yanzu yan'mata ne za adama dasu yan matan university basu kula kowa balle mgn da mutune wasu har cewa suke yaran familyn gidan kawu baba akwai girman kai duk mgnr da zasuyi basu saka sunan yarinya daya domin sunsan halinta sarai ba kauwar lasa bace tunda yanzu an girma amma babu abinda

Please Login or Register in order to submit comment