Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakin Aliyu Rashid.
Acan kuma waje gurin da masu
jinyar marasa lafiya ke zazzaune
Imran da mahaifiyar Aliyu Rashid,
gami da mahaifiyar Rabi'atu tare
da yan uwanta su goma sha
daya. Domi lokacin da Imran ya je
musu da labarin mahaifin
Rabi'atu bayanan, kafin wasu
lokuta, tuni rade-radin labarin ya
watsu a kusan duk rabin asibitin
kamar wutar daji.
Tunda mahaifiyar Rabi'atu tazo
gurin take kuka, su kuma sauran
matan suna ta bata hakuri, gami
da dada jaddada mata cewa
komai fa me wucewa ne in Allah
yaso.
"Sai dai munji daga bakinta
insfecta Ja'afar yace da Aliyu
Rashid.
"Domin ba zamu iya yadda da
abin da kace ba, sai in munji
daga bakinta."
A daidai lokacin ne to, malamar
asibitin ta kwankwasa kofar
sannan ta shigo tana rausaya.
"Yallabai kuna iya ganinta yanzu."
Aliyu Rashid ya mike jikinsa na
rawa yace:
"Yaya jikinnata."
"Da sauki, daman cikinne ya sami
yar tangarda, to amma yanzu ya
koma yadda yake, da dai ace kun
dauki tsawon lokaci baku zo
asibiti ba, to da juna biyun
zubewa zai yi me yiyuwa ma
itama ta mace a hannunku." Aliyu
Rashid yayi ajiyar zuciya sannan
ya juya yabi bayan Insfecta
Ja'afar da sajen Danlami
wadanda tuni su sun kai kofar
dakin.
Sauran yan uwa da abokan arziki
dake zazzaune a dakin jinyar
suka dubi yansandan biyu tare
da Aliyu Rashid ayayin da suka
nufi dakin da Rabi'atu take, koda
suka karasa kofar dakin sai
Insfecta Ja'afar ya juya ya dubi
Aliyu Rashid gami da tattausan
murmushin dake cewa kada ka
damu, yace.
"Ina ganin da zaka dan jiramu a
waje da yafi, domin mu kadai
muke son ganawa da ita."
Kafin Aliyu Rashid yace wani abu
tuni yansandan biyu sun wuce
cikin dakin, suka rufe kofar dum!
A fuskar Aliyu Rashid.
Mahaifiyar Rabi'atu ta taso tana
kuka ta tari Aliyu Rashid tace. Me
ake cikine bawan Allah?".
"Kada ki damu in Allah yaso babu
abin da zasu yi mata" Aliyu
Rashid Yace.
Mahaifiyar Rabi'atu ta sake
fashewa da kuka. Acan gefe
guda Sagir da Imran na zaune
basa ko wani kwakkwaran motsi
kowa na karatun wasikar jaki.
******
Karfe hudu dai-dai suka fito daga
dakin. Mutane gaba daya suka
bisu da kallo. Aliyu Rashid ne ya
fara bin yansandan a baya."
"Yaya ake ciki yallabai"
"Kada ka damu" Insefecta Ja'afar
yace dashi."
"Labarinta akwai alamar gaskiya,
amma babu wani abu indai
hukuma ta tabbatar da cewa
labarinta gaskiya ne, to tana iya
tsira tunda tsaron kanta tazoyi,
kuma ba niyyar ta bace ta kashe
Bose, musamman ma idan akayi
la'akari da juna biyun dake
jikinta. Yanzu dai zamu bar
yansandannan uku anan, mu
kuma zamu je mukai maganar
gaba, domin Ojo Uban gidan
Bose ya shigar da kara, amma
kada ku damu, ku dai kawai ku
dauki lauya, ammam ina tabbatar
maka babu inda Ojo zashi, domin
(Club) dinma nasa dayake tara
yayan iska irin su Bosen an
rufeshi tunda Allah ya kawo
mana rahamarsa, ansamu canjin
shugaba mai Adalci."
"To insfecta na gode." Aliyu
Rashid yace, gami da ajiyar
zuciya.
"Ba komai." Insfecta Ja'afar yace,
sannan ya miko musu hannu
suka gaisa, shima sajen Danlami
ya miko hannu suka gaisa
sannan yace.
"Acikin yansamarin can wanene
Sagir, idan yana gurin kuce dashi
wai Rabi'atu tana son ganinsa."
Yansandan biyu suka yi gaba
abinsu, sannan yan uwan
Rabi'atu suka zo suka zagaye
Aliyu Rashid, wanda ya fara yi
musu bayani akan su kwantar da
hankalinsu babu abinda zai faru.
Adai dai lokacin ne to ya dubi
Sagir yace.
"Kaje tana son ganinka, amma
kayi sauri ka fito domin
yanuwanta da kuma mu kanmu
muna son muje mu duddubata.
To amma yanzu dai sai kaje babu
mamaki wani abun ne take son
fada tunda tace kai kadai take
son gani."
Sagir ya juya ya nufi dakin da
Rabi'atu take, sauran mutanen
kuma suka bishi da kallo Imran
yayi mamakin me Rabi'atu ke son
fadawa Sagir ne take son
ganinsa shi kadai. Allah ya tserar
da abar kaunarsa Rabi'atu, yace
cikin zuciyarsa, domin ko yanzu
shi mai iya aurenta ne.
Sagir ya tura kofar dakin a
hankali ya shiga, sannan ya dubi
Rabi'atu, Rabi'atu na kwance
tana kallonsa. Fuskarta ta kara
fari, haka nanma idanunta.
"Sannu Rabi'atu" Sagir yace a
sanyaye.
"Sagir! Sako zan baka ka kaiwa
Abdul "Rabi'atu tace a hankali
kusan a cikin rada, Sagir ya
dubeta kawai, amma bai amsa
ba. Rabi'atu taci gaba da cewa.
"Idan kaje kace dashi, bana
kaunarsa, na tsaneshi, bana
kuma sake kaunar ganin
mummunar fuskarsa mai munin
hali, kace dashi, Allah ya
dawomin da masoyina Imran, shi
zan aura indai Allah ya tserar
dani daga kangin dana shiga.....".
Tayi shiru tana shesshekar kuka
sannan tace gaba da cewa.
"Sagir, kace dashi nayi bakin ciki
da banyi barin dansa ba, kace
dashi naso juna biyun dake jikina
ya zube domin na tsane shi
saboda shi"
"Sagir ya dubta, sannan hawaye
suka fara zuba daga idanunsa.
"Ki yafe shi Rabi'atu, don Allah ki
yafe masa, domin indai don
Abdul ne to kisa ranki a inuwa,
domin kuwa Allah ya dauke
abinsa, Abdul ya mutu ya barki,
ya kuma barni a duniya ba Uwa
ba Uba, ba kuma wani dan
uwana na jini sai wannan dan
dake jikinki, dan da kike cewa
kin tsana, idan kin haife shi
Rabi'atu, ni inaso ki kawomin shi,
domin kuwa bani da wani dan
uwa a duniya sai shi."
Kafin ta farga Sagir ya fice daga
dakin da gudu yana kuka.
Rabi'atu ta fashe da kuka. Ba
mutuwar Abdul take yiwa kuka
ba, sai dan da zata Haifa maraya,
ba Uba shi take yiwa kuka.
.
ƘARSHE
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment