Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gode!"
Imran yace a rude sannan sai ya
bude jakar wasikar ya zaro farar
takardar dake dauke da rubutu
cikin siraran harrufa ya
warwareta. Gabansa ya yi ras!!. A
saman wasikar a rubuce jimla ce
kamar haka.
RAYUWA TA TSANANTA A GARENI
MASOYIYAR
KA RABI'ATU
.
Wani Sassanyan
gumi ya fara barkowa tun daga
tsakiyar kan Imran har zuwa
gadon bayansa sannan lokaci
guda kuma sai wani fitinannen
kuda yayi wuf ya fada cikin
kunnan sa, ya fara kuka
Wurrrr!!!, Imran ya kai masa
duka a fusace, kudan ya tashi
sannan Imran ya mari kunnensa tas!.****
.
ABDUL ya Juya firgigit a tsorace
ya dubi duhun yana kokarin
fahimtar daga inda yar siririyar
muryar take fitowa. Adacan tun
wani zamani daya shude, wayar
wutar lantarki ta taba jan Abdul,
a lokacin baifi dan shekara goma
sha bakwai ba, a tunaninsa kuma
a wannan lokacin baya
tsammanin a duk duniyarnan
akwai wani abu mafi girgiza
mutum da tada hankali daya
wuce wayar lantarki. To amma
sa'ad da siririyar murya ta keto
cikin duhun sai Abdul ya fara
shakkar tunaninsa, domin duk
irin abinda ake kira girgiza a
wannan lokaci to Abdul yaga
abinda yafi wannan ma, wani
sassanyan gumi wanda yasha
bamban da ruwan kankara ya
fara sartu akan doronbayansa.
"Wa...nene?" Abdul ya tambaya
cikin raunanniyar murya. Shiru
ba'a amsa ba, amma duk da haka
Abdul yana iya jin hucin mutumin.
"wai wanene anan!!" Abdul yace
a fusace. "Nasir Jaka ne" siririyar
muryar tace. "Shin baka gane
muryata bane Abdul, ko kuma
rashin gaskiyar mummunan aikin
daka aikata ne ya fara tambayar
ka tun yanzu."
"Hantar cikin Abdul ta ya mutse,
idanuwansa suka firfito waje,
kamar zasu fado saboda kaduwa
da abinda yaji daga bakin Nasir
Jakal.
"Ban...bangane abinda kake nufi
da mummunan aikin da na aikata
ba" Abdul yace muryarsa na rawa
kamar gangar jikin rubabbiyar mota.
"Da sannu zaka gane abinda
nake nufi ko kuma ince dakai da
sannu zan kara jaddada maka
abin da kasan ka aikata, kai dai
kawai shiga gaba mu koma daki
domin aganina cikin duhu ba
gurin harkar kasuwanci bane ko
kuwa me ka gani Malamin yanbariki.?"
A dai dai lokacin ne yaran unguwar
suka dauki ihu "NEPA!!
.
Kafin kiftawa da bismilla zauren da
kuma cikin garejin sun gauraye
da haske.
Abdul ya dubi Nasir Jakal tsaye
yana yi masa murmushi, irin
murmushin da jami'i mai horar
da yan wasan kwallon kafa kanyi
a duk sa'adda yaga yan wasansa
sun lallasa abokan karawarsu da
ci shida babu ko daya. Kadan ya
rage Nasir Jakal ya fashe da
dariya sa'ar daya dubi fuskar
Abdul tayi sharkaf da gumi tana
naso.
.
Abdul ya juya ya nufi cikin gidan
gwiwarsa a sanyaye, yayi
mamakin ta yadda akayi har
gwiwowinsa suka iya daukar
gangar jikinsa. Nasir Jakal ya
bishi a baya, sannan ya dada da
cewa.
"Shin daman abin da naji dazu ka
jefar Tim kamar buhun siminti
gawar Bose ce, gaskiya fa
shiyasa ka hanani shiga, to don
ma Allah ya horemin tunanin
jiran ganin kwakwaf, da badan
haka ba, da
KACI BULUS
Malamin Bariki?***
.
Bani na kasheta ba Nasiru,
Wallahi bani na kashe ta ba,
kasanni ai Nasir tun muna yara
yaushe zan iya kashe koda
kadangare ne da ransa ballanta
na mutum."
Abdul yace, muryarsa na rawa a
daidai lokacin da suka zazzauna
a kujerun dake dakin Abdul suna
duban juna.
"Nasan bakai ka kasheta ba
Abdul" Nasir Jakal yace yana
murmushi.
Abdul yaji wani dadi ya lullube
shi jin cewa Nasir jakal ya yarda
bashi ya kashe Bose ba.
"To amma kana tsammanin
akwai alkalin duniyar da zai
yarda ba kai ka kasheta ba,
Nasan cewa tana cikin bayan
motar yayanka Sagir, ina kallon
sa'ar da duk kake kokarin jefata
ciki. Ta hakan da kayi ba karamar
dabara bace, sai dai kuma binda
kawai zanyi ka shiga bala'i shine
na tashi yanzunnan na bugawa
yansanda waya na sanar dasu
duk abin da ke faruwa, idan nace
dasu Ojo ne uban gidan Bose ya
turoni na kirawo ta babu abin da
zai hana su yarda dani
musamman ma idan su kayi
bincike suka gane cewa a daren
jiya kunyi fada kaca-kaca da Bose
a (Rose mary Club) me kake ji zai
faru, kana tsammanin idan
yayanka yaga gawar cikin but din
motar sa zai kyaleka, ko kuwa
kana tsammanin yayanka bai san
Bose yarinyar kace ba." Nasir ya
danyi shiru yana duban fuskar
Abdul, a yamutse, ga mamakinsa,
sai yaga kusan shekaru goma
sun karu akan hakikanin
shekarun fuskar a duniya.
Wani dunkulallen abu ya taho tun
daga hanjin cikin Abdul har zuwa
makogwaron sa ya tsayar da
numfashinsa cak.
"Haba Nasir Jakal" Abdul yace a
shashshake.
"Amma ai bai kamata kayimin
haka ba, tun da kasan wani ne ya
kasheta, kuma ko ni nakashe ta
ai kai mai rufamin asiri ne Nasir,
dan Allah ka taimakeni... Don
Allah..." "Kada kayi kuka, ba tashin
duniya bane yazo "Nasir yace
yana murmushi.ACI BULUS - 10
.
"Ni mai iya rufa maka asirine
idan zaka rufa nawa asirin, ni
mai iya taimakon kane idan
kaima zaka iya taimako na, ina
fatan zaka iya taimako na, ina
fatan ka gane abin da nake
nufi..." Abdul ya girgiza kai cikin
rashin fahimta. "Abinda nake son
ka gane shine, duk mutumin da
ya taimaki mutum mai yansulalla
kamar ka to babu abinda zai
hana shima yasa rai da dan wani
abin hasafi da zai magance
matsalolin sa dasu." Nasir yayi
shiru yana maida numfashin sa.
"Kamar me kake so...nawa kake
son na baka..." Abdul yace
bakinsa na rawa. Nasir yayi
murmushi. "Da kyau mutumina
ashe dai kana ganewa. To ina
ganin zan iya rufa maka asiri,
zanyi shiru da bakina, zan kuma
karbi aron motar taka nabi bayan
Sagir domin ganin duk yadda
za'ayi na dauke gawar kafin ya
ganta a ciki, (Domin indai
yaganta al'amura sun lalace gaba
daya)." "Nawa kake so? Abdul ya
sake tambaya, zuciyarsa ta fara
tunani a halin yanzu. "Dubu dari
biyu da Hamsin ma Kawai ta
isheni". Nasir Jakal yace kai tsaye,
"Dubu nawa!! Haba Nasir ai sunyi
yawa, ina zan samo su ba ka
ganin nima a jikin Sagir nake ci".
"Idan sun yi maka shikenan, ban
damu da yadda zaka bi ka samo
su ba, kai kasan hanyar da zaka
bi, ko kabi dare ko kabi rana dole
ne ka bani dubu dari biyu da
hamsin dina ko da kuwa hakan
na nufin ka saida motar ka ne.
Daman na dade ina tunanin
ranar da zan jefa kugiyata a
makwogwaron ka Abdul, domin
tunda ka shigo gari kake yi min
wani gani-gani to lokaci yayi da
nima zan shigo gari, kasan
daman sai ta hanyar wani wani
yake arziki." Ya dan yi shiru ya
maida numfashi san nan yaci
gaba. "Zabi ya rage naka ko dubu
dari biyu da hamsin, ko kuma
kwalawa su cikama gida da
bakaken kaya, "Meka ce malamin
yan bariki?"***
.
Zazzafan gumin dake kokarin
shiga idanun Imran bai hanashi
ci gaba da karatun siraran
kalaman dake rubuce ajikin farar
takardar ba.
MASOYIYARKA RABI'ATU
IMRAN Ina san ka sani cewa
rayuwa ta tsananta a gareni, na
shiga cikin dabaibayin sarkar
bala'in da ban san mai fitar dani
ba, sai subahanahu wata'ala. Ba
ka ga irin halin dana shiga ba
Imran bani da wanda zan
fadawa sai Allah sai kuma kai
Imran. Dan Allah kayi hakuri
Imran da dukkan bakin cikin da
ka sami kanka a ciki saboda ni,
sanin kanka ne Imran bani da
wani abin so sai kai, kai kadai ne
kuma Imran har yanzu cikin
zuciyata sanin kankane Imran
ban taba iya son wani idan ba
kai ba, amma idan kaddara ta
fadawa abu sai kaga duk ya
jirkice ya sauya kamanni tamkar
yadda kalanzir kan sauya
kammanin ruwa.
Imran tun ranar da muka rabu
da kai rabuwarmu ta karshe
wani abu mai suna farin ciki bai
sake zuwa zuciyata ba, ni kaina
ban san abin da ya sameni ba,
kawai dai na farka ina mai bakin
cikin dukkan abinda nayi maka,
wallahi ni kaina Imran bana ce
ga abinda ya sani na auri Abdul
ba, ya doke ni, ya azabtar dani, ya
zagi iyayena, sannan daga karshe
kuma yayi sanadiyyar da tilas
badon na so ba na aikata wani
mummunan al'amari, al'amari
akan kuskure da idan ka jishi kai
kanka sai ka kyamace ni.
Kada incika ka da surutu Imran,
domin tuni na riga na bar garin
nan, bana jin kuma zan sake
dawowa sai ko wani abu na
kaddara ka yafeni ya masoyina
Imran, dan Allah ka yafemin ni
kam tawa ta kare, daman na
rubuta maka wan nan wasikane
domin kawai na nemi gafarar
abin da nayi maka abaya. Nasan
kai mai kaunata ne a kullum, to
nima ina son ka sani cewa ko
bayan raina bani da wani abin so
sai kai, kayi hakuri Imran, Allah ya
baka wacce ta fini, shikenan
Imran dan Allah kaje ka nemar
min gafara ga iyayena.
Sai wata rana (Darling)
sai wata rana
.
Wani zazzafan hawaye ya
kwarara akan kumatun Imran
sannan ya mike tsaye cikin kunan
rai ya hada takardar a hannunsa
ya dukunkunata kadan ya rage
yayi jifa da ita to amma sai wata
zuciya tace dashi kada ka jefar A
hankali sai ya cusa takardar cikin
aljihun wandonsa sannan ya
juya a fusace ya nufi gida, abin
kawai dake ransa shine yayi
sauri yaje tasha domin ya sami
mutumin nan daya kawo masa
wasikar ya tambaye shi inda ya
baro Rabi'atu duk da yake dai
mutumin ya fada masa sunan
garin to amma yana bukatar
hakikanin inda suka hadu da
Rabi'atu Dole ne yabi bayanta
Imran yace da kansa
***
.
Abdul ya dubi Nasir Jakal a fusace
yace, kana nufin yanzu ke nan
tursasani zakayi ta dole na biyaka
kudin?"
"To kana da zabine taimakon ka
nayi fa ko dai ka kawo ko kuma
ka mika dan gajeren wuyanka ga
jami'an tsaro ka tuna fa ko ba'a
kasheka ba dole ne ka karasa
sauran rayuwar ka a gidan maza
Me yiwa ko za'a sake ka alokacin
baza ka ganu ba saboda tsufa,
kuma TSUFAN MA na banza domin
kowa ya kalle ka yasan ba tsohon
arziki bane".
"To....to amma Nasir Jakal,
wannan shine abotar da kake
nufi ina laifin na..." Nasir jakal ya
katse shi.
"Kada ka batamin lokaci". Nasir
yace, gami da mikewa tsaye
sannan ya tura hannayensa cikin
aljihun shudin (Jeans) wandon
dake jikin sa.
"Na gaji da ciniki, ka tashi kawai
ka lalubamin karafana nasan a
gida kake ajje kudadenka". Abdul
ya mike tsaye jikinsa na rawa, ya
dubi Nasir Jakal cikin takaici,
akwai wani abu a tattare da irin
kallon da yake yi masa, wanda
shi kansa Nasir Jakal sai da yayi
tsalle ya koma gefe guda domin a
tunaninsa Abdul kutufo zai kawo
masa, amma maimakon hakan
sai Abdul ya wuce kai tsaye ya
nufi can cikin dakin. Ba'a dade ba
sai Nasir Jakal yaji wani sauti
Zuuuu!!, kamar ana zuge zif din
jaka, nan da nan yayi sauri ya
nufi cikin dakin shima. Abdul yayi
firgigit gami da daga kai yana
duban Nasir Jakal cikin kunan rai.
"wanne irin iskanci ne kuma
haka, sai ma ka....biyoni" Nasir
Jakal yayi murmushi sannan ya
mika hannunsa ya dauke jakar
daga cinyar Abdul yaleka ciki.
Yawun bakinsa ya kafe lokacin
da yayi ido biyu da wazobiyoyi fal
a ciki sabbbi suna daukar ido,
Nasir jakal ya zuge zif din jakar a
hankali sannan ya dubi Abdul.
"Nawa ne a ciki?" ya tambayi
Abdul. Har yanzu busashen
murmushin na nan a labban
bakinsa bakikirin sabo da
hayakin taba.
"Ba....ba zai yiyu ka tafi ba Nasir,
Naira Dubu Dari Uku da goma ne,
sai dai mu raba walla..."
"Kada ka bata numfashin ka a
banza" Nasir Jakal ya katseshi.
"Domin babu abin da zaai hanani
tafiya dasu, kaga Allah ya taimake
ka kenan ba sai ka sayar da
motarka ba."
"To....to amma ai ba haka mukayi
da kai ba" Abdul yace, kamar ya
fashe da kuka.
"Kada kayi kuka Abdul, domin
Dubu Dari Uku da Goma ba
komai ba ce, indai har rabuwa da
ita din na nufin ka tserar da
ranka, amma duk da haka zan iya
kyalema kudinka idan kana ganin
sunfi rayuwarka, sai dai kuma
sanin kanka ne babu abin da zai
hana na rerawa yansanda
wakata."
.
Nasir Jakal ya jefawa Abdul jakar
kudin tim a kirji yana murmushi,
sannan yace,
"Sai ka zaba Abdul, tsakanin
mummunan aski da sa kai a
wuta, wanne ne yafi maka."
Abdul ya mike tsaye a hankali jiki
na rawa, bakinsa ma rawa yake,
ya rasa abin dake yi masa dadi,
bashi da mafita alokacin, yace
cikin zuciyarsa, mafitarsa daya ce,
shine ya mikawa Nasir jakar
kudin, amma yasan tabbas sai ya
rama rashin mutuncin da Nasir
Jakal yayi masa.
Abdul ya dauki Jakar wasarairai
yana jujuyata a hannunsa kamar
yadda sarkin fawa kan yiwa fatar
da yake tsammanin akwai huda a
jikinta.
"Gashi nan Nasir, na gode da
abin da kayi min, bazan manta da
kai ba, yanzu kam kaci nasara, to
amma fa kada ka manta ba
kullum take salla ba, ba kuma
kullum guda ba inji matar
barawo, kaje ka, na gode, kuma
kada kamanta, wallahi duk
wanda ya hadiyi kibiya saita
tsaya masa a wuya, zamu hadu
dakai Jakal, kada kuma ka dauka
KACI BULUS
domin kowa yaci
ladan kuturu dole ne yayi masa
aski, kowa ya shaki barkonon
tsohuwa dole ne yayi ruwan
idanu." Shima sai ya jefa jakar
gurin Nasir jakal, Nasir ya cafe
jakar yana murmushi.
"Kada kayi fushi Abdul Lamarin
kasuwanci ne yazo da haka, nayi
maka Alkawarin baka biya kudin
ka abanza ba, yanzu nan zanje na
dauke gawar daga bayan motar
Sagir, zan jefar da ita inda mai
yiyuwa sai an yi wata ma ba'a
ganta ba, akwai kududdufi a
unguwarmu."
"Nasir yayi shiru gami da mika
hannun sa gurin Abdul," "Bani
dan makullin motar na bishi, tun
kafin ya buda lamarin ya lalace
baki daya".
Abdul ya laluba aljihunsa ya sake
jefawa Nasir dan mukullin motar.
"Ka dawomin da motata gobe da
safe, fice daga gidannan bana
son kara ganin ka matsiyaci"
Nasir ya fashe da dariya.
"Kada kayi fushi Abdul babu
abinda zaka iya, ka riga ka hadiyi
fatsa ta, ta kuma kamaka a wuya,
baka da damar kwacewa tunda
dai kai karamin kifi ne, baka kai
koda karfasa ba, balle tarwada."
"Fice daga gidan nan."
Abdul yace cikin karaji, tuni ya
gama kulewa Nasir.
"Tabbas....tabbas." Nasir Jakal
yace,
ya juya a hankali gami da yiwa
Abdul murmushin karshe,
sannan ya juya da gudu-gudu ya
nufi kasan benen, koda ya
tabbata ya fice daga dakin sai ya
dada dacewa.
"Abdul kayi kokarin taramin
wasu kudin kafin wannan su
kare na dawo." Abdul yayi sororo
tsaye cikin takaici tuni ya fara
tunanin
hauhawar jini zaiyi.ACI BULUS - 11
.
A daidai lokacin da wani agogo a
can cikin daya daga cikin
shagunan dake tashar motar ya
fara rurin sanar da tuzuran dake
barci a ciki cewa to yanzu fa
karfe daya tayi, to a daidai
lokacin ne kuma wata
zungureriyar marsandi ta turo
hancinta cikin tashar motar. Tana
shigowa tashar sai duk sauran
yantsirarun motocin suka zama
wani abu daban, domin in har
zaka hadasu da motar da ta
shigo a yanzu, to baka iya
kiransu da motoci, sai ko dai
kace musu sunduki da taya, ko
kuma kace dasu shankwalatin
bangaro, kamar yadda ungulu ta
kirasu.
zungureriyar motar taja ta tsaya
a hankali gaban teburi wani mai
shayi da yafi kowa naci a cikin
masu shayin garin dan'asi. Wasu
al'majirai uku, da magidanta
guda biyu suna zaune akan
teburin mai shayin suna hira
abinsu, ba tare da sun kula da
duniya ba, babu abin dake
damun su sai hirarsu, hakan
nema yasa basu kula da
shigowar motar tashar ba har sai
bayan da hasken fitilar ta ya
dallare idanuwansu.
"Wane ne kuma wannan." Wani
daga cikin mutanen ya tambaya,
"Baka san wannan ba kai kana
garin nan??" Mai shayin ya
tambaya. "Aliyu Rashid kenan,
tsohon kwamishina ne a
zamanin janhuriya ta farko, baka
san babansa bane, dangidan
Rashidu baduku nefa, na nan garin,"
" to amma da yake nima inba
karshen sati ba bana zuwa garin,
ba dole ne ba na sanshi". Kofar
motar ta bude Alhaji Rashidu ya
fito Dogo ne kakkaura baki, mai
gashin baki, a iya tunanin kuma
wandada suka sanshi tun yana
kwaminshina, ance ba'a taba
ganin sa da wasu kaya ba inba
farare ba. "Assalamu Alaikum."
"Ameen Wa'alaikassalam"
Mutanen suka amsa baki daya,
sannan duk gurin suka yi tsit, irin
shirun da kakanji a yayin da
malami ya shigo aji yara suna
surutu. Mai shayin ne ya fara
bude shirun da cewa.
"Alhaji barka da dare." "Yauwa
mai shayi ya kasuwa, don Allah
ko yarannan masu sai da fetur
sun yi barci, wallahi maina
kadanne, kuma gobe da sassafe
nake son na bar garin nan," yace
cikin sauri,
"Wallahi Alhaji duk sun tashi
amma bari inje shagon su
dan'asabe ina jin shi baiyi barci
ba, don naji hayaniyarsu dazu
suna karta."
"Yauwa da ka kyauta wallahi,"
Aliyu Rashid ya nemi guri kusa da
mutanen ya zauna akan bencin.
Tun kafin duwawunsa su taba
bencin sauran mutane hudun
dake zaune akai suka mimmike
suka bar masa bencin shi kadai.
"Kai...kai miye haka, ku zauna
mana meye na tashi, ku zauna
mana ko ni bakwa son ku yi hirar
da ni."
Mutanen sukayi yar dariya cikin
jin kunya da nauyin sa, na mai
hannu da shuni, sannan suka
zauna, amma ba'a sami mai iya
sake ce wa komai ba. Bayan
wasu yan dakiku mai shayin ya
bullo daga can cikin duhun dare
daya mamaye tashar, a kusa
dashi wani yaro ne dauke da
gallan din man fetur guda biyu,
ya kafa bututun ya zuba man a
kansa, yana tafe yana wakar mai
asharalle, bai damu da komai a duniya ba,****
.
Acan wani bangare na tashar
wasu runfuna ne, na masu sai da
abinci da rana. Babu komai a
cikin rumafar sai tebura da
murahun karfe na dafa abinci. To
amma sabanin sauran lokutan
baya, a wannan dare ba tebura
bane kawai a cikin rumfunan, a
cikin su harda Rabi'atu kwance
akan kwali, tayi matshin kai da
jakar kayanta, idanunta sharkaf
da hawaye tana tacin uban kuka.
Tun sa'ar data iso garin take
kuka, koda yake lokacin data iso
garin bata bari mutanen dake
tashar sun gane kuka take ba,
domin in suka gane haka, suna
iya yi mata tambayar yaya akayi
aka haifi uwarki, Har sa'ar da
duhun dare ya fara shigowa
Rabi'atu bata gama yanke
shawarar ta shiga garin ko kuma
ta wuce ba, to amma ita a son
samunta kamata yayi ace ta dada
lulukawa can cikin uwa duniya,
inda babu wani abu ma da zata
sake gani daya shafi gida,
balantana ma ya tuna mata da
mummunan al'amarin da ya faru
tamkar a mafarki.
Lokacin da tazo garin, sai taga ba
karamin kuskure tayi ba data
baro gida bata nemi gafarar
iyayenta ba, da kuma tsohon
masoyinta Imran.
To amma ai har yanzu bata baci
ba tace da kanta,
A lokacin ne ta bude jakarta ta
dauko takarda da biro ta rubuta
wasika zuwa ga Imran, sannan
ta fara duba izuwa tsalibar
fuskar da zata amincewa, domin
bata sakon ta zuwa ga Imran,
alokacin ne to ta hango
Abdussalam, ba karamar magiya
tasha ba, kafin ya amince da zai
kai sakon. To amma har yanzu da
take kwance cikin rubabbiyar
rumfar tashar tana sharbar kuka,
bata taba yarda da cewa alokacin
wasikar ta sami Imran ba.
.
Wani dankararen bera ya bugo
sufa daga cikin tarkacen rumfar
ya fado a kan ruwan cikin
Rabi'atu Tim! Rabi'atu ta mike
zaune zumbur gami da yan
addu'o'in da suka iya zuwa
bakinta Ita kanta tasan ba
karamin hadari zamanta a
rumfar ke tattare dashi ba to
amma ranta ya gama baci
zuciyarta ta gama rudewa
rayuwarta ta dagule tunaninta
ya zama kankani hakanne yasa
zuciyarta ta bushe daga duk
wani abu na ban tsoro bata ma
damu da duk wani abu da zai
sameta ba
A daidai lokacin da take kokarin
turar da beran daga kanta ne to
hasken mota ya dallare mata
idanu Aliyu Rashid yayi mamaki
domin ganin kyakkyawar fuskar
zaune cikin tsohuwar rumfa cikin
wannan talatainin dare fargaba
da tsoro suka tattokare kirjinsa
domin yasan babu mamaki ma
matar aljanace ke son bude masa
ido
Tun yana yaro tun kafin ya bar
kauye ya koma birni yasha jin
mahaifinsa Malam Rashid baduku
na fadin labarin wani abu wai shi
fatalwa to amma a yadda yaji
mahaifin nasa na fadi yasan
wannan ba fatalwa bace sai dai
ko aljana domin ance ita wai
fatalwa ko yaushe cikin fararen
kaya take Duk da irin tsoron
dake kokarin cin karfin zuciyarsa
hakan bai hanashi tsayar da
motarsa ba gefen rumfar
Ya dubi Rabi'atu ta cikin gilashin
motar sai yaga ta daga hannunta
ta kare fuskarta wanna ce tasa
ya fara tunanin ba aljana bace
mutum ce to koma dai menene,
sai ya sauka ya gani, wa ya sani
ma ko irin matan aljannunan ne
dake auren mutane suna kawo
musu daloli. Aliyu Rashid ya danyi
wani murmushi, lokacin daya
tuna makudan kudin da aka
damfari abokinsa Alhaji Rabi'u
Hamza, wai za'a aura masa
aljana, mai kawo kudi.
Kafarsa na rawa ya nufi gindin
rumfar, fitilar motar a kunne
take, tun kafin ya karaso gurin
Rabi'atu ta lillube jikinta da
hannun mayafinta.
"Baiwar Allah me kike yi a nan ke
kadai?" Aliyu Rashid ya tambaya
muryarsa na rawa. Bata amsa ba
sai ta fashe da kuka.
A can wajen mai shayi, kuna sun
zubowa gindin motar ido. Suna
masu mamakin abin da ya tsaida.
Aliyu Rashid gindin rumfar.
"Kaga fa ina jin matar nan ce ta
dazu, har yanzu bata bar tashar
nan ba." mai shayin yace da wani
magidancin dake rike da kofin
shayi shi bai kai baki ba kuma
bai ajiye ba hankalinsa ya tafi ga
rumfar.
"Wace ce kenan kake nufi."
"Haba matar nan mana wacce
nake ce maka tun dazu da
yamma ta sauka amma duk an
watse an barta."
"Oh to, na tuna kwarai kuwa
kuma kaga fa inajin irin korarrun
karuwannan ne dake gudun
shari'a daga burni zuwa kauye,
su wai a tunanin su shari'ar baza
tayi wani tasiri a kauye ba, to nan
ma dai korar su zamu yi gayyar
tsiya, arna a idi, shari'a dai Allah
ya kawo, don haka ba ruwanta
da birni ko kauye ko ina aiki zata
yi." Mutanen suka fashe da
dariya, sannan mai shayin yace,
"Mai yiyuwafa, yallabai daukarta
zaiyi
Ya kai ta ina wani ya tambaya
mai shayin yayi dariya ce Ashe
kai har yanzu bakasan
shugabanninmu ba kenan da
mata ai kai irin abubuwan
masha'a da suke aikatawa da
mata sai abin da ka gani domin
wallahi kashi saba'in da biyar
daga cikin dari basu da aiki sai
lalata da matan banza
To Allah ya kiyaye Allah ya shirye
su mu kuma Allah ya karemu
Sauran suka ce Ameen-ameen
To amma har yanzu idanun mai
shayin bai bar gindin rumfarba
In badon ba badon ba, da babu
abin da zi hana shi zuwa ya leko
abin da ke faruwa saboda tsabar zato
***
Dogon Saurayin mai fuskar
matsorata ya dubi Sagir a firgice
saboda ganin abin da ya gani
cikin bayan motar
"Na shiga uku" Sagir yace a rude
yana duban saurayin Sagir ya
juya ya dubin inda sauran
samarin masu saida kayayyakin
suke tsaye Abinda ya bashi
mamaki sai yaga ko kusa ko
alama ma hankalinsu bai zo
kanshi ba Sagir ya tara tunanin
gaggawa a cikin zuciyarsa daga
nan kuma ya gane hanya mafi
sauki itace yayi sauri ya bar gurin
tun kafin rudadden saurayin
dake gabansa ya rusa ihun da zai
janyo hankulan sauran mutanen
dake can gefe guda Tunanin
haka ne yasa Sagir ya mai da But
din motar garam Ya rufe
Sannan yayi sauri yace da yaron
Koma gurin kayan ka kada
kuma ka sake naji labarin a bakin
wani inka sake ka fadawa wani
sai na raba wannan dogon
wuyan naka da gangar jikinka
kai wacce ka gani a but din
motar nan ma sai ta fika kyan gani
Kafin dogon saurayin ya gama
girgijewa daga kaduwar abinda
yaji, tuni sagir har yafada cikin
motar ya tasheta, ya juya kan
motar ya ruga a guje ya koma ta
inda ya fito hantar cikinsa na
rawa
Dogon saurayin yayi sororo baki
bude yana kallon danjar motar
har sa'ar data kule yayi ajiyar
zuciya lallai duk yadda akayi
wannan mutun irin yan mafiya
dinnan ne da yake jin labarin
masu yanka mutane suyi tsafi da
gangar jikinsu.ACI BULUS - 12
.
Lallai duk yadda akayi wannan mutun irin yan mafiya
dinnan ne da yake jin labarin
masu yanka mutane suyi tsafi da
gangar jikinsu, yace da kansa yau
Allah ya rufamin asiri, bari inyi
shiru da bakina ko nasami damar
ganin sallar badi.
To amma can cikin zuciyarsa
yasan dole ne ko ba dade ko ba
jima sai ya labartawa wani
labarin, kamannin gawar kuwa
daya gani kwance cikin but din
motar ba zai taba barin zuciyarsa
ba, yayi mamakin in zai iya barci
a ranar, kai me yiyuwa ma sai ya
dade yana munanan mafarkai.****
.
Ba karamin namijin kokari Sagir
ke yi ba, don ganin ya dafe
sitiyarin motar, domin tun daga
dan yatsan kafarsa, har zuwa
gashin kansa rawa suke, Abdul,
me kuma Abdul ya zama? Me
Bose ta yiwa Abdul ya kasheta?
Me Abdul ke nufi da ya boye
gawar Bose cikin but din Motata?
Ashe yanzu duk irin abinda nake
yiwa Abdul wannan shine abinda
zai saka min dashi
Haka yayi ta jerawa kansa
tambayoyi iri-iri amma babu
amsar koda ta farko balanta
kuma ta karshe Adaidai lokacin
ne to ya hango lambar motar
Abdul, cikin hanzari ya zuro
hannunsa ta cikin tagar motar
yana yiwa Abdul alama da ya
tsaya. Nan da nan motar ta rage
gudu sannan a hankali ta sauka
gefen titi, shima yayi fakin guri
guda, sannan sai ya lankwasa
kan motar ya koma can
bangaren motar Abdul, yana
zuwa ya taka burki kusa dashi ya
tsaya, sannan Sagir ya bude kofar
motar cikin fushi jikinsa na digar
da gumi kamar ledar kankara.
Sannan a hankali sai kofar motar
Abdul ta bude, sannan dan
kakkauran saurayin daya sanya
shudin wando (Jeans) da farar
riga ya fito.
"Barka da war haka Sagir."
"Ina zaka ne naga kana zuga wuta
haka, kamar zaka birnin Caina?"
Nasir Jakal yace yana busashen
murmushin sa, Sagir ya dubi
Nasir Jakal cikin kaduwa yace.
"I....ina Abduul!"
"Wallahi yana gida yana hutawa
abinsa cikin nitsuwa da
kwanciyar hankali"
"Nasir Jakal yace, har yanzu
murmushin na nan makale a
fatar bakinsa. Akwai wani abu a
tattare da murmushin da ya fara
baiwa Sagir Tsoro, domin duk
sa'ar da Nasir Jakal yayi
murmushin sai ya dubi fuskar
Sagir, sannan kuma ya dubi but
din motar Sagir, to a wannan
lokacin kuwa idan akwai wani
abu da zai ta dawa Sagir hankali
fiye da komai a duniyarnan to
shine wani yayi kokarin koda
taba but din motar ne.
"Ab...Abdul...din yana gidane?"
"Acan dai na baroshi" Nasir Jakal
ya amsa kai tsaye, Sagir ya
fuskanci idan ya biye ta wannan
sakaran saurayin abokin Abdul
dake gaban sa to ko shakka
babu kwabarsa ruwa zata yi.
Domin ya tabbatar nan ba da
dadewa ba. Sandararriyar gawar
dake but din motar zata fara
wari. Kuma koma ba zatayi komai
ba, to hadarin dake tattare da
gawa a bayan motar mutum to
bambancinsa kadanne da kuma
ashana a gaban tankin fetur.
"Sai ka dawo" Sagir ya ce a
takaice.
Kafin Nasir Jakal ya farga tuni
Sagir ya shiga motar sa yana
kokarin take totur.
"Sagir!" Nasir Jakal ya kira
sunansa, ba kiran sunan ne yasa
Sagir sandarewa cikin fargaba
ba, sai irin yadda muryar Nasir
tayi kiran sunansa shiya sa shi
fargaba, musamman da yaga har
sa'ar daya shiga motar Nasir
Jakal na nan tsaye bai motsa ba,
hannunsa na hagun na saman
motar Abdul abokinsa.
Sagir ya dubi Nasir Jakal a firgice,
kafarsa daya a cikin motar, daya
kuma a waje,
"Mene...ne?" Ya tambaya, cikin
fargaba, bakin Nasir jakal ya sake
washewa cikin sabon murmushi,
Sagir ya kufala ransa ya baci, wai
shin me zaisa wannan saurayin
ya sashi a gaba haka ne yana tayi
masa dariya kamar wani
mahaukaci.
"Kaga in baka da abin fadi ni zan
tafi kaji ko!! Kada ka batamin
lokaci".
Sagir yace a fusace. Nasir Jakal ya
fashe da dariya sannan yace.
"Kada kayi fushi Sagir (Cool
down) in bata lokaci kake gudu,
ka gamu dashi domin kuwa ina
ganin ba da bara bace ace ka
ratsa ta tsakanin yansandan can
na kan danja masu cakin din
motocin mutane da wannan abin
a bayan motarka."
Sagir yaji kamar an sokeshi da
mashi a kirji,
"Me kake nufi!!" Sagir yace a rude
cikin fusata,
"(Cool down)" Nasir ya sake cewa
a karo na biyu yana murmushi.
"Kayi a hankali Sagir, ko so kake
ka tara mana jama'a da wannan
sandararriyar gawar yar budurwa dake but din motar ka?"
.
Mai shayin ya ajje kofin shayin
dake hannunsa kwaf akan
tsohon teburin dake lillibe da
leda shudiya, gami da nazarin
mutanen dake zazzaune akan
dogon bencin mai kamar makara
suna kukkubar ruwan shayin
gami da zazzare idanu. Domin da
yawa daga cikin kwastomomin
da suke zaune gindin teburin
shayin badon dadi suke sha ba,
sai don sabo, wasu kuma a
tunaninsu wai burgewace a
ganka a garin Dan'asi da sassafe
kamar haka kana shan shayi,
koda kuwa dandanon shayin
bashi da bambanci da ruwan
gishiri da sukari.
Bayan da mai shayin ya tabbata
duk kusan kwastomomin dake
gurin sun wadata da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment