Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaata fitar dani amma karyace banason nayiwa mahaifina saboda wancan karon danayi masa karya banji dadi ba musamman dana lura da cewa jina kawai yayi amma bai yarda ba sauda yawa mukanyi tunanin zamuyi wa iyayenmu wayo amma karya ne duk abinda muka fada sun san gaskiyarsa da karyar sa......

(jikan sidi mai jaka)
YARIMA A. GANGARIYA
[3/16, 4:59 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-11

Sau dayawa mukanyi tunanin zamuyiwa iyayenmu wayo amma karya ne duk abinda muka fada sunsan gaskiyarsa ko karyarsa saidai kawai su kyale mu kurum tunanin hakan shiyasa ni faduwar gaba cikin sa'a saina tarar ashe tun ranar da mukayi sallama dashi na tafi birnin sarauniya shima sai tafiya ta same shi ta gaggawa zuwa wani garin nan dake kusa damu baifi kilomita talatin ba daga garinmu ayadda naji bazai dawo ba sai yayi kwana biyar yau kwanansa uku kenan acan.

Miliyan uku!!! Na muskuta akan kujerar da nake zaune sannan na mike tsaye na fara safa da marwa daga kofar gidanmu zuwa karkashin bishiyar da nake ajiye kujerata hannayena biyu acikin aljihuna. Hakika salma ta shuka wani IRI acikin zuciyata sannan wasu sassa na zuciyata suna cewa dani me zai hana naci gaba da baiwa irin ruwa domin shima yaji dadi yaci gaba da yado?
Ba wani IRI nake magana ba daya wuce irin naira miliyan uku don taci gaba da yado cikin zuciyata nasan kam yanzu rayuwata tana tsakanin abu uku ko halaka ko arziki kokuma talauci idan na amince zan auri salma to daya daga cikin abubuwan dana ambata na baya zasu iya kasancewa akaina kodai halaka kokuma mutuwa.

Munga bayan samari uku sai kayi hankali kar kaima muga bayanka.....

Gargadin Ijakala yaci gaba da kururuwa cikin zuciyata hakika idan naki amincewwa dana aureta to na tserar da kaina daga halaka saidai kuma me?.... Ma'ana zancigaba da zama cikin talauci har sai randa Allah yakawo karshensa.
To amma anya kuwa zan iya barin miliyan uku abanza ta wuce ni saboda gargadin wani me dogon gemu....? Na juya maganar cikin zuciyata nakuma yi tunanin wahalar dana sha tun bayan gama karatuna na tuna irin wahalar da iyayena ke ciki na tuna irin wulakancin da mahaifina yace KWARORI nayi a kamfanin dayake aiki.

Ba zan taba manta ranar da mahaifina yayi kwana hudu ba akulle a ofishin yansanda mudai bamu san abinda ya faru ba saiji mukayi wai an rufe mahaifina lokacin daya fitone nake tambayarsa dalilin anan ne yake cewa dani cikin sassanyar murya saboda ya manyanta yau shekaruna ashirin da uku ina aiki a kamfanin farisu tun ma ba'a haifeka ba amma saiga shi wai saboda galan din SINADARI daya tak ya bata a sashen mu shine aka rufemu wai mu ake zargi mun sace shi sai daga baya aka ganoshi a ofishin wani babban ofisa dake kamfanin.

Kabar aikin to mana baba dole ne saikayi aiki a kamfanin? Idan to nabar aikin a kamfanin ina zasu daukeni. Samari majiya karfi ma suna wahala da neman aiki ballantana ni.. Yayi murmushin karfin hali sannan yace dani Farisu kome na duniya yanada karshe....

Tunanin hakan shiyasani yanke shawarar auren nata kai tsaye cikin zuciyata mai rabon ganin badi sai ya gani koda ana ruwan masu. Barazana da gargadin Ijakala basu isa su karkade mafarkin dake zuciyata ba ahalin yanzu ba kuma wani mafarki ne daya wuce na dora ahannuna akan naira miliyan uku ba
Kwana Uku kawai na saketa saki ukiu shikenan miliyan uku ta zama tawa?

KWANA UKU
SAKI UKU
MIILIYAN UKU
naci gaba da nanata su cikin zuciyata babu wanda ya isa ya hanani saka hannuna akan kudin koda ijakala ne wannan ai wata dama ce Allah yabani nace cikin zuciyata na tabbata wahalar da zan sha ahannun su Ijakala bazatayi koda daya bisa hudun wacce mahaifina yasha abaya ba
rashin kudin ne ya hanani cigaba da karatuna naci gaba da kawo dalilan da zasusa dole na halartawa kaina dora hannuna akan naira miliyan uku. Acan kuma wani bangare na cikin zuciyata nasan ba daidai bane na yanke hukuncin son zuciyata ba kawai nabi amma wanda yayi nisa baya jin kira tuni har nafara tunanin wai ganinan acikin wata dankareriyar mota na kama hanyar zuwa jami'a abokaina na ta dago min hannu suna adawo lafiya.

***** ****** ******* ****** ****** ****** ********

Naci gaba da safa da marwa duk minti biyu saina duba agogo domin munyi da ita zata zo a asirce ta sameni domin jin shawarar dana yanke kodai ban fada maka ba kasan abinda ke zuciyata ka kuma san shawarar dana yanke.
Ayadda mukayi da ita in har na amince zan aureta din to gobe ne za'a daura auren tace wai ko iyayena bata son su sani domin abin a asirce za'ayi shi babu wanda ake son ya sani daga ni sai ita saikuma tsohon mijinta.

Miliyan uku saki uku kwana uku na dubi tsohon ginin gidanmu wanda a tsammanina ya girmi kakana tuni har nafara kwatanta inda za'a ruguje asake sabon gini gobe warhaka na zama miloniya. Ayadda tace dani ana daura auren zata bani kudin gumi ya lillibeni dana tuna da cewa gobe wai zan zama miloniya alokacin ne wani tunani yafado min wanne irin bayani zanyiwa mutanen unguwa idan sukaga na fara wasa da kudi...? Na tambayi kaina na farko dai kowa a unguwar yasan mu ma su karamin karafine bana jin kuma ko mu aka sayar zamu kai naira miliyan uku yau da'ace inada wani kwakkwaran aiki ne irin aikin da mutane keyiwa kallon kudi to da da sauki ina iya fakewa dashi kowa ya ganni ina facaka da kudi zaiyi tsammanin harkoki ne suka bude wannan itace matsalar data cigaba da addabar zuciyata nayi iya tunanina don gano maganin matsalar amma abin yaci tura.

Bari ita matsalar ta magance kanta zuwan.........
[3/16, 4:59 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-12

Bari matsalar ta magance kanta zuwan miliyan uku din yafi wuya idan ina da miliyan uku wa ya isa yayi min tsurku nace da kaina sannan na dada da cewa waya isa yafada kan uwar sarki da kaho?

Na sake duban agogona karfe biyar da minti arba'in da biyu adaidai lokacin ne abu biyu suka faru lokaci guda naji tsayawar mota sannan lokacin dana juya na fuskanci motar kamshin turare yayiwa hancina sallama.
Assalamu Alaikum wata zazzakar murya tace dani daga cikin tagar motar data tsaya ne muryar take kwararowa sannan lokaci guda kuma naji an sake sallama akaro na biyu saidai wannan karon muryar namiji ce. Abokina sagir ne banji dadin zuwansa awannan lokacin ba saboda atsammanina hajiya salma ce a acikin motar data tsaya gabana.
Sannu da zuwa sagir kwana biyu nace dashi bai sami damar bani amsa ba lokacin da duk hankalin mu yatafi kan motar dake gabanmu kofar motar ta bude santala-santalan kafafunta ne suka fara fitowa wadanda ke sanye da bakin takalmi mai dabbare-dabbare kamar fatar kada sannan ta fito gaba dayanta.
Tana sanye ne da riga da wando na yadin makaranta ruwan kwai agaban bajon dake gaban rigar an rubuta
EL-BASIR GIRLS SENIOR SECONDARY SCHOOL
nayi mamakin ganinta da kayan makaranta sannan kuma wacce irin makaranta ce haka har kusan magariba tun safe? Na tambayi kaina.

Bari na zana maka hotonta acikin zuciyarka ko ban fada maka ba nasan zaka canki irin haduwar datayi saboda zuwan wannan yarinya adaidai lokacin danake sauraron wacce zata zo min da kamshin naira miliyan uku tuni har ta gundureni.

Zakayi mamaki idan nace maka HINDU elbasir kyakkyawa ce ta karshe ajin farko duk fadin unguwar mu babu saurayin da bai san labarin kyawunta ba sannan kuma babu wanda baisan girman kanta ba dakuma rashin mutuncinta ta wulakanta samari da dama takuma sa wasu sun zautu don kawai masifar sonta samari da dama sun kamu da ciwon sonta tun kafin ma su ganta a zahiri daga kawai kallon hotonta atarihi ba'a taba samun saurayin dayaci nasarar tsayawa da ita ba domin ita wai bata dauki bakin mutum da daraja ba kasancewar mahaifiyarta balarabiya ce sannan ubanta baki ne kamar mu. Ganinta agabana yanzu yayi matukar bani mamaki abin kawai daya rage min jin dadin zuwanta shine tunanin naira miliyan uku ba karamin daga aji bane azo wucewa aganni tare da ita nace cikin zuciyata.

Doguwa ce ba can ba tana da dan kauri daidai misali idanunta dara dara sannan fari tas kamar takarda cikakkun labban bakinta dakuma jerin fararen hakoranta masu kyalli da walkiya wadanda idan tayi dariya saikaga fuskarka ciki su suka hadu da dan siririn dogon hancinta mai kamar biro suka bata kyawun daya zamanto wani maganadisu azuciyar duk wanda ya hada ido da ita shikuma yasa samari da dama sukance wai fuskarta har kyalli take kamar Diamond hindu kenan Elbasir wannan ma ya isheka hoton kyawunta.

Tayi murmushi adaidai lokacin data matso kusa damu sannan tace sannun ku tana murmushi a gabanmu hannunta rike da alkalamin rubutu (Roller Pen) tana wasa dashi sannan ta rike gudunta tace damu.
Don Allah Farisu nake tambaya har yanzu murmushin na fuskarta na dubi abokina sagir wanda ke tsaye kerere kamar an dasa shi sannan mukayi murmushi mu duka biyun sannan na juya na sake dubanta akaro na biyu NINE FARISU nace da ita tayi far da fararen idanunta sannan ta lumshe su lokaci guda kuma ta bude su kamar idon yar tsana kallon da takeyimin awannan karon akwai alamar mamaki afuskarta kaine Farisu? Ta sake neman tabbaci abinda nace na gyada kai sannan muka sake duban juna akwai alamar na tsayu a fuskarta don haka sainayi shiru ina sauraronta.
Don Allah wani taimako nake son kayi min idan zan samu... Wane irin taimako? Na tambaye ta cikin mamaki nasan zakayi mamaki amma ba abin mamaki bane idan akayi la'akari da irin sakamakon daka samu a jarrabawarka ta karshe a sakandire tayi murmushi duk unguwarmu wane ne baisan da labarin sakamakon ka ba? Farisu da'ace ni Allah ya baiwa basirarka danaji dadi amma yanzu ma Alhamdulillahi tun da gaka na sameka daman roko nake don Allah ko zaka samu damar zuwa gidanmu domin kana koya min wasu abubuwan da suka shige min duhu Wallahi farisu munada malamai masu hazaka saidai ina tsammanin zanfi fahimtar taka laccar domin naji ance lokacin kana makaranta kasha cin gyaran malamanka.
Banda dai zuga nace da ita muka kyalkyale da dariya.
Dariyarta datafi komai dadin sauraro acan kuma cikin zuciyata ina tunanin lallai na samu maganin matsalar data addabeni yan sa'o'in da suka wuce duk wanda yaji labarin ina koyar da yar gidan elbasir zaiyi tsammanin lallai kam ni kakata ta yanke saka domin an san dolene na sami albashi mai tsoka zan iya fakewa da aikin nacigaba da badda naira miliyan ukuna batareda mutane sun zargeni akan ina nake samun kudi ba atake agurin na amince dana fara koyar da ita. Zanso na taimake ki din saidai kuma banajin zan iya zuwa gidanku batareda sanin mahaifinki ba.

Karka damu da wannan tace dani idan kazo gobe saiku tattauna da mahaifin nawa tayi murmushi sannan tace aishi yabani damar daukar duk wanda
NAKE SO YA KOYAR DANI AMMA FA........
[3/16, 5:00 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-13

Karka damu da wannan tace dani idan kazo gobe sai ku tattauna da mahaifin nawa. Tayi murmushi sannan tace ai shi yabani damar daukar duk wanda nake so ya koyar dani.
Can cikin zuciyata wani abu na cewa dani duk maganar da take fada karya ce domin akwai kwazazzabai acikinta. karfe nawa zanzo na tambayeta......
Wannan shine kuskuren farko dana aikata

Lokacin da ta tafi sai abokina sagir ya dubeni yace dani ban yarda da tatsuniyar datayi maka ba kanajin mahaifinta bazai iya daukar furofesa yazo har gida ya koya mata ba?
Zai iya nace dashi amma kasan ra'ayi.
Ra'ayi kukan jaki yace dani kai dai kayi ahankali farisu sharrin mata na da yawa musamman ma ita hindu kasan fa rashin mutuncinta ba sai na fada maka ba.
Hakane nace dashi tuni na kosa yabar gurin saboda kowane lokaci daga yanzu salma na iya zuwa Ahaka muka rabu da abokina sagir lokacin da zamu rabu dashi saiyace kasan fa tace zubar da ajine ta tsaya da bakin mutum kana tsammani kai don fari ne ta bukaci dakaje har gida ka koya mata karatu?

***** ***** ***** ****** **** *** ***** ***** *****

Da farko bangane ta ba sai bayan data matso kusa dani tayi sallama sannan na shaida muryarta salma ce.
Na idar da sallar magariba kenan ina jan tasbaha tazo ga mamakina sai naga tazo kusa dani ta zauna tana fuskantar gabas bayanta a rakabe da jikin bangon gidanmu babu wanda zai iya ganeta ahaka babu wanda kuma zai iya tantancewa shin matar aure ce ko budurwa saboda alokacin datazo sainayi sa'a duk fadin unguwarmu an dauke wuta don haka sai ko'ina ya gauraye da duhu musamman ma kofar gidanmu wacce ke lillibe da katuwar bishiyar darbejiya. Nasan duk mutumin dayazo wucewa zai gane ni amma bana tsammanin akwai mai iya ganeta koda kuwa dan ta'addan nan Ijakala ne.
Wacce shawara ka yanke? Tace dani cikin sanyin murya da karayar zuciya tuni gurin ya gauraye da kamshin jikinta.
Zan iya aurenki nace da ita kai tsaye banko yarda mun hada ido da ita ba. Haryanzu gabas muke fuskanta ita a tsugunne ajikin bango nikuma azaune akan dardumar danayi sallah.

Tayi ajiyar zuciya sannan ta dafa kadafata tace Farisu na....gode kunya da mamaki suka rufeni don jin wai har godiya akeyi min don zanyi auren kwana uku kuma abiyani naira miliyan uku.
Bansan daga inda ta zaro salular ba ko daman tana makale ne ahannunta Allah masani ta daddana yan lambobi sannan tace dani yanzu yakamata ka gana dashi tunda ka amince. Na dubeta cikin mamaki sannan nace wanene? Tsohon mijina mana nayi shiru na dan lokaci sannan taci gaba da cewa kudin dana nuna maka rannan ma shi ya bani su domin biyan duk wanda zai iya aurena daga baya ya sakeni akwai maganganun dayake son ya sanar dakaine. Sannan kuma zakuyi yarjejeniya.

Akan me na tambayeta.
Tayi murmushi sannan tace haryanzu gani yake wai idan ka aureni bazaka sakeni ba. tayi murmushi na fada maka yana masifar sona abinda yasa kenan yarsa ta tsane ni bata kaunar taga na koma gidan. Amma yanzu nafi karfinta tunda ka amince zaka aureni sannan ta turo min salular tace dani yi magana dashi yana jiranka. Na karbi salular hannuna na rawa wannan shine karo na farko da zan fara magana da SALULA

FARISU NE? Wata sasasanyar murya tace dani nine nace dashi muryata na rawa toh farisu ina fatan duk tayi maka bayani abinda kawai da nake so dakai atakaice shine bayan kwana uku ka saketa ka kama gabanka ita ma ta kama gabanta daga rannan babu ruwanka da ita ka gane ko
eh! Nace dashi muryata na rawa gobe za'a daura auren da yamma misalin karfe biyar amma kafin nan zamu hadu dakai agidanta domin sake tattaunawa. Hudu tayi maka agidanta daga nan ne zaku wuce inda za'a daura auren aboye bayan mun gama tattaunawa.

Shirun danaji ita ta tabbatar min daya kashe tasa salular sannan ne nima namika mata tata salular gumi duk ya rufe ni adaidai lokacin ne ta mike tsaye tace dani zo mu je can yanzu zaka dawo.
Nabita abaya nayi sa'a bamu hadu da koda mutum daya ba wanda ya sanni har muka tsallaka titi inda ta ajje motarta ta bude bayan motar sannan tace dani dauki naka ne dankakreriyar akwati mai taya ce bansan ko menene aciki ba nidai kawai na dauka ne. Kada ka manta zan jiraka gobe kamar yadda ya sanar dakai karfe hudu

Nagode farisu tayi murmushi sannan ta rufe but din motar ta shiga ta tada Ita. me zanyi da akwatin? Na tambayeta. Kabari idan kaje daki ka buda ita zata fadama abinda ke cikinta. Taja motar tayi tafiyarta tabarni nan tsaye da kinkimemiyar akwati.

Na sunkuya na kinkimi akwatin na dora akafadata da kyar sannan na tsallaka titi na nufi gida ina numfashi dakyar akan hanyata ta zuwa gida na hadu da mutum biyu dana sani daya abokina ne daya kuma makwabcin mu ne wanda yayi min sannu da zuwa saboda ganina dayayi da akwati amma daya abokin nawa mai suna ALIYU cewa yayi dani Lallai mutumin ka taki sa'a muka kyalkyale da dariya yayi gaba daman akan keke yake don haka bai tsaya tsurku ba saiya wuce
Kai tsaye yana zolayata.

Lokacin dana shiga cikin gida babu kowa abangaren da dakina yake yan gidanmu suna cikin bangarensu daban hakan shiyabani damar shiga da akwatin batareda kowa ya ganni ba.
Saidai kuma Ashe..........
[3/16, 5:01 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-14

Hakan shi ya bani damar shiga da akwatin batareda kowa ya ganni ba.

Na lalubi ashana na kunna fitilar kwai sannan na buda akwatin sannan naga abinda ya sani daukewar numfashi akwatin a dankare yake da wazobiyoyi sababbi fil. Kodai ban fada ma ba kasan na zama miloniya mafarkina ya zama gaskiya hakika salma tabani mamaki bantaba tsammanin zata biyani kudin haka da gaggawa ba azatona sai gobe idan an daura auren.
Na fara kasafta yadda zan kashe kudin. Abinda bansani ba shine na aikata kuskure akaro na biyu na manta ban baiwa salma labarin yarinyar data nemi da inje har gida na koya mata karatu ba dana fada mata to da abinda yafaru akaina washegarin ranar bai faru ba.

BABI NA BIYAR

Aranar banyi cikakken barci ba duk sa'adda na rufe idona saina ci gaba da ganin damin damin wazobiya ajere reras acikin akwatin data bani
banyi barci ba har saida na tabbata na samarwa akwatin kyakkyawan maboyi acikin daren na samo wani abin cire kusa da guduma na cire daya daga cikin rubabben silin din dake saman dakina na ciccibi akwatin da karfin tsiya na taka kujera na tura ta cikin silin din sannan na mai da silin din dana barke gurin zamansu na gyara babu wanda zai iya tsammanin akwai naira miliyan uku aboye a saman dakin.

Sai bayan dana karbi kudin ne sannan naji matsaloli sun fara damuna na farko bansan yadda zanyi na sanar da mahaifina bayanin kudin ba domin na tabbata inna fadawa mahaifina gaskiyar lamarin bazai goyi bayana ba nasan sai raina yayi matukar baci kuma nasan dole ne saiya sani na maida kudin. Har gari ya waye ban cimma wata kwakkwaran shawarar abinda zanyi da kudin ba. Yau da ace iyayena zasu bani hadin kai to da da sauki to amma nasan wannan wani abune marar yiwuwa na san muddin na nuna musu kudin sai sun bukaci sauran bayani haka nayita saka ina warwarewa awashegarin ranar har kusan karfe dayan rana sannan na tashi na nufi gidan bayan na yi wanka saina sauya tufafin dake jikina da wasu wankakku sannan na dauki yan litattafaina na turanci dana lissafi don daurewa karya gindi har da karan alli guda uku na nufi gidan su Hindu El- bashir ayadda na tsara shine bayan na gama abinda zanyi agidansu Hindu daga nan saina wuce kai tsaye zuwa gidan Salma inda zamu gana da tsohon mijinta to amma abubuwa basu kasance yadda nake tsammani ba.

Unguwarsu Hindu el'bashir tana makwabtaka ne da unguwarmu ta bangaren yamma sannan dankakareren gidan el'bashir shiya mamaye kusan rabin unguwar bari na zana maka hoton gidan el'bashir azuciyarka domin ka fahimci irin tsaruwar da kuma makudan kwandalolin daya hadiye.

Lokacin daka dubi kofar gidan zakuyi ido hudu da tangamemen lambu wanda ke boye abayan doguwar farar katanga wacce keda katuwar kofa kamar kofar gari.
Ga mamakina sainaga asaman katuwar kofar lambun wacce nake tsammanin ita zata kai ka har gidan an rubuta cikin hanyan haruffa launin gwal kamar haka SALMA GARDEN

Nayi mamaki saboda ganin sunan salma ajikin kofar gidan amma daga baya saina daina mamaki ai masu suna salma na da yawa agarin nan nace cikin zuciyata.
Kamshin furanni da kayan marmari ya bugi hancina lokacin dana jera koda lambun na shiga gabana nata dar dar sassanyat iskar tsabtatacciya ta bugi fuskata gamida kamshin ganyen bishiyar lemon zaki da kashu (yazawa) sannan ne fa na fara hango tangama tangaman gine ginen alfarmar dake boye abayan shuke shuken lambun.
Wani dan siririn mai gadi fari sanye da bakaken kaya da farin rawani daya ziraro tun daga kansa har bayansa ya bayyana a gabana kamar an jefo shi.
Kai kazami ina zaka ba sallama.. Ya buga min tsawa na dubi bakin zaren ulun dake daure adan siririn wuyansa mai kamar lilo nace.
Dankerere shin mamanka hindu tana nan? Fuskarsa ta canza launi sanan idanunsa suka kada sukayi ja kafin ya yanke shawarar abinda zaiyi dani sainayi sauri nace dashi nine sabon malamin da zaike koya mata karatu shin ko kanada labarina?

Ya dubeni a yatsine yana hadiyar zuciya nayi zaton zai kawo min duka amma maimakon hakan sainga fuskarsa ta washe kaine Farisu? Ya tambayeni kwarai kwarai nace dashi yayi murmushi kayi sa'a kazami ai bangane ka bane tace idan kazo ka jirata anan zatazo ta sameka.... Kodai kaje kafada mata nazo?... Ya girgiza kai abinda tace dani kenan kazami to dankere nace dashi wannan karon baiyi fushi ba maimakon hakan ma sai ya kyalkyale da dariya sannan yace nayi mamakin ganinka da farko datace min wani sabon malaminta zaizo nayi zaton zanga abu tsaf tsaf amma saina katse. Ya isa haka in ba so kake yanzu na murde maka dankereren wuyanka ba yayi murmushi sannan ya nuna min wata kujerar katako dake karkashin bishiyar yazawa Jeka can kajirata.

Na nufi kujerar da nufin na zauna sannan sainaji kamar an sokeni da kibiya su hudune daya da manjagara yana sharar matattun ganyayyakin da suke zubowa na itatuwan kayan marmari ne biyu kuma dauke da fatanya suna saran kasar gindin kananan bishiyoyin da ake reno suna gina ramin da ruwa ke taruwa dayan kuma dauke da abin ban ruwa na hudunsu dauke da katon kwando yana tsintar kayan marmari yana tarawa aciki shine yafi daukar hankalina acan cikin lambun na hango su amma kayan dake jikinsu shi yayi min tarnaki na kasa tsaye na kasa zaune kowannen su sanye yake da yankakkun wando jeans kafi shanu wuya iya gwiwa sannan kuma da bakar suwaita gumi ya lullube ni sunyi kama dasu......

Lokacin daya dago kansa sama saina gane shi lokaci guda tun kafin ma ya gama juyowa mu hada ido dashi dogon kansa mai kamar shantu ma kawai ya isa na gane shi kansa sai kyalli yake acikin hasken ranar kamar madubi dogon gemun sa mai kamar burushi ya hada gumi sharkaf muka hada ido dashi kafata na rawa sannan sainaga ya ajiye kwandon kayan Marmarin akasa ya laluba aljihunsa ya zaro karan taba sannan ya kunna mata wuta ya fesa hayakin sama yayi min murmushi da bai kai har idonsa ba sannan ya juya kan aikin sa na tsintar kayan marmari yana zubawa a kwandon a gaban rigar sa an rubuta IJAKALA

****** ******* ****** ******* ******* ******* ****

NA SHARE GUMIN DAKE KWARAROWA KAN GOSHINA...
[3/16, 5:02 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BININ SARAUNIYA-15

Sannan ya juya kan aikinsa na tsintar kayan marmari yana zubawa a kwando agaban rigarsa an rubuta IJAKALA

***** ****** ****** ***** ******** ******* *******

Na share gumin dake kwararowa kan goshina sannan jikina na rawa na juya na yafuto dan siririn maigadin nan.
Yau kam sai abinda hali yayi nace cikin zuciyata nasan na kawo kaina ga halaka.
Menene kuma nace kayi jiranta yanzu zatazo yaushe wadancan suka fara aiki agidan nan? Na katse shi maigadin yayi shiru sannan bayan ya danyi yan waige waige ya tabbata aikinsu suke ba kallonmu suke ba saiya matso kusa dani yace cikin rada jiya suka fara aiki agidan nan ita ta kori wadancan masu gadin na shekaran jiya. Wallahi nima bana farin ciki da zuwansu ni tsoro suke bani kaganta dai kyakkyawar yarinya amma halinta mummuna ne kullum saita zageni gata da shegiyar rowa bata tabayi min kyauta ba kaima ina mamakin........
Yayi shiru lokacin daya lura cewa bashi nake kallo ba daga can cikin gidan hindu ce ita da wani mutum wanda nake tunanin shine mahaifin nata suka nufo inda nake.

Koda maigadin ya fahimci abinda nake kallo sai yayi sauri ya sulale yabarni nan tsaye kamar nayi fitsari awandon don tsoro yanzu na fara gane abinda ke shirin faruwa abinda yafi sani kaduwar fiyeda komai shine lokacin danaga fuskar wanda nake tsammanin mahaifinta ne ko shakka babu shine mutumin danaga hotonsa shi da salma amakale ajikin bangon dakinta yanzu na tabbata yarinyar data nemi na koyar da ita karatu ba wata bace data wuce yarinyar datake son a hallakani don ganin ban auri matar ubanta ba wato salma. Tun daga nesa ta nuna ni da dan yatsa tace Baba gashi can sune irin barayin nan

Please Login or Register in order to submit comment