Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafi da gidanka akan gado.
Nayi kusan mintina goma sha biyu ina zaune dauke da.........HINDU - 20
.
Nayi kusan mintuna goma sha biyu ina zaune dauke da wayar a hannuna ina mai kokarin samun kwarin gwiwar bugawa.
Farkon bugawa naji gabana sai faduwa yakeyi domin haryanzu na kasa yin imani da cewa wai Hindun da aka kawomin amatsayin amarya ce adaren jiya duk ta jefani acikin wannan bala'i na rashin sanin makama.
Hakan nace cikin zuciyata akwai wani bangare dake cewa dani idan ka buga wayar sakamakon da zan samu ba zai zamo mai faranta rayi agareni ba.
Jijiyoyin jini dake duk wani bangare na jikina sai harbawa suke zil il kamar ana zukemin jinin jikina.
Na kalli wayar tafi da gidanka dake hannuna sai naga duk da yake zuciyata na kururuwar na ajjeta na fasa bugawa bazan iya ba domin kome zai faru saidai ya faru dan daga nan zuwa dare za'ayita ta kare kodai na gano inda Hindu take kokuma na sanar da mahaifinta azuciya nayi mamakin irin yadda mahaifinta zai dauke zancen.
Hannuna gamida duk bangaren jikina na rawa nafara daddana lambobin ba'a jima ba na shigar dasu.
.
Acan daya bangaren naji ina bugawa sa'ar dana karata a kunnena nayi mutuwar tsohuwa ina jiran naji muryar Hindu... Yawin bakina ya kafe karfin bugun zuciyata ya tsananta domin ji nakeyi kamar zata tsaga kirjina ta fito bayan yan dakiku sainaji daga can daya bangaren ance...
Hello... Jikina ya dauki tsuma na buda baki zanyi magana sai naji na rasa kalmar data dace nafara da ita don haka kawai nayi fakare da wayar a hannuna ina sauraron hucin maganar.
Wake magana? Wata kakkausar murya ta sake cewa dani daga can daya bangaren abinda yazo min a bazata yakuma yi bala'in sani kaduwa domin zazzakar muryar matata Hindu nake tsammani ba wannan kakkausar muryar ba mai kama da muryar rago. Zuciyata ta hasala don haka sai nace a fusace.
Mijin Hindu ne ke magana
Me? Aka tambaya daga can bangaren
Nace dakai mijin Hindu ne ke magana in tana kusa bata wayar da ita nake son magana na danyi shiru ina sauraro ina mamaki ko kunnuwana ne suke tsammanin wani abu daban. Amma in banda dahaka ba da sai ince naso inji ya rike numfashinsa daga can bangren.
Malam inajin ba wannan lambar kake nema ba... Ka sake kokarin bugawa ko ka sami.... Na katseshi.
Babu wani kuskure ga lambar dana buga tabbas lambar wayar matata na buga shiru na dan lokaci acan daya bangaren can sai naji kakkausar muryar tace.
Lallai kam da gaskiyarka me yiwuwa ta matar takace saidai kuma ina mai fargabar sanar dakai cewa nima wayar nan tsintarta nayi.....
Tsinta? Na tambaya cikin kaduwa..
Kada ka kara damuna kaje can ka nemi matar ka. Yana gama fadi sainaji hanyar wayar ta katse.
Jikina na tsuna gumi na zuba ta ko ina ajikina kamar an kwara min ruwa cikin bokiti nadubi gawar wayar tafi da gidanka dake hannuna tabbas nasan mai kakkausar muryar ne ya katse wayar.
Ina nan zaune akan gadon cikin kunan zuciya har sa'ar da agogon dake jikin bangon dakin ya buga karfe daya na rana.
Wani fari ne kyakkyawa... Suka fita dashi... Fari ne tas.... Inajin ma kwara ne.....
Maganganun da maigadi ya fada daren jiya ne suka fara dawomin zuciyata shin kakkausar muryar danaji ta kwaran ce.? Na tambayi kaina wata zuciya tace dani kaifa baka rabuwa da sakarci inbanda abinka kataba jin murtar kwara kakkausa kamar muryar rago? Wata kuma zuciyar tace dani tabbas za'a iya samu domin suma ai halittace kamar kowa?
Wannan ita tasani na sake daukar wayar nasake buga lambobin hindu akwai abinda nake son sani.
Hello kakkausar muryar ta sake cewqa dani raina ya baci domin nayi zaton bayan maganar da mukayi dashi dazu ko zai baiwa hindu wayar.
Bance dakai kada ka kara damuna ba..... BARI MANA.
.
Zuciyata ta hasala waye akusa dashi da har yake cewa BARI MANA dawa kake magana anan kusa dakai? Na tambay muryara na rawa.
DA UWAR KA NAKE MAGANA.!
Ya bani kyakkyawar amsa.
*** *** *** ***
Abba Ali ya dubeni cikin takaici sa'ar dana gama bashi labarin haka nan kuma akwai alamar tausayina karara a fuskarsa.
Kana nufin kace min yanzu kenan jiya ko wayar gari batayi agidanka ba? Na dubeshi da murmushin yake nace.
Uhm abba kenan to in banda abinka inda ta wayi gari agidan nawa me zai kawomi nan duk na rude ka da wannan dogon surutun.
Inda muke zaune acikin dan madaidaicin dakin shakatawar gidan Abba ali ne gidan da abba yake zaune aciki ajikin jami'ar sarauniya yake gidajen gwamnati ne da aka tanada acikin makarantar daga can bangaren arewa da dakunan karatu dan malaman jami'ar sai dai kuma akwai tafiya mai yar tazara daga dakunan karatu zuwa inda gidan yake.
Tun sa'ar da muka fara koyarwa ajami'ar aka bamu gidaje biyu nida abokina abba ali gidan mai lam 7 nikuma mai lamba 6 jasancewa mahaifiyata data jajirce akan cewa lallai bazanyi nisa da ita ba shi ya hanani tarewa tuntuni domin tunda mahaifina ya rasu ta dora idanunta akaina bata son rabuwa dani in ba dole ba domin acewarta in tana ganina kamar mahaifina take gani.
Abba ali ya muskuta akan kujerar yake zaune ya dubeni dogon kallo.
To ai ni duk abubuwan ne naka isma'il sun rudani wallahi.
Bai kuwa kamata ka rude ba domin ni ke da rudewaHINDU - 21
.
Bai kuwa kamata ka rude ba domin ni ke da rudewa ayanzu amma kai nutsuwa ta kamace ka domin dakai na dogara ka bani shawarar da zata fitar dani daga wannan kangi.
.
Abba yayi tagumi yana duban shudin kilishin dake mamaye da daban dakin akwai alamun zuzzurfan tunani a fuskarsa.
Kusan mintuna biyu muna nan zaune mun zurawa juna idanu kamar zakaru daga inda muke muna iya jiyo dirin motoci da kuma hayaniyar dalibai acan cikin farfajiyar jami'ar anan abba ali ya tsunduma cikin kogin tunani ya kasa fitowa saina dubeshi gamida sauya magana na dan lokaci nace.
Abba hayaniyar me akeyi ne haka yau acikin makaranta bayan kuma yau lahadi naga motoci jingim wasu ma sai kara shigowa suke.
Abba yayi ajiyar zuciya wai zaben (Miss Campus) sarauniyar kyau a jami'a zasuyi amma yanzu ba wannan bace agabanmu dawo kan maganarmu. Na dubeshi nace
To ai kai na gani kayi shiru shiyasa nima na sauya maganar kaga dakai na dogara domin tunda Garin Allah ya waye wallahi ko wani kwakkwaran abu bansa abakina ba ni yanzu duk tunanina yakare. Nayi shiru ina duban agogo.
Kaga yanzu har shida tayi magariba ta kawo jiki gaskiya abba kaine zaka bani shawarar karshe domin dana bar nan so nake na bugawa mahaifinta waya kasan yana hongkong da naso naje na fadawa gwaggwanta Rahimatu dake nan titin baron to sai naga kuma mahaifinta yafi dacewa yafara sani. Abba ali ya sake ajiyar zuciya karo na biyu sannan saiya dubeni ido da ido yace.
Gaskiya Isma'il ni shawarar da zan baka bazakaji dadi ba... Shiyasa kaji tun dazu nayi jugum na kasa yin tasirin komai akan al'amarin.
Kamar yaya bazanji dadinta ba?
Na tambaye shi cikin mamaki abba ali ya kara bubbuga wani katon litta dake kan cinyarsa da danyatsa lokaci guda kumayana duban fuskata.
Ssaboda nasan haryanzu nan Da hindu matarka tagama kwance maka zani a kasuwa kana matukar kaunarta..
Kaunarta,.. Naso ace kwance muryata ta sake ban iya karasawa ba.
Kagani ko abba yaci gaba ni nasan yanzu kana kaunarta ai gashi nan karara a fuskarka domin ko makaho ya shafa yasan da haka.
Na muskuta nace to amma duk da haka bai hana ka bani shawara,
Kwarai kuwa isma'il amma kasan dai babu yadda banyi dakai ba akan ka rabu da Hindu... Ni nasan ba alheri bace agareka akwai abinda yasa nace dakai haka....
Naso na fadama cewa ba kai kadai bane abokina data taba jefawa cikin Bala'i da masifa banda kai ma akwai (FARISU).
.
Waye kuma Farisu? Na tambayeshi.
Wani abokina ne zan baka labarinsa nan gaba domin dogon labari ne.
Mukayi shiru na dan lokaci. To yanzu wacce shawara zaba bani mu manta da duk wani tsohon batu domin abinda yafaru ya faru yanzu yaya za'ayi agyara gaba?
Abba ali ya dubeni. Shawarata babu dadi isma'il.
Na dubeshi cikin mamaki nace fadi muji ko wacce iri ce.
Indai zaka dauki shawarata Abba yace dani to KA SAKI HINDU DA GAGGAWA.
Domin ba matar zama bace ta alkhairi.
Naji kamar ya watsamin garwashin wuta a fuskata dayace na rabu da Hindu gara ya hauni da duka na mike tsaye jikina na rawa na dubi Abba ido da ido nace.
( I Am Sorry ) bawai naki shawararka bane to amma inasan ka sani cewa Hindu ta zama Ruhina ban iya rabuwa da ita har abada koda zatayi sanadiyar barina duniya ne. Sai anjima nagode da shawararka.
Nabarshi nan zaune da Littafi.
.
BABI NA HUDU 4
Lokacin dana dawo gida duk wata gaba tsoka kashi da jijiya na jikina ciwo sukeyi atun hanyar bayan nabaro gidan Abba ali naji yawun bakina yafara karewa gashi dai wuni guda tun safe ban ci komai ba amma duk da haka nan bana sha'awar sha ko cin wani abu. Dakyar na samu nayi sallar magariba amma fa daga nan kan daddumar na idar da sallar sai duk jikina ya dauki rawa wani sanyi marar dalili ya mamayi jikina ba'a dade ba sai jikina ya dauki zafi Kau. Kamar kwanan tuya zazzabi ya rufeni.
Ina nan zaune akan dardumar bayana jingine da kujera jikina na bari hakorana na haduwa da juna saboda tsabar zazzabi har karfe takwas na dare tayi.
Gadai zazzabi ajikina amma saboda masifa idanuna akan manya manyan hotunan Hindu dake makale ajikin bangon dakin ba'a dade ba sai naji idanuna kamar sun fara yi min dishi dishi bana iya ganin hoton sosai dan haka sainayi ta yan maza na mike tsaye juwa ta daukeni nayi taga taga kamar zan fadi Allah ya taimaa na dafe kujera. Na dan huta na dakiku hannuna rike da jikin kujerun sannan sai na lallaba na nufi inda hoton yake.
Na mika hannuna na dauko hoton daga inda yake a makale abin tsautsayi jikina na rawa sai hoton ya subuce yafado atsakar dakin gilashin ya tarwatse atsakar dakin ban damu ba sai na zare takardun hoton na zauna nan akan kujera sannan na dora hoton akan cinyata na zurawa hoton idanu acikin tattausan hasken fitilun alfarmar da suka haskake dakin.
.
HINDU.. HINDU...
Dan me zakiyi min haka. Nace da hoton ina dubansa kamar wani mahaukaci ni kaina nasan abinda nakeyi aikine irin na masu shan kwaya to amman ai ance MAI SO WAI MAHAUKACI NE daga wanda ke ganinsa daga bayan fage.
Baki kyautamin ba Hindu naci gaba da magana da hoton. Kiji tausayin raina Hindu KECE RUHINA..HINDU - 22
.
Kiji Tausayin raina Hindu... Kece Ruhina.... Jijiyata.. Bargona.. Kashina... Ke hatta jinina baya gudanarwa sai in dake kusa dani Hindu...
Hindu na kira sunanta daga karshe cikin daga murya.
Ammsa kuwwar kirana ta daki dodon kunnena.
.
Ina nan zaune zazzabi sai kara tsananta yakeyi domin tuni har hoton ya kware daga hannuna ya fado akan kirjina idanuwana rufe bansan sa'adda karfe goma na dare tayi ba.
Me yiwuwa zazzabin ne ya sauka don haka barci ya daukeni babu mamaki kuma sumewa nayi to koma dai menene yafaru yafaru ban kuma san takamaimain ko menene ba nidai kawai naji idanuna sun bude kamar wanda akace dashi tashi farka. Dan haka ina bude idanuna da agogo muka fara ido biyu sa'ar ne to naga ashe tuni karfe goma na dare ma tayi har ma taso ta dan wuce.
Na dafa kumatuna sai naji sanyi garai nayi mamaki domin babu alamar zazzabi ajikina hakanan na daina jin sanyi in banda ma muguwar kasala dake jikina da bazan taba imani da cewa iya sa'o'i biyu da suka shude zazzabi mai tsanani nakeyi ba.
.
Cikina yafara kara yunwa nakeji tabbas yunwar ma mai tsanani. Na dauke hoton hindu dake kan ruwan cikina na sumbace shi sannan na dorashi akan kujera ahankali cikin kulawa kamar mai ajiye kwai akan dutse na mike tsaye gabobina na barazanar baballewa ahaka nan na lallaba zuwa dakin girke girke ina tafiya kamar mai tata ina zuwa saina bude katon firjin aciki nayi ido biyu da tsohuwar kaza lullube acikin wata leda da takarda mai kyalli kyalli launin azurfa na dauko kazar gamida kwalbar tataccen lemo nadawo cikin falo na zauna kan kujera naman kazar yayi matukar sanyi... Amma bandamu ba domin cikina sai rugugi yake yi yana tafasa kamar tukunyar ruwan zafi gashi kuma saboda tsabar yunwa jikina har tsuma yakeyi.
Kusan mintuna goma ina figar sassanyan naman kazar ina hadiya dakyar kamar danko. Duk sa'ar da zan hadiye saina mike wuya kamar zalbe wata sa'ar kuma idan naji kamar zan shake sai in kwara sassanyar ruwan tataccen lemon
dan haka dai na daure na cunkushe tumbina badon inajin dadin naman ba sai dan cikina dakejin yunwa bayan wasu yan mintuna kuzari yafara dawowa jikina.
Ganin haryanzu a rude nake da al'amarin Hindu kuma na rasa abinda zanyi saina sake daukoar hoton naci gaba da kallo kamar mai karatun littafi adaidai lokacin ne to wayar tarho ta gidan danake kusa dani ta dauki ruri cikin lalaci na dauki waya ina mai mamakin wanda ke bugo waya karfe goma da minti ashirin na dare.... Koda yake da laifina ne ma danake barinta a bude.
Wake magana na tambaya cikin wata murya dani kaina nakasa gane ta amatsayin tawa.
Abba ne.. Abba Ali. Akace dani daga can daya bangaren mamaki ya kamani ba dazun nan kusan magariba muka rabu dashi ba na fara fadi cikin zuciyata.
Oh... Abba kaine.. Nace dashi cikin jin nauyi domin matukar jin kunyar irin yadda nayi fatali da shawararsa dazu dan Abba ali mutum ne.
Shiru dan lokaci can saiyace
A ina kake yanzu? Agida ko kuwa agurin....? Na shafi kaina da hannuna na hagu cikin mamaki yayinda hannuna na dama ke rike da wayar.
A..gida nake.. Ai kai dazu da muka rabu dakai Abba zazzabi ne ya rufeni.
Shiru acan daya bangaren
Abba... Abba kana nan? Nace cikin daga murya. Inajinka Abba yace dani
kayi sauri ka shirya kafin na karaso gani nan zuwa... Abba ali yace cikin tattausar murya. To amma duk da tausasa murya tasa bai hanani jin alamar doki acikinta ba.
Abba lafiya dai bangane inyi sauri in shirya ba me zan shirya...
Kada ka damu idan nazo zakaji komenene kadai shirya kafin nazo domin danazo tafiya zamuyi... Nan da mintuna goma zan karaso tunda dai dare ne babu cunkoson motoci.. Abba yayi shiru.
Abba... Nida duk ka rudani.. Naji layin ya katse na duba kan wayar nasan da gangan abba ya katse layin.
.
Na mike tsaye zuciyata na tunane tunane da sake sake duk yanda akayi dai akwai wani abu.
Mintuna biyar nagama sauya kayana dan kayan daman dana dawo dasu ajikina dasu nayi sallah nakuma kwanta dasu sa'ar da zazzabi ya rufeni yan sa'o'in da suka wuce wannan shiyasa na sake sauya wasu domin duk sun tattare sunyi sifirin kamar an kwatoni daga bakin saniya. Bayan nagama sai nayi kiran mai gadi nace dashi da zarar abba yazo ya nuna masa inda zai biyo kai tsaye domin ba'azo dashi sayan baki ba jiya. Kasancewar mahaifiyarsa da akayiwa tiyata asibiti adaren na jiya shiyasa muka dauke masa nauyin zuwa.
Ina nan zaune aka danna kararrawar na mike cikin sauri na budewa Abba kofa ya shigo.
Ka shirya ko?
Yace dani batareda ya damu daya zauna ba na kurawa abba idanu ina kokarin ganin shin kayataccen falon sabon gidan nawa ya burge shi?
Abinda na gani a fuskar abba ya sani kaduwa... Domin irin kallon dayayiwa dakin shakatawar irin kallo ne da dillalin kaji keyiwa jogo lokacin cutar kaji ta bazai.
Sai mu tafi ko... Abba yace dani lokaci guda kuma idanuna na kallon hoton Hindu dake kan kujerar gami da nazarin fasassun gilashin dake warwatse akan tattausan kilishin dakin. Na dubi abba sannan nace dashi akaro na farko Tun sa'ar daya shigo dakin.HINDU - 23
.
INCE DAI BA SAYAR DANI ZAKAYI BA ABBA.
Aamma ai yakamata ka sanar dani inda zamu tafi ka barni acikin duhu.
Abba ali ya harde hannayensa akan kirjinsa sannan ya dubi hoton hindu dake kan kujera ya nuni hoton da baki yace.
GURINTA ZAMU....
Na gano inda take. Na ji wani abu mai kama da tsinin kibiya ya soki kirjina..
Kana nufin.... Nayi shiru ban karasa ba sakamakon gyada kai dayayi.
Ita nake nufi Hindun ka ba.
A ina ka ganota... Na tambaya muryata na rawa kamar zan fashe da kuka.
A inda baka taba tsammani ba.. Abba yace dani yana dubana cikin damuwa.
Tana can dakin makaranta gurin zaben SARAUNIYAR KYAU (Miss Campuss).
.
Abinda yasa ma dazu kaji naki in fada maka cikin waya. Abba ali ya fadamin sa'ar da muka doshi makarantar cikin motarsa Fijo.
Saboda ina fargabar kada kaje cikin doki ka haifarwa da kanka hadari ahanya domin nasan yarinyar nan tagama zame maka masifa... Kokuma ince matar nan taka... Ya danyi shiru.
Saidai ka gafarce ni isma'il amma ni bazan taba daina fadama aibun hindu ba domi ni naga halinda Farisu yashiga a sanadiyyarta.
Ka tabbata ita kuma... Ka gani? Na tambaye shi muryata na rawa.
Bari na karasa gani ai ya kori ji.. Abba yace dani lokaci guda kuma yana duban kan kwalta.
Shiyasa to nace ka jirani agida sainazo na daukeka.
Wani kuda ya shige cikin kunnena na dama yafara yi min guda buuu na kai masa duka saiya tashi na mari kuncina.
Ita dawa ka ganta? Na dada tambaya Abba ali ya dubeni.
Isma'il wannan al'amari dai Allah ne ya jarrabe ka dan haka ba wani zance bincike binciken donin abinda ido bai bai gani ba zuciya bata damuwa dashi kuma indai na kane ai gara nayi shiru sai munke kaga da wanda suke tare.... Abba yayi shiru akwai alamun dake fuskarsa wadanda suka gargadeni da cewa kada na kara yi masa wata tambaya.
Na lura da cewa ransa abace yake dani musamman ma fatali danayi da shawarar dazu.
Dan haka sainayi gum da bakina naci gaba da kukan zuci gamida azabtuwa da ciwon dani kadai nasan inda keyimin zafi.
.
Tun kafin mu karasa farfajiyar makarantar na hangi motoci burjik kamar fari. Wannan ba wani sabo abu bane ga rayuwar jami'ar birnin sarauniya duk inda ka duba samarine da yan mata musulminsu da arnansu sunata dabi'u irinta arnanci basu kadaine agurin ba harda ma jama'ar gari wadanda ba dalibai ba suna zuwa kallon wannan haramtaccen zabe domin wai kawai suga yadda ake tafka masha'a.
Sa'ar da muka karasa sai abba ya lura da cewa gurin acike yake taf. Babugurin fakin hakan shi yasa abba yace mu karasa gidansa mu aje motar saimu dawo akasa.
Bayan mintuna gomane muka nufio gurin zaben. Tun daga nesa muka fara jin hayaniyar tayi yawa.
Hayaniyar menene hakane? Na tambayi abba.
Hayaniyar zabe mana.
.
Uhm Uhm Uhm.. Yaya nakejin yaji yaji a idona. Abba ali yace dani tun kafin ya rufe bakinsa sai muka hango dalibai nata gudu nan da nan masu motoci suka fara janye motocinsu suna fita aguje acan daidai farfajiyar babban dakin taron take yake gauraye da farin hayaki... Ko shakka banayi nasan barkonon tsohuwa ne.
Fada akeyi abba yace dani naji gabana yafadi duk da abinda tayi min sai naji bazan bari ayiwa Hindu rauni ba.
Fada fa kace
a'a kanajin barkonon tsohuwa kuwa...
Can sai muka hangi jami'an tsaro cikin dan hasken kyandiran lantarki da suka haskaka farfajiyar gurin yansandan nata kokarin korar dalibai ta hanyar buga musu barkonon tsohuwa dakuma kulake.
Ina zuwa! Nace da abba cikin zafin nama abba yayi caraf ya rike hannuna yace.
Ina zaka kuma kada fa ka manta kai malami ne ba daliba ba tunda fada ake agurin jami'an tsaro ma na iya kama ka agurin. Na dubi abba cikin kunan rai sannan saina fincike hannuna da karfi nace.
Ko za'a mani saina fitar da matata.
Ina fadin haka saina rufa aguje kamar mahaukaci na shiga cikin yamutsin.
Nayita dube dube dalibai nata kokarin tserewa nikuwa sai kara shiga nake duk kusan inda ka duba matane keta gudu kusan tsirara wasu su kadai wasu kuwa rike da hannun samarin su.
Na shafe kusan sa'a guda ina neman Hindu cikin hargitsin amma ko mai kama da ita ban gani ba saidai jifa jifa na kan hangi daidai daga cikin dalibaina. Dakyar nake numfashi idanuna tun suna zubar da hawaye har sun gaji sun bushe sai zogi da sukeyi kamar zasu fado kasa
tuni wajen kashi uku bisa hudu na dalibai duk sun gudu. Sai daidaiku dake can gefe suna neman hanyar gudu. Adaidai lokacin ne to naji wata murya abaya ance dani Malam barka da dare.... Na juya cikin sauri mukayi ido biyu da wani dalibina waishi SALISU UBALI.
Yawwa Sannunka dai salisu.. Meke faruwane haka nace dashi cikin matukar kokarin ganin nasami nutsuwa nagodewa Allah dayasa inda muke tsaye cikin dan duhu muke babu hasken lantarki sosai.
Wallahi malam fadane ya barke tsakanin masu zaben Miss Campus din nan da yan kungiyar dalibai masu kishin musulunci sun dage akan baza'ayi ba.. Domin al'adar banza ce akeyi agurin karara.. Kuma.. Ban karasa jin abinda yake fada ba sai naji saukar dutse agoshina tar,,, dalibin yayi tsalle gefe guda sa'ar dayaji na rike numfashinHINDU - 24
.
ƘARSHE
.
(c) Nazir Adam Salih
.
Dalibin yayi tsalle gefe guda sa'ar dayaji na rike numfashina lokaci guda na dafe goshina. Nan da nan jini ya fara wanke fuskata kamar ruwa.
**** **** ****
Karfe goma sha biyu na dare daidai dan kabu kabu ya ajjeni akofar gidana sa'ar dana kwankwasa Gate mai gadina ya leko yana huci dauke da gora da kwari da baka ya dubeni sai ya rike numfashi cikin kaduwa yace.
Dan Amina Muhammadu. Alhaji...
Na katse shi da cewa..
Kada ka damu dan hadari mukayi da wannan abokin nawa da muka fita dazu ina gama fadin haka ban bashi dama ya sake cewa wani abu ba saina wuce zuwa cikin gidan kai tsaye.
.
Haryanzu jini zuba yke akan fuskata bazanzo abba ya ganni da fasashshen goshi ba domin nasan zaice daman saida yafada min nakiji wannan shiyasani na dauki dan acaba tun daga kofar makarantar har zuwa gidana. Har yanzun nan da goshina ke zubar da jini ban damu ba abu daya ne ke tayar min da hankalki itace RUHINA Hindu bansan halin da take ciki ba.
Na bude kofar dakin shakatawar ga mamakina sainaji kamshi ya bugi hancina tunanin Abba ali ya fado min a ina ya samu turare haka mai kamshi gashi bayan fitarsa da kusan awa biyu haryanzu kamshin sa na makale da iskar cikin falon.
Ina shiga falon saina nufi bandaki kai tsaye da zummar na wane jinin dake zuba kan goshina amma mamakin hakan sai nayi turus zuciyata na bugawa wani abu na aje akan kujera kusa da hoton dana bari anan da nan na dawo da baya na sunkuya na dubi abun da kyau domin idanuna dakyar suke gani saboda fuskata data fara kumbura ko shakka babu jaka ce ta mata.
Ba'a dade ba sai naji zubar ruwa cacikin bandaki... Wake zubar da ruwa ? Tabbas wani ne ke wanka.
Wanene anan? Nace cikin wata irin fasasshiyar murya mai amo irin na gogen tsumma.
Wanene anan? Na sake maimaitawa shiru ta gaida kunnuwana.
Sannan sai naji takin sahu an nufo cikin falon taf taf ahankali.
Yawun bakina ya kare karaf kafata ta fara rawa zuciyata tafara kokarin fasa kirjina ta fito.
.
A tsaye agabana jikinta babu komai sai farin tawul data daura a kugunta....
MATATA CE RUHINA HINDU.
Ta dubeni sa'ar da gwiwowina suka kasa daukata na zzauna jabar akan kujerar kamar tsohuwar saniya.
INA KA TAFI TUN DAZU BAKA DAWO BA DUBI FA HAR KARFE GOMA SHA BIYU NA DARE ?
.
WAYACE KA FASA MIN HOTONA ?
.
.
KU GAFARCE NI DAN ALLAH MAKARANTA NA.
ZANCI GABA ACIKIN WANI SABON LITTAFI MAI SUNA
(RUHINA).
NAZIR ADAM SALIH (NAS).
.
KARSHE
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment