You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
sai dai yaki nuna musu location saboda number bata shiga gbdy bare su samu location din da akayi amfani da wayar har suka hau babban titi .
dcp ya kira commissioner yana d'auka yace "sir layin nan bai shiga ba bare mu samu locacin din Inda suke amman zamu k'arasa 1829 plaza dake igando ko zamu dace a nan akayi amfani da layin yanzu dai zamu cigaba da Kiran layin har mu Isa ."Allah yasa ba fahimta yayi ya kashe wayar ba ? "Dan Allah kuyi aiki yadda ya kamata dan yarinyar ta kira cikin mawuyacin hali da alamun tana cikin tsaka me wuya, wannan wata dama ce me kyau da muka samu kada ku bari ta subuce mana "okay sir inshallahu zamuyi iyakacin k'ok'arinmu ".
Commissioner ya katse Kiran yana juyi akan kujera gashi dai shirin tafiya gida yake Kiran minister ya same shi Amman a yanzu ya zama dole ya fasa tafiya gida ya zauna zaman jiransu idan ta kama ya kwana ma a office zai yi ".
gudu motocinsu suke sosai akan titi tare da jiniya ,kowacce mota ta gansu sai ta kauce ta basu hanya ,irin gudun da sukayi yasa cikin kankanin lokaci suka k'araso 1829 suka faka motocinsu suka firfito cikin sauri wasu suka nufi babban get din plaza din , yayinda wasu suka tsaya abakin kofar motocinsu rike da bindugu suna mazurai kamar wasu zakuna ,mutane kuwa tuni suka fara bawa kafarsu iska kar tsautsayi ya rutsa dasu .
a hankali police suka kusa cikin plaza din ,bincike suka fara yi kafin daga baya suka bukaci ganawa da manager gurin , Kai tsaye aka Kai su Inda yake , tun kafin su fito da Id card dinsu ya fahimce su din su waye , nan take ya rikice yana kallonsu .Jimi'an tsaro ne suka nuna masa I'd card "akwai wani mai laifi daya shigo plaza dina a mintunan da suka gabanta ko zamu iya ganin cctv camera dinku ?muryarsa na rawa yace babu matsala yalla'bai ya juya ya soma lalu'bo daukar yau dan Daman a qunne yake , a hankali suke kallo har ya kawo zuwa sanda suka shigo babu wanda ya shigo me irin fuskar da suke nema tare da yarinyar dan haka suka juya cikin sauri suka shishiga motocinsu suka nufi wani branch din dake ikotun ."
Jaguwa na isowa gida yayi parking yana ƙoƙarin bud'e mota domin ya fito da sauri tanweer ta rike shi gam ajikinta "dan Allah kada ka sake shigar dani cikin gidan nan "ya waigo a natse sai dai a fusace yake kallota sai daya d'auki second biyar yana kallon sannan yace "wai meke damun tunaninki ne ?"me ya samu gidan nan da kike son barinsa bayan rayuwarki ake k'okarin karewa ?
Tayi shiru tana kallonsa da nazarin maganarsa kullum maganarsa kenan rayuwarta yake son karewa "ka fad'a min waye wanda yake son d'aukar rayuwata da har kake k'okarin karewa ? tayi masa tambayar jikinta na rawa tare da sheshekan kuka."ganin yadda ta rikice yasa ya kamo hannunta ya rike cikin nashi gam suna jin dumin juna "ki natsu zan fad'a miki amman ba yanzu ba "ni dai ka fad'a min ko waye shine samun kwanciyar hankalina da samun natsuwar zuciyata, Idan ma
ta kama zan hakura da gidanmu na cigaba da zama da Kai ,"ko Kuma ka siyo min sabon layi ka had'a min waya sannan ka fad'a min ko waye sai na fad'awa mahaifina a d'auki mataki akansa , wallahi nayi maka alkwarin bazan fad'awa kowa ba ."
Yayi d'an murmushin gefen baki wanda ya bayyana ainihin sirrin kyawun da Allah yayi masa "Ina ce kince zaki tona min asiri byn kin bar gidan nan ? "tayi saurin girgiza masa Kai alamun a'a "bazan yi ba na maka wannan alkwarin duk runtsi duk wuya bazan aikata hakan gareka ba muddin ka fad'a min ".
"kada ki damu idan kin shirya fad'awa duniya kiyi karki fasa , idan kin koma gida ki tara gbdy 'yan jaridan garin nan ki sheida musu cewar Adnan dan fashi ne abinda nayi Imani dashi Allah bazai basu nasara akaina ba , mahaifiyata tana tsaye a kaina da adduointa haka mutane da dama suna min addua , duk da Ina aikata zunubai Allah zai tsareni daga sharrin duk wani jami'n tsaron albarkancin adduar mahaifiya data mutanen kirki ."
shiru tayi tana kallonsa hawaye na gangaro mata cike da sanyin jiki ta zare hannuwanta dake cikin nasa ta soma k'okarin zare jikinta daga garesa ,yana kallonta tayi baya da kujeran da take zaune ta maida jikinta ta kwanta tana mai runtse idanunta , yatsun hannunta ya kamo bai san yadda akayi ba ya tura cikin bakinsa ya fara tsotsa , wani iri ta dinga ji a sansar jikinta kmr ana zarar ranta , tayi k'okari cirewa ya rike yatsun da karfi yana cigaba da tsotsa kamar ya samu sweet sai daya tsotsa son ranshi sannan ya cire bakinsa ya ciro hanky ya goge mata hancinta dake digar jini yana cewa "ki kwantar da hankalinki zan fad'a miki ko waye amman ba yau ba ". yana gama fad'ar haka ya sakar mata hannu ya bud'e murfin motar ya fito ya zagayo bangarenta da take ya bud'e mata ta fito jiki a sanyaye, ya d'auki ledar maganin da aka basu ta dubeshi fuska da hawaye .
bai tsaya bi ta kanta ba ya riko hannunta ta turje alamun bazata ba ya juyo ya watsa mata idanunshi fuskarsa a d'aure "karki min taurin kai " ya fada tare da sake juyawa suka shiga cikin gidan bakinsa d'auke da addua (bismillahi walajna
wa bismillahi kharajna wa'allahi rabana tawakkalna ) tana jinjinawa girman iliminsa, gashi tantiri gashi malami ta fad'a acikin ranta .
Kai tsaye d'akinta ya shiga daita ya kamota ya zaunar daita abakin gado ya janyo kujerar madubi ya zauna yana bin d'akin da Kallo duk ta hargitsa d'akin ko d'azu daya shigo yaso yayi magana yanayinta yasa ya share ya girgiza Kansa sannan ya fuskanceta ,baya jin dadin yadda take d'aga hankalinta akan gida ,
shi bashi da niyyar cutar daita , ko abinda ya faru daren shekaranjiya ma ba yin Kansa bane itace sila , tillastawarta ce ta janyo hakan ta faru ban cin haka babu abinda zai kai shi aikata zina daita.
"tan ...!
Ya kira sunanta cikin kasalalliyar muryarsa yana sake kamo hannunta tare da kafeta da tsumammun idanunshi masu kashe mata sansar jiki , d'ago idanunta tayi ta zuba masa tana sauraronsa tare da jin wani iri a sansar jikinta duk sanda zata kalleshi sai taji wannan yanayi wanda babu tantama na qunar da take masa ne . "wanda ya tura mu fashi gidanku bashi da hannun cikin zamanki tare damu , rikeki da nayi Kuma nayi amfani da maganar da mukayi dashi a karshen maganarmu cewa "yayi yana da wasu target akanki a dawo dake ya aiwatar da nufinsa wannan shine dalilin da yasa na rikeki ba dan raina na so ba ".
"Dan ranka na so dai ka rikeni idan ba haka ba meye aciki ? tayi maganar a matukar fusace " ka mayar dani Inda ka d'auko ko ka fad'i wanda ya turaku gidanmu kawai a wuce gurin , ya runtse idanunshi yana nazari wasu abubuwa akanta .
ta dubeshi idanunta cike da ruwan hawaye "adnan ka d'auke ni a daren nan ka mayardani gidanmu dukkanin alamun sun nuna min iyayena na cikin tsananin damuwar rashina da.... ...."
"na sani Kuma zan mayar dake amman ba yau ba ki bani lokaci wallahi zan mayar dake akwai binciken da nake da zarar na gama zamammu tare zai zama tarihi ".
ta matso kusa dashi sosai har gwiwowinsu na gogan juna "naji amman dan Allah ka sanar dani Wanda ya tura ku gidanmu fashi ?ya girgiza mata Kai sannan yace "idan ma kika ji ko waye ba lallai ki yarda ba, Killa Kuma ma kiji kin tsanani kanki sannan tabbas wasu rigingimu zasu faru saboda kusancin dake tsakanin mahaifinki da wanda ya bamu aikin ." ta kamo hannunsa ta rike gam cikin wani yanayi "cikin dangin dad dina ne ko na mum dina ke son ganin bayan iyayena da ni kaina ? ya girgiza mata Kai alamun "a'a"to sanar dani dan Allah zan barwa cikina bazan ta'ba fad'awa kowa ba ".
Shiru yayi yana nazari akan lamarin ya fad'a mata ne ko ya shareta "abinda yasani tabbas idan batun
ya fito ya sa'bawa dokarsu domin a aikinsu babu wannan tsarin ,duk runtsi duk wuya ba'a tonawa juna asiri tunda tun farko da wajewa ake tsara komai ba'a juyawa juna baya.
ta katse masa tunani ta hanyar cewa "kana ganin zan iya tona maka asiri ne ?" Allah na dai fad'a ne amman bazan iya aikata hakan ba. "na sani dan fad'awa soyayya ba abu ne me sauki ba da har zaki tona asirin masoyinki I know you can't do that to me tanweer bazaki iya fad'ar komai akaina ba saboda qaunar da kike min."
ta lumshe tsumammun idanunta na second biyu tare da jan tsaki acikin zuciyarta dan muddin tayi a fili balai zai mata a hankali ta bud'e idanunta akan kyakkyawar fuskarsa "ba wannan story din na tambayeka ba ,ka ajiye batun wani soyayya dan a yanzu babu ita acikin raina buqatata ka min bayani wanda yasakaka aikin bana son jan aji da salo tayi mgnr tana murgud'a masa k'aramin bakinta .yayi murmushin gefen baki yace "to da gaske zaki rufa min asiri agurin iyayenki ? da sauri tace "me zai hana in bukatar hakan ya taso ?"
"sannan Ina fatan zaki fahimceni ?" ta gyada masa alamun zata fahimcesa, shiru tayi tana jiran ya faiyace mata Komai kawai taga ya zare hannunsa ya mike tsaye tare da zura hannuwansa duka cikin aljihunsa , a hankali ya juya mata baya yayi taku zuwa daf da kofar bayinta ya tsaya tare da waigowa yace "ni zaki yaudara ko ? ta girgiza masa Kai alamun "a'a "karya kike tanweer yaudarata zakiyi dan zuciyata bata yarda dake ba duk da d'arurar soyayyata dake cikin kwayar idanunki da zuciyarki kina son na fad'a miki wanda ya tura mu fashi gidanku sai ku taru ke da jami'an tsaro ku cutar damu ko ?
yana rufe baki yaji ta rungumesa tsam ta bayansa tana cewa "wallahi kaji na rantse maka bazan sheidawa kowa ba ,bazan zamo me Saka hannu gurin cutar da kai ba ,ya juyo daita gabansa suka fuskanci juna "dame zaki gamsar dani bayan tun farko kice da bakinki kika fad'a min zaki tona min asiri ?" ta tsugunna gwiwowinta biyu a kasa ",ka yarda dani Adnan na rantse maka bazan aikata hakan ba ". ya tako a hankali ya tsugunna a gabanta "na sani bazaki fad'a ba amman ni ba mahaukaci bane da zan fad'a miki wanda ya tura mu a aiki gidanku , babu wannan ajandar acikin aikinmu ko gaban alqali za'a Kai d'aya daga cikinmu da wahala ya fad'a ,kada ki damu ki bar son jin komai gida ne dai zan kaiki a duk sanda wa'adi ya kai ya fad'a yana janyota jikinsa ya makaleta tare da Kai bakinsa daidai kunnenta "ki K'ara natsuwa da jin dumin jikina ."
Tayi shiru zuciyarta na quna da tuttukin bakinciki ,duk abinda take tana yi ne dan ya fad'a mata wanda ya bashi aikin amman shine zai rainawa kansa hankali yace ita ya rainawa ?" cike da matsanacin bakinciki fixge jikinta tace " kar Allah yasa ka fad'a kuma Allah ya Isa da rungumata da kayi ban yafe maka ba mugu kawai me zuciyar dutse duk irin rantsuwar dana yi maka bai sa ka yarda dani ba saboda muguwar zuciya irin taka ." cikin dariya ya sake janyota jikinsa sosai ya rungumeta tsam yana busa mata numfashinsa tare da cewa "kada ki damu da irin zuciyata dan babu abinda zai qareki dashi Allah ya Isa Kuma daman allah isashe ne ko baki ce ba , wayonki yayi matukar burgeni I love it keep it up yayi mata kiss a goshi sannan yace "zaki cigaba da zama da Adnan har zuwa sanda yaga damar maidake gidanku sannan kiyi k'okari ki rage wannan soyayyar da kike masa idan ma da hali ki cireta gbdy ya saketa ya koma jikin window ya tsaya yana kallon farfajiyar gidan kusan minti biyar yana tsaye sannan ya juyo "me zaki ce akawo miki kici ki sha magani ? babu abinda zanci ta fad'a a fusace tana dubansa hawaye na tsiyayowa akan quncinta "daman Kin saba kwana da yunwa idan shi kike ra'ayi fine ,I don't care ya nufi kofar fita daga d'akin ya barta cikin tsananin damuwa da sake shiga tashin hankali ."
Yana fita number minister ya fara nema kira uku yayi kafin a d'auka ,hajiya zainab ce ta dauka cikin sanyayyiyar murya tace" hello yana jin sautin muryar ya fahimci mahaifiyar tanweer ce dan bazai manta da muryar ba da irin kuka da kururuwan da tayi a daren da zai taho da tanweer muryarsa a dikile ya soma magana cikin Isa " Ina minister ?ta waiga a sukune ta Kalli Inda minister yake zaune aqasan tayis yayi tagumi da hannunsa d'aya cikin tsananin tashin hankali "wake magana ?ta tmby cike da faduwar gaba "babu buqatar sanin haka sai dai dalilin Kiran shine ki fad'awa mijinki idan yana kusa " cewar ya dakatar da kawalayen daya tura haushi gari dan nemammamu wato jami'an tsaro idan ba haka ba zai zama sanadin rasa rayuwar diyarsa tanweer ".
nan take jikin hjy zainab ya kama rawa hawayen dake makale a kwarnin idanunta suka sauka akan quncinta , a hankali ta soma karanta hasbinallahu wa ni'imal wakil tana cigaba da sauraransa "ki fad'a masa ya janye if not you'll lose your daughter ko Kuma musa ayi reping dinta mu yada a social media yana gama fad'ar haka yayi disconnecting din kira yana fesar da iska.
wani kuka hjy zainab ta fashe dashi ta zube kasa tana furta kalmar " inna lillahi wa inna ilaihi rajiun da sauri minister ya matso kusa daita dan tunda ta d'auki wayar tana kallonsa shima ya tattara hankalinsa da natsuwarsa gurinta a rud'e yake tambayarta "menene zainab me akace miki a wayar da'aka kira ?" dan girman Allah ka kira office din commissioner yanzu yanzu ka sheida masa a tsaida jami'an tsaron nan bana son na rasa tanweer ,bana son wani mummunar abu ya faru daita iya abinda ta fad'a kenan ta zube jikinsa tana sake fashewa da wani sabon kuka numfashinta na sama da kasa. kamota yayi ya rungumeta yana shafa bayanta"is okay zainab babu abinda zai samu tanweer dinmu da izinin allah lafiya zata dawo garemu . yayinda ita Kuwa hjy zainab babu abinda take cewa sai "ka kira commissioner ."
Can bangaren jami'n tsaro kuwa suna Isa 1829 plaza dake gaban isalo a matukar harzuke suka firfito suka shiga ciki kmr d'azu wasu suka tsaya a waje Wanda suka shiga suka fara tambayar manager gurin, Kai tsaye aka nuna musu Inda yake nan da nan suka fara aika masa tambayoyi akan mutane da suka shigo plaza din a wanni da suka gabata "ai mutane dayawa sun shigo a yau din nan yalla'bai "ko zaka iya gane fuskokin wanda da suka shigo ya fad'a tare da nuna masa hoton jaguwa ?" gsky bazan iya ba amman tunda ga hoto bari mu qunna cctv camera mu duba " take yayi rewarning cctv suka tsurawa tv din dake gurin kusa guda biyar idanunsu , idanun manager ne ya Kai kan motar jaguwa "yalla'bai ga wata mota nan ta tsaya a haraban plaza a awa biyu data gabata nan dukkaninsu suka bada attention dinsu suna duban motar suna sauraronsa " mutun d'aya ne ya fito daga cikin motar fuskarsa rufe da face mask nima Kuma a wannan lokacin na fita Kuma tabbas naga wannan motar mai number 2548 bayan ya shigo nima na dawo Ina kallonsa yana daukar dogayen riguna na mata haka kawai naji hankalina bai kwanta dashi ba idanuna na kanshi har sanda ya biya kudin kayan ya wuce duk yadda akayi wannan mutumin ne duk da fuskarsa bata bayyana ba kamar yadda hotonsa yake suna tsaka da sauraronsa kiran commissioner ya shigo wayar dcp, ya d'auka cikin sauri yana cewa "hello sir "kuyi maza ku dawo akwai matsala "matsala Kuma sir ?
"Eh babba kuwa domin rayuwar yarinyar na cikin hatsari idan aka cigaba da bibiyarsu ga dukkanin alamun akwai wanda yake yiwa hukuma zagon kasa". aikuwa yayi babban kuskure ya cuci alluma har ma da zaqaqarun yansanda masu k'okarin ganin an kawar da ta'addanci a kasa inji cewar dcp batare da bata lokaci ba dcp ya juya yana bawa yaransa umarni ."Tafiya kawai dcp yake baya ko gamin gabansa saboda takaici da bakinciki wai sai yaushe ne zasu yi nasara akan jaguwa ?sai yaushe zasu yi nasara akan shi Kawar dashi daga doron duniya da wannan tunani ya Isa gidansa.
Jaguwa ya dade tsaye a lambun gidansa byn ya gama waya da mahaifiyar tanweer yana shawagi agurin tare da tunani kala dabam dabam cikin haka wayarsa ta soma ringing ya d'auka ya manna a kunne ya tura hannunsa cikin aljihun wandonsa maganar minti biyar kacal sukayi ya katse Kiran ya cigaba da shawagi sai gasu anas kowannensu hannunsa rike da tabar wiwi yayinda anas ke rike da biyu ya mikawa jaguwa d'aya, ya amsa ya kai bakinsa ya fara zuka sannan gabad'ayansu suka samu guri suka zauna suna magana akan mata "ya kamata mu dan fita yau ko Kuma muyi invent dinsu zuwa gidan nan ?"ai rayuwa babu mace quntatawa ne kasamu mace lafiyiyayya Kuma me shaye shaye ka sauke gajiyarka akanta inji cewar jubi murmushi jabir yayi "wallahi kamar kuwa kasani mace me shaye shaye tafi dadin muamula ga juriya saboda bata haiyacinta haka dai sukayita hirarsu akan mata
yayinda jaguwa ya lula duniyar tunanin wanda tunanin kusan duk na tanweer ne .yana jin kamar ya shareta amman zuciyarsa ya kasa aiwatar da hakan ko babu komai tana bukatar kulawarsa tunda bata da lafiya kuma idan bata ci abinci ba taya za'a yi ta sha magungunanta ?
wannan tunanin yasa ya kira aliyu ya aika siyo mata abinci bayan kamar awa d'aya aliyu ya dawo hannunsa rike da farar leda ya amsa ya ajiye ya cigaba da zugar wiwi , sai da yayi mankas sannan ya mike ya nufi d'akinta bakinsa d'auke da sallama hannunsa rike da farar leda yayinda gbdy jikinsa ke warin wiwi hade da turaren jikinsa .
shigowarsa ke da wuya d'akin ma ya kaure da warin wiwi dana turarensa wani irin haushi ya kamata idan akwai abinda ta tsana shine warin wiwi ko ta'ba , kallo d'aya tayi masa ta d'auke kanta ta mayar wani gefe tana wasa da yatsun hannunta .
Ya ajiye ledar hannunsa yana cewa "ga abinci nan kice ki sha magani kin ma kuwa yi sallah isha'i ? "ban yi ba Kuma bazan yi ba, wallahi idan ka sake min magana akan sallah sai na kashe kaina "Allah ya bada sa'ar tafiya dadin abun idan kin kashe kanki bazaki rataya a wuyan Adnan ba kice zaki mutu kafura ".
"Kai ne dai kafuri Kuma Kaine zaka mutu a wannan rayuwar da kake. "are you out of your sense ? ya fad'a a fusace " ni kike fad'awa haka ?" shiru tayi tana dubansa kafin idanunta ya kawo ruwa "amman Kai me yasa kullum sai kayi min magana akan sallah kamar wata kafura ? "Alama na gani na bakin son yinta " .
shiru ta sake yi kamar me nazari numfashi ya fesar ya juya zai fita
yaji sautin muryarta a raunane "kazo ka d'auke banzar abincinka dan ba zanci ba" kad'a kafad'unsa yayi yace "daidai kenan Ina son haka ,Kinga rashin cin abincinki ko rashin walwarki bazata dameni ba saboda bana sonki bakya cikin rayuwata kisan Allah ko nemanki nayi na rasa bazan damu ba dan bayan mahaifiyata da kannena ban san ciwo kowa ba, bayan darajan kannena dana sani ban San darajan kowace mace ba Kinga Kenan Kema kina cikin matan da bana ganin darajansu ,yana gama fad'ar haka ya fice daga daki ."Kuka ta rushe dashi tana Kiran tashi uku sai da tayi me isarta sannan ta janyo ledar daya ajiye mata dan yunwa take ji sosai , taci kad'an ta bar sauran ta shiga bayi tayi wanka ta fito ta sha magani tayi sallah ta kwanta lamo akan bed tana tunanin iyayenta, "Allah sarki dadynta muryarsa ta nuna yana cikin damuwa " dad dinta da bai iya cikakken awa d'aya ba tare daita ba ,ko zuwanta turai karatu baya jimawa batare daya ganta ba, kullum Kuma cikin video call suke ,ko ya dad dinta zai ji idan ya ga ta dawo garesa ? tasan rungumeta zai yi a karshe ya d'auketa sama yayita juyi daita yana cewa "my tan ta dawo I really miss you my tanweer wasu hawaye masu zafi ne suka biyo gefe da gefen idanunta.
"Ko waye wanda ya tura musu yan fashi ?waye wannan ? ta tambayi kanta "waye cikin family dinmu ?dangin mumcy dina ne ko dangin dad dina ne ?"dangin dad dina basa zaune a lagos tunda shi din haifafen garin Kaduna ne, mumcy dina Kuma yar d'aura ce ",ai daga koina mugu zai iya idar da nufinsa ya farmaki rayuwarka,Allah sarki mugu bashi da kama suna tare dashi Amman basu san cewar shi din makiyinsu bane "shiru tayi tana sake zurfafa tunaninta ,babu abinda ya shiga
yawo acikin kwakwaluwarta kamar hirarsu jaguwa a wacan ranar data san dan fashi ne "tabbas taji sun ambaci sunan Alhj tahir a hirarsu .
a lokacin ta zurfafa tunanin domin sanin me sunan a karshe zuciyarta ta tsayu akan mahaifin Ib shi kad'ai tasani me wannan sunan, tashi tayi zaune ta zauna "tabbas shine me sunan Ibrahim Tahir ta furta a fili "Kai ba dai shi ba bazai ta'ba aikatawa mahaifinta haka ba sai dai idan suna ne ya zamo daya , to Kuma ai maganar Adnan ta nuna Wanda ya turasu na tare dasu to meye gaskiyar lamari ? take zuciyarta ta shiga wasi wasi wata zuciyar tace shine wata zuciyarta ta karyata hakan .
wasu hawaye ne masu zafi suka
zubo akan kuncinta " tana bukatar ganin iyayenta tana son ganin dad dinta da mum dinta tana bukatar Jin dumin jikinsu kamar yadda ta saba dan girmanta bai hanata kwanciya ajikinsu ba she really miss them .".
Daren ranar kasa runtsawa tayi jikinta yayi zafi rau kamar garwashin wuta sai faman juyi kawai take akan mamaken bed din da take kwance tana tunanin mafuta kwakwaluwarta ta sake lula kogin tunani mai zurfi akan yadda zata bar gidan ta kowani hali dan dole tasan yadda zatayi ta bar gidan tun bai canza ra'ayinsa akanta ba ya fara kusantarta.
da kyar bacci barawo ya saceta washegari da safe bai shigo yaga halin da take ciki ba yayita lamuran gabansa ita Kuma hakan ya bata damar tsara yadda zata bar gidan kota halin balai, ta fito sanye da doguwar riga baka har kasa tayi rolling kanta da mayafin rigar Kai tsaye ta wucesu a falo zaune tare da abokansa har ta fito haraban gidan
ya fito ya biyota yana cewa " ke Ina zaki kika wani wuce mutane dan iskanci ?
"Bansani ba Kuma karka sake tambayata Inda zani dan ni ba diyarka bace sannan ba abar ikonka bace da zaka wani tsareni da banzar ta....." shiiiii wuce ki koma ciki" "bazan koma ba gidan nan zan bari Kuma a yanzu ta fad'a tana cigaba da tafiya taku uku yayi ya riko tsintsiyar hannunta "muje babu Inda zaki sai wadin zamanki a gidan nan ya Kai .
ta juyo a fusace ta sanya kwayar idanunta cikin nashi cike da balai tace "Kai waye da zaka hanani tafiya?.
"ni Adnan amad ".ya bata amsa yana kallon cikin idanunta fuskarsa a had'e babu alamun wasa .
"wallahi baka Isa ba who the hell are you? duk da me gadi gidan nan abun ikonka ne zanyi duk yadda zanyi na bar gidan nan Kuma a yau .
jaguwa bai saurarata ba ya jingina jikinsa ajikin motarsa ya tsura mata Ido yaga iya gudun ruwanta . tanweer ta Isa Inda taga makulan motoci rataye ajikin bangon rufar motaci ta d'auki ta camery ta rike gam zata bude moto tuni yaransa suka tareta bisa umarnin jaguwa da yayi musu umarni
Book Chapters
Chapter 20
Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67