Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa hannu ya tsaya.

Ina zuwa? Ya tambayeni cikin rubabbiyar hausarsa na zaro katin na tura masa shi cikin tagar motar yayi nazarin katin na dan dakiku sannan ya girgiza kansa yace. Birnin sarauniya ko? Nace masa Eh yayi murmushi sannan yace SHIGO.

Na bude gidan gaba na shiga sannan direban ya fizgi motar aguje kamar wanda ya sato ta. Ya dubeni sannan yayi murmushi adaidai lokacin da muka hau babban titin BAROON.
direban dogo ne siriri bayerabe doguwar fuskarsa kamar anja ta da rula kowanne kunci an tsaga shi taya-taya kamar kwarya sanye yake da riga da wando na atamfa doguwar hularsa kamar husumiyar masallaci.

Birnin sarauniya tab unguwar manya bayeraben yace dani. Naji ance duk fadin kasar nan babu tsararriyar unguwa data kai koda rabinta. Kafadawa kowa nace dashi lokacin dana muskuta sannan nace dashi naji ance wai babu gidan kasa da naira miliyan goma a unguwar gaskiya ne? Direban yayi wana gaba da shi ham sannan ya dauke kan motar muka hau kan titin TANIM
ai sai abinda ka gani ma in dai birnin sarauniya ne domin ayadda naji ana jita-jita ance wai kana shiga unguwar zakaji tana kukan
NAIRA NAIRA NAIRA
direban ya fashe da dariya nayi sauri na toshe dodon kunnena banajin dariyar tasa zatafi kukan jaki dadin sauraro. Shi azatonsa wai ai yayi abin dariya ne jita jita zancen banza.
Nace dashi gamida dan murmushin yake don dai karya gane cewa banji dadin dariyar da yayi ba.

Kafin nacigaba da labarin danake shirin baka bari na baka hoton birnin sarauniya.
Lokacin da muka shiga unguwar saina lura da duk kusan ginin unguwar irinsu daya tun da nake bantaba ganin unguwa mai tsafta irin ta ba kyawawan tituna na sheki sun mamaye ko ina cikin unguwar kofar gidan kowa a unguwar korayen ciyayi ne lif lif lif kamar ka yaga ka ci inda kuwa kaga babu ciyawa to tayil ne a shimfide unguwanninmu namasu karamin karfi sai suka fado mini azuciya lokacin dana tuna ko ina ka duba takardu ne da yayi marasa amfani ga bola ko ina.

Wani abin bakin ciki kuma shine wadanda alhakin kwashewar ya rataya a wuyansu basu damu dasu kwashe ba.
Kallo daya nayiwa gidan na tabbata shima ba wani babban gida bane amma tsarin gidan ya firgita ni hakan shiyasa ni tunanin ashe mu a kango muke kwana

Direban ya taka burki sannan yajuyo yace dani Munzo nagani nace dashi ai komawa zakayi dani inda ka dauko ni. Direban ya dubeni cikin mamaki sannan yace EH. Bai sake cewa komai ba. Na dubi gidan a zagaye yake da yar madaidaiciyar katanga mai launin ruwan madara kyawawan furanni masu yado sun mamaye jikin katangar ko ina abin dai sai wanda ya gani kofar gidan ta farin kyaure ce ruwan azurfa amakale ajikin kofar wani dan karfe mai launin gwal an rubuta cikin kananan Haruffa kamar haka
LUMFA STREET NO 007.

Yanzu kam na tabbatar da gidan ne.
Mu tafi nace da direban adaidai lokacin dana dubi karamin masallacin dake kofar gidan wanda kuma na tabbata baifi yaci........
[3/16, 4:55 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-07

Wanda na tabbata baifi yaci mutum tara ba har da liman nayi mamakin masallaci ne ko kuwa dakin kiwon kaji daga karshe dai na yardarwa kaina masallaci ne nayi kokarin hangen tsakiyar gidan amma dogwayen bishiyoyin turaren da suka zagaye gidan su sukace basu yarda dana hango aljannar duniyar dake boye abayansu ba.

Abin da kawai nake iya hange shine shekin karfen da akayiwa tagar wani daki dake saman benen ado. Aduk lokacin da hasken hantsin ranar ya fada kansa saiya haske mini ido ta cikin tagar motar.
Kafin na rufe bakina direban ya fizgi motar mukayi gaba nagama ganin abunda nake son gani. Na farko naso na sauka kasa nayi nazarin gidan amma abu biyu suka hanani na farko shine kayan da suke jikina basuyi daidai da yanayin unguwar ba domin naji jita jita cewa idan ka shiga Birnin sarauniya da wulakantaccen kaya ajikinka yansanda na iya cafke ka amatsayin barawo don haka duk wanda ka gani a unguwar tsaf tsaf yake sai su 'ya su wadanda suka isa sannan naira ta daure musu gindi abu biyu kuma shine tun lokacin da dan taksi din nan ya daukeni na lura da bakar motar nan da aka jefani cikinta ajiya na binmu abaya idan har ba idona ne yake fada min karya ba to na so na hango mutumin nan mai dogon kai kamar shantu acikin motar wannan shine abinda ya hanani fitowa daga cikin motar bankuma bari dan taksi din yagane cewa ana bin mu abaya ba.

Abin ya wuce sanina koda yake nayi alkawarin sainaga yarinyar nan saikuma ta fada min dalilin dayasa ta janyo min duka haka kawai ba gaira ba dalili sannan kuma saina rama dukan da akayi min amma da farko bari na fara ganin yarinyar.
Nayi murmushi lokacin dana juya na hango bakar motar na binmu abaya motoci biyu ne atsakaninmu da muka sake hawan titin Baron.

****** ****** ****** ***** ********** ***** ******

Na dubi kaina ajikin dogon mudubin dake dakina nayi murmushi sannan abinda yake jikin mudubin shima yayi murmushi. Sannan na tabbata nine. Tunda nake ban taba sa kaya masu tsada kamar wadannan ba kusan duk rabin kudin data bani awajen kayan yatafi farin kambas din da kuma bakin wandon jeans sunyi matukar dacewa da farar suwaitar dake jikina don daurewa karya gindi harda hula hana sallah baka sannan na rataya katuwar jaka abayana kamar dai irin yadda yaran masu hannu da shunin dake birnin sarauniya suke shiga haka nima nayi.
Hakika irin yadda na ganni a mudubi abin ya burgeni sannan na rufe fuskata da bakin tabarau shiri yagamu sai BIRNIN SARAUNIYA.

Karfe goma sha daya da minti uku na isa birnin sarauniya tun dana shiga unguwar babu wanda yayi miki koda kyakykyawan kallo domin na saje da sauran samarin dake unguwar tun daga nesa na hango mai gadin gidan yana alwala azatona kiyamulaili zaiyi don haka saina make saida nabashi kusan minti uku bayan na tabbata yafara sallar saina nufi kofar gidan nayi sa'a kasan takalmana na roba ne don haka basa wani kwakkwaran sauti da takun nawa yake bayarwa acan cikin zuciyata wani abu na ta kururuwar kira na a'a'a'a'a!!!
Farisu ka dawo ka koma gida kada ka jefa kanka cikin abinda yafi karfinka amma duk kururuwar bata sa ni nayi koda gezau ba.
Na tura kofar gidan kai tsaye kamar wanda yasan inda zashi ga mamakina sainaga kofar ta bude nayi sauri na rufo kofar bayana sannan na nufi cikin gidan ahankali koda yake banko damu na boye takun sawuna ba na nufi dan karamin benen dake tsakiyar gidan rabin gidan ahaske yake kamar rana da kwayayen lantarki amma daya bangaren cikin duhu yake abin yabani mamaki sannan kuma yabani damar lallabawa ta cikin duhun ta hanyar boye jikina cikin bishiyoyin turare dana dorawar turawan dake ko'ina cikin farfajiyar gidan. Ina cikin tafiya saina hangi kafar benen daga bangaren kudu batareda na sake tunani ba saina tasamma kafar benen.....

Bako babu sallama wata siririyar murya tace dani lokaci guda kuma naji wani sassanyar hannu mai taushin gaske ya dafa kafadata tsigar jikina ta tashi naji kamar wayar lantarki ta tabani sannan kamar nayi fitsari a wando domin razana na juya ahankali cikin rawar jiki azatona zanyi ido hudu da mai kan shantu nayi ajiyar zuciya alokacin datayi maza ta kama hannuna muka tafi saman benen ta danna wani abu kofar ta bude sannan muka shiga dakin.

Kamar sauran dakin masu hannu da shuni shima mamaye yake da kilishi gamida manya manyan kujeru na alfarma wadanda ke barazanar hadiye duk wanda ya zauna cikinsu.
Dakin ya tsaru iya tsaruwa abinda yafi kuma daukar hankalina fiyeda komai shine wani hoto dake makale ajikin bangon dakin. Hotonta ne ita da wani mutum gajere mai dogon sanko kamar titin mota hancinsa kamar gutsurarran nakiya idanunsa can ciki kamar na kififiya nayi mamakin ko wanene mutumin. Na zabi kujera daya na nutsu aciki sannan na bude jakar danazo da ita na dauko lemo da aya acikin jakar leda na ajiye a tsakar dakin sannan nace da ita GA SAKON KI NA KAWO.

Tayi murmushi sannan tace nasan yanzu ka daukeni makaryaciya kuma mayaudariya amma inason don Allah ka saurareni da kunnen basira. Inajinki nace da ita.

Da farko dai kamar yadda nasan tuni ka fahimta shine duk maganar da..........
[3/16, 4:56 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-08

Da farko dai kamar yadda nasan tuni ka fahimta shine duk maganar da mukayi jiya zancen sayen lemo duk bogi ne sannan ba gaskiya bane.

Nayi murmushi sannan nace da ita kice kawai karya kike yi ko kunyar fada kikeyi? Bata amsa ba saitaci gaba da cewa Farisu ni dai sunana SALMA kuma na kasance marar sa'a da rabo shine nake son don Allah ka taimakeni.

Na dubeta kamar wanda yake tunanin ba kanta daya ba sannan nace bangane inda kikasa gaba ba.

Shekaru biyar da suka wuce akayi mini auren fari nida wani hamshakin mai kudi taci gaba da cewa sannnan watanni uku da suka wuce wani sabani ya shiga tsakaninmu dashi amma laifina ne ni na uzura masa har yayi fushi dani cikin bacin rai yayi min SAKI UKU

Tayi shiru tana tunani sannan ta tashi tsaye ta leka waje ta cikin tagar dakin bayan ta danyi dan lokaci tana tsaye awajen saita dawo ta zauna inafatan kana fahimta tace dani.
Ina dan fahimta amma zancen ya gundureni domin kuwa bai shafeni ba abinda kawai nazo naji shine menene hadinki da mutanen da suka casa ni jiya da daddare
tayi banza dani bata amsa ba sannan taci gaba da cewa yana da 'ya daya amma uwarta ta rasu bayan rasuwarta ya aureni yana mutuwar sona saidai kuma idan da wani abinda yarsa taki jinin ta gani aduniyar nan nice ta tsaneni matukar tsana saboda ganin ya manyata kuma muna tsammanin da kyar zai kara shekara biyu aduniya duk da yake dai sanin gawar fari sai Allah amma kasan anfi baiwa mara lafiya da tsoho mutuwa tayi murmushi sannan taci gaba da cewa yana da tarin dukiya kamar dan karuna kuma inada labarin cewa duk kusan rabin dukiyar ni zai baiwa tun kafin ya mutu saikuma gashi acikin rashin sa'a da tsautsayi yayi mini saki uku to amma kuma yanzu yadawo yana mutuwar sona saidai babu damar sake aure tsakaninmu dashi har sai na auri wani idan na fito saina koma gidansa tayi shiru tana maida numfashinta sannan tace dani...
Watanni biyu da suka wuce nayi kokarin samun yaro matashi wanda zai aureni idan munyi sati guda kuma saiya sakeni na koma gidan mijina. Shikuma na biya shi.
Tayi kwafa sannan tace Farisu Wallahi samari uku nayi kokarin aura amma duk shegiyar yarinyar nan tasa yan ta'addar mahaifinta sun tsorata su kai akwai wanda tasa suka.....
Kofar ta bude kamar iska ta doko ta sannan ta fado cikin dakin kamar aljannu kowannensu rike da katon kulki babbansu na da dogon gemu kamar burushi sannan agaban rigarsa an rubuta cikin manyan haruffa IJAKALA.

BABI NA UKU

Nayi tsalle na tashi daga cikin kujerar sannan cikin hanzari na shiga gaban salma wacce ke zaune akan kujerar kamar ruwa ya cinyeta alamun razana karara a fuskarta.
Bakaji kashedinmu ba ko? Mai kan shantu da dogon gemun ne ke magana yanzu ne zakaga amfanin taurin kai babu mamaki daga yau bazaka sake amfanuwa ba. Sannan katon ya juya ya kalli sauran ukun masu jajayen idanu kowannen su ya daga kulkinsa sama sannan suka fara matsoni idanunsu akan gangar jikina atsammanina kowa na auna inda zai dukeni ne adaidai lokacin ne salma ta tashi tsaye sannan tayi sauri ta shiga gabana tareda kareni.
Kuyi min duk abinda kuke so amma kada ku sake ku taba shi. Tace dasu cikin rawar murya inason sa don haka babu wanda ya isa ya taba min shi kuma baku isa ku hanani aurensa ba ku koma kuce da SHEGIYAR data aiko ku na hana adake shi mai dogon gemun ya fashe da dariya yar tsakuwa mun ji ki ba sau daya ba ba sau biyu ba kin sha fadar haka akan guntun samarin da kika son kiyi auren kisan wuta dasu shin kina tsammanin kurinki zai hana mu aikata shi?
Ba'a bamu iznin tabaki ba don haka ki kauce ki bamu guri sauri muke mu aika ta shi.
Bazan kauce ba tace dashi saidai ku kashe ni mai dogon gemun banza tace dashi a fusace.
Hakan data fada shi ya kawo karshen hakurinsa yayi taku biyu gaba ya kifa mata mari karfin marin shiya jefota baya ta maku ajikina nayi sauri na riketa ta kwalla kara alokacin daya sake kawo wani marin tsakaninmu dashi babu nisa domin ina iya jin hucin numfashinsa a fuskata hankalinsa gaba daya ya koma kanta hakan shi ya bani damar dunkule hannuna na kirba masa naushi a kahon zuciya naji kamar na naushi dutse hannuna ya sage babu mamaki kirjin karfe ne dashi naushin bazatan danayi masa shi yasa shi yayi taga taga kamar zai fadi sannan fuskarsa ta zama ruwan toka toka wata kumfa tafara fitowa daga bakinsa ya yiyo kaina da gudu kamar mahaukacin kare.
Na ture salma gefe guda lokaci guda kuma na tsugunna kasa mahaukaci naushin daya kawo ya wuce ta saman kaina shuuu...
Kamar iskar damina sannan yayi tuntube ya wuntsula bayan dakin ya girgiza saboda karfin faduwarsa..

Salma ta nufi kofar dakin dake fuskantar wanda muke ciki da gudu ta bude dakin sannan tayi sauri ta kulle kanta ciki.
Naji saukar kulki abayana daya bayan daya kamar zubar ruwan sama na fadi rub da ciki sannan nayi kokarin tashi tuni mai kan shantu ya mike tsaye ya daga kulkinsa sama ya sake tika min shi abaya nakoma na kwanta jagwaff atsakar dakin kamar kayan wanki.
Mai dogon gemun yasa kafa ya daki ruwan cikina dukan da yayi min shi ya sani aman ruwan dana sha kafin nafito daga gida

MU CI GABA KO MU DAKATA ANAN SAI JANGO ??
[3/16, 4:57 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-09

Mai kan shantu ya mike tsaye yadaga kulkinsa sama ya sake tika min shi abaya nakoma na kwanta jagwaf tsakar dakin kamar kayan wanki.
Mai dogon gemun ya daki ruwan cikina dukan dayayi min shiyasani aman ruwan dana sha kafin nabar gida sannan ya cakumi kwalata ya dagani sama yayi murmushi afuskata sannan yace dani Dan samari taurin kai babu dadi ka hakura ka rabu da yarinyar nan in ba so kake mu kashe ka abanza ba idan mun kashe ka mun kashe banza kamar kisan kurciya ne babu mai ita idan ka kasheta babu mai cewa yaya haka

Sannan yayi jifa dani gaban sauran ukun tun kafin na taba kasa yasa kafa yayi Ball dani sannan ya take kirjina da takalminsa naji kamar duniyace aka doramin a tsakiyar kirjina hanjin cikina yafara barazanar fitowa ta bakina.
Haryanzu kafarsa na kirjina ya jawo kwalin taba daga aljihunsa ya zari guda daya sannan ya kunna mata wuta ya busa hayakin sama ya sunkuya kasa kansa dab da fuskata kan nasa mai kamar shantu na kyalli kamar mudubi dogon gemunsa na barazanar tsokane min idona.
Idan har muna raye toh bazaka taba cimma nasara ba gurin aurenta wannan shine kashedi na karshe idan ka sake muka sake hada hanya dakai to lallai kam badi kamar haka ana sadakar cika shekararka daya a kiyama.

Ya tashi tsaye daga durkuson dayayi akaina sannan yace dani kodon gaba in mun hadu dakai ahanya zaka iya kirana da IJAKALA
ya kyalkyale da dariya wadda a sanadiyar hakan har saida sauran yaransa sukaja da baya alokacin ne to na lura cewa ashe hakoransa biyu na gaba sun zube hakan shiya kara mai dashi dodo abin tsoratarwa adaidai lokacin ne mukaji takun sawu ga dukkan alamu kuma saman benen aka nufo da gudu mai dogon gemun ya nufi tagar dakin ya leka kamanninsa suka canza cikin zafin nama saiya juyo da gudu yace da sauran yana dariyar yake YANSANDA

Yayi sauri yasa sakata ababbar kofar da yake tsammanin ita kadaice hanyar da yansanda zasu shigo cikin dakin sannan ya nufi tagar bangaren arewa yayi kokarin bude tagar amma yakasa saboda kasancewar mabudin kofar na zamani ne ya juyo da gudu zuwa tsakar dakin yana dube dube tuni har an fara kwankwasa kofar sauran kattin na tsaye sololo suna kallonsa kuji wani abin mamaki yace dasu cikin karaji kafin kiftawa da Bisimillah sai daya daga cikinsu ya nufo tagar dakin taki budewa ya kama da karfin tsiya yana jijjigata amma abin yaci tura abin ban haushi kuma kofar ta gilas ce amma duk fadin tsakar dakin babu wani kyakkyawan madoki da zai iya fasa gilashin kartin sukayi ta nauhsin gilashin amma abanza ba irin gilashin da suka saba fasawa bane.

Akaci gaba da dukan kofar ayayinda kartin ukun suka cigaba da kokawa da tagar dakin amma ko motsi batayi ba nikuwa numfashina sama sama da kyar nake iya ganin abinda ke faruwa sabodan duk idanuna sun kukkumbure.
Ga mamakina sainaga mai dogon gemun wanda ya kira kansa Ijakala ya kyalkyale da dariyar rashin tsoro dakuma ko in kula din da ya nuna yayi matukar sani kaduwa na raa abinda yakeyiwa dariya amma daga baya saina fahimci ashe kartin dake kokawa da tagar dakin yakewa dariya
dukan kofar ya kara tsananta ina tsammanin yansandan dake kwankwasa kofar sun gaji sun fara kokarin karya kofar ta hanyar yin amfani da karfin tsiya.

Ijakala yayi murmushi sannan ya kunna doguwar tabar dake bakinsa ya kashe ashanar gamida shafar dogon kansa mai kyalli kamar shantu sannan alokaci guda kuma ya shafa dogon gemunsa mai kamar burushi yace ku saurara haka ku sakarkarun banza suka yi tsaye cak kamar ruwa ya cinye su kowannensu ya hada gumi sai haki sukeyi kamar wadanda suka hau bene hawa dari.

Ijakala ya busa hayaki sama ya tashi dan karamin gajimaren da bana tsammanin zaiyi ruwa sannan lokaci guda ya nufo tagar dakin da gudu kamar an harbo shi ya sa dogon kansa mai kamar shantu ya daki gilashin tagar atake anan ya tarwatse sannan ya juyo yace dasu maza kuyi ta kanku karku bari wankin hula ya kaiku dare yan samari ya kyalkyale dariya sannan ya juyo gareni tuni sauran kartin uku sun sulale ta cikin tagar dakin nayi mamakin hanyar da sukabi suka sauka kasa
Dan karamin sautin motsin reshinan bishiyoyin turaren dake daf da tagar dakin suka bani amsar tambayata

Ya shafi dogon gemunsa sannan ya shafi kansa mai kyalli kamar mudubi abinda yayi matukar kara sani tsurewa lokacin dana dubi kan ijakala sainaga ko karcewa baiyi ba lallai to in ba kan karfe ne dashi ba to aljani ne nace cikin zuciyata domin na tabbata in da ni na daki tagar dakin da kaina babu abinda zai hana kaina rabewa gida biyu.

Wannan shine kashedin karshe farisu yace dani adaidai lokacin da kofar dakin da yansandan suke kokarin karyawa ta fara motsi alamu ne dake nuni da cewa sun ci karfinta na cigaba da addu'ar Allah yasa su bude cikin gaggawa saboda ko kusa bana son zama tareda wannan naman dajin Ijakala wani mummunan tunani ya ratsa zuciyata yanzu idan mai dogon gemun nan yayi niyyar kasheni zai iya dukan kirjina ko kaina da dogon kansa.

Nayi ajiyar zuciya sannan jikina ya dauki rawa lokacin dana tuna da irin dukan da yayiwa gilashin tagar dakin da dogon kansa.

KUNA KARANTA WANNAN LITTAFIN NE MAI SUNA BIRNIN SARAUNIYA
Wanda Nazir Adam Salih ya rubuta

Nikuma Yarima A Gangariya
Nake kwafowa daga littafin nake muku posting dinsa

YARIMA A GANGARIYA
(jikan sidi mai jaka)
[3/16, 4:58 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-10

Nayi ajiyar zuciya sannan jikina ya dauki rawa lokacin dana tuna da irin dukan da yayiwa gilashin tagar dakin da gogon kansa.

Ba karamin sakarci bane idan har kaci gaba da kudurar aniyarka ta auran salma kama godewa Allah dayasa ba a bani damar kashe ka ba kai tsaye.

Amma ina tabbatar maka da cewa nasan wacce tasamu aikin zatayi farin ciki idan akace baka raye fiyeda ace ka auri salma. Ina fada maka duk wannan ne saboda na lura da irin kamanninka bana mutanen banza bane kuma duk halin daka tsinci kanka yanzu aciki ba laifinka bane jefaka akayi ko kuma nace kayi rashin sa'a da har salma ta zabe ka amatsayin saurayi na hudu da take shirin yin auren kisan wuta dashi. Munga bayan ukun farisu.

Yace dani saikayi hankali kada mu ga bayan ka sannan kuma dadin dadawa ina tsammanin wannan karon zamuga bayan ka gaba daya sabanin sauran samarin da muka raunata abaya kai batar dakai zamuyi ma'ana
KASHE KA ZATA SA MUYI
Ina baka shawarar daka janye ka hakura ko mai zata baka kada ka sake ka nuna alamar aurenta.
Kai daga yau ma kada ka sake mu kara ganin ku tare wanda baiji bari ba yaji hoho.

Yace dani cikin karaji na gargadeka cikin abota lokaci na gaba bazamu zama abokai ba.
Kafin na farga shi ma ya sulale ta cikin tagar dakin yabi duhun dare ya bace kamar aljani

Kofar dakin ta karye ta fado gamida karar data girgiza dakin sannan lokaci guda itama salma ta fito daga cikin dakin data kulle kanta sannan tace da yansandan sun gudu ta taga me kukeyi da har kuka bari suka shigo mini gida. Kalli yadda suka lakadawa kanina duka nima dakyar na tsira na kulle kaina cikin dakin.
Daya daga cikin yansandan wanda nake tsammanin igiyarsa biyu yace da ita kiyi hakuri hajiya wallahi munga shigowarsu amma damukaga motarsu mai tsada ce kuma tayi daidai da irin ajin motocin da suke shigowa gidan sai muka dauka bakinki ne.
Salma ta harare shi sannan tace bakina ne mana tunda sun lakadawa kanina dukan tsiya saiku taimaka mini na kaishi asibiti.
Yansandan sukayi mini cali cali ita kuma tana binsu a baya nayi mamakin abinda yasa taki fadawa yansandan gaskiyar al'amarin.

****** ****** ******* ******* ******* ****** *****

Cikin sa'a bayan danayi kwanaki biyu asibiti aka sallameni salma ce ta daukeni a motar ta itace kuma ta dauki nauyin duk dawainiyar jinyata abin mamaki ita kuma ke kwana gurin jinyata hakan kuma shiya bata damar lallabani tun tana bani baki ina kin kulata har ta yaudareni da daddadan kalamanta na soma sauraronta.
Farisu ta kira sunana aranar da aka sallameni da safe bayan mun shiga motarta zata kaini gida nasan dai yanzu duk ka san abinda ake ciki don Allah ka taimakni ka aureni koda na kwana uku ne ka sakeni kuma kaga taimakon da zakayi bani kadai zaka taimakawa ba kaima zaka taimaki kanka domin zan biya ka ko naira miliyan biyu ne don ganin ka cika min burina

Numfashina ya dauke gamida wani sassanyan gumi dake kwararowa akan fuskata na dubeta adaidai lokacin dana tuno muryar Ijakala yana cewa MUN GA BAYAN WADANCAN UKUN SAURA KAI.

Na girgiza kaina sannan nace da ita kin cika son kanki salma na kira sunanta akaro na farko bakya tunanin irin halakar da zan fada idan na aureki ko kuma idan aka cigaba da ganinmu tare? Abinda kawai kika damu dashi shine dukiyar mutumin da zaki aura shin kuwa ko kina sane da cewa auren da zamuyi dake haramun ne? Kuma mutumin da zaki aura amanarsa zakici domin shi azatonsa kina kaunarsa kamar yadda yake kaunar ki kina tsammanin daya san abinda ke cikin zuciyarki yanzu zai yarda yabaki rabin dukiyar tasa kamar yanda yayi alkawari? Kiji tsoron Allah salma abin duniya ba'a bakin komai yake ba Ubangiji fa ba zai barki haka ba........
Nasan da wannan ta katseni abinda kawai nake so naji daga bakinka shine amincewarka Bawani zance ba.
Zo nan... Tace dani lokacin data bude kofar motar ta nufi but dinta duba nan tace dani.
Na leka abinda na gani aciki yaso yasani hauhawar jini buhuna ne guda biyu kowannensu cike yake da wazobiya sababbi fil.

Naira miliyan uku ne idan ka amince zaka aureni KOWANNE KWANA DAYA DAIDAI YAKE DA MILIYAN DAYA.
Gumi ya rufeni naji kafata gaba daya tana rawa ga koshi ga kwanan yunwa idan na amince arabani da rayuwata idan kuwa na tsallake to na zama miloniya.
Zanyi shawara nace da ita bakina na rawa duk wa'azin danayi mata abaya na manta dashi.

BABI NA HUDU

Idan ka aureni kowane kwana daya amatsayin naira miliyan guda yake kwana uku naira miliyan uku kenan.....

Maganganun da salma tayi min ne suka ci gaba da yawo cikin zuciyata zaman danayi yanzu akofar gidanmu bai hana ni cigaba da tunanin kudin datace zata bani ba idan na aureta nayi sa'a ranar data dawo dani gida gabana na faduwa saboda bansan abinda zance da mahaifina ba idan ya tambaya ina naje kwana biyu nasan zan iya yin karyar da

Please Login or Register in order to submit comment