Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruwan
shayin, wadanda da yawa daga
cikinsu duk manoma ne da
leburori, wadanda kuma sukayi
imani da cewa wai ruwan shayin
maganin basir ne, sai ya juya a
karo na farko ya dubi
kyakkyawan saurayin dake tsaye
a gefen teburin shayin tun kusan
mintina biyar da suka wuce yana
jiransa.
"Uhm Hum! Malam me kake so,
sai hakuri fa, kasan in mutane
sukayi ma yawa sai ka rasa ma
mezakayi".
"Tabbas" Imran ya amsa, gami da
nazarin tauyayyiyar riga dake
jikin mai shayin daya tabata
rabonta da ganin ruwa tun na
daminar bara."
"Daman dan Allah wata mace
nake tambaya wacce nake
tsammanin ta sauka a garinnan
jiya, ban sani ba don Allah ko kai
kaga inda tayi tunda kai anan
kake sana'arka."
imran yayi shiru yana jiran amsar
mai shayin tuni gumi ya fara
sartu bayansa me yiyuwa ko dan
saurayin hantsin ranar daya fara
dukan bayansane, babu mamaki
kuma shirun da yaga duk jama'ar
dake gurin sunyi suna
saurarensa ne ya sashi diga ta
baya kamar ledar ruwan sanyi.
"Ih to, bana ce ban ganta ba,
hakan kuma bana na ganta ba."
me shayin yace yana kifkifta
idanu kamar birdiddigi."
"Domin Allah ne yasan yawan
matan da suka sauka a garin nan
jiya, koda yake mafi yawa daga
cikinsu karuwai ne masu gudun
shari'a daga birni zuwa kauye, to
amma zai yi wuya na iya
tantancewa ko wacece takan
daga ciki tunda dai ni ba kai
bane, kuma bansanta ba, sai
yanzu kai daka zo min da
tatsuniyar."
"Farace doguwa mai kauri amma
ba sosai ba, ina tsammanin kuma
tana dauke da jaka." imran yace
yana duban maishayin gami da
addu'ar Allah sa yaga Rabi'atun.
Mai shayin ya daga kansa sama
yana tunane tunanen karya,
domin kuwa ya tabbata matar da
Alhaji Rashid ya dauka ce jiya da
daddare.
"To, in banda abinka ai duk
kusan matan da jakunkuna suke
zuwa, to amma... uhm" Ya sake
yin shiru yana tunanin karya.
Sannan yaci gaba da cewa,
"Ina ganin naso naga wata mace
jiya mai kama da wacce kake
siffantawa, sai dai kuma ita
waccen din wani mutum ne ya
dauke ta a mota jiya da daddare,
to amna kayi sa'a dannan
garinne sai dai kuma a cewarsa
yau zai bar garin da sassafe
domin ma'aikacin gwamnatine a
can birni." Me shayin ya washe
baki cikin abinda yake
tsammanin wai murmushi ne.
"Ai kaima naga hala daga birnin
ka fito ko, bari in kwatanta maka
gidan kaje, ko Allah yasa ka dace,
idan itace to shikenan idan kuwa
ba ita bace to kana iya dawowa
sai a sake bincikawa gurin yan
yuniyon din can na tsangayar
arewa, mai yiyuwa su sun ganta.
"Yar uwarka ce ne?" ***
.
"Da...daga nan shine naga
ni...ba...bazan iya zama ba su
kashe ni da wannan cikin dake
jikina shi...shine na gudu."
Rabi'atu ta fashe da kuka lokacin
da ta kawo karshen labarin.
"Daina kuka yarnan kin ji, dena
kuka in Allah yaso babu me
tabaki, ai ba da gangan kika
aikata ba, kaddara ce." To amma
duk da hakurin da mahaifiyar
Aliyu Rashid ke baiwa Rabi'atu,
itama hakan kuma bai hanata
zubar da hawaye ba cikin
tausayawa. Aliyu Rashid ya
girgiza kai cikin tausayin abinda
yaji daga bakin wannan
kyakkyawar mace, abinda ya
kasa fahimta shine, soyayyar ta
tsakanin Imran da Abdul, domin
acewarta, Imran take so, kuma
tace bata taba son wani ba sai
shi, hakanan kuma iyayenta basu
takura mata akan dole sai ta auri
wanda bata so, to idan hakane
kuwa menene dalilinta na auren
Abdul, Babu amsa, kuma har
yanzunnan daya sa Rabi'atu a
gaba cikin tausayi, bai zo koda
kusa da amsarba.
A cikin katon falon mahaifiyar sa
suke zaune, lokacin da ya
dauketa a daren jiya sai yaga
babu abinda zai iya yi da ya wuce
ya dauketa ya kaita gidansu wato
inda mahaifiyarsa take, idan gari
ya waye sai ya tambayeta
labarinta, domin da ganinta kai
ka san tana cikin tashin hankali
mara misaltuwa, wani kuma abin
bakin cikin ga al'amarin da
tausayi shine juna biyun dake
jikinta. Aliyu Rashid yasha
karanta labarai na ban tausayi, to
amma bai taba ganin abin
tausayin da yafi na Rabi'atu ba,
koda yake lokacin da ya karanta
littafin
WANA KAMA
har kusan
hawaye ya sashi, to amma kuma
wannan wani lamarine na labari,
ba kamar....ACI BULUS - 13
.
Koda yake lokacin da ya karanta
littafin WANA KAMA har kusan
hawaye ya sashi to amma kuma
wannan wani lamarine na labari
ba kamar wannan ba da yake
faruwa a zahiri
Agogon dake makale a babban
falon Wanda a da can na
mahaifin Aliyu Rashid ne tun
kafin ya rasu ya dauki ruri karfe
tara da rabi na safe
"To yanzu dannan me ka ke gani
zamuyi da yarinyar nan, kaga dai
halin data ke ciki kuma kune a
birni ban sani ba ko akwai
abinda zaka yi ka taimaki
wannan yarinya
Mahaifiyar Aliyu Rashid take fadi
Aliyu Rashid yayi shiru yana
tunani na tsawon lokaci sannan
yace
"To, Inna wannan abu dai ba
abune mai sauki ba domin abu
ne da ya shafi kisan kai to amma
dai gaskiya daya ce kuma Allah
yana wajen mai gaskiya, ina
ganin abinda zan iyayi shine
zanyiwa lauyana maganar, ina
ganin idan har yarinyar nan zata
kai kanta ga hukuma ta baiyana
duk abinda ya faru to in Allah
yaso sai kaga ta kubuta, tunda
dai tsaron kanta tazo yi tsautsayi
yafada a kanta, da yayi
sanadiyyar da yarinya ta zame
daga benen ta fado, kinga kuwa..."
.
Sallamar da aka kwalla a waje ita
ta katse kalaman Aliyu Rashid,
mahaifiyarsa ta mike tsaye
sannan ta fice daga falon ta nufi
tsakar gidan.
"Wai ana sallama da mai
gidannan." Wani almajiri mai
yagagen gajeren wando kamar
siket yace.
"wane ne kuma yake son ganin
mai gidannan."
"Nima bansan shi ba wallahi,
amma dai ina ganin kamar daga
birni yake, yaron yace yana soshe
soshe kamar zai yaga rigar, "Bari
to in kirawo dannan ya gano ko
wanene". Ta juya da sauri ta
shiga falon.
"Ina zuwa Rabi'atu" Sannan ya
fice daga dakin.
Aliyau Rashid ya dubi
kyakkyawan saurayin dauke da
jaka, sannan kuma babu alamar
kwanciyar hankali ko farin ciki a
tattare da yanayin kyakykyawar
fuskar.
"Kaine kake son ganin mai
gidannan?"
"Nine wallahi, Alhaji barka da
asuba."
"yauwa barkan ka dai an tashi
lafiya."
"Lafiya lau." Saurayin ya amsa
sannan sai yaci gaba da cewa.
"Daman tambaya na zoyi don
Allah ko zaku taimakeni, wata
mata ce yar uwata data gudu
daga gida jiya, ta zo garin nan, to
shine na biyo sahunta, da na zo
tasha ne aka kwatantamin gidan
nan aka ce dani me yiyuwa zaku
taimakamin domin wai jiya anga
wani mutum ya dauki wata mata
bakuwa wanda kuma akace
anan gidan yake ban sani ba ko
kaine?"
Aliyau Rashid ya dubi saurayin
cikin mamakin irin yadda gumi
yake zuba kamar ruwan sama
yace.
"Me yiyuwa nine, me yiyuwa
kuma bani ne ba, ni dai abinda
nasani kawai shine jiya na sami
wata mata da daddare tana barci
a rumfar tasha, shine na tausaya
mata naga kuma ya dace na
taimaketa da gurin kwana shine
to na kawota su kwanta tare da
mahaifiyata, domin ni bama anan
nake da zama ba, iyalina suna
birni, nan dai zuwa nake yi
lokaci-lokaci kamar karshen sati
na gaida mahaifiyata da sauran
yan uwana."
"To Alhaji don Allah ko zan iya
ganin waccen din, babu mamaki
itace wacce nake nema"Imaran
yace kirjinsa na bugawa.
"Eh to, amma bana tsammanin
itace, domin ita wannan bata ce
dani tana da wani dan uwaba."
Aliyu Rashid yace yana duban
fuskarsa.
"Me tace dakai tana dashi." Aliyu
Rashid ya danyi murmushi
sannan yace da Imran " haba
Malam kana ganin ya dace na
sanar dakai sirrin wani?"
"Bai dace ba," Imran yace da
Alhaji Rashid.
"Amma don Allah Alhaji idan
babu takurawa ko zaka
taimakeni kace da ita Imran ne a
waje yake san ganinta, idan
kuwa tace bata sanniba to bani
bane."
Wani kuda yai tsalle ya fada
kunnen Aliyu Rashid ya fara yi
masa zuza a kunne Zuuu!!, hakan
shiya hada da wur-wur din da
kwakwalwarsa keyi tana kokarin
tabbatar da abinda yaji."
"Me...Imran kace". Aliyu Rashid ya
tambaya bakinsa na rawa, kallo
daya Imran yayiwa fuskarsa ya
tabbata Rabi'atu ce a gidan."
"Imran nace, kace da ita tsohon
saurayinta ne."
"Shigo daga ciki." Aliyu Rashid
yace.
"Imran, sannu Imran kaji wallahi
an cuci wannan tsohuwar
budurwar taka." Aliyu Rashid
yace yana girgiza kai.
Acan wani bangare na kofar
gidan, wani mai tallar alewar
dinya ya girgiza kai cikin mamaki
domin jin wata siririyar murya
tana shashekar kuka a cikin
gidan yallabai Aliyu Rashid.
"Lafiya kuwa gidan Yallabai?"
Me alewar ya tambayi kansa, to
sai dai kuma babu amsa sai tarin
kudaje bataliya guda dake
kokarin dauke farantin alewar.***
.
.
"Ni ban....ban...san abinda kake
magana ba" Sagir yace cikin
firgita muryarsa na rawa. "Kafini
sainin abinda nake magana akai,
ina ganin kuma ba dabara bace
kaci gaba da batawa kanka
lokaci da wannan kayan gawar a
bayan motarka ba." Nasir Jakal
yace yana murmushi sannan yaci
gaba da cewa
"Ni mai taimakon mutane ne......
Sagir, ni mai iya taimakon kane
na jefar da gawar inda bazama a
taba iya ganinta ba Domin nasan
a tunaninka yanzu kokwanto
kakeyi ka koma gidan Abdul ka
tambaye shi dalilin da yasa
gawar ta shiga but din motar ka
to bari kaji Sagir idan ka yaudari
kanka kabi ta hanyar nan
kashinka ya bushe domin
jami'an tsaro suna nan suna
cakin din motocin mutane duk
da yake dai ba dole bane su buda
but din motar to amma zaka iya
caca da hakan in zaka iya to ga
hanya nan a dawo lafiya Nasir
jakal yayi nuni da hannunsa
zuwa kan titin yana murmushi a
dai dai lokacinne agogon dake
jikin motar Abdul ya buga karar
goma sha daya na dare
Sagir ya dubi Nasir Jakal a
kideme cikin rashin fahimta duk
ya rudashi hakika kuma ya gama
tsorata
"To...to yanzu me kake son
muyi?" Sagir ya tambaya bakinsa
na rawa
"Ina ganin Dubu Dari Uku ta isa
ta kula da dukkan wata wahala
da zansha gurin jefar da gawar."
Nasir Jakal yace a sanyaye yana
murmushi. "O ho! Daman abinda
kake nufi kenan!!" Sagir yace a
fusace
"Kusan haka nake nufi Sagir
kuma gaskiya ina mai fargabar
baka da wani zabi da ya wuce ka
shiga motar ka mu koma gidan
ka ka biyani karafana ni kuwa
nayi maka Alkawari zan jefar da
ita inda ba za'a taba ganinta ba
in kuwa kaki shawarata to ina
mai fargabar baka da zabi
domin (Simply) ina iya kirawo
kurtun dansanda yanzunnan ince
dashi ya bude bayan motarka
ban yarda da kai ba shin ya zaka
so hakan?" Sagir ya dubi Nasir
Jakal cikin takaicin, to sai dai shi
ba kamar Abdul bane domin
kwakwalwarsa tana tunani fiye
da kima." "Mu tafi to" Sagir yace
Da nasir.
"Amma fa indai na baka kudin
dole ne ka jefar da gawar
"Tabbas-tabbas." Nasir Jakal yace
cikin mamakin ganin yadda Sagir
ya amince nan da nan.
Mintuna goma sha daya kacal
sunzo gidan su Sagir.
"Ina zuwa" Sagir yace da Nasir
Jakal, bayan duk sunyi fakin da
motacin a kofar gidan, Nasir Jakal
yabi Sagir da kallo cikin mamaki
anya kuwa Sagir ba yaudarar sa
zai yi ba, shifa abin ya fara bashi
mamaki, haka a saukake kamar
shan ruwa, tabbas kam akwai
wani abu a tattare da lamarin da
kesa gaban Nasir Jakal faduwa
To amma lokacin da Sagir ya fito
daga cikin gida dauke da bakar
jaka, duk sai Nasir ya manta da
fargabar sa
"Gasu ni na gama sai...sai gareka"
Sagir yace yana rawa da
muryarsa.
"Nasir Jakal ya dubi Sagir yace.
"Sai ka bani makullin motarka, ni
zan tafi, ga mukullin motar Abdul
nan ka kai masa motarsa ni
kuma gobe da safe zan dawo
maka da taka motar idan na jefar
da gawar". "yaushe zaka jefar da
gawar?" Sagir ya tambaya.
"Yau din nan da asuba."
"To shikenan, don Allah Nasir ka
rufa mana asiri kada kowa yaji
zancen nan kaga dai ni bani na
kasheta ba kuma..."
"Kada ka damu". Nasir jakal ya
katse shi,
"Ka dai zauna kayi ta addu'ar
Allah sa kada na dawo neman
karin kudi."
.
Kafun Sagir ya tanka tuni Nasir ya
fada motar Sagir ya tayar sannan
ya fice daga layin da gudu ba
tare daya damu daya kunna fitilar
motar ba, sha daya da minti
ashirin a lokacin. Sagir yayi ajiyar
zuciya sannan ya dubi danjar
motar yayi murmushi cikin
duhun daren sannan yace. Shege
ACI BULUS
in kasan wata
baka san wata ba karamin
macuci."
.
Abdul ya dubi Sagir a fusace cikin
fushi mai tsanani yace. "Yanzu
kana nufin kaima wannan dan
iskan bai barka haka ba, sai da ya
karbi wani abu daga gurin ka."
"Ni ba wannan na tambayeka ba,
na dai baka labarin ne domin in
nuna maka abin da kajefa ni
aciki, kai dan uwanane Abdul,
duk abin da ya sameka kamar ni
ya samu, ina son kasanar da ni
abin da yasa ka ai kata wannan
kisan kai..."
"Wallahi bani bane, Allah kuwa, ni
na fada maka ina baro wajen
zaman makoki nazo na sameta
kwance a kan gadona a mace,
Allah bani na kasheta ba."
Sagir ya dubi Abdul cikin mamaki,
domin a yadda yaga alamun dake
fuskarsa ya tabbata bashi ya
aikata laifin kisan kan ba, "To wa
ya kasheta, Abdul". sagir ya
tambaya.
"Ni ma shine nake fatan Allah ya
sanar dani, wallahi ban sani ba."
Samarin biyu sukayi shiru na
kusan mintuna uku suna duban
juna kowa na kokarin fahimtar
abin dake gudana a zuciyar dan
uwansa batare da sun cimma
nasara ba. Sannan ba zato ba
tsammani sai Sagir yace
"Ina Rabi'atu?"
Wani abu kamar kibiya ya soki
zuciyar Abdul sannan yawu ya
kauracewa bakinsa In banda
yanzu da Sagir ya tambaya
kwata-kwata shi a gurinsa
Rabi'atu ba'a ma hallice ta ba
Bala'i da tashin hankalin da ya
shiga a cikin sa'o'i kusan biyar
din da suka wuce su suka dauke
kusan ko wanne tunani daga
zuciyar sa sai na fuskar gawar
Bose.
.
"Ba...bata dawo ba tunda ta fita
"Kana nufin tunda ta fita da rana
bata dazwo ba dubi fa yanzu
shabiyun dare saura minti uku
"Wallahi...bata dawo ba ni kuma
duk mutuwar nan ta baba da
kuma ta Bose dana tarar itama a
mace gami da wannan dan iskan
daya damfare mu su suka rudani
na manta da ita."
Yayi shiru yana...ACI BULUS - 14
.
"Wallahi...bata dawo ba, ni kuma
duk mutuwar nan ta baba da
kuma ta Bose dana tarar itama a
mace gami da wannan dan iskan
daya damfare mu su suka rudani
na manta da ita
Yayi shiru yana duban Sagir
amma Sagir bai ko kallo shi ba
yace
"Ina ganin ta dawo gidannan
Abdul amma ka tambaya a
makwabta me yiytuwa akwai
wanda yaga dawowarta
Abdul ya mike tsaye zumbur cikin
fushi jikinsa na bari
"Wallahi banyi tunanin haka ba
kana nufin ita ta kashe Bose."
"A'a ni bance da kai haka ba."
sagir yace a tausashe kamar
yadda liman kanyi yayin radawa
jariri suna a kunnensa
"Amma ba abin mamaki bane
domin ka san mata abin tsoro ne
musamman ma idan ta sami
Bose adakinta kwance abin da
daman nake guje maka kenan
gashi kuma ina mai fargabar..."
Babu zato babu tsammani sai
Abdul yayi wuf, ya fizgi dan
mukullin motar dake hannun
Sagir ya ruga da gudu ya nufi
kasan benen
"Abdul!!" sagir ya kwala masa
kira cikin kaduwa
"Abdul ina zaka miye haka!"
Baiko juyo ba balle ma ya kalle
shi Sagir ya taso shima da gudu
ya biyo bayan Abdul. To sai dai
kuma ya makara domin kafin ma
ya gama saukowa daga kan
benen sautin injin motar Abdul
ya cika shirun dake daren lokacin
da Sagir yazo kofar gidan tuni
motar Abdul ta harba da gudu
kamar kibiya
Sagir ya dubi danjojin motar biyu
cikin kaduwa baki bude ba'a
dade ba suma suka saje da
duhun dare Sagir ya daina ganin
komai sai duhun dare. Adaidai
lokacin ne wani agogo mai rurin
tsiya a makwabta, ya fara garam!
Garam!. Karfe goma Shadaya na
dare kenan a gogon Najeriya kamaru da Ghana.
***
Dattijuwar Matar ta dubi Rabi'atu
sannan kuma ta daga kanta a dai
dai lokacin da taji motsin
shigowar su Aliyu Rashid, sannan
ne to shima Imran ya shigo
dakin. A cikin dan lokacin sai duk
dakin akayi shiru ana duban
Imran, Sannan kwatsam sai
Rabi'atu ta ganeshi bata taba
tsammani ba shine mutum na
karshe da take tsammanin zata
gani a gurin
"Imran" Rabi'atu ta kira sunansa
sannan sai ta fashe da kuka me
tsananin gaske.
"Rabi'atu...daina kuka don Allah
gani nazo duk abin da zai sameki
sai dai ya same mu tare."
"Hawaye ya fara zuba akan
kumatunsa.
.
"Babu abin ma da zai sameku in
Allah yaso." Aliyu Rashid yace.
Cikin tausayi yana duban yaran
biyu. A daidai lokacin ne Rabi'atu
ta dafa cikinta tana cizon baki. Da
farko da sun dauka zuwan Imran
ne to amma can sai ta fara kuka
mai tsanani tana nishi.
"Wayyo...Imran....cikinq ciwo"
"Rabi'atu menene kuma!!" Imran
ya tambaye ta a rude. Bata amsa
ba tuni ta fadi a tsakar dakin
tana murkususu. Mazan biyu tare
da mahaifiyar Aliyu Rashid suka
mike tsaye lokaci guda suna
kokarin fahimtar Abinda ke
faruwa. Mahaifiyar Aliyu Rashid ce
ta kama kafadarta sannan ta
tabota tana salati.
"Lah'ilah ha illallah, ni yasu na
shiga uku wannan yarinya kuma
me..." Tayi shiru bata karasa fadi
ba saboda abin da ta gani mai
kamar jini yana sartu kan
kafafunta.
"Yi sauri maza mu kaita cikin
mota, ina tsammanin juna biyun
dake jikinta ne ya sami matsala
me yiyuwa zubewa zaiyi."
Kafin ta rufe bakinta Aliyu Rashid
ya ruga da gudu katuwar babbar
rigar dake jikinsa tana daukar
iska kamar kumbo a folo minti
daya kacal ya dauke shi ya fito da
zungureriyar motar daga cikin gareji.
"Ku...ku kamota mu kai...ta ciki"
yace dasu Imran da mahaifiyarsa
da ke tsaye carko-carko kamar
zakaru suka dubi Rabi'atu
kwance tana murkususu. Imran
ya cicibeta su kuma suka bishi a
baya har sa'ar da ya kwantar da
ita a bayan mota, Imran bai daina
zubar da hawaye ba. Allah ka ceci
ran yarinyar nan, Allah-Allah ka
bata Lafiya yayi addu'a cikin
zuciyarsa. Sannan ya shige gidan
gaba na motar, ita kuma
mahaifiyar Aliyu Rashid ta shiga
gidan baya domin tana kula da
Rabi'atu.
"Wan...ne asibiti zamukaita" Aliyu
Rashid yace a takaice gami da
kunna injin motar. Gaban imran
yafadi domin jin cewa za'a maida
Rabi'atu inda ta gudo.
"Amma...ina ganin ai da wani
garin muka wuce tunda dai ga
halin da ake ciki kada muje...
Aliyu Rashid ya katse
mahaifiyarsa ta hanyar daga
mata hannu.
"Kada ki damu Inna, domin ina
ganin wannan itace damarta ta
kubuta tunda dai kina ganin
gashi yanzu in ba wani ikon Allah
ba barin cikin zatayi sakamakon
dukkan da Bose tayi mata. Ni ina
ganin kamata yayi idan Allah ya
kaimu birni na ajje ku a asibitin
na wuce kai tsaye wajan jami'an
tsaro na basu gaskiyar labarin,
domin irin wannan gara ma ka
fadi gaskiya ko kuma wayonka
ya janyo maka matsala shin
yanzu zata tabe ne har abada
tana gudun boye kanta?
.
Ya sawa motar giya sannan ya
tuka da gudu suka nufi birni.
To sai kuma abin da Allah yayi.
Imran yace cikin zuciyarsa. Har
suka fice daga kauyen garin
Dan'asi idonsa rufe suke yana ta
sake-sake a zuciyarsa.
***
Dan tsinken dake nuni da adadin
manejin motar ya haura a hankali
har izuwa kan dari da casa'in, da
yawa daga cikin yantsirarun
motocin da dare yayi musu akan
titin sukan ringa sauka daga kan
titin su bashi guri ya wuce baki
bude. To amma duk hakan bata
dami Abdul ba, domin ko
manejin motar baya kallo
balantana ma ya lura da irin
gudun da yake. Burinsa daya a
wannan lokacin ya kai ga
Unguwar su Rabi'atu lallai ko
shakka babu indai ya tabbata
Rabi'atu ta halaka Bose, to shima
kuwa zai halakata, idan kuwa ba
haka ba to sai yayi mata dukan
da me yiyuwa a asibiti zata
karasa.
Lallai Rabi'atu! Ya sake nanatawa
cikin zuciyarsa, yanzu in ban....
.
Tunaninsa ya katse a daidai
lokacin daya hango jerin manya
manyan motoci a gabansa,
motocin katako ne guda uku,
sannan acan gefensu kuma
motar yansanda ce bakikirin da
ita kamar kurtun tawada, idan ba
dan hasken fitilar motar ba babu
ta yadda za'ayi Abdul ya iya ganin
motar a cikin duhun daren
saboda bakinta.
Yansandan biyar dake ta fama da
binciken kola da manya manyan
motocin da ke dauke dasu, suka
hangi mota ta nufo su gadan-
gadan kamar Alburushin bindiga.
Acikin yan dakikun da abun ke
kokarin faruwa babu abinda
Abdul bai yi ba domin ganin ya
rage gudun motar to sai dai
kuma kaddara ta riga fata.
Ya taka birkin motar gaba daya
tayoyin motar sukayi kara
kuuuu!! Sannan tayoyin motar na
gefen hagu suka daga motar ta
wuntsula sau biyu a sararin
samaniya sannan ta sake direwa
ta nufi inda yansanda ke tsaye
gindin motocin katakon.
Yansandan biyar sukayi tsalle
gefe guda, hular daya daga
cikinsu ta tashi sama kamar
filfiluwa. Ba'a dade ba motar
Abdul ta karaso gurin da gudun
sa gashin jiki mimmikewa ta daki
motar katakon garam!, sannan ta
nannade kamar alkaki atake a
gurin wani bangare na motar ya
fara cin wuta, gangar jikin motar
katakon dake dauke da kwalayen
madara da buhuhuwan Omo, ya
tuntsure, gami da danne karan
motar dake can sama donono
kamar biri, shi ya fara shekawa
barzahu kafin Abdul ya biyoshi a baya.
.
Jama'ar da akayi hadarin a
gabansu, suka dubi motar a rude
suna salatin da ba karewa, ba'a
dade ba sai yansandan da suka
watse da gudu suka sake
haduwa a gurin ana kokarin fito
da dan sauran abin da ya rage na
daga gangar jikin Abdul.
Lokacin da aka fito da gawar sai
duk yansanda da mutanen dake
gurin suka dauke kawunan su a
firgice da abin da suka gani.
Sajan Danlami ya dubi Abdul
wanda duk da yake kafafunsa
biyu sun rabu da gangar jikinsa,
amma har yanzu yana numfashi
sama-sama, ba karamin mamaki
yayi ba lokacin da Abdul ya bude
idanu, yace su kirawo masa
Sagir. To amma kafin ma yakara
fada masu adireshin tuni ya
mutu a hannun sajen Danlami.
Sajen Danlami ya dubi
rattakakkiyar gawar sannan ya
mike tsaye ya bugawa mutane
tsawa subar gurin, koda ya mike
tsaye daga kan gawar sai
yahango jerin gwanon motoci
makil akan titin duk sun yi fakin
suna kokarin ganewa
idanuwansu hadarin.ACI BULUS - 15
.
Sagir ya tashi firgigit a rude. Da
farko da ya dauka mafalki yakeyi,
domin tun sa'ar da Abdul ya fice
da gudu a mota ya dawo gidan
ya zauna, yana jiran Abdul ya
dawo, duk kuwa da cewa bai san
inda Abdul din zashi ba, to amma
yasan koma ina ya tafi nan da
karfe dayan dare zai dawo.
Sagir ya dade a zaune yana
tunane tunane, abinda ya kamata
suyi idan Abdul ya dawo, yace da
kansa sai suyiwa wancan dan
iskan sharin da har abada bazai
kara marmarin ya damfari wani
ba. Nasir jakal yace dashi da
asuba zai jefar da gawar, to indai
kuwa hakane abin kawai da
za'ayi shine ya chuna masa
yansanda su cafke shi da gawar
dumu-dumu a hannu. To sai dai
kuma motar sa domin ba dole ne
yansanda su so jin abinda ya
kawo matarsa hannun Nasir
Jakal. Yana wannan tunanin barci
ya sace shi zaune kan kujera.
Kansa a kife a kan teburin cin
abincin dake dakin Abdul, Don
haka lokacin da agogon dakin ya
dauki jiniyar bugun karfe daya
sai ya tashi firgigit, domin a
tunaninsa asubace tayi, to sai dai
kuma banda karan agogon acan
wani bangare kuma kararrawar
dake kofar gidan ce take ta
faman ruri kamar zata fasa
kwakwalwarsa.
Sagir ya tashi a rude ya nufi
kasan benen, wanne irin iskanci
ne haka kuma Abdul yakeyi, in
banda ....tunaninsa ya katse, ai
kuwa idan Abdul ne ba zai tsaya
waje yana danna kararrawa ba,
to in kuwa bashi bane wanene
to cikin wannan dare haka, Sagir
ya bude kofar sannan yayi turus
kamar wanda aka rutsa da
bindiga yansanda biyar, gami da
na cikon shidan mai murdadden
gashin baki kamar igiya suka
dubi Sagir suna muzurai.
"Ka ne Sagir?"
"Eh ni...ne" Sagir yace yana
wasiwasi, amma in kuwa Abdul
ne ya tura masa....
"Kaine Yayan Abdul?"
Gaban Sagir ya fadi lokacin da
yaji tambayar.
"Eh nine". Sagir yace.
Sannan ne to suka bayyana masa
hadarin.
Sagir ya dubi yansandan a rude
yace.
"Ab...dul ya mutu!!"
"Tabbas, kana iya zuwa gobe da
safe ka dauko shi yana
mutuwaren asibitin garin nan."
"Ku shigo ina son magana daku".
sagir yace yana zubar da hawaye."
***
Bakar motar yansandan ta shigo
cikin asibitin a hankali, sannan
kuma kurtun dansanda dake
tuka motar yayi mata
matsugunni karkashin daya daga
cikin bishiyoyin da tafi kowacce
inuwa a harabar asibitin.
Kofar motar ta bude, sannan
yansanda takwas suka fito, Sagir
na tsaye a tsakiyarsu, kansa babu
ko hula, hakanan idanunsa a
kukkunbure, takalmin dake
kafarsa ta hagun bashi bane a
kafarsa ta dama, rigarsa duk ta
cukwikwiye kamar wanda aka
kwato ta daga bakin saniya.
Yansandan takwas da Sagir suka
nufi bangaren da mutuwaren
asibitin take, yayin da majinyata
dake zazzaune a gindin bishiyoyi
suka bisu da kallo baki bude, Kai
kace wasu halittu na daban suke
kallo wadanda sam ma ba'a
wannan duniya suke ba.
Hakika Sagir ba karamin tashin
hankali yasami kansa a cikiba.
Domin a zamansa da yayi a
amurka, yasha ganin mutane iri
daban-daban da Allah ya jarabta
da masifu iri-iri, to amma babu
wacce tayi kama da tasa. Gashi
dai cikin yan sa'o'i kalilan, ya rasa
mahaifinsa ya kuma rasa
kanensa, wannan abu da ciwo
yake, to sai dai kuma babu yadda
ya za'ayi abin da Allah ya kaddara
sai dai addu'a.
.
Tun karfe tara na safe suka so
suzo, to amma saboda
cukucukun Kama Nasir Jakal da
yansanda suka yi shiya kawo
suka yi shiya kawo suka makara.
Ba karamin girgiza yansanda suka
yi ba lokacin da Sagir ya basu
dukkan labarin abin da yafaru
tun daga farko har karshe, basu
bar gidan ba sai karfe biyar da
rabi, acikin daren ake kawo
yansanda sukayi ta gwaje-
gwajensu na al'ada idan anyi
kisan kai a guri.
Acewar insifecto Ja'afar, wanda
yai kisan shekararsa talatin da
doriya yana aikin dansanda
tunda yake bai taba ganin kes,
mai abin mamaki irin wannan ba
sai sau daya, shima wannan
wata matace ta kama mijinta da
karuwa a daki, to amma ita
wannan mata wuta ta banka
musu gaba daya suka kone suna
barci
Akan dole suka taho da Sagir
mutuwaren badan komai ba
kuwa sai dan ya tabbatar da
gawar idan ta Abdul ce. To amma
a gurin Sagir yaso ace bai ganshi
ba, domin idan ya ganshi a halin
tagayyara tunanin na iya
makalewa a zuciyarsa, har zuwa
karshen rayuwarsa
Adaidai lokacin da yansandan da
sagir ke kokarin tsallake wata
magudanar ruwa dake rufe a
harabar asibitin sai wata farar
mota zungureriya taja ta tsaya a
dab dasu Ba'a dade ba wani
mutum sanye da babbar riga kai
babu hula ya fito sannan wani
kyakkyawan saurayi ya biyo
bayansa suka bude bayan motar
wata mata dattijuwa ta fito
sannan sai suka janyo wata mace
ranga-ranga suka nufi cikin
asibitin da ita Daga inda suke
suna iya jin nishin yarinyar sama
sama
Yansandan suka ci gaba da
tafiyar su domin su ganinsu
wannan ba wani sabon al'amari
bane balantana ma yasa su
tausayi.
To amma basu fi taku
uku-ukuu ba, sai duk suma suka
tsaya, saboda ganin Sagir yayi
turus yana duban mutanen dake
dauke da yarinyar.
"Me ya faru kuma?" Insfecta
Ja'afar ya tambayi Sagir cikin
gwarjejiyar muryarsa.
Sagir bai amsa ba sai yaci gaba
da kallon matar da ake dauke
ranga-ranga. Sannan sai yaji
gabansa ya fadi, lokacin da ya
dubi fuskarta sai yaji yawun
bakinsa ya kafe, numfashin sa na
neman kauracewa huhunsa. Ko
shakka baya yi RABI'ATU ce. Wani
kuma abu daya kara bashi
mamaki shine dogon saurayin,
tabbas ya sanshi, to amma kuma
ya kasa tuna inda ya taba
ganinsa. Nan da nan Sagir ya
juyo a gigice.
"Yal...labai ga....tacan".
Duk sai yansandan suka juyo
lokaci guda suka dubi Sagir,
saboda jin abin da yace."
"Wa cece?" Insfecta Ja'afar ya
tambaya.
"Rabi'atu! Mana matarsa da nake
baku labarin ita muke zargin ta
kashe Bose...gatacan za'a shiga
asibiti, babu mamaki juna biyunta
ne ya motsa akan hanyarta ta
gudun kisan...."
Kafin Sagir ya karasa yansandan
sun juya da gudu gudu sauri
sauri sun nufi cikin asibitin
wajen inda akayi da Rabi'atu.
Wata yar siririyar malamar asibiti
mai wuya kamar lilo tayi tsalle
gefe guda ta basu guri suka
wuce kusan suna fareti.
"Na shiga uku ! Yau kuma me zan
gani haka" ta tambayi kanta.ACI BULUS - 16
.
<<<<< KARSHE 🔚 >>>>>>>
.
Agogon tangamemen falon
karbar baki dake asibitin ya buga
karfe uku na yamma.
"To kungani ba laifinta bane,
indai kuka duba lamarinnan."
Aliyu Rashid yace da Insefecta
Ja'afar.
Kusan sa'o'insu uku kenan cikin
dakin suna ta jujjuya maganar.
Ba karamar kaduwa Aliyu Rashid
yayi ba, lokacin da yaga yansanda
sun zagayesu. Lokacin da suka ce
dashi wanan matar suna
zarginta da laifin kisan kai, sai
yaga babu abinda yafi daya wuce
ya bayyana musu gaskiyar
al'amarin. Bayan da likitoci hudu
suka hau aikin ceton ran
Rabi'atu, sai insefecta ja'afar ya
aje kurata uku domin suyi gadin
dakin da Rabi'atu take, sannan
kuma yace da sauran kurata
ukun suje can su jirasu a gindin
mota, shi kuma da sajen Danlami
suka wuce zuwa dakin karbar
baki inda suka fara sauraron
labarin daga

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment