Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai kace itace nan tsaye ba hoton ta ba.
Hindu... Meyasa kike son tozartani bayan duk duniya babu abinda nake kauna idan bake ba? Wani zazzafan hawaye yayi sahu akan fuskata. Cikin sauri na juyawa hoton baya sannan na nufi tagar dakin na janye labulen sa'annan na dubi farfajiyar lambun sassanyar iskar safiyar na bugun fuskata. Nayi ajiyar zuciya lokaci guda kuma idanuna suka kai ga maigadi wanda ke zaune karkashin wata bishiyar lemon zaki kwanon abincin karin kumallo agabansa haka shi yasa cikina ya dauki kara... Ashe yunwa nakeji haka shi yasani juyawa na nufi dakin girke girke wanda aka kawata shi da duk wani abu da mutum yake bukata.
Najima akofar dakin girke girken tsaye ina kallon kayan gilas da aka cika dakin dashi duk inda ka duba cikin dakin kana iya ganin fuskarka jiki kamar madubi daman duk bangon dakin dabensa na farin tayal ne. Takaici ya lullube zuciyata sa'ar dana lura da cewa duk fa wanan saboda ni da Hindu mahaifinta yasa akayisu sai gashi tun ba'aje ko ina ba har
AMARYAR TA GUDU TA BARNI.
Daga nan kwaryar dakin girke girken daga arewa wani katon firji ne fari yanata aiki gamida bada wani irin sauti wur wur na nufeshi cikin lalaci na bude kofar firjin cikin ganda. Acike yake da kayan tande tande da lashe lashe wanda mafi yawa daga cikinsu abincin gwangwani ne dakuma wasu nau'ika na bubuwan da ake bukata a dakin girke girken domin shirya abinci na musamman dayawa daga cikin kala kalar abincin ma bantaba ganinsu ba. Dan haka sa'ar danayi tsaye ina duban kayan dake ciki sai nafara sha'awar abinda zan zaba na watsawa tumbina bayan wasu yan dakiku na hangi wani abu mai kamar biredi ma'abocin kwaroron ciki da wasu abubuwa aciki masu kama da nau'in kayan zaki cikina yafara kara ciikin damuwa da kuma kaguwa saina kai biredin bakina sanu a hankali sainaji bakina ya kauraye da zaki amma abin mamaki nan da nan sainaji duk abincin ya gundureni cikin sauri najefa sauran cikin firjin sannan na rufe gamida goge bakina da gefen hannun rigata ban damu ba.
.
Meyasa hindu tayi min haka?
Naci gaba da tambayar kaina. Irin wadannan tambayoyi marasa amsa su suka sa abincin ya gundureni duk kuwa da cewa cikina najin yunwa.
Sa'ar dana gangaro zuwa farfajiyar gidan sanye nake da doguwar riga da wando na danye boyel kafafuna sanye cikin bakin takalmi saidai kuma kaina babu hula ahaka na gangaro cikin sauri ina duban agogo karfe tara na safe.
Tun daga nesa maigadin ya hango ni nan da nan ya keto aguje yana zuwa sai ya zube agabana jiki na rawa kamar mazari.
Alhaji barka da asuba...
Lafiya kalau nace dashi lokaci guda kuma ina dubansa adurkushe agabana...
Nayi mamakin inhar yana yiwa iyayansa irin wannan ladabi nakuma tabbatar dacewa yan kwanaki kadan da suka wuce ban ishe shi koda kallo ba ballantana ma har ya durkusa min. KUDI. Lallai kudi gumakan zamani ne ni nasan bawai ni yake girmamawa ba ko kusa ko alama ban taba zolayar kaina da wannan zancen banza ba. Nasan duk girman dayake nuna min kudi yake girmamawa bawai ni ba.
Bakaji motsin komai ba cikin dare ko? Na tambaye shi ina dubansa maigadin ya girgiza kai cikin sauri kamar kadangare daga inda yake tsaye ina iya sautin kashin wuyansa a sa'ar dayake girgiza kan.
.
Wallahi.... Banga motsin komai ba ai danaga wani abu da tun sa'ar dana sameka dinnnan bansake ko tsugunnawa ba ballanata ayi zancen wani abu waishi gyangyadi. Barci kuwa daman ni banshi ba sam.
Zirga zirga na dingayi daga bangaren gabas zuwa na yamma daga na arewa kuma zuwa na kudu banji motsin komai ba.
Yayi shiru ga barin shegen surutunsa nasan kusan kashi casa'in na daga abinda yafada duk karya ne to saidai nikuma alokacin banida lokacin da zanbi kwakkwafi...
Abinda yafi damuna shine
Ina hindu ta shiga? Dawa kuma ta fita?
Me kuma yasa ta fita?
.
Kasa idanu akan duk wanda zaizo gidan nan... Ni zan fita saina dawo.
Cikin sauri na juya na nufi inda motocinmu guda hudu sukke uku ne kawai suka rage da marsandi honda sai kuma fijo din 306 wannan shiya tabbatar min da cewa lallai hindu acikin Ledus dinta ta fita.
Maigadin ya wuni aguje sa'ar dayaga na nufi motocin suke tsaye cikin jerin sahu.
Tun kafin naci rabin gurin shi tuni har ya karasa yana zuwa saiya tsaya jikin marsandi yana jirana na karasa...
Ina zuwa saiya miko hannu cikin yadabi yace.
Alhaji kawo dan makullin
cikin jin nauyi da dimbin kunya na mika masa dan mukullin akan dole badan ina so ba domin irin wannan rayuwa bakuwace agarenHINDU - 16
.
Domin irin wannan rayuwa bakuwace
agareni na saba duk abinda zanyi nayi
kawai da kaina.
.
Cikin abinda baifi yan dakiku ba ya bude min
gidan gaba na motar nashiga sannan yayi
tsalle gefe guda yabani hanya sannan ya
dubeni gamida tattausiyar kunya yace To
Bismillah. Koda na dubeshi alokacin sai naga
alamar da ace zan bashi dama shi mai iya
dagani ne cancakat ya sakani acikin motar
saboda tsabar iya fadanci.
Adawo lafiya alhaji Allah kiyaye saika dawo....
Yana nan yanatayi har sa'ar dana tuka motar
na barshi nan tsaye.
Sa'ar dana dubi madubin motar saina hango
shi tsaye daga can nesa haryanzu yana
kallon motar. Tuni jikina yabani cewa
maigadin bai daukeni akomai ba face yana
mai sha'awar auren kyakkyawa da kudi.....
Wacce kuma tun ba'ayi nisa ba har na fara
dandana kudata. To koma dai me zuciyata
ke ayyanamin alokacin duk abanza domin
abu dayane kawai araina shine A INA ZAN
SAMI HINDU ?
*** *** ***
A wannan karon sabanin lokutan baya hon
daya kawai na danna saiga masu gadin
aguje suna rigegeniyar bude min kofar kai
kace tsammani sukeyi ko banida burki.
"Barka da zuwa! Sukace baki daya sa'ar
dana wuce su ahankali cikin motar ina daga
musu hannu na nufi cikin farfajiyar gidan.
Bayan nayi fakin da motar saina wuce kai
tsaye zuwa kofar gilashin da ayanzu
nagama sabo da ita duk da yake dai
amaryar ta gida ta kami amma haryanzu da
ina daukan gidan amatsayin gidanmu.
Lokacin dana karasa kofar saina tsaya nan
da wani dan lokaci ina numfasawa bayan
yan dakiku saina danna Kararrawar ahankali
tun kafin ma na dauke hannuna daga kan
kararrawar kofar ta bude sannan ahankali
kamar aljani sai dattijon ya bayyana abayan
kofar yana kifkifta idanu kamar budiddigi
har yanzu sanye yake fa fararen kayansa
doguwar riga da wando kansa babu hila to
amma tana nan rike ahannunsa. Barka da
zuwa alhaji.
Yace dani bakinsa na wangale. Nasan
abinda yasa shi rikicewar domin yasan
yanzu ba da bace. Dan na zamo sukuri
agidan hakanan daidai nake da kowanne
dan gidan mai yanci.
Yauwwa sannunka dai nace dashi sannan
lokaci guda saina fuskanci ashe banma san
me yakamata na tambaye shi ba.
Domin abinda yafaru adaren jiya wani
abune dayake sirrina.
Shigo mana daga ciki yallabai ko abin sha ne
akawo maka.... Saidai kuma kayi hakuri da
abinda zan kawo maka domin gidan babu
kowa aciki. Naji gabana yafafi.
Babu Kowa Aciki ?
Dattijon ya gyada kai kwarai kuwa kasan ai
alhaji baya gari. Ya danyi shiru wani
sassanyan gumi yafara sakkowa jikina. Wato
dai hindu batazo gidan ba kenan nace cikin
zuciyata koda na dubi dattijon sai naga ya
kuramin idanu yana kallona akwai alamun
tambaya a fuskarsa me yiyuwa saboda
gumin dayaga inayi ne to saidai kuma na
tabbata bashida kwarin gwiwar da zai iya
tambayata.
Af. Na mance alhaji zaiyi tafiya.
Nace dashi cikin gaggawa lokaci guda kuma
ina kokarin share gumin dake kokarin shiga
cikin idunana.
Basai ma ai na shiga ciki ba.
Naci gaba da cewa Ina duban agogo.
Sauri nakeyi ina ganin ma ba sai na shiga
ba... Daga nan zan koma daman zuwa nayi
na gaida shi datttijon ya dan rankwafa
agabana gami da susar kansa da busassun
yan yatsunsa wadanda babu alamar tsoka
ajikinsu sai jijiya.
Ina kyautata zaton ma in ya dawo ai zai
aikowa da Hajiya cewa yadawo. Dattijon
yace na dubeshi a rude ina tunanin wacece
kuma hajiya?
Wata zuciya tace dani kai sha sha sha
Matarka hindu yake nufi tunanin hakan shi
ya sani sauri nace. Oh... Eh insha Allahu idan
Allah yadawo da shi zan dawo na tuna da
cewa kallona yakeyi yana nazarin fuskata
akwai wani abu acan cikin raina dake
takurani yana ingiza zuciyata yana cewa
dani fada masa fada masa isma'il halin da
kuke ciki kaida amaryarka Hindu.
Ban yarda da kururuwar ba dan haka saina
toshe hakan dan ma gudun kada kururuwar
taci gaba saina lalubi aljihuna na dauko
takardun kudin dani kaina bansan ko nawa
ne ba na mika masa.
Ga wannan baba... Sai ya dawo.
Cikin sauri busassshen hannunsa na rawa
ya warci kudin daga hannuna sannan saiya
durkusa cikin girmamawa.
Nagode Alhaji.. Allah yasaka ma.
Bakomai nace dashi sannan na juya cikin
sauri zan nufi motata.
Alhaji....dattijon ya kira sunana muryarsa na
rawa sannan ya dada da cewa. Dan Allah
idan kaje gida ka isar min da gaisuwata ga
HAJIYA HINDU.
.
BABI NA BIYU 2
Lokacin dana baro gidan cikin dankareriyar
motar sai zuciyata ta shiga rudani domin
daga nan bansan kuma ina zan dosa neman
hindu ba.
Da farko wata zuciya tace dani yakamata ka
sanar da mahaifanta... Wata zuciyar tace
dani a'a bai kamata ba haka tun da wurwuri
ka sanar da danginta kamata dai yayi ace
kayi iya kokarinka idan daga yanzu zuwa
dare baka gano Hindu ba saika sanar da
danginta.
Kai wannnan masifa dayawa take nace da
kaina sa'ar dana dubi fuskata ajikin
madubin motar.
Na dauke kan motar ahankali nayi fakin da
ita agefen babban titi mafi girma aduk cikin
titunan birnin Sarauniya bayan na kashe
injin motar saina kifa kaina akan sitiyarin
motar nafara karatun wasikar Jaki.
Yanzu Ina ka nufa? Na tambayi kaina.
Nasan abune mai wuce ace.HINDU - 17
.
Nasan abune mai wuya ace hindu tana daya daga cikin gidan kawayenta... Kuma in ma acan din take gidan wacce kawar zan fara zuwa tunanin gagaruwar walimar da mukayi ajiya kafin Hindu ta tare agidanta ya fadomin.
Lokacin da gurin liyafar ya cika makil da samari da yan mata sainaga na zamo bako domin in ka dauke yan tsirarrun abokaina wadanda na gayyata zuwa liyafar babu wanda na sani cikin gayyar Hindu.
ASIYA zo ki gaisa da angon nawa mana.
Isma'il Darling wannan itace babbar kawata MANUBIYA... Waccan mai Blue din gwaggoron Class mate dinace a sakandire sunanta ZAHIDA... Maganganun hindu na gurin liyafar sukaci gaba da daddawowa cikin zuciyata garai garai kamar a faifan garmaho.
Dan haka sa'ar da zuciyata taci gaba da tunanin ko naje nemanta gidan kawayenta saina fuskanci hakika tunanin yanada matukar rauni domin ko kawarta daya ban taba sani ba sai abikin aurene na gaggawa.. Aure ne na rashin fahimtar juna... Aure ne na kuskure a tunanina aure ne da akayi shi a murde... Murdewar da haryanzun nan ban gano bakinta ba balle nayi kokarin warwareta.
Na dago kaina firgigit na dawo daga dogon tunanin da zuciyata ta tsunduma ciki adaidai lokacin danaji anata danna hon din mota daf dani. Na juya ahankali sannan saina ganshi yanayi min Murmushi.
Lalala... Lala... SHEHU HARUNA... Mafarki nake koko da gaske nake ganinka nace cikin fara'a mutumin dana tsaida motar honda legend adaf da tawa wani tsohon abokina ne wanda rabona dashi tun muna jami'a
ba mafarki kake ba isma'il nine dai kake gani. Ya matso daga kan kujerarsa ta direba zuwa kujerar dan zaman banza ya miko min hannu tacikin tagar motar muka cafke.
Ashe dai rai kanga rai wai dan koli yaga fura... Nace dashi cikin dariya
Wallahi isma'il harkoki ne sukai yawa... Ya danyi shiru saikuma yaci gaba. Naji dadin ganinka Wallahi isma'il daman na dade ina nemanka amma saduwa tayi wuya... Kodayake dai... Ya danyi shiru gamida kashe min idanu yace.
Yaya kwanan amarya? Gabana ya fadi gamida mamaki
A ina kuma ka sami labarin aure na?
Haba isma'il ai duk dayake kai kun jefar damu kun manta damu to hakan bazai hanamu samun labarin aurenka ba...
Duk dayake dai ba'a gayyace mu ba to amma dai muna murna.
Ahaba shehu haruna ai kai kasan dana san inda kake ai danazo sanin kanka ne wancan tsohon gidan ku na da nasani.... Shehi haruna ya katseni cikin murmushi yace.
Yanzu dai mubar wannan zance zaman me kakeyi anan kai kadai...
Gabana ya fadi ras.
Wani friend dina nake jira yafito tare dashi mukazo yashiga gidan can... To ka sanni fa daman ni bansan yawan gaishe gaishe shiyasa nace yaje yafito zanjirashi anan.... Shehi ya dubi kofar gidan dana nuna masa acan tsallaken titi...sannan ya zunkuda kafafa gamida duban agogo.
Kai amma dai isma'a kabaro amaryar da wuruwi... Ba jiya jiyan nan ne naji ance zata tare ba? Zuciyata na kuna na dube shi nasan abinda yafada gaskiya ne bai halatta ace nabaro gida da sanyin safe ba. Na dubi agogona.... Sha daya saura kwata na safe.
Haba shehi... Nace cikin karfi hali karfe sha daya fa saura kwata. Shehi ya harareni.
Ai Wallahi in nine keda sabuwar amarya kama kai wallahi bazan fito ko kofar gidan ba sai hudu haba ka tuna fa yau fa lahadi ba aiki zakaje ba.
Kai Shehi. Muka fashe da dariya tsawon lokaci muka danyi muna tattaunawa sannan sai yace.
Isma'il daman ba wani abune yasa nake nemanka ba sai wata dan matsala dana sami kaina aciki.
Na dubeshi nama rasa haushi zanji ko kuwa fashewa zanyi da dariya. Matsala! Ni kuwa yanzu awannan lokaci har akwai wanda zaice da wata matsala wadda ta fi tawa?
Waccce matsala kuma?
Yawwa tsohon abokina nasan wallahi da tuni gurinka nazo da wannan matsalar da tuni ka warware min ita Shehi yace dani.
Bari dai na gyara fakin sai in dawo cikin motar taka mu dan tattauna da kyau.
Maganganunsa sun gama gundurata yaya zaiyita damuna da wasu zantuttuka bayan ni ga irin bala'in dana shiga naji kamar na kwala masa ihu nace dashi ya rabu dani... Amaryar tawa ta gudu to amma bance hakan ba.
.
Bayan yagama fakin sai ya bude gidan gaban motata ya zauna kusa dani.
Isma'il me yiwuwa ka daukeni shashasha... Kokuma ma mahaukaci idan kaji abinda zan fadama ayanzu... To ko ma dai me zakace dani ban damu ba. Ya danyi shiru.
Ina jinka.. Nace dashi cikin kaguwa don yayi maza yafadi abinda yake son fada ko ya barni natafi neman abar kaunat Hindu.
Isma'il... Na kamu da ciwon so...
Ciwon son wacce ayanzu haka banma san takamaiman inda take ba.
To kuma menene amfanin maganar in bakama san inda take ba nace dashi a fusace.
Kada ka jani da sauri... Bini ahankali in baka wani labari.
Nayi shiru ina sauraronsa. Badon inaso ba sai dan babu yadda zanyi na iya cewa dashi fice daga motata.
Na dade da ganinta isma'il shehi yafara bani gudurarren labarin.
Kyakkyawace fiyeda yadda baka zato lokacin dana fara dora idanuna akanta saida naji kamar banida lafiya saboda tsabar kaduwa.
A WATA LIYAFA.
Nafara ganinta lokacin dana ganta saina kasayi mata magana ka sanni Isma'il tun muna jami'a ni ba..HINDU - 18
.
Ka sanni Isma'il tun muna jami'a ni ba mutum bane mai iya tunkarar mace da zancen soyayayya kai tsaye. Ahaka inaji ina gani har aka watse daga liyafar lokacin dana koma gida saina kasa moruwa barci da tunanina duk nata ne...
Babu wani numfashi da zanyi batareda nayi tunaninta ba da naga abin yana neman sani zautuwa saina fara bin abokaina ina neman ko akwai wanda yasanta kowa sai yace shima anan yafara ganinta kuma duk ta burgesu.
Yau kusan wata shida kenan sai kwanan an wani abokina yace min wai ya ganta a jami'ar sarauniya zaka sha mamaki idan nace dakai ko sunanta ma ni bansani ba.. Amma yadda tashiga zuciyata da'ace ni wani kwararre ne abangaren zane to dana zana ma hotonta... Kuma...
Na katse shi da cewa
To in banda abinka Shehi yarinyar da bakasan daga inda take ba bakasan sunanta ba me zan iyayi ma akai?
Shehi ya dada matsowa daf dani yace.
Kaifa isma'il wallahi banza ne yanzu fa nake fadama yarinyar nan a jami'ar sarauniya take... Ko bakasan inada labarin cewa kai malami ne a jami'ar ba? Bakada hankali Shehi.. Nace dashi cikin mamaki.
Banyi mamaki ba dan ka kirani da mahauci daman duk sauran abokaina ma idan nafada musu labarin hakanan suke cewa dani.. To amma in banda abinka menene abin rauni dan ka bayyana ra'ayinka da kuma damuwarka ga abinda kake so?
Hakan ba laifi bane... Amma kai yanzu da hankalin ka da komai shehi yaya kake tunanin zan iya ganin yarinya daya jal... Daga cikin dubunannan daliban jami'ar sarauniya? Shehi yayi ajiyar zuciya lokaci guda kuma yana duban katon titin dake gefenmu motoci nata zirga zirga.
Isma'il... Yakira sunana. Ni walllahi duk na rude kaji na rantsema da Allah wallahi in banga yarinyar nan ba bana tsammanin zan auri wata 'ya mace adoron kasa. Da Allah isma'il ni da kai na dogaro kaine Last hope dina domin na tabbata yarinyar nan daliba ce a makarantarku.
Dole kasan kai zan bari ka tsaramin ita..
In kuwa kudi yana amfani aduniya ko nawane koda zan tsiyace na zamo ina yawo rabin jikina tsirara saina aure ta.
Yau naga abinda ya isheni. Shehi yafa kamata inma tabuwa kayi to ka dawo cikin hankalinka.
Me kake nufi to? Ya tambayeni.
Shehi mu ma dauka yarinyar nan da kake so dalibar jami'ar muce to ni dai kasan ban santa ba a ido bansan sunanta ba to yaya kake tsammanin zan iya gano maka ita?
Shehi yayi shiru yana dubana shi kansa ya fuskanci abinda nace dashi yana da alkibla. Mukayi shiru na kusan mintuna biyu muna duban juna can sai shehi yace dani.
Gaskiya ne abinda kafada isma'il
nayi ajiyar zuciya cikin jin dadi bawai dan ya fahimci abinda nake nuna masa bane sai dan ina tsammanin zancen namu yazo karshe zaifice yabarni natafi neman amaryata.
Isma'il duk da haka idan yanzu Allah ya nuna min ita zamuje dakai ka tayani tsari?
Kwarai kuwa me zai hana. Nace dashi cikin gaggawa domin na matsu ya rabu dani in kama gabana nasan bazai ma tba ganinta ba har abada.
Shehi ya dubeni cikin murmushin jin dadin abinda nafada sannan saiya lalubi aljihunsa ya dauko wani kati wanda aka rubutu ajikinsa da tawada mai launin azurfa ya miko min.
Itace lambar GSM dina kaima saika bani taka kaga in an dace saina sanar dakai. Cikin gaggawa na dauko katina nima na mika masa wanda shine ke dauke da lambar wayata na sake yin ajiyar zuciya akaro na biyu sanda naga shehi haruna ya bude kofar motar yafita sannan saiya sunkuyo da kansa ta cikin tagar motar yace.
Banza naga sai wani shashshan kunu kakeyi... Na dame ka ko naga har wani korata kakeyi to bari kaji daga yau ma duk sati zaina ziyarci ofishinka ko Allah zaisa na dace.
To saikazo din uban soyayya
muka fashe da dariya.
Kada ka manta idan kaje ka mikamin gaisuwata ga amarsu... Saura kuma ka bata labari. Muka sake fashewa da dariya saidai kuma shine ke dariyar domin ni Yake nakeyi.
*** *** ***
Karfe goma sha biyu saura mintina ashirin nakoma kofar sabon gidana ba wani abu ne yasani komawa gidan ba sai dan na rasa inda zan dosa ne neman Hindu kwakwalwata duk ta rude bayan rabuwata da shehi sai naga abinda yakamata shine nakoma gida na sake tunani a nutse.
Mai gadina ya taso da gudu ya bude min kofa sanan yabiyoni aguje har zuwa filin fakin ina firowa daga motar saina lura da wata katuwar marsandi ruwan toka motar bakuwace.
Barka da zuwa Alhaji ya gaidani cikin damuwa na lura shima hankalinsa a tashe yake.
Babu wanda yazo nemana ko?
Maigadin ya dubi kayataccen gidan dake boye abayan furanni da bishiyoyin dabino yace.
Akwai baki acikin dakin shakatawa suna jiranka.
Naji gabana yayi ras! Baki? Maigadin ya gyada kai yace kwarai kuwa yan matane su biyu ga motarsu nan.
To ina zuwa jirani naje na gano ko su waye kirjina na dukan uku uku na shiga falon da sallama
.
SANNU DA ZUWA ANGO
Yan matan biyu suka gaisheni da zazzakar murya kamshin turaren dake jikinsu ya bugi hancina nayi sa'a ina dubansu na gane fuskarsu kawayen Hindu ne tabbas na gansu acikin liyafa da akayi jiya.
Ango mijin amarya wata mai dogon wuya kamar barewa daga cikinsu tace dani.
Ina ka dauke amaryar ne tunda sassafe.....HINDU - 19
.
Ina ka dauke amaryar ne tunda sassafe kuka bar gidan ba kowa gurinta mukazo mu ba gurinka ba.
Cikin fara'a na tsaya kamar ruwa ya cinye ni ban iya mai da mata da murmushinta ba kuma kai kanka kasan banida amsar bata.
.
BABI NA UKU 3
Na karasa shigowa cikin falon kafata na rawa kamar kafar roba na tabbata in har na dada dakiku goma atsaye faduwa zanyi agabansu dan haka saina nemi kujerar dake fuskantarsu na fada ciki Jagwam kamar kayan wanki.
Na dube su da murmushin yake gamida share gumin dake zuba kan goshina kamar kuturu.
Yaya gajiya... Ina fata dai kunje gida lafiya...
Lafiya lau ango suka amsa lokaci guda suna kallona saidai kuma akwai alamun mamaki a fuskarsu na ganin haryanzu amarya Hindu bata shigo ba domin daga abinda suka fara fada lokacin dana shigo falon na tabbata su tsammanin suke tare muka fita da amarya hindu.
Nayi shiru zuciyata nata dawurwurin neman irin karyar dayakama na shirya musu.
Ina ka boye amaryar ne?
Ko rowarta kakeyi ne naga haryanzu ita bata karaso ba Mai dogon wuyan kamar barewa ce ke maganar dayar ita tayi shiru bata magana saidai in mai wuyan barewar tayi magana ita saita saki tattausan murmushi da kan tunamin da amaryata Hindu.
Haba dai rowa. Nace cikin karfin hali gamida dariya
Ni ina isa na boye muku kawarku... Ai kun fini kusa da ita Mai wuyan barewar ta harareni.
Haba dai ango wannan tsohon zance kenan amma yanzu ai duk duniya babu wanda ya fika kusa da Hindu. Muka fashe da dariya, su cikin farin ciki ni kuwa cikin zullumi da kunan zuciya.
(Ina ma abinda ta fada hakane babu wanda yafini kusa da hindu)
Nace cikin zuciyata.
Ashe bata fada muku ba... Jiya.
nace dasu kwakwalwata kuwa tana kokarin kirkirar hanyar da zan rufe musu sirrina yan matan biyu suka dubeni cikin mamaki akwai dan alamun razana a fuskarsu na dube su da murmushin karfafa gwiwa nace Chab.
Ah kai bafa wani abin tashin hankali bane daman ai yau da asuba zasu tafi ita da baba... Na danyi shiru ina dubansu ina kokarin ganin ko karyar ta sami matsugunni.
Ina suka tafi...
Hongkong suka tafi... Kinsan yadda Hindu take wasu kayayyaki ne aka siyo mata na al'amuran zaman aure shine data gansu ta raina tace saidai a tafi da iya ta zabo. Nayi shiru kirjina na dukan uku uku ina nazarin fuskokinsu shin zasu gane karyata?
Ga mamakina sai naga mai dogon wuyan ta tafa hannu gamida sakin wata malalaciyar dariya cab ta tafi Hongkong ta barka anan kai kadai... Gaskiya hindu ta gama da kai.
Kwana daya da tarewa kuma ko wani cikakken kwanan batayi ba... Yar banza Hindu. Yan matan biyu suka fashe da shewa harda tafawa da juna nayi ajiyar zuciya jikina ya dauki rawa.
Ai ba komai abinda... Sati uhm kwana uku ma zatayi ta dawo. Budurwar mai wuyan barewa ta dubeni gamida tabemin baki.
Saikayi ta zaman amarci kai kadai
yan matan biyu suka mike zumbur lokaci guda suna murmushi.
Mu zamu tafi angon kai kadai in ta dawo kace ta bugo mana waya.
Suka nufi kofar falon. Na mike jikina na rawa na bisu abaya muna kaiwa daf da kofar fita sai mai dogon wuyan tayi kwafa sannan ta juyo ta dubeni tace.
Wannan Amaryar taka makaryaciya ce Wallahi kaga dai banida wata kawa data fita amma wani lokaci irin wannan karyar da take samu bata na dubeta cikin mamaki.
Kowacce karya tayi miki kada fa ki takurawa amaryata... Dan kinga bata nan.
Wani zancen takura wallahi ai ita tayi min laifi dole ne na fada.
Laifin me tayi miki? Na tambayeta ina murmushin yake.
Sai fa dana bugo mata waya kafin na zo tace dani nazo tana nan!
Murmushin dake fuskata ya subuce lokaci guda kamar kwallon mangwaron dake hannun yara.
Kin bugo mata waya? Na tambayeta muryata na rawa.
Kwarai kuwa na bugio mata..... Wai don tsokana ma dana tambayeta kai saitace wai gaka nan kusa da ita wai kana barci kuma bazata tasheka ba.
Wani irin abu mai kama da kafafun giwa ya fara zungurin kirjina kamar zai karya kasusuwan hakarkarina.
Da misalin karfe.... Karfe nawa ne kika bugo mata? Na tambaya awannan karon muryar tawa na rawa kamar ana girgizani.
Yarinyar ta danyi shiru na dan lokaci hannunta dafe da kugunta ta dubi farfajiyar gidan cikin tunani can saita juya tace
Inajin waje karfe tara na... Kwarai kuwa tara ma saura minti uku na safiyar nan. Ta dubi agogon dake hannunta gashi yanzu har sha biyu tayi..... Yanzu kusan awana uku da bugowa kenan!
**** **** ****
Harzuwa karfe daya saura na rana ina nan zaune bana ko motsi kamar wanda aka tsafe zuwa siffar dutse.
Hakika abubuwa da dama sun faru tun daga karfe uku na dare zuwa yanzu.
Wato ashe dai hindu har magana tayi da kawarta asafiyar nan abin dana fara tambayar kaina shine a ina take sa'ar da kawar tata ta bugo mata wayar?
Babu amsar tambayar dan haka sai haushi ya dada kasheni lokaci guda kuma zargi kaina da batan basira domin abinda ya kamata kenan nayi tun daren jiya na buga lambar GSM Di Hindu.
Jikina na rawa na mike tsaye juwa sai kokarin fyadani da kasa takeyi na nufi dakin kwananmu inda na baro wayar

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment