Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mike ahakali na nufi tagar gilashin ofishin dake rufe na leka waje. Ruwan yafara sassautawa domin tuni har dalibai sun fara zirga zirga sosai a farfajiyar makarantar.
Wallahi Isma'il dazu wata bebi dana... Bai karasa ba sa'ar da ya lura da cewa bashi nake sauraro ba taga na kurawa idanu bana ko kiftawa.
Me kake leke ne? Naso nayi banza dashi to amma sai naga idan na kyaleshi ban kirawo shi ba to hakika naci amanar abokin zaman.
Zoka gani.. Nace dashi cikin doki.
Tun kafin na rufe bakina abba yayo tsalle daga kan kujerar dayake zaune ya matsa jikin tagar muka kurawa farfajiyar idanu kamar wasu sababbin dalibai.
Azamanin danake dalibi nasha ganin kyawawa masu daukar hankali da burgewa dasa sha'awa dakuma sa zuciyar mutum harbawa dan begen mallakarsu
to amma duk da hakan nan ban taba jin zumudin na yunkura domin na sami karbuwa ba. Domin naga kala da dama tun suna bugeni har ma suka daina daga karshe ma saina gane ashe duk rashin sabo ne na zama da kyawawa yasa nake rudewa.
Amma sa'ar da muka tsaya ni da abba sai naji wancan tsohon tunanin nawa ya bar jikina nayi mamaki sa'ar danaji numfashi na yana neman daukewa kamar wanda ke fama da cutar Asma.
.
Lokacin da abba ya karaso inda nake tuni har santala santalan kafafunta sun gama fitowa daga cikin motar mai kamar kwai sa'annan ta fito ahankali dauke da wata doguwar ambulan ruwan kasa. Ko da doguwar riga da wandonta launin kwanduwar kwai kanta lullube cikin wani dan fingilgilan farin kyalle mai dauke da wasu irin duwarwatsu launin azurfa sai daukar idanu sukeyi kamar taurari. Fara ce tas a mulmule take babu alamar tabo ko wata tawaya a tattare da fatar ta sumbul take kamar macijiya tana da yalwar gashi lullubin datayi bai hana siraran gashin kanta fitowa ba na tabbata koda acikin duhun bakin dare na hangota babu abinda zai hanani ganin fararen idanunta banda wannan kuma kundukukinta da kuma jerin madaidaitan hakoranta da dogon hancinta mai kamar biro sun isa su sa duk wani namijin duniya dimauta.
.
Koda ta fito daga motar sai muka hangi wata daliba ta nufi inda take cikin fara'a tana zuwa sai suka rungume juna fuskarta tana duban bangaren da muke koda tayo dariya sai naga kumatunta sun lotsa kadan abin gwanin birgewa.
Lah! HINDU... Ashe kinzo? Mukaji dayar tace. Tsawon lokaci muna nan tsaye kamar gumaka muna lekensu ta tagar ofishin.
Abba ne yafara dawowa hankalinsa sa'annan ya tabani akafada yace.
Dawo ka zauna isma'il yafa kamata mu rinka dabi'a irin ta malamai domin abinda muke ayanzu rayuwace irin ta dalibai. Na juya firgigit. Nasan abinda yafada gaskiya ne dan haka banyi musu ba sai muka koma kujerunmu muka zauna.
Na zaro kyalle daga aljihuna na share gumi sannan naci gaba da juya sunan danaji an kirata dashi cikin zuciyata.
HINDU. Kai amma sunan da dadi yake nace cikin zuciyata itace irin matar danake burin mallaka akullum kwanan duniya matar da bata da makusa irin matar da ko acikin aljanu sai sun yaba halittar ta.
Muna nan ahaka jugum tsahon lokaci har zuwa sa'ar da dalibi na farko ya kwankwasa mana kofar
ruwan saman ya dauke abba ne yafara farkar dani daga dogon tunanin dana tsunduma.
Isma'il ya kira sunana da karfi wannan shiya tabbatar min da cewa yakira ni sau da dama banji ba. Na juyo firgigit.
Na'am... Abba... Ya.... Akayi?
Yace tunanin me kakeyi ne haka ka kusan minti ashirin fa ahaka kawai dai kyaleka nayi.
Na dubeshi sannan na dubi kofar adaidai lokacin da aka sake kwankwasawa a karo na biyu sannan sai nayi kasa kasa da muryarta nace dashi.
TUNANIN HINDU NAKEYI WALLAHI.
*** *** ***
Wasa-wasa har kwanaki uku suka shude ban sake ganin hindu ba. Kullum idanuna a bude suke ko zan sake ganin hindu kunnuwana a bude suke ko zan sake jin daddadar dariyar hindu amma duk a banza. Adacan bisa ka'idata idan na shiga ofishinmu bana sake fita sai ko idan koyarwa zani dakin karatu. To amma run daga ranar dana dora idanunawa akan hindu sai zama ya gagara. Duk da yake dai har yanzu ba'a fara daukar darasi ba. Domin dalibai nata fama da hada hadar rijistar sabon zangon karatu.
Dana zauna sai naji kamar an tsikareni da allura sai na mike tsaye zan fice.
Ina kuma zaka fice daga zuwanka?
Abba yakan tambayeni.
Nan dakin kwamfiyuta zani zan..HINDU - 06
.
Dana zauna sainaji kamar an tsikareni da allura saina mike tsaye zan fice.
Ina kuma zaka fice daga zuwanka?
Abba ya tambayeni.
Nan dakin kwamfiyuta zani na amsa masa atakaice saina fice abina ina kallon sababbi da tsofaffin dalibai ina muzurai wai ni malami. To amma a hakikanin gaskiya duk zagayena na neman sake ganin hindu ne.... Na ganta kawai ko hankalina ya dan kwanta.
.
Sa'ar dana dawo gida sai na kasa zaune na kasa tsaye da zarar kuwa na kwanta sai inga fuskar hindu tana murmushi kundukukinta yana sheki kai. Abin dai ya zame min kamar masifa domin abinci ma bana iya cin wani abin kirki saidai nayita shan ruwa kamar kwado.
ARANA TA HUDU ina shiga ofis sai abba Ya dubeni cikin damuwa yace.
Isma'il meke damun ka ne yan kwanakin nan naga duk ka canza?
Na dubeshi na dan lokaci.
Kamar yaya kenan na canza?
Haba isma'il ai ko kujerun dake ofishin nan da sunada baki da sun bada shaidar cewa lallai ka sauya. Kaga dai na farko rabonka da muyi wata kwakkwarar hira tun ran da aka dawo idan ka shigo ma bakason zama kuma kaga duk kan teburin nan ayyukan daya kamata kayi ne amma gasu nan baka taba komai ba.... Ko bakajin dadi ne?
Ya kamata kaga likita idan akwai matsala. Shiru nayi na dan lokaci ni ban bashi amsa ba shikuma baici gaba ba. Can dai sai ya nisa yace.
Bakace komai ba isma'il bawai aikin da bakayi bane yafi damuna daman wannan duk ina iyayi ma kamar ka fara ramewa.... Ko kuwa idanuwana ne?
Nayi ajiyar zuciya.
Abba... Wallahi wata masifa ce ta sameni... Sai yawan tunane tunane nakeyi bana iya aiki bana iya cin abinci gashi kuma yanzu abin yakai tsananin ko da barci bana iyayi. Abba yafara buda wasu fayilulluka dake gabansa.
Tunanin me kake kuma isma'il? Na sunkuyar dakaina kasa ina wasa da biro akan teburin.
Tunanin.... Uhm.... Nayi shiru ban karasa ba.
Abba ya yi saurin fahimtata.
Kai isma'il kardai kace min haryanzu tunanin wannan yarinyar kakeyi? Wai kai da gaske kakeyi ko kuwa zolayata kakeyi? Na dago kai babu wani batun zolaya abba... Wallahi... Ni kaina bansan yadda akayi ba naji duk ta mamaye zuciyata ban isa nayi wani tunani ba sai nata... Abin ya zame min masifa... Jiya har addua nayi allah ya cire min kaunarta na huta domin nasan koda na sake ganinta ma tafi karfina nesa ba kusa ba. Abba ya girgiza kai cikin jimami.
Cab! Babbar magana.. Kaga dazun nan kuwa na hangeta. Tun kafin ya rufe bakinsa na mike tsaye cikin doki.
A ina ka ganta dan allah? Na tambaye shi bakina na rawa abba ya dubeni cikin mamaki.
Me zakaje kace mata?
Ganinta kawai zanyi abba... Ganinta kawai zanyi ko na sami hutun zuciya.
*** *** ***
MAKO GUDA KENAN da dawowa makaranta tun da sassade na isa makaranta domin a ranar ne nake son fara koyar da darasina. Karfe takwas dalibai na isa kofar makeken ajin koyar da karatun tuni duk dalibai sun nemi wuri sun zazauna ni ake jira don haka ina shiga sai duk wadanda ma ke tsatstsaye suka zazzauna sannan ajin yayi tsit.
Na fara nazarin daliban tun daga kujerun gaba gaba har zuwa can baya sai naga dayawa daga cikinsu duk yara ne yan shekaru sha takwas zuwa ashirin.
Abinda nake koyarwa amatsayina na malami a jami'ar shine LISSAFI. Hakan ita tasa mafi yawan daliban dake ajin duk maza ne domin na lura matan basu fi kashi daya bisa hudu na mazan ba.
Nafara gabatar musu da darasin nawa na farko sannu ahankali har kusan minti arba'in da biyar. Adaidai lokacin ne to ta shigo a makare domin duka duka baifi mintiuna goma sha biyar ba darasin ya kare.
Ta shigo ajin ahankali amma amsa kuwwar tsinin takalminta dake kwas kwas shi ya sani juyowa. Nayi mamaki domin tun kafin na juyo naji gabana ya fadi ras wani ni'imtaccem kamshi ya bugihancina sa'ar dana juyo a fusace domin ga al'adata bana son zuwa a makare dan duk dalibin daya bari har muka yi mintuna goma da fara darasi bai shigo ba to saidai ya tsaya awaje.
Koda na juya sai mukayi ido hudu da ita ta tsaya cak agaban ajin sa'ar dataga na kura idanu HINDU ce.
Tsahon dakiku biyar muna duban juna dalibai sunyi tsit idanunsu na kanmu.
Ga mamakina sai naga duk hindu ta firgice domin ita kanta tasan ta karya doka ga kuma idanu guba duka akanta.
INA DA WATA DOKA! Nace da daliban cikin harshen turanci.
Duk da yake dai ku baki ne yanzu kuka fara to daga yau ku sani duk wanda yazo amakare daidai dana minti goma saidai ya zauna awaje (I Am Clear?) sukace (Yes) baki daya.
Na dubi hindu wacce ke tsaye nace je ki zauna daga yau kada ki sake makara ni kaina nasan muryata ta sarke sa'ilin da nake fadin hakan. Ban taba tsammanin ana fara gumi ta dan yatsa ba sai aranar. Ga mamakina sai naji duk darasin ya gundure ni. Na dubi agogona sannan na dubi dalibaina nace
duk dayake dai akwai sauran mintuna sha biyu amma ina ganin anan zan tsaya sai gobe kuma idan Allah yakaimu. Ko dana daga kaina sai na hangi Hindu tana kallona. Akwai alamar murmushi a fuskarta.
.
BABI NA BIYU.
Abba ali ya dago kai ya dubeni cikin mamaki sa'ar dana shigo ofishin na ajiye takarduna akan teburin sannan na share gumin dake zuba akan...HINDU - 07
.
BABI NA BIYU 2
Abba ali ya dago kai ya dibeni cikin mamaki sa'ar dana shigo
ofishin na ajiye takarduna akan teburin sannan na share
gumin dake zuba akan fuskata kamar ruwa.
.
Lafiya kake ta faman gumi haka ko kunama ka hadiya? Ko
kuma na'urar sanyaya dakin dake ajin ta lalace ne? Na dai
zauna batareda na amsa masa ba.
Yaya naga jikinka kamar yana rawa ko zazzabi ne yake shirin
hawanka?
Na dubi abba na girgiza kai.
Ba zazzabi bane abba HINDU nagani a cikin daliban da nake
koyarwa.
Hindu....? Abba ya tambaya bakinsa na rawa.
Kuma shine duk kabi ka rikice haka isma'il kamar kaga
fatalwa... Ya mike tsaye yana duban agogo domin lokacin
shiga nasa darasin yayi.
Ni ashawarata isma'il ina ganin kamata yayi ka danne tunanin
yarinyar nan ka manta da ita domin yarinyar nan matsalace
agareka kaga dai na farko kai malaminta ne ba dan uwanta
dalibi ba
ballantana kayi kokarin neman soyayyarta tun da yanzu dai ka
riga ka shiga rigar malinta ba girman ka bane bakuma
mutuncinka bane ka tareta da wata magana da ta shafi
soyayya domin duk amsar da zata futo daga bakinta tamkar
zabin shaidanne acikin biyu babu daya na kirki.
Kaga idan ma har ka dace ta amince da soyayyarka toh
juyata kuma zaiyi ma wuya kasan kuwa hakan babban gibi zai
janyo ma tsakaninka da sauran dalibai sanin kanka ne lamarin
jami'a ba sani ba sabo... Zama ne ake tsakanin dalibai da
malamai irin zaman sabo da kaza baya hana yankata.
Abba ya danyi shiru yana dubana gamida yi min murmushin
yake.
Ina shakkar in har sabon dakayi da taka kazar zai iya bari ka
yankata idan kuwa taki yankuwa sauran kajin ma basu
yankuwa agareka. Abin Allah ya kiyaye kuwa idan taki
amincewa da soyayyarka al'amura sun kwabe kenan domin
kullum a banza zata ke ganinka da zarar kuma kayi kokarin
zartar da wani hukunci akanta saita ga kamar dan taki
amincewa da soyayyarka ne kake son tursasata... Idan kayi
rashin sa'a kuma duk saitabi kawayenta da tsugemin zancen.
Abba ya sake yin shiru a karo na biyu. Har yanzu gumin dake
fuskata zuba yake na dago kai na dubi abba sainaga akwai
wata alama a fuskarsa dake nuni da cewa lallai abinda ya
fada gaskiya ne.
.
Ka rabu da ita isma'il. Abba yaci gaba... Ka rabu da ita... Na
dada maimaita maka ka rabu da ita domin ba alheri bace a
gareka domin tana iya rusa ma rayuwar daka dade kana
ginawa wannan kyawun dake rudarka duk kyalkyal banza ne.
Mafi yawancin irinsu balbelu ne bayansu fari cikinsu baki.
Ya saurara yana maida numfashi.
Ni zan wuce lakca saina dawo amma kayi nazarin abinda
nafada maka.
Yana gama fadin haka sai ya kwashi takardunsa ya fice da
sauri yana duba agogo.
Yabar ni anan zaune na kifa kai akan tebur idanuna rufe ina
kokarin dawo da hoton fuskar hindu cikin zuciyata sa'ar da
naga kamar tanayimin murmushi.
.
Baifi mintuna biyu da fita ba sainaji an kwankwasa kofar na
dago kaina ina duban kofar sannan sainace Shigo mana.
Kofar ta bude sannan ta shigo ahankali kamar wacce ke
kokarin turawa zaki danyen nama. Hindu ce tsaye akaina tana
dubana.
Mun jima ahaka batareda munce da juna kala ba ni kaduwa
ta hanani magana ita kuwa bansanalili ba.
Bayan tsahon dakiku na girgije daga kaduwar danayi sannan
sai wata zuciyar tace dani.
Kai sha sha sha (you must be careful)
kaine fa malaminta kai yakamata kayi mata kwarjini ba wai ita
tayi maka ba.
Tunanin hakan shiyasani karfin halin dubanta ido da ido
fuskata a murtuke wai ni azuwan babu wasa nace da ita
gamida daga mata girar ido
Yes me kike so?
Hindu ta jefeni da tattausan murmushi wanda kusan jehoni
daga kan kujerar sannan saita dan matso daf da teburin tace.
Zuwa nayi na maka GODIYA.
*** *** ***
Godiyar me. Na tambayeta ina wani yatsine fuska amma
aboye acan cikin zuciyata kamar nasa ihu dan dadi tayi far far
da fararen idanunta.
Baka ganeni bane malam? Na girgiza kai.
Nice ai wacce dazu na shigo dakin karatu a makare lokacin
da kake lakca na dubeta gamida duban sama kamar wanda
ke kokarin tuno wani abu.
Oh! Daman kece? Ta rangwada agabana
Wallahi nice... Da duk na tsorata na dauka zaka.... Ta danyi
shiru tana inda inda kamar da zatayi amfani da ita agurin..
Zanyi me? Ta dauke kai gefe guda na dauka zaka kunyatani
agaban tarin daliban nan... Domin naji ance wai malaman
jami'a akwai su da kunyata dalibai... Cikin sauri na girgiza
kai.
A'a bahaka bane duk wanda yace dake haka to yaso
zuciyarsa ne kawai.
Na danyi shiru ina girgiza kafa.
Kodayake dai kowa da irin halinsa.
Jin haka sai hindu ta karkatar da kanta gefe guda tana
rausaya.
Abin kenan da yasa na zo na gode maka malam... Dan nasan
da wanine saiya kunyata ni. Ta danyi shiru sa'a dataji bance
komai ba me yiwuwa zatayi tsammanin ko kosawa nayi da ita
amma agaskiyar al'amarin ban gaskata magana da muryata
bane domin duk jikina rawa yakeyi kamar mazari.
Malam... Ni zan tafi sai gobe tafara juyawa. To har zaki tafi?
Ina fada nasan nayi kuskure. Ta dubeni da fararen idanunta
gamida daga gargasar girar idanunta tace.
Uhm tafiya zanyi.. Ko akwai wani abu? Jikina na rawa nayi
kokarin.....HINDU - 08
.
(c) Nazir Adam Salih
.
Uhm. Tafiya zanyi.... Ko akwai wani abu? Jikina na rawa nayi kokarin rike kaina cikin gaggawa. Domin waa zuciya sai kururuwa takeyi min tana cewa dani
Ce mata kana kaunarta mana... Fada mata kawai duk ma abinda zai faru ya faru.
.
Nayi watsi da kururwar lokaci guda kuma na girgiza kaina ina duban Hindu.
Babu abu... Ke dai kiyi kokarin kina shiga aji cikin lokaci. Adaidai lokacin danake fadin magana takai daf da kofa dan haka sa'ar data dafa mabudin kofar saita juyo ta dubeni akwai wani tattausan murmushi daya subuce akan fatar bakinta ta kashe min idanu tace.
Daga yau bazan sake zuwa a makare ba malam... Natafi sai gobe din. Ta bude kofar sannan saita dada da cewa (Have A Nice Day) da haka ta fice ta barni ina mika baki gaba kamar karen ruwa. Ga mamakina tana fita sai naji ofishin yayi shiru! Ya kuma kara fadi wani matsanancin kadaici ya lullubeni tamkar wanda ke barci ne ya farka ya ganshi tsakiyar dokar daji.
Nayi ajiyar zuciya duka faruwar al0arin baifi tsawon mintuna hudu ba amma sainaji tamkar na farka ne daga wani dogon mafarki.
Na shiga uku nace da kaina ni kadai.
*** *** ***
Sannu ahankali dakiku na kiftawa mintuna na juyawa lokaci na wuce kwanaki na shudewa har dai aka sami wata guda da rabi da fara sabon zangon karatu a jami'ar sarauniya.
Tun daga ranar da hindu tazo ofishina kusan kullum saitazo ta gaidani wani abin mamaki kuma bata taba zuwa ta samemu tare da abokin aikina malam abba ali ba kullum saita daidaici ya shiga dakin karatu saita shigo ko yaushe ta shigo zancen dai bai wuce Kala Uku 3
Malam zuwa nayi na gaisheka...
Malam yaushe ne zamuyi (test)....
Malam wane littafi yakamata na nema akan kwas kaza... Aikin kenan aduk sa'ar data shigo.
Nikuwa dayake tsananin begenta yagama cinye zuciyata saina zauna tamkar shashashar uwa yayinda take wasa ko hira da dan autanta domin duk tambayar datayi min sai inyi ta bata amsa.
Duk lalacewar tambaya kuwa ta taba tambayata wata rana tace dani
wai malam me yasa ne idan kana lakca sai inga ko tuntuben harshe bakayi?
Na dubeta sannan na amsa.
Wani sa'in ne idan ina koyarwa sai inji kamar wahayin abin da zan fada akeyi min shiyasa kikaga bana bata.
Idan tayi fashin kwana daya kuwa batazo ba har leke ta taga nake ko zan hangota domin aduk lokacin data shigo ofishin da farin ciki nake komawa gida.
Wani sa'in idan tazo ta tafi sai nayi sama da awa uku cikin ofishin ina shakar kamshin daddadan turaren da ta tafi ta bari a makale acikin iskar dake ofishin.
Jinakeyi kamar muna tare da itane idan kuwa nayi sa'a ta taba wani dan abu acikin ofishin kamar littafi ko dasta to rannan da abindata taba zan tafi gida idan nashiga dakina saina dauki abin na kwanta akan gadona sannan na karashi akan hancina ina shakar kamshin turaren jikin hindu.
.
Watarana hindu ta taba daukar dasta akan teburina dan haka dana tashi tafiya gida saina tadi da ita ina zuwa sainayi kwance akan gadona na dora dostar akan hancina inajin kamshin turaren wanda lokaci guda kuma ina bijiro da daddadar muryarta cikin zuciyata.
Ina cikin wannan hali ne karamar kanwata AMINA ta shigo dakin to ashe farin garin allin dake jikin dastar duk ya zuba akan fuskata koda amina ta dubeni sai tace.
La! Yaya ashe kana shafa hoda?
**** **** *****
Wata laraba tsakiyar mako na tashi daga makaranta ina kan hanyata ta zuwa gida cikin tsohuwat motata hajiya ba duwawu wacce keta faman barin hayaki kamar jirgin kasa dan haka nan lokaci lokaci wani mugun tunani kan darsu azuciyata yanzu idan ta kama da wuta fa?
Adaidai lokacin danake kokarin kaucewa wani katon rami ne dake tsakiyar hanya dunkuleliyar motar fara sol mai kamar kwai tazo daf da motata suka yi jerin sahu bana ita ganin wanda ke cikin motar domin duk gilashin motar an sa musu bakin gilas sannu ahankali sai gilashin motar na gidan gaba yafara yin kasa ahankali gabana yafadi ras sa'ar dana hangi Hindu ciki tana daga min hannu da in tsaya cikin gaggawa gami da mamaki ina rage gudun adaidai sa'ar da muka kawo daf da wani gidan mai.
Ganin cewa bayan gidan man babu komai fili ne fayau inda yara suke wasan kwallon kafa saina dauke kan motar daga kan hanya na nufi bayan gidan man ba dan komai ba nayi haka sai dan gudun kada dalibai masu wucewa su hangeni da hindu tsaye abakin hanya suna ko iya hada biyu da biyu tabasu hudu.
Hindu ce ta fito daga cikin tata rantsatstsiyar motar ta nufo inda nake tana zuwa bata bata lokaci ba saita bude gidan gaba na tsohuwar motar ta zauna kusa dani nan da nan naji motar ta game da kamshi. Hakan shi yasani sansana hannun rigata sai naji ashe duk warin hayaki ma nakeyi.
Lafiya dai ko? Na tambayeta fuskata adan hade domin inason idan ma ta manta to ta tuna da cewa fa da malaminta take zaune. Hindu ta dago kai karo na farko ta haskakeni da fararen idanunta nan da nan sainaji duk jikina ya dauki rawa wannan shine karo na farko data taba zama daf dani. Hakan shiyasani rudewa domin akwai wani abu mai kamar mayen karfe dake jikinta wanda ke fizgar zuciyata aduk lokacin dana....HINDU - 09
.
(c) Nazir Adam Salih
.
Domin akwai wani abu mai kamar mayen karfe ajikinta wanda ke fizgar zuciyata aduk lokacin dana kalleta.
.
Malam Isma'il inason ka ajiye malantarka agefe nikuma na ajiye dalibtata agefe sai mu fuskanci juna amatsayin mace da namiji.
Naji numfashina ya tsaya cak daman yawun bakina ba'a zancensa domin tun da zata zauna daf dani ban kara hadiyarsa ba.
Ban fahimce ki ba... Kamar yaya na ajiye malantata agefe? Hindu ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yan yatsunta sannan kwatsam sai ta dago kanta tace
saboda bansan nace da malamina yana burgeni... Zaifi kyau dai idan ka ajiye malantar gefe guda in yaso sai ince isma'il kana burgeni... Wani zazzafan gumi ya fara sartu akan dogon wuyana. Na dubi hindu a rude nace.
Hindu (Make Me Clear) duk kin rudani da kasa fahimtarki hindu ta dada matsowa daf dani sannan ta dubeni ido da ido tana murmushi tace.
Ba wani rudewa dakayi isma'il kaifa ba karamin yaro bane kasan abinda nake nufi.... Tun sa'ar dana fara hada ido dakai nasan kana kaunata shiyasa nima kake burgeni harka shiga raina.... Ta danyi shiru kamar tana tunanin abinda zataci gaba da cewa. Tsawon lokaci bamuce da juna kala ba can dai ta muskuta tace.
Isma'il kayi shiru ka kyaleni fadamin abinda ke zuciyarka mana in kuma nayi kuskuren fahimtar ka ne to fada min
BA KA SONA ?
sainafice maka daga mota mu manta da zancen. Naji kamar ta watsa min wuta nayi sauri nace.
Bahaka bane hindu...
Nasan abinda kake tunani hindu ta katseni cikin daga murya.
Kana ganin faduwa ce ka nemi soyayyar dalibarka ko? Na share gumi na sunkuyar da kaina.
Banda wannan ma akwai wani abu daban hindu
menene shi? Fadi naji?
Kowa ya dubeki ya dubeni yasan hanyar jirgi ba wurin tafiyar mota bace.. Hindu kinfini aji kinfini komai... Hindu ta girgiza kai cikin murmushi sannan tace.
Allah sarki isma'il... To bari ingaya maka ba ruwan so da duk wannan so shi yake kirkirar kyau bawai kyau ne ke kirkirar so ba.... Isma'il ta kira sunana daga karshe. Na dago kai na dubi kyakkyawa hindu.
Fada min kalmar nan daya....
KANA SONA ?
Jijiyoyin kaina suka fara harbawa domin lokacin boye boye ya wuce.
Hindu.. Waye zai dubeki aduniya yace baya sonki.... Idan har akwai abinda yafi so ma to inayi miki shi... Duk da yake dai.... Hindu ta katseni.
Ya isa isma'il kagama min komai wallahi ni zan tafi sai goben idan mun hadu ko?
Na dubeta ta dubeni saitayi min murmushi ga mamakina sainaji na rama mata murmushinta.
.
Hankalina ya kwanta isma'il...
Wani... Hanzari ba gudu ba. Nace da ita awannan karon cikin sakin jiki fadi jawabinka. Tace tana dariya a kunyace.
Inason don Allah hindu mubar abin nan dagani saike kada dalibai su san tsakaninmu. Hindu ta girgiza kai tace
babu waye zai sani?... Kuma kullum a makaranta zamuyi ta haduwa bazaka zo gidanmu ba...?
Ai bansan gidanku ba. Bansan daga inda ta zaro shi ba kamar budar idanu sai naga ta miko min kati.
Komai da komai yana jiki idan kaje nemana shi zaka nunawa masu gadin.
Farin ciki ya lullubeni cab! Yanzu yaya zakaha idon abba gobe idan nabashi labarin. Nace cikin zuciyata.
Yaushe yakamata nazo?
Ko yaushe ma isma'il hindu tace cikin dariya ko yaushe ma kana iya zuwa babu inda nake zuwa. Wannan shine abinda ya gudana tsakanina da hindu tun daga ranar da muka fara haduwa da ita.
.
Don haka sa'ar da tsohon ya sani agaba zuwa kofar fita sai naji wani matsanancin bakin ciki mara misaltuwa ya lullube zuciyata yanzu yaya za'ace hindu tayi min haka bayan ita tace nazo gashi nazo ta sauya min fuska kamar ma bata taba ganina ba. Ahaka cikin rudani na shiga motata kodana fara tafiya sainaji GISHIRI-GISHIRI abakina dakunya dai nace da kaina
DA KUNYA DAI SOYAYYAR DALIBA TA SAKA KUKA ISMA'IL,
*** *** ***
Na farka firgigit a tsorace kaina sai sarawa yake kamar ana doka min guduma kofar dakina ake kwankwasa na mike zaune dakyar akan gadon haryanzu kaina ciwo yake.
Bansan sa'ar da barci ya daukeni ba daren jiya. Lokacin dana dawo daga gidansu hindu dakyar nasamu nayi sallar magariba da isha'i abinci kuwa yafewa nayi.
Nashiga daki na rufe sannan na kwanta akan gado inata kukan zuci tunanin maganar abba ta fado min
KA RABU DA ITA ISMA'IL... Ka rabu da ita ba alheri bace agareka na nemi barcin sama da kasa na rasa... Ina nan dai kwance bansan sa'ar da barci ya daukeni ba. Koda na yunkura zaune sainaga ashema da kayan dana dawo dasu na kwanta ajikina ban cire ba.
Aka sake kwankwasa kofar dakin.
Shigo mana kanwata amina ta shigo.
Mama ce tace azo afada ma wai kayi bakuwa wai ta shigo?
Gabana ya fadi na dubi agogon dake jikin bangon dakin karfe takwas da rabi daidai. Na dubi amina nace.
Kamar yaya take bakuwar?
Amina

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment