Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke zaune bisa lallausan carpet ɗin falon gab da ƙafafun Abie ɗinta, yayinda hankalin Abie kacokan ke akansa da alama ma bai san da shigowarta ba.
     Sosai ƙirjinta ya harba dan ko kusa batai zaton ganinsa anan ɗin ba, tunma data duro gidan addu'arta shine karma su haɗu kwata-kwata. Zancen Aysha na ɗazun ya tabbatar mata yana ƙasar, hakan kuma na nufin dole su haɗu koda ba yau ba. Amma batai tsammanin yanzu ba. Kamar yanda tai masa kallo ɗaya ta ɓata fuska da gyara yanayinta haka shima yay mata kallo guda duk murmushin fuskarsa ya ɓace, har wani yamutse fuska yay tamkar yaci karo da tutun safiya na cikin sanyi......
      “Mamanmu ƙaraso mana”.
Daddy ya katsesu a tare dan duk yaga irin kallon tsanar da sukaima juna. Shikam ya rasa wannan ƙiyayya ta Anam da Shareff bayan kowa yasan irin dunbin son daya nuna mata tana jinjira har zuwa sanda ya wuce Indonesia, amma a yanzu baka ganin komai sai ƙin juna a tsakaninsu tamkar basu taɓa sanin juna ba. Yitai kamar bata gansa ba taje ta zauna kusa da ƙafafun Daddy, cikin marairaice fuska tace, “Daddy ina jin yunwa sosai”.
       “Ya salam mamana garin yaya haka? duk abincin dake gidan nan ga wasuma ko taɓawa ba'ai ba kuma dan k kawai aka shirya su”.
      Kanta ta girgiza kamar zatai kuka. “Daddy bana son su ban iya ci ba ai”.
          “Sai ki fara koya yanzu ai”.
Abie ya faɗa kafinma su Abba suce wani abu yana hararar Anam duk da kuwa bai kai zuci ba, dan ransa cike yake da damuwar zamanta da yunwar tunda yasan da gasken ba iya cin tai ba.
     Daddy yace, “A'a ba'ayi hakaba ai. Tunda tace bata iyaba da gaske bata iya ɗinba kuma bataso. A bita a sannu zata koya ci insha ALLAH tunda tana nan. Shareff ka ɗauketa kuje a sama mata abinci dan kaine kafi kowa sanin inda kake ciyo abinda ta iya ci”.
       Tamkar saukar aradu haka Shareff yaji saukar zancen Daddy a kansa. Ya ɗago da sauri yana duban mahaifin nasa tamkar a razane. Harara Daddy ya zuba masa. “Lafiya ka tsareni da idanu halan?”.
       Ƙasa ya risinar da idanunsa batare da yace komai ba. Sai dai fuskar ta sake rinewa tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa.
          “Daddy ni dai nama ƙoshi kawai zansha ko tea to”. Anam da itama ta haɗe fuska tana hararsa ƙasa-ƙasa ta faɗa baki a tunzure”.
      Maimakon Daddy ya amsa mata sai ya kira sunansa a tsawace. “Shareff Are you daft?”. Kansa ya girgiza kawai yana miƙewa, idonsa a ƙasa yace, “Zanje na sayo kawai.....”
      “Da ita zakaje ta zaɓa abinda take so”.
     Dady yay saurin faɗa cikin katse masa hanzari. Wani irin rumtse ido yay da ƙarfi da cije lip ɗinsa na ƙasa uwa zai huda shi. Sai dai baice komai ba ya kama hanyar fita. “Basai kaje ɗakko key ɗin mota ba zo ka dauka wannan”. Abbah ya katsesa dan ya tabbatar Mommy ta gansa zata hana itama. Nanma baice komai ba ya dawo ya amshi key ɗin hanun Abban.
       “Maza bishi mamana kuje, ki kuma zaɓo duk abinda kike so kinji”.
    Kanta ta ɗagama Daddy tana murmushi, dan ganin yanda Shareff ɗin keyi yasata jin zama ta bisa kodan ta baƙanta ransa...
        Kasancewar ya fita zafin nama sanda ta iso harabar gidan harya tada motar yana reverse, maimakon ya faka saitin inda take ya ɗauketa sai ya harba motar har bakin gate. Anam tai ƙwafa da taɓe baki, cikin kunƙuni da gurɓatacciyar hausarta tace, “Duk baƙin halin da kake sai naje saika mace idan kasha zuciyanka mugu mai baƙin rai”.
       Oho baima san tanai ba. Cike da wani takun isa tazo ta buɗe murfin ta shiga kanta a gefe. Bawani duban kirki yay mataba a ciki, dan haka bai gama tantance kayan jikinta ba. Tana shiga ya fisga motar da ƙarfi har yanayi kamar zai taka mai-gadi ma, sai da yay tsalle gefe ya bashi hanya cike da mamakin mike damunsa. Dan shi shaidane Shareff mutum ne daya san mutuncin mutane, ko yaya kake a ƙasansa bai yarda ya ƙasƙantaka ba balle wulaƙantaka. Yayi imani da ALLAH ransa a ɓace yake bada son rai yay masa haka ba.
           
      ★ Sosai gidan abincin ya haɗu, ya samu waje yay parking batare da yace da ita komai ba ya fice a motar. Baki taɗan taɓe kaɗan da yima ƙeyyarsa gwalo, sai kuma ta zabura ta buɗe motar tamkar wadda ta tuna wani abu. Yana gab da shiga ta cimmasa saboda da ɗan gudu-gudu take tafiya. Cak ya tsaya, dan haka itama ta tsaya kanta a ƙasa dan duk fitsararta a bayan idone kawai dama.
       “Idan kika bari ƙafarki ta shiga wajen nan sai na ɓallata”. Da yaren malay yay maganar, dan haka komai ya shiga kunnenta tsaf. Baki ta tura fuska a kumbure idonta na tara ƙwalla harya shige tana kallon bayansa ta ƙasan ido. Maimakon ta koma mota sai ta nema waje a gefe tai tsaye tana kallon mutanen dake. a ciki ta cikin glass da aka ƙawata wajen.....
       “Hallo....”
  Aka faɗa a bayanta cikin wani irin sallon daya tilastata ɗago idanunta masu haske, matashin saurayine ƙyaƙyƙyawa fari tas. Sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar karɓarsa ga wani ƙamshi na musamman a tare da shi. A hankali ta janye idanun nata ganin yanda ya tsareta da idanunsa birkitattu. Gefen data maida fuskar ya sake dawowa yana gyaran murya, ta sake ɗauke kanta gefe....
      “Dan ALLAH ki kulani ƙyaƙyƙyawa ”. Ya faɗa cikin marairaicewa da haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo. Baki taɗan taɓe gefe tana yamutsa fuska da kai hannu ta gyara glass ɗin idonta dake ƙara fiddo ƙyawunta duk da tana sakawane badan gayu ba, kamar bazatace komaiba sai kuma dai ta tanka masa saboda ALLAH daya haɗata da shi. “Ka fara koyan sallama tukunna kamar zaifi bature”. Kansa ya dafe, cike da jimami yace, “Am sorry Assalamu alaiki ƙyaƙyƙyawa”. Nan ɗin ma bata amsaba sai da tasha masa ƙamshi tana wani ɗauke kai. “Wa'alaikassalam. kuma ni ba sunana ƙyaƙyƙyawa ba”. “Tabbas sunan shine ya dace dake, sai dai dazanji na yankan zanfi yin farin ciki”. Banza ta masa har kusan minti ɗaya, ganin yana neman matsowa jikinta tai saurin ɗagowa a masife......
       A dai-dai nan Shareff ya fito daga wajen hanunsa ɗaukeda ledoji masu tambarin wajen abincin. Duk da idonsa a kansu ya fara sauka sanda yake buɗe ƙofar sai ya ɗauke tamkar bai gansunba. Sai dai ya sake tsuke fuska. Yazo zai giftasu a fisge yace, “Second ɗaya kika ƙara a wajen nan jikinki sai ya faɗa miki”. Daga ita har saurayin da sauri suka maida dubansu garesa dan ita bama ta lura da shi ba da farko. Ko kaɗan bazaka taɓa cewa shine yay maganar ba. Tuno dukan da sukaci ita da Aysha randa sukaje birthday party ya sata zabura da sauri tabi bayansa bakinta a tunzure tana hararar bayansa, da sauri shima saurayin ya take mata baya. Tana ƙoƙarin rufe murfin motar ya riƙe da hanzari..........✍
      


KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)
BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR
ZENITH BANK
2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽
[10/3, 10:47 AM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_04_*


..........Kallon juna sukai cikin ido, tai saurin janye nata saboda wani irin harbawa da ƙirjinta yayi......
     “Please Beauty ko details ɗinki ki bani mana”. Saurayin ya faɗa a marairaice. Ai kafimma ta bashi amsa mai gayya mai aiki ya fisgi motar da ƙarfi. Da sauri saurayin ya saki murfin yana mai yin tsalle gefe dan saura kaɗan ya takashi. Sosai yanzu kam Anam ta firgita, dan har hannunsa ta riƙo batare data sani ba. Tureta yay a jikinsa tare da mika hannu ya rufo ƙofar gefen da take ɗin. Sai kawai ta fashe masa da kuka tana kiran sunan Mamie da Abie. Bai nuna yama san tanaiba, saima hankalinsa daya maida ga motar dake bin bayansu, sai da suka hau titi sosai hasken solar ya bashi damar ganin fuskar guy ɗin da suka baro ne. Lip ɗinsa ya ciza da ƙarfi yana wani fici-fici da idanunsa, sai ya koma tafiya a slow-slow harya zam saurayin ya ɗan gota su. Gefen titi ya gangara, sai da yaga saurayin na ƙoƙarin dai-daita nasa gudun danya sauka gefe titi shima saboda ganin sun tsaya sai kawai yay warming motar da wani irin karsashi ya sake harbata saman titi tamkar shikaɗaine a kansa. Tabbas da ace akwai ƙasa babu abinda zai hanashi bulama saurayin ita.
       Wani irin duka saurayin ya kaima steering ɗin a ƙulle da kufcewar damar daya samu. Ya kife kansa yana furzar da huci mai zafin gaske, dan harga ALLAH yarinyar ta matuƙar tafiya da dukkan imaninsa.

        Kamar yanda ya fita a fusace haka ya dawo a fusace, ko parking bai gama daidaitawaba da ƙyau ta ɓalle murfin motar ta fice da sauri. Wani irin mugun kallo yabi bayanta da shi, sai kuma ya janye yanayin ƙwafa ya kashe motar ya fito. Zaune ya sameta kusa da Abbah tana zuba surutu, dan har yanzu suna a falon suna hira. Sosai takaici ya riƙe masa maƙoshi, ya harareta yana ɗauke kai da zube ledojin hanunsa gabanta. Fuskarta ɗauke da murmushi kamar ba itace ta gama kuka a hanyaba yanzu tace, “Jazakallahu khairan Yaya Shareff”. Ta ƙare maganar da masa gwalo yanda su Abba basu luraba sai shi.
         Yi yay tamkar baima gantaba duk da tsaurin idonta na bashi mamaki, sosai ƙanensa ke shakkarsa a gidan, amma sam babu irin wannan tsoron da yake gani a idon ƙanensa tattare da ita. Kai tsaye take abunta garesa, abunda ya fuskanta dukane kawai bata so, dan tun dukan da ya taɓa mata ita da Aysha ta shiga hankalinta a lokacin har tana wasan ɓuya da shi. Sallama yayma su Abie dake saka masa albarka ya fita fuskarsa ɗauke da murmushin daya saka Anam sakin baki tana kallonsa da mamaki. Dan inba Abie ɗin ba da wahala kaga murmushi a fuskarsa, kullum fuska a ɗaure kamar ɗan raka gawa....

         Washe gari da ƙyar Aysha ta iya tashinta danta shirya. Haka tai wanka tanata mitar ita barci bai ishetaba. Shiri tai cikin wando da riga, sai dai anan babu maganar fita a haka duk da  zafi da ranar da akeyi a Nigeria, dole ta ɗaura abaya, Sosai tayi ƙyau kamar ka saceta ka gudu. ɓata fuska taketa faman yi dan bada son ranta tasa abayar ba, sai dai yanda Mamie ta gargaɗeta ta dingayi tunda tasan kayan nata duk ba irin na sawar Nigeria ba ne. Shiyyasa ta zubo mata abayoyi kusan goma tanata mita bata kulata ba. Kasancewar akwai sanyin safiya sai bata damu da saka abayar ba sosai.
       Sashen Mommy suka nufa ita da Aysha, sai dai daka kalleta kasan ba'a san ranta bane. To amma kodan Aysha da kunya tace bazataje ba. Mai aiki kawai suka samu a falon tanata aikin gyarawa, suka gaisa Anam na amsasu cike da fara'a, dan haka kawai ita dai Ladi ke birgeta. Bedroom ɗin Mommy suka nufa daga nan, bayan sallama aka basu iznin shiga. Zaune suka sameta a kujerar mirror tana murza ɗauri, ganin aysha ta rissina tana gaisheta itama saita ɗan rissina batare data yarda sun haɗa ido ba. Bata amsa na Anam ɗin ba, sai Aysha data watsama harara... “A ina kika kwana?”.
      “A sashen Mom ne”.
Aysha ta bata amsa cikin ɗari-ɗari dan tasan faɗa zata sha. Aiko kamar jira Mom ta rufeta da faɗa, ta inda take shiga batanan take fitaba. Itadai Aysha haƙuri kawai take bata. A tsawace tace. “Ɓacemin da gani shashasha da bata san ciwon kanta ba”.. Kafinma aysha tai yunƙurin fitowa tuni Anam tai waje ranta fal ƙarin mamakin masifar Mommy ɗin...
      Da sauri tai baya jin suna neman yin karo da mutum. Ta tura baki gaba tare da ɗan matsawa gefe saboda hararar da yake watsa mata. Yana ƙoƙarin raɓata da nufin wucewarsa tai tunanin bugeta zaiyi, kamar ƙiftawar ido yaga ta zura da gudu ta fice. Idanunsa ya ɗan lumshe tare da girgiza kansa kawai. Anan ɗin ma yana ƙoƙarin shiga ɗakin Mommy Aysha ta fito tana sharar hawaye, rissinawa tai ta gaishesa, maimakon amsa mata sai ya jeho mata tambaya idonsa kafe a kanta, “Mike damunki?”.
     Kanta ta girgiza masa. “Ba komai Yaya Mom ce, dan naje sashen Mom na kwana shine taketa faman faɗa, ni kuma saboda naga Anam ne tunda nasan idan mukazo nan bazata barta ta kwana ba”. Shiru yay yana cigaba da kallonta kawai, batare da yace komaiba kuma sai ya raɓata ya wuce ɗakin Mommy ɗin.
         Anam kam sai da ta tabbatar tabar sashen sannan ta ƙara kumbura baki, sashen Gwaggo ma da tun jiya batako kallaba sai da Abie ya korata sannan ta tafi fuska a haɗe kamar zatai kuka. Bata son kakar tasu dan itama tasan ba sonta take ba. Koda ta shigo sashen tsohuwar a ciccije take. Tamkar bama tasan Anam ɗin ba take kallonta, hakan yasa itama Anam ɗin tsumewa tai kamar bama wajenta tazo ba. Cikin ƙunar rai Gwaggo ta ture ƙaton kofin shayin da take sha gefe tana kallon Anam cike da tsana,
        “Fitsararriya cokalin banza. K ko kunyar kanki bakijiba sai yau kike zuwa gaisheni? Da yake baki da mutunci. to in bakizoba k ai ubanki shi yazo dan uwarki”.
   Shiru tai taƙi cewa komai, hakan sai ya sake tunzura Gwaggo ta fara bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba. Ko motsi Anam bataiba ballema tai mata gaisuwar da akace tazo tayi, sai da ta tabbatar mintunan da Abie bazai zargi komai ba sun cika sannan ta gaida Gwaggo dake yayyafa ruwan bala'i da zage mata iyaye tai ficewarta batare da ta jira amsa ba. Biyota Gwaggo tayi tana ƙwala mata kira.
      “Zuwairah!! Zuwairah!! yanzu nan ni kikema wannan ɗibar albarkan? To ko ubanki ai bai isaba, ke ko kakarki ma data haifi uban naki balle ke yarin....”
      “Ki cinye kanki fitinanniyar tsohuwa”. Anam ta faɗa a hankali tana ƙara sauri dan ko muryarta bata buƙatar ji. Taji daɗin samun Abie harya shiga mota, dan haka ta buɗe wuf ta shige duk da bataji daɗin yin tafiyar da wanda ta gani zai jasu ba. Sai da suka fita a gidan gaba ɗaya Abie daya lura bata gaida Shareff ɗin ba ya dubeta ta mirror.....
      “Anam!”.
“Na'am Abie ”.
   “Kin gaida Yayanki kuwa?”.
Ido suka haɗa da shi ta mirror, ita ta fara ɗauke nata idon ganin kallon banzar daya jefa mata. “Abie na gaishesa tun ɗazun ma ai da muka haɗu a sashen Mommy”. Idanunsa da basu gama bajewar kumburin barci ba ya sake ɗagowa ya dubeta. Itako ta ɗauke kanta cike da basarwa. Abie kam daya yarda sai kawai yay murmushi da maida hankalinsa ga lap-top ɗin dake a cinyarsa yana dubawa, ta Shareff ɗince yake nuna masa ayyukan company duk da dama can komai za'ayi yana sanar masa. Sai dai a kullum cikin ƙara bashi wuƙa da nama yake da nuna masa duk yanda yayi dai-dai ne kawai. Koda suka iso inda zatai daidaita komai daya shafi hidimar ƙasar nata bata yarda tako kalla Ya Shareff ba, shima bai shiga sabgartaba dan koba komai yana jin nauyin Abie sannan shi sam baya wasa da yara dama can, itacema kawai za'ace ta ciri tuta a wajensa tana ƙarama.
     Komai da taimakonsa shi da Abie ya kammalu, basu sami nutsuwa ba sai kusan azhar. Maimakon gida sai suka wuce company. Tunda akai
Companyn Anam batazo Nigeria ba, dan haka ta ɗan nutsu a kallon tsarin wajen da yanda ma'aikata keta kaikawo na daidaita kansu tun shigowar motar tasa. Koda suka fitoma sai gaisuwa ake miƙa musu cike da girmamawa da mutuntawa har suka isa katafare kuma haɗaɗɗen office da yaji komai na more rayuwa da saka nutsuwa ga mazaunin cikinta.  Abayar jikinta ta shiga ƙoƙarin cirewa. “Wayyo Abie zafi”.
      Yanda tai maganar ya sashi ɗan juyowa ya dubeta, ai da sauri ya ɗauke kansa ganin kayan dake a jikinta. Wando ne dayay matuƙar fidda surar jikinta da ƴar riga da itama bata ɓoye komai ba. Sun mata ƙyau sosai kuma dai-dai da halittarta ta masu ƙaramin jiki. Har veil ɗin data naɗa bata bari ba sai da ta yaye, ɗaurarren gashinta da yasha gyara ya bayyana, sai dai tuna gargaɗin Mamie yasata warware veil ɗin duk da ba wani girmane da shiba sosai taɗan yafa tana duban sashen da yake....
       “Yaya Shareff Please kasa ac zafi”. Tayi maganar ne tamkar zata fasa kuka, dan da gaske zafine ya taso mata lokaci guda, har wani dimm kanta ke mata. Ta ƙasan ido ya harareta, sai dai baice komaiba ya ɗauka remote ɗin ac dake a desk ɗin office ɗin nasa ya kunna ɗin. Ajiyar zuciya ta sauke cike da jin daɗin jin yanda sanyin ya wani buso mata da faɗin, “Alhmdllhi, Abie ALLAH da kamar ana dafamin fatar jikina fa”.
     Ƴar dariya Abie yay yana mai girgiza kansa da kallon Shareff dake ƙoƙarin buɗe wajen da yake gudanar da duk ayyukansa na zane. Babu mai shiga wajen sai shi kaɗai, sai ko Fharhan da Khaleel da yakan bama dama a wasu lokutan su kuma Engineers ne, dan company ɗin nasu aikinsa kenan, mai buƙatar zane amasa, idan da gini duk a haɗa, kai dai kawai ka ajiye kuɗi ne kaga biyan buƙata.
      “Babana kaji fa wani shirme, dama zafi na dafa fata ne?”.
       Murmushi ya ɗanyi cikin sanyin muryarsa da shafa kansa yace, “Abie akwai zafinne ai”.
     “Oh ka goya bayanta kenan dai kawai”.
            Murmushi ya sake saki mai faɗi fiye dana ɗazun. Sai dai baice komaiba, saima ɗan hararan Anam data saki baki tana kallonsa ganin murmushi a fuskarsa yayi. Itako ko gezau kallonsa take kamar ta samu hoton bango. Fuska ya ɗan tsuke da ɗauke kansa daga saitinta. Itama sai ta janye tana taɓe baki.
       Tare da Abie suka shiga, yayinda gaba ɗaya hankalin Anam ke ga littafin data ɗauka mai tambarin company ɗin nasu da alama samples ɗin ayyukan sune a wajen. Koda taji shigewar tasu bata maida hankali kansu ba, ta jima tana kalle-kalle, wasu su birgeta wasu ta taɓe baki harta fara hamma. Sai kawai ta zame ta kwanta a kujerar.........✍


KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)
BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR
ZENITH BANK
2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽
[10/4, 1:29 AM] Zeenaran🫶🏻: *_Typing📲_*




*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_Ƙarshen free page_*


*_05_*


...........Sun jima a ciki yana nunama Abie abubuwa, yanda yaketa faman bayani da murmushi saika rantse bashi baneba. Dan har dariya sukeyi tare da Abie. Kiran sallar la'asar ne ya fiddosu, hakan yayi dai-dai da shigowar ɗaya daga cikin ma'aikata office ɗin, sannan kuma dai-dai da farkawar Anam data sha barci hankali kwance sanyin ac ya gama ratsata.
        Shigowar ma'aikacin mai suna Abeed tazo masa a bazata, dan hankalinsa gaba ɗaya nakan system ɗin gabansa, sai sallamarsa da buɗe ƙofa ne a lokaci guda suka shiga kunnensa. Da sauri ya ɗago idanunsa batare daya amsa sallamar Abeed ɗin ba ya kai dubansa gareta. Anam da bata san mike faruwaba duk da itama taji sallamar tai yunƙurin miƙewa tana laluben veil ɗinta da nufin ɗan lulluɓama jikinta. Abie ya riga ya shige toilet ɗin cikin office ɗin ɗaura alwala tunkan sallamar Abeed....
       “You are vary stupid!! Zaka shigo min kai tsaye”.
A yanda yayma Abeed tsawar da jefa mata rigar suit ɗinsa dake a jikin hanger ba shi Abeed ɗin ba hatta ita sai da ta zabura. Da sauri ta ɗane kujerar baki ɗaya ta ƙudindune kanta dan sam bata ƙaunar tsawa a rayuwarta. Cikin rufewar ido da manta Abie na'a office ɗin ya sake dakama Abeed tsawa da cigaba da masa masifa. Shi dai yay ƙasa da kansa dan bai san laifinsa ba anan har yanzu, tunda ya san ya yi sallama ya kuma yi knocking....
        “Get out!!”.
Ya sake faɗa a tsawace. Da sauri Abeed yay baya da rufe ƙofar. A fusace ya maida dubansa ga Anam da ke leƙosu ta cikin rigarsa. Ya watsa mata wata uwar harara, cikin gargaɗi mai kaushi,
      “Idan kika ƙara fitowa da wannan ƴan iskan kayan saina kashe fuskarki da marukan da bazata ganuba. Stupid girl! An faɗa miki nan muna buƙatar sune”.
    Baki ta tura gaba duk da ta mugun tsorata da yanayinsa. “To ni Yaya MM wannan duk sune kayana ai, kuma ni su na iya saw.......”
    Ganin ya yunƙuro zai tashi ta miƙe da sauri ta koma bayan kujera fuska a kwaɓe. Ƙwafa yay da sake watsa mata harara. Abie dake tsaye da ga bakin ƙofa yana kallonsu tun ɗazun basu lura da shi ba yay murmushi, domin kuwa wasu abubuwa masu ban mamaki ya hango a cikin ƙwayar idon ɗan nasa, ya girgiza kai kawai da ƙarasowa ciki. Sai lokacin Shareff ya lura da shi. Ƙasa yay da kansa dan shi gaba ɗaya yama manta Abie na'a office ɗin. Miƙewa yay sum-sum ya nufi toilet batare da ya yarda sun haɗa ido da Abie ba. Shima baice masa komai ba sai binsa da yay da kallo kawai. Anam dake a laɓe sai da taga ya shige sannan ta fito, cikin taɓe fuska ta ƙaraso inda Abie yake tana faɗin,
     “Uhhm Abie ALLAH Yaya Shareff baida kirki, yanama staff ɗinsa ihu bai masa komaiba kuma”.
    Nanma murmushi kawai Abie yay baice komai ba. Zata ƙara magana Ya Shareff ɗin ya fito tai saurin komawa bayan Abie ta ɓuya. Sai dai hakan bai hanata ganin hararar daya watso mata ba.

★★★★★

         Washe gari su Abie suka wayi gari da shirin kai kuɗin auren Ya Shareff, wanda dama yana ɗaya daga cikin dalilinsa na zuwa Nigeria, dan data Anam ne kawai turota zaiyi tunda yasan akwai mai iya mata komai ai. Ita dai Anam bata san mike faruwaba ma, dan ta jima bata tashi a barcin safe ba kasancewar daren jiya tunda aka ɗauke wuta ta kasa komawa barci saboda zafi, duk da kuwa Mom ta kawo mata fan ta kunna

2 Comments On BABU SO
avatar
aisha-6-7-7

5 months ago

Reply

Inason littafinnan sosai

avatar
aisha-6-7-7

5 months ago

Reply

Inason littafinnan sosai

Please Login or Register in order to submit comment