Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace watace mai kyau kamar balarabiya... Irin wanda muke gani a TV.
Zuciyata ta fara harbawa abinda yabani mamaki shine anya kuwa zaiyu ace HINDU ce agidanmu tazo gurina da sassafe bayan cin mutuncin datayi min ajiya? To kuma a inama tasan gidanmu?
.
Kice da ita ta shigo amina ta fice daga dakin aguje. Ba'afi dakiku goma ba sainaji an sake kwankwasa kofar.
Shigo......HINDU - 10
.
(c) Nazir Adam Salih
.
Shigo nace muryata na rawa tun kafin ma ta shigo nasan kowacece domin kamshin turarenta yarigata shigowa.
Hindu ta shigo dakin cikin murmushi kai kace ba itace Hindu data hade min fuska ajiya agidansu ba.
Yaya naga duk ka bata rai ko bakaji dadin zuwana bane? Hindu tace sannan ta matso ta zauna abakin gadon danake zaune.
Hindu... Don Allah ki kyaleni haka in ba so kike kisani zautuwa ba.. Hindu ta fashe da dariya.
Kai da Allah can ka saki ranka. Kasanta da gulma kanaso kana kaiwa kasuwa
ta danyi shiru sannan sai tasa alamar nutsuwa a fuskarta tace.
.
Isma'il dan Allah kayi hakuri wallahi jiya gwada ka kawai nyi kuma naga abinda nake son gani.
Me kika gani...
Hindu ta fashe da zazzakar dariya daman so nake in gani ka damu dani?
Amma indai gwaji ne don Allah daga yau kada ki sakeyi min irin wannan domin yana iya sani ciwon zuciya. Hindu ta murguda min baki cikin wasa tace.
TOH AI TAMA KARE.
Na kalleta cikin rashin fahimta. Ta kare me. Hindu ta daga kanta sama tace.
Babane yake son ganinka da gaggawa shiyasa ka ganni da sassafe domin yanzu yake son ganawa dakai don jirgin karfe goma zaibi zuwa Hongkong.
Naji gumi ya dawo min.
Kinga hindu dan Allah banason wasa yaushe mahaifinki har ya sanni da zai.... Hindu ta daga min hannu.
Isma'il tun ranar dana fara ganinka na kaiwa mahaifina zancenka.. Bakasan wani abu ba duk abinda nake so shi daddy dina yake so duk kuma abinda nake so shi za'ayi min kaidai ka hanzarta ka shirya muyi sauri mu tafi nafada maka kasar zaibari.
.
Al'amarin duka sunzo min a murde... Ni kuma haryanzu ji nake kamar mafarki nake.
Hindu to ni yanzu idan naje maganar me zamuyi.. Kinga dai zuwana fa daya kawai shima ko hirar arziki bamuyi ba to kuma maganar me zamuyi?
Hindu ta dada matsowa daf dani sannan ta kashe min idanu tace.
So yake yaji daga bakin idan da gaske ne KANA SONA domin yace idan yaje Hongkong zai sayo min duk kayan da muke bukata.
Kayan me? Na tambayeta a rude.
Kayan aurenmu mana.
.
BABI NA UKU 3
Muka shige cikin dunkulalliyar motar mai kamar kwai hindu ta tuka muka tafi adacan sa'ar dana gaji tsohuwar motata daga gurin mahaifina na dauka mota nake shiga to amma sa'ar danaji na nutse acikin tattausar kujerar motar hindu saina fara tunanin shakka babu ni motata batayi kama da komai ba sai AMALANKE.
Tunanin me kakeyi ne isma'il ? Hindu ta tambayeni. Nayi ajiyar zuciya
gaskiya hindu abubuwa ne duk suka rudani daman abin duk yazo cikin gaggawa. Hindu ta danyi shiru na dan lokaci ta sassauta murya tace.
Kayimin afuwa isma'il duk rudewar daka sami kanka aciki laifina ne domin ni na bata maka rai kuma....
Bahaka bane nufina Hindu kinga komai yana bukatar lokaci kinga dai yadda komai yana bukatar lokaci kinga dai yadda gidanmu yake ba wani karfine damu ba yanzu idan na aure ki...
Hindu ta bata rai.
Wato dai yanzu kana nufin dai kenan ban kwanta maka arai ba...
Bahaka nake nufi ba hindu. Kinga komai yana bukatar lokaci kinga dai yadda gidanmu yake bawani karfine damu ba yanzu idan na aureki yaya zanyi dake yadda kika saba jin dadi da kyale kyalen rayuwa kiduba kigani fa dankunan dake kunnenki kawai ya isa ya sayi motata harda sauran chanji kuma...
Ya isa haka isma'il kaidai in dai kawai kana sona to kasa aranka a inuwa domin duk abinda nake so mahaifina yana son sa idan kuwa yaso abu to babu abinda bazaiyi masa ba. Kaidai kabari mu karasa zakayi mamakin baba ne.
Hindu ta dan rage gudu da motar sa'ar data lura har yanzu ina cikin damuwa.
.
In kuma baka sona ne isma'il kasanar dani saina mayar dakai gida...akwai alamar karaya azuciyarta.
Nayi shiru ina tunanin gaggawa abinda yakamata nayi kenan alokacin nace.
BANA SONTA.
Ta kyaleni na huta
Tunanin abokin aikina abba yafado min.
KA RABU DA ITA NA MAIMAITA KA RABU DA ITA BA ALKHAIRI BACE AGAREKA.
Saidai kuma tsananin kaunar hindu tasa igiyar sarkar bege ya daddaure duk wata jijiyar tunani dake kwakwalwata hakan shi yasani na dubeta da rarraunan murmushi nace.
INA KAUNARKI HAR ABADA.
Wannan ita kalma mafi dadi dana tabaji tun randa aka haifeni.
Hindu tace cikin wata malalaciyar murya mai yaudarar zuciya.
*** *** ***
Hindu tayi fakin da motar adaf da kofar kayataccen ginin gidan. Gabana sai faduwa yakeyi zuciyata nata dawurwurin abinda zance dashi idan munyi ido hudu da mahaifin nata.
COOL DOWN DARLING.
Hindu tace dani tana murmushi.
Kada ki damu daman ai ba'a sama nake ba. Muka fashe da dariya duk da yake dai ni dariyar Yake nakeyi.
Hindu ta danna wani abu kofofin motar guda biyu suka bude. Ta dubeni tace
Sai mu shiga ko... Gumi na diga akan goshina kamar ledar ruwan sanyi na dubeta nace
To in banda abinki basai ki shiga ba kiyimin iso. Hindu ta sake fashewa da dariya.
Na shiga uku isma'il duk ka wani bi ka rude kamar wanda ke fuskantar fara tambayar cikin kabari Na dada share gumi
To shige gaba.. Nace muryata na rawa cikin murmushi nabi hindu abaya sannu ahankali sai gamu awani katon dakin shakatawa wanda ya linka wanda aka kawoni jiya wajen sau biyu
Hindu ta juya ta dubeni tace....HINDU - 11
.
Hindu ta dubeni tace.
Zauna ka jirani anan.
Ta wuce ciki tana rangwada. Nan na zauna inata dube dube kamar sauna azuciyata inata kokarin kiyashin makudan kudin da aka kashewa dakin shakatawar amma abanza domin kiyashin gagarata yayi duk kuwa dacewa ni malamin lissafi ne.
Ina nan zaune ina waige waige sai idanuwana suka kawo kan wani katon hoto na wata kyakkyawar mace kai wannan mace da kyau take gashi dai ta manyanta amma haryanzu sai sheki takeyi kamar hindu. Nayi mamakin ko itace mahaifiyar Hindu wacce tace min tun tana karama ta rasu. Ko dana kurawa hoton idanu sainaga daga sama an rubuta cikin manyan haruffa
SALMA.
Ko yayar hindu ce ? Na tambayi kaina amma kuma ai hindu tace dani ita kadaice batada yaya. Me yiwuwa matar babanta ce. Na dada duban hoton sannan sai nace cikin zuciyata TSARKI YA TABBATA GA SARKIN DAYA HALACCI WADANNAN KYAWAWA BIYU AGIDA DAYA.
.
Motsin danaji na takun sawun hindu shiya dawo dani cikin hankalina na daina waige waige.
Ta shigo cikin dakin shakatawar tana rausaya kamar bishiyar turare acikin iskar damina. Akwai alamun farin ciki da nishadi karara akan fuskarta.
Yace na shigo dakai. Na mike tsaye hindu ta wuce gaba ina binta abaya kamar makaho da dan jagora duk indamuke takawa tattausan kilishi ne jajur ya mamaye ko ina agidan. Kofar dakin da muka tsaya ta gilashi ce. Amma mai duhu domin baka iya ganin abinda ke cikin dakin saidai kaga fuskarka ajiki. Hindu ta tsaya gaban kofar lokaci guda kuma na dubi fuskata jikin gilashin kofar sainaga tayi sharkaf da gumi sai naso takeyi kamar funkaso cikin sauri Hindu tasa hannun rigarta ta goge min fuskata sannan saita matso daf dani har ina iya jin hucinta akan fuskata tace dani.
Cool Down mana isma'il don Allah ka kwantar da hankalinka.
Tana gama fadin haka saita tura kofar dakin muka shiga nayi tsaye cak cikin kaduwa dakin da muke ciki tsukakke ne amma mai tsayi sosai bakomai aciki sai tarin littattafai akan wata irin kanta ta farin karfe kujeru biyu ne kacal acikin dakin suna fuskantar juna da teburin gilashi agabana.
Azaune akan kujerar kofi ahannunsa sanye da doguwar riga kai ba hula EL-MAHDI ne.
.
Wannan shine karo na farko dana taba ganinsa ido da ido nasha jin labarinsa nasha ganin hotunansa a jaridu dakuma mujallu haka nan nasha ganinsa a kwatinan talabijin... Amma bantaba ido biyu dashi ba azahiri.
Koda na dube shi ayanzu sai naga yafi kyau ajikin mujallu nesa ba kusa ba fiyeda azahiri.
.
Kafin naci gaba bari na baku hoton El Mahdi dan gejere ne kakkaura baki kansa dunkulalle ne shan kwai, yana da manya manyan kumatu kamar tumfafiya hakanan duk dayake azaune yake katon tumbinsa saida ya bayyana afili yayi dare dare akan cinyarsa kai kace wani kullin kayane yake rungume dasu.
Tun daga keyarsa har zuwa gaoshinsa babu alamar gashi sai dogon sankon daya raba goshinsa biyu hadu da dama yana kyalli kamar titin mota cikin hasken farin wata. Duk wannan na lura dasu ne kallo guda.
.
Baba ga isma'il din.
Fuskar El Mahdi ta washe cikin fara'a nan da nan sainaji kamar ya kwanta min arai to amma sa'ar dana dubi yan siri sirin idanunsa masu kama dana maciji saina fara shakkar hakan.
Malam Isma'il... Sannu da zuwa.
El Mahdi yace dani cikin wata shakakkiyar murya sannan saiya dubi hindu kafin yace kala hindu tafice daga dakin tabarni dashi mu kadai.
Zauna mana ya nuna min katuwar kujerar dake fuskantarsa na durkusa cikin girmamawa na gaidashi sannan na hau kujerar na nutse aciki.
Muka sake duban juna akaro na biyu sai naji Hindu ta fado min arai. Ko kusa ko alama basuyi kama da El Mahdi ba babu abinda ya hadasu saita abu daya.
Na lura dacewa duk sa'ar da zaiyi magana saiya kashe min idanu kamar yadda hindu takeyi. Na godewa Allah dayasa hindu batayi kama dashi ba domin datayi kamar dashi to da saidai ahada da addu'a kafin ta sami shiga.
Kaine Isma'il din kenan da take bani labari. Na gyada masa kaina ina sunkuye
Tace kana sonta ko? Fadi da bakinka naji shiru ban amsa ba.
Yi magana mana kana sonta? Na gyada masaina a kunya ce ga mamakina sai naga ya saki tattausan murmushi.
Naji dadi isma'il da har kuka sami daidaituwa tsakaninka da hindu domin na dade ina fada akan ta nemi mijin da za'a aura mata taki.... Shiru dai ni nayi banyi magana ba dan ayadda yake magana bai nuna alamun yanason amsa ba.
Yarinyar nan hindu ita kadai nake da ita aduniya dan haka inason ka rike min ita da kyau... Kaga tace kai take son ta aura...
Kuma nan da sati biyu za'ayi bikin kamar yadda na shaida ma duk abinda take so ko menene indai inada iko saina bata shi. Ya dan saurara yana mayar da numfashi gamida shafar dogon sankonsa.
.
Hindu tace kai take son ta aura nan da mako biyu. Nikuma nayi mata alkawarin aura mata kai... Me kake gani gameda batun ko kanada magana....
Gumi yafara rufeni na dubeshi akaro na farko bakina na rawa nace.
Eh.. To gaskiya ni baba abubuwan duk sunzo min cikin hanzari kaga dai ni ba wani kwakkwaran shirin aure ne dani ba... Kuma mahaifina...
Kaga duk wannan karta dame ka El Mahdi ya....
.HINDU - 12
.
Kada duk wannan ta dame ka.
El Mahdi ya katseni tun sa'ar data kawo min zancenka
Nasa akayimin bincike akanka. Ya dubeni sannan yaci gaba
.
Mahaifinka malam bala tsohon ma'aikaci a ma'aikatar al'amuran gona ta kasko ya taba yin hedimasta a wata firamare ta gwamnati tsahon shekaru goma daga baya yakoma ma'aikatar kasko.
Allah yayi masa rasuwa shekaru kusan bakwai da suka gabata sakamakon ciwon hanta dake damunsa, mahaifiyarka safiya ku biyu ne agurinta kai da wata yar karamar kanwarka Amina kannenka guda hudu duk sun mutu sakamakon wani mummunan hadarin mota daya rutsa daku kaida mahaifiyarka ne kawai kuka tsira alokacin kanwarka amina ba'a haifeta ba...
Baka gaji komai ba daga gurin mahaifinka ba sai mota daya Bitil dakuma kudi yan kadan da kananan gidajen guda biyu....
Na dubi El Mahdi cikin kaduwa sa'ar dayake dubana cikin murmushin ganin yasani kaduwa.
Ya ya akayi duk kasan haka?
Ya dubeni gamida daga girar idonsa ta dama.
Ta hanyar bincike.... Isma'il idan kanada kudi abubuwan dzasu gagareka sani ko samu aduniya kadan ne... Shin bakasan babban limamin dayayi rabon gadon mahaifinka duk shekara saina aika masa da zakka ba. Ko kuwa ka mance da cewa sunan asibitin da aka kwantar da mahaifinku aciki
EL-MAHDI MEMORIAL HOSPITAL ??
Na share gumi banida tacewa.
Saboda haka da zarar na dawo daga Hongkong jibi zanzo na sami mahaifiyarka har gida domin mu shirya yadda bikin zai kasance kaje ku zauna da hindun yanzun nan ku rubuto min duk abinda kuke bukata na bikinku zanzo muku dashi. Ya danyi shiru sannan sai ya lalubi aljihun doguwar rigarsa ya dauko takardar cek ta kudi ya mika min.
Ga cek din naira miliyan biyu nan kaje kafara shirye shiryen biki idan na dawo jibi zan kara maka wasu.
Kada ka damu da zancen gida idan kun fita yanzu Hindu zata nuna maka sabon gidan dana saya muku motocin da zakayi amfani dasu kuwa duk zan taho ma dasu daga waje.
Na rufe idanuna na bude su cikin rudani. El mahdi ya dubeni cikin murmushi yace.
Ba mafarki kake ba isma'il kadan ma kagani isma'il... Me ma akayi da maza inji karya. Ai tunda kace kana kaunar auren 'yata hindu to kakarka ta gama yanke saka. Tashi ka tafi ka fitar da kudin ko kwa fara shirye shiryen bikinku.
Na... Nagode Alhaji nace bakina yana rawa Allah yasaka ma da alherinsa.
Bakada bukatar godiya ai ni keda godiya da har ka dauki hankalin Hindu takeson ta aureka. Yau shekara biyar kenan ina fama da ita... Na mike tsaye na sake gaidashi cikin girmamawa sannan na nufi kofa abubuwa kamar amafarki.
.
Af Isma'il eh mahdi ya kira sunana sa'ar dana kai kofar dakin. Na juyo cikin girmamawa.
Akwai wata farar JEEP tana nan filin fakin kace hindu ta dauko ma dan makullinta saikaje kayi maleji kafin na dawo.
*** *** ***
Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba. Zancen auren mu da hindu ya watsu ko ina duk inda na wuce sai kaga ana nuna ni wasu nacewa na dace yayinda wasu ke tayin Allah wadai suna ganin auren jari zanyi.
Abba Ali ya dubeni cikin kaduwa sa'ar da labarin ya riske shi.
Wai da gaske kakeyi? Nayi masa murmushi.
Kwarai kuwa Wallahi ni kaina abin na bani mamaki domin kaina duk a daure yake... Wannan wani abune daga ubangiji...
To amma kace fa yau saura kwana biyu a daura auren? Abba ya sake tambayata cikin damuwa.
Ga zahiri nan kagani tun shekaranjiya ko bakaga katin gayyata bane babu mamaki kuma ka dade baka saurari rediyo ba. Ganin haryanzu a rude yake saina zaunar dashi na bashi duk labarin abinda ya faru tun daga farko har karshe.
Mahaifiyata ma ba karamar kaduwa tayi ba da jin zancen. To amma sa'ar da mahaifin hindu El Mahdi ya sameta sai duk ta saraya ta hakura saboda nuna mata dayayi ya dade da sanin mahaifina.
Daga karshe yasa a ruguje gidanmu ya sake tashin sabo.
Kullum gidanmu baya kafewa da yan zuwa yi min barka wasu son gulma ne yake kawo su yayinda wasu kume ke zuwa suyi min nasiha ahaka dai har RANAR DAURIN AUREN NA da hindu tazo aka daura auren agaban shaidu sama da mutum dubu dari wanda kusan kashi tara daga cikin goma duk gayyatar El Mahdi ce.
*** *** ***
Daga inda nake zaune adakin amaryata hindu ina iya hangen cikin lambun shakatawar wanda ke haske tarwai da hasken rana. Ko a mafarki ban taba tsammanin zan sami gida kamar wanda yakai rabin wannan ba.
Hindu na kwance akan cinyata duka duka baifi mintuna ashirin da tafiyar abokaina da suka rakani sayen baki ba.
Duk daukacin dakin kamshi yake ga fitulunan naci tarwai ga kayan kyale kyale nan burjik ko ina kamar dakin amaryar indiya.
.
Isma'il... Hindu ta kira sunana ashagwabe
Na'am hindu ta shafo kaina da kyawawan siraren yan yatsunta tace. Yau burin masoya ya cika. Na lumshe idanuna cikin farin ciki domin abinda ban taba zata bane gashi kuma yana faruwa.
Tunanin gargadin abba ya fado ya fado min nan da nan sainaji haushinsa ya kamani wato ashe hassada ce kawai tasa yake neman rabani da HINDU.
Na rungumo masoyiyata hindu zuwa kirjina... Muna nan muna wasannin soyayya cikin farin ciki marar misaltuwa sannu ahankali har barci ya kwashe mu cikin ni'ima.
.HINDU - 13
.
Muna nan muna wasannin soyayya cikin farin ciki marar misaltuwa sannu ahankali har barci ya kwashe mu cikin NI'IMA.
*** *** ***
Bansan ko menene ba nidai ina barci sai kawai naji kamar ana cewa dani tashi zaune..... Nan da nan naji idanuna sun bude tarwai.
Ga mamakina sainaji duk jikina ya dauki rawa tsoron da fargabar da bansan dalilinsu ba. Dakin cikin duhu yake dan haka saina lalubi inda hindu take kwance kusa dani. Ina lalubawa sai naji WAYAM.
Na tashi zaune cikin kaduwa. Hindu.. Na kira sunanta shiru bata amsa ba sai amsa kuwwar muryata ni kadai cikin duhun.
Na lalubi makunnar lantarkin na kunna nan take dakin ya gauraye da haske. Babu hindu babu alamarta hatta dan lullubin da aka kawota dashi babu. Na sauko daga kan gadon a rude jikina na tsuma na nufi dakin shakatawa. Hindu... Nakara kiran sunanta shiru ta gaida kunnuwana. Na leka dakin girke girken Hindu. Shiru bata amsa ba. Me yiwuwa ko bandaki ta shiga tunanin hakan shiyasani murmushi.
Shashashan banza matsoraci nace da kaina meyasa da can bakayi tunanin haka ba duk ka rude. Na nufi bandakin cikin sauri na kwankwasa.
Hindu! Shiru ta gaida kunnuwata gumi da tsoro suka sake lullube zuciyata. Yanzu kam tabbas nasan hindu bata gidan na dubi agogo karfe uku na dare.
Hindu... Dan Allah in ma wasa kikeyi to ki bari kifito fili na ganki..
Shiru sautin muryata babu dadin ji.
Adaidai lokacin dana nufi kofar falo ne to da niyyar na bude na leka cikin lambu sai naji ana kwankwasa kofar a tausashe.
Wanene? Na tambaya lokaci guda muryata na rawa Hindu. Aka katseni da cewa
Yallabai nine... Muryar maigadin muce daman tun yammacin da muka fara zuwa ganin gidan nida hindu na gane muryarsa. Cikin gaggawa na bude kofar. Mukayi ido biyu da mai gadin wanda ke tsaye cikin shirin kota kwana dauke da kwari da baka. Akwai alamar damuwa karara a fuskarsa.
Yaya lafiya? Na tambaye shi.
Daman batare kuka fita da hajiya ba?
Na dubeshi a rude.
Me kake nufi... Kaga fitar tane?
Maigadin ya yatsine fuska a tsorace yana dubana
tun karfe daya ina lura da dakin sainaga an kashe wuta ba'a dade ba sai hajiya suka fito ita da wani suka shiga mota suka fice ni ne ma na bude musu kofa Wallahi na dauka tare kuke to sai yanzu kuma dana hango dakin ya gauraye da haske shine na leko naga ko wanene domin ni atunanina ma babu kowa acikin gidan.
.
Gwiwowina suka fara rawa kamar ba zasu iya daukata ba. Maigadin ya dubeni cikin damuwa sannan saiya waiga hagu da dama sa'annan yace dani cikin rada.
Ka rufa min asiri don Allah zan fada maka gaskiya tsakanin ni da kai da kuma dakin nan.
Naga wanda suka fita tare.
Hajiya ce ma ta takura min na bude musu kofa.
Kamar yaya yake.? Na tambaye shi kwalla na kokarin kwacewa daga idanuna.
Wani kato ne fari kyakkyawa mai kamar kwara.... Inajin ma kwara ne.
.
ZANCI GABA A LITTAFI NA BIYU.
IN ALLAH YASO.
.
NAZIR ADAM SALIH (NAS) 2003
.
HINDU LITTAFI NA BIYU.
BOOK 2
.
BABI NA DAYAHINDU - 14
.
LITTAFI NA BIYU.
.
BABI NA DAYA
.
Wasu abubuwane masu kama da tabaren dakan sakwara suka fara lugude acikin kwakwalwata nan da nan naji juwa na shirin daukata lokaci guda nayi sauri na dafe kofar dakin shakatawar don gudun kada na fadi. Mai gadin dake tsaye agabana cikin kaduwa yana dubana baki bude ya fahimci irin halinda Tseguminsa ya jefani.
.
Al...haji.. Wallahi ni kaina banyi niyya na nafada ma ba.. Domin na dauka mutumin dan uwan hajiya ne... Amma karfe uku fa na dare yanzu.
Duk maganganun dayake yi ina jinsa amma saboda juyawar da kwakwalwata keyi sai dishi dishi nake gani daga inda nake alokacin sa'ar dana dubeshi sainaga kamar surar mai gadin dana baro yayi tsayi zankal-kal kamar falwaya sabanin yanda na ganshi lokuta kadan da suka shude.
Hindu... Ta fita da wani... Ranar daren amarcinmu na farko?
Wannan tunanin shi ke dada sa kwakwalwata juyawa kamar tayar mota.
.
Alhaji ka koma ciki ka dan runtsa.. Naga kamar bakajin dadi. Maigadin yace dani shi kansa yasan abinda yafada tsabar shirme ne yaya wannan kato zai dauke min mata ina barci su fice tare aranar daren amarcinmu na farko sannan kuma yace dani wai na tafi na runtsa!
Chab... Runtsawa wacce iri???
.
Kayi hakuri Alhaji. Naji maigadin yaci gaba da fadi.
Mu barwa gobe komai... In kuma kana ganin akwai matsala babba... To kaje ka bugawa yan sanda waya... Maganar daya fada tasa tayimin ma'ana to sai kuma wani tunani ya sike maganar shawarar tasa lokaci guda daga cikin zuciyata ayanzu dai dagani sai shi kawai muka san da labarin cewa wani kato ya fice min da matata karfe uku na dare... Haka zuciyata taci gaba da cewa idan ko na sanar da jami'an tsaro asirinka yagama tonuwa kenan domin bashi kawai ba duk labarin saiya watsu ako ina kamar wutar daji.
Tunanin haka shi yasa na godewa Allah dayasa dawakan dake sukuwa acikin kwakwalwata basu take zararrukan tunani na ba.
Na...gode mai gadi. Nace dashi muryata na rawa.
Koma gurin aikinka kasa ido kada ka bar kowa ya shigo ko fita daga gidan nan.
An gama yace dani yana zazzaro idanu cikin barazana saikace wata uwar bindiga ce ahannunsa ba kwari da baka ba.
Tsahon mintuna ina nan tsaye kaina nata kewayawa har maigadin ya bace cikin lungunan dake farfajiyar gidan.
Na lallaba ahankali domin na koma dakin barci amma abin yaci tura domin in banda taimakon manyan kujerun dake dakin shakatawar da sai keyata ta sha kasa sakamakon juwar dake daukata.
Ganin ina neman naji wa kaina rauni shiyasa na nemi sulhu na zabi daya daga cikin dogayen kujerun daban taba hawansu ba sai ayanzu na kwanta akai rigingine cikin bakin ciki da kunan rai sai naji hawaye yafara sartu akan kumatuna... Nan da nan sainaji na fara sheshshekar kuka.
.
Hindu... Hindu!! Yaya zakiyi min haka! Nace ni kadai cikin dakin. Yanzu ashe hindu bakida tausayin wanda zuciyarsa take kan begenki... Haba Hindu.... Shashshekar kuka ta sarke muryata.
.
Acan wani bangare na makwabtanmu wani zakara ya rangada cara kikiriki nasan bazan dade ba kuma zakara mai hula shima zai rangada tasa carar takiran sallar asuba.
Har sa'ar da hasken rana yafara fitowa zuciyata bata gano dalilin da zaisa hindu tabi wani katon banza ba adaren amarcinmu na farko.
*** *** ***
Ina nan kwance ko wani kwakkwaran motsi banayi ni ba barci ba ni kuma ba ido biyu ba gani nan dai nayi fakare idanun na bude amma bana ganin komai sai abinda ke zuciyata. Tambayoyin dake zirga zirga cikin zuciyata sunfi cikin carbi mai dubu to amma tambayoyi uku suna so ace nasami amsar su awannan lokaci
Shin meyasa Hindu ta nuna tana matukar kaunata?
Meyasa ta takura akayi mana aure cikin gaggawa?
Shin me kuma yasa duk da wannan bai hanata fita da wani katon banza ba aranar daren amarcinmu na farko.
.
Kasani ma ko dan uwanta ne suka fita tare... Wata zuciya ce ke cewa dani... Amma kuma ko dan uwanta ne saita rasa lokacin da zasu fita sai karfe ukun dare?
Kafin hasken ranar dake ratsowa ta cikin tagar dakin dake fuskantar kayataccen lambun shakatawa ya fara zafi hakan shi yasani mikewa zaune idanuna sai zafi sukeyi kamar zasu fado haka nan hakarkarina na dama sai ciwo yakeyi ga gefen wuyana duk ya sandare domin tun dana kwanta da bangaren banyi juyi ba ko sau daya.
Na wuce bandaki kai tsaye ina tangadi kamar dan giya tsawon mintuna shirin ina kwarara wa kaina ruwan sanyi da shawa ruwan yayi matukar taimakawa wajen wartsakar dani tsawon mintuna goma sha biyar nayi alawala sannan nayi ramuwar sallar asuba data wuceni cikin hargitsin rayuwa.
Sa'ar dana gama dan shishshiryawa sai na nufi madubi na dubi kaina aciki abin dana gani yayi matukar tsoratani naga fuskata ta jajjeme idanuna sun faffada acikin ramukansu haka nan sunyi jajur kamar gauta. Cikin sauri na dauke fuskata daga fuskar madubin sannan na saje nazarin kyawawan dakin shakatawar da kayan alatu babu abinda yarasa.
Sannu ahankali sai idanuna suka kai kan tafkeken hoton mu dake jikin bango nida Hindu ne ajikin hoton tana sanye da bakin leshi wanda aka kawata shi da dishi dishin faffaÉ—an duwatsun lu'ulu'u.......HINDU - 15
.
Sai idanuna suka kai kan tafkeken hoton mu dake jikin bangon nida Hindu ne ajikin hoton tana sanye da bakin leshi wanda aka kawata shi da dishi dishin fafaffen duwats na lu'u lu'u har jikin hoton daukar idanu sukeyi kamar agaske. Hoton an dauke shi ne kwanaki uku kafin daurin aurenmu.
.
Na matsa daf da hoton kwalla na kokarin kwacewa daga idanuna na dafa hoton gamida kurawa kyakkyawar fuskar hindu idanu bana ko kiftawa kamar bala'i ina nan tsaye bacin rai da wutar begenta sai dada ruruwa sukeyi acikin zuciyata Hindu... Na kira sunanta a tausashe

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment