Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shirginsa.

"Owk a dawo Lafiya Allah Ubangiji ya tsare". Ta fada tare da mai murmushi.
"Ameen Umma bye". Ya fada lokacin daya dau suitcase din nashi ya fita ya barta zaune tana cigaba da k'okarin yadda  Ibrahim zai yarda yaci abinci tare da kwantar masa da hankali .
Yana fita babban falo ya tunkara jin muryar Abban Ibrahim a falon da alama waya yake, da sallama ya shiga cikin falon. Kallonsa Alh.Tahir yayi tare da saurin magana. " can I call you later?". Ya fada cikin sauri tare da ajiye wayar yana kallon Nazifi.
"Abb...".
"Muje muje waje Nazifi we need to talk ". Alh.Tahir Ya fada lokacin da yayi gaba nazifi na binsa a baya cike da matsanancin damuwa. "Yauwa a nan zamu iya magana". Alh.Tahir yayi maganar yana kallon fuskar nazifi wacce ke nuna damuwa.
"Haba Nazifi, Me yasa kake damun kanka bayan na fad'a maka so nake kawai ka keeping dinshi na d'an day's har na samu abunda nake kallo ya yu...". "Amma Abba me kake nema wanda zaisa kasa nayi ta kashe ma Ibrahim jiki da samai zazzabi haka bayan kafi kowa sanin yanzu ne yake buk'atar jarumtarsa wajen nemo Tan....".
"Dakata Nazifi!". Alh. Tahir ya fad'a cikin b'acin rai tare da d'aga mishi hannu.

"Who is Ibrahim to you? In tambayeka ma". Yayi maganar cikin bacin rai. Cikin girmamawa Nazifi yayi k'asa da kansa.
"Tambayarka nake!". Ya fad'a da d'an k'arfi saboda damuwa.
"Abokina ne". Ya bashi amsa batare da ya kallesa ba. "Good naji dad'i da kasan wannan, so stay within your limits kaima you are like a son to me karkayi abunda zai b'ata zumuncina da kai da iyayen ka, I know
What is good and bad for Ibrahim karka damu bazan cutar da d'ana ba shi kad'ai gareni nima kamar yadda Tanweer take gun iyayen ta na tabbatar babu abunda zai sameta she will be back kaji?"ya karasa maganar cikin sanyin murya .
"To Abba, ni zan tafi aiki". Ya fad'a lokacin daya d'au hanya.
"Owk sai ka dawo my son god bless you for me zaka ji alert kaji ko". "To". Abunda Nazifi Ya fada kenan ya fice cike da mamakin halin Alh.Tahir ya rasa dalilinsa na sa d'ansa a wannan halin gaba d'aya da harara Alh.Tahir yabi bayan Nazifi daga bisani ya koma cikin gida abunsa ya cigaba da wayarsa ...

***
ba'a dauki  cikakken minti shabiyar   ba  eku  ya  karaso yana knwoking din kofar a daidai lokacin daya fito daga bathroom kugunsa daure da towel ya amsa da" Yes yana  dakatar dashi sai daya goge jikinsa ya karasa jikin wordrobe dinsa ya zaro jallabiya  milk colour  design  mai shegen kyau da santsi ya zira ajikinsa ya fesa turare mai sanyin kanshi  sannan  ya karaso bakin kofar ya bude ,ya  amshi farar  laida  da flaks din dake rike a hanun eku ya sallameahi ya murd'a kofar dakin da take  ya  shiga bakinsa ɗauke da sallama ,tana tsaye a   lokacin sanye   da daya daga cikin  dogayen rugunan da yasa aka siyo mata, kallo daya yayi mata ya dauke kanshi daga gareta  saboda wani irin abu daya ji ya tsinkari ilahirin jikinsa mai kama da sukar allura   , ya karasa shigowa  tamkar  bashi ne   ya dawo mata  tamkar  bawa ba a dazu ko wani mayunwacin zaki ,ya balain hade ransa kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa tun daya shigo hankalinta da idanunta tatare da natsuwarta suka koma  kansa ta kasa dauke idanunta akanshi  ina ma zai aureta ....
tayi kewar iyayenta sosai sai dai bata son rabuwa dashi, tuna sauran awani kadan ya rage ya sadata da gidansu kamar yadda yace  yasa hankalinta ya sake tashi  "why will you disturb yourself over him? Uhm! kika sani ko yana da mata shiyasa yaki amincewa dake, why bother your mind? Why?!".  zuciyarta ta jiho mata wannan tmbyr take idanunta yayi raurau ya cicciko da ruwan hawaye , sosai take kallonsa tana jin wani irin sonshi nabin lugu da sako na gangar jikinta  ,ta bala'in kafeshi da  idanunta , ya ɗan dago ya kalli inda take batare da yayi magana ba ya ajiye flaks da laidar hannunsa "menene kuma kika  wani tsareni da idanu?  yayi maganar cikin rashin damuwa "a ranta tace kaji da munafurci kana wani ciccin magani like he is not the person that try to...". Da sauri ta katse tunanin. " ga abincin nan ki tabbatar da kin ci nan da awa biyu zaki koma hannun iyayenki ta yatsin fuska tana turo masa karamin bakinta cike da shagwa'ba tace "ni ni babu abinda zanci sannan babu inda zani, I won't go anywhere I will stay here!".
niyyar fita yake Jin abinda tace yasa  dole ya dawo ya zauna wanda zuwa  lokacin itama ta zauna a gefen gado tana fuskantarshi ya kafeta da kyawawan idanunshi yana kallonta a tsanake, bata fuska tayi tace "meye na wani tsareni da ido kamar zaka cinyeni kana tunanin maidani batare da nasan matsayina ba, ni dole sai ka fada min matsayina kafin! Are you marrying me or not?!".
"ba ke kike da wannan ikon ba ganin damana ne ko akasin haka yayi maganar a dake yana mikewa  ya karasa ya dauko cup da spoon  ya dauraye wannan tsarin na cikin tsarinsa da  dokokinsa tun bai san zai taka matsayin da yake a yanzu ba ,ya dawo inda take tamkar an dasata ya hada mata coffer ya tsiyaya zuma a ciki ya juya ya  mika mata "ki sha karki 'bata min lokaci dan lokacin sallah ya karato dole ta Kai hannu ta amsa  saboda  yadda ya  hade rai ta soma kurba kadan kadan tana kallonsa , ya janyo farar laida ya buɗe ya ciro takeway ya buɗe ya janyo karamar stood gabanta ya ajiye tayi murmushin karfin hali tace " laila kamar wata matarka gsky i will love to be tha...". "shut up I don't want hear ....
Sai kuma yayi shiru ya kasa karasa maganar  "ki daina kusanta kanki dani zaki sa zuciyarki cikin rudani  da wahala  dan I can't be that person".

shiru ne ya biyo baya kafin daga baya yaja numfashi ya  cigaba da motsa lip's dinsa  "ina ke ina ni  ? "da kinsan koni waye na tabbatar da ba zaki yi kwadayin kasancewa dani ba har kiyi muradin son zamowa mata agareni , nasan kyawuna ne ya rudeki ko ?".

tayi saurin hadiye ruwan shayin data kurba tana girgiza masa kai  "no just like that I fa...".
"Shiii! karki bata bakinki duk abinda zaki fada bazan taɓa yarda ba dan dubunki sun fada Kuma ta nan yake bi  ya fita ta nan ya nuna kunnenshi ,  ta narkar da fuska kamar zata yi kuka " ka fahimceni dan Allah give me chance to sho...". "nace bamu dace ba sam! Let's this be the first and last" ya kasara mgnr yana tsura mata idanunsa dake bugar mata da zuciya"Anyway daga yau basai kin Kuma ganina ba".
yayi mgnr  a fusace "ki ci abinci kawai , girgiza masa  kai tayi "ka kwantar da hankalinka wallahi da zuciya daya nake son zama abokiyar rayuwarka ,zan zauna da Kai tsakani da Allah, baxan damu da wani abu naka ba idan kuma kana da mata ne yasa kaki   amincewa dani ka fada min bazan so na shiga tsakanin ma'aurata ba? ".  ta karasa maganar kmr zatayi kuka cike da hassala ya katseta  "just eat!

yana zaune ta soma tsakuran abinci kamar bata son ci  har sanda aka soma Kiran  sallah  magrib ,ya  mike tsam ya shiga bayin dake manne da dakin bai wani dauki lokaci ba ya sake bayyana a parlour a kallon da yayi mata ya fahimci gbdy attention dinta yana garesa "ki tabbatar da kin cinye abincin da shirin barin gidan  nan  kafin na dawo daga masallaci". ya  fita daga d'akin yana taku cikin isa da izza kamar wani jinin sarauta tabi bayansa da kallo har ya bacewa idanunta "ya rabbi Allah ! You alone knows that I am not attracted to him for his handsome face, haka kawai  na tsinci kaina Allah ka kawo min ɗauki ya fahimceni before is too late".   ta lumshe idanunta wasu siraran hawaye suka gangaro mata  yana fita ta saki spoon din hannunta  ..

Kai  tsaye matsallaci ya nufa da kafafunsa yana tafiya kamar baya son taka kasa yayinda mutane unguwan suke gaisheshi cike da girkamawa yana amsa musu a mutunce  lokacin daya karaso cikin matsallacin tuni sawun gaba dana biyu ya cika bai ji dadin haka ba  yabi sawu na uku cike da ladabi ga ubangijinsa yake tada kabbara  bashi ya fito daga massalacin ba  sai da akayi isha'i yana fitowa daga masallaci Kai tsaye gida ya dawo ya sameta kwance cikin bargo  idanunta a lumshe "ke ki tashi muje kou gabanta ne yayi mummunar faduwa  har ga Allah tana son komawa gida  ga iyayenta dan tasan suna can cikin tashin hankali most especially mum  dinta sai dai  bata son barinsa dan tasan ba lallai ta sake had'uwa dashi ba kamar yadda ya furta , akwana  daya datayi dashi ta fahimci shi din mutukin kirki ne wanda samun irinsu ke da wuya "ki tashi muje there is no time to waste".
tana jinsa tayi shiru ta sake  lafewa  haɗe da kamkame jikinta ....

DARLING'S💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

    WRITING BY
*BAGUDO& MIMI'S QUEEN*
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

🅿️07

......Kusa daita ya ɗan duka  yana  kallonta ,a hankali yaji ta kamo yatsun  hannunsa cikin nata tana murzawa bai san sanda   ya  zauna a gefenta yana sauke numfashi tare  da tankwashe ƙafarsa  ɗaya yayinda d'ayar kafar ke kan tayis yana jijigawa , matso da kanta tayi ta d'aura  a saman  cinyarsa, idanunta a lumshe take jin yadda idanunshi ke yawo a fuskarta ,motsa hannunsa yayi da niyyar zarewa daga cikin nata saboda yanayinsa daya ji yana sauyawa, ta bud'e idanunta  tar akanshi Ido cikin ido suke kallon juna lumshe idanunshi yayi na second biyu sannan ya bud'esu akanta ya mik'e  dan baya son kusancinsu tare "me yasa baki jin magana ?"

  cikin sanyi murya tace " me nayi maka ?" tana janyo hannusa ya rankwafo jikinta bakinsa ya sauka a daidai kunnenta hucin numfashinsa  yasa ta runtse idanunta da sauri.  "Ki tashi muje na maidake gidan ku" yayi mgnr yana sakin numfashi haɗe da ciza gefen kunnenta  ta saki qara mara sauti tana jin wani iri a gabad'aya ilahirin  jikinta ."No! bance maka bazan tafi gida  ba but atleast na.....
"Shiii!". ya katseta ta hanyar d'aura yatsansa a kan lip's d'inta,  shiru sukayi gbdy zuciyarsu na bugawa da karfi  "ka hanzarta maida yarinyar nan  tun bata zame maka kaska ba'. zuciyarsa ta faɗa masa haka, mik'ewa ya sake yi  yana kamo hannunta "Ke! tashi muje Karki bata min lokaci ". banza tayi masa tana  yatsina fuska "bana son Ki sake min mutsu  akan komai " yayi maganar yana matse yatsun  hannunta cikin nashi yana ko'k'arin sauko dai ta, Cikin rashin sani ta fad'o jikinsa tare dan sakin  k'ara  "Ahm!". Idannunta rufe, yadda ta runtse su yasa ya k'ura mata idanunsa masu matukar  kyan gaske, dan kanne d'aya idon tayi ta bud'e sai tayi saurin mayarwa  ta rufe hakan ya bashi murmushin da  bai shirya yiba me sauti jin haka yasa  tayi saurin bud'e idannunta akansa.

Murmushin  ya k'ara mishi kyau sosai kamar kar ya daina  , d'an k'ara ware idanunta tayi tana kallonsa wanda har lokacin fuskarsa na d'auke da murmushin. Ko'k'arin gyara tsayuwarta ya soma yi , Tanweer kuwa da sauri ta kai ma bakinsa cafka tamai peck a lips d'insa , ware idannunsa yayi sosai  yana kallonta cike da mamaki  'Do want to kill me wannan yarinya'. Ya furta a ransa Tan kuwa murmushi take masa, sake kai mai Cafka tayi a karo na biyu sai dai wannan karon taji ya bude 'yan lip's dinsa inda ya soma kokarin kissing d'inta,ya  cafko laulausan harshenta cikin nasa kamshi sweet taji mai kamshi lemun ,ware idannunta tayi ganin kallon da yake mata yasa tayi saurin runtse idanunta jikinta na dan rawa saboda wannan shine karo na farko a rayuwa  data yi  kokarin shan bakin wani nmj .

Tsura mata idanunshi yayi tare da d'an murmushi, yana jin yadda take jujjuya harshenta da sweet din dake  cikin bakinsa take zuciyarsa ta dasa masa  ayar tambaya akanta. 'anya kuwa yarinyar nan  cikakkiyar buduwar ce ? anya kuwa ba watsatsiba ce take neman kawowa zuciyarsa farmaki? to idan itace kai meye ?Me ye marabinka daita? " wata killa ma ta fika tunda bata aikata abinda kake .......
Kasa k'arasa zancen zucin nasa yayi saboda yadda take bin kunnensa da lallausan yatsunta tuni ya kasa jure abinda take masa a hankali ya cafko harshenta yana tsotsa a tare suka shanye sweet din sai ji sukayi sweet din ya kare aiko ta saka masa kukan shagwa'ba. "Wayo! Why?"
Tsura mata ido yayi yana kallonta tare da d'an janyewa, Tanweer banda tab'e baki ba abunda take tana kallonsa. "Ba...ka..kaine ka shanye sweet din byn bai isheni ba". Tayi maganar a shagwab'e kamar zatai kuka. 'bata face  yayi wannan karon ba alamun wasa  yanzu a fuskarsa. "okay tashi muje idan ma dubunsu kike so zan miki guzurinsa ta sauko tana gama saukowa ta rungumeshi a jikinta "i love you Mr.No Name!" I will miss you no name   tsintar kanshi yayi da kasa rabata da jikinsa "Just one day with you but ina jinka tamkar kar mu rabu, is it necessary sai mun rabu?". bakinsa ya kai cikin kunneta yana busa mata  hucin  numfashinsa, lumshe ido tayi "ka barni zuwa gobe plz ban gaji da kasancewa tare da kai ba"ta furta cikin sanyin murya kamar zatai kuka, dan ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta. "ta kowani bangare mahaifinki ya baza mataken tsoro ya damu sosai da rashinki me yasa zaki so zama dani fiye da iyayenki why?"
yay  mata tambayar tare da ko'karin kaucewa.

"I know zasu damu sosai hatta I.B ma zai damu da rashina mutumin da muryata kadai idan bai ji ba a rana  babban tashin hankaline gareshi "
take qirjinsa ya buga zuciyarsa ta shiga rawa  shiru yayi yana ƙoƙarin 'ban'bareta a jikinsa idan bai manta ba shine mutumin da suke waya daita a wancan ranar da tayi accindent "wannan kuma damuwarki ce yayi maganar cike da rashin damuwa , murmushin karfin hali tayi wanda yafi kuka ciwo "mutum mai dakakkiyar zuciya kamarka bai dace ya damu da lamuran mutane ba sai dai acikin kwayar idanunka kadai za'a iya hango tarin tausayi mutane bila'adadin". "Ki daina wasa da zuciyarki da tunaninki  muje kawai". Yayi yunkurin sake  bambareta a jikinsa ,sake   manne masa tayi tana gyara tsayuwarta a jikinsa gabansa na bugawa da matsanancin karfi yayi nasarar  zareta a jikinsa suna fuskantar juna " ki daina bata mana lokaci saboda hakan babu abinda zai janyo sai tarin damuwa dan bazan taɓa sonki ba kuma ki daina sona dan soyayyata babu amfanin da zata miki , sannan daga yau ki sawa ranki  bazaki sake ganin ko mai kama dani ba, kiyi rayuwarki  tare da wanda kika fara zai fiyye miki , ni ba irin  mutumin da zaki yi rayuwa dashi bane"

gabanta ya dinga dokawa da karfin gaske jikinta ya kama rawa bakinta ya kasa furta komai a dalilin  maganarsa  dake  bugar mata da zuciya ,  riko tsintsiya hannuta yayi, yana gaba tana d'aga kafafunta da kyar tana kallon bayansa yayinda wani duhu mai haɗe da juya ya gilma cikin kwayar  idanunta daidai tsikiyar d'aki yaji jikinta ya sake tana kokarin yin baya ya juyo idanunsa ya sauka akanta gbdy yanayinta ya sauya ta dafe daidai goshinta da hannunta daya  cak ya tsaya a lokacin da take  kokarin zubewa kasa yayi saurin tarota jikinsa hankalinsa a matukar tashe gabadaya ya rungumeta , ita kuwa cike da bakinciki take fidda numfashi kusan minti biyar suna tsaye tana rungume ajikinsa tuni hawaye ya wanke  fuskarta, cike da tashin hankali take motsa lip's dinta " muje ka maidani gida kawai   thanks for all the helps tun daga ranar farko da muka hadu har zuwa yantoni daga hannun yan fashi". magana take jikinta na rawa take yanayin jikinta ya sauya daga  dumin zuwa  zazzaɓi mai  zafi, cikin tsoron da bai san yana dashi ba ya matseta gam  ajikinsa yana fidda numfashi tare da lumshe idanunshi,  "ki dawo daidai sai na maidake" ni muje kawai ina son ganin  iyayena, i really want to see them". ta k'arasa maganar tana shirin zubar da hawaye jin numfashinta na kokarin tsayawa ya fara  tafiya  daita cikin sanyin jiki ,ya kwantar daita a gefen gado a hankali  hannunsa daya dafe da byn  kanta, yayinda d'ayan hannun ke   tsarke cikin  nata  ya rankwafo jikinta  "ki natsu plz qirjinta na dokawa tace "dan Allah say you love me ka fad'a min  dan Allah koda itace zata zamo kalmar da zanje karshe daga bakinka ina son ji ...
cike da matsanancin fargaba yace "dan Allah ki bar zancen nan babu wata soyayya a gabana, soyayyata ga kowace mace bata da  wani  amfanin ,bare ke karamar yarinya dake banason zunubin laifina ya shafe ki ,gara duk wani hukunci da zai zo min ya sameni ni kad'ai bazan ta'ba barin zunubina ya shafi kowa ba bare ke plz, dan Allah ki dawo daidai mu tafi dan hankalina bazai taɓa kwanciya  ba idan  na kai ki gidanku cikin wannan yanayin lumshe idanunta tayi numfashinta na tsarkewa heart beat d'inta na k'aruwa akai akai.

A tsanake ya zare hannunsa cikin nata ta sake runtse idanunta gam jikinta na sake ɗaukar zafi  jallabiyar jikinsa ya zare, ya ajiye akan madaidaicin table din dake  gefen  gado, idanunshi na kanta yana zance zuci. 'Allah kada kasa wani abu ya sameta a dalilin wannan shirmen nata na banza ,ban da abunta ma  guda nawa take da zata d'aurawa kanta damuwar  soyayyarsa ?  tayi kankanta da daukar wannan nauyin, matan da suka fita girma da wayewa da komai  fiyye da nata  sun kasa shawo kansa a batu na soyayya bare ita , shi sam babu wannan a ransa "

   Rankwafowa yayi  jikinta tare da tokare hannunsa  da katifa idanunshi na kanta zuciyarsa cike da matsanancin tausayinta duk cikin masu nacin sonshi ita kadai zuciyarsa da gangar jikinsa ta tausayawa ,bai sani ba ko dan ita din yarinya ce mai karancin shekarun da bata wuce autar d'akinsu ba ,hannuta daya ta Kai gefen kanta da taji yana sara mata da karfi  a hankali ta soma  motsa bakinta, matsota ya sake yi dan jin abinda zatace "mr.no name am feeling very dizzy". tayi mgnr tana bude idanunta akan shi eye's into eye's suke kallon kwayar idanun juna "bana gani sosai ta karasa maganar tana kai hannunta kan  damtsen hannunsa ta rike gam jikinta na sake daukar zafi  "Mr.no name!". ta sake  kira sunansa tana lumshe ido "na kasa fahimtar meke damuna kaina ke..."
tayi shiru tana sake rike gefen kanta, cike da sanyi jiki yake binta da idanunshi yana shafa gefen fuskarta har ya kai   hannunsa daidai kunnenta tare da zira yatsansa ɗaya , wani irin zirrrrrrrr taji a  gbdy ilahirin jikinta mai kama da shoking  take jikinta ya ɗauki rawa ganin haka yasa yayi saurin  yin kasa da hannunsa zuwa gefen fuskarta ya cigaba da  shafawa a hankali ta sake Kai hannunta kan damtsen hannunsa tana lumshe ido matso da fuskarsa yayi daidai nata  har karan hancinsa na gugan nata tare da   riko yatsun hannunta ya dunkule guri daya yana kallon kyakkawar fuskarta yana jin yadda bugun zuciyarsa ke karuwa ,numfashi kawai take janyowa tana fitarwa da kyar .

Motsin kwankwasa kofar d'akin yasa ta tsaitsaita numfashinta  ta buɗe idanunta fess tana kokarin kallon kofa shi kuwa har lokacin hannunsa na kan shafa fuskarta haka idanunshi na kan fuskarta ya kasa daukesu "mr.no name, kamar wani yana buga kofa". Ta furta a hankali "karki damu babu Wanda zai shigo d'akin nan sai da izinina tayi shiru "ki yarda dani babu wanda zai shigo hannuwanta duka ta Kai qirjinsa tana yarfesu,  sautin wata murya ce ta doke dodon kunnenta "hey adnan open the door plz, is me". hade da buga kofor da karfi kamar za'a balla a hankali ya dan juyo yana kallon kofar sakamakon jin kuryar zahra "adnan!"..........
ta furta sunan   tana lumshe idanunta  wani irin dad'i taji ya mamayeta atleast she know his name yadda  yake da tsananin kyau haka sunansa ke dadin ....... .

Tsura mata ido yayi saboda jin sunan daga bakinta "sautin mace naji ko matarka ce?!". tayi maganar hankalinta a matukar tashe tana mai sake Kai hannuwanta qirjinsa ta fara turesa ya mike yayinda take kokarin saukowa yayi saurin maidaita "ki kwantar da hankaliki ki kwanta ki dan huta bari naje na dawo sai mu tafi". ya janyo rigarsa ya zira ya nufi kofar  sai ganinta yayi ta mike tana neman hanyar buya yayi saurin riko hannunta "ina  zaki?!"hannunsa tabi da ido  ",ki koma  ki kwanta ki bani minti biyu yanzu zan dawo mu wuce"

  " adnan dan Allah ka bude min kofa mana!". Aka Kuma fad'a daga daya bangaren take jikinta ya kama rawa ta soma zazzare idanu hannunsa  duka yasa ya riko kafadunta ta zaro ido tana  kokarin fixge  jikinta "wayyo Allah tsoro nake ji kar matarka ta ganni, if she see me what will she do nasan! kasheni zatai "yes she will definitely kill me, dan Allah ka boyeni".  tayi mgnr a rud'e sound dinta na tashi tana ko'k'arin buya a jikinsa , hade rai yayi "ke malama ki kwanta nace!".
yayi mgn a tsawace  yana nuna mata katifa cike da sanyin jiki da tsoro tayi taku biyu ta zauna a gefen katifa jikinta na rawa  ya k'arasa jikin kofar ya Kai hannunsa kan handle yaji kofar a kulle gam tsaki yaja "a she a rufe kofar take  shiyasa Zahra ta kasa shigowa" yayi magana a k'asan ransa , murda key yayi  hade da zarewa ya fito yana sauke idanunshi akanta "Kai da waye  a cikin d'akin?!". tayi tambayar kamar wata zararriya tana wani irin huci tamkar mijinta .

"Muje". Ya mata alamu da hannunsa yana nuna mata daya part d'in. Kallonsa tayi cikin zafin rai tabi ta gefensa ta tunkari ko'far da Tanweer take cikin zafin nama yasa hannunsa ya fincikota baya. "Me kake nufi Adnan karuwa ka kawo gidan nan ?". Tayi maganar tare da k'ura mishi ido. "Ba karuwa bace kar....". "Karuwa ce mana" ta sake  furtawa cikin d'aga murya, runtse idannunsa yayi jin tana Kuma had'a Tanweer da mummunar kalmar sosai ranshi ya soma baci.
"Na fada miki ki daina kiranta da wannan mummunar kalmar dan ba ita bace". ya fada cike da bacin rai  yana huci  yayi  cilli da hannunta daya rike , Kallonsa tayi tare da murmushin takaici ta kara yunk'urawa. "Koma wacece wannan karuwa sai na...". Fisgota yayi da karfi  tare da shimfid'a mata wani irin gigitaccen  mari, kan ta dawo hayyacinta ya fisgeta tuni zuwa hanyar da bataso, bai ajiyeta ko Inaba sai wani katon d'aki.
  Cillata yayi gefe ya juya zuciyarsa na masa wani irin zafi. "Adnan!"ta Kira sunansa cikin d'aga murya tana sha gabansa. "Wacece kuke magana? Wace matsiyaciyar yar kar...". Tasssss ya sake  d'auke  kyakyawar fuskarta da wani  gigitaccen mari wanda yafi wanda ya mata a baya, fashewa tayi da wani irin kuka. "Nace ki daina me yasa bakya...". "Yanzu akan wata 'ya mace kad'au hannu Ka mareni? na shiga uku!". Ta katse shi cikin muryar kuka tare da k'ara fashewa da wani sabon kukan ta koma gefen gadon ta zauna baka Jin komai sai fitar sautin kukanta.

Shiru yayi qirjinsa na masa wani irin rada'd'i da zafi  wanda baisan na meye ba b'acin raine ko kukanta ko kuma kalmar karuwa  da zahra ta danganta yarinyar dashi ne , shiru yayi yana sauraron kukanta gashi  abunda yatsana kenan  a rayuwarsa  yaga mace na kuka ,sanin hakan yasa Zahra ta k'ara k'arfin kukanta, bud'e  idanunsa dake runtse  yayi , cikin wani irin zafi ya soma taku a hankali har ya k'arasa bakin gadon, zama yayi daga gefenta. "Look Zahra! Kiy...". Sake fashewa tayi da wani sabon kukan  "Ya Salam!  dan girman Allah kiyi shiru ki daina wannan kukan dan Allah"ya fad'a lokacin daya  Kai hannu yana d'an bubbuga kafad'arta, a hankali Zahra ta sulale ta shige jikinsa. "Baby  wacece wannan yarinyar daka mareni  akanta ? "tayi masa  tambayar tare da sauke  ajiyar zuciya ..

"Bakowa bace!". Ya furta hakan cikin ko'k'arinsa na kauda zancen dan jinta a jikinsa ba k'aramun tada mishi sha'awa tayi ba musamman yadda ta tura hannunta cikin k'irjinsa tana wasa da kan nipple's dinsa lumshe idanunsa

Please Login or Register in order to submit comment