Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kofar
dakin da sauri ko da ta je kofar
dakin sa ta juya domin kawai ta
yiwa dakin kallon karshe, sannan
ta dubi gawar Bose da ke kan
gadon kwance tana barci, barcin
da ba za ta farka ba, sai ranar da
aka busa kaho, Rabi'at ta juya a
hankali ta nufi kofar gidanm tana
sharar hawaye, cikin takaicin
auren Abdul, wanda ya janyo
mata sanadiyyar kisan kai, ta san
cewa da zarar an kamata kashe
ta ita ma za a yi. Za ta shiga
duniya, ta ce da kanta. Sai ta
haife za ta dawo ta kawo kanta
ga hukuma. Abin da ba ta sani
ba, shi ne, koda laifin kisan kan
ya tabbata a kanta, ba za a zartar
da hukunci ba har sai ta haihu, to
amma kuruciyar Rabi'atu ba ta
bari tasan hakan ba ita a shi ne
tunaninta da an kama ta haka za
a kashe ta.
Rabi'atu ta jingina kanta a jikin
kujerar motar hayar, sannan ta
shafi dan matashin juna biyun da
ke jikinta tace cikin zuciyarta.
Allah ya sa na miji ne, Allah ya sa
kuma bai yi halin ubansa ba,
sannan ta ce a hankali kamar mai
tsammanin dan da ke cikin nata
zai ji abin da take cewa Allah ya
raya min kai ka ji
IMRAN
wannan shi ne sunan da ta
kudurce a ranta za ta sawa dan.
Sunan tsohon saurayinta abin
begenta Ko da Rabi'at ta dubi
yadda gine-gine da bisoshin
garin su ke ta giftawa ta jikin
gilashin motar sai ta yi mamakin
in har za ta sake ganinsu nan
gaba. Me yiyuwa ita da su har
abada
.
Mutuwar mahaifin su Abdul ta
girgizashi da farko sai dai kuma
daga karshe sai ya ji kamar an
daure masa nannauyan kaya
daga bayansa Domin sau da
yawa tsoron mahaifin su ne ya sa
Abdul ke rage wasu abubuwan
Bayan da aka dawo daga
jana'izar mahaifin nasu. Sagir da
Abdul suka zuna a kofar gidan
suna ta karbra gaisuwa kamar
dai yadda ake yi a al'ada
"Mene ne sanadiyyar mutuwar
tasa ne Abdul ya tambayi Sagir
lokacin da mutane suka dan
tsagaita da zuwa Sagir ya kalle
shi sannan ya ce "Abin da ya
saba damun sane hahhawar jini
kasan tun kafin na tafi Amurka
yake ta fama da cutar ashe Allah
dai ya kaddara ita zata kai shi
kushewa yau da asuba."
"Allah ya jikansa." Abdul ya ce,
gami da namijin kokarin ganin ya
sanya alamun damuwa a
fuskarsa.
"Ameen." Sagir ya amsa yana
duban Abdul cikin mamaki, bai
taba tsammanin zai yi wa
mahaifin nasu addu'a ba. Kamar
Abdul shi ma Sagir mutuwar bata
dameshi ba, domin mutuwar
mahaifin nasu tamkar wani
sabon lasisi ne a ka bashi na
sheke ayarsa yadda yake so
domin babu wani sauran me yi
masa fada.
Har zuwa magariba, mutane ba
su daina zuwa ba, Abdul da Sagir
suna ta karbar ta'aziyya. Da yake
Insifecta Rabi'u watau
mahaifinsu mutum ne mai adalci
da mutunci a zamanin
kuruciyarsa, mutane da yawa sun
girgiza da mutuwar da ya yi haka
ta karo daya babu wata doguwar
rashin lafiya.
Abdul bai tashi tunawa da Bose
ba sai bayan karfe shida da Rabi.
Shi kansa bai san abin da ya
mantar da shi ba, to amma a
tunaninsa yawan mutanen da ke
zuwa gaisuwar ne ya mantar da
shi wanda da yawa daga cikinsu
suna zubar da hawaye sharaf-
sharaf suke zuwa. Abdul ya mike
tsaye sannan ya ce da Sagir.
"Zan je gida na dawo, ka san ko
matata ban fadawa ba, tun da kai
da kaje kin fada min ka yi." Sagir
ya dube shi, sannan ya ce.
"Ka ga kada ka rana min hankali,
ka ce kawai za ka je gurin Bose,
na ga fa shigarta gidan, na kuma
ga lokacin da matar taka ta fita
tana sharar hawaye, duk a kan
idanuna." Abdul ya dubi Sagir
cikin kaduwa.
"To...to kai kana ina lokacin."
"Kaga Abdul yi tafiyar ka ni ban
rike ka ba ban kuma hana ka ba
abin kawai da nake son na
gargade ka akai shi ne, idan ka
san wulakanta yarinyar nan zaka
yi to ka sake ta sai ka ci gaba da
neman matan ka, ban hana ka
ba, amma ina tabbatar maka da
cewa muddin ka ci gaba da haka
to wata rana za ka ga ba daidai
ba, ka yi a hankali ba ka san mata
ba ne, suna iya jure komai amma
banda kishi, irin wannan ne wata
mace ta harbe mijinta a Amurka,
kwanaki biyu ya rage na dawo
gida." Sagir ya dan yi shiru yana
duban Abdul wanda ke tsaye
cikin kaduwa yana dubansa.
"Ai gara ka tafi kada ka bari
Rabi'atun ta dawo gidan su
hadu, domin suna iya yin rigima,
kuma ka z ka kwana ciki, tun da
matarka na da ciki, idan
karuwarka ta lahanta ta kai ta
janyowa, ba ka san mata ba ne
har yanzu." Sannan ya dada da
cewa.
"Ai muna tare da makwabcinka
Alhaji Ibrahim ina sanar da shi
rasuwar baba na ga fitowar
Rabi'atun daga gidan, ba a dade
ba kuma na ga Bose ta zo, ni
daman ina gani na san abinda ka
kulla. To ka yi a hankali mata sun
fika sharri sau da yawa sai ka yi
musu abu kana zaton ka ci Bulus,
to wallahi ba ka ci ba, domin idan
ka yi wasa sai ka yi amanta...".
.
Maganganun Sagir na ta
kururuwa cikin kwakwalwarsa
ya isa gidan. A motar Sagir ya zo
gidan, domin gudun kada ya
shigo motar haya ya bata lokaci
har Rabi'at ta dawo ta sami Bose.
Gashi kuma ya ce da ita ta dawo
bayan magariba. Bakwai saura
minti biyu kacal ya iso, yana
zuwa ya yi fakin da motar Sagir
cikin gareji kusa da tasa sannan
ya nufi saman benen da gudu.
"Bose Darling!". Ya kwalla mata
kira shiru ta gaida kunnuwansa.
"Bose kina ina ne!". ya sake
kwalla mata kira shiru dai babu
motsi. Abdul ya yi murmushi, ya
san dole ne Bose ta yi fushi
saboda barin ta da ya yi na
tsawon lokaci. Ya nufi kofar
dakin yana fito. Ya san dole ne su
hau sama da Bose kafin ya
shawo kanta.
Ya tura kofar dakin.
"Bose....". Ya yi shiru bai karasa
ba cikin mamaki. Lafiya Bose ya
Yaga Bose haka a kwance har
yanzu..........????ACI BULUS - 7
.
"Bose....". Ya yi shiru bai karasa
ba cikin mamaki. Lafiya Bose ya
ga Bose haka a kwance har
yanzu, Abdul ya san cewa Bose
gwana ce wajen barcin rana,
amma bai yiwuwa ace har
magariba tana kwance, abin
mamaki kuma shi ne wai har da
lillibe da wannan uban zafin.
Abin na da ban mamaki. Tabbas
Bose ba ta da lafiya.
Abdul ya matsa bakin gadon
sannan ya dan daki Bose a
gadon baya.
"Bose...bose tashi mana me ke
damunki...?".
Ya ji tsigar jikinsa ta tashi, domin
lokacin da ya ke dukan bayanta,
sai ya ji kamar ba jikin mace yake
duka ba, domin abin da ya ke
duka ya yi tauri da wuya a iya
kiransa jikin mace, sai ya ji kamar
yana dukan buhun siminti. Ya
mika hannunsa sai ya ga kudaje
sun yi sama buuu!! Mamaki da
fargaba suka kama shi, sannan
ne to ya ga wani bangare na
mayafin ya rine da wani abu jajur
kamar jini. Gaban Abdul ya fadi
ras! Kwakwalwarsa ta kasa
tunanin komai. Sannan sai ya yi
ta yan maza ya yaye mayafin.
Yawun bakinsa ya kafe cak
kamar an tsotse.
Cikin fargaba marar misaltuwa
Abdul ya dubi kumburarriyar
fuskar bose. Idanuwanta a
jirkice, harshenta ya cika bakinta,
idan ba don kayan da ke jikinta
ba sai Abdul ya rantse da Allah ba
Bose da ya sani ba ce.
Abdul ba ya bukatar sake taba
Bose domin ya tabbata gawa
yake kallo. Ya yi ta yanmaza ya
dafa jikinta sai ya ji ya yi sanyi
karau kamar kankara, jikin ya
sandare sandar-dar kamar itace.
Abdul ya mike tsaye jikinsa na
rawa kamar mazari, ya dubi
fuskar gawar da ke kwance a
kan gadon. Sai ya ji wani zazzabi-
zazzabi yana neman rufe shi, Abu
na farko da ya fara tambayar
kansa shi ne wa ya kashe Bose.
Rabi'at ta fado ransa, ya dubi
agogo bakwai da mintina biyar.
Kuma kowanne lokaci daga
yanzu Rabi'at na iya dawowa.
Abin daya kamata ya yi shi ne ya
boye gawar kafin Rabi'at ta
dawo. Da farko ya yi tunanin ya
nemi taimakon yansanda, to
amma sai ya yi tunanin me zai ce
da su, shi kansa bai san abinda
ya kashe Bose ba, shin idan ya
kirawo yansanda za su iya yarda
da cewa ba shi ya kashe ta ba
kuwa. Tabbas ko sun yarda da
labarin da zai ba su yanzu to za
su ci gaba da bincikensu.
Gabansa ya fadi ya tuno da
hayaniyar da suka yia a daren
jiya shi da Bose a (Rose Mary
Club) abin da yansandan suke
bukata su lankaya laifin kisan kan
a kansa, shi ne su sami wata
shaida da za ta nuna sun yi
hargitsi shi da Bose. Tabbas
daruruwan mutane sun ji Bose
na ta fada cikin daga murya a
daren jiya.
Abdul ya share gumin da ke sartu
daga goshinsa sannan ya nufi
baki gadon. Ya zama dole ya
boye gawar Kafin Rabi'at ta
dawo. Dole ne ya boye gawar
kafin ya yi tunanin abinda zi yi da
ita. Sai dai kuma a ina zai boye
gawar kafin ya yi tunanin abinda
zai yi da ita. Sai dai kuma a ina
zai boye gawar. A take a gurin
amsar ta zo masa. Cikin but din
motar sa. Ciccibo sandararriyar
gawar mai nauyin tsiya yayi ya
dora ta a kafada kamar tsani ya
nufi kofar dakin. A daidai lokacin
ne to aka kwankwasa kofar daki.
Abdul ya yi sororo yana haki
gawar a kafadarsa, "Wane ne
ku,a, ya tambayi kansa, Rabi'at?"
Aka sake kwankwasa kofar,
Abdul ya jefar da gawar tim a
tsakar dakin cikin kaduwa ya
nufi kofar dakin ya bude. Nasir
jakal ya yi murmushi sannan ya
ce.
"Me ka jefar ne haka na ji tim!
Kamar buhun siminti?
Abdul ya dubi Nasir (Jakal) Sororo
cikin kaduwa yana son ya yi
magana, amma yawu ya gama
kauracewa bakinsa.
"Shegen sama ina ka shiga ne
kwana biyu?". Nasir yace yana
murmushi sannan ya fara
kokarin turar da Abdul ya kauce
ya shiga dakin Abdul ya yi sauri
ya sake bambanke kofar dakinda
kafadarsa. "I...ina nan." Abdul ya
sami kansa yana cewa Nasir ya
dubi fuskar Abdul sai ya ga duk
ta yi sharkaf da gumi duk a
firgice. "To mu shiga daga ciki
mana sai wani bambanke kofa
ka ke yi kamar wanda ya ajiye
wata uwa a ciki, ko Bose din ce
ba ka so na gani a dakin
matarka." Nasir Jakal ya yi
murmushi. "Kai da Allah mu shiga
ciki, na san fa tana nan, yanzu ma
nemanta na zo, OJO ne ke son
ganinta, da gaggawa shi ne yace
da ni na nemo masa ita a duk
inda take, to sai ya ce da ni wai
duk idan ka ke ya san Bose tana
nan domin ta ce da shi wai
gurinka za ta zo." Duk maganar
da Nasir Jakal ke yi, Abdul kawai
jinsa yake yi cikin sa na kugi cikin
tsoro da fargaba. Abdul ya dubi
Nasir ya yi murmushin yake ya ce.
"Kai dai ba ka da mutunci, wallahi
yanzu kai har tsammanina ka ke
zn kawo Bose dakin matata?". "Ai
ba karamin aikinka ba ne." Jakal
ya ce yana dariya kasa-kasa.
"Nasan halin ka fa, malamin
bariki, ai iskancinka ya fi da haka
na san baka da kyau ne, na san
idan ka yi niyyar kawota ma kana
iya korar Rabi'atun tun da ba
damuwa ka yi da ita..." "Kaga
idan ka fara magana ka yi ta yi
kenan kamar mai wa'azi sani
kanka ne ina da guri-guri da
dama da zan iya kai Bose ba tare
da na kawo ta gida na ba to ka
ga
ni rabona da Bose ma ya fi
kwana biyar." Murmushin da ke
fuskar Nasir Jakal ya subuce
sannan mamaki ya maye gurbin
murmushin. "Haba Abdul kada ka
raina min hankali mana, jiya ma
fa da daddare kuna tare, kuma
Ojo ya ce da ni gurinka Bose ta
tafi, domin ba ta taba tafiya wani
guri ba ba tare da ta sanar da
Ojo ba. Amma yanzu don rainin
hankali sai ka ce da ni wai
kwananka biyar ba ka ganta ba,
a'a kwananka dubu!". Abdul ya
dubi Nasir cikin fushim domin ya
fara isarsa, duk ya matsu ya bar
gidan, domin ya san ba karamin
hadari ba ne Nasir jakal ya ga
gawar Bose dan kuwa yana iya
tsorata ya tona masa asiri. "To
shi Ojo ubanta ne da duk idan za
ta tafi sai ta sanar da shi." Abdul
ya ce. "Ba ubanta ba ne, amma ka
san a harkar Zaman bariki ya fi
ubanta, domin Ojo shi ne ya
kawo Bose garin nan tun tana
karama, shi ne ya daga ajinta a
idon samari har ake
warwasonta, ka ga kuwa ai dole
ne duk inda za ta ta sanar da
shi." Abdul ya kauce daga kofar
dakin, sannan ya juya a hankali
kamar zai shiga dakin sai kawai
ya janyo kofar dakin garam! Ya
rufe, sannan ya dubi Nasir Jakal
ya ce. "Ka je ka ce da Ojo din.
Bose ba ta guri na, idan ma tace
da shi gurina ta zo to ka ce karya
take kuma..." Nasir ya katse shi
cikin fushi. "Ka ga Abdul ni ba
yaro ba ne, tunda abin naka ya
zama wulakanci shi ke nan, mene
ne na boye-boye, ni yanzu har ni
za ka kife da kwando don ka
kawo karuwa dakin matarka,
ashe kurarin da ka ke, na cewa
kai ne malamin yan bariki ya
zama shirme. Ni zan tafi kawai ka
gane, daman na fuskanci a yan
kwanakin nan tun da ka shigo
cikin kudi ka ke wani neman
dizdizga mutane, to idan kana
ganin kudin ka muke bi an daina
zuwa gurin naka, Ojo kuma zan
ce
da shi Bose tana gurinka amma
ka hana ta zuwa." Kafin Abdul ya
maida martani tuni Nasir Jakal ya
juya cikin fushi ya nufi kasan
benen daf! Daf!! Daf!!. Abdul na
tsaye a bakin kofar benen yana
duban Nasir Jackal har sai da ya
fice daga gida. Abdul ya yi ajiyar
zuciya a lokaci guda kuma ya sa
gefen hannun rigarsa ya goge
fuskarsa. Sannan ya juya a
hankali jikinsa na rawa ya sake
bude kofar dakin ya dubi gawar
Bose kwance ta yi sandar-dar.
Hanjin cikinsa ya yamutse, ya
zama dole ya san duk yadda zai
yi ya boye gawar kafin ya yi
tunanin inda zai jefar da ita.
Abdul ya sunkuya a hankali ya
tallafo kan gawar ga mamakinsa
sai ya ji hawaye ya fara sartu a
kan fuskarsa, ya tuno irin zaman
da suka yi da Bose, ya tuna sa'ar
da suka fara haduwa da ita a
Rose Mare Club duk cikin yan
matan Abdul babu wacce yake
kauna kamar Bose shin wa ya
kashe Bose? Abdul ya tambayi
kansa. Sannan ganin cewa bashi
da amsar tambayar, sai ya sake
ciccibar gawar ya dora ta a
kafada ya tura kofar dakin
sannan ya nufi kasan benen da
gawar a kafada da kyar yake
numfashi
***
Garejin da Abdul ke ajiye motarsa
kofa biyu ce da shi, a kwai kofar
garejin ta waje wacce da ita ne
ya ke amfani gurin shigar da
motarsa idan ya dawo. Sai kuma
kofa ta biyu wacce ita daga
zauren gidan ta ke, wacce ta
cikinta ne Abdul ke shiga garejin
ta zauren gidan da ita ce Abdul
ke amfani a duk sa'ar da zai fitar
da motar daga gareji. To yau ma
kuma sai gashi zai yi amfani da
kofar garejin da ke zauren gidan
sai dai wannan karon ba shiga
zai yi ba ya bullo ta can ba
DOMIN......ACI BULUS - 8
.
Sai dai wannan karon ba shiga
zai yi ba ya bullo ta can ba
DOMIN
kuwa ko ya shiga dole ne ya
dawo ta inda ya shiga tunda
kuwa dauke yake da gawa a
kafadarsa
Abdul ya sunkuya da kyar yana
nishi, ya aje sandararriyar gawar
a kan daben da ke zauren cikin
gaggawa ya janyo kofar gidan ya
rufe domin gudun kada Allah ya
kawo wani bakon ba zata ya
kama shi da gawar dumu dumu
a hannu
Rigarsa ta jike sharkaf da gumi ta
kowanne bangare sai diga yake
yi kamar kuturu A haka ya nufi
kofar garejin da ke zauren cikin
gaggawa ya bude ta sannan ya
dawo ya sake sungumar gawar a
kafada ya nufi cikin garejin
Agogon da ke saman benen
gidan ya buga kararrawar sa da
ke nuni da cewa yanzu fa karfe
takwas na dare Gaban Abdul ya
fadi lokacin da ya ji kararrawar
agogon tana ruri domin ya san
ko wane lokaci daga yanzu
Rabi'atu na iya dawowa tun da
babu mamaki Rabi'at jira take sai
an yi sallar Isha za ta dawo. Dole
ne ya boye gawar cikin but din
motar kafin ta dawo domin ya
san indai har ya boye gawar a
bayan motar to babu abinda zai
hana shi fita cikin tsakar dare ya
jefar da gawar daga nan kuma
atunaninsa ya tsira kenan sai dai
kuma ya dawo ya yi tunanin
wanda ya kashe masa Bose..."
Tunaninsa ya katse sakamakon
duhun bakinkirin da ya mamaye
shi a acikin garejin. A can wani
bangare na Unguwar yaran
makwabta suka dauki shewa
(NEPA!!)
Abdul ya yi gunaguni sannan ya
ce kai Allah ya tsine wa (Nepa)
din nan. Abdul ya sunkuya a
hankali da nufin ya ajiye gawar
sai ya ji ya dunguri bayan motar
domin duhun ya hana shi ganin
gabansa don haka, sai ya kintaci
inda bazai sake cin karo da booth
din motar ba ya kwantar da
gawar domin ya sami damar
laluben (Lighter) abin kunna
sigarin sa da ke aljihunsa to
amma sai ya ji ya sake dungurar
bayan wata motar sannan ne to
ya tuna da cewa ashe motoci
biyu ne a garejin da motarsa da
kuma motar yayansa. Don haka
sai ya lallaba a hankali ya jingina
sandararriyar gawar a jikin
bangon garejin ya dafe ta da
hannu daya sannan ya lalubi
aljihunsa domin ya dauki
(Lighter) din dazai kunna don
ganin haske a daidai lokacin ne
to ya ji kararrawar da ke zauren
gidan ta dauki ruri. Gaban Abdul
ya fadi tsoro ya kama shi
sannan babu zato babu
tsammani sai ya ji an fara bugun
kofar gidan sannan sai wata
murya ta biyo tana cewa.
"Abdul! Abdul!!, ka bude mana."
Ba muryar kowa ba ce muryar
yayansa ce Cikin gigita sai Abdul
ya saki gawar ta sulale ta fadi
kasa tim! Sannan cikin gaggawa
ya laluba aljihun wandonsa ya
dauko yan mukullan motocin
guda biyu Abdul ya kasa gane
wanne ne dan mukullin motarsa
a ciki domin duhun da ke garejin
bai barin sa ya gani gashi kuma
tsoro da fargaba sun hana shi ya
yi amfani da hankalinsa don
gane wanne ne dan mukullin
motarsa daga cikin tunda ya
saba rike shi. Aka sake buga
kofar "Abdul".
Cikin gigita sai Abdul ya zabi daya
daga cikin yan mukullayen motar
sannan ya jefa daya a aljihunsa,
cikin gaggawa ya lalubi bayan
but din daya daga cikin motocin
biyu, tsoro da fargaba da
kidimewa, sun mantar da Abdul
bangaren da tasa motar take, to
amma sabo da yana tunannin
dan mukullin dake hannunsa na
motarsa ne sai kawai ya lalubi
wajen bude but din motar ya
tura dan mukullin ciki, cikin sa'a
sai ya ji dan mukullin ya shiga,
Abdul ya murza dan mukullin sai
but din ya bude. Ya juya da sauri
ya yi lalube cikin duhu yana
neman gawar sai ya ji hannunsa
ya taba wani abu kamar kafar
mutum, kuma ga alamu mutumin
a tsaye yake, cikin fargaba sai ya
yi sauri ya dauke hannunsa,
sannan ya sake lalubawa sai
hannayensa suka taba kan
gawar Bose, Abdul ya tallabo kan
Bose sannan ya dago ta sama da
duk karfinsa ya jefa ta ciikin but
din motar ya rufe, sannan ya
ruga da gudu ya nufi zauren
gidan yana zuwa sai ya bude
kofar gidan ya dauka Rabi'at ce.
A tsaye a kofar gidan, idanunsa
boye cikin bakin tabarau, Sagir
ne yayan Abdul. Abdul ya yi turus
kamar wanda ya ga fatalwa.
"Wanne irin iskanci ne haka zaka
rufe kofa haka da wurwuri,
kasan kuma zan zo na dauki mota
ta, kai fa ka ce da ni yanzu za ka
dawo, ka sa na yi ta jiranka, ban
dan mukullin motata." Sagir ya
mika masa hannu, sai a lokacin
ne Abdul ya lura da cewa ashe
dan mukullin motar da ya jefa
gawar a but din ta har yanzu
yana hannunsa, sannan kuma
dan mukullin motar na sagir ne.
Hantar cikin Abdul ta kada, ko
shakka ba ya yi ya san ba a cikin
but din motarsa ya boye gawar
ba, a cikin but din motar Sagir ne
"Bani mukullin mana sauri na ke
yi." Sagir ya ce Abdul ya rasa
yadda zai yi sai ya mika masa
dan mukullin
Sannan ya juya
cikin sauri kwakwalwarsa duk ta
rikice, ya bude masa kofar
garejin ta waje, sannan sagir ya
shiga garejin bai damu da duhun
da ke ciki ba, yana lalubawa ya
gane motarsa, ya bude ya shiga
sannan ya fice daga garejin da
gudu, bai ko damu da ya sake
duban Abdul ba.
Abdul ya yi sororo yana kallon
bayan motar Sagir sa'ad da yake
fita daga layin. Abin da Sagir bai
sani ba shi ne Gawar Bose na
kwance cikin but din motarsa.
Abdul ya juya jikinsa na rawa ya
shiga cikin garejin da niyyar ya
rufe kokofin garejin kafin ya yi
tunanin abin yi. Sannan ne to ya
ji wani hannu ya sulalo ta cikin
duhun daren ya dafa kafa darsa,
Abdul ya juya a tsorace ya ce.
"Wane ne?". Wata murya tace da
shi.
"Lallai Abdul ashe abin naka ya
fara nisa haka, daga malamin
bariki kuma ka koma kisan kai!".***
.
Sagir ya ja birki a gaban yan
samarin. Kayan marmari fal a kan
teburin da ke gabansu, akwai
ayaba, lemo gwanda, da Tufa kai
har da biredi a can gefe guda to
amma tufa din ita tafi daukar
hankalin Sagir, domin ko sa'adda
ya ke Amurka, babu abin da ya fi
so a kayan marmari irin tufa.
Sagir ya sauko daga motar.
"Malam me ka ke so?". Wani
saurayi fari mai fuskar dolaye ya
tambaye shi.
"Tufa." Abdul ya amsa kai tsaye.
Bayan wasu yan dakiku, yaron ya
zubawa Sagir Tufa din da ya saya
cikin jakar leda, sannan ya nufi
bayan motar da ita. Sagir ya bishi
a baya ya bude masa bayan
motar. Yaron ya daga jakar ledar
zai sa a ciki, sai ya yi tsalle gefe
guda cikin kaduwa.
"Mene ne." Sagir ya tambayi
yaron.
"Leka ka gani." Yaron ya ce a
tsorace, cikin mamaki sai Sagir ya
leka but din motar. Hasken kwan
lantarkin da ke makale a jikin
rumfar kayan marmarin ya isa ya
nunawa Sagir fuskar gawar
Bose, idanunta a juye, harshenta
a waje, sagir ya rufe fuskarsa
cikin kaduwa.
"Wayyo Allah!! Bose ce!!".
.
WAN NAN SHINE KARSHEN LITTAFIN
ACI BULUS BOOK ONE
ZAMU DORA DAGA
LITTAFI NA BIYU
.
SAURAN samari ukun da suka
rage a majalisar suka mike tsaye
zunbur lokaci guda,
"Mu tafiya zamu yi" wani daga
cikinsu yace, Imran yayi frgigit
daga cikin al'adar tunanin da ya
sabawa kansa tun watanni shida
da suka wuce. "Haba dai tun
yanzu zaku tafi, ku bari mana su
Ishaq su karaso." Wani dan
gajere daga cikin samarin ya
dubi Imran sannan ya girgiza kai
yace, Zaman majalisar in babu
hayaniya ba dadi, sai kaga duk
anyi jugum-jugum kamar masu
jiran sakamako". To ai shi yasa
nace daku kuyi jiran su Ishaq su
karaso, samari biyu daga cikin
ukun suka yi gaba suka bar
dayan tsaye akan Imran yana
kokarin nuna masa cewa su fa
basu iya zaman majalisa babu
hayaniya, daman shine shugaban
majalisar, to kuma shi yanzu
gashi ya shiga halin kurame.
"Idan anjima zamu dawo, kaga
kafinnan majalisar ta cika, kaga
kuma sai ka samu damar
tunaninka a nutse ba tare da
surutun mu sun dame ka ba."
Kafin Imran ya sami ta cewa tuni
daya saurayin daya rage a gurin
ya dafewa sauran biyun da suka
yi gaba baya. Imran yayi imani da
cewa tunda Allah ya jeho dashi
wannan duniya mai hargitsi iri-
iri, bai taba ganin hargitsin
rayuwa da tsananin tashin
hankali ba irin na wadannan
bakaken watanni shida kamar
yadda ya kira su. Hakika rashin
masoyi ba karamar masifa bane,
domin rayuwa takan dagula
tunani ya hargitse sannan kuma
rashin nutsuwa da tashin hankali
sukan yi hadin gwiwa su fada
wa shi wannan gangar jiki daya
rasa abin kaunarsa. Imran bai
san da haka ba sai bayan daya
rasa masoyiyarsa, sashen jikinsa
a yadda ya kirata, Rabi'atu. Da
farko da har Imran ya saduda, ya
fitar da komai daga ransa, tun da
dai ya tabbata babu makawa
Abdul ne zai aure masa Rabi'atu,
to amma fa da zarar anyi kiran
sunanta, kai ko arubuce ya ga
sunan, sai duk narkakkiyar
kaunar nan mai azabar da zuciya ta dawo ta mamaye tasa zuciyar, akwai lokutan ma da har
yakan guji bi ta guri indai har
yana tsammanin za'a tuna masa
da abar begensa domin tuna
masa da ita shi yafi komai narka
zuciyarsa a duniyar nan tun da
dai ya tabbata ya rasa Rabi'atu
har abada. Da yawa daga cikin
abokan Imran sun dauka Imran
ya kama hanyar zarewa ne, dan
haka yake yawan tunane tunane,
yayin da wasu kuma kadan daga
cikinsu masana harkokin rayuwa
kance Allah sarki Imran har
yanzu dai yarinyar nan ce ke
ransa, shi yasa yake yawan
tunane-tunane. To koma dai me
ne ne Allah ne kawai masanin
halin da Imran ke ciki.
"Imran" wata murya ta kira sunansa daga
baya. Imran ya juyo a hankali ya
dubi dogon saurayin dake tsaye yana..ACI BULUS - 9
.
"Imran" wata murya ta kira sunansa daga
baya Imran ya juyo a hankali ya
dubi dogon saurayin dake tsaye
yana murmushi kyakykyawa ne
in banda sharbeben billen da ya
mamaye rabin fuskar sa, babu
abin da zi hana ya wuce a
matsayin kwararren jarumi
kyakkyawa na shekarar. Saurayin
sanye yake da doguwar riga da
wando na shadda launin toka
kansa babu hula dogayen
kafafun sa sanye cikin bakin
takalmi Sannan a rataye a
kafadarsa jakace katuwa irin ta
matafiya launin kasa-kasa tana
reto kamar mushen zakara jikin
danga
Sunana Abdussamad
Dogon saurayin yace har yanzu
dan saurayin murmushin nanan
makale a kyawawan fatar
bakinsa Imran ya dubi saurayin
tun daga sama har kasa, irin
duban da likita kan yiwa mara
lafiya a duk sa'ad da yace wayyo
cikina to amma har zuwa
sa'adda idanuwansa suka zo ga
takalman saurayin Imran bai
gane ko wanene ba kai a iya
sanin sa ma shi kan bai taba
ganin saba Nasan cewa baka
sanni ba nima kuma ban san ka
ba don haka kada ka bata lokaci
gurin tunanin sai ka gano ko ni
wanene domin kuwa baka sanni
ba Yayi shiru yana duban Imran
sannan a hankali cikin sandar da
ta yiwa hawainiya tazara da
kadan sai ya zura hannunsa cikin
aljihunsa ya zaro farar Ambulan
ya mikawa Imran "Gashi
Saurayin yace "Wata ce tabani
adireshin ka tace idan na karaso
garin nan na baka wannan shine
to da na zo gidanku yara suka
rakoni nan Imran ya dubi
dogon saurayin cikin mamaki
sannan kuma lokaci guda ya fara
tunanin anya kuwa kansa daya
to sai dai kuma tun daga sama
har kasa babu ta inda yayi kama
da mai tabin hankali Wacece
kuwa wannan ita batada suna?
Imran ya bukata adai dai lokacin
da hannun sa ya karbi wasikar
Dogon saurayin ya shafi habar sa
cikin kaguwa daya bar gurin.
"Tace dani idan ka karanta za ka
ga komai a ciki amma ni bata
fadamin sunanta ba domin nima
a tashar garin Dan'asi muka
hadu da ita shine tayi ta yimin
magiya tace don Allah nayi kokar
na kawo maka wannan. "Malam
yaya kam...manninta suke?"
Imran ya tambaya a rude
murmushin dake fuskar
mutumin ya subuce sannan
damuwa ta maye gurbin fuskar
"Haba malam wacce irin tambaya
ce wannan yaya za'ayi na tsaya
kallon matar da ba maharramata
ba kawai daga mun tsaya ta bani
sako kaima ai kasan ba zai yiyu
ba ina ganin idan babu damuwa
to ni zanyi gaba domin motarmu
tana tasha tana jirana don in
banda sakon kama da babu
abinda zai shigo dani cikin garin
nan." "Mutumin ya yi shiru
sannan sai yaci gaba da cewa,
"Abin da na lura dashi kawai
shine matar tana cikin wani irin
matsananncin hali da bakin ciki
domin baka ganta ba, dole ka
tausaya mata." Kafin Imran ya
farga mutumen ya juya gami da
cewa "Sai anjima." "To na

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment