Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farka nayi mafarkin dan siririn maigadin nan zaune gabana yana yi min dariya.

Lokacin dana farka babu kowa adakin dagani sai gadon danake kwance akai gamida fankar dake juyawa asaman kaina wacce duk lokacin dana dubeta sainaji kaina yana juyawa nakanyi kuma addu'ar Allah yasa karta kwace ta fadomin akai.
Agogon dake jikin bangon dakin yayi nuni da karfe goma sha dbiyu na rana saura kwata adaidai lokacin ne kofar dakin ta bude sannan ta shigo SALMA CE.
Haryanzu sanye take da rigar da tazo da ita awancan lokaci saidai wani abin mamaki kuma daban idanuwanta duk a kukkumbure suke sun kada sunyi ja ko shakka banayi yawan kukan da tayine ya haifar mata da hakan
ta matso kusa dani ahankali sannan ta zauna abakin gadon idanuwanta akan fuskata bata ko kiftawa alamun tausayi da kuma nadamar halin data jefani karara suke a fuskarta.
Sannu farisu tace a sanyaye muryarta na rawa.
Kofar dakin ta sake budewa akaro na biyu atsammanina zan sake ido hudu da yansanda amma sabanin hakan sai wata yar siririyar yarinya ta shgio ciki dauke da kurtun zuba abinci fara ce sanye da doguwar riga baka mai farin aiki agaba bugu da kari ta lillibe kanta da dan siririn gyale fari mai digo digon baki shekarun yarinyar zasu iya zama komai tsakanin goma zuwa sha biyar.
Ta ajje abincin agaban salma sannan ta juyo fararen idanunta kan fuskata tace Sannu yaya jiki?
Da sauki nace da ita sannan ta juya ahankali ta fice daga dakin simi simi kamar yadda ta shigo nayi mamakin cewa basu ko damu da suyi musayen kalma ba tsakaninta da salma.
Na dubi salma itama ta dubeni mukayiwa juna kuri da ido na dan lokaci munyi kimanin tsawon dakiku talatin da wani abu batareda muncewa juna uffan ba. Salma ce tafara yiwa shirun karantsaye da cewa.
Farisu.... tace bakinta na rawa don Allah kayi hakuri ka yafeni duk ni na jawo maka kana zaman zamanka ni kaina ban taba tsammanin azzaluman nan zasuyi maka haka ba Wallahi dana sani farisu da ban jefaka ciki ba dan Allah farisu ka....
Kada ki bata yawun bakin ki salma na katse maganar da takeyi kada kuma ki sake imani da cewa zan sake amincewa da tatsuniyarki nima hadama ce da rashin godiya ga Allah shiya jawomin. Amma inason ki sani har bayan rayuwata salma bazan taba mantawa da abinda kikayi min ba sanin kankine tuni kinyi sanadiyyar nakasa dakuma halakar mutane uku abaya wannan yafarune kafin haduwata dake amma saboda son kai da son abin duniya kika yaudareni ta hanyar nuna min dukiya saboda ganina da kikayi talaka kikayi sa'a kuma kika sameni marar wadatar zuci hadamamme kamar sauran talakawan da kika yaudara abayana maganina kenan salma dana godewa Allah nayi zamana ahalin dana kasance ada to da wannan bata faru akaina ba kinsan yan magana sunce Talauci da kwanciyar hankali yafi arziki da tashin hankali..
Sheshshekar kukan da salma keyi shiya katse kalaman dake fitowa daga bakina.
Dan Allah farisu ka yafeni Wallahi farisu idan baka yafeni ba Farisu na shiga uku da rayuwata dan.... Dan Allah kayi hakuri....ta sake fashewa da kuka har hawayenta yafara zuba akan kirjina nayi sauri na kawar da fuskata amma hakan baiyi maganin komai ba kukan da take ya karyar da zuciyata.

Taci gaba da sharbar hawaye nikuma idanuna na kallon bangon dakin zuciyata cike da tunani dakuma fargabar abinda zai faru Akaina nan gaba ko da........

(jikan sidi mai jaka)
[3/16, 5:07 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 20

BOOK 2

Ni kuma idanuna na kallon bangon dakin zuciyata cike da tunani dakuma fargabar abinda zai faru akaina nan gaba ko kadan bana yaudarar kaina nasan kam ni tawa ta kare babu abinda Elmahdi bazaiyi ba don ganin an rataya min laifin kisan maigadinsa akaina kudine yana dasu zai iya daukar duk lauyoyin dake birnin sarauniya don ganin an bataddani tunda abin da yarsa ke so kenan to amma.....
Salma ta katse tunanina Farisu takira sunana dan Allah farisu ka dubeni ka kuma yafemin kona ji sanyi azuciyata domin Allah ne yasan irin radadin dake cikinta.

Na juyo fuskata ahankali muka dubi juna akaro na biyu ita tafara dauke idanunta.
Tausayinta ya sake lillibe zuciyata na dubeta ahankali muryata na gargada nace.
Salma. ta juyo ahankali ta dubeni sanan tace na'am farisu. Tausayinta ya dada lillibeni sannan nace da ita.
Kiyimin alkawarin abu daya salma zakiyi min?

Fadi mana farisu ni mai yi maka komaice ayanzu raina ma ni mai iya sallama maka ce in dai har inada iko
inason ki taimakeni salma ki sanar da iyayena duk abinda ke faruwa ki kuma rokamin gafara agurinsu domin ni tawa takare babu wani abu da zan iya yi sai ko abinda Allah ya yi....
Ka daina fadar haka farisu salma tace dani babu abinda zai faru dakai kaidai kabani hadin kai zan turo maka lauyan da zai kareka idan kunje kotu zaizo yayi maka tambayoyi ina fatan zaka bashi hadin kai kwararre ne nakuma tabbata duk lauyoyin da Elmahdi kedasu basu isa su kayar dashi ba sai munyi narasa farisu karka damu kaji ko? Tace dani tana dubana abinda na gani a idonta shi ya tabbatar min da cewa tana nufin abinda tace har cikin zuciyarta.

Ka yafeni farisu sannan taci gaba da cewa nasan yanzu ka tsaneni farisu amma inason kasan da abu daya farisu. Na yi shiru ina dubanta taci gaba da cewa.
Wallahi farisu tunda nake bantaba sanin wani abu wai shi so ba har zuwa lokacin dana hadu dakai kai kanka farisu bana kaunarka alokacin da muka fara haduwa ina dai kawai son cimma wani buri nawa ne tayi shiru tana dubana sannan tace Farisu zakayi mamaki idan nace maka duk duniyar nan ayanzu banida abin kauna kamar Ka.

Kwalla tafara cika mata idanu tasa gyalenta ta share sannan taci gaba da cewa
nasan ka tsaneni farisu amma inason ka sani banida abinso aduniyar nan kamar ka babu yadda na iya da raina haka kawai na farka rana guda na tsinci kaina ina begenka ayanzu kam farisu na gane cewa so yafi komai dadi na gwammace Ace ina tare dakai har abada da ace ina tare da Elmahdi Tayi shiru na dan lokaci sannan tace kada ka damu farisu zamuyi nasara in Allah ya yarda ta dubeni tayi murmushi ga mamakina saina tsinci kaina ina mai yi mata murmushi akaro na farko tun bayan zuwan yansandan sai yanzu ne naji hankalina ya dan kwanta.

Atunanina salma zata iya tserar dani wannan shine kuskurena na biyu.

Salma ta dafa hanuna da lallausan tafukan hannunta sannan tace ya kamata kadan ci wani abu dafa hannun nawa datayi shiya tuno min da haduwar mu ta farko inda take cewa bazaka fada min sunan naka ba?

**** ***** ***** ***** ********* ***** ***********

Kafin mu rabu da salma sai da ta tabbatar min da cewa kada na damu domin wai tunda tana sona to babu yadda za'ayi tabarni na halaka. Na kuma yarda da duk abinda tace nakuma sami kwarin gwiwa ayadda tace dani jibine za'a fara sauraron shariar tamu.

Bazan taba mantawa da lokuta biyu da al'amuran biyu suka faru kusan lokaci guda ba.

Lokaci na farko karfe hudu saura minti biyu ne kofar dakin ta bude mai ziyara na gaba ya shigo ya dan mayanta yana sanye da bakar kwat da wando bakake dakuma bakin takalmi wankan tarwada ne mai matsaikacin tsawo idanunsa kanana bakinsa daidai misali dogon hancinsa yayi matukar dacewa da farin tabaran dake shakatawa a samansa sannan ahannunsa na hagu yana rike da bakar jaka.
Dabi'un mutumin suna da ban mamaki kallo daya nayi masa na tabbata nutsatstse mai hankali da kuma kaifin basira da kwakwalwa lokaci guda kuma naji zuciyata ta kwanta dashi tabbas zuciyata na son mutumin.

Farisu ya kira suna LAUYA MUKHTAT ABBAS ina fatan salma tayi maka zancena banyi mamakin ji cewa shine lauyana ba amma kasancewarsa agabana yabani mamaki saboda ban taba tsammanin zuwansa da gaggawa haka ba atsammanina sai gobe ne zata turoshi to amma tunda bata sanar dani lokacin zuwan nasa ba sai na saki jikina dashi.
Ta sanar dani nace.
BARKA DA ZUWA.

Kwananka nawa asibitin nan? Ya tambayeni nayi shiru ina tunani ni kaina bazan iya cewa ga iya adadin kwanakina ba domin lokacin da aka kawoni hankalina baya jikina abinda kawai zan iya tunawa shine abin yafaru ne ranar shida ga watan bakwai.
Yau nawa ga wata? Na tambaye shi ya dubeni anutse sannan yace yau sha biyu ga wata nayi shiru ina dubansa cikin mamaki indai hakane to yau kwanana shida kenan anan.
M. Abbas ya zaro wasu takardu daga cikin jakarsa sannan yafara yan rubuce rubuce bayan dan lokaci ya juyo ya dubeni sannan yace Farisu saidai fa ka dan yi hakuri domin inada yar matsala akunne inason kayimin bayanin abinda yafaru tun daga farko amma ka dan daga murya

Na amaryarsa masa da duk abinda na sani tun..........
[3/16, 5:08 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 21

BOOK 2

Na amayarsa masa da duk abinda nasani tun daga ranar da muka fara haduwa da salma har zuwa yanzu nayi shiru ina dubansa yana yan rubuce rubuce sannan ya dago kai ya dubeni akaro na biyu.
Kaine ka kashe shi farisu? Tambayar tazo min abazata don haka sai naji kamar an karamin wayar lantarki agadon baya saboda tsabar kaduwa na dubeshi galala atsammanina ya dan tabune.
Da hankalina farisu yace dani yana murmushi kamar wanda ke kallon abinda ke zuciyata yanayin aikin ne haka farisu don haka yanada matukar muhimmanci ka amsa duk tambayar da akayi maka.
Ai.... Ai... Na dauka kafini sanin haka nace dashi muryata na rawa shin kai ka kashe shi? Ya sake maimaita tambayar na dubeshi duban ido da ido sannan nace bani na kashe shi ba.
Me yasa ka tsammanin ba kai ka kashe shi ba?
Me kake nufi? Na tambayeshi.
Abinda nake nufi shine ka amsa duk tambayar danayi maka batareda kayimin taka tambayar ba dolene kuma kayi duk abinda nace kayi wannan umarni ne daga SALMA yace dani haryanzu dan gajeren murmushin na nan afuskarsa.
Goyon bayanka yaci gaba da cewa dakuma amsar da zaka bani ita zata taimaka wajen cin nasararmu idan munje dakin shari'a to ai ni ban gane tambayar da kake yi min bane nace dashi ina dubansa ya dubeni sannan yace
kasan wani lokaci dan adam yakan rasa kwakwalwarsa na dan lokaci saikaga ya aikata abu batareda ya sani ba ina fatan kagane abinda nake nufi yace dani yana dubana ido da ido.
Ni kam da hankalina domin naga lokacin da Ijakala ya daga addar ya kawomin sara da addar na kauce gefe guda shine ya sari maigadin awuya.
Ko zaka iya tunawa lokacin da ya kawo saran ko dabarar ka tura maigadin gabansa bata zo maka ba kasan wani lokaci dan adam yakan tura duk abinda ke kusa dashi amatsayin garkuwa idan wani abu ko wani bala'i yana shirin fada masa.
Na girgiza kaina ko kusa hakan bata faru ba.
Lauyan da yakira kansa da Mukhtar Abbas ya dago kansa ahankali ya dubeni sannan ya cire gilashin dake idonsa ya goge shi da farin kyallen dake hannunsa sannan ya maida gilashin daraf bisa hancinsa kamar daman anan Allah ya halicce shi.

Mukhtar Abbas ya mike tsaye sannan ya hada yan takardunsa ya maidasu cikin jaka yace me yiwuwa zan sake ganawa dakai gobe kada ka damu zamuci nasara sannan ya dada dacewa sai goben ya nufi kofar dakin ahankali.

Irin yadda yace zamuci nasara dakuma kallon karshe dayayimin shiyasa jikina ya dauki rawa kamar mazari ni kaina bansan abinda ke damuna ba amma acan cikin zuciyata wani abu nata yi min kururuwar cewa kayi kuskure farisu me yasa salma bata fada maka sunan lauyan ba in har ita ta aiko shi kofar ta sake budewa kamar kowanne lokaci sannan shima ya shigo dogo ne fari yana da dan siririn gashin baki shima sanye yake da bakar kwat da wando irin na wacan hancinsa dogone saidai ya dan lankwasa kadan daga can karshen karan hancin shaho babu alamar farin ciki ko bakin ciki a fuskarsa ya nufo inda nake yana takawa daidai kamar mai tafiya akan igiya.
Sannu farisu yaya jikin yace dani fuskarsa ta washe da murmushi bana ko shakka lauyan farko ba salma ce ta aiko shi ba.

Lauya IDRIS ABUBAKAR shine sunana yace dani ina fatan salma ta sanar dakai cewa ina nan tafe nayi shiru ina dubansa makoshina abushe yawu ya karanta abakina nasan na fada babban tarko.

Tunda sassafe yan sanda bakwai suka shigo suna muzurai acikinsu harda Abdul shiya fara zaro ankwa daga aljihunsa sannan ya buga min ita ahannu baiko damu daya samin ita ahankali ba saboda ciwon dake hannuna inda ijakala ya sareni bai gama warkewa sosai ba.

Wani dansanda gajere mai tarin gashin baki kamar shekar kurciya ya aza keyata gaba su kuma sauran suka dafa mana baya.
Wanan shine karo na farko tun ranar da aka kawoni asibitin dana fito farfajiyarsa nayi mamakin ganin asibitin saboda babu wani abin azo agani cikinsa shima dai kamar su daya da sauran asibitocin daka saba gani yau da kullum na masu rufin asiri.
Tun daga kofar dakin farko da aka fita na fara ganin irin tsatstsauran tsaron da akeyimin ashe danayi niyyar gudu ma to da iya kata kofar dakina abin mamaki kusan yansanda biyar ne.
Ke gadin kofar dakin danake na lakanci hakane alokacin da ake fitowa dani.

Tun kafin mukaraso kofar shiga asibitin na hango bakar motar baki kirin da ita har sheki take dan baki.
Yansanda biyar ne atsaye abakin kofar shiga motar suna muzurai hancin bindigoginsu asaitin gangar jikina ko da aka matso dani daf da motar sai duk yansandan suka ja kunamar bindigarsu kyat kyat.
Wani dogon dan sanda kakkaura ya bude bayan motar shiga ba biya. Budewarsa keda wuya sai yansandan suka kasu gida biyu wasu bindigarsu na saitina sauran kuma suka juya hancin bindigoginsu saitin bakin kofar alokacinne to na gane cewa ashe bani kadai za'a sa acikin motar ba tuni daman akwai wasu aciki.
Lokacin da aka karaso dani bakin motar sainaji kamar ance dani daga kanka.
Na juya ahankali tuni mutane sun hada yan kungiyoyi daga can nesa suna baiwa idonsu abinci yawancin majinyatan dake asibitin duk sun lelleko suna kallona wasu akasa wasu kuma ta saman bene idan kuma har ba kunnena ne ke fada min karya ba naso Naji wata siririyar murya nacewa
TAURIN RAI IRIN NA ƁARAWO KINGA KO AJIKINSA MA OH!!!!

Zuciyata tayi kuna bakin ciki mai tsanani Yayiwa zuciyata mayafi babu abinda yafi bata min rai fiyeda komai irin yadda sunana zai baci nasan tuni labari ya sami iyayena dakuma sauran mutanen unguwar mu tausayin kaina ya kamani sannan tunanin sallau ya fado min arai ko ina mutamin nan mai bamu bashin lemo?
Na tambayi kaina ko me zaice idan yaji labarin? Na sake tambayar kaina me yiwuwa ya fashe da dariya na amsawa kaina cikin NADAMA.

****** ****** ***** ****** ****** ***** **********
[3/16, 5:09 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 22

BOOK 2

Na tambayi kaina ko me zaice idan yaji labarin? Na sake tambayar kaina me yiwuwa ya fashe da dariya na amsawa kaina cikin NADAMA.

***** ***** ***** **** **** ****** **** ***********

Yansanda biyu suka kafa hancin bindigarsu agadon bayana yayinda wasu uku ke kokarin turani cikin shiga ba biya alokacin ne to na hangota.

Tana tsaye daf da motar daga can nesa nisan dake tsakaninmu zaikai taku hamsin na gajeren mutum. babu alamar bakin ciki a fuskarta tana sanye da doguwar riga ruwan hoda takalminta baki ne (Cover shoe) mai dauke da ado na sarka ruwan gwal bata ko damu data lillibe gashin kanta ba maimakon hakan saita hada gashin kan nata abaya ta daure shi da ribon launin fari wanda akayiwa shan fure. Mukayi ido hudu da ita sannan wani faffadan murmushin nasara ya bayyana akyawawan labban bakinta burinta ya cika tayi min kallon kaje can ka karata sannan ta juya ta nufi motarta bakin tabaran dake idonta bai hanani gane ta ba HINDU ELMAHDI ce.
Wannan shine gani na karshe danayi mata ban kuma sake ganin taba sai bayan shekaru uku.

Yan sandan suka angizani cikin motar kamar wani buhu sannan suka garkame kofar mu uku ne acikin motar mutum biyu din dana tarar duk sun ji jiki tsammanina sun dade agidan tuhuma kafin ayi niyyar kaisu ga shari'a. Dayan yaro ne kamar ni amma na biyun ya dan tsere mana da yan shekaru kamar biyar.
Mutanen biyu suka dago kai suka dubeni suna muzurai dayan wanda nake tsammanin kusan shekarunmu daya farine dogo siriri daga dogon hancinsa har zuwa bakinsa babu wani abin aibu a tattare dasu amma idan ka dubi idonsa anan ne zaka iya cankar dabi'unsa idanunsa sun fi kama dana maciji fiye dana mutum.
Mutum na biyu bawani abun ku gani bane irin dai mutanen daka saba gani yau da kullum kan titunan birnin sarauniya suna yawo ne babu sabon al'amari ko siffa atattare dashi in ka dauke katon cikinsa mai kamar salka nayi mamakin ganin cikin nasa bai sace ba duk kuwa da irin azabar da nake tsammanin ana gana musu.

Kayi sa'a dogon yace dani yana kifkifta idanu sa'ar ka daya itace da za'a yanke maka hukunci haka da gaggawa batareda an ajjeka lokaci mai tsawo agidan tuhuma ba. Na dubeshi cikin fushi sannan nace menene abin sa'a ga wanda ke fuskantar hukuncin kisa?

Ba kai kadai ke fuskantar hukuncin kisa ba akalla dai bakaci dukan tsiya ba yace dani
nayi shiru ina mai mamakin abinda sukayi har suka sami kansu airin wanan mummunan matsayi irin nawa.
Adaidai lokacine mukaji motar ta fara tafiya bakin ciki ya sake lillibeni kowannen mu na tare da masaniyar cewa mutuwa muke fuskanta ga mamakina sainaji ni ko mutuwar bana tsoro na rufe idona kammanin salma suka bayyana karara a zuciyata alokacin data dafa hannuna farkon haduwarmu da ita tace min
Bazaka fada min sunan naka ba? Nayi tsammanin sassanyar muryarta cikin zuciyata.

**** ***** **** **** **** ********* ***** *********

Abinda yabiyo bayan shari'ar abin bakin ciki da takaici ne gareni dakuma duk mai kaunata.
Abin yazomin abazata ban kuma taba tunanin bazamuyi nasara ba yaudarar da lauyan farko yayi min ita ta basu damar cin nasara akanmu ashe lauyan dayafara ziyartata asibitin ba salma ce ta aikoshi ba bansan yadda akayi suka san cewa salma zatayi tunanin lauya ba amma atsammanina su Elmahdi ne suk hada baki da malaman asibiti don yi musu leken asiri.

Me yiwuwa kayi tunanin zan baka labarin abinda yafaru a kotun to ko kusa kada kafara tunanin haka domin bazan iya ba saboda fadin abinda yafaru akotun bashi da amfani tunda bamuyi nasara ba abubuwan da suka faru na bakin ciki aranar basa misaltuwa abinda ya faru ya riga ya faru babu irin kokarin da lauyana baiyi ba aranar don ganin ya cece ni amma ina mun makara domin su elmahdi sun shiryawa komai sun kuma zo da shaidu na karya wadanda suka rantse tsakanin karya da gaskiya wai sun ga lokacin dana sari mai gadin da adda awuya.

An kuma kawo shaidun ne amatsayin masu hidima agidan elmahdi kuma acewarsu wai lokacin da akayi ihu barawo su suka fara kawo agaji kuma akan idon su na sari mai gadin lauyan yayi ta kokarin kareni bazan taba mantawa da ranakun shari'ar ba zama uku kotu tayi abinda yafaru kuma adan tsakanin kwanakin babu dadin ji.
Inaji ina gani saboda banida gata akan laifin da banawa ba aka yanke min hukunci. Aranar da aka yanke min hukuncin karshe ne naji abinda ban taba jiba arayuwata abinda yafaru aranar shine nake tsammanin zan iya sanar dakai.
Bayan lauyana yayita babatu kamar ransa zaifita amma hakan baisa ya cimma nasarar komai ba nasara daya kawai ya samu itace anyimin afuwa baza'a kashe ni ba amma za'ayimin daurin rai da rai lokacin da mai shari'a ya zartar da hukuncin sai duk kotun akayi ajiyar zuciya sanan hayaniya ta barke.

Salma wacce ke cikin yan kallo ta fashe da kuka wiwi kamar karamar yarinya ta nufoni da gudu zata rungumeni amma yansanda suka maida ita tana ta kurururwa.
Farisu Farisu Farisu na shiga uku Farisu wallahi ni a janyo maka wayyo Allah farisu nima mutuwa zanyi banga amfanin rayuwata ba amsa kuwwar kuka da kalamanta suka daki dodon kunena abin babu dadin ji dakyar aka fitar da ita waje.

Ana cikin hargitsin ne sai kawai.......
[3/16, 5:10 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 23

BOOK 2

Amsa kuwwar kukan da kalamanta suka daki dodon kunnena abin babu dadin ji dakyar aka fitar da ita.

Ana cikin hargitsin ne to na hango mahaifina shida babata sun nufo inda yansanda suka zagayeni da bindigogi idanuwan babata duk sun kukkunbura saboda kuka shakaru sun karu akan nata nada saboda tsananin bacin rai wasu yan sanda biyu suka yi musu jagora har zuwa inda nake.
Mahaifiyata tayi wuf ta kankameni tana kuka yan sandan dake zagaye dani suka dan dare domin su baiwa mahaifina damar karasowa kusa dani idonsu akaina basa kiftawa a tunanina suna tsammanin zan iya gudu ne.
Dannan mahaifiyata tace dani tana kuka kamar ranta zaifita sunan kenan data saba kirana dashi shi kenan kuma dannan mun rabu dakai wayyo Allah!! Allah ka saka masa Allah kayi sakay... Kukan ya shake mata makwogoro ta kasa karasa abinda take son fada.
Ku yafeni nace dasu cikin kuka kukan da suke ita da mahaifina sharaf sharaf shiyafi komai bata min rai fiyeda komai shine kuma ya karyar da kwarin zuciyata harna fara kuka.
Mun yafe maka farisu sukace gaba daya mahaifina ya matso kusa dani ya dafa kaina sannan ya matso kusa da bakinsa daf da kunnena cikin rada yace Farisu kada ka damu mun yafe maka abu na karshe danake son ka sani shine ka yarda da kaddara haka Allah ya kaddara zata faru akanka kaci kuma gaba da addu'a aduk inda suka kaika Allah yana taimakon wanda ya rokeshi kada ka yanke kauna farisu nasan bazaka dauwama har iya rayuwarka acan ba domin Allah zai bukutar dakai da yardarsa nasan duk abinda kayi da wanda bakayi ba duk kayi shine saboda tunanin irin halin da muke ciki na talauci da matsi...zuciyarsa ta karye yafara shashshekar kuka akunena Allah na tare dakai Farisu sai... Sai... Wata.. Rana....

Wani dan sanda dogo ya dan taba mahaifina abaya sannan yayi masa nuni da cewa dan lokacin da aka basu don ganawa dani ta karshe ya wuce har akayi waje dasu babata bata daina kukaba amma mahaifina ya dan saurara lokacin dayazo fita sai ya juyo maka hada ido yan sandan na tsaye suna kallon mu babu wanda yace uffan munyi kimanin dakiku goma sha biyu babu wanda yace uffan sannan ga mamakina sai naga yayi murmushi nasan murmushin karfin hali ne irin na namiji amma hakika murmushin ya karamin kwarin gwiwa.

Mintuna biyar da faruwar hakan sai suka iza kyeyata zuwa inda motar take shiga ba biya wacce ke tsaye bakikirin tana sheki acikin hantsi suka turani ciki sannan suka nufi babban gidan yarin dake birnin sarauniya dani motar tana tafiya nikuma ina leken waje ta yan kofofin da aka bari domin iska ta sami gurin shiga kallon karshe nakeyiwa birnin a tsammanina nida sake dawowa nan saidai ko a makara idan na mutu. To amma abubuwa basu faru kamar yadda nake tsammani ba. Wasu yara na wasa akofar gida suka dago mana hannu duk da yake kuwa basa ganin wanda ke cikin motar na danyi murmushin karfin hali sannan nace Allah ya shiryeku yara na lumshe idona ina sauraron shiga sabuwar rayuwar da bai kamata ace ta zama tawa ba.

Wani kakkauran hannu mai kama da bayan kada ya mari wuyana nayi firgigit na bude idanuna tun kafin na gama mutsutstsuke idanuna nagane wanda ke dukan nawa.
Wannan bashine karo na farko ba bakuma na biyu ba kai bama na dari kona dari biyu ba wannan shine kusan dubu daya da chasa'in da biyar 1095 da kakkausan hannunsa ya mari wuyana shekara kamar kwana indai har lissafinda nake daidai ne to yau kusan shekaruna uku kenan agidan maza. Aduk kuma iya kwanakin danayi wannan kakkausan hannun shine ke tashina barci.
Kamar kullum saina bude idanuna ina dubansa ahankali ina duban mai tashin nawa.
Dan siriri ne mai kamar langa langa saidai kuma zuciyarsa irin ta manyan mutane ce masifa da mugunta kuwa ko sauro ya rufa masa asiri dogone baki koda yake ayanzu ya rikide ya koma launin shudi shudi saboda tsabar wahala mukuma farare fararen mun koma launin kunun kwankwa kasuma duk ta cika mana fuska duguzum-zum babu kyan gani da ace zamu fito cikin mutanen dake cikin gari to da babu abinda zai hana musa kananan yara mafarki.

Barcin ya isa hakanan yace dani yana zazzare idanunsa

Please Login or Register in order to submit comment