Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu mana sata. Tace cikin karaji kamar da gaske. Inajin ma sune suka sace maka na'u'rorinka masu kwakwalwa na kwanakin nan sannan ta kwalla ihu kai masu gadi ku tare barawo.

Yanzu ne na fahimci abinda take nufi so take tayimin kamun barawo idan yan ta'addar da ta dauko amatsayin masu aiki sun kasheni to sun kashe barawo kenan.
Na zubar da litattafaina da karan allina guda biyu na zura aguje domin tserar da kaina na tabbata babu abinda zai fitar dani daga sharrin datayi min idan na tsaya kuma nasan sakamakon abinda zai faru.

Ijakala ne yafara fitowa ya biyo ni da adda tsirara ahannunsa sannan sauran suka rufo masa baya da gudu yakawo min sara da adda amma bai sameni ba sannan muka cigaba da gudu duk kokarin da nake shine nakarasa kofa nasan indai na fita daga gidan shikenan banajin zasu iya biyoni waje.
Ku tare barawo hindu ta sake kwalla ihu adaidai lokacin dana kusan karasa kofar gidan ba zato ba tsammani sai ga dan kereren mai gadin nan yashiga gabana alokacin ina kokarin kaiwa ga kofar nayi kan maigadin da gudu ashirye nake na banke shi domin tserar da rayuwata.
Na runtse idanuna na banke maigadin adaidai lokacin da Ijakala ya kawo min sara da addarsa.
Banke maigadin danayi shiyasa ni tuntube dashi na fadi fuskata ta daki kofar gidan ji kake gau gau naji wani radadadi ya soki kaina har wani kara nakeji a kunnena wur wur wur abin tsautsayi faduwar danayi ita ta cece ni cikin nufin Allah sai addar ijakala ta sauka awuyan maigadin nan take anan maigadin yafadi kasa yana shure shure tuni jini yayiwa rigarsa wanka.

Ganin abinda yafaru shiyasani mantawa da nawa ciwon nayi zumbur na tashi sannan Ijakala yakawo min sara da addar na sunkuya ya sari kofar gidan sannan yayi sauri ya tsare kofar da adda a hannunsa tsirara tana walkiya
ku gama dashi mana ya bugawa yaran tsawa daya daga cikinsu ya daga manjagaran dake hannunsa sama da niyyar ya sauke min shi a tsakiyar kai ganin cewa sauran basu karaso ba sai nayi amfani da damar na shige shi kafin ya sauke min manjagaran na daki ruwan cikinsa abinka da wanda yake gudun ceton rai dukan danayi masa shiyasa ya jefar da manjagaran gefe guda shi kuma ya durkusa nan rike da cikinsa nayi sauri na rarumi manjagaran daya yar.

Ijakala ya sake kawo min sara nasa manjagaran na kare ji kake kal! Hakora uku na manjagaran suka balle adaidai lokacin dayake shirin sare min kafata ne naji an tika min wani abu abaya dam nafadi agurin ina murkususu azatona kashin bayana ne ya karye daya daga cikin yaron Ijakala na tsaye akaina hannunsa rike da dankareren icen bishiya yayi yani atsaye azatona irin icen da ake tashen zan buge dashi ne.
Mai dogon gemun ya sake kawo min sara wannan karon kuwa saina sa hannu na kare saboda radadin dukan da akayi min bazaisa na kauce ba.
Addar tasa ta tsarga min hannu jini yayi tsartuwa sannan ya sake daga addar nayi zumbur na mike adaidai lokacin daya sake sauke min ita agadon baya nayi sa'a bata sameni ba adaidai amma ta tsarga min riga nayi taga taga kamar zan fadi amma na cije domin nasan idan na sake na sake kaiwa ga faduwa kasa to ni shikenan tawa ta kare.

Suka rufa min baya don tsabar sharri irin na mace su suna kokarin halakani ita kuma tana faman kururuwa wai barawo barawo nasan nufinta so take ta janyo hankalin sauran mutanen unguwa suzo su karasa ni.

Nayi cikin shuke shuken gidan da gudu ina cikin gudu sai kayar bishiyar lemon tsami ta rike min riga nayi nayi na kwace amma......
[3/16, 5:02 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-16

Nayi cikin shuke shuken da gudu ina cikin gudu sai kayar bishiyar lemon tsami ta rike min riga nayi-nayi na kwace amma abin yaci tura gashi kuma Ijakala na biye dani ko wannen su dauke da makami. Shi da adda wani da manjagara dayan kuma da katon itace shikuma na cikon hudun dauke yake da dagi na hakar kasa. Ku rike shi na soke shi!! Yace dasu ijakala cikin karaji.

BABI NA SHIDA

Na fizge rigata da karfi daga jikin kayar anan nabar rabin rigar ajikin kayar nayi gaba da gudu duk kokarina bai wuce na kai wa ga katangar gidan ba gashi kuma lambun yanada fadin gaske abinda yafi damuna kuma shine kayoyin bishiyar lemon tsami da suke yayyagata duk sun kekketa min riga. Ga saran da sukayi min da adda yana zubar da jini duk kaina ya daure yayi wani dum..
Idona yakai ga wani katon sungumi dake jingine ajikin itaciyar goba nan da nan na dauke shi na rike ahannuna su kuma suna biye dani. Nafisu gudu nesa ba kusa ba don haka sainaga abinda yadace nayi shine na tsere musu na buya saboda na fuskanci sun fara gajiya.
Nasha wata kwana sannan na zagaya bayan wata katuwar bishiyar mangwaro wacce keda yawan ganye lif lif har kasa na shige cikin ganyen namakale ina sauraron sautin takun kafafunsu suna ta gudu adaidai lokacin ne kuma naji shiru kamar an dauke ruwa nayi mamakin abinda ya tsaida su nasan kodai rashin ganina ne ya tsaida su kokuma wani abu yafaru....

Kuzo nan shashashan banza gabana yafadi danaji muryar Hindu ce. Ki bari mu karasa shi mana.... Ijakala yace da ita yana haki.
Yadda addar dake hannunka shashashan banza tace dashi to hajiya ya jefar da addar.
Babane yakirawo yan sanda tace dasu abinda nake so daku shine kowa ya koma kan aikinsa ku manta dashi babu ta inda zaifita domin yansanda na nan ako ina abayan gidan abinda nake so daku shine idan yansanda sun tambaye ku inason ku bada shaidar cewa kunga lokacin da barawon ya sari maigadi da adda wannan ma kawai ya isa kuma barshi da yansanda tunda dai Allah yasa maigadin ya mutu sai mubar laifin kisan akansa wannan ya ishe shi....
Ya mutu? Naji muryar ijakala na rawa lokacin daya tambayeta ko bai mutu ba nasan asibiti zai karasa sannan taci gaba da cewa idan kuwa yansanda basuci nasarar kama shi ba kodayake da wahala ma amma dai in hakan ta faru to kuna iya nemansa da kanku duk inda yake ku karasa shi yan sanda na iya tsammanin dukan da akayi masa ne ya kashe shi amma wannan babu wani abu nasan baba na iya kwantar da maganar musamman idan muka tsaya masa laifin kisan mai gadin.......

**** ***** ***** ****** ******* ***** ****** ******

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'una abinda naci gaba da cewa kenan lokacin danaji sun bar gurin yanzu kam nasan banida mafita nasan mabiyota a yanzu bazata hana yansanda ganina ba.
Nayi karfin hali nafito daga karkashin ganyayyakin bishiyar mangwaron adaidai lokacin ne fa na hango ginin daya zagaye katon injin dake baiwa gidan wuta acan kuryar gidan yake aboye abayan shuke shuken itacen ayaba.
Nan da nan nufo gurin dakyar nake tafiya juwa na daukata saboda karancin jinin daya zuba ajikina.

Ajere abayan ginin wasu manya manyan durarruka ne na mai guda hudu biyu afafe suke amma sauran ba'a fafe su ba wata dabara ta fado min amma ni kaina nasan caca zanyi domin banida wata hanyar tsira data wuce wannan.
Na daga daya daga cikin faffun durarrukan na rude kaina ciki idan baka sani ba saikayi zaton kawai kife duron din akayi.
Banfi minti biyar da shiga ba naji takun sawun yansanda suna zazzagaya lambun suna nemana.
Ba'a dade ba naji sunzo inda nake boye zamu duba nan naji daya daga cikinsu yace. Kana tsammanin zai buya anan ne kaima dai da wasa kake shima yasan ai dole ne mu duba nan na fada muku wahala kawai zamuyi domin ina tsammanin ya sulala tun kafin muzo. Abin kawai dayafi shine muyi sauri mu fita farautarsa tun kafin yayi nisa kamata yayi dai mu duba mu tabbatar baka sani ba kome na iya faruwa.
Idan baku gaji da batawa kanku lokaci ba ni kunga tafiyata naji takun samunsa yabar gurin ba'a dade ba naji daya dansandan daya nace sai an duba ko ina cikin harabar mashin din shima ya hakura yabar gurin.

Bansan iya tsawon lokacin danayi acikin duron a takura ba nidai azatona rashin isashshen jinine ya sumar dani na yunkura da duron na turar dashi gefe guda sannan nima na fadi gefe guda duhun dare yafara shigowa kaina yace me zaiyi ba ciwo ba na jingina ajikin ginin daya zagaye injin bada wutar na lumshe idona iskar hadarin daya fara hadowa ta fara kadawa sauran tsummar rigar dake jikina fal fal.
Na bude idona na dubi farin gajimaren daya mamaye sararin samaniya adaidai lokacin ne na hango wata tsuntsuwa dauke da wani kyalle wanda nake tsammanin launin ja da shudi ne tsuntsuwar nata kokawa da dan karamin kyallen dake bakinta taki saki ita kuma karfin iskar ya hanata tafiya yarda take so iskar sai maida ita baya takeyi. Nayi mamakin abinda ya hana tsuntsuwar sakin tsumman kyallen wai shin ina amfani badi ba rai na tambayi kaina. Yanzu kam mafarkina na zama miloniya yabi iska ga kudin can na boye adaki nikuma gani nan ina shirin halaka shin dana hakura da yadda da Allah ya ajiyeni amatsayina na talaka da wannan zata faru akaina? Na tambayi kaina dana rabu da salma tun farko da yanzu ina gida zaune lafiya amma yanzu fa na sami kudin saidai kuma kudin bazasuyi mini amfani ba.

Haryanzu tsuntsuwar na kokowa da tsumman dake bakinta me zai hana ta saki tsumman da kanta ta tserewa halaka? Na tambayi kaina saidai kuma can cikin zuciyata wani bangare na cewa abinda ya hanaka rabuwa da salma harka samu kanka ahalaka shine ya hana tsuntsuwar sakin tsumman.
Hadama da rashin godiya ga Ubangiji..... Naji kaina yayi dum idanunwa sun fara rufewa ina shirin suma. Adaidai lokacin ne naji an take kafata da wani katon takalmi aka fara ci gaba da rugugi na bude idona don ganin wanda ya take kafar tawa gabana ya yafadi tsigar jikina tayi yar!!! Yanzu kam nasan ni rashin godiya ga ubangiji yakaini ga halaka yana tsaye akaina da kafceciyar adda ahannunsa dogon gemunsa kamar burushi dogon kansa mai kamar shantu na sheki kamar madubi IJAKALA NE.

Ya daga addar sama sannan yace
WANNAN SHINE KARSHEN MAI TAURIN KAI

NAYI KALMAR SHAHADA NA RUFE IDONA INA JIRAN JIN SAUKAR ADDA.

KADA KA RABA SHI GIDA BIYU WATA SASSANYAR MURYA TACE DAGA BAYA...

ZAN CIGABA A LITTAFI NA BIYU
Nazir Adam Salih.

Saiku biyo ni a littafi na biyu don jin yanda zata kasance

YARIMA A GANGARIYA
(jikan sidi mai jaka)
VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.



We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors



We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.



AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.



Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.
DANDANO DAGA LITTAFIN

VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.



We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors



We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.



AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.



Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.

BIRNIN SARAUNIYA

( NA BIYU 2 )

Na Dallara hasken cocilar acikin dakin ga mamakina sai naga haryanzu dakin yana nan kamar yadda yake tun shekaru uku da suka wuce.

Na bude akwatin ahankali sannan na haska cikinta kudin na nan kamar yadda na barsu, na dauki damin wazobiyoyi daya ina jujjuyawa ahannuna asannan ne naji gabana yafadi rassss Domin kudin dake kasan wanda na dauka duk ba kudi bane Damin yankakkun takardu ne farare sol ba kudi bane........
[3/16, 5:04 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 17

BOOK 2

LITTATTAFAN NAZIR ADAM SALIH

*KIBIYAR AJALI
*ME YAFI KUDI
*TALEKO TA KOMA
*BIRNIN SARAUNIYA
*NAIRA DA KWABO
*ALJANI YA TAKA WUTA
*MUTUWAR KASKO

SADAUKARWA NE GA.
Kannena Mustapha Adam Salih
Harisu Adam Salih.
Mas'ud Adam Salih
Shafa'atu Adam Salih
Binta Adam Salih
Dakuma
Lamira Adam Salih

Tukwuici ne ga Abokaina kamar su
Bala Magnet(Hamilton)
Nasir Asir Guy(warrios)
Aminu Siba (Warrios)
Abba United (Boys)
Audu Madda (Strangers)
Hamisu Manya.

TUKWUICI NE GA
Ma'awuya Yusuf Adam
Sagir Fancy (Strangers)
Musbahu (Abey)
Barrister Mijin Hajiya (France)

KYAUTATAWA NE GA MALAMAINA KAMAR.
Malam Mustapha Abubakar Sadiq Islamiyya
Malam Ussaini
Malam Danladi
Malam Danbaba
Malam Musa

BIRNIN SARAUNIYA (2)
Copy Right (c) Nazir Adam Salih 'nas' 1998
Hakkin Mallaka (c) Nazir Adam Salih 'nas' 1998

Tarihin Bugawa
1998

AKULA
Wannan Littafin Kagagge ne ba'ayi shi ba dan cin zarafain wani ko kuma bata masa suna ba sai dan gargadi dakuma nishadi ga al'umma Allah yasa mu amfana daga darasin da Littafin ke koyarwa kuskuren dake ciki kuma Jama'a a Gafarceni Allah yayi mana jagora Ameen.

NINE NAKU
Nazir Adam Salih(Nas)
P.O Box 4792 Abubakar Saddiq
Islamiyya Dakata.

BIRNIN SARAUNIYA (2)

Na Nazir Adam Salihu (NAS)

Kada ka raba shi biyu wata sassanyar murya tace daga baya...

Tuni na yanke kauna da rayuwa amma jin sassanyar muryar ta daki dodon kunnena sai naji farin ciki ya dan lillibeni.
Idanuwana sunyi nauyi basa buduwa saboda jinin daya zuba daga jikina. Amma jin sassanyar muryar shi ya sani kunan bakin wake na dan bude idona kadan tuni daman sassanyar muryar ta bani hasken wanda ke maganar.
Tana tsaye abayan Ijakala kanta lullube da farin gyale sanye take da doguwar riga shudiya babu alamar jin tausayi ko kuma razana afuskarta. Hannun ijakala wanda ke rike da addar yayi sororo sannan addar ta kwace ta fado daga hannunsa ya juya a sanyaye ya kalleta itama ta kalle shi sannan ya shafi dogon gemunsa sukayiwa juna kuruu na dan lokaci shine yafara kawar da idonsa.
Wa yasa ka raba shi biyu? Yayi kimanin dakiku takwas baiko daga kai ya dubeta ba.
Sannan ahankali saiya dago idonsa suka sake kallon juna akaro na biyu awannan karon ma shine yafara kawar da idonsa sannan ya shafi dogon gemunsa yace
KI TAMBAYI HINDU
Idan kina son sanin wanda ya sani na raba shi biyu bai ko sake dubanta ba saiya juya ahankali yakoma ta inda yafito yar sassanyar iskar dake kadawa ko ina cikin lambun taci gaba da karkada rigata.

SALMA na tsaye tana kallonsa har ya kule acikin korayen bishiyoyin lambun
sannu farisu tace dani adaidai lokacin data durkusa da gwiwowinta akasa sannan ta dafa hannun da aka sareni ahankali kamar wacce ke dafa maciji dafa hannun nawa datayi shiya sani cije baki tayi sauri ta dauke hannunta sannu Farisu kaji ta sake cewa dani akaro na biyu muryarta na rawa kamar zatayi kuka.

Kaina yayi nauyi jikina yayi zafi sannan naji radadi marar misaltuwa ya soki jikina salma tayi sauri ta matso kusa dani ta dafa goshina sannan ne to naji tafara sheshshekar kuka hawaye suka fara kwararowa daga kumatunta.
Farisu.... Farisu shi.... Shi... Yayi ma haka? Sautin kukanta yafara fitowa fili cikin murya mai ban tausayi ta sunkuyar da kanta kasa kamar zata dorashi akan ruwan cikina amma batayi hakan ba sai kawai ta tsaya ahaka taci gaba da kuka cikin yar siririyar murya.

Ta dau kimanin mintuna uku tana kuka hawayen dake zuba daga idanunta yafara jika gaban rigata adaidai lokacin ne to wani dan kwakkwaran motsi abayanta yasa ta juya ahankali ta dubi bayanta.
Atsaye abayanta sanye da doguwar riga sankon sa na kyalli kamar mudubi arana EL-MAHDI ne yansandan hudu ne abayansa kowannensu rike da bindiga harbi ka ruga suna zazzare idanu kamar saci babu
El-mahdi ya daga kakkauran dan yatsansa ya nuna ni yace shine wannan kafin kiftawa da Bismillah sun cakume ni kamar buhu sukayi sama dani sakayau kamar gadon kara sannan suka sakeni na fadi tim akasa wani haske ya gifta ta kwayar idanuna sannan wani duhu ya maye hasken abu na karshe danaji shine kukan salma
kada kabari su kashe shi Alhaji shine Farisun da nake Fadama.........
Iska ta dauke maganar adaidai lokacin dana daina jin komai da komai wani duhu mai tsanani ya rufe zuciyata.

**** **** ***** **** **** ****** **** **** *******

Abu na farko daya fara zuwa zuciyata yakuma sa kwakwalwata juyawa shine maganganun mutane dana keji sama sama sannan daga can wani bangaren danake nakanji sautin dakikar agogo tik tik kamar ana dukan kwarya da sillen kara.
Da farko na dauka mafarki nakeyi ne nayi mamaki cikin zuciyata kai Amma fa wannan mafarki daban mamaki yake domin idan har ba kwakwalwata ce ke fada min karya ba naso naji muryar salma na kiran sunana.
Farisu naji wata sanyayyar murya ta doki dodon kunnena Farisu kana jina? Haba hajiya dakin dan kyale shi ya huta kinsan da wahala ya tashi yanzu tunda allurar baccin da akayi masa tanada karfi dayawa.

Wannan muryar dake magana bakuwace akunnuwana irin yadda sautin muryar ke fita da shashshake shiya sani nafara tsammanin kowanene mai muryar dole ne ya kasance.......

(jikan sidi mai jaka)
[3/16, 5:05 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 18

BOOK 2

Wannan muryar dake magana bakuwace a kunnuwana. Irin yadda sautin muryar ke fita shakakke shi ya sani nafara tsammanin kowanene mai muryar dole ya kasance babban mutum a tunina lukuti sannan alokaci guda nafara kokonto anya kuwa mafarki nake.
Sannan kamar amsar tambayata sainaji wani lallausan hannu ya dafa fuskata kamshin turaren dake hannun ya doki hancina.

Duk da yake ina tsammanin mafarki nake hakan bai hanani bude ido don ganin wanda ke dafa min fuskar ba.
Banyi mamakin ganinta ba tana tsaye akaina sanye da doguwar riga shudiya wacce akayiwa ado da maballai tun daga samanta har kasanta kanta lullube yake da farin gyale sannan iskar fankar dake kadawa asaman dakin ita ta dan turar da lillibin dake kanta hakan kuma shiya haifar da sanadiyyar da siraran gashin kanta masu sheki da walkiya suka sami yancin fitowa suna kadawa gwanin sha'awa kamar gemun masara yayin iskar damina.
Hajiya kiyi hakuri har zuwa lokacin da zai farka da zarar yatashi zanzo na sanar dake da kaina.
Ai ya farka Salma tace da mai maganar a sanyaye. Na dan kara bude idona don ganin wacce ke maganar ga mamakina sainaga bakamar yadda nake tsammanin ganinta ba sabanin yadda zuciyata ta fasaltamin ita yar siririya ce doguwa ta dan tankwara kadan daga sama baza kuma ka iya sanyata acikin ajujuwan launin fatar jiki da muka sani yau da kullum ba domin kuwa baza ka iya kiranta fara bako ko kuma wankan tarwada ba kasancewarta zabiya kwayar idanunta launin ruwan kasane. Sannan gashin kanta launin ruwan kasane wanda suka so suyi kama da gashin masara tana sanye da doguwar riga fara iya kwauri irin kayan dai daka saba gani yau da kullum ajikin malaman asibiti sannan amanne asaman aljihun rigarta daga bangaren hagu wata yar roba ce shudiya dauke da sunanta
TURAI SARAKI duk wannan abun na lakancesu ne akallo daya.

Salma ta buda baki zatayi magana kenan sai kofar dakin ta bude ahankali atsammanina dan karamin yaro ne ke turota gabana yafadi alokacin dana ga sun shigo dakin ahankali kamar wadanda ke tafiya akan bawon kwai dayan saurayi ne kamar ni dan kyakkyawan wanda fatar bakinsa ta sama ke dauke da gashin bakin dake nuni da cewa dan sanda ne. Mutumin dan gajere ne fari kakkaura rigarsa hularsa da kuma komai dake jikinsa yadace dashi inka dauke wandonsa wanda ya dan dage kadan daga kasa kamar wanda ke shirin shiga ruwa. Dansandan na biyu magidanci ne shekarunsa zasu iya zama talatin ko arba'in kokuma hamsin Allah dai masani bakine dogo bakinsa dauke da tarin gashin baki kamar ciyawar bakin ruwa fatar bakinsa da hannayensa sun dafe baki-kirin da hayakin taba saman robar dake makale ajihun rigarsa an rubuta ABDUL S.
Salamun Alaikum . Abdul din yace damu lokacin da suka shigo dakin yana murmushi hakoransa sun dafe sun koma launin zuma jajayen idanunsa akan fuskata tuni zuciyata tafara yi min gargadin cewa kada ka yarda dashi mayaudarine.

Hajiya mu yakamata mu fara ganawa dashi kafin kowa ina fatan zaki gafarceni ranki ya dade. Yana yin aiki ne yazo da haka ga mamakina sai naga salma ta nufi kofar dakin tana kuka zazzafan hawaye na zuba akan kyawawan kumatunta.
Tafice daga dakin lokacin data fice sainaji kamar wanda aka yiwa tsirara hankalina yatashi sannan jikina ya dauki rawa naji wani kadaici ya lullubeni kamar jaririn da aka dauke daga kirjin mahaifiyarsa ni kaina nayi mamaki ban kuma san menene dalilin hakan ba.

Kada ku wuce minti biyar yar siririyar malamar asibirin tace dasu sannan ta dada dacewa kada ku takura masa da yawan tambayoyi domin yana bukatar hutu.
Kada ki damu dansandan yace da ita sannan itama ahankali saita nufi kofar dakin dingyal-dingyal kamar mai tafiya akan tako tako lokacin data fice daga dakin sai naga kamar sun tsere sun barni ne acikin garken zakuna.
Abdul ya kyasta ashana sannan ya kunnawa tabar dake bakinsa wuta ya zuki tabar sannan ya fesa hayakin afuskata.

Menene sunanka dan samari yace dani yana zazzaee idanu sannan ya dada da cewa in zaka fadi fadi gaskiya yaro! Komai taja maka ka biya. Sannan ya kyalkyale da dariya gashin bakinsa ya baje akan fatar bakinsa muzu muzu kamar ciyawar bakin kogi.

***** ****** ***** ***** ***** **** **** ***** ****

Saurayin dan sandan ya matso daf dani ya zauna abakin gadon. Alokacin ne na lakanci ashe sunansa IBRAHIM.
Yansandan biyu suka dubeni ido da ido na dan tsawon lokaci sannan abdul ya sake maimaita tambayar sunana.
Na motsa lebban bakina dakyar sannan nace dashi cikin rada Aikafini sani.
Dansandan ya dubeni a yatsine sannan ya dauke idanunsa daga kan fuskata ya maida su kan bangon dakin kamar mai tunanin wani abu. Kusan tsawon dakiku talatin cif sai yajuyo ya dubeni sannan yayi murmushi.
Farisu ko? Ya tambayeni kaji shi yana magana alokacin saika rantse da Allah da gaske ne bai san sunan nawa ba.
Ya muskuta ahankali sannan ya zaro wata farar ambulan daga aljihunsa anutse saiya zaro wani abu daga cikin ambulan din mai kamar hoto ya dan daga abin sama yana dubansa kamar wanda ke kokarin gane komenene sannan saiya miko abin gaban fuskata daidai yadda zan iya gani yace
KO KASAN WANNAN ??
[3/16, 5:06 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA 19

BOOK 2

Ko kasan wannan? Nayi shiru na dan lokaci ina nazarin hoton sannan ne to naji wani abu ya soki hantar cikina bana ko shakka shine abinda kuma yasani kaduwa sannan yasa kwakwalwata tafarfasa shine abin dake hoton an dauke shine a irin wanda nake kwance idonsa ajujjuye bakinsa abude hangam-gam kamar wanda ke kokarin zuke iskar duniya gaba dayanta. Idan badon dan siririn wuyansa mai kamar lilo ba to da bazan taba gane shi ba dan siririn mai gadin nan ne wanda Ijakala ya sara awuya wajen kokarin sarana. Yanzu ne na fahimci abinda dansandan yake nufi yana nufin yace nine na kashe shi? Sannan dansanda ya dubeni sannan yayi murmushi sannan ya dada dacewa.
Nasan daman zaka gane shi Farisu duk da yake dai nasan me yiwuwa baka yiwa fuskarsa kyakkyawan kallo ba lokacin da kake kokarin sararsa amma nasan hakan bazata hanaka gane shi ba.
Me kake nufi na tambaya cikin kaduwa na dan dago daga kan gadon danake kwance jikina na rawa.
Abinda nake nufi shne ana tuhumarka da laifin kisan maigadin gidan El-Mahdi wanda Allah yayiwa rasuwa jiya da daddare.
Abdul ya zuki sigarinsa sannan ya karawa sama hazo ina fatan yanzu ka gane hausata ko haryanzu turanci nakeyi? Ya tambayeni yana zazzare idanu.

Fitarsu keda wuya sai kofar dakin ta sake budewa ahankali yar siririyar malamar asibitin nan zabiya ta shigo wata yar gajeriyar malamar asibitin baka na biye da ita dauke da dan karamin faranti launin azurfa wanda ke dauke da sirinji da kuma ruwan Allura.
Malamar asibitin ta dubeni sannan tayi murmushi tace.
Ina fatan dai basu dameka sosai ba?
Saidai kar akara nace cikin zuciyata na girgiza mata kai ahankali zuciyata cike da zulumin halin dana tsinci kaina.
Malamar asibitin ta dafa kafakata ahankali sannan tayimin allura ahannu ba'a dade ba sai wani duhu mai tsanani ya rufe idanuna dakuma dukkan tunanin dake zuciyata na tsunduma barci kafin na

Please Login or Register in order to submit comment