Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din mace a tsaye cak masu dadin murzawa , jin yadda idanunta ke yawo a jikinsa yasa hannusa ya janyo gefen  zanin gado ya rufe iya jijiyarsa ya bar qirjinshi cigaba da kallon nipple's dinsa tayi tana sake jin wani fellings dinsa  , 
a hankali ta tako zuwa inda yake  ta kai hannu ta murza nipple's dinsa daya bayan daya sannan ta durkusa a gabansa tana kallon zara zaran yatsun kafafunsa dake kowane ke kwance da gashi   zuwa gobobinsa  , hannu ta kai   tana shafa yatsun kafafunsa daya bayan daya   a hankali tana jin kamar ta cinyeshi komai nashi mai kyau kafafunsa kamar baya takasu , kusan minti  biyar yana kwance yana jin tafiyar hannunta ajikinsa ,wani tuttukin bakincikin yaji yana kawowa zuciyarsa ziyara duk sanda ya aikata zina yana jin kuna da rad'ad'in mara iyaka most especially idan ya tuno mahaifinsa,mutumin kirki mutumin daya samu kyawawan sheida daga bakin mutane bila'adadin ,bazai taba manta kyawawan halayan mahaifinsa ba ,mahaifinsa bai taba aikata zina a rayuwarsa ba har ya koma ga mahalincisa  sai gashi shi yana aikata fiyye da abinda yafi zina muni ,bazai taba mantawa ba akwai wata rana sunje massalaci da mahaifinsa wani malamin tafisri yayi wa'azi akan illar zina daga karshe yace waye wanda bai taba aikata zina ba  tun daga ganinyar quruciyarsa har zuwa wannan lokacin ?
Gabadaya  massalaci ya dauki shiru babu wanda yayi magana haka duk taron mutanen dake zaune acikin massalaci babu wanda yayi gigin daga hannunsa sai mahaifinsa kukan zuci yake daga kwance da yake...
Yayinda   ita kuma take  aikin matsa masa  yatsun kafafunsa tana shafa gobobin jikinsa domin sake dawo dashi ruwa dan ita sam bata gaji dashi ba , a natse  ya mike ya shiga  bathroom  din  dake d'akin  domin  watsawa jikinsa ruwa "

Tana ganin shigar sa  ta mike ta  zube saman gado tana sauke ajiyar zuciya , wanka tsarki ya fara yi sannan ya haɗa ruwan dumi ya zuba turaruka  wanka kala kala masu sanyi kamshi dan kawar da kamshin turaren zahra a jikinsa sannan ya shiga cikin ruwan ,jin  dumin ruwan ya ɗan sanya shi jin natsuwa a cikin zuciyarsa  , a hankali zuciyarsa ke masa faɗa "me yasa adnan ka biyewa yarinyar nan  kai daya kamata ka mata mugun duka har sai ta fita haiyacinta shine ka bige da biye mata? girgiza kànshi yayi a filli yace "duk sharrin wannan dan iskan ne amman zan san abun yi dan dole na yakice zahra daga rayuwata domin samun kwanciyar hankali."

Kusan minti talatin ya ɗauka a bawon wanka  yana cuta jikinsa sannan ya fito yana taku da kyar kugunsa d'aure da towel  yayinda hannunsa ke rike da wani karamin white towel yana goge sansar  jikinsa ,cike da karuwanci  tabi jikinsa da wani mayataccen kallo sannan ta tsurawa  kan  nipple's dinsa  ido  ita tana son su suna  matukar mata  kyau da  ɗaukar hankalinta, lumshe idanunta tayi a daidai lokacin da ya juya mata baya ya ci-gaba da goge jikinsa  muryarsa a sanyaye yace "kwanciyar me kike yi ya kamata  ki tashi ki shirya ki wuce "?
"Anan zan kwana ta bashi amsa tana gyara kwancinyarta  a fusace ya juyo yana mata wani irin kallo   "ki tashi ki kama gabanki ya fada yana sake juya mata baya  ya ɗauki body lotion yana shafawa jikinsa bayan ya gama ya dauki kwalban   turare ya shiga fesawa jikinsa  da bayan kunneshi ,ita kuwa murmushi tayi tace "haba adnan wai me yasa kake min haka  ?"me yasa kake son guje min?
" kaki ka tsaya mu fahimci juna  kullum da zarar mun gama sex ka dinga Allah Allah na barka  , nifa  har ga Allah nake sonka kuma da aure " ta karasa maganar kamar zata yi kuka "

Shiru yayi mata  yaki cewa komai ya cigaba da abinda yake ta sauko daga kan gadon ta tsaya a bayansa har lokacin babu komai sanye  ajikinta tana kokarin haɗe jikinta da nashi
  ta kai hannunta jikinsa tana kokarin kifesu a qirjinshi dan murza kan nipple's dinsa yayi saurin juyowa tare da tsareta da kyawawan idanunshi yana mata gargadin abinda take son aikatawa bata damu da irin kallon da yake mata ba ta kai yatsanta kan nipple's dinsa zata soma zagayewa taji  ya  ɗauketa da wasu maruka guda biyu ajere tasa tasa  ..
Saurin dafe kuncinta tayi  tana  fidda numfashi da kyar gabad'aya marin ya dimautata ya  gigiceta da kyar ta samu ta sauke numfashi da karfin gaske idanunta na kanshi  "minti biyu kawai na baki ki tattara abinda kika san naki ne a dakin nan  ki bar min gida kar na sake ganin kafafunki  ya  karasa  maganar a fusace sannan ya soma daga zara zaran yatsun kafafunsa ya isa gaban wordrobe dinsa ya bude  ciro wasu kananan  kaya bakake wando masu taushi da kyau    ya soma shirya kanshi.

jikinta a sanyaye ta dauki rigarta ta saka tana kallonsa har ya gama shirinsa tsaf   bandir din yan dubu dubu guda biyar taga  ya dauko ya watsa mata "kije dan Allah ki bar rayuwata bana son damuwa idan ina bukatarki zan nemeki da kaina "naji zan tafi amman dan Allah ka dinga  ɗaukar   kirana .."
  "Bazan miki alkawari ba saboda ina da abubuwan yi idan bukatar ɗauka yayi zanyi  "bata ce masa uffan ba ta dauki jakarta batare da ta dauki kudin ba  a dan zafafe yace "kudin fa"?
Ta juyo kamar zatayi kuka  "bana bukatar su dan nafi bukatarka dasu ..."tana gama fadar haka ta sake juyowa idanunta cike da ruwan hawaye, ta bude kofar d'akin zata fita  hannunsa ya kai ya shako wuyanta ya dawo daita cikin  bala'in da tashin hankali ya amshi jakar hannunta ya kwashe dukan kudin ya zuba mata  cikin jakarta , tayi shiru kawai tana kallonsa kamar ta daura hannunta bisa kanta ta fashe da kuka , yanayinta ya bashi tausayi  sosai kamar ya lalla'bata su rabu lafiya  sai kuma yaga hakan bai dace ba kamar wata dama zai sake bata.."

Muryarta a raunane tace  "meye laifina adnan da kake wulakantani  ? "shin laifi ne dan zuciyata ta soka ?  ta k'arasa maganar wasu zafafan hawaye na zubowa a saman face d'inta, girgiza  mata kai yayi yana furzar da iska sannan ya motsa lip's d'insa a hankali  "laifinki daya  zahra da kike takurawa rayuwata alhalin kinsan ni din mutun ne da bana son damuwa "  sannan baki da wani sauran mutunci da darajan da zan soki zahra ,gaskiya ɗaya ce wallahi zahra bana sonki koda kuwa  akwai budget din soyayya arayuwata bare babu  mafi mahimmanci abu arayuwata shine  ahlina  "
ba iya soyayya kawai zata iya da zuciyar jaguwa ba Bare lalacewata bata kai na amincewa auren mace irinki ba ,"zahra da ƙaruwar gida da karuwar waje akwai bambamci idan aure kike bukata me zai hana ki koma gaban iyayenki ki tuba Allah zai duba lamarinki ya baki wanda yafini wanda zai soki da d'aukacin rayuwarsa  amman batu na soyayya ko aure tsakanin zahra da adnan babu....."
"To mu'amular fa ?"idan bazaka aureni ba ka barni na rayuwa da kai shi kadai zai sanyaya zuciyata sannan zai sa na  dangwama cikin farinciki "shima bazan yi alkawari ba dan ita kanta zinar ina son na daina shiyasa kika ga ina gujewa haduwata dake ,ta durkushe a gabansa "karka min haka adnan karka juya min baya ka  taimakeni ka taimaki rayuwata wallahi bazan iya rayuwa babu kake "enough Zahra ya fada a tsawace "Haba me kike son nace miki kinga tashi tashi dan Allah yadda taga ya soma birkicewa yasa ta tashi da sauri tana fuskantar shi ido cikin ido yake kallonta"Ni ne na samo having sex dake ? "Ko ni ne na baki ticket din fitowa yawon duniya ?"ko ni nace dole sai kin soni ? yayi mata duka a lokaci tayi shiru hawaye na gangaro mata "kin yi shiru ki bude baki ki bani amsa yayi maganar yana zaro mata ido tayi saurin girgiza masa kai"okay tunda kinsan  bani bane me yasa zaki ce kar na miki haka kar na juya miki baya ?"daga yau Karki sake tunkarata da batun soyayya bare wani aure okay ?"oya out idan kika sake tunkarata sai ballaki idiot Kawai ..

Tana gama jin abinda ya faɗa  ta juya da sauri ta fito daga d'akin tana goge hawayen idanunta a bakin kofar suka kusan ci karo da Anas ,da sauri ta wuce shi ya biyo bayanta yana  kiranta "zahra! zahra !! amman ina  taki tsayawa ta wuce  tana kuka  yayi saurin biyota ya sha  gabanta "plz Ki tsaya ki saurareni menene? " me yayi miki kike kuka plz tell me ko akwai abinda zan iya yi " muryata cike da kuka tace  "tabbas nayi kuskuren  afkawa cikin soyayyar adnan "
"Wani irin mutun ne shi    nayi iyakar kokarina akan soyayyarsa amman sam yaki fahimtata na rasa yadda zanyi adnan ya fahimci irin matsanancin soyayyar da nake masa gabad'aya zuciyata ta kasa hakura dashi ka faɗa min me ya kamata nayi  ya aure ni ? duk Sanda zamu kasance tare  sai ɓacin rai ya biyo baya" why !why!! ? Ka faɗa min abinda ya kamata nayi ?"Ni kaina   babu wannan tsarin arayuwata ban shiryawa aure a yanzu ba amma  na rasa dalilin da yasa  na nacewa mutumin da bai ɗauki kowa da mahimmci ba ? gabadaya ta fita haiyacinta sai maganganu take faɗa masu taba zuciya "kiyi hakuri muje muyi magana aciki "babu inda zani dan nasan kona koma wani sabon bakinciki zai kunsa min , kawai ka barni na tafi abuna  ajiyar zuciya ya sauke tare da matsawa gefe ya bata hanya dan ta wuce kamar yadda ta bukata dan shima yasan ko ya maidaita sabon bala'i za'a yi a hankali ya juyo ya nufa cikin gidan
Yana ƙoƙarin tura kofar dakin jaguwa ya  fito yana ciccin magani tamkar wani jinin saurata.

"me ka yiwa yarinyar mutane jaguwa  ?',me tace nayi mata yayi masa tambayar atakaice , cikin natsuwa ya raba ta grfenshi yayi gaba "ko bata faɗa min  ba nasan kayi mata wani abu shiyasa ta fita cikin fushi da ɓacin rai  dan Allah ka dinga sausauta   yarinyar nan tana bala'in qaunarka "kace mata daga yau  ta daina son adnan  dan babu   wani amfani da zai mata ya karasa maganar yana ci-gaba  tafiya " Anas ya biyosa  da sauri  "na rasa dalilinka nakin yarinyar  nan bayan irinsu ne kawai zasu iya rayuwar aure  da irinmu, ko kana tunanin akwai wata mace mai mutunci da daraja da zata iya da irin rayuwar da muke ?

Jaguwa ya tsaya cak tare da juyowa ya fuskanci Anas sannan ya  zuba hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa ya zubawa Anas idanunshi yana kare masa kallo tsaf  "kai kake ganin haka amman lalacewata bata kai na auri mace kamar zahra ba, karka manta inda muka tsinto   zahra da irin rayuwar da take   duk gidan rawan fela   kowa yasan wacece Zahra,  nasan nima  mai tarin zunubi ne agurin Allah  amman ta nemi mijinta a gaba  adnan baya sonta kuma bazai taba sonta a rayuwarsa ba kai gabad'aya ma babu wata soyayya a tsarin rayuwata  "

"Wannan kuma karya ne dan da alamun ma a yanzu zuciyarka  ta kamu da soyayyar diyar Minister of health dake cikin gidan nan  "dariya jaguwa  yayi wanda ya bayyana tsantsar kyawunsa sannan   a hankali ya sake gyara tsayuwarsa ,fuskarsa cike da mamakin jin furucin Anas  ",this is rubbish anas what are you try to say ? wannan maganar  naka ba gaskiya bane abinda nake son ka sani zuciyar Adnan amad tayi nisa a kiyyaya  babu wani mutun mai darajan da zan so kamar ahlina idan ma soyayya ce wannan yarinyar tayi min  karama Anas , kuma idan duk duniya zasu taru akan na sota itama  bazan sota ba "ya wuce ta gefensa ya soma tafiya da baya baya  kamshin turarensa na tashi ya nufi dakin da tanweer take ya daura hannunsa akan handle din kofar ya murd'a ya shiga dakin Anas bai daina kallonsa ba har ya karasa shigewa dakin ya maida kofar ya rufe .."

Cikin natsuwa yake  kallon inda  zaune  take akan kujera ,juyar da kanta gefe tayi kamar bata ganshi ba , ya jingina jikinsa da bango dakin  yana Kallonta ,sosai yaga ta rame akan ranar daya d'aukota sai dai fuskarta tana nan da kyawunta ..."
ganin taki kallon inda yake yasa shi takowa  a hankali ya tsaya a gabanta shiru taki dagowa ta kalleshi ya cire hannunsa daya  acikin aljihun wandonsa tare da d'ago ha'barta ya tsura ma kwayar idanunta nashi idon yana Kallonta , da ido yayi mata alamar taci abinci ? bata fuska tayi cikin son nuna masa  abinda yake son sani bai shafesa ba, furzar da iska yayi yana tabe bakinsa sannan ya cire hannunsa ya buɗe kwanon tangaran din  dake ajiye akan table ,abincin na nan kamar yadda akawo shi   ya waigo ya kalli inda take a hankali ya maida murfin ya rufe "you don't eat ?why don't you eat?" I don't want to eat food in this situation "why ? ya tambayeta idanunshi na kanta kamar zai had'iyeta  "I'm not hungry"bakya jin yunwa ? ya sake tambaya  ta yatsina fuska cike da shagwa'ba.

"yarinya  idan kika sake ɗaukar lokaci baki ci abinci ba zaki mutu just for nothing yayi maganar tare da zama a bakin gado ya fuskanceta "tun safe  rabon da ki sanyawa cikinki wani abu hakan fa babu kyau "it's not good for your health okay ? Ya kamata kici wani abu saboda taimakawa rayuwarki a matsayinki na likita kinsan yunwa na daya daga cikin abinda ke saurin kashe dan adam ko ba haka ba "?

shiru tayi taki cewa komai sannan taki kallon inda yake "you need to eat my friend  so that you can survive ya karasa maganar a tsawace "go and eat I'm to talking to you ..........."
take jikinta ya dauki rawa gabanta ya shiga faduwa a hankali ta  sake juya masa baya taki bin umarninsa  kamar yadda ya bukata  tana sheshekan kuka , gabad'aya hankalinta ya karkata zuwa gida tana son ganin iyayenta bata ga amfanin zamanta  tare dashi ba alhalin jikinta na bata iyayenta na can cikin tashin hankali, wasu hawaye masu zafi suka gangaro mata a hankali ya sausauta muryarsa cikin tsigar rarrashi  "you need to eat so that you can have strength because you don't know the task ahead right? you need food to live plz  duk yadda yayi mata magana da tsigar rarrashi amman sam taki ci sannan taki magana  sai kuka take tana ciza lip's dinta .
a can bangaren hajiya Zainab kuwa itama kukan take saboda jikinta na bata diyarta na cikin damuwa ,ta mike daga zaune da take ta shiga zagaye d'akinta zuwa babban parlou'n gidan  ta wuce matar danuwan mijinta  da suka kawo musu ziyara tare da yarinyar su zuwa   haraban gidan tana baza idanunta gani take kamar zata ga diyarta daga sama matar danuwan Alh Abubakar da suke uwa daya uba daya ta biyo bayanta ta rungumeta ajikinta  "kiyi hakuri inshallahu za'a ganta "jikina na bani tanweer tana cikin damuwa Allah kasa basu ma yarinyata wani abu me suke bukata daga garemu su kira mu su tambayi duk abinda suke so wallahi a shirye nake zan mallaka musu duk abinda nake dashi muddin zasu dawo min da farincikina ..."

Tunda Hajiya zainab ta fito  hankalin minister ya rabu gida biyu  wani bangaren ya koma gurinta yayinda wani bangaren ke gurin d'an'uwansa  da suke tare "Haba Abubakar taya irin wannan babban abun zaifaru ace bazaku sanar damu ba 'yan uwa? Wannan wace irin rayuwace ta rashin zumunci kuka zab'a kai da zainab ?". Matashin Dattijon yayi maganar cike da b'acin rai yana binsu da kallo,
kallo d'aya zaka ma dattijon matashin kaga kamanni sosai da suke da Alh.Abubakar sai dai Ko a fuska zaka fahimci ya girmemishi.
"Kayi hakuri yaya Walh tallahi kaga dagani har zainab bama cikin hayyacinmu tunda wannan  tashi hankalin ya faru, gaba d'aya Zainab bataci baresha ni kaina Walh bazan iya cema when last nasa abu a cikin nan nawa ba" Alh.Abubakar yayi maganar cike da damuwa wacce kallo d'aya zaka fahimci damuwa a kan fuskarshi me tsanani dan duk yayi baki ya rame kamar ba Minister of Health ba.
"Allah sarki Ubangiji Allah ya fito mana da ita lafiya dan walh tashin hankali ya zama dole. To wai basu Kuma kiranku Ko suna buk'atar k'arin kud'iba?". Yayi maganar cike da tausayin d'an uwansa.
Girgiza mishi kai Alh.Abubakar yayi. "Kod'aya walh! Ni da zasu kira Ko duka dukiyata ce saina had'a daita su dawo da munda Tanweer". Ya k'arasa maganar cikin rawar murya wacce ke k'ara fitar da damuwar shi. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un". Alh.Usman yayi maganar cike da tausayawa nan ya shiga lallashin Kanin nasa tilo musamman ya jima bai ganshi ba kasancewar shi a Arewa yake da zama kaduna State da iyalansa hakan yasa bai sama labari ba sai da aka kwana biyu, yaji ciwo amma yanzu jin zantukan d'an uwansa yasa yaji jikinsa ya mai sanyi gaba d'aya a tare suka koma cikin parlou'n inda diyar Alh Usman rukkaya ke kwance akan kujera mai zaman mutun uku .

Numfashi  jaguwa ya furzar ya mike tsaye zai bar daki  "ka maidani gidanmu plz yaji sautin muryarta cikin sanyi  ya doki dodon kunnenshi  "nasan ka taimaka min ,ka karasa taimakon  ta hanyar maidani ga iyayena "idan kina bukatar zuwa gida ki ci abinci kina gama ci ko second biyu ba zaki kara a cikin gidan nan  ba zan maidake gaban iyayenki "yana gama fadar haka yaga ta matso da kujera da take zaune  ta bude kwanon abinci daya fara yin sanyi ta soma tsukura  ...." wayarsa ce ta dauki qara sauti ya ciro wayar daga cikin aljihunsa yana duba screen din wayar sunan Alh Tahir ya gani yana yawo ya  lumshe idanunshi sannan ya dauka batare da yayi magana ba "cike da in inna alh Tahir ya soma magana "har yanzu baka dawo da yarinyar nan ba gashi akwai next taget dina akanta ya kamata zuwa yanzu kasan yadda zakayi ka dawo daita plz "doka ce ko iko kake son min ? ya furta  masa haka a natse wanda zaka ɗauka maganar ba daga bakinsa ya fito ba sai agurin alhaji Tahir kamar saukar aradu yaji maganar .

saurin girgiza kai Alh Tahir yayi kamar yana gabansa "no babu ko daya naga dai ya kamata ne a dawo daita haka nan "to baza'a dawo daita ba kayi duk  abinda zakayi ya ja tsaki yayi disconneting din kiran ya maida wayar cikin aljihunsa tare da zura hannunwansa ciki ya juya "ki tabbatar da kin ciye abinci nan  tass kin shanye  driks da ruwa ke everything dake gurin make sure kin gama dashi idan kina son barin gidan nan  ", Allah bazan iya cinyewa ba yanzu ma da kyar nake tura wa ",Karki yi kiga abinda zai faru "ya karasa maganar yana barin dakin kai tsaye bangaren daya tanada domin shakatawa ya nufa a can ya iske abokansa da yaransa suna shaye shaye , masu shan wiwi nayi masu shan win nayi, duk sun cika gurin da hayaniya da hayaki suna  ganinsa suka hau sara masa suna masa  kirari gutun wiwin dake rike a hannun jubi ya amsa ya ɗan zuka yana fitar da hayaki ta hancinsa da bakinsa sannan ya  fita ta kofar baya yana tunanin mugun hali irin na Alh Tahir ko me zai yiwa ƙaramar yarinya kamar wannan gashi kuma shi din aminin mahaifinta ne?
Kusan minti goma yana tunanin agurin "

*****

"Wai Ibrahim kana so ka kashe kanka ne akan mace". Momynsa tayi maganar cike b'acin rai wanda ke had'e da tsantsar damuwar halin da d'anta ke ciki. "Momy I can't live without Tan, ta riga ta zama rayuwa ta, inda abunda nakeso bai wuce Tanweer ba Mo...". "Dakata!". Ta katse shi ta hanyar daga masa hannu da tare da mai tsawa. "Ibrahim bazan taba son ka rasa ranka akanta  ba duk da nima ina matukar kaunarta saboda irin son da kake mata ,but at least ka duba lamarina  kai kad'ane d'ana taya zanso akan wata 'ya mace wani abu ya sameka ?".
Tayi maganar tana kallon Ibrahim wanda tunda ta soma maganar idanunsa ke runtse.
"Ibrahim!". Ta kira sunansa cikin wani irin yanayi wanda bai taba saninta dashi a rayuwarsa ba" gaba daya Inaso kayi hakuri da Tanweer!". Ta karashe maganar cikin dakiya tana kallonsa ganin yadda har ya samu courage d'in tashi zaune shida tun b'atan Tanweer bata ganshi a zaune ba.

"Mom!". Ya fada cikin daga murya tare da gyara zamansa yana binta da wani irin  kallo idanunsa ko kiftawa ba yayi, already ya gama zazzarosu waje gaba daya what !". Yayi maganar  yana kallonta kamar bai fahimci abunda yake faruwa ba musamman furucinta. "Mom!". Ya Kuma fad'a yana kallonta cike da mamakin furucinta."Haba Momy, taya zakiyi wannan furucin na rabu  da Tanweer bacin kinfi kowa sanin irin son da nake mata? How could you utter such words uhm?!". Ya jero mata tambayoyin cike da damuwa lumshe idanu tayi tare da fadad'a murmushinta tana shafa sumar kanshi.

"Ibrahim kenan,". Ta fada tana kad'a kanta ,sannan ta  tashi ta soma taku yana binta da koda'dd'un idanunsa da suka sha wahala saboda rashin ganin abincin su  Tan, har ta Kai k'ofa sai Kuma ta juyo tayi murmushi me sauti tana kallonsa  lokaci guda Kuma fara'a dake tattare da fuskarta ya d'auke nan take bacin rai ya maye gurbinshi."Hmm! Yaro yarone nan gaba zaka gane da kanka nasan dalilin da yasa nace ka hakura da yarinyar nan ". Tana fad'in haka ta fice ta barshi zaune zuciyarsa cike da tunanin zantukan ta musamman bacin rai daya hango cikin idannun Momyn nasa wanda kusan ya jima baiga hakan tattare da fuskarta ba. Wayarsa da ta soma ruri ne ya katse mishi tunanin daya shiga ya soma zurfi, hannunsa na rawa ya kai hannunsa ganin me kiran, da sauri ya manna wayar a kunnensa banajin me ake fada masa a can d'aya bangaren naga ya tashi da sauri. "What?!". Ya furta da d'an k'arfi tare da runtse jajayen idanunsa  ya bude su tuni suka k'ara rinewa tare da k'ara tiruwa zuwa ja sosai kamar jan gauta. "Alright I am coming". Ya fad'a da sauri tare da wullar da wayar kan bed d'insa.
Yunku'rin k'arasawa wardrobe yayi amma me wani irin jirine ya kwasheshi da sauri yasa hannayensa akansa saboda wani irin nauyi da rada'dd'i da suke masa, yana ciza pink lips d'insa kanana wanda suka sauya colour saboda azabar ciwo a d'an bushe   "Ya Salam I.B!". Dadynsa ya furta wanda ya bud'e ko'farsa kenan a daidai lokacin da I.B ke ko'k'arin k'arasawa k'as, cike da matsanancin tashin hankali Alh.Tahir ya k'arasa ya tallafoshi zuwa jikinsa inda yak'arasa sauke su kan bed d'in. "Ta...Ta...Tan! Da....". Karasa kulle idanunsa yayi hankalin Alh.Tahir ya tashi a wannan lokacin banda ihun kiran sunan matarsa cikin tashin hankali babu abinda yake  dan ya fara tsorata da yanayin dan nasa .."
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

PAID BOOK

 WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686
alert  domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu  a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

🅿️12

......Cike  da   dakiyar    zuciya   alqali   ya   cigaba  da   bin  bayan motar   jaguwa    land  cruiser   prador   yana sake   neman   layin  IB  domin  bashi  direction  din  Inda  yake a daidai wannan   lokacin   sai  dai  Kiran  na   shiga   ba'a  d'auka   ,ya   kira  ya  kai sau   goma    bai    d'auka   ba  wanda a  wannan    lokacin   nazifi  da  alhj  Tahir  da    hjy    baseera    ne  tsaye a kanshi     nazifi   na  qakokarin   bashi  taimakon   gaugauwa ,   haushi  ya  kama   alqali   ya   ciza   gefen  lips dinsa   yana    dukan    sitiyarin  motarsa  "oh  my goodness   ko   me  yasa  yaki  d'aukar  Kiran yanzu bayan  bamu  gama  wayar  ba ya  ajiye   ? yayiwa   kanshi   tambaya  yana  d'an  rage  gudun  motarsa   dan  kar  jaguwa  ya  fahimci su yake  bi  ."

yayinda   a hankali  motar  jaguwa  ke  sharara  gudu  akan  titin  onipan a natse    ya  d'an  juyo  gefen  da  tanweer   ke   zaune   shiru   sanye  da   doguwar   riga   pinky  colour  ta  yane kanta   da 

Please Login or Register in order to submit comment